Littafan Hausa Novels

Sakayya Namiji Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Sakayya Namiji Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM.

 

 

 

 

 

 

 

…Kuluwa! Kuluwa!!Kuluuuu!!!

 

Aka shiga kwalamata kira.

 

 

 

Karcet ta yanko da gudu cikin palon har tana zamewa jikinta na ɓari ta durkushe kasa tace. Hajiya gani dan girman Allah kiyi Hakuri yarone ya tashi nike shayar dashi. Cewar matashiyar Matar da Ashekaru bazatafi shekara 26 ba.

 

 

 

Dogon tsaki yarinya taja dan bazatafi shekara 20 ba ashekaru ta girmema Yarinya da takira da Hajiya nesa ba kusa ba.

 

 

 

Afusace tace toh tsaya kiji,wlh tallahi kin kusa barin gidan nan,akan me,nida gidana,Sallamaki fa nike,wane irin shegen yarone dake mai masifar kuka ba dare ba rana ,to Bari Baby yazo wlh sai kinbar gidan nan dama Alfarmarsa kikeci shegiya bakauya kawai wlh na tsane ki.

 

 

 

Hawaye na zubomata tace kiyi hkr in sha Allah zan kiyaye.

 

 

 

Tsaki tayi tace kin daiji na fadamaiki,kuma kitashi kimaza ki shirya Dining Yanzu xai mijina zai shigo .

 

 

 

Da sauri ta tashi kuka na kwacemata tashiga hadaddan kiching din ta hada komi ta kawo palon ta shirya, lokacin Khadija nata kai komo sai bude window take amma shuru ba alamar abinda take jira.

 

Ajiyar zuciya ta sauke tare da dawowa ta zauna ta zubama Kuluwa ido tana kallo, Kuluwa had’ad’d’ar macace sosai,Itadai ba fara bace kuma baka isa kacemata baka ba ,kalar fatarta mai kyau mai sheki, doguwace sosai gata da madaidaicin jiki daya dace da tsawonta,dukkan wanda ya kalli fuskarta zayyi fatan ya ƙara dan wani irin sihirtaccen kyau ne da ita,ga mayun idanuwa masu daukar hankalin duk wani lafiyayyan namiji,Kullum zakaga idonta a lumshe tamkar mai bacci,Tsayayyan hancinta mai ɗauke da tawwadar Allah bakaramin karama fuskar ta kyau yayi ba,Goshin ta luf-luf da kwantaccen gashi.

 

 

 

Wani irin rin Haushi da takaici ya turnike khadija ganin yanda tasanya atamfar roba doguwar Riga manyan hips dinta duk sun fito cikakken kirjinta kau yayi dam dam cikin breas cup din dake a dinki.

 

khadija dake sanye da tsadddan lace ta zubama kanta ido cikin madubin dake palon ,zahirin gaskiya babu abinda zata nunama Kuluwa sai fari,domin khadija yar busassa d’iyace kyam kyam jikinta yake sai uban fari da d’agawa ,irin yaran nan ne masu wulakanci yayin da sukaga Allah ya budamasu,kyan Kuluwa yasa ko alama bata kaunarta,gashi mijinta kuma ya dage akan dole ta barta dan wani Abokin shine yasamo mai ita a kauye suke da zama sai karshen wata take zuwa gida wajen mijinta, Dan da zawarace bazata taɓa barinta ta zaunamata A gida ba gudun kar Baby ta ya kalleta duk da bataga alamar yama taɓa sanin tana gidan ba.

 

 

 

Kuluwa kau dukawa tayi tace nagama akwai abinda zan maki.

 

 

 

Fuska ta yatsina tace haura sama dakko gajerun wanduna Baby da nawa ki wanke su ki tabbatar sun fita.

 

Toh tace ta dakko tanajin danta na kuka har ranta amma tason taje wajen shi bakaramin tashin hankali za’ayi ba shiyasa tabar shi fatan ta yagaji yayi bcci.

 

 

 

Saida ta dakko komi ta dawo ta kwashi kayan tafito ta kofar palon,tana fitowa ana bude get din gidan hadaddar motar mai gidan na cinno kai,Tindaga nesa ta kafe motar da ido tama manta da abinda xatai har suka karaso kusa da ita.

 

Cikin natsuwa ya buɗe yafito yana kallonta afizge kamin ya kawar da kai yana kallon nesa.

 

 

 

A’Hankali tace sannu da zuwa.

 

 

 

Kije kiyi aikin gaban ki. yace batare daya bari yako kalli inda take ba.

 

 

 

Baya ta wuce sumi sumi ta wanke kayan tass ta shanya.

 

 

 

 

 

Khadija kau dake tsaye wajen window kamar Tsaka ta daka sallen murna ganin yanda mijinta ke kawar dakai in yaga mace tace nawa ni kadai ta fita ta tarbo shi suka rungume juna ashagwabe tace nayi Missing naka sosai wlh da binka zanyi shago .

 

 

 

Kumatunta yaja yana murmushi yace karkisoma,domin duk kan wanda ya kalleman kyakyawar Matata sai nayi Shari’a dashi,nima gabaki daya hankalina na kanki,yanzu dai yunwa nikeji fara zubamin Abinci naci nayi wanka.

 

 

 

Tace ba wankan zaka fara ba?.

 

 

 

Yace” a’a ci nagaba da komi.

 

 

 

Zuba mai tayi yaci yanajin masifar dadin abinci A’hankali yace. Yaushe zakimin.girki naci itin na matata amma kinbarman mai aiki sai yamutsamun abinci take son ranta haba Khady,wlh kawai dan bani da yanda zanyi amma banason Abincin matar nan som,saboda banson yanda take sarrafa shiba.

 

 

 

Fuska ta daure tana zubamai harara tace yau kuma da tsogwami ka dawo,amma dai aikason ban iyaba som gidan mu ko indomie bama dafawa komi masu aiki ke mana,kai wlh nifa ko tafasa ruwan zafi ban iyaba tsoroma nikeji karnaje na kone,Ai amfanin dukiya kenan ka huta ka dau masu aiki ni.kama ɓataman rai wlh.

 

 

 

Allah yabaki hakuri Baby nah karki damu bazan sake ba yafada cikin sanyi jiki.

 

 

 

Fuska ta yamutsa tace Ameen , Yawwa waccen Jakar nakeso ka kora amma kafara samoman wata tukunna karta tafi kuma babu mai kulawa da gidan.

 

 

 

Cikin Manaki yace mitamaki?

 

 

 

Tace kawai nidai bataiman ba wlh bana sonta.

 

 

 

Fuska ya dan daure yace yanzu ni dani na samota saina koreta amma ina ganin darajar Habib bazan iyamasa haka ba,kijifa matar nan da auranta karshen watane kawai take zuwa ganin gida kuma kwana biyu take kadai ta dawo to mita tsare miki haba khadija.

 

 

 

Baki ta turo tace toh wlh wannan karan in’taje sai dai ta kwaso kayan Kakarta masu datti kuma daban daban,amma kulkum cikin dogayen riguna take duk da atamfar robace tanamata kyaufa kuma kana kallonta.

 

 

 

Ido ya zaro yace wlh in kina gabana babu macen da nike kallo Amatsayin mace ,in kina gabana kowa ganinsa nike kamar ni din nan,Khadija sonki a jinina yake dashi aka halicceni kuma dashi zan koma ga uban gijina,bazan taɓa iya hada sonki dana kowa ba,Kuma karki damu da kaina zanma Habib magana ya samo mata kayan da kikeso yayi maki?

 

 

 

Ido ta lumshe tace yayi toh tashi ka goyani.

 

 

 

Da sauri ya Mike yana dukawa ta daga kafarta kenan zata hau sukaji faduwar abu.

 

 

 

Da sauri suka kalli bakin kofar kiching sukaga kuluwace tsaye boket din hannutane ya fadi.

 

 

 

 

 

A rikice tace kuyi hkr dan Allah dama sauran sabulun da omo ne na kawomaki.

 

 

 

 

 

Aguje khadija tayi kanta ta daka tsalle ta yankamata mari ta karamata wani tace jaka dabba,tare da fesamata yawu tace duk yanda akai da jaki sai yaci kara,kauyancin ki baya taɓa boyuwa,ina tare da mijina kikemana gittayya dan kiga salona ki kwasa akaima na kauye ko?

 

 

 

 

 

Idon Kuluwa yayi jawur ta zubama khadija ido jikinta na rawa ta bude baki zatai magana.

 

Mijin khadija ya dakamata tsawa da fadin bar wajen nan akace malama.

 

 

 

Da sauri ta juya ta fada dakinta ta saki mahaukacin kuka ..

 

 

 

 

 

Shikau rawa jikin shi ya fara ahaka ya ɗauki khadija sukayi daki daganan wasan ya sauyawa.

 

Bayan sati daya kuluwa ta shirya zuwa kauye,bayan tama khadija sallama itama khadija ta hada kayanta dan tafiya gidan su,dama haka sukeyi,shikuma Khalid mijinta Kasuwa yake zuwa yayo sayayya duk karshen wata so sadda Kuluwa zata dawo kana kowa sai ya dawo.

 

 

 

Saida ya aje khadija kana yatafi dan Aje motar kasuwa Ya hau Babbar da suke zuwa da ita Ƙudu, lokacin Kuluwa ta dade da tafiya.

 

 

 

 

 

Khadija zaune katafaran palon gidan su ita da mahaifiyarta , Hamshakiyar mace dagani kudi sun samu muhalli a wajen bayin Allah nan.

 

 

 

Mummy ta kalli khadija cikin kulawa tace Auta ya gidan naki da fatan ba wani matsala.

 

 

 

Fuska ta yamutsa tace babu Mummy,wannan yar aikince kawai matsalata tafiye kyau.

 

 

 

Dariya sosai mummy tayi tace.

 

Hohoho khadija kishi,hmmm yo ina wani kyau ga talakkan daya baro mijinsa yazo neman arziki,Ai baruwanki da ita kema kinson tana taimaka miki,yanzu bagashiba dole duk karshen wata kina nan gida shima mijin ya falla ƙudu nema dan ataru arufama kai asiri,da kin iya abubuwa ai kinga kana zaki koreta, yanzu kika koreta yana iya samo miki budurwa,ko asamomiki tsohuwa da zata kasa aikin daya kaita,shawarata anan gareki shine,ki bar saka mata ido,ki kama kanki kawai kibar kulawa da ita balle abin ya shamaki kai.

 

 

 

Tsaki tayi tace to Mummy inaso in’bada asawomata kaya mafi wulakanci da zata dinga sawa agidan.nan.amma kullum.cikin doguwar Riga,so nike asawomata zannuwa da T shirt wulakantattu tana sawa,Ga uwayen mazaunai yanda kikason An ɗora mata ruwa takaf takaf haka take Juyasu kilama ciko take yar iska.

 

 

 

Dariya mummy ta dingayi tace ba matsala ko Baraka kiba ta nemo miki,Sannan wannan kuma halitta ne in kinso.saikimata Hijjob tana sawa agidan in ce shikenan

 

 

 

 

 

Mikewa tsaye tayi tace Hakan ma yayi bari in dan kwanta ta fada dakin Ta dake hadadde ta dauki wayarta ta hau kiran Khalid,Saida ta mai kira goma kana ya dauka yana ta sauke numfashi kamar wanda Yasha gudu.

 

 

 

Gabanta ne yayi mummunan faduwa domin tason sai in gamsuwa ya samu yake wannan hakin..

 

 

 

Murya na rawa tace Baby mizan gani haka minikeji haka?.Dama amanata kaci?

 

 

 

 

 

More Comment more typing

 

 

 

 

 

Account number

 

9150660333 Hafsat Dahiru opay bank

 

 

 

Ko kuma katin glo banason Mtn.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*SAKAYYA NAMIJI

 

 

 

*UMMY AYSHA*

 

 

 

*PAGE 2&3*

 

 

 

 

 

..Cikin wani low Voice yace. zan kiraki,ina nan cikin Ramin maciji,domin yan garkuwa da mutane ne suka tare motar mu nishin da kikaji inayi na gudu ne da tsoron wannan katuwar mesa karta saran.

 

 

 

A rikice tace. Subhanallahi Baby dan Allah kayi sauri ka Fita banason abinda zaiman wasa da rayuwar ka.

 

 

 

Numfashi ya sauke yace tayani Addu’a. ya kashe wayar shi.

 

Mulki Hausa Novel Complete

 

A rikice ta fito hannuta aka ta rushe da kuka tace Mummy wlh mijina na cikim hadari,mummy dan Allah Daddy ya samar masa aikin campany yabar wannan kasuwar da ke cike da hadari,.

 

 

 

Salati tasaki tace miyafaru.

 

 

 

Cikin haki takwashe yanda sukai ta faɗamata.

 

 

 

Sosai uwar ta rikice tace kinga in sha Allah zai fita lfy,dan Allah ki kwantar da Hankalin ki, ni Tashin hankalin ki ne banaso Auta,kinson ba cikakkiyar lfy ne dake ba karkije ciwon ki ya tashi abanza,Auta ki rage son namiji haka dan Allah dan Annabi haba inama Amfani,,.

 

 

 

Kuka tasa tana diddira kafa tace” mummy miyasa ke baki damu da abinda nike so ba sosai kamar Daddy,?,.

 

 

 

Afusace tace ke dakata banason Iskanci,mi zan miki ne,Ince dai addu’a ce kuma namasa,da kike fadin ubanki ya bashi aiki uban mi ya karanta mutumin da ko secondary baida takaddunta ai kasuwancin ne dai dai shi,Kuma shi dama mai nema ai yana tattare da kalubale,Sai ace komi nan za’a masa bazaki bari yazama namiji ya nema ba.

 

 

 

 

 

Cikin jin haushin kalaman mahaifiyar tata ta watsa da gudu saman benen su inda dakinta yake tafada kan bed ta fashe da kuka mai ciwo tare da sake Kiran Number Khalid amma bai ɗauka ba.

 

 

 

Haka ta yini wannan rana cikin tashin Hankali sai cen cikin dare yamata text kamar haka.

 

 

 

 

 

*Baby nah kiyi bacci Allah ya fiddoni Lfy, amma maganar da nike maki ina nan saman bishiya kuka sai Abinda Allah yayi,dan banson ta inda na shigo ba wannan dajin Allah ne kawai zai fiddani,In.gari ya waye zan nemi hanya in fito,In nafitoma bazanje cen Legos dinba gida zanyo ,Ki kwana lfy in kinkira kinji shuru wayata ce ba charge ki kulaman da kanki My khady i love you so much*,

 

 

 

Tana gama karantawa ta fashe da kuka ta tashi tayi Toilet ta dauro Alwallah ta dinga kwarara sallah da nema masa hanyar tsira a wajen Allah har bacci ya kwashe ta .

 

 

 

Tin daga wannan ranar basu sake magana ba saida akayi kwana hudu ya mata text cewa gashinan gidan wani monomi daya tsince shi kafarsa ce cike da ƙayoyi bazai iya fitaba magani ake masa.

 

 

 

Hankali tashe ta fara kiran wayar shi amma bai dauka ba sai wani message din dayamata kan cewa tabar kiran shi saboda koya dauka baji zataiba som network din su baida kyau,Shi dai tamai Addu’a baison ranar dawowar saba,Bari ya kira Habib Ya turomata Kuluwa kawai su koma ai’bata ta zaman gida ba.

 

 

 

 

 

Da hanzari tamai text cewa.

 

*Bazata iya zaman gidan nan ba kona kwana daya, muddun baya nan zata zauna gida ta kuma sanya ai’tamai addu’a da sadaka*

 

 

 

gdy ya mata shikenan bata sake jin shiba.

 

 

 

 

 

A yau daya cika sati biyu da tafiya tana zaune palo ta zuba uban rama dama gata kamar Shinge.

 

 

 

Mummy na duba wayar ta ta dago ta zubamata ido tace ina mamakin yanda kika tayar da hankalin ki akan yaron nan khadija,Akan mi,namiji nefa,namiji nefa,Toh wlh tallahi kibari tin wuri karki kashe kanki abanza,tinda kika hadu da yaron nan kika rikice kika haukace kika zauce saida kika aure shi Hankakin ki ya kwanta, yanzu kuma dan yayi tafiya shikenan tindama kinajin sa a message ba shikenan ba inda shuru kikaji ai shine zaki tashi Hankali.

 

 

 

 

 

Hawaye ta share tace Mummy kauye fa yake.

 

 

 

Afusace tace dama ai dagacen ya fito kefa banason iskanci kinji.

 

 

 

Da sauri ta mike ta haura sama Tare da kiran Number shi cikin Sa’a taji ya dauka tare da sauke Ajiyar zuciya yace my khady yanzun nan na daga hannu zan kiraki , Allah yaman fitowa duk da mutanan garin basuso ba dan sun bani wahala sosai dakin fiddoni hanya , Amma gani nan alhamdulillah yau zan kwana tare da matana ko.

 

 

 

Ajiyar zuciya taita saukewa tana yake baki da dagamai kai tace Baby.

 

 

 

Yace Na’am Babyn Baby.

 

 

 

Cikin kuka tace I miss you so much,Wannan tafiyar na tsaneta,banasonta kuma kagamata daga yau,saboda zataman shamaki dakai,bakason yanake kwana biyun nan ba baka,amma yau satina biyu agida batare dana rabeka ba, dukkan abinda zai zama shamaki tsakanina dakai wlh Azeem banda makiyi daya fishi,banason kowa ya rabeka,kai Baby ko robar ruwa banaso naga ka dorata bisa kafar ka balle jikka,saboda inajin matsanancin kishinka a rayuwata,banaso kowa ya rageka bayan iyayen ka,Kamar yanda Allah yayoni domin kai haka nima akayika domin Ni,Wlh wlh Yan kauyen nan da zanson inda suke tabbas sai nasa An kamasu,saboda sun zalinceni sun Rikeman miji,Sunbar yaran su da Dabbobinsu suna kalleman kai,Sun katseman kwanakin jin dadina Ajikin ka.

 

 

 

Ajiyar zuciya ya sauke yace ngd sosai Baby amma dan Allah ki Rage wannan kishin kinji.

 

 

 

Afusace tace kana nufin kana tinanin zaka iya hadani da wata ne ko miye daka damu.

 

 

 

Da sauri yace Aa ba haka nike nufi ba,Kawai dai banaso kina kawoma ranki wannan tunanin ne balle ya ɓatamiki rai ko kiji damuwa,Ni kuma dukkan abinda zai saki wannan damuwar Banason sa domin ke daice Arayu….

 

 

 

Khaliddddddd……

 

 

 

Khadija taji an’kirashi da mugun karfi, hakan kuma yasa shi katse wayar da sauri ya kasheta baki daya.

 

 

 

 

 

A gigice khadija ta mike jikinta na rawa numfashinta na sama da kasa ,Cikin rawar jiki tafara neman layin sa amma kiran duniya bata samu ba An kashe wayar..

 

 

 

Cikin nazari da zargin dake ranta tace tabbas khalid da mace yake,tabbas macace ke kiran khalid,.

 

 

 

Wani irin cije baki ta fara kamin ta fada saman gado Ba numfashi Jikinta..

 

 

 

 

 

A’Hankali ta bude idonta tana kallon Rufin dakin da take,Abinda yafaru ne ya dawomata a kwalwa da sauri ta zabura tana kiran khalid.

 

 

 

Da sauri ya Rungumeta yana fadin sannu Sannu Khadija miyafaru dan allah miyarage kikeson min Asarar kanki.

 

 

 

Khalid kaidawa,khalid dan Allah karkaceman da mace kake khalid dan Allah ka tausayaman,taɓa nan kaji Khalid zuciyana zafi take dan girman Allah ka karyata Tinanina karkaceman watace kake tare da ita,Wacece take kiran ka har ka kasheman waya.

 

 

 

Ido ya zubamata yace yanzu khadija Kawai dan kinji An kirani shine zaki daga Hankalin ki ? miyasa kike haka ne,Yan sanda nefa suka kamani Saboda ina tuki ina waya,Saboda jiya na sauka yau na dakko motana da niyyar zuwa daukar ki, To suna Tsaidani akwai wani dan Daudu dake kusa dasu yana zuwa kasuwa yana sayayya shinefa ya kirani kinson yanda suke karya Murya wane Wata Macen.

 

 

 

 

 

Ido ta zuba mai cikin gamsuwa da kalaman sa tare da fadin kayi Alkawari hakan ne ya faru?

 

 

 

Kai ya jinjinamata da fadin sosai kuwa.

 

 

 

A’Hankali ta rungume shi tana fadin na yarda muje.

 

 

 

Rungumeta yayi yace bara nakira Dr ya sallame mu naje gida nayi jinyar Abuna,Su Mummy ma suna waje.

 

 

 

Kai ta daga mai tana binshi da wani sassanya kallo ya fita bada jimawaba suka shigo su duka hankali tashe mommy tayi kanta tace. Auta Lfy ko, ga Daddy nan ma zasu taso da Yayan ku aunty kuma tace zatazo .

 

 

 

A shakw tace Mummy kice subar shi tinda ya dawo.

 

 

 

Dariya likitan yayi yace wato ciwon so ne ya kwantar dake.

 

 

 

Khalid ya zubamata ido tana sakin murmushi shi kau idonshi cike yake dam da hawayen da Kowa ya kasa gane wa.

 

 

 

Sallama su akai kiri kiri taki bin Mummy tabi Khalid suka fasa gidan su,

 

 

 

Tindaga palon suka tabbatar da kuluwa ta dawo dan kamshin girki kawai gidan keyi.

 

 

 

Suna shiga palon suka isketa goye da Danta tana jera Abinci.

 

 

 

Ko kallon inda suke bataiba tacihaba da hidimarta.

 

 

 

 

 

Cike da Mamaki Khadija ta kalli Khalid shima ita yake kallo.

 

 

 

Cikin isa da gadara tace kaga kuwa abinda na gani,yau ni kuluwa zata kalla ta watsar kamar taga kashi,tanaci tana sha daga kasana amma zataman wannan kallon banza,ban isa taman sannu da zuwa ba balle ta karɓi jikkana,Zuwa kauyen iskanci ya karamata koya.

 

 

 

 

 

A’Hankali yace kiyi hkr kinga baki da lfy.

 

 

 

Kamin ya karasa ta fizge daga hannusa ta isa inda Kuluwa ke tsaye Ta juya baya ta fizgota da karfi tare da fadin ke mikike haka,ni zaki.kallah ki watsar kedin diyar uban wacece karki manta ƙasana kike,kodan shinkafa da kaji sun rsataki zakimn.iskanci .

 

 

 

 

 

Kuluwa ta juye a natse tare da kama hannuwan khady ta sauke su daga jikinta ta kalleta kallo mai cike da ma’anoni,kamin tayi gajeran murmushi tace yaro yaro ne.Hadiza ina Umartar ki da karki kara kai hannuki jikina,aiki kalkashin ki bashine zai baki damar ciman fuska ba son ranki,domin nayi kanwa dake wajen ta ukku koma hudu,In takamar ki biyana kike nima ina bautamiki da gangar jikina ki kiyaye gaba.

 

 

 

 

 

Ihu khadija ta buga tana kallon khalid daya juya baya afusace tace Bazakai wani abu akai ba.

 

 

 

Hankali tashe yake kallonta yana kallon kuluwa data zubamai Mayun idonta bata ko kyaftawa fuskarta som ba walwala haka kuma ba damuwa..

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment