Akwai Sirri Hausa Novel Complete

Akwai Sirri Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*AKWAI SIRRI……!*

*PAID BOOK*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*

 

NA

 

_*ZEE BAWA*_

Da

_*HAJJA CE*_👈

 

 

*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE KARO NA BIYU.*

*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*

 

 

 

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*

*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”

*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*

Mun gwada mun gani 💯

Mun gani mun shaida 💯

Anyi mun gani 💯

MAGANIN SANYI

MAGANIN NONO

MAGANIN HIPS

MAGANIN SLIMMING

MAGANIN NANKARWA

GYARAN AMARE

GYARAN MAIJEGO

MALLAKAR MIJI KO MATA

SUBULU DA SCRUB

MAYUKA NA GYARAN JIKI

TURAREN WUTA

MATSI

MAGANIN NI’IMA

MAGANIN TSUMI

INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace

 

08142800199

07068558096

 

Page 1

 

Taron mutane ne cike a gabaki ɗaya illahirin wajan gudanar da taron, Idan aka yi duba daga gefen kudu da arewa ko’ina cike yake da manyan mutane masu mulki, ƴan siyasa da alamu suka nuna cewa na mutumci ne da kuma cikar kamala wacce ta bayyana a tattare dasu gaba ɗaya. Gefen kudu kuwa mata ne a zazzaune, yayin da gefen arewa kaff ɗin su maza ne, sannan daga bisani idan aka yi duba a ɓangaren gabas alarammomi ne zaune a kujerarsu ta alƙalanci wanda da dukkan alama musabaƙar karatun alƙur’ani mai girma ake gabatarwa a wannan waje. Gefen yamma kuma manyan-manyan malamai ne da manyan mutanen da aka gayyata zaune a gefen wajan suna kallan yadda ake gudanar da komai. Sanann ko wane tsakanin gefen maza da mata akwai shamakin da aka yi wanda ya tsare kusancin namijin dake wajan ba zai samu damar ƙarasawa gefen matan dake wajan ba, alokacin mutane suke ta cincirindon shigowa wajan taron. Bayan mafi yawa daga cikin mutanen da ake buƙatar ganinsu a wajan sun gama hallara a wajan cikin mintunan da bazasu wuce talatin ba aka fara gudanar da musabaƙar karatun alƙur’ani mai girma.

Kurman Allo Hausa Novel Complete

Lumshe idanuwanta tayi tana jin wani irin sanyi yana ratsa zuciyarta a lokacin da sanyayyen sautin karatun alƙur’ani ke shiga cikin kunnuwanta. Tsawon lokaci ta kasance a wannan yanayi wanda bata taɓa tsintar kanta a ciki ba sai idan tana sauraron karatun alƙur’ani mai girma. Tunda ya fara karatun har aka yi masa jaaa aka gama bai yi ɓata koda sau ɗaya ba. Sai bayan ya tashi daga gaban alƙalai sannan ta buɗe idanuwanta. Ajiyar zuciya ta sauƙe dan kuwa tabbas da akwai aiki a gabanta. Kiran sunan wanda zai gabatar da karatu na gaba aka yi ya tashi zuwa wajan ya fara karatu, wannan karon ma hakan ta kasance daga gareta. Mutum uku suka samu damar gabatar da karatun sannan aka tafi hutun wani ɗan lokaci domin azahar ta gabato sannan za’a ci abinci bayan anyi sallah sannan adawo acigaba da karatun.

 

Ɗaya daga cikin jagororin mata dake wajan ta nufota kai tsaye, sai da ta ƙaraso gareta sannan ta tsaya tana faɗin.

 

“Fannah ana buƙatar ganinki daga ciki idan babu damuwa yanzu muje nayi miki jagora zuwa wajan.” Murmushi wacce aka kira da Fannah tayi sannan ta amsa da cewa.

 

“Babu komai muje.” Jakarta ta ɗauka ƴar madaidaiciya sannan tabi bayan wannan matar da already ta fara tafiya zuwa hanyar da mata suke shige da ficensu. Tana biye da ita fuska yalwace da annuri suka ratsa ciki har izuwa ƙofar palourn da manyan mutane idan zasuyi taro a wajan suke meeting ko hutawa. Knocking ƙofar mai yi mata jagorancin tayi sannan taja baya ta dubi Fannah tana cewa.

 

“Zaki iya shiga idan an bada izinin shiga. Bari na koma bakin aiki na.” Kai kawai fannah ta gyaɗa mata ta tsaya daga bakin ƙofar tana jiran tsammani. Ƙamshin turaren da hancinta yake shaƙa yaso ya sanar mata wanda yake ciki, sai dai kasancewar waje ne na jama’a sosai yasa ƙamshin ya gauraya da sauran ƙamshin da mutanen da suke ratsa wajan ya sanya bata gama tsayarwa ranta shine a cikin wajan ba. Tana tsaye har aka bata izinin shiga ciki. A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar sannan ta sanya kai da sallama a bakinta. Muryar wanda taji ya amsa sallamar ne ya sanya duk wata fara’a da annashuwa dake kan fuskarta ta gushe lokaci guda, yanayin fuskarta ta canja ta tsinci kanta cikin matsanancin ɓacin rai da zafin zuciya.

 

Daƙyar ta iya ɗaga kanta ta dubi cikin wajan don tabbatarwa idanuwanta abunda kunnuwanta sukaji. Karaf suka haɗa alokacin data ɗaura idanuwanta akansa, yana sanye da shadda ɗinkin Babbar riga kansa sanye da hula zanna, bai cika saka babbar riga ba sai occasionally, hakan yasa yau ɗin ma suka yi masa kyau sosai, sannan suka amshi fatar jikinsa. Faɗuwar gabanta ce ta tsananta tana jin wani irin kunci a cikin ranta. Kauda kanta tayi izuwa gefe gudu domin bazata iya cigaba da kallon fuskarsa ba. Ƙarasawa tayi ta zauna can nesa dashi tayi ƙasa da kanta a hankali ta furta.

 

“Ina wuni?” Murmushi yake yi tun daga shigowarta har izuwa zamanta yana jin wani irin sanyi mai saka nutsuwa yana ratsa cikin ransa. Cike da kulawa ya amsa gaisuwar sannan ya ɗaura da faɗin.

 

“Sorry ban samu zuwa da wuri ba ina isowa ana tafiya hutu hope baki yi karatun naki ba already?” Tambaya yake mata cike da kulawa amma yanayin da takeji aranta babu daɗi, tana jin wani irin ɓacin rai. Daƙyar ta iya sarrafa ƙawa zucinta wajan ganin batayi amfani da dauɗaɗɗiyar kalmar da zata iya raunata jin kimarsa wajan bashi amsa ba. Cikin rawar zuciya da bugawar kirji fiye da kimar da ta dace ya buga ɗin take cewa.

 

“Da saura.” Haka kawai ta iya furtawa cikin son gajarta maganar dake tsakaninsu,

 

 

“Okay i got lucky kenan? I’m so happy da hakan ya kasance. Kinci abinci kuwa?” Kai ta girgiza masa.

 

“Ohhh! Dama nayi tunanin hakan shi yasa nayi miki order, zai iso nan bada jimawa ba insha Allah.” Ɗagowa tayi jin yanda yake magana cike da kulawa aranta tana faɗin ‘kamar dagaske’ Haɗa ido suka yi domin tunda ya ɗora nashi akan fuskarta ya kasa janyewa. Fannah kuwa tsantsar gaskiyar abunda yake faɗa mata tagani kwance akan fuskarsa, ita kam bazata iya musa masa ba idan har fuskarta tana kallon tasa hakan yasa ta kalli gefe guda sannan tace.

 

“No! Da ka barshi kawai.”

 

“Fannah..” Cike da karsashi ya kira sunanta cikin yanayin rashin jin daɗin yanda ta musa masa akan abinda yake ƙoƙarin yi mata. Ɗagowa tayi ta dubeshi ganin fara’ar dake kan fuskarsa ta kau sai da ta haɗiyi miyau. Ɗan matsawa tayi gefe a tsorace kamar wacce aka dewa zai kai mata duka. Kallo yake ƙare mata sannan daga bisani ya sauƙe ajiyar zuciya, iska ya ɗan furzar sannna yace.

 

“Idan na barshi yaya zaki yi? Haƙura zaki yi ki zauna da yunwa ko me? Ko zaki fita cikin mutane ki nemi abunda zakici ne?” Fannah ta hadiye wani yawu mai matuƙar daci tana jinsa ya ci gaba da cewa.

 

“Toh ni ko ɗaya acikin biyun nan bazan iya ɗauka ba, yanzu dai zanje nayi sallah kafin time ɗin abincin ya iso, kema kitashi kiyi sallah lokaci yayi sannan ki jirani anan ina dawowa.” Kai ta gyaɗa masa ya miƙe ya fice daga cikin wajan. Saida ya fita sannan tabi palourn da kallo tana karewa yadda komai na ciki yake. Babba ne sosai da kujeru zagaye dashi sai ƴar madaidaiciyar Tv da bata cika girma ba. Ƙofar da ta gani a ciki ita ta miƙe ta nufa tana murɗawa taga toilet ne. Alwala tayi ta fito taso ta fita waje tunda za’a yi jam’i harda mata tayi sallah sai dai tana tsoro domin tunda yace ta jira shi bataso ta saɓa hakan don zai iya riƙiɗe mata ya dawo Hamma Jalal ɗin data sani abaya. Ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta ƙarasa cikin palourn tayi sallar ta. minti bakwai bayan idarwarta ya shigo hannunshi ɗauke da packs na abinci ya ajiye agabanta.

 

“Kici ina tunanin baifi saura 30minute a koma daga hutun ba.” Kai ta gyaɗa masa sai dai takasa buɗe abincin, miƙewa ya sake yi yana cewa.

 

“Bari na nemi Kawu.” Bata kai ga gyaɗa masa kai ba ya fice daga waje tasan yayi hakan ne domin yabata damar samun cin abincin ta. Buɗe abincin tayi cike da nutsuwa ta fara ci, kusan 10minute saiga shi ya dawo da Wani matashin magidanci da bazai wuce shekara arba’in zuwa da uku ba, sannan akwai ɗibar kamanni a tsakaninsu duk su ukun. Ƙarasowa ciki suka yi, Kawu ya zauna shima ya jawo pack ɗaya na abincin yana faɗin.

 

“Ai ina ta nemanki ashe kina nan? na kira wayarki baki ɗauka ba.” Abincin ta rufe duk da bata ƙoshi ba tana amsawa Kawun.

 

“Tun da zamu shigo wajan taron nan na sakata a silent shi yasa banji ba.” Fannah ta faɗa.

 

“Ba dai har kin ƙoshi da abincin ba?” Cewar Kawun. Kai ta gyaɗa alamun eh. Murmushi mai cike da takaici Hamma Jalal yayi yasan cewa ta rufe ne saboda kasancewar yana wajan. Bai sake bi takanta ba har Kawu ya gama ci ya miƙe kasancewar lokacin hutun ya ƙare.

 

“Bari na koma saboda wajan zamana idan aka kammala dawowa zai yi wahala na samu, yafi naje da wuri kafin a tsare min.”

 

“Muma yanzu zamu fito in sha Allah.” Hamma Jalal ya faɗa shi kuma Kawu ya sanya kai ya fice. Kallonta yayi sannan yace.

 

“Fannah buɗe abinci kici.” Yayi maganar cike da bada umarni sannan kuma babu wasa. Hakan yasa ta jawo abincin gabanta dan bataga fuskar da zata musa masa ba. Yanayin yanda takecin abincin ya sanya shi kauda kai domin yasan tana hakan ne kawai don ta sake tunzura shi a tunaninsa. Lokaci yana tafiya sai dai ba ta da niyar kammalawa saboda yanayin da take ɗiban abincin.

 

“Idan kin gama ki tashi muje.” Ya faɗa, da sauri ta miƙe kamar wacce take kan ƙaya ta zari jakarta. Bai yi ƙoƙarin miƙewa ba hakan yasa ta juyo ta kalleshi domin bata buƙatar yin wani laifi dan tasan shi komai a wajansa idan tayi toh laifi ne. Kallon packs ɗin da ta bari a wajan yayi hakan yasata dawowa ta tattara komai ta riƙe. Idanuwansa suna kan hannunta wanda yastun suka sha maroon ɗin lalle na sale-tape. Hannunsa ya kai ya riƙo hannunta, a razane ta juya tana dubansa alokacin da idanuwanta suka sauƙa acikin nasa ji tayi duk gaɓoɓin jikinta suna neman su susuce daga mahaɗin su. Da sauri ta fara ƙoƙarin zare hannunta sai dai bai bata damar yin hakan ba, narai-narai tayi da idanuwa tana jin wani irin yanayi na rashin jin daɗi a cikin ranta. Hawaye ya cika idanunta taff ƙadan suke jira su zubo zuwa sama kumatunta. A hankali ya murza hannunta sannan ya matse su a cikin nasa ya ɗaga idanuwansa zuwa kan fuskarta, ganin yanayin da ta shiga ya sanya jikinsa yin wani irin sanyi. Sakar mata hannun ya yi dan ya san gab take da yi masa kuka. Ita kuwa yana sakin ta tayi saurin mai da hannunta cikin hijab ta miƙe ta fice daga palourn. Bin bayanta yayi da kallo yarasa yaushe al’amura zasu daidaita, ya rasa sai yaushe Fannah zata cire wannan haushin ko yace tsana da take masa a cikin ranta. Jiki babu ƙwari ya miƙe ya fita shima sai dai ko ƙyallinta bai gani ba hakan yasa ya shige wajan taron. Yana shiga wani daga cikin jagororin musabaƙar maza ya iso gareshi cike da girmamawa ya gaishe shi sannan yayi masa iso zuwa seat ɗinsa dake a gefen arewa a cikin kujerun da aka ajewa manyan malamai da wasu daga cikin manyan mutanen da suka samu hallatar musabaƙar. Kujerunsu haɗe da sunansu a rubuce. Bai zauna ba sai da yabi wajan manyan malamai da wasu daga cikin mutanen dake layin suka gaisa, yanayin yanda suke gaisawa cike da fara’a da girmamawa tun daga kan manyan malaman addini zuwa ƙanana za’a gane wani mataki mai muhimmanci ya taka acikin al’umma. Wala Allah a cikin malaman ne ko kuma cikin mutanen dake da nagarta a wajan.

 

Sai da suka gama gaisawa sannan ya zauna a kujerarsa wacce aka rubuta Dr Abdul-jalal Sadis Moddibo. Tuni aka ci gaba da gudanar da abinda ya haɗa taron har zuwa lokacin sallar la’asar, shima haka aka yi wato aka tafi hutun ƙaramin lokaci. Acan palourn Fannah ta zauna kamar lokacin da tayi sallar azahar sanann suka dawo. Sai wajan karfe 6pm kafin aka tashi har lokacin kuma Fannah bata yi nata karatun ba sai dai sama da rabin wanda zasu gudanar da karatun sunyi sannan kuma ana saka ran cewa zuwa gobe za’a kammala gabaki ɗaya.

 

Fannah tana zaune a cikin wajan har mafi yawan mutane suka watse, Kawu take jira yazo su tafi masauƙin su sai dai bata hangeshi ba tsawon lokaci. Har ya zama saura ƴan tsirarrun mutane a wajan, lokacin ne ta fara damuwa na rashin ganin Kawu da ba ta yi ba. Sai a sannan wayarta ta fara ringi tana amsawa Kawu yace ta fito ta sameshi a harabar wajan taron yana jiran ta.

 

Miƙewa tayi ta fita da sauri domin magriba ta ƙarato san samu kuma su isa masauƙin su kafin lokacin sallar magriba. Dube-Dube ta fara yi yanda zata hango Kawun nata, sai dai Idanuwanta basu ganshi ba sai Hamma Jalal da suka gano mata a sa’ilin da yake fitowa daga wani ofishin meeting tare da sauran manyan malamai da kuma sauran manyan mutane da ga dukkan alamu ana tashi meeting suka shiga. Ɓuya tayi a jikin wata mota saboda kar ya ganta dan ita kam tafi so sai ya tafi kafin ta fito. Wayarta ce ta fara ruri ganin Kawu ne ya sanyata amasawa da sauri.

 

“Fannah kinata ina ne?” Tace,

 

“Kawu gani na fito amma ban ganka ba.” Kawun yace,

 

“Toh ki sake dubawa yanzu gamu nan a tsakiyar wajen muna jiranki.” Jin ya ambaci gamu ya sanyata a matsanantacciyar faɗuwar gaba, daƙyar ta iya daurewa ta fito daga maɓoyarta. Ganin su jikin mota shi da Hamma Jalal ya ƙara tsananta mata faɗuwar gaban da takeyi. Ta isa gare su jiki a sanyaye, Hamma Jalal yana ganinta yace.

 

“Toh Kawu muje koh?” Kawu yace.

 

“Muje ina kuma Jalal?” Hamma jalal yace.

 

“Gida na acan zaku sauƙa ai.” Kawu ya yi saurin faɗin.

 

“A’a-A’a haram Abdul-jalal, ni kan bazan iya sauƙa a gidanka ba sai dai ita kaja ta kuje tare ita keda masauƙi a gidanka amma ni tun kafin nazo nan na gama kama masauƙin.” Gaban Fannah ya tsannata faɗuwa, da sauri ta fara girgizawa Kawu kai alamar karya barta amma sai yi yayi kamar bai ganta ba yace.

 

“Kuje nima yanzu zan kama hanya.” Ya juya zai wuce tayi saurin cafke rigar sa jikinta yana rawa. Juyowa yayi ya dubeta da mamaki a fuskarsa yake cewa.

 

“Ke meye hakan kuma? nace kuje tare da Hamma koh?” Girgiza kai ta keyi a yayin da hawaye ya fara sauƙa akan kuncinta. Fannah jin zuciyarta take kamar zata kome idan har aka ce dole ta bishi tabbas zata iya haɗiyar zuciya a wajan dan gara ta kwana a titi a dandagaryar ƙasa da ace a gidan Hamma Jalal zata kwana, ita kam babu wani gida data tsana a rayuwarta kamar gidansa wanda ko amafarki bata ƙaunar sake ganinta a cikin gidansa. Kasa cewa komai tayi nan da nan kuka ya ƙwace mata cikin kukanta ta fara faɗin…….

 

*BAQEER*

Ayusher Muhd

Umm Asghar

 

*KURMAN ALLO*

Asmy b Aliyu

Jidda Aliyu

 

*AKWAI SIRRI*

Zee Bawa

Hajja ce

 

*MUTALLAB ASAD*

Nana Diso

Billy S Fari

 

*KULUWA*

Zee yabour

Sadiya Dan

 

Duka Biyar ɗin akan 2k

Hudu 1600

Uku 1200

Biyu 800

Ɗaya 500

Post a Comment

Previous Post Next Post