Kudirar Allah Hausa Novel Complete
K’UDIRAR ALLAH.
Page. 1
NAZEEFAH SABO NASHE
08033748387.
******
Idanunsa ya Lumshe a hankali Bayan ya gama kallon fuskarta da take d’auke da Tsananin farin ciki, da alama sak’on da mahaifinta ya bayar ta isar masa shine abinda ya saka ta tarin farin ciki da annashuwa.
Bata sani ba shi sak’on yazo masa a hagunce da ta ta fassarar madadin farin ciki kwatankwacin nata, nasa hankalin tashi ya yi ya kuma shiga irin wancan yanayin da yake riskar kansa a duk sanda budurwa zata gaya masa sak’on mahaifinta ya ce ya turo. Ya bu’de tattausan idanunsa masu tsananin kyau da haiba ya zuba mata su, k’walla ce kwance a saman idanun wanda k’arfin zuciya da taurin rai yasa ya kasa sakin su su zubo. Namijin gaske ne da yake iya b’oye rauni da gazawar zuciyarsa a lokuta da dama, duk da matsalar da yake ciki ya ci
A koka mata koda kuwa kuka ne mai kuwa da kururuwa. K’addarace mai girman gaske take watangaririya da rayuwarsa, irin k’addarar da kai tsaye mutum zai ce dama Allah bai haliccesaba matuk’ar bai jajirce akan doron Imaninsa ba, da sanin cewa Allahn ne dai shine yake jarrabarsa don ya auna nauyin mizanin sa. Ya gani shin bawansa zai iya yarda da k’addarar har ma ya rungumeta a yarda ta zo masa. Hawayen da Khairi ta gani cikin idanunsa su suka k’arya mata gwiwa har nata farin cikin ya zagwanye ya bi iska. Cikin mabayyanin tashin hankali ta ce “Me ya faru Hubby? Kada dai maganar Abba ce ta b’ata maka rai baka shirya aurena bane?” Ya girgiza kai yana k’ok’arin togace tashin hankalinsa ya ce “Na shirya Habibteey, sai dai ke da kan ki tun a farkon fari na sanar da ke wanene ni? Abinda nake tsoro idan Har ke kin amince kina tunanin Abba za su amince idan suka yi bincike a kaina suka gano ni ba kowa bane face d’an mahaukaciya da bata san inda kanta yake ba, balle ta gano waye ya mata ciki har ta samar dani?” Khairi shiru ta yi zuciyatta itama tana tsallen tashin hankalin. Tuni ta manta da wannan matsalar ta JAHEED sai yanzu da ya farkar da ita, tabbas ita ta san waye mahaifinta mutum ne mai zafin gaske mai kafaffiyar Ak’ida wanda ba’a tab’a tankwara zuciyarsa idan har ya gano wanene JAHEED ko zata mutu ba zai bari ta aure shi ba, ita kuwa a yarda take jin soyayyarsa a zuciyarta zata iya aurensa da amincewar mahaifinta ko babu.
Sakayya Namiji Hausa Novel Complete
Don haka ta saki ajiyar zuciya tana kallon JAHEED cike da tausayin yanayin k’addararsa da ba laifinsa bane asali ma da za’a tambayeshi zab’i ba zai yarda yazo duniya ta wannan hanyar ba. Murya cike da rauni ta saki ajiyar zuciya hawayen da ta kasa b’oyonsu suka fara karakaina a kan k’uncinta bata san sanda ta kama hannun JAHEED ba ta ce “Ba mai raba
Mu JAHEED ko suna so ko basa so sai na aureka. Da sonka Allah ya halicceni na tabbata ina jin kai ne maha’din rayuwata, ruwa da iska ina tare da kai am always your’s.” Ta fa’da tana saka fuskarta a cikin tafin hannun JAHEED d’in tana sakin kuka mai k’arfin gaske mai saka tausayi a zuciyar mai sauraro. Shiru JAHEED ya yi yana sauraran kukan nata da yake raunata zuciyarsa yana jin shima kamar ya saki nasa kukan, sai dai dakiya da k’arfin zuciyarsa ya hana shi aikata hakan. Madadin hakan wani irin ciwo da bugu zuciyarsa take yi kamar yarda ta saba a lokuta da dama idan haka ta faru da shi. Sau hu’du yana neman aure sau hu’dun kuma ana hanasa dalilin rashin asali da cikakken tushe yana ji yana gani yake rasa abinda zuciyarsa take so da Muradi. Khairi itace budurwa ta biyar da yaso yana ji kuma a jikinsa wannan shine zai zama ganin da zai mata na k’arshe. Shikkenan shi haka rayuwarsa ta zo a juye irin tasa k’addarar kenan mai zafi da wuyar sha’ani. Kalaman Khairin da take sake kwararo masa mai nuni da tsananin soyayyar da take masa basu k’arfafa masa gwiwa ba, don suma wa’dancan Matan ba abinda basu ce masa ba k’arshe bisa tilas suka rabu bai sake jin d’uriyarsu ba.
Ya janye fuskar Khairin daga tafukan hannunsa yana kallon hawayen da take zubar wa yana jin zafin zubar su kamar dalma a zuciayrsa. “Ki yi shiru Khairi ni na san tabbas a wannan karan ma banda sa’a, kuma In sha Allah daga kanki ba zan sake soyayya ba zan yi hak’uri haka Allah ya k’addaro min.” Kuka ta saka sosai tana sake k’arfafa masa gwiwar ya turo neman aurenta In sha Allah zata yi addu’a tana ji kuma a jikinta wannan karan Abbanta zai amince ya ba shi aurenta.” Ya yi shiru yana nazarin idanun Khairin soyayyar Khairi mai girma ce a zuciyarsa zai iya cewa bai tab’a tsintar kansa a kwatankwacin soyayya irin ta Khairi ba. So yake mata irin son da ake kira Pure love, wanda shi da kansa ba zai ce ga dalilin da yasa yake son Khairi ba. Tun bayan da ya ha’du da ita bai sake samun nutsatstsen barci ba kullum itace a cikin barcinsa da tunaninsa. Kamar yarda kullum zuciyarsa take cikin fargaba da rauni akan kada a zo gab’ar da zai rasa Khairi, baya jin a wannan karan zai iya jurewa. Ya saki ajiyar zuciya yana jan siraran yatsunta ya sake murza zoben sa da yake hannunta da nata da yake hannunsa wanda suka kira zoben Alk’awari. Allah yasa mfarkinsu ya zama gaske yau ya gan su a matsayin ma’aurata shi da Khaireey bai san wace irin godiya zai wa Allah ba, tabbas zai iya yin azimi sittin don murnar auren Khaireey. “Shikkenan Habibteey ki je gida, zan je na yi magana da Baffa, za’a turo idan Allah yasa an dace shikkenan idan kuma ba’a dace ba ina rokonki ki yi hak’uri mu rik’e k’addararmu.” Da sauri Khaireey ta girgiza kai “No JAHEED I can’t ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba JAHEED love. Idan bai yarda ba mu gudu kawai mu yi auren mu.” JAHEED ya saki murmushi wanda yake bayyana ciwon da zuciyarsa take masa ya d’aga mata kai kawai ba wai don ya amince da tunaninta da ya kira shirme ba sai don son ya
Kwantar mata da hankali. Ya ce “Okay maza ki je gida, ki yi mafarkin JAHEED mafarki mai kyau kin ji Khaireey, ki yi mafarki na ina kissing those sweetable lips.” Ya fa’da yana k’urawa lab’banta da suke fusgar hankalinsa ido. Da sauri Khaireey ta runtse idanunta ta fice da Motar da gudu. JAHEED ya saki raunataccen murmushinsa kafin ya lumshe ido hawayen da yake ta killacewa suka samu damar silalo masa. Tabbas soyayyar Khaireey daban ce a zuciyarsa tunda har ya tsiyayar mata da k’walla. Da k’yar ya samu ya ja motarsa a hankali ya har harabar gidan zuciayrsa na ayyana masa ba mamaki ban kwana ya yi da Khaireeynsa.
_
Yarda yake tuk’in cikin rashin nutsuwa shi da kansa bai yi tsammanin zai iya sa gidan da ake rik’onsa lafiya saboda yarda zuciyarsa ta rasa sukuni ko ka’dan. Mai gadi ya bu’de masa gate ya yi parking a wajen da aka tanada don ajiye motoci. Nan d’in shine gidansu gidan da tun yana jariri anan ya taso shi da mahaifiyarsa bai san kowa ba sai mai gidan shi ya ba shi duk wata kulawa da shi da Uwar gidansa da yake jin ta tamkar mahaifiyarsa tunda ita ta raineshi har kawo yanzu da ya kai munzalin aure. Ba zai ce baya fuskantar k’alubale a zamantakewar gidan ba a’a yana samu daga b’angaren Matar gidan ta biyu dama y’ay’anta gaba d’aya da suka d’au karan tsana suka d’ora masa shi da mahaifiyarsa da suke tunanin Akwai dalili mai girma da Baffa yasa yake kula da Mahaukaciyar, duk a zuciyar Baffa bakomai illa son cika umarnin Manzon Allah da kuma tausayi da jin k’ai irin na duk wani managarcin d’an Adam. Sam Baffa baya banbanta shi da yaransa na cikinsa k’aunarsa yake kamar y’ay’an da ya tsuguna ya haifa, idan banda Anty da take kwaza ba Baffan bane ya haifeshi ba wanda zai gane idan ba fa’da maka aka yi ba.
Ya dad’e cikin motar saboda yarda gabbansa suke cikin rashin kuzari da raunin zuciya. Kafin ya d’auke kwantacciyar k’walla da take idanunsa ya saki ajiya zuciya a hankali ya bu’de motar ya fito yana zuro k’afarsa. Idanunsa suka fa’da cikin na Haidar da ya sakar masa murmushi don nufo motar ya yi da ya gaji da jiran Jaheed d’in. Haidar tare suka taso shima d’an Umma ne ita kuma ta rainesu kamar y’an biyu, bata banbanta su ko a wajen kayan sawa har abada ba zai manta karamci Umma a kansa ba. Haidar ya d’an daki kafa’darsa yana furta “Mutumin daga ina?” Jaheed ya saki ajiyar zuciya ya ce “Daga wajen Khaireey.” Murmushi Haidar ya yi yana furta “Na Khaireey ba da kanka a sare, amma naga mood d’inka is not good me ya faru?” Jaheed ya d’an dube shi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya tuna yarda suke da Haidar basa iya b’oyewa junansu damuwa kamar dai y’an biyun zahiri. Ya saki ajiyar zuciya ya ce “Abbanta ya bani umarnin na fito neman aurenta idan da gaske nake yi.” Haidar shiru ya yi shima hankalin sa na d’an tashi yana tsoron afkuwar rashin nasara kamar yarda wa’dancan neman aurarrakin suka dinga lalacewa, an kuma rasa makirin da yake zuwa dangin Y’an matan ya kwatsa musu asalin Jaheed. Tun lokacin da shi Haidar ya yi nasa auren Jaheed d’in yake ta walagigin neman aure amma an rasa dacewa saboda waccan gundumemiyar matsalar. Jaheed ya dubi Haidar da ya lula duniyar tunani ya ce “Ina ji soyayya ta da Khaireey itama ta zo k’arshe kamar yarda wa’dancan ma suka wuce
Kamar ba a yi su ba, amma ban tab’a jin haushin rasa budurwa ba kamar yarda yanzu zuciyata take cike da rauni da k’unci na rasa Khaireey da zan yi a karo na biyar, Ina son Khaireey Haidar.” Haidar ya ‘dago idanunsa da suka ka’da suka yi jajir ya zuba akan Jaheed shi d’in zuciyarsa ta raunata matuk’a ainun saboda tausayin halin da d’an uwansa yake ciki. Tabbas da ace Najwa ta girma ta isa aure ba abinda zai hana shi aurawa Jaheed, tunda itace k’anwarsa da suke ciki d’aya da ita yake iko kaf gidan ita ka’dai ce mace a cikin y’ay’an Umma su biyar, sai dai she is too young shekarunta 14 only. Su kuma wad’ancan fitsararrun da suke Uba d’aya Nasma Da Najma dama ba a zancensu don sun raina Jaheed d’in matuk’ar raini sun tsani ko bu’de ido su yi su gan shi a gidan. Gudun kada ya sake raunata Zuciyar Jaheed d’in sai ya dafa shi. Ya CE “Kada ka karaya mana Bro, In sha Allah Lokaci yazo da kaima zaka angwance ina jin hakan a jikina just pray Nima kuma Zan taya ka. Sannan mu samu Baffa mu sanar masa In sha Allah za’a dace, fatan mu kada Allah ya bawa makirin da yake zuwa ya rusa maka maganar aure dama a wannan karan.” Jaheed ya d’aga kai yana furta “Ameen” ba wai don har a zuciyarsa yana saka rai zai samu Khaireey ba sai dai dole zai bi shawarar Haidar don basu tab’a k’in yiwa juna Biyayya akan shawara ba.
Daidai lokacin rantsatstisyar motar bak’a wuluk ta shigo cikin gidan a mugun speed, ga wani ki’da mai k’arfin gaske an ware a cikin motar. Sauti yake bayarwa sosai. Haidar take ransa ya b’aci don ya san ba kowa bace sai Najma itace mai wannan banzar d’abi’ar yarinya kamar rainon kafirai, ba Kuma laifin kowa bane sai na Uwarta data ke d’aure mata k’ugu. Jaheed kuwa ji ya yi kamar zata tarwatsa kan sa don a rayuwarsa baya son hayaniya shi mutum ne very cool bai Kuma son shiga shirgin kowa.
Wawan parking ta yi a gefensu, ta fito cikin takun k’asaita da nuna isa na isassun mata. Idanunta sanye da bak’in shade da ya k’ara mata rantsatstsen kyan da take alfahari da shi. Ta cikin glass d’in take jifan Jaheed da wani wulak’antaccen kallo ta isa ta gefensu zata wuce. Murya a ciki ta ce “Ya Haidar barka da yamma.” A ciki ya amsa tana shirin shigewa ya kira sunan ta a tsawace, cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba duk da suna shakkar Yaya Haidar ‘din da fa’dansa amma ba zata nuna a gaban mutanen da ta tsana ba. “Ni ka’dai kika gani a wajen?” Ta juyo a zafafe tana kallon sa kafin ta ce “Kai ka’dai ne ya wajaba na gaisa da kai.” Mamaki bai bar Haidar ya mata magana ba, tsananin mamakin gadara da tsaurin idon ta. Kunyar Jaheed ce ma ta kama shi, da sam bai nuna ya san me suke ba danna wayar sa kawai yake, duk da maganar yarinyar ta doki dodon kunnensa kuma ta yi masa zafi matuk’a sai dai bisa tilas ya shanye don ba yau ya fara karb’ar wulak’ancinta da rashin mutuncinta ba ya Riga ya saba da ita da y’ar uwarta da ma uwarsu gaba d’aya basa ganin k’ima da mutuncinsa duk da dama shi d’in ya sani a wajen mutane ba shi da wata k’ima balle daraja irinsu da aka haifa a titi rashin Uba ya kan janyo musu tsana da wulak’anci daga wajen jama’ar da ba su kai su ba ma balle su taka k’afarsu, balle ita wannan da yake ganin karanta ya kai tsaiko, a k’ark’ashin Ubanta yake, cin sa da shansa tun yana zanin goyo Ubanta ne ya d’auke su shi ya samar masa da nagartaccen ilimin da yake tunk’aho da shi a yanzu. Don haka ba zai damu ba so samu ne shine zai zama mai gaisheta da nuna ladabi a wajenta abinda suke so kenan, shi kuma ya kasa musu girman kansa da fa’din ransa da yake jin sa kamar basarake ya kasa yarda ya amince wa zuciyarsa ya Zauna a taka shi. Ya yarda shi shege ne mara gata mara galihu amma bai amince shi d’in mara daraja bane, yana kallon kansa a wani mutum mai daraja ta farko a cikin mutane, don haka ba zai tab’a k’ask’antar da kan sa ba. Haidar ya saki ajiyar zuciya yana kallon Jaheed da ko a fuskarsa bai nuna damuwa da abinda Najma ta masa ba, madadin haka ma wani k’ayataccen murmushi ne kwance a kan kyakykyawar fuskarsa mai d’auke da zagayyen saje. Cikin sakakkiyar murya ya ce “Yaushe ka ke ganin ya dace na samu Baffa da maganar?” Haidar ya saki ajiyar zuciya shima ya nuna bakomai d’in kamar yarda Jaheed ya bagarar ya ce “Ko yau da Magriba sai mu same shi mu ji abinda zai ce.” Jaheed ya diro daga kan motarsa yana mik’a masa hannu ya ce “Allah ya kai mu, ka gaisar min da yara na da madam, ace da d’an rigimata wannan week end Zan zo na kai su park.” Haidar shima murmushin ya yi ya mik’a masa hannu yana jinjina zuciya irin ta Jaheed mai k’ok’arin nuna komai ba komai ba duk tsananin b’acin ran da yake ciki ba dai ka gan shi a kan fuskar sa ba, sau tari har mamakin hakan Haidar yake yi. Ya saki ajiyar zuciya yana fad’awa motarsa don ya isa gida da wuri don yaga yamma ta yi.
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/EZyeAwHEGGhJz1pRBmmale
K’UDIRAR ALLAH.
Page. 1
NAZEEFAH SABO NASHE.✍🏽

: K’UDIRAR ALLAH
2.
NAZEEFAH SABO NASHE
08033748387.
Bin motar Haidar ya yi da kallo kafin ya saki sassauk’ar ajiyar zuciya yana lumshe idonsa wani irin zafi da turiri yake jin zuciyar sa take yi, duk da k’ok’arin danne b’acin ran da yake yi hakan bai hana bayyanuwar b’acin ran akan kyakykyawar fuskarsa ba. Tausayin kansa ya sake mama ye shi kafin ya d’au hanyar da zata sada shi da ainahin cikin Gidan direct.
Faffad’ar haraba ce mai girman gaske fiye da ta wajen da ake ajiye motoci. Bakomai a harabar sai manyan bishiyu da suka yiwa tsakargidan ado da inuwa mai k’ayatuwa a idanun mai kallo. Yanayin damuna da ake ciki ya sake k’awata wajen baka sha’kar komai sai k’amshin tarin bishiyun da suke cikin harabar lemon tsami guava mango da sauran dangoginsu. Ya sake mai da hankalinsa kan k’ofar da zata kai shi sashen da Umma take marik’iyarsa inda anan aka warewa tasa mahaifiyar nata d’akin mai d’auke da parlour da toilet aka kuma saka mata duk wani abin more rayuwa duk da zamantowarta mara hankali bai hanata tsaftace d’akin ba idan ka shiga zata zaka yi mai cikakken hankali ce mamallakin sashen.
Umma da take zaune a babban parlourn da ya raba sashenta da na Mahaifiyar Jaheed d’in ta bi shi da kallo murmushin kan fuskarta na sake yalwata ta ce “Ka dawo kenan Mujaheed?” Shi d’in ma murmushin da kai tsaye za’a kira na k’arfin hali ya saki yana d’aga mata kai kafin ya rusuna ya gaisheta. Ta amsa masa cike da kulawa saboda yarda take jin Jaheed d’in kamar ita ta durk’usa ta haifesa bata banbance soyayyar sa da ta nata y’ay’an data tsuguna ta haifesu abu d’aya ta sani Ba ita ta yi nak’udarsa da shayar da shi amma duk wata hidima da Uwa take wa d’anta ita ta yiwa Jaheed, shayarwa ce dai a hakan a haukar Uwarsa ita ta shayar da shi, abin mamaki yarda take ba shi kulawa ba zaka ce k’wak’walwarta da motsi ba duk da akwai wani keb’antaccen sirri da ita ka’dai ce ta sani.
Jaheed ya dubi Najwa yana fa’din “Najee samo min ruwa.” Da sauri ta mik’e don a rayuwarta tana girmama lamarin Jaheed da kuma duk wata hidima data danganceshi, yarda take son sa bata jin tana son nata jinin haka. Ruwan mai sanyi ta d’auko a fridge d’in da yake dinning area d’in Umma. Ta kawo masa a k’aramin tray. Bai bi ta kan cup d’in da take mik’a masa ba ya b’alle murfin ruwan ya fara kwankwa’da. Sai da ya shanye tas kamar ruwan ne zai tafi da bak’in cikin da ya masa dafifi a zuciyarsa sannan ya ajiye robar yana sakin huci a hankali. Umma murmushi ta saki ganin yarda yake wayancewa wajen son kawar da b’acin ran da ya kasa b’oyuwa a fuskarsa ba duk da k’ok’arin danne shi da yake. Ta fi kowa sanin Jaheed da halayensa kaf idan yana cikin farin ciki ta sani kamar yarda idan yana cikin b’acin rai duk k’ok’arin sa da son danne b’acin ransa hakan baya b’oyuwa gareta a k’wayar idanunsa take banbance halin da yake ciki, don haka cikin raunin murya ta dubeshi tana furta “Sun ce ka turo ko?” Da sauri Jaheed ya d’ago yana kallonta cikin mamakin jin abinda ta ce, ya yi mamaki k’warai da gaske da har ta gano abinda yake ciki, kamar ya ce mata ya aka yi kika gane sai dai ya ja bakinsa ya tsuke yana duban T.V ha’de da ‘d’aga kai a hankali muryarsa ta kasa b’oye b’acin ran da yake ciki saboda yarda ta raunana ya ce “Sun ce Umma.” Sakin ajiyar zuciya ta yi tana furta “Kada ka damu wannan karan za’a dace In sha Allah, abin buk’ata ka dage da addu’a.” Shiru ya yi yana jin sauk’in nauyin da k’irjinsa ya yi, kalamin Ummansa ya sauk’ak’a masa fargabar sa da b’acin ransa. Umma ta dubi Najwa ta ce “Je ki zubo masa abinci daga ganin wannan idon kana jin yunwa.” Murmushi ya saki a hankali yana jin dad’in kulawar da Umma take ba shi har yanzu ganinsa take kamar yaro, ko don bai yi aure bane oho, ko kuma tausayawa irin rayuwar da ya taso a ciki take shine bai sani ba. “Ka ci abinci ka je ka samu Nene ka gaya mata.” Ya
D’aya kai kawai yana mamakin duk sanda irin wannan zata faru sai Umman ta umarceshi da ya gayawa mahaifiyarsa ta kan ce “Ko kallonka ta yi bata maka addu’a ba zai da’da’da maka balle idan ka furta addu’ar itama zata maimaita Allah kuma Zai amsa In sha Allah.” Jaheed murmushi kawai ya saki yana amsar Abincin da Najwa ta zubo masa a plate ganin favorite food d’insa ne Alkubus da miyar taushe yasa ya saki murmushi gefe guda kuma kunun aya ne. Zamewa ya yi ya zauna a kan carpet don yafi ganewa ya ci abinci k’afar sa a tank’washe kuma yafi cin abinci da hannu idan ba’a bak’on waje ba shi yasa sau tari yafi ganewa cin abinci a falon Umma inda zai bararraje ya tsoma hannunsa ya ci son ransa. Ya wanke hannun A wash hand basin da yake dinning area d’in sannan ya dawo ya fara cin abincin yana fa’din “Madalla da Umman mu mai da’din tuwo.” Murmushi Umma ta yi ta ce “Ka hango Alkhbus ba dole Ai ka fara
santi, dama sai kacewa Khairin ta dage ta iya Alkubus mayensa zata aura.” Murmushi ya saki a zuciyarsa yana fatan Allah ya amsa addu’ar Umma yau ya gan shi ga shi ga Khairi a gida d’aya matsayin ma’aurata da yafi kowa murna a duniya don ya tabbata a ranar ba na biyunsa wajen farin ciki, bai san kuma irin godiyar da zai wa Allah ba gani yake ko kwana ya yi yana sallah godiyar ta yi ka’dan. Sai da ya cinye abincin tas ya kuma taune tantak’washin sannan ya yi Hamdala yana duban Najwa da take kallonsa k’asa k’asa, haka kawai Jaheed yake burgeta duk wani abu da ya yi burgeta yake yi, sau tari tana hasasho Mijin da zata aura ya zama mai halaye kamanni da komai irin na Jaheed, tun kan ta san ba d’an uwanta bane da suke ciki d’aya balle yanzu data fara girma sai take auna Jaheed d’in a matsayin Mijin aurenta tun bayan data san ba maharraminta bane. Jaheed ya dubeta yana furta “Zo ki kwashe kwanukan nan, kullum
Baki da aiki sai kallo ya kamata Umma ta fara saka ki aiki Wallahi kada ki tashi baki iya komai ba.” D’an mitsitsin bakinta ta turo kafin cikin shagwab’a ta ce “Kai Ya Jaheed Wallahi ina aiki yau fa ni na yi alkubus d’in nan.” Wani irin waro ido ya yi yana kallonta ba Najwa ba hatta Umma sai da ya sata dariya yana furta “Lie Lie ya mik’e kafin ya kai mata rank’washi a kai ya ce “Mai k’arya dai d’an wuta.” Ta dubi Umma tana furta “Umma gaya masa don Allah ba ni na yi ba?” Umma tana murmushi ta ce “Gobe ya tsaya ki yi a gabansa sai ya tabbatar.” Girgiza kai ya yi yana fa’din “Ah to kin dace tunda kin gado hannun Umma.” Ya fad’a yana tura k’ofar da zata kai shi Inda parlorn Nenensa yake. Najwa zata bi shi Umma ta saka baki ta kirata sau tari ita take hanata binsa musamman a irin wannan lokacin da yake matuk’ar buk’atar d’umin mahaifiyarsa ko dai bata magantu ba idan ya gaya mata damuwarsa Zai ji sauk’i cikin k’irjinsa, don haka ta hanata bin sa Najwan ta dawo tana turo bakinta gaba na jin haushin rashin binsa duk da sonta da hakan don tana son kullum ta dinga ganin Nenen musamman idan suna tare da Jaheed sai ta dinga jin wani irin farin ciki data kan rasa dalili.
A zaune ya tarar da ita tsaf da ita cikin shigar doguwar rigar atamfa jikinta sanye da hijab kamar kullum. Ba abinda zai da ka gane tana hauka sai idanunta idan ta zazzaro maka su sai kuma yanayin yarda take mayar maka da maganar da duk ka furta sai ta maimaita maka kamar mai karatu. Tana ganinsa ta d’ago a fisge tana kallonsa fuskarta na d’an sakin murmushi ka’dan mai bayyana matsayin ta na mahaukaciya. Jaheed murmushi ya saki ya zauna a gefenta kamar yarda ya saba yana kama hannuwanta ya matsa su ka’dan ya ce “Yau Nene ba kya kallo?” Sake maimaita masa abinda ya ce ta yi. Jaheed ya saki ajiyar zuciya yana fatan ranar da Ummansa zata samu waraka ko Zata fa’di inda asalinta da danginta suke ko da wannan ya tsira zai gode wa Allah idan ma bai samu dangin mahaifin nasa ba, fiye da yanzu da bai san kowa nasa ba yake watagangaririya a rayuwa. Idanu ya sauke cikin na Nenen data kafa masa nata idon kamar mai son gano wani abu a cikin idon nasa. Shiru zuwa wani lokaci suna kallon kallo kafin Jaheed ya sauke nasa idon yana furta “Ki yi min addu’a Nene sun ce na turo.” Ta sake maimaita abinda ya ce Jaheed ya d’ago yana kallonta yana mamakin yanayin damuwa da ya gani tattare da ita kamar yarda ta saba a duk sanda zai zo mata da makamanciyar magana irin wannan mamakin hakan yake sosai tunda ya san bata da hankalin da Zata dinga feeling farin ciki ko bak’in ciki a cikin ranta, bai san me yake janyo mata wannan yanayin ba mai bayyana zallar damuwar da take ciki. Idan ba idanunsa ne ya gaya masa ba har tarin k’walla ya gano kwance cikin k’wayar idanunta. Bai ji komai a ransa ba tunda ya san Nenen ba abinda ta sani irin maimaita magana na ta salon haukan kenan da tun tashinsa a haka ya santa. “Allah ya baka abinda kake so Jaheed Allah yasa su baka aurenta Jaheed.” Hakan kuwa da yake so ta furta hakan ta maimaita masa ya saki murmushi har lotsawar hab’arsa tana sake k’aruwa, itama murmushin ta saki tata lotsawar hab’ar na sake bayyyana wanda wannan ne kawai abinda suke kamanceceniya da shi banda haka ba ta inda Jaheed yake kama da ita komansu mabanbanci ne. Kwanciya ya yi a cinyarta yana sakin ajiyar zuciya a hankali kafin ya d’au hannun Nenen ya saka a kansa a duk sanda yake cikin damuwa wannan d’in yana dag cikin abinda yake kawar masa da Rabin damuwarsa. Nenen ta shiga yamutsa masa Sumar kansa tsawon lokaci kafin ya d’ago yana mayar da k’wallar idanunsa da suke zuba ba shiri, a gaban Nene kawai yake iya sakar k’wallarsa ta zuba bai damu ba banda haka ba wanda zai ce ya san k’wallarsa tun bayan girmansa sai Nenne da yake iya bayyana rauninsa kai tsaye a wajenta. Bai juyo ya kalleta ba da itama zai ga tata k’wallar da take zuba ba k’akkautawa saka kansa kawai ya yi ya fice daga d’akin. Sai da ya tsaya a corridor ya kawar da duk wata fuska ta damuwa sannan ya saka glass d’in idanunsa bak’i wuluk don bata son Umma taga idanun da suka canja sannan ya fice da sauri ya ji da’di sosai da bai samu Umman da Najee a babban parlourn ba.
Yana fita Nene ta kifa kanta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, kukan tausayin Jaheed yake da yarda da sanin ta ta b’oye masa waye shi? Sannan ta d’auki haukan k’arya ta d’orawa kanta duk don gudun kada a tambayeta asalinta da na Jaheed d’in. Tana tausayin d’anta kamar yarda sau tari zuciyarta take son ta bayyana masa asalinsa sai dai tsoron bala’in da sanin asalin nasa zai haifar yana togaceta daga aikata hakan, zamanta a matsayin mahaukaciya da rashin sanin asalin Jaheed shi ya fiye musu alheri daga ita har Jaheed d’in fiye da bayyanar gaskiyar lamarin, tabbas abinda ta b’oye shine alheri garesu gaba d’aya daga ita har duk wani masoyin ta. Da sauri ta mik’e tana dannawa k’ofar d’akin mukulli kafin ta juyo ta fa’da toilet da azama ta d’auro alwala. Tana fitowa sallaya ta shimfi’da ta fuskanci alk’ibla cikin nutsuwa ta tada sallah. Rako’i da yawa ta yi kafin cikin sujjadar k’arshe ta fashe da kuka tana furta “Ya Allah ka zama gatanmu ni da Jaheed a rayuwa, Allah ka bashi mata ta gari ka gajarta masa wahalar rayuwar neman aure.
To fa! Wai me Nenne take b’oyewa ne? Menene asalin Jaheed da rashin bayyana hakan yafi alheri garesu fiye da bayyana hakan? Daga ji dai kun san tafiyar mai zafi ce akwai rikita rikita ta gasken gaske yanzu aka fara. Shin kin biya kuwa 500 kacal dai kada ta gagareki hajiya a yi wannan tafiyar ba ke. Kai tsaya ki biya ta asusun banki kamar haka 2118666253 UBA
Sai ki tura shaidar biya ta wannan numberr 08033748387.
Vip 1k (Za’a tura musu kai tsaye har gida.)
Nagode sosai
JIKAR NASHE CE✍🏽