Azal Hausa Novel Complete
AZAL!
*SAJIDA NIJAR*
*PAID BOOK*
_Bismillahir rahamanir-rahim._
*1*
Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak’a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*
Kwata kwata ya manta cewa wayarsa ce jone a jikin lasifikar motar dake tafiya da su daga sabon Gari zuwa Anguwar Jeune cadre, hakan ya sa ya gyara zamansa daga gaban motar dake dauke da su, su uku yana sake buga numbar yarinyar nan ama cikin ikon Allah sam ba’a daga ba.
Da mamaki ya sake dubawa, eh lalle numbar ce, tunda aka turo masa numbar da hoton mai numbar bai cenza komai
Da dan dabara ya kalli wanda ke hakimce a bayan motar yana kallon hanyar nan baya ko kiftawa hannunsa sama wajen girarsa a hankali yana shafa wajen yana tunanin abinda ke cikin ransa
A kira na kusan tara aka daga wayar, sai dai babu amsar da aka bada da ta wuce shiru da shuuuuuuuuuuu tamkar karar fanka
Mummunar Kama Hausa Novels Complete
“Asalamu alaiki, dan Allah ina magana da RAUDA ne?” Ya fada yana sauraro da tabacin zai ji amsa daga ɓangaren wace aka kira da RAUDA domin a irin labarin da aka bashi na ita din wacece ya san ko Muryar yaro karami ta ji in dai namiji ne zata saurara
Shiru ya dauki wayar da motar baki daya
Sai da ya ja numfashi ya sake furta” Wai ko ba’a jin muryana daga wayar ne?”
Daga ɓangaren wace aka kira da RAUDA ta ja wani arnen tsaki sannan ta datse kiran
Tsakin da ya ratsa baki daya motar har cikin kwakwaluwar mutumen dake bayan motar nan zaune
A hankali ya lumshe idannuwansa sannan ya bude a kan wanda ke gaba zaune daidai lokacin da ya zarro ido ya ciro wayar a rikice ya zuba dubansa yana duban wayar tamkar wanda ke son karantar wani abu a jikin wayar
Muryarsa a yannayin dimauta ya shiga magana tamkar ba abokinsa ne ke zaune a motar Ba ya ce” YUSEF, Walahi ban san bata da mut……”
Shiru ya yi da maganar da yake yi sakamakon gannin motar na tsayawa dan a bude masu get YUSEF din ya bude motar ya fice bai ce da shi ci kanka ba
A kafarsa ya shige baban get din gidan nasa , du irin tsayin tafiyar dake gabansa cikin tafiya ta nutsuwa da kwonciyar hankali
A birkice wanda ke cikin motar ya dafe gaban goshinsa lokaci daya ya shiga kiran numbar wace ta bashi numbar
Nafisa na dauka ya shiga masifa yana fadin” Yar gidan uban waye kika bani numbarta? Dama bata da mutunci ko bata san abinda ake iya kiranta dominsa bane? A kan mi zaki bani numbar baki min bayanin komai ba?”
Nafisa ta yi dan firgigit sakamakon barcin da ya fara fizgarta na bakin magariba dan ta gaji ainun , daga wajen biki take har juwa ke kwasarta dan gajiyar rawar da suka tika tana wara idannuwanta ta ce” Ban gane ba da ka kireta me ta ce da kai?”
Rai bace ya ce” da na yi kiranta tsaki ta yi ta katse wayarta, ke kin san waye za’a kawowa ita?”
Nafisa ta dantse lebe cike da takaici ta ce” Ba yar uban kowa bace , dama a yadda na ga alamun fadin ranta sai da nace da kai oga du yan matan nan ita ta maka? Kace eh, menene kake nema a wajenta wanda babu a wajen sauran? Ama ka yi hakuri zan tardata sai na mata rashin mutunci, Duda ba ni ta ba numbarta ba , Ni ko magana bata taɓa hadani da ita ba dan na tsani ire irin yan matan nan masu shegen dagin kan tsiya!”
Takaici ya saka shi kashe kiran ya bude motar ya fice shima ya shiga a kafar yana takawa da sauri dan burinsa ya je ya bashi hakuri , dan shi ya san shirunsa ba alkhairi bane
A lokacin da ya karasa bangarensa da kyar ya kama madubin kofar ya bude ya shiga , a nan ya sake yarda cewa mutumen da ya tsane su na wajen, dan haka sai ya kama kansa bayan ya yi salama ya nufi kujerar zaman mutun daya ya zauna yana sake kama kansa
Tunda ya shigo RISLAN ya yi shiru da bayanin da yake yi sannan ya daure fuska yana jin kirjinsa har zafi yake yi saboda yawon da ɗan uwansa ke yi da ISHAK , yawo na shashanci, yawo na watsar da kai da watsar da adini
Murmushi kadan YUSEF ya yi yana dauke dubansa daga kan RISLAN ya dan dubi Ishak ya ga ya gyara zama bashi da niyar tashi bayan ya tarda magana suke yi wace ta shafi family isu
Dan gyaran murya ya yi a hankali ya ce” ishak shiga ciki mana ”
Ishak din ya mike yana jin zafin RISLAN har kasan zuciyarsa, domin a duniya wannan mutun yana matukar saka masu ido a shige da ficensu da YUSEF, ama shi jiransa yake yi wata rana ya shiga huruminsa WALAHI sai ya nuna masa bashi da wayo! Dan ya nuna masa dan duniya ne shi
Ciki ya shige yana hura hanci,
Sai da ya shige RISLAN ya iya sauke ajiyar zuciya ya sake fuskantar YUSEF
A tausashe ya ce” ya dace ka san me kake ciki zuwa yanzu, ya dace ka yiwa kanka wa’azi ka kuma gane a kulun shekarunka karuwa suke yi ba ragewa ba, ka sada kanka ka yafe wasu abubuwan ka kuma kyale wasu ka rayu da su a haka, ka je ka ga HAJIA ana ruwan saman nan na jiya ta fadi ta samu karaya kuma an kirayeka an sanar maka, HAJIA fa mahaifiyar mai martaba ce YUSEF”
Murmushin nan nasa wanda yake kama da ashariya ya sakar masa kafin ya dauke dubansa a Nutse ya ce” To ”
RISLAN ya zuba masa ido da duba irin na tsoron yannayinsa
Hannayensa ya hade yana dubansa ya ce” Yaya zaka ce to bayan na san ba yi zaka yi ba? Dan Allah na roke ka ka je…..”
“Kar ka saki ka rokeni kan abinda bai zame mini wajibi ba!, na goge zumuncina da ita, ubana ta haifa ba Ni ba shine dolenta, maganar na bar abinda nake yi nace maka to zan bari, me yasa kake so sai ka saka na daga maka murya ne?” Ya fada a kausashe, ama a hankali dan ko me yake yi tsakaninsa da ɗan uwansa bai taba yarda wani ya ji ba
RISLAN ya rintse idannuwansa da suka cika taf da kwallah, wannan wani irin Fitina ne ke yawo a jinnin ahalinsu, sai kace ba jinnin sarauta ba? Daga mashaya sai mazinata, sai masu halaya irin na bera? Ya Allah ka dubu lamarin wannan ahali
A hankali ya ce” Ka tabbata zaka je dan uwana?”
Shiru ya yi da farko, sai kuma ya sakar masa murmushi a hankali ya gyada masa kai ya ce” Zan je bi izinillah”
“Ka san me Abanmu ke buri? Burinsa ya ga ka yi aure kaima, ka san burinsa ya ga kaima ka kawo matar da kake so ka yi aure Dan uwana” RISLAN ya fada a tausashe yana sake zuba masa ido dan gannin reaction dinsa
Mikewa YUSEF ya yi a Nutse ya bale rigar dake jikinsa ya cireta ya ajiye nan saman kujerar falon ya zamto abinda ya rage a jikinsa farar singileti ce
cikin nutsuwa ya juya ya nufi wajen frij din falon ya bude ya ciro galan din ruwa mai sanyi ya juyo ya dawo falon ya bude yana mika masa
Amsa RISLAN ya yi yana furta” Thank you”
YUSEF ya zauna yana janyo computersa ya bude ya yi connecting da wifi din gidan sannan ya ajiye ya juyo ya zubawa RISLAN ido kamar yadda shima yake kallonsa
Murmushi ya yi a Nutse ya ce” Ni fa ba mata bane bana so, Idan na ki mata waye zai bani abin sakin mara?, Usatz soyayya da mace daya ne nake yiwa lakabi da *AZAL*!, ba zan taba yarda ganganci ya jani wannan ba, aure kuma ka cewa babanka kar ya damu idan na shiryawa hakan zan kawo mashi hudu ya kula!”
Tunda ya fara bayanin a tausashe ne, harufan a bayyane ne, sai dai yannayin maganar wani iri ne tamkar wanda baya son fitar da amon muryarsa , ko dan abokinsa na ciki? Wanda yake yiwa boyon sirin dake tsakaninsa da ɗan uwansa ne? Maganar dai gatanan tamkar wanda ya maku haka dai , sama sama dai kuma kasa kasa dai, maganar kamar wanda yake so daga shi sai RISLAN zasu ji ta
“Soyayyar ce *AZAL?* soyayya itace abar da ta fi komai dadi a duniya, wanda baya so bai morewa rayuwa ba, kai da ba dan so ba ai da duniyar nan ta tashi, soyayya farin ciki ce, kwonciyar hankali ce, nutsuwa ce, kar ka yi mamakin ka wayi gari ka samu kanka a cikin so YUSEF ” RISLAN ya fada a tausashe yana kallon Yusuf
Dan murmushi ya yi ya masa shiru, bai dauki computer ba da da irin tarin aikin dake gabansa, dan shi din yana da halaya mabanbanta ne, koda Akoy hali taurare Akoy sansanyan hali a tare da shi, YUSEF yana da daraja mutane da yannayi irin nasa
Gannin yanzu firar ta zama ta shi daya a dole ya mike ya yiwa YUSEF Salama sannan ya yi tafiyarsa yana ji inama zai iya da ya shiga ya fitar da wancen dan dabar dake ciki dan ba zai so ya fitar da shi ba a gabanan kuma, yana addu’a a kulun Allah ya shiga tsakanin dan uwansa da bata garin nan, su din da kansu yana binsu da Adu’ar shiriya
Bayan tafiyar RISLAN da kamar minti goma sha biyar ishak ya fito daga ciki ya karaso ya zauna dan nesa da YUSEF kadan a tausashe ya ce” Dan Allah ka yi hakuri da wannan banzar cikar da ta yi maka tsaki dazun a mota””
YUSEF ya dan dakatar da dogon rubutun da yake yi dan yana nema ya bada shi sanadiyar maganar da ya fada wace bata da wani tsari
Ishak ya ci gaba da fadin” ban san marar rabo bace sai da ta aikata aikin jahilai da wa’inda basu da rabo ba, ama Ni na yiwa kaina alkawarin sai na masheta doki ta yadda kowani kare zai hau tunda har ta kasa amsar mai daraja irinka”
“Ka daina magana sama sama mana ina typing din abu muhimi ne” YUSEF ya fada tamkar bai ji magangannun da Ishak ke fada ba
Shiru Ishak ya yi, baya so ne ya fita ya bar shi a wannan yanayin ya san ya bata masa, shi yasa ya tsaya dole dan ya bashi hakuri,
Sai da YUSEF ya gama rubutunsa sannan ya rufe computer bayan ya kashe ya dubi Ishak dake zaune gannin ya kashe computer ya ajiye wayar dake hannunsa
A Nutse ya ce” Ta san Ni ne da zata raina Ni?, kaine ka raina Ni, ina fatan zai zamo na farko kuma na karshe da zan ga irin wannan rainin ka fahimta?”
Ishak ya yi gagawar amsashi har yana bashi hakuri, hakan sai ya daure min kai, domin a tunanina a kuma zatona YUSEF aboki ne wa Ishak, ba yaron gida ba, sai abin ya daure min kai ainun domin shi din kansa ishak shigar jikinsa ta manyan kudade ce, shin menene ya sa yake yiwa YUSEF magana kamar yana yiwa wani wanda ya isa da shi? Isa irin ta iyaye ba ƙawance ba?
Ishak bai bar falon ba sai da ya kawowa YUSEF abincinsa dake saman table sannan ya tafi
YUSEF ya jima a falon nan bayan ya gama cin abincin sannan ya nufi dakinsa yana jin gajiya tatare da shi da kuma launin bukata irin ta lafiya, wace lafiya ke kawota, ama bacin ran jin tsakin nan ya tsaye masa a kahon zuka
Murmushi ya yi kawai yana janyo filonsa fari ya rungume dan ko ba komai ai zai tashi sallar asubahi sannan ga auren Elhaji goben wanda ya tabbata idan bai halarci auren ba yana iya haduwa da surutu mai girman gaske da jajen bai kyauta ba, sai kace auren fari a wani damu mutane da gayata……….
Asalamu alaikum jama’a….mun zo maku da nagartacen ingantaccen maganin Ulcer, magani ne na Hausa jikake wanda Dubai suka gwada suka ji dadinsa, nagartatun tsatatatun itaciyoyin da suka bamu sasake masu anfani ne ake anfani da su, a nan jamhuriyar Nijar a garin Damagaran a farashi mai rahusa dubu biyu yan naija , yan nijer kuwa 1500francs mai bukata ga numbar +227 96897192 , HAJIA RAHAMA