Littafan Hausa Novels

Mummunar Kama Hausa Novels Complete

yadda ake tsara budurwa a waya
Written by Hausa_Novels

Mummunar Kama Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*MUMMUNAR KAMA*

*(hot love & special romantic)*

~Paid Book~

 

300

for paid 09074017484

 

WRITTEN BY

By

 

(ƳAR AMANA)

 

 

 

 

*A mini afuwa na jin ya ci megida ne kuma waccan wayar na yi missing komai babu zan dawo baya*

 

 

free 🅿️1-2️⃣

 

 

 

“Keee dalla malama kiyi kibar nan kin wani bi kintsayawa mutane aka da wannan MUMMUNAR KAMAR taki”,wata matashiyar mata ke fadàr haka ga wata da alama mai aiki ce”,”haba Aunty NUSAIBA Dan Allah kina bin baiwar Allah a hankali mana tana miki iya biyayya fa amma kina mata haka”

wani matashin saurayi ke faɗar haka da alama mai faɗan yayace a gareshi” to ubana su sauran ba suyi magana ba sai kai mai zuciyar tausayi ko”,”ba haka bane Allah ya baki haƙuri”,ya fadà yana haƙar shinkafar dake gabansa,tsaki tayi ta tashi tureta ta fadí can gefe,tashi tayi ta kar kaɗe jikinta ta fita akatafaran falon wanda kana ganin maishi kasan an tara,

Yayi Sake Hausa Novel Complete

Can bayan floor ɗin ta zagaya ta zauna tasha kukanta kamar ranta zai fita,tana magana a fili “wai daga hutu an maidani ƴar aiki amma ba komai laifin mai gidanne daya bada fuska tunda ko ba komai tsakanin mu aini ƴar uwarsa ce amma ba komai”,

Saida ta gaji sannan ta tashi ta koma falon a ƙofar falon tayi karo da mutum baya taja sa sauri amma saida ya ɗaga hannu ya fesa mata mari mai shiga jiki sannan ya fice yana huci,dafe wurin tayi bayan juwa ta gama ɗibarta ta wuce,dariya Nusaiba tayi”Allah shi ƙara akanki aka sauke fishin kenen” dama ita ta kunno shi tun daga jaji ya taho dan ya biya buƙartarsa akanta matsayinta na matarshi amma taƙi shine na wannan fushin kuma tace yabata kuɗi yaƙi wai shi saidai ta amince dan kanta bazaina biyanta kuɗiba duk sanda yake da buƙatar haƙƙinsa tunda ai ya biya sadaki,sai dai ta tambayi kuɗi sa’in dayake free ita kuma taƙi dan ƙawayenta sun gaya mata cewa muddin kinason abu kina tambaya sanda miji yazo gareki da niyar kwanciyar aure, wannan maganar tasa aranta shi yasa take masa haka,shi kuma mulki da isa bazasu barshi yayi abinda take soba.

#########

Da sauri hadiman dake falon SULTANA HUSAINA suka yi ta kansu ganin ƴan mazan Sultana ya shigo a fusace,wata hadimarta ce ta nufi can lambun gidan inda Sultana ke yawan zama tana kallon tsirai da tsintsaye dan kaf wani nau’i na tsuntsu akwai shi a gidan,daga nesa ta tsaya ta sunkuya”matso mana Jummai”,”abarni daga nan Ƴar sarki jikar sarki matar sarki uwar sarki kuma kakar sarki da ikon Allah”,”Allah yasa Jummai meke tafe dake?”,”Allah ya ƙara tsawan rai Yarima ne ya shigo kuma da alama yana buƙatar kulawarki”da sauri tamiƙe dan akan tilon ɗanta bata mulki ko ƙasaita,amma fa tafiyar nan ta gado tana nan cikinta ta iso falon yana kwance kan kunjera ya buɗe rigar kakinsa sai farar army less”MIRZA lafiyanka kuwa”,kamar bai jita ba ya yi shiru,”Mirza ba dakai nake magana ba”,bai tashi ba baiyi magana ba,”MIRZA bana son raini fa”,janye hannunsa ya yi a kan fuskarsa”to me zance miki Umma”,”ba abinda zakace min amma meke damunka”,”ba komai Umma kawai na gaji da zama da Nafisa ne”,”bangane ka gaji da zama da itaba wai kai kanka ɗaya ma kuwa”,”wallahi Umma in Nafisa bata gyara halayenta ba ko to agabanta zanna kawo mata ina kwanciya dasu”,kan yagama maganar tasa bayan hannu ta bige mai baki cikin ɓacin rai ta fara magana”MUHAMMAD kana kuwa da hankali da bakinka ka ke maganar bin mata”,kamar ba soja ba ya fashe da kuka,gyara tsaiwa Sultana tayi tana binsa da kallo bata ankaraba ya kwaso wani magani a aljihunsa ya watsa abakinsa ko ruwa bai nema ba,da hanzari tai kansa”Mirza!Mirza!!na shiga uku ni Usaina”Jummai ta fara ƙwalawa kira da gudu ta shigo”ranke daɗe lafiya kuwa”,”maza bani ruwan ɗumi”kafin ta gama magana ta fita da gudu cikin ƴan mintuna ta dawo da ruwan ta sunkuya ta bata ruwan,hannu na rawa ta karɓa ta kafa mai abaki kaɗan yasha ya rufe ido ba jimawa bacci ya kwashe shi,filon kujera tasa masa ta gyara mai kwanciyar ta miƙe zuciyarta na tafasa dan tasan maganin me yake sha tun Mirza baikai hakaba tasan wane irin namiji ne shi ya yi auran ashe ita batasan na banza bane ta masa wani kuma yana wasa dashi a fusace ta fito su Jummai suka miƙe suna sunkuyar da kai kusan su talatin ne agidan dama,kallonsu tayi”Jummai ku goma kushirya zuwa gidan Yarima”,”to ranke daɗe an gama ku mu shirya Bilki ki kula da gida”,nan duk suka shiryo itama ta gama shiri dama nan suka shiga motocin gidan zuwa gidan Mirza.

 

Tsabar tana waya bataji sanda motocin suka shigo gidan ba tun kan azo abuɗe ma ta tabuɗe ta fito a zuciye bayanta suka bi zuwa babbar ƙofar falon,koda ta tura abuɗe take hakan yasa ta saka kai tana sallama,masu aiki uku da ta bata ne suka rankayo da gudu suna zubewa agabanta”ranke da ɗe barka da zuwa fatan kinzo lafiya”,batabi takan gaisuwar ba tace”ina ita uwar ɗakin naku ma za kusanar ma ta da zuwana”,kan ta gama rufe baki ɗayar ta wuce sama tana sauri,ƙwanƙwasa ƙofar tayi tace ma ta tashigo,tana shiga ta balbaleta da masifa”nifa kunsan bana son damu miye kuma”,Allah ya huci zuciyar matar Yarima dama Sultana ce ta zo kuma tana buƙatar ganinki”,da sauri ta miƙe cikinta na ƙullewa dan komin iskancinta tana shakkar uwar mijin nata dan cin uban mutane take baran ma akan wannan ɗan nata da take gani kamar yafi komai na duniya awurinta,”kice gani nan zuwa”ta miƙe tana ƙarewa kanta kallo a mudubi hoda ta shafa dan ta ƙara ɓoye yadda blicing yawa fuskarta sannan ta sakko itama sai dai ta dake ba tsoro ko ɗaya afuskarta,harararta Sultana tayi”ke kem kinyi asara babba Nusaiba kalleki mace har mace amma musaka to kinyi da ƴar halak akan Mirza ya salwantar da lafiyarsa akan ki gwara na san me zanyi shashashar banza kamar ba mace ba ina ƴata dana kawo gidan nan”,duk maganar da take Nafisa bata razana ba saida ta ambaci ƴarta sannan ta kalleta”kina kallona kamar baki sanni ba ina Asi take”,kan tayi shiru ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta shigo da gudu zuwa falon “Hajiya ki zo kigani wannan baƙuwar me aikin bata motsi harma ta sandare kamar ta daɗe da mutuwa”kan kowa ya motsa Sultana tabi inda me aikin ke nunawa tana isa kitchen ɗin kan tiles a cikin wannan uban sanyin taganta akwance da wani uban kaya mai dauɗa ajikinta sai fatar fuskarta baƙaƙirin wani razana Sutana tayi dan da gangar jiki ta gane wace,kanta tayi da sauri ta zauna awurin ta ɗagota zuwa jikinta”Asi! Asi!! dan Allah karki min haka ki daure” kallonsu tayi “ku ɗauketa kusa min amota”da hanzari suka cicciɓeta suka fita da ita Sultana ta biyo bayan su a falon ta tsaya ta ƙarewa Nusaiba zaune kan kujera tana kaɗa ƙafa kallo”keee ƴar marasa kunya kin manta wace ni ko ki ke kaɗa min ƙafa kamar wata sa’arki ko to ki sani a yau zakisan wace ni kuma akan Asi keda shi kunci bashi ku jirani”tana kaiwa nan ta fice,ita kuwa Nafisa harga Allah gabanta dukan tara tara yake amma ta maze tashi tayi ta wuce samanta batasan me zai biyo ba.

Tun kamin su ƙaraso ta kira likitanta suna isa gidan ta tarar harta zo dan dama basu da nisa kuma asabar ce ba aiki,ɗakin da ta fara sauka nankusa dana Sultana aka shiga da ita nan likita ta fara dubata allurori ta ma ta nan da nan ta fara numfashi bacci kuma ya yi gaba ita,Dr kallon Sultana tayi”ranke daɗe suma tayi kuma sanyi ya kama ma ta jiki haka yunwa da damuwa amma inta gama wannan baccin zataji ƙwari banda haka ba abinda ke damunta”,”nagode sosai Dr”,”ba komai rankedaɗe zan koma”,tare suka fito saida ta fita sannan ta wuce falon da Mirza ke kwance batai wata wata ba falla mai mari abinda bata taɓa yi ba,cikin kiɗima ya tashi amma sai ya maida kiɗimar tasa tunda agaban Sultana yagansa ba afilin yaƙi ba,kamin ya yi magana ta rigashi cikin tsantsanr ɓacin rai”sannu Muhammad kaji ka kyauta to katashi ka buɗe kunnen ka ka saurare ni,kaida matarka yau kun shiga gonata kuma bazaku fita ta daɗi”,”wai me na miki ne Umma ki ke wannan faɗan”,hannu ta ƙara ɗagawa amma ta sauke tana yarfewa”bakasan me kayi ba ashe,to SUHAIMA dana baka ka kai gidanka ta huta ita ku ka mayar ƴar aiki maragalihu bayi ma na gidan sun fita gata da kyan gani”,jigum ya yi sannan abinda ya faru ya faɗo masa arai zaro idon gado ya yi”Umma dama Suhaima ce wadda muka tafi da ita kwanakin baya”,hararar sa tayi”au dama bakasan wace ba shine baka riƙe amanar dana baka ba Mirza ka manta wace Suhaima bare waccan maras kunyar daka aje”,kansa ya dafe yana miƙewa zai yi magana ta ɗaga mai hannu”fita agidan nan kamin nayi losing sense na ɓata maka rai kuma ka faɗawa matarka tayi da ƴar halak ta jira sakamako”tana kaiwa nan ta nuna masa hanya,jikinsa ba ƙwari ya fita ko gidan bai kallaba dan ta layin yabi direct ya wuce Jaji dan yana tunanin kwanyarsa ta kusa bugawa.

 

 

 

 

PLEASE SHARE SISTERS

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment