Littafan Hausa Novels

Kurman Allo Hausa Novel Complete

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace
Written by Hausa_Novels

Kurman Allo Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

*KURMAN ALLO*

(A beautiful Love Story)

Na

JEEDDAH ALIYU

&

ASMY B ALIYU

 

#Love Story

#Gwagwarmaya

#Team Tagwaye

 

001.

 

*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*

*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*

 

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*

*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”

*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*

Mun gwada mun gani 💯

Mun gani mun shaida 💯

Anyi mun gani 💯

MAGANIN SANYI

MAGANIN NONO

MAGANIN HIPS

MAGANIN SLIMMING

MAGANIN NANKARWA

GYARAN AMARE

GYARAN MAIJEGO

MALLAKAR MIJI KO MATA

SUBULU DA SCRUB

MAYUKA NA GYARAN JIKI

TURAREN WUTA

MATSI

MAGANIN NI’IMA

MAGANIN TSUMI

INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

 

08142800199

07068558096

 

Taƙure take can ƙarshen gado ta sunne kanta tsakanin guiwayoyinta biyu. Wani irin kuka take yi wanda sautinsa baya fita sosai a dalili dusashewa da muryata tayi. Jikinta lulluɓe da lafayya pink and white colour ƙafafuwanta ɗauke da lalle na salatif maroon color sai ɗan baƙi kaɗan da aka bi gefe da gefen ƙafafuwan nata dashi. Bata taɓa tsammani ko hasashe ƙaddarar ta za ta kawo ta izuwa wannan mataki ba. Ko kuma matsayi da yau ta riske kanta a ciki. Abu ne da ta kasa yarda da faruwarsa, take ganinsa tamkar a mafalkinta, ga wasu tarin tambayoyi da ke ta shawagi a cikin ƙwaƙwalwarta. Shin miyasa mahaifinta ya kasa yarda da cewa wannan aure da ya zama sila kuma jagora haɓakawa ba abu mai yiwuwa bane? Ta rantse ta kuma sake maida rantsuwa koda sama da ƙasa za ta haɗe ba za ta taɓa karɓa AB (Abba Bashir )a matsayin mijin aurenta ba. Wannan ai abin kunya ne babba a gareta kai har ma dashi kansa AB ɗin. Ta ya za su tashi a gida ɗaya uba ɗaya sannan kuma uwa ɗaya ce ta raine su, ta tarbiyyarta dasu da kalar tarbiyya ɗaya sai kawai ta wayi gari ta tsinci kanta a gidansa kuma a matsayin matar aurensa. Haba Wannan kwamacala ba da ita za a yi ta ba. Dole ta nemowa kanta mafita. Ko za ta iya haƙura da komai ban da zama da AB a matsayin mijinta. Aure tsakani ta dashi ya haramta duk da addini Musulunci bai haramta ba amma ita ta haramtawa kanta shi.

Tun sanda ƙanwar mahaifinta ta shigo da ita wannan gida kuma cikin wannan ɗaki ta zaunar da ta ƙara yi mata nasiha ta fita, tawagar ƙawayeta ‘yan rakkiyar amarya ke bata baki amma kuma tamkar suna zugata ne. Ita kaɗai za ta iya misalta adadin raɗaɗin da take ji a ƙahon zuciyarta.

“Haba Sady-B(Sadiya Bashir)wannan kukan naki ya yi yawa tun gida ki ke ta wannan kukan, da kuka zai iya sauya miki ƙaddararki da ya sauya ta daga safe zuwa dare nan. Sai dai kash! bakin alƙalami ya riga da ya bushe dole ki rungume ƙaddararki. AB shine mijin da ƙaddararki ta zaɓar miki.

Ɗaya daga cikin ƙawaye nata ta faɗa da sigar son ta rarrashe ta ko Allah zai sa ta daina wannan kukan na fitar hankali.

“Ba za ki taɓa fahimtar hali da nake ciki ba Maryam Abdallah, taya Daddy yake tunani zan samu farin ciki a gun mutumin da nake masa kallo a matsayin ɗan uwana wanda uba ɗaya ya haife mu. Wallahi-tallahi Daddy ya tafka babban kuskure ya zantar da hukunci cikin fushi ba tare da la’akari da irin abinda fushin nasa zai haifar ba. Ban yarda da wannan aure ba, ba kuma zan taɓa amincewa dashi ba. Idan har Ya Abba yaƙi kawo ƙarshen wannan bahagon aure to ni nan da kaina zan kawo ƙarshensa, ban damu da tsinuwa da Daddy yake ikirarin zai min ba.

Har Maryam Abdallah ta buɗe baki da zimmar sake magana suka ji shigowar ango tare da abokansa.

Tun sanda suka shigo ɗakin shi da abokansa bai kalli gun da amarya tasa take ba, yana tunani taya zai iya kallon ƙanwarsa Sadiya Bashir a matsayin matar aurensa. Miyasa ƙaddara za ta zo musu ta wannan siga duk da yaso ya danne zuciyarsa ya yiwa Daddynsa biyayya wanda ya kasance duniyarsa, kamar yadda ya saba yi masa a can baya, sai dai shigowar da ya yi yanzu ya kuma hango Sadiya a taƙure sai ya ji wani irin kololon baƙin ciki ya dunƙule masa a maƙoshinsa. Ya yi kuka har sai da hawaye idanuwansa suka ƙafe ya dawo kukan zuci wanda har yanzu yake kan yi. Wannan wacce irin baƙar ƙaddara ce ta yiwa rayuwarsa shigar kutsu.

Tabo kafaɗarsa da Al-Ameen ya yi ya dawo dashi daga duniyar nema da lallube da ya afka. Yayin da Al-Ameen ya ci-gaba da faɗin “AB ga ƙanwarka nan Sadiya a yau matsayin ta ya haura wanda kasanta dashi a can baya, kada ku yi la’akari da alaƙar ku ta can baya ku yi duba izuwa da wannan da a yanzu ku ke kai. Dukkanku kusan halaye juna kuma kusan like and dislikes ɗin junanku tun da already kun tashi a karkashin inuwa guda ne, sai kuma gashi Ubangiji masani sirrikan fili da na boye ya sake kawo ku wani mataki na daban wanda ku dukkanku ba ku taɓa tunani riskar kanku a cikinsa ba. Koda kuwa a mafalki ne, tun anan ya kamata kusan cewa ƙudurar Ubangiji tana da yawa sannan shi kaɗai yasan hikimar da yasa aure ya kasance a tsakanin ku.

Nurhaan Hausa Novel Complete

Har Al-Ameen ya dasa aya a zance sa babu wata kalma guda ɗaya kwakwara da AB zai buga ƙirji ya ce ya ji, domin hankalinsa ga baki ɗaya ya ta’allaka ne ga tunani makomar rayuwarsa ta nan gaba, domin duk abunda ya faru dashi kafin zuwan wannan rana shafin vasiline ne a bisa wacce zai tunƙara anan gaba.

Kusan kowanne daga cikin abokansa su biyar ba wanda bai tofa albarkacin bakinsa ba, domin sun san ta yadda auren abokin nasu da ƙanwarsa ya kasance abu ne wanda kafin hankali da tunani su karɓe sa za a sha gwagwarmaya.

Abdulkarim Safana ne ya rufe musu da addu’a kana abokan ango suka sallame ƙawaye amarya da sallama mai tsoka, daga abokan ango har ƙawaye amarya basu sami damar taɓa barkwanci a tsakaninsu ba kamar yadda aka saba ya yi kawo amarya ɗakinta, a wannan karon su kansu abokan ango da ƙawaye amarya aure ne da ya zo musu very complicated.

Bayan AB ya yi musu rakkiya zuwa farfajiyar gida idan suka yi parking motacin su kana ya dawo sai da ya rurrufe kofofi tare da kashe bulbs ɗin dake kunne kana ya wuce ɗakinsa ya yi wanka, ya saka fararen pajamas ƙafarsa sanye da flip flops sai da ya biya ta main parlor ya ɗauki leda da ya baro kan centre table kana ya wuce ɗakin amaryarsa.

Bakinsa dauke da sallama ya tura ƙofa yayin da shigowarsa tsakiyar ɗakin ya yi daidai da fitowar Sadiya daga maɓoyarta cikin curtain ƙaifaffiyar wuƙa dake riƙe da hannunta ta dabawa AB da dukkan ƙarfinta a daidai gefen cikinsa, kamar daga sama ya ji shigar wuƙa a cikinsa zaro wuƙar da Sadiya tayi ya haddasa wa AB saki rikitaccen ihu cikin tsanani azaba ya dafe gun da ta caka yayin da jini ya dinga zuba kamar an buɗe famfo. “Ka yi haƙuri Ya Abba banso haka ta kasance tsakanin mu ba sai dai banida wani zaɓi da ya wuce wannan. Na tabbata koda duniya za ta taro akanka ba za ka taɓa warware wannan baƙin auren naka dake kaina ba. A dalili tsanani biyayyar da ka ke yiwa Daddy za ka zaɓi ka dawwama a baƙin ciki, muddin Daddy zai kasance a farin ciki. Ni kuma bani da ƙarfin imani da zan iya irin wannan biyayya taka, kasancewar ina so na rayuwa cikin farin ciki, kamar kowacce mace dake ɗakin aure. Wannan buri nawa tuni ya bi ruwa gani ba zan taɓa samun cikar muradina ba na yanke shawara gara na kashe ka idan yaso nima a kashe ni, a lokaci Daddy zai

farga ya gane babban kuskure da ya tafka.

Sadiya tayi magana cikin muryar kuka dake bayyanar da irin tsanani baƙin ciki da take ciki, sannu a hankali AB ya sulale ƙasa ya zube guiwayoyinsa kan tiles da kyar ya iya buɗe bakinsa saboda irin raɗaɗi da yake ji cikinsa na masa “Miyasa za ki yi haka Sadiya miyasa ki ka zaɓi wannan gurguwar hanya domin dawo da farin ciki da ki ke hasashen kin rasa?”

Ita ma Sadiya zubewa tayi gabansa tana wani irin gunji kuka na fitar hayyaci “Bani da zaɓi ne Ya Abba na gwammace na kare rayuwata a gidan kaso da na rayu da igiyar aurenka. Babu wani babban mugun abu a wurina da yawuce wannan aure naka.

Kasa magana Abba ya yi saboda jini da ya soma bugar dashi, a hankali ya kai kwance, har zuwa lokaci Sadiya tana durƙushe a gabansa tana kallo yadda ransa ke fita daga gangar jikinsa, sai kuma wani irin tsoro ya fara shigarta tai sauri jefar da wuƙar hannunta, tayi kansa tana jijjiga shi gami da kiran sunansa “Ya Abba ka tashi dan girman Allah ka tashi kada ka mutu Ya Abba, wayyo Allah na shiga uku na kashe sa Ya Abbaaaaa!

Ta ƙarashe magana cikin sauti mai amon gaske. Can kuma ta miƙe ga baki ɗaya ta gama fita hayyacinta ta ɗora hannu aka sai ta kai bango gabas ta dawo na yamma tana gunji kuka. Sai kuma ta nufi wayarta dake kan bedside drawer tayi dialling number best friend ɗinsa Abdulkarim Safana.

A lokaci har Abdulkarim ya yi shirin kwanciya bacci sai dai bai kai da yi bacci ba, kira nata ya shigo wayarsa nan take ya ji wani irin mashahurin faduwar gaba jikinsa ya ɗauki rawa ya ji wani kalar sanyi-sanyi yana huda kasusuwan jikinsa, da kyar ya tattaru jarumtarsa ya furta “Hello Sadiya lafiya ki ke kira na a daidai wannan lokacin??

“Na kashe shi wallahi na kashe shi.

“Wa ki ka kashe Sadiya Dan Allah ki faɗa min wa ki ka kashe?

Yayin da Sadiya sai maimaita kalmar ta kashe shi take yi, hakan kuwa ba ƙaramin tashin hankali Abdulkarim ya shiga ba, ya wutsillo daga gado yana ture duvet daidai Sadiya tana hanging up abu na farko da ya fara shi ne ɗaukar car key ɗinsa ko takalma bai tsaya sakawa ƙafafunsa ba, ya fice da wani kalar sauri kamar zai tashi sama tun kafin ya ƙarasa parking lot ya shiga kwaɗawa maigadi kira “Malam Habu! Malam Habu zo ka buɗe min gate.

Sadiya tana kyalla ido taga yadda jini jikin AB yake kwance male-male akan tiles ta ƙara tsorata sai lokaci wata irin nadama ta soma shigarta, tsoron irin hukunci da zai biyo kanta ya shige ta, ƙwaƙwalwarta ta fara mata refreshing irin hukunci da ake zantarwa da duk wanda ya yi kisan kai shima kashe shi za a yi “tabbas kashe ni za a yi ko Daddy ba zai taɓa bari na a raye ba kawai ki gudu Sadiya ki gudu ki tseratar da rayuwarki wani bangare na zuciyarta ya umarce ta, ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗauki lafayyarta da ta cire dake ajiye a gefen gado bata tsaya naɗa ta ba ta lulluɓa ta kawai a jikinta dama wayarta na riƙe a hannunta, da gudu ta fice daga ɗakin, har ta kai main parlor sai ta tuna da dole tana buƙatar kuɗi, ɗakinsa ta shiga wallet ɗinsa da wayarsa na ajiye akan bedside drawer jikinta sai faman kakkarwa yake ta buɗe wallet ɗin gaba ɗaya kuɗaɗen dake ciki ta kwashe ta fice da gudu. Idan Allah ya taimake ta maigadi yana ɗakinsa cikin sanɗa ta zare sakata dake jikin ƙofa, ta yanka da gudu ceton rai tana dab da isa titi ta hango motar Abdulkarim Safana kasancewar tsakani gidansu zuwa titi akwai tazara sosai kuma sabuwar unguwa ce babu mutane sosai. Da sauri ta laɓe jikin gini wani gida da ba a ƙarasa gininsa ba, har sai da taga ya wuce kana ta fito ta ci-gaba da tafiya mai haɗe da gudu-gudu.

Uban horn ɗin da Abdulkarim Safana ke dannawa ya yi nasarar tashe da maigadi dama yana ciki mutane masu nauyi bacci, a tsorace ya dauko adda cikin sanɗa ya fito daga ɗakinsa, zuciyarsa cike da tu’ajjabin waye yake musu horn ciki silasili dare. Ƙaramar ƙofar da ya gani a buɗe ya haifar masa da matsanancin faɗuwar gaba alhali yasan kafin ya kwanta sai da ya rufe ta. Abdulkarim yana gani zai ɓata masa lokaci ya buɗe murfin mota ya fito ta ƙaramar ƙofa dake buɗe ya shigo yaga maigadi tsaye ya dafe da kofa da hannunsa sai wuƙi-wuƙi yake da idanuwa a fusace ya daka mishi tsawa kasancewar Abdulkarim Safana ba bako bane a wurinsa ya hanzarta buɗe masa gate, kana ya Abdulkarim ya shigo da mota sai dab da entrance ɗin gidan ya yi parking ya fice da gudu ya tura ƙofar shiga main parlor. Da gudu ya haura sama firstly ɗakin Ab ya fara buɗewa yaga ba kowa a ciki dole ya dawo na Sadiya buɗe ƙofarsa ke da wuya ya hango amininsa kwance cikin jini “Innalillahi wa’inna illahim raji’um! Kalma ta farko da Abdulkarim ya fara furtawa kafin ya isa ga gawar Ab, ga baki ɗaya Abdulkarim ya ruɗe ya rasa ta ina zai fara jikinsa ko’ina rawa yake wannan shine karonsa na farko da ya fara gani gawa ido da ido. Zubewa ya yi gefen Ab ya sa wani irin kuka mai ban tausayi da taɓa zuciya, kafin ya kai hannunsa ya taɓa kafaɗar Ab ciki rikitatciya murya ya kira sunansa “Ab! Ab!Abba Dan Allah ka tashi karka yi min haka Abba Dan Allah kada ka mutu, kasani mutuwarka za ta taɓa zukata da dama ka tashi Abbaaaaa!

Sai kuma ya tashi a rikice zuwa farfajiyar gida ya kwallawa maigadi kira wanda tun shigowar Abdulkarim jikinshi ya bashi babu lafiya, shiyasa kasa komawa daƙinsa ya yi tsaye jugun! Da gudunsa ya zo suka ciccibe Abba zuwa mota duk da dukkansu biyu sun gama amincewa da Ab ya mutu saboda ko jikinsa ya yi wani irin sanyi ga kuma uban jini jikinsa da ya yi kace-kace a ɗakin. Maigadi da ya gaza haƙuri sai da ya tambaya gari ya haka ta faru duka bai fi two hours da rabuwarsu ace har an kashe shi waye yai masa wannan aika-aikar.

“Amaryarsa ce.

Abinda kaɗai Abdulkarim Safana ya iya furtawa maigadi shima gudu kada ya bar shi cikin tunani kaitsaye softcare private hospital ya nufa duk da yana da tabbaci Abba ya riga da ya mutu amma don ya kara tabbatarwa ya kawo shi asibiti. Bayan an shigar dashi ɗaki duba marasa lafiya likitoci suka ce dole sai an kira ‘yan sanda saboda murder case ne sai lokaci Abdulkarim ya yi tunani ya kira Daddy domin bai ga amfani boye masa ba.

Alhaji Bashir yana kwance akan katafaren gadon sa da ke bedroom ɗinsa a gefensa maidakinsa ce Hajiya Mariya bacci suke cikin kwanciyar hankali, can cikin bacci nasu suka ji ring ɗin ɗaya daga wayoyin Alhaji Bashir, kusan su dukka a tare suka falka. Alhaji Bashir mutum ne da baya taɓa nisanta da wayarsa a cewarsa waya tafi amfani a cikin dare domin wani zai iya shiga matsala ya kuma nemi taimakon ka, hakazalika kai ma za ka iya shiga matsala shiyasa koda yaushe wayoyinsa suna ajiye kusa dashi. Ya zabura da sauri ya tashi zaune ya tabbata koma waye ya kira sa a irin wannan lokaci ba lafiya ba. Yana miƙa hannunsa ya dauko wayar kiran yana tsinkewa sai kawai ya ji wani irin faɗuwar gaba, har sai da ya kai da furta “Hasbunallahu wal-imaal wakil! A bayyane.

“Lafiya Alhaji?

Hajiya Mariya ta faɗa tana kallon mijinta da fuskarsa ta fara jiƙewa da gumi tamkar babu Ac a ɗakin, yana daukar wayar wani kira na sake shigowa, “Abdulkarim!

Ya faɗa a bayyane sai kuma ya yi gaggawar receiving “Assalamu alaikum Abdulkar……

“Daddy ka zo yanzu-yanzu nan Softcare private hospital Allah ya yiwa AB rasuwa.

“Innalillahi wa’inna illahim raji’um! Abdulkarim me ka ke cewa ne?

“Daddy Abba ya rasu Abba ya mutu Sadiya ta kashe mana Abba.

Tsanani shock da Daddy ya shiga jikinsa ya ɗauki rawa bai san sanda wayar dake maƙale a kunnensa ta zame ta faɗo, firgici da tashin hankali gami da razanarwa suka taro lokaci guda suka yi masa dirar makiya, yadda yake ta maimaita “innalillahi wa’inna illahim raji’um! Yasa ita ma Hajiya Mariya jikinta ya shiga kakkarwa da kyar ta iya haɗa kalmar “la….fi….ya…Alha…ji??

Shiru Daddy ya yi yayin da bugawar zuciyarsa ya tsananta sai da ya sauka daga gado kafin ya iya furta “Allah ya yiwa Abba rasuwa kuma ‘yarki ce ta kashe shi.

“Innalillahi wa’inna illahim raji’um! Na shiga uku ni Mariya wannan wacce irin masifa ce? Sadiya ce za ta yi kisan kai kuma ta rasa wanda za ta kashe sai ɗan uwata yayanta, mijinta Ya Allah kada ka jarabce mu da wannan baƙar ƙaddara.

Nan take Hajiya Mariya ta rikice da wani irin kuka tana sambatu Alhaji Bashir ya ɗauki key ɗin mota ya fice da sauri Hajiya Mariya ta sauko daga gado ta bishi a baya sai da ta kai ƙofar fita ta tuna da bata suturta jikinta ba gashi kuma kayan bacci ne take sanye dasu. Duk girman jikinta haka ta kwasa da gudu ta shiga bedroom ɗinta ta sako hijabinta na sallah, koda ta fito compound har Daddy ya jawo mota tsananin tashin hankali da suke ciki ba zai misaltu ba. Koda suka iso Softcare kowanne su zuciyarsa na dab da bugawa. Zuwan Daddy yasa likitoci suka dukufa duba Abba duk da suma suna da tabbaci ya riga da ya mutu, kawai dai za su duba shine saboda yana aikinsu.

Sadiya tana isowa bakin titi mutum na farko da ta fara kira Hafiz Sale shine wanda za ta aura a kuma wurin ɗaurin aure nasu ne rashe ya juye da mujiya ƙaddara ta faɗa mata igiyar aure ta ratse tsakaninta da yayanta. Sai da ta jeranta masa kira yafi goma kafin ta samu ya yi picking cikin dassashiyar murya ya kira sunanta saboda kwata-kwata babu alamar bacci a idanuwansa ya kasa karɓar ƙaddarar rasa ta da ya yi kwatsam sai ga kiranta ya shigo wayarsa.

“Hafeez Dan Allah ka zo ka taimake ni ina cikin tashin hankali idan ba ka taimaka min ba, bansan ina na nufa ba.

“Subhanalillah! Sadiya meke faruwa ne ki natsu ki yi min bayani?

“Maganar nan ba za ta yiyuwa a waya ba.

“Shi kenan kina ina gani nan zuwa.

“Ina tsaye a bakin titi gidan Ya Abba dan Allah Hafeez karka bata lokaci domin komai zai iya faruwa.

Kusan ten minutes da yi wayarsu sai gashi ya zo, jikin Sadiya yana rawa ta buɗe mota ta shiga, Hafeez Sale ya ja motar da gudu ya halba kan titi sai da suka yi tafiya da nisa kafin ya juya ya kalleta da idanuwansa da suka soye ya ce “faɗa min dalili da yasa ki ka fito gidan mijinki a darenku na farko ki ka rasa wanda za ki nemi taimakon sai ni??

Wasu zafafan hawaye ne suka wanke mata kumatu ta kasa magana saboda batasan yadda Hafeez Sale zai karɓi al’amarin ba.

 

#Love Story 2023/2024

#Jiddah Aliyu

#Asmy b Aliyu

#Team tagwaye novels

#Kurman Allo.

 

*BAQEER*

Ayusher Muhd

Umm Asghar

 

*KURMAN ALLO*

Asmy b Aliyu

Jidda Aliyu

 

*AKWAI SIRRI*

Zee Bawa

Hajja ce

 

*MUTALLAB ASAD*

Nana Diso

Billy S Fari

 

*KULUWA*

Zee yabour

Sadiya Dan

 

Duka Biyar ɗin akan 2k

Hudu 1600

Uku 1200

Biyu 800

Ɗaya 500

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment