Littafan Hausa Novels

Maza Biyu Hausa Novel Complete

Saran boye
Written by Hausa_Novels

Maza Biyu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MAZA BIYU

 

*NA:SLIMZY*

Wattpad@slimzy33

 

*marubuciyar:*

 

*K’ADANGARUWA*

 

*RUD’ANI*

 

*DUHU…..*

 

*1*

 

Hannunta dafe da kuncinta, batare da yabari ta dawo hayyacinta daga azabar data sauka a tsakiyar kwalwalwarta ba, cikin zafin nama ya ƙara sauke mata wasu tagwayen maruka, yana nuna ta hannu ya ce “How dare you talk to me like that eh? Sai na kashe ki a banza na kashe jakar ƙauye babu abinda uban wani ya isa ya yi, empty head” Sameer ya riƙe hannun abokin nasa yana dukan kafaɗar shi ya ce “Common my friend, akan wannan kake ɗaga jijiyoyin wuya?” A fusace Mansoor ya ɗaga hannu ya ce “Sam, barni irin jakan ƙauyen nan maganin su kaci uban su” Cike da tsiwa hawaye na zuba a kuncinta, amma bata karaya ba DINA ta ce “Kaci ubanka dai, nawa uban ba zai taɓa ciwo ba, daman daka ganinka maye ne kai wlh” Sam ya saki baki yana kallon Dina ganin bakinta yaƙi mutuwa, Mansoor wanda ake masa laƙabi da Man ya ce “What!” Sai kuma ya yi kanta, da gudu ta take ƙafafuwanta ta ruga a 136 tana cewa “Ohho dai kaji da warin wiwinka…..”

Kanwar Matata Hausa Novel Complete

cikin zafin nama samir ya rukosa wanda tuni dariya ta cika masa ciki ya cafko mansoor da jikinsa ke rawa kamar mazari yace”calm down man ya karamar yarinya kamar wanan zaka bita?idan ka bita me zakayi mata?bayan kaine zaka zama abin kallo a cikin garin nan dubeka fa?”samir na nunasa da yatsa ya cigaba da magana “karka zubar da class dinka akan DINA kaji abokina kaima narasa dalilin dayasa kake shiga sabgarta”wani kallo mansoor yayi masa batare da yace komi ba kawai ya jinjina kai saidai kallo daya zakayi masa kasan cewar yana cikin tsananin bacin rai yayi fushi,samir murmushi kawai yayi dan yasan man bazai taba magana ba yayi mamaki ma da har yayi musayar wadanan words din da Dina shida maganarsa ma in kana tare dashi zaka iya kirgawa kasantuwarsa miskili marason magana da izza,….wucesa yayi kawai magana kasa kasa kamar bayaso yace “kasameni a mota”be jira mai samir zaice ba yayi gaba abinsa yana bin yaran dake tsaitsaye suna kallonsu da wani irin kallo mai cike da kyama yana mamakin meye abun kallo a wajen su?bude motarsu yayi ya zauna a mazaunin mai zaman banza ransa a bace yake idanuwansa sun kada sunyi jajir kansa ya dau carji maganganun DINA ke yawo a kwakwalwarsa”kaci ubanka dai daga ganinka maye ne kai nawa uban bazai ciwo ba…mai warin wiwi”ransa ya kara baci ya runfe idonsa ita yake gani lokacin da take fada masa wadanan maganganun tunda yake wata mace bata taba masa kallon banza ba ballantana ta daga harshenta ta zagi ubansa……DINA….ya furta a zuciyarsa,yaja gauron numfashi ya sauke yayi murmushin gefen fuska kamar yadda ya saba kuma dabiarsa ce koda yana cikin bacin rai,

 

Sam kuwa shafa sajen fuskarsa yayi ya saki lallausan murmushi yace “DINA Akwai karfin hali amma burgeni kikayi inason mace mai courage”ya cije lebensa yana bin yaran wajen da kallo ya hangi wata yarinya tsaye ta tsaresa sa ido kamar zata cinyesa,murmushi yayi mata ya yafitota da hannunsa ta juya zata gudu ya karasa da sauri “dakata babu abinda zanyi miki kinji tambayarki zanyi ina ne gidansu DINA?”yace yana murnushi ganin dik yadda ta tsorata yasan halin yan kauye,

 

cikin hausarta ta kauyawa tace”can ne gidansu bari muje in nuna maka amma kada kace nice na nuna maka kaji?”jinjina mata kai kawai yayi yana murmushi burinsa kawai yasan gidansu dan tunda suke haduwa da ita bai taba sanin gidansu ba gashi yau sun kwashi kallo da mansoor beyi hira da itaba yana kewar hirarta da wawtarta, haka suka taka dik inda suka gifta su ake kallo,

 

Mansoor dake cikin mota na mamakin ina kuma sam zashi?yana kokarin kunna wiwi a hannunsa ya janyo wayarsa zai latso numbersa kiran da ya shigo wayarsa ne ya kara bata masa mood yayi jifa da wayar gefensa ya kwantar da kansa jikin kujerar motar yana sauke numfashi minti minti yana zukar wiwi…..

 

******

“Dina meyasa kikeso ki rinka saka kanki a matsala?yanzun gashi saade tace taga lokacin da kika zagi wadanan yan birnin guda biyu da suke zuwa gidan gonar nan dake bayan gidan mai gari?meyasa kika zageshi?har ya mareki?dubi yadda yatsunsa suka fito a gefen kumatunki?ko kin manta matsayinki ne?babanki ba kowa bane a garin nan face mai facin tayar mota ni karki daukomin masifa”innahrta cike da fada takeyi mata magana,

 

dina tadan tura baki tasa dumamen tuwo a gabanta ta gagara koda gutsurar loma daya tsananin takaici da bakin ciki yasa wasu sabbin hawaye masu zafi ke kara zubo mata daga kyawawan feraren idanuwanta masu daukar hankali,dikda haka bakin Dina be mutu ba “Innah ubana fa ya zaga harda cewa sai ya kasheni fa wai yaga wanda ya tsayamun harda zagina yayi da turanci ya fadi wasu maganganu”ta zumburi baki,innah ta tabe baki tace “koma meye yayi miki kece kikaja tunda kike shiga sabgarsu tunda ai ana ganinki da dayan aka fadamun dik garin nan labarinsu akeyi baa san daga ina suke ba kuma an tabbatarmun kina zuwa wajensu to ki shiga hankalinki tunda har maganar kisa ta shigo ciki”kwafa DINA tayi “innah ba abinda ya isa yayimun in turanci yake takama dashi nima ai baba yace zai kaini makaranta in zama likita”innah bata kara saurarenta ba ta dauko bokitin ruwan data ja a rijiya ta soma tatar kullun koko,

 

sallamar yarinya ce ta sa innah juyowa “ke yau bazamu siyi gyadar ba anata ciki wanan zamanin waye yake ta maganar siyen gyada?”girgixa kai yarinyar tayi tace “ba gyada na kawo ba wai DINA tazo inji wani balarabe”

 

“balarabe?kodai wanda ta tsokana ne ya biyota ya kasheta?”innah jikinta ya soma rawa,zumbur DINA ta mike taci dammara da dankwalin ta ta dauki tabarya “koni koshi a garin nan idan be kasheni ba ni zan kasheshi “DINA ta fice bata jira mai innah zatace ba hanlalin innah ba karamin tashi yayi ba tayi jifa da abun tatar koko ta soma salati tana kwalawa DINA kira,ko saurarenta batayi ba sai surutai da takeyi,

 

Sameer na tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa yana facing kofar gidansu tun daga jikin labulen buhu yake hangenta ya soma tuntsirewa da dariya yana hango abinda ke hannunta Yana kara kwashewa da dariya yace “DINA…ho”yana murmushi tana yaye labulen buhun tace “ina yake dan wiwin nina fishi…”kasa karasawa tayi ganin samir tsaye yana tuntsurewa da dariya,sakin tabaryar tayi tana murmushi tana kici kicin kwance dammarar da tayi “ah ah Dina kinyi shirin fada ne?”ta zumburi baki cike da shagwaba tace “ehh mana ba yace kasheni zaiyi ba?”tayi farr da ido ya kurawa fusharta ido yadda tayi jajir ga shacin hannun mansoor kwance a fuskarta cike da tausayawa yace “taho nan kawata DINA zo inji na biyoki ne nayi bikonki sam bazan juri zama nikadai batare da kawar hirata ba”

 

tad’an washe baki tace”Allah dagaske?”gira ya daga mata yana murmushi ta hararesa”kaima bazakayi magana bane irin na abokinka kurma?”tuntsurewa da dariya yayi yace “nasan sai kin magantu yanzun dai nazo bikonki kizo muje wajen hirarmu”

 

“Allah ya sauwake inje ya dukeni ya kasheni?bazanje ba banason ganinsa”bata fuska samir yayi ransa yadan sosu ganin haka yasa DINA tadan natsu “banason kina fadin haka akan abokina kinsam yadda nake tsananin kaunarsa kuwa?”ta ware ido. ta harde hannuwanta a kirjinta tace “saika fada ku Yan biyu ne?”girgiza mata kai yayi yace “ko daya mu abokai ne aminina ne inajin tsananin kaunarsa mudin abu daya ne da Ruhi mabanbanta abinda ya bambantamu kenan kowa nada gangan jiki da ban da ace gangan jiki daya ne da nafi farin ciki babu abinda zai rabamu”murmushi tayi ta fahimci akwai tsananin shakuwa da kauna a tsakaninsu saidai sunada banbanci wajen halaye,

 

“Yanzun dai ki gafarci abokina ki yafe masa marukan da yayi miki kinji?”ta tabe baki kamar zatayi kuka tace “da zafi fa?”cike da shagwaba tayi maganar,ya zuba mata manyan idanuwansa yana murmushi yace “nasani kiyi hakuri da wanine yayi miki marin nan da zan rama miki amma bazan iya rama miki marin nan ba sakamakon Man ne yayi mikisu?”tace “meyasa?”

 

“saboda idan na maresa tamkar kaina na mara”tayi yar dariya tace “shikenan muje”ya jinjina kai yaja wata sassanyar ajiyar zuciya,suka jera innah ta fito da sauri ta kwala mata kira “DINA ina zuwa?”murmushi Dina tayi mata tace “ba dadewa zanyi ba yanzun zan dawo”cike da ladabi sam ya gaida innahr DINA sanan suka jera tabi bayansu da kallo cike da fargaba da tsorom kada yaudararta sukeyi su aikata mata wani mugun abin tasan halin DINA sarai gabanta na faduwa ta juya ta Shiga gida….

 

******

daga cikin motar ya kure kida yana bi a hankali idonsa a lunshe hannunsa rike da wiwi yaji ana kwankwasa glass din windown motar dan tsaki yayi yasa hannu ya rage wakar sanan ya bude motar a fusace yaga waye,sam ya gani tsaye da Dina tana ta dariya sun shagala suna dariya ransa ya baci ya tsaya yana kallonsu saidai gabansa ne ya yanke ya fadi idonsa dayayi tozali da shacin hannunsa a kumatunta,ya lura hira sukeyi basusan ya bude ba hakan yasa yayi gyaran murya,take dukkansu suka tsaida dariyar da sukeyi sam ya nisa yace “ohh ashe ka bude nayi tunanin baka bude motar ba bakaji ba ai”DINA ta dan yatsina hanci warin ya dake hancinta tasa hannu ta rike hancinta tana mazurai,wani kallo mansoor keyi mata wanda taji kamar ta saki fitsari,da sauri ta cire hannunta daga hancinta taji kawai yayi kwafa yace “ashe kinada tsoro”ta murguda masa baki kawai,yayi dariyar gefen fuska ya juya yana fuskantar sam yace “yadai what do you want”girgiza masa kai kawai yayi “nadauka baka ciki ne ka Shiga gida ai shiyasa”ya jefa masa wani kallo “kadameni dayawa”mansoor yace yana satar kallon DINA samun kansa yayi da son kallon kwayar idanuwanta,juyowa tayi suka hada ido yana kallonta take ya kauda idonsa gefe daya yace”sai ka shigo bari na Shiga ciki yau zamu koma?”yana tambayar Samir ne cike da isa da gadara,

 

“yadda kace”samir na murmushi cike da zolaya yace “kardai wanan fad’an ya rikide ya koma soyayya”,

 

wani kallo yayi masa,kawai bece komiba yayi gaba abinsa,

 

“a gayas”DINA tace tana binsa da harara,murmushi man yayi kawai ya juyo idonsa da nata suka hadu wani yarrrrr Dina taji tayi saurin dauke idonta cikin zucuyarta tace Allah yasa beji ba……

********

“momy tun safe nake kiran ya mansoor baya daukar wayata bansan meyasa ba”cike da shagwaba matashiyar budurwar ke magana tana kallon momy idonta yayi rau rau,

“tou ke ya nabeeha inda sabo ai kin saba da miskilancin ya mansoor meyasa kikeso kidamu kanki kinsan yanayin abu lokacin da yakeso kuma ya gadama ne ni narasa gane kan wanan abun naku”

 

“bazaki gane ba rufaida ni bansan meyake zuwayi wanan kauyen ba ma nafara suspecting dun wani abu”tayi maganar a kufule cike da kishi sai lokacin momy ta yi magana “nabeeha kinfi kowa sanin mansoor ai karma ki tunanin akan mace yake zuwa wanan wajen raayinsa ne nima banida yadda zanyi kuma shi yasan bazai dauko mun wata yar kauye ya kawo ba”..

 

rufaida tadan ja tsaki tace “a birni ma beso mata ba sai a kauye?dama kincire wanan a ranki kawai kiyi kokarin samun soyayyarsa kawai in kinada saa”rufaida na maganar ne tana kokarin saka kayan bacci tana daure da towel momy ta yunkura tace “da nasan abinda kika kirani kicemun kenan da banzo ba wallahi keda mansoor bazan iya da fitinarku ba”momy na maganar tana kokarin fita cike da tausayn nabeeha,

 

kara dialling wayarsa tayi a karo na ba adadi,

 

 

 

yana kwance ya kishingida yana kallon kiran nabeeha na shigowa ko motsi beyi ba balle asa ran zai dauka sam dake gefensa yace “baka ganin kiran nabeeha ne?ka dauka mana kaji me zatace”

 

mamsoor ya kallesa ta gefeb ido yace “amma kasan DINA dazun tabani mamaki?”samir yayi murmushi yace “mamakin me ta baka abokina?”shiru yayi bece komiba ya lumshe idonsa kawai kwayar idonta yake gani masu zara zaran gashi da yalwar gashin gira,sanan amon sautin muryarta tana zaginsa keyi masa yawo samir ya cigaba da danna laptop dinsa har ya manta da suna magana yaci mansoor yace “tanada courage sosai….babu macen data taba kallon tsabar idona ta fadamun magana sai ita”murmushi samir yayi yace “toh fa to kayi mata magana mana?nima inaso ku sasanta ko saboda…..”sai kuma yayi shiru be karasa ba ya cije lebensa yana cigaba da danna laptop dinsa,

 

“dawa zamu sasanta?ni?hmmm lets see”kawai yace ya dauko wayarsa dake cigaba da ruri ransa a bace yace “owoooo nabeeha why?you are disturbing my peace”ya dau wayar a fusace yace “i dont want to talk”

ta sauke ajiyar zucuya tace “why?”zucuyarta na cigaba da azalzalar ta da tsananin kaunarsa yace “later”kawai ta kashe wayat gaba daya yayi jifa da wayar ya janyo bargo ya lullube kansa ya lumshe ido DINA yake gani kawai dariyarta da fararen hakoranta,idonsa a lunshe yake murmushi,…

******

DINA na zaune a gaban mahaifinta bayan innah ta gama labarta masa komi daya faru yau ta dora da “kaja ma yarinyar nan kunne kada ta daukar mana abun kunya a garin nan dan dik garin nan maganarta akeyi ni banason alakartq da yan birni”

 

mahaifin dina yayi murmushi yana kallon dina yace”kinji abinda innahrki tace ko?nima ina wajen gyaran facin taya aka fadamun abinda ya faru anga lokacin daya zabga miki maruka ya biki aguje DINA ki rufamun asiri idan daukar magana zaki aurar dake zanyi”da sauri ta zabura tace “haba baba ka manta kace zaka kaini birni inyi karatu?ka manta likita nakeson zama?”mahaifinta ya daura fuska yace “tou indai kinason zama likita kada na sake ganinki da wadanan yaran yan birni kinji na fada miki ko?idan nasake ganinki dasu aure zanyi miki kuma bazaki karatun likitancin ba”sosai Dina ta tsorata ta gyadawa mahaifinta kai “bazan sake zuwa wajensu ba”

 

“dakyau tashi kije ki kwanta dare yayi”mahaifinta ya bata umarni,ta mike ta kwashe kwanukan da sukaci abinci sanan ta Shiga dan dakin dage gefen na innahrta ta rufo kofar,

ta jingina da jikin kofar tace “yanzun ya zanyi da abokina samir mai kirki?gashi baba ya hanani muamala dasu”zuciyarta babu dadi tayi rau rau da ido tad’anyi tsaki tace”gashi inada kudirin ramuwar gayya akan wancen dan wiwin yanzun ya zanyi?bazai mareni yaci bulus ba”ta shiga safa da marwa a cikin dakin tana tunani yadda zaayi ta dauki fansa akan mansoor….murmushin mugunta tayi take tace “yauwa nasamo mafita bazan taba barinka haka ba”tayi tsalle ta fada yar katifarta tana dariyar mugunta……

 

 

*SLIMZY*

MAZA BIYU….

 

*NA:SLIMZY*

Wattpad@slimzy33

 

*Marubuciyar:*

 

*K’ADANGARUWA*

 

*RUD’ANI*

 

*DUHU…*🌑

 

*2*

washe gari,

Innah na zaune akan tabarma ta kunna radiyo baban Dina na zaune a gefenta yana gyara jakarsa zai fita yace “ina Dina?ko har yanzun bata tashi ba tana kwance tana sakarci?”innah ta girgixa kai tace “natasheta sallahr asuba dai amma banida tabbacin ta tashi tayi sallahr yanzun nake shirin daukar bulala na shiga na tasota”bata rufe baki ba Dina ta fito tana Mika hade da salati wani kallo baba yayi mata yasa ta katse hammarta ta durkusa a gabansa “ina kwana baba katashi lafiya?ina kwana innah?”kusan hada baki sukayi “kinyi sallah ne?”ta jinjina kai “ehh nayi sallah”tace gabanta na faduwa alhalin batayiba fashin sallah takeyi kunyar ta fadawa innah takeyi,”dakyau dama ke nake jira na gargadeki kafin na fita kar inji kinje wajen yan birnin nan kin nemesu fada kinji na fada miki ko su sakaki a mota su gudu dake bamu saniba”murmushi Dina tayi tace cikin ranta “ai saidai su koma a kafarsu dan badai da wanan motar tasu ba badai akanta dan jiji da kan nan ke hura hanci ba kamar wani basarake”baba ya daka mata tsawa ganin tayi shiru tana murmushi yace “ke murmushin me kikeyi?”ta girgiza kai a tsorace “wani abun dariya na tuna,Allah ya tsare ya bada saa”tacewa mahaifinta ganin yana kokayim zura takalminsa tun sassafe yake fita daga kauyen yaje bakin hanya gyaran tayar mota,bayan fitarsa ta zauna a gefen innah ta soma zuba mata hirarta mara kan gado cikin hirar harda labarin sameer take ba innahrta wadda gaba daya batasan ina ta dosa ba,

 

minti kadan kamar an tsikareta ta mike “innah zani gidan su lubabatu na dubota kinga idan Rana tayi bazan iya zuwa ba”shiru innah tayi tana karantar DINA ganin ta zuba mata manyan idanuwanta yasa ta gyada mata kai “kiyi sauri kada kidade kuma karki biya wajen wadanan mutanen”ta jinjina mata kai tana murmushi,

 

 

mansoor kasa sukuni yayi haka kawai yakeson ya fita zaga gari ko zaiga mara kunyar daya dauki dammarar koya mata hankali dan haka Sameer na bacci ya dauki wayarsa yasa ear pice kunne daya,yana sanye da wasu kayan sanyi masu ruwan toka kansa babu hula yabi cikin garin yana tafiya yana haduwa da almajirai yana basu sadakar kudi dik wanda ya gaishesa saidai ya daga musu hannu yayi musu murmushi,DINA ya hango ta bullo ta wani lungu tana tafe tana rera waka da zazzakar muryarta tsaki yayi yace “shashasha tana tafe tana waka kamar ba mace ba”yad’anyi tsaki ya makale a jikin bango tazo ta wuce,wani iri. faduwar gaba taji da sauri ta juya babu kowa sai wani irin kamshin turare takeji wanda ta rasa a ina ta taba jinsa,jim kadan tayi a cikin lungun tana waige waige yana kallonta da narkakkun idonsa gashin kansa yasha gyara sai walkiya yakeyi tayi tsaki “sauri nakeyi kafin su tashi subar garin nan in rama abinda nayi niyya yau saidai mutum ya koma birni a kafa”tayi maganar tana kwafa,ransa yadan sosu yasan dashi take ya danne zucuyarsa kada ta gansa yabi bayanta tana tafe yana biye da ita wayarsa ya fito da ita ya danna recording da video tana wakar sarmadan ya masoyi sarmadan sarmadan….tsaki yayi yace “village girl baki sai rashin kunya”ya girgiza kai har suka isa kofar katafaren gidan gonar mahaifinsa ya makale a jikin gate,tana waige waige babu kowa a wajen sai kukan tsuntsaye dake bishiyoyin dake cikin gidan ta daga kanta tana kallon bishiyoyin cike da tsiwa tace “ni tsorom wanan bishiyoyin nake da wadanan tsuntsayen masu kukan tsiya”da sauri ta cire abun iskar tayar motarsu duka hudun tana cikin cire na karshe ta gagara cirewa tayi gumi kawai taga mutum tsugunne a gefenta,damm gabanta ya yanke ya fadi ta dago ido nan da nan jikinta ya soma kyarma tana kokarin mikewa ya cafki hannunta “Dan Allah kayi hakuri kaji karka fadawa innah ta kada ka kasheni kaji zan gyara muku tayarmu na iya wallahi”sosai tabashi dariya yadda jikinta ke rawa yasan tsananin tsoro take ciki da furgici,cije lebensa yayi hade da sakin murmushin gefen fuska yace “let me help you and removed it”kallonsa take bata gane meyace ba sai gumi dake karyo mata,

 

“kace?”ya girgiza kai yace “wawuya batajin turanci”tadan tura baki tace “niba wawuya bace”a ciki yace “me kikace”girgiza masa kai ta shigayi tana kokarin kwace hannunta daga rukon da yayi mata ko motsa hannunsa ta gagarayi,

 

sameer ne zaune gefen gado ya shirya tsaf yana kiran wayar mansoor bata shiga tsaki yayi “ina kuma man ya shiga?inaso na fita na nemi DINA kafin mubar garin nan amma ya kama ya fita ina kiransa baya Shiga”

 

ya sake kiran wayar cikin saa ta shiga yana rike da hannunta ya kafeta da ido waya ta shigo wayarsa yace “yauwa ina tunanin hukuncin da zanyi miki ne ga abokinki ya kira”fuskarsa a daure yayi maganar take hantar cikinta ta kad’a cikin seconds hawaye suka shiga zubowa daga idonta yasa hannu ya dangwalo hawayen yayi murmushi sanan ya danna recieve yace “yes i can hear you”

 

“kana ina ne haka?natashi tun dazun na shirya inaso na shiga cikin gari sanan mu wuce ban ganka ba ya kamata mubar garin nan da wuri ana jirana ne nasa hannu a wata takadda a kamfani”harshensa ne ya sarke ganin yadda ta jike da gumi har zai fadawa Sameer yana tare da DINA sai kuma ya fasa still idonsa na kanta bayaso sameer yayi wani tunani,bayajin zai iya fada masa cewar ita ya fita nema bawai dan yanajin wani abu akanta ba “kadan jirani ganinan zuwa”be jira mezaice ba ya katse wayar,

 

tsaki samir yaja ya kalli agogo ya dafe kansa “bazan tafi ban hadu dake ba kawata kodan in kara baki hakuri akan abinda man yayi miki”cikin takaici yace…..”ko ina yayi oho mtswww”yaja tsaki,

 

share mata hawaye man keyi batare da yace komiba ya saketa ta mike da sauri ya hango nadama a kwayar idonta dikda yadda suke fada yasan ta tsorata “goge fuskarki”yace cike da isa,ba musu ta goge fuskarta yace “meyasa kikayi hakan?menene dalilinki na bata mana mota”tayi shiru batare da tace komi ba shima shirun yayi yana Danna waya amma yana kallonta ta gefen ido yana kallon yadda take gyara tsayuwa yasan guduwa zatayi ya juyo da sauri “idan kika gudu ko?har gidanku zan biki”yace a takaice ta tsugunna a gabansa “kayi hakuri ya mansoor”yadda ta kira sunansa a marairaice yasashi saurin kallonta ta hada gumi sai zare ido yakeyi “ina jinki kina cewa zakiga a ina zamu tafi gida ko?”ta girgiza kai ta tabe baki cike da shagwaba tace “ba marina kayi jiya ba shine nazo na cire muku iskar tayar mota dan in rama abinda kayimun jiya kuma ai nabaka hakuri”shiru yayi yace “is okay you can go”bataji me yace ba yasa ta cigaba fa tsayuwa yayi banza da ita kamar bazaice wani abu ba yace “kitafi nace”a dam kausashe yayi maganar ta tsorata yasa tayi kamar zata zame sanan ta runtuma aguje tanayi tana waigensa murmushin gefen fuska yayi ya shafa kansa sanan ya karasa ya shige gate din gidan yana murmushi,

 

kicibis sukayi da sameer ya rukosa “where are you going”wani kallo sameer yayi masa yace “kaida zaka fita kona tambaya inda kaje?ba ina bacci ka fita ba?”Sameer yayi maganar cikin fushi,mansoor yayi murmushi ya dafa kafadarsa “am sorry friend na fita zaga gari ne coz i cant sleep daren jiyan nan”Sameer ya sassauta yace “menene ya hanaka bacci?”cike da kulawa ya tambayesa ya girgiza kai “nothing”sam yace “abinda ya hanaka bacci ba karamin abu bane its okay ina zuwa”be jira shima me zaice ba ya fice mansoor ya tabe baki ya wuce ciki abunsa yanata murmushin nasarar tsorata DINA da yayi yasan bazata kara mai rashin kunya ba koda yazo watarana sun hadu,

 

 

kusan awa guda sameer ya kwashe yana neman DINA be ganta ba sosai ransa yadan baci,beji dadin hakan ba , gashi mansoor nata kiran sa a waya yasan kiransa yakeyi su tafi bayan shi yaja masa rashin gani DINA din dikda mansoor besan me yakeso yayi ba,haka ya kamo hanya ya nufo gidan daidai baban DINA ya gama saka musu iskar tayar mota mansoor ya ciro kudi wajen dubu goma ya mikawa baban DINA yana kallonsa kamarsu daya da mahaifinta dan dai ita fara ce”yaro wanan kudin yayi yawa”cike da girmamawa yace “baba ka karba ka kara ka siyi kayan abinci”shiru baban DINA yayi kamar fa su akace DINA tayiwa rashin kunya kamar zaiyi magana ya wuce yana mamakin ladabi irin na mansoor,shima sameer mamakin yadda mansoor ya girmama mutumin yayi “ya ina kasan wanan?meyasamu tayoyin motar?”bece komiba yayi gaba abunsa ya zauna mazaunin driver yace “shigo ni mu kama hanya”Sameer yasan ran abokinsa ya baci dan babu abinda ya tsana kamar jira…..

 

cikin zolaya Sameer yace”nafika kosawa mutafi ko ka manta masoyiyata tayi kewata nima nayi kewarta sosai?”mansoor yayi murmushi “nasani ai tunda kwana kukai kuna waya kamar zaku cinye juna shegen kaya dik ka gama tsotse yar mutane bayan su daddy kai sukewa kallon mutumin arziki dan dai kawai ina shaye shaye”ntsww yaja tsaki,

 

sameer ya shafa sajensa yacev”bazaka gane yadda nakejin shaukin kairatu bane”tabe baki mansoor yayi yace “shege ka fito ka aureta”Sameer ya bugi kafadarsa “ko bakace ba”

 

mansoor ya cigaba da driving minti minti Dina ke fado masa a rai…

 

******

“wai nikam yaushe yaran nan zasu baro kauyen nan sudawo ne?yau kwnansu biyu a can fa kamar “dattijon da bazai wuce shekara sittin a duniya ke magana kallo daya zakayi masa ka hango tsananin kamar sa da mansoor,yana kallon mahaifiyarsa da kannensa dake zagaye da dining table din kowa na break fast rufaida ta kalli nabeeha daketa juya tea tun dazun bataci komiba sai juyawa takeyi tayi kasa da murya “tin dazun bakici komiba fa”momy ba lura dasu suna kus kus tace”kus kus din me akeyi ko kunsan mansoor din na hanya ne”rufaida tayi murmushi tace “ah ah kawai dai”da sauri nabeeha ta take kafar rufaida ta girgiza mata kai maana kar tayi magana a gaban Abbah,”tou kuyi ku tashi a shirya musu kayan karin kumallo in sungadama da wuri zasu dawo”ta kalli agogo sha daya da rabi na safe nabeeha ta ture cup din tea din tace “nakoshi idan kingama ki sameni a kitchen mu hada musu breakfast”rufaida ta jinjina kai momy tausayin nabeeha takeyi fatanta kawai mansoor ya amince,

daddy yace “wainikam ko yar gida zaayi da nabeeha ne?”momy murmushi tayi kawai tana gyada kai sallamarsu ce tasa parlorn ya rude “laa ga yaya man gasu sun dawo”rufaida farin ciki ya lullubeta shi kuwa gogan kallo kawai ya bisu dashi sameer ne yaketa faraa ya tsugunna a gaban momy da daddy “daddy barka da safiya”

 

“ai nadauka a can zaku zauna muzo biko ko mu biyoku da kayanku yan kwal uba dam kunga baku da mata?”d kunada iyali bazaku tafi kuki dawowa ba”sai lokacin mansoor yayi magana “just two days dady shine mun dade?”ya ja kujerar gefen momy ya zauna “good morning momy”cike da farin ciki take bubbuga bayansa,”welcome,sameer bismillah kuzo kuyi breakfast ga nabeeha can yanzun ta shiga kitchen naga yar gulmar nan taje sanar mata kundawo “sameer yayi murmushi ya dubi mansoor “a nan zamuci abinci ko can gida wajen ummah nasan tayi maka alkubus”murmushi yayi “yes muje can kaima din nasan kafison can bakaso dai katafi kabarni yanzun mu shiga muyi wanka sai mu wuce”daddy yace “ai dama nasan bazaku rabu ba zamu gani in kukayi aure koda yake dukkanku baku shirya yin aure ba”Mansour ya lumshe ido DINA ta fado masa sai kawai ya share yana dariya suka nufi sashen mansoor don suyi wanka….

 

********

zaune suke a wani kayataccen garden a cikin gidansu sameer matawalle kallo daya zakayi musu su baka shaawa domin hatta da gyaran gashin kansu iri daya ne,sameer na rike da glass cup yana sipping juice hannunsa rike da wayarsa suna video call da khairat,minti minti yakan saci kallon mansoor dake faman blushing hannunsa daya rike da tabar wiwi da yake zuka ko cikin kwanciyar hankali,lumshe ido samir yayi akwai wani bakon lamari a tattare da mansoor dake Sashi wanam blushing din dikda yasan dabiarsa ce kasaita da rashin son magana da tsananin zurfin ciki, ajiye wayar yayi batare da yacewa khairat komi ba”wai nikam man naso ace ka nemi gafarar abokiyar fadan ka DINA”juyowa yayi da sauri cikin wani irin yanayi yace “ni kuma?bayan zagina da rashin kunyar da tayimun da haduwar da mukayi dazun na kamata?”sameer ji yayi juice na kokarin sarkesa cikin mamaki yake kallon abokin nasa “ka kamata a ina?kana nufin kai ka hadu da DINA yau?”gyada masa kai yayi cikin ko in kula yace “yess na hadu da ita,a karo na farko that village girl ta bani tausayi na fahimci jahila ce saidai kuma haka kawai abubuwanta kedan bani nishadi”wani kallo sameer yayi masa yace “really? don’t tell me you are in love”

 

“with who?….that village girl?. haka,kawai dai tadan burgeni ne i just want to change her”gaban sameer yayu dan kayataccen murmushi yace “ohh really kodai soyayya?da ka gwada yar soyayyar nan da ita kaga idan munje kauye ka rinka rage zafi a birni kuma ga nabeeha gida biyu maganin gobara” yayi maganar yana wani shu’umin murmushi. ya cigaba da magana “hmm am so happy to hear that from you of all people mansoor……”lumshe ido mansoor yayi take ta fado masa a rai ya dire tabar wiwi din ya janyo gorar swan water ya bude ya duddula a bakinsa idanuwansa suka kankance yace”see ba soyayya zanyi da ita ba i just want to change her,da kake maganar rage zafi a kauye tayaya?wanan yar kankanuwar yarinyar?see look bazan iya abinda kake magana ba, ballantana inji ina sonta” ya janyo wayarsa “come and see something”yacewa sameer da tun tuni ya ajiye cup din dake hannunsa ya matso kusa dashi , videon Dina ya kunna musu suka fara kallo daidai lokacin data dan furgita ba karamin dariya taba mansoor ba sai kawai ya soma dariya,sameer kuwa mamaki ne ya kashesa tunda yake be taba ganin dariyar mansoor ba dik amintarsu kodai son DINA yakeyi?take zuciyarsa ta gargadesa “ba sonta yakeyi ba anya mansoor zaiso Dina?bayan ga nabeeha dake hauka akansa ko kallo bata ishesa ba”suka cigaba da kallo,sameer ya rinka yiwa mansoor hirar dina shi kuwa samun kansa yayi da jin dadi sai murmushi yakeyi yana kara bashi support akan ya canjata, zaiyi matukar farin ciki idan ya kasance mansoor yasamu abokiya…..wuni sukayi a garden suna hirar Dina kafin daddare mansoor yayi sallama da sameer ya nufi night club….

 

sameer kuwa wajen khairat ya nufa,

 

suna zaune a cikin mota yana rike da hannunta suna fuskantar juna yana shafa lallausan hannunta yana lumshe ido ta dubesa cike da tsananin shauki tace “nayi kewarka sam….katafi kauye kayi zamanka abunka kullum sai nayiwa ummah kuka idan ta tambayeni menene saina kasa fada mata”

 

“khairatu nima ina tsananin kewarki musamman….”ya kashe mata ido yana nuna mata kirjinta da suka cicciko a cikin rigarta ta lumshe ido “nida kai yan uwane me zaisa bazaka bari na sanarwa ummah cewar soyayya mukeyi ba?muyi aure?? munada dangantaka fa kasani”ajiyar zucuya ya sauke “haka ne karki damu ni zan sanarwa da ummah cewar ina sonki kuma aurenki zanyi”wani farin ciki ne ya lullubeta ta fada kirjinsa da sauri ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya yana son khairat sosai kullum kara tsunduma yakeyi a kogin kaunarta,bayaso yayi aure yabar mansoor ne yafiso suyi aure tare haka yasa hannunsa yana murza nipples dinta tana sauke numfashi yana kara jadadda mata irin kaunar da yakeyi mata sun dade tare sanan ya kira mansoor kafin yabar wajenta,

*********

juyi DINA tayi tacewa innah “nifa mamakin wanda ya bawa baba kudin nan nakeyi gaskiya beji dakyau ba ba Mansoor bane sameer ne”innah tayi mata wani kallo “kinfisa sanin su kenan?yace mansoor yaji ankirashi ke kince sameer to wai ya akayi kikayi musu farin sani haka?murmushi kawai DINA tayi cikin zucuyarta tace “banajin wanan mai girman kan tsiyar yasan darajar Manya ballantana har ya dau kudi ya bada a matsayin kyauta kuma cikin girmamawa” innah tace”ke tashi kibani waje inata magana kinyi banza dani?”tura baki DINA tayi ta koma gefen tabarma ta zauna ta rafka tagumi yau tayi abun kunya,mutumin daya tsaneta yake kyamarta shi ya kamata tana musu barna Allah yasa dai bai fadawa abominsa ba mai kirki…..ta gyara kwanciya akan tabarmar haka kawai tasamu kanta da shafa hannunta tacw “dan iska harda wani tabani dama mashayi ai ba abinda suka sani sai iskanci “tace a fili innah ta zaburo “waye ya tabaki DINA?na shiga uku ni hajara “tayi kan DINA a tsorace dina ta mike tana mazurai da ido waye zata fadawa innah ya tabata?gabanta sai faduwa yakeyi…..

 

 

 

*SLIMZY*

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment