Kaidin Mace Hausa Novel Complete
𝐊𝐀𝐈D𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐂𝐄
✍𝐵𝐼𝑆𝑀𝐼𝐿𝐿𝐴𝐻𝐼𝑅𝐴𝐻𝑀𝐴𝑁𝑈𝑁 𝑅𝐴𝐻𝐼𝑀
E 1-2
ABUJA.
“Neehal!Neehal!.
Tunani na ne ya katse sakamakon muryar Ramlat data ratsa dodon kunne na. A hanzarce na juyo ina kallanta. “Wai tunanin me ki ke haka ne gashi mun iso tun ɗazu?” wannan kalma data fada mun iso yasa na juya ina kallan ƙaton ginin da muke tsaye a gaban shi da aka rubuta A&E INDUSTRIES a gaban ginin da kuma katon Ad ɗinshi gefe. A take naji tsoro ya shige ni duba da irin mutanen da naga suna kai kawo a wajen. Suturar jikina na kalla da sam bata dace da gurin ba . Jiki a sanyaye nake bin kayan jikin nawa da kallo da sukai mugun koɗewa tunda ba wata sutura ce dani ba ishashshiya, dan basu fi a ƙirga ba, wannan na jikina sune sababbi na zuwa unguwa. Murya ɗan sahun da muka ɗauko mukaji cikin faɗa yana cewa ” Dalla Malamai ku sauka haka mana, tun ɗazu na kawo ku guri kuma fitar ta gagara, da kunsan cewa nan ɗin ba irin gurin ku bane kuka zo?, shi talaka in baiyi bara da maula bayajin dadɗi a rayuwanshi ,a nemi nakai baza a nema ba” . A harzuƙe Ramlat ta juyu kanshi dan mayar masa da martani nai suarin riƙe ta ina girgiza mata kai.
Maza Biyu Hausa Novel Complete
Tashin hankali sam ba namu bane yanzu ,kuma ai gaskiya ya faɗa neman muka zo yi amma ba irin wanda yake tunani ba. ƙwafa tayi ta fito daga cikin ɗan sawun nashi a zuciye. Murmushi nayi dabai kai zuci ba ina kallan ɗan adaidaitan nace masa ” kayi hakuri don Allah, nawa ne kuɗin?” Juyuwa ya yi ya kalleni, kallo mai cike da izgilanci ya ce ” ki barshi kawai, dan banga alamum kuna dashi ba, dama dai san zuciyar ku yasa baku gayamin baku da ƙudin mota ba saida mukazo zaku tsaya kuna tunani tunanin banza” Ba ƙaramin ciwo maganan tashi tayi min ba. Duk da haka Murmushi na ƙirƙira da bai kai zuci ba na fito daga cikin ɗan sawun ina masa godiya tare da miƙa masa naira ɗari biyar, fisgar kuɗin ya yi daga hannuna yaja motar da mugun gudu .
A can bakin ƙofa na hango Ramlat kaman zatayi bindiga saboda haushi sai bina take da mugun kallo. Da murmushin dai kan fuskata na ƙaraso gabanta . A fusace ta ce ” wai ke wane irin hakuri ne dake haka?, shikenan kuma dan anga kina da hakuri sai ko wane jaki da doki ya dinga taka ki yanda yaga dama? Haba ,walahi da kin barni da ɗan iska sai na gaya masa maganan da har ya mutu bai manta dani ba a duniyar nan. Talauci hauka ne?” Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi cikin sanyi nace ” Ni banga abin ɓacin rai ba tunda gaskiya ya faɗa ,sannan kuma mu muka ɓata masa lokaci bamu saukar masa a mota ba da wuri” .Wani irin kallo ta yi min tanaji tamkar ta zubamin mari. Bata ƙara cewa komai ba ta wuce a fusace cikin ginin ta barni a tsaye ina binta da kallo fuskata ɗauke da murmushin da a yanzu ya zame min jiki, duk irin bacin ran da nake ciki ba dai ka gani a fuskata ba sai dai murmushi. Numfashi naja tare da lumshe ido na fesar kafin na rufa mata baya.
Tafkeken building ne da baka iya hango karshen sa. Wajen reception muka nufa Ramlat ta samu guri ta zauna saboda rakoni ta yi. Matar dake zaune bayan taberin nake kallo sanye cikin suit na mata riga da sket da sukayi mata kyau sosai sai naji duk nakara tsargar kaina. Da siriryar murya nayi mata sallama. Ɗagowa tayi daga rubutun da take ta kalle ni.
Cikin ɗan yake nace “don Allah inda ake yin Interview na masu nema aiki” saida ta ƙaremin kallo kafin a tace ” 25 floor ne” ta nunamin hanyar lifter da zanbi. Godiya nayi ,nayi saurin wucewa nabi lifter din data nunamin. Ina shiga cikin lifter wata yarinya ta shigo itama da kana ganinta kasan baza tayi mutunci ba, ko daga irin yanayin shigarta. Wani kallo tamin tare da matsawa can gefe tana taɓe fuska,Sosai naji na ƙara muzanta, domin kuwa inhar itama aikin tazo nema kaman ni toh nasan cewa tabbas ita keda nasara.
Ƙarar da lifter tayi alamun mun iso yasa na maida hankali kan ƙofar dake buɗewa a hankali. Ƙirjina ne ya buga ƙafafuwana sukayi sanyi ƙalau ganin mutane cikin ɗakin interview ɗin wajen mutum ashirin maza da mata, sai dai matan sunfi yawa. kusan rabin su kana ganinsu kaga cikakkun graduate dake da babban kwali.A matuƙar sanyaye na fito na samu guri can gefe na zauna duk nasare. Toh a saboda yanda kowa ke burin ganin ya ƙure iyawarsa dan samun nasara yasa babu wanda ya kalleni bare su kula dani a gurin, dalilin da yasa na ɗan samu saukin muzantar da nayi .
Cikin minti talatin kusan rabin mutanen da suke gurin suka fara watse wa. Na ƙara shiga damuwa sosai sanin cewa a kowane lokaci za’a iya kirana. Ile kuwa sai ga sunana ana kira “Neehal Maleek” A ruɗe na tashi na amsa tare da bin wanda ta kirani office ɗin da naga ta shiga.
Zama nayi kujerar dake fuskantar tebirin da aka rubuta CEO cikin wani ɗan frame dake kan tebir ɗin. Banga wane ba saboda ya bani baya. Wajen minti biyu da zamana kafin kujerar ta juyu tana fuskatan ta ta . Ga mamakina nayi tunanin ganin namiji sai naga mace. Kyakyawar Macece da bata wuce shekara 35. Farace sal kana ganinta kaga shuwa. Da murmushi a fuskarta ta karɓi takarduna tana dubawa. Ido na zuba mata ina admiring ɗinta da kuma tuna rayuwa ta ta baya.
Ɗagowa ta yi daga kallan takarduna ta kalle ni tace ” me yasa ki ka ɗauki har tsawon shekara biyu bayan kin gama secondary baki cigaba ba?” Rasa me zance mata nayi . A sanyaye nace mata “matsala ce ta family ” kai ta jinjina ta cigaba da cewa ” kuma gashi kina da grades masu kyau, amma alamu sun suna kaman kin ƙarasa makarantar ne a government bayan kin fara a private” Yanda ta yi maganan sai naga kaman tana tuhuma tane. Cikin ƙosawa da tambayar na ƙara ce mata ” kaman yanda nace matsala ce ta family tasa na kasa affording na privates school dana fara” kai ta jinjina kaman ta fuskanci halin da nake ciki. Komawa ta yi ta jingina jikin kujera “kina da wani special skills ne ,Neehal?” Ta ambaci sunana,ɗan Jim nayi kafin nace ” Eh ina making coffee da hot chocolate” murmushi naga ya bayyan a fuskarta ta ce ” Hot chocolate da coffee major requirement abu ne” nima murmushin nayi ganin na fara samun nasara. Tana ƙoƙarin ƙara jehomin wata tambayar aka shigo office ɗin nata.
“Eman, ya kamata ace kina cikin conference room , waɗannan Chinese delegates din suna jira” Murya ce kakkausa dake so Masculine ta yi magana so deep and hot. Wani irin bugawa ƙirjina ya yi saboda sai nake ji kaman nasan muryar
“Oh, kaga kuwa na manta walahi” cewar matar da yakira da Eman tana ƙoƙarin miƙewa tsaye.
” yauwa tunda ka shigo ma ka ƙarasa yi mata Interview ɗin please”
bata tsaya jiran me zaice ba ta yi saurin ficewa a office ɗin. Ajiyar zuciya na sauke ina sauraran takun ƙafarsa yana nufo inda nake. Kujerar data tashi ya zauna yana fuskan ta ta ba tare da ya ɗago ba ya fara duba takarduna data ajiye. Sosai ƙirjina ke bugawa ina kallanshi cikin matsanancin tashin hankali. Addu’a nake Allah yasa ba idona ke min gizo ba. Ɗagowa ya yi zaimin magana daga ni harshi muka zubawa juna ido cikin firgici. Tashin hankali wanda ba’a sa masa rana.
Mutumin da nake gujewa tsawon shekara shida sai gashi ƙaddara ta ƙara haɗani dashi a inda banyi tunani ba.
Ya chanza sosai da sosai, wannan light brown eyes ɗin da jawline nashi da suke hade guri ɗaya alamun shima ya gane ni. Worse abun ma, ya tuna duk abinda nayi masa.Wani irin matsanancin bacin rai ne na gani kwance kan fuskarsa. Ɗauke kallan sa ya yi daga kaina ya mayar kan takarduna. tsabar ɓacin rai har wasu jijiyoyi naga sun fito a goshin sa abunka da farin mutum. Jiki a matuƙar sanyaye na sunkuyar da kaina ƙasa cikin matsanan ciyar kunya. Who will have thought all this running da nake sai gashi fate ya ƙara haɗamu. Ɗagowa nayi ina ƙara ƙare masa kallo . Wannan ƙibar da ada nasan shi da ita duk da ba wata ƙibace ta azo a gani ba yanzu babu.
Sanye yake cikin wata well business tailor suit dark ash da tayi masifar kamashi. Ya tattare hannun rigar zuwa damtsen hannunsa. Damtsen hannun nashi kawai na kalla na san cewa ba ƙaramin ɓata lokaci yake ba gurin gyming.
“Miss..?” kallan fuskata yake cikin nazari yana jiran na gaya mishi full sunana. Takardu na dake gabanshi ɗauke da sunan nawa da profile ɗina na kalla, bai damu da dubawa ba yana so yaji daga baki na. Gira ya ɗagamin alamun yana jiran amsata. Wani irin guilt naji ya rufe ni a sanyaye nace “Neehal” ina sunkuyar da kaina ƙasa.
“Neehal wa? Ahmad?” Ya faɗa muryar sa babu alamun wasa idanuwan sa a kaina kaman zasu haƙa rami tsakiyar goshi na.
Nace ” Neehal Maleek” cikin borin kunya. Ina kallan hannunsa da ya yi fisting kaman mai shirin kai naushi. Hakan ya ƙara tabbatar min da tsananin ɓacin ran da yake ciki, amma yana ƙoƙarin boyewa .
“Ki na tunanin ke mutumce mai gaskiya da riƙon amana?”
“What?” na tambaye shi cikin rashin fahimtar inda maganan tashi ta dosa.
Ya ƙara cewa ” Loyalty abu ne mai muhimmanci da muke buƙata tattare da ma’aikatan mu, so Miss Neehal tell me, do you consider yourself loyal?”
Cikin inda- inda nace ” ban sani ba ” dan gaba ɗaya ya kullemin kai.
“zaki iya tafiya Miss Neehal, team ɗinmu za suyi contacting ɗinki idan kin samu aikin “yace cikin dismissing tone ya mayar da hankali kan takarduna. A matuƙar sanyaye na fice daga office ɗin.
Na riga da na saddaƙar yanzu zan ma bazan samu aikin nan ba, dan haka ina fitowa ko takan Ramlat ban bi ba nayi waje zuciyata na wani irin zafi hawaye masu ɗaci suna bin fuskata. This is my last option nasan in ban samu anan ba babu inda zan samu.
E 3-4.
Toh har mukaje gida babu irin tambayar da Ramlat bata yimin ba na kasa cewa komai. Haushin rashin bata amsan da nayi yasa muna tsayawa ta fice a fusace ta shige gidansu dake kusa da namu anan unguwar Suleja dake can hanyar Kaduna road. Tunani nake idan har ma na samu aikin bansan taya zan dinga sammakon zuwa ba, saboda tazarar dake tsakani dan a kalla za kayi tafiya ta wajen minti talatin zuwa arba’in daganan zuwa cikin Abuja. Da kallo na bita harta shige gida na sauke ajiyar zuciya na fito daga ɗan sahun bayan na sallame shi da kudin da Ramlat ta bani.
Gidanmu ƙaramin gida ne dake ɗauke da ɗakuna biyu sai banɗaki. Babu kitchen a gidan a nan ɗan tsakar gidan namu muke kunna kirifoti. Da sallama na shiga gida. A tsakar gida na tadda Innati tana ƙoƙarin sauke abinci. Da sauri na ƙarasa inda take ina mamakin inda muka sami abinci dan nidai nasan na fita bamu da komai a gidan da zamuci.
Murmushi kwance kan fuskar Innati tace
” Har kun dawo auta?, Allah yasa na gama abincin, ina ta sauri nagama kafin ki dawo dan nasan kina jin yunwa tunda baki karyaba ki ka fita ”
Mamakina na kasa ɓoyewa nace “ina muka samu abinci haka Innati? Nidai nasan bamu dako ƙwayar shinkafa, gashi kuma naga kin dafa mana taliya da manja” Bata bani amsa ba saida ta ɗauko kwano ta zubamin abincin ta turomin shi gabana sannan tace cikin rashin damuwa
” Ɗan kunne na da yarage na gwal na siyar na siyo mana shinkafa kwano uku, sai taliya rabin katan da su mai da magi, da kuma barkono kwano ɗaya .ban siyo kayan miyan da yawa ba na ɗari biyu ne kawai saboda rashin inda za’a zuba suda suke da saurin lalacewa ” yanda take maganan cikin rashin damuwa da ko in kula yasa naji hawaye masu ɗumi sun biyo ƙuncina .
Nace “amma Innati shi…” saurin katse ni tayi ta ce
” karki damu kanki Neehal, Allahn da yabamu a wancan lokacin ya kuma ƙarbe abunsa, shi bawa a koda yaushe yana cikin jarabawar Ubangijine dan ƙara kusanci dashi. Mai imani ne kaɗai yake iya fuskantar hakan. Babu wanda ya wuce ƙaddarar sa, shi Ubangiji yana tare da masu hakuri . ki daina damun kanki dan nasiyar da wani abu, mene amfani na idan na kasa ciyar dake Neehal?, a koda yaushe ke ce cikin yawon nema mana abinda za muci , kece kullum yawo can yawo nan amma Allah bai bamu nasara ba har yanzu ba kuma zamu sare ba zamu cigaba da nema da yardar sa har ya bamu nasara, shi dama duk me nema yana tare da kalubale iri-iri.”
Murmushi tayi min tana shafa fuskata idanta cike da hawaye ta ce ” Allah ya yi miki Albarka ya baki abunda ki kaje nema”
Wasu hawaye ne masu zafi suka bi fuskata dan nasan a yanzu ma ba zan samu aikin ba. A da suna kin ɗauka tama ba tare da dalili ba kawai saboda yanayin rayuwata da suka gani, ina kuma yanzu da yake da dalili mai ƙarfi. Cikin hikima Innati tasani a gaba naci abincin nan tana bani labarai masu daɗi da yasani mantawa da damuwar da nake ciki. wajejen la’asar bayan na gama duk abinda ya dace na shirya cikin doguwar rigata ta zaman gida na fito riƙe da wayata ƴar touch. Zaune a tsakar gida na samu Innati ta kishingiɗa tanajin redio. Gabanta na ƙaraso nace
“Bari na leƙa gurin Ramlat Innati dan fushi take dani zanje biko” da murmushi na ƙarasa maganan tunawa da nayi yanda muka rabu ɗazu da ita. Kai Innati ta ɗaga tana cewa kar nayi dare tunda yamma tayi.
**
Toh koda naje gidansu Ramlat saida nayi ta lallashi dan saida Mamanta tasa baki sannan ta haƙura. Nasan Ramlat da zuciya amma bata taɓa yimin zuciya irin wannan ba. Can ƙuryar ɗakinta muka ƙule ina bata labarin duk abinda ya faru zuwan mu A&E INDUSTRIE. Mamaki ne ya rufe Ramlat .
Ta ce” Anya kuwa Neehal kin tabbata shi ne?, ba kince shi ɗin da direban ki bane?, ta ya akayi har ya iya samun aiki a wannan babbar Company da duk Abuja babu kamarta?”
Aziyar zuciya na sauke mai karfi nace “Walahi Ramlat ko shekara ɗari zanyi bazan manta kamannin saba, duk da irin chanzawar da ya yi amma nasan shi ne. Na riga da na fidda rai da samun aikin nan, kawai zan cigaba da binki restaurant ɗin da ki ke zuwa na cigaba dayi musu wanke-wanken suna biyana”.
ƙarasa maganan nayicikin raunin murya. Kafaɗata ta dafa tana cewa ” Kar kiyi saurin yanke hukunci. Idan har ya tabbata basu ɗauke kiba saboda abinda ya faru shekara shida da suka wuce to tabbas sun zama mutane da basu da imani, a wancan lokacin duk abinda ki kayi kinyi shi ne saboda yarinta, in harkuwa sukayi amfani da wannan toh basu cika mutane masu aiki da hankali ba”.
A tare muka sauke ajiyar zuciya nida ita shiru ya ratsamu na ɗan wani lokaci. Ƙarar ƴar touch ɗina ce ta katse mana shirun. Cikin hanzari na ɗauko wayar dake kan gado ina kallan baƙuwar number dake kirana. Dagani har Ramlat saida gabanmu ya faɗi dan nidai bani da saurayi ko ɗaya a yanzu da yasan number ta. ƙwace wayar Ramlat tayi daga hannuna ganin na kasa ɗauka ta yi saurin ɗagawa ta karamin ita cikin kunnena.
“Is this Miss. Neehal Maleek?” Wata irin muscline voice ta yi maganan cikin serious tone. Haɗiyar yawu nayi muryata na rawa nace “eh nice ” na riga da nasan cewa zasuce bazasu ɗauke ni bane , shi yasa suka kira su yi rejecting ɗina.
“Miss .Neehal, i’m talking from A&E INDUSTRIES and you’re being appointed as the personal assistant of Eman Lamin. you’re expected to be here on monday at 8pm sharp.” ya ce ba tare da jira nace komai ba ya katse wayar.
Daskarewa nayi a zaune na kasa cire wayar daga kunne na. Ramlat duk ta ruɗe ta zubamin ido tana jiran taji abunda sukace. Jiki a matuƙar sanyaye na juyo ina kallanta . Hannu ta ɗaga tana kaɗawa idanuwa a waje tace “me suka ce sunyi rejecting ɗinki?” kai na girgiza mata. Murmushi ne ya kubcemin cikin rashin yarda da abinda naji nace ” sun bani aikin?” zare idanuwa ta yi kafin ta saki wani ihu ta faɗo jikina ta rungume. Dariya na fashe da ita da rabon da nayi dariya haka harna manta.
Hayaniyar ihun mu da Maman Ramlat taji yasa ta shigo ɗakin tana
“Lafiyarku dai ihun me kuke haka? ”
Ramlah ce ta bata amsa cikin farin ciki ” Mama aikin da Neehal taje nema A&E ne suka bata yanzu aka kirata a waya sun ɗauke ta”
“Kai MashaAllah, Alhamdulillah,Allah shi ne abin godiya, Ubangiji yasa ki fara a sa’a Neehal ” cewar Mama fuskarta ɗauke da murmushi.
Nida Ramlah muka amsa da Amin. Ficewa ta yi ta barmu muka cigaba da hira.
Kallan Ramlat nayi nace ” ni abinda yake damuna yanzu ba zuwa aikin ba, bani da wata sutura ta arziki da zan dinga sawa ga kuma kuɗin motar da zan dinga kashewa kullum”
Mikewa tayi ba tare da tace komai ba ta buɗe kwabarta ta fito da wata atamfa sabuwa dan baifi sau ɗaya ta saba. Miƙo min atamfar tayi tana cewa ” ga wannan sai kisa ranan Monday ɗin, dama tun-tuni nake da niyar bar miki ita” Ido na zuba mata ina kallanta ban karɓi kayan ba nace ” wai don Allah me yasa ki ke min haka ne?, toh idan na karɓa ke kuma fa?”
A harzuƙe ta ce ” idan bazaki karɓa bane kawai ki gayamin, sai kice kin raina kayan kawai”
Sanin halin Ramlat na saurin zuciya yasa na karɓi kayan badan naso ba ina mata godiya. Harara ta zubamin tare da jan wani mugun tsaki. Murmushi nayi kawai ina kallanta dan nasan godiyar tawa ce ta bata haushi. Mayafi ta ɗauko min da takalmi wanda zasu shiga da kayan. Shima saida muka kai ruwa rana da ita sannan na karɓa amma da sharaɗin a ransu nayi ba duka ta barmin ba.
***
Ko dana koma gida na nunawa Innati kayan saida tayi min faɗa akan su, nidai shiru nayi bance komai ba. Ban gayawa Innati nasarar samun aikin ba na bari saida safe.
Toh washegari da safe ina ƙoƙarin ɗora mana shinkafa da mai bayan na gama shara da wanke -wanke Innati ta fito daga ɗaki riƙe da carbi tana ja. Cikin sauri na ɗauko tabarma na shimfiɗa. Zaman Innati keda wuya mukaji muryar Baba salmanu. Shi ɗin kawu na ne dan wan Mahaifina ne. Batun yau yake so ya ɗauke ni ba tun bayan da Mahaifina ya rasu. Innati ta hana saboda shima ba wani karfi ne dashi ba tace za’a ɗora masa nauyi kuma bayan hakama idan suka ɗaukeni bata da wani da zata dinga gani tanajin daɗi, tunda ni kaɗai ce gare ta.
Bayan ƴan gaishe- gaishe Baba Salmanu ya gyara zama yana kallan Innati ya ce ” Yanzu Khadija kin kyauta kenan da hanani yarinyar nan da ki ka yi?, ki bada ita ta shiga cikin yan uwanta kin ƙi, me ki ke yi mata anan?, ita ba karatu ba bakuma aure ba tana zaune a gida babu gata, yaci ace yanzu tayi aure tana ɗakinta tunda karatun ya gagara, na lura indai tana gurinki toh baza ki bari tayi aure ba dan haka zan tafi da ita yanzu ko kina so ko baki so”
Hawayene masu zafi suka biyo fuskar Innati ta fara kuka ba tare da tace komai ba. Nima ganin tana kuka yasa na fara hawayen dan sam banaso a rabani da ita. Ajiyar zuciya Baba ya sauke yana kallona yace “Tashi maza Auta ki haɗo kayanki mu tafi” . Matsanancin kuka na rushe dashi ina bashi hakuri ya yiwa Allah ya barni gaban Innati na, bana san abunda zai rabani da ita. Toh kukan da yaga mun haɗu munayi ya sauke ajiyar zuciya mai karfi dan Innati harzuwa lokacin batace komai ba.
“Shikenan Auta bar kuka zan barki, amma da sharaɗin zan dinga zuwa akai-akai ina dubaki duk ranan da naga abunda baimin ba dole ki bini, dan tarbiyar ƴa Mace abu ne mai matukar wahala dole sai da jagora a rayuwarta.” Dubu biyu ya fito da ita ya miƙo min yana cewa ” ungo ki riƙe wannan kinji ko ,ko kina da bukatar siyan wani abu babu yawa,ei shiru ki daina kukan na fasa tafiyar dake” ajiyar zuciya na sauke na karɓi kuɗin ina masa godiya. Shafa kai na ya yi yana kallan Innati dake sauke ajiyar zuciya yace ” Zan wuce Khadija ki kula da yarinyar don Allah” murya a shaƙe Innati tace “InshaAllahu Baba”
“Toh MashaAllah,Allah ya tayaki riƙo” .
Bayan tafiyarshi ne muka samu damar karyawa. Lura da nayi har zuwa lokacin ran Innati a ƙuntace yake yasa na kawo mata zanchen samun aikina.
Murmushi ta saki cikin jindadi ta ce ” MashaAllah auta Allah ya yi mana jagora yasa ki fara aiki nan a sa’a, ina san kiyi aikin nan Auta ko dan na samu sauki wajen dangin Mahaifin ki, saboda suna ganin kaman na barki cikin halin kuncin rayuwa na kuma hana su ɗauke ki tunda suna ganin suna da hakƙi akan ki. Ki kula da tarbiyar da nabaki Auta don Allah”. Addu’a ta yimin sosai da fatan farawa a sa’a.
Duk irin murnan da nake na samun wannan aikin, ƙasan zuciya ta cike yake da zullumi da fargabar irin rayuwar da zanyi a ƙarƙashin mutum da ada ban dauƙeshi a bakin komai ba. Sai gashi a yanzu nike ƙarƙashin sa.
MUJE zuwa.