Nisan Kiwo Hausa Novel Complete

Nisan Kiwo Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Nisan Kiwo Hausa Novel Complete

_Mom Islam_

 

 

Domin samun more pages kuyi following ɗina arewabook

 

 

Page1

 

“Shin kinsan da cewar ciwon mahaifiyarki baya buƙatar damuwa akan me zaki dinga kusantar ta bayan tace babu abinda ta tsana kamar ta buɗe ido ta ganki?”

Cikin shesheƙar kuka Anum tace “akan me zata dinga furta min irin waɗannan kalaman kodan saboda taga Allah yayini da Halitta ba irin taku ba?”

Tai maganar tana toshe bakinta da hannu saboda kuka yaci ƙarfinta. cike da tsananin damuwa gami da tsantsar tausayi Jannat ta kamo hannun Anum suka fito daga ɗakin da Ummu take, a parking space suka tsaya, inda jerin danƙara-danƙaran motocin masu gidan ke a parke, “Anum nasani abin da ciwo ace mahaifiyarka wace ta ɗauki cikinka tun yana watanni ɗai-ɗai har tara da kwanaki yau a wayi gari tace bata ƙaunarka duk inda zakaje kaje wannan sam ba ɗabi’a bace, sannan gaskiya anyiwa Allah butulci”

Kyandir Romantic Love Story Hausa Novel

Jannat ta faɗa tana dafa kafaɗar Anum, magana take son yiwa Jannat ɗin amma ina bakinta da zuciyarta gabaki ɗaya rawa sukeyi yayinda takejin kanta nayi mata matsanancin ciwo kamar zai tsage, cikin ƙarfin hali tana dafe da kanta tace “anty Jannat Ummu fa musamman ta baro gidanmu saboda ni, ta dawo gidan mutanen da ba danginta ba ta tare, tace inci gaba da zama acan, nikam bazan iya zama ni kaɗai a gidan ba duk da akwai Arshi”

“Haba Anum ya ya inason kawo miki ingantacciyar shawara kina kawomin wani zaman gidanku, ki nutsu ki saurareni, duk da cewar Allah yayi miki Halitta guda biyu, mace da namiji kinga mudai ba wani hali ne damu da zamu iya taimakawa ayi miki aiki ba, tabbas Arshi tana bani tausayi kodan Lalurar juyewar ƙwaƙwalwa da take tare dashi, amma wlhi nafi tausaya miki, dama shawarar da zan baki itace..”

Kiran Ummu ya katse Jannat, ta amsa tare rugawa a guje.

Anum ta durƙushe a gurin zuciyarta na faman yi mata zafi, ta kalli takalmin mazan dake a ƙafarta sannan ta shafi gashin bakin da ko ta aske gurin a baƙi yake zama, sannan ta kalli nonuwanta da suke a tsaye ƙyam kafin ta taɓo gabanta da ya kasance akwai na maza a jiki, ta ɗaga idanunta sama tare da dawo dasu ƙara hawaye na zuba sharr kamar an buɗe famfo,

“Jannat wlhi tallahi idan kika ƙara dawomin da Anum cikin gidannan mai rabani dake sai Allah tunda na gaya miki bana sonta bana sonta ko ana dole ne? inace ni na haifeta sannan nace bana ƙaunarta?”

Ummu tai maganar tana nuna Jannat dake tsaye a bakin ƙofa bata ma samu damar ƙarasa shigowa ba, a hankali ta tako tare da zama gefen Ummu cikin tausasa murya tace Ummu mai yasa kikeyin abu sai kace ba musulma ba, karki manta idan har kina tunanin kin gujeta ne, nan gidan da kike gadara dashi wlhi masu gidan suna iya dawowa a koda wane lokaci sannan sai sun tozartaki dan ba isasshen mutunci ne dasu ba”

Ummu ta miƙe kamar mai shirin yin tafiya, sai ta dawo da baya ta watsawa Jannat mari tana hoci tace “kar Allah yasa su bari inkai safiya, gidane nazo bazan fita ba tunda dai kema bana ubanki bane ai saiki barni da masu gidan ko?”

Dafe da kumatu ta miƙe daga zaman da tayi akan gado, kana ta miƙe jiki a sanyaye ta raɓa ta gefen Ummu ta fice, tana fitowa harabar gidan ta hango Anum na a durƙushe a gurin da ta barta ga uban rana da akeyi mai zafi, da sauri ta karasa gurin Anum ɗin tare da kamo hannunta, sukayi hanyar fita bakin get.

Jiki a sanyaye Jannat ta buɗe get ɗin suka fice, duk da shirun da ya ratsa anguwar bai hanasu samun wani dakali a ƙofar gidan dake a kusa da wanda suka fito suka zauna ba, har yanzu Anum kuka takeyi, Jannat ta sanya hannu ta buɗe kan Anum, da sauri ta fashe da kuka tare da rungume Anum, cikin kukan take cewa “Anum akwai matsaloli a tare dake masu tarin yawa, gashin kanki irin na maza ga gemu sannan kuma ga nono bayan nan..”

“Anty Jannat ki sanar dani abinda kikeson gayamin lokacin da Ummu ta kiraki”

Anum ta faɗa sbda wannan dogon lissafin da sukeyi ba wani ƙarewa zeyi ba,

Jannat ta mammatsa hannayenta kafin ta shafi gefen fuskarta da yayi jajir sannan tace “naji kafin nan gayamin nan gurin ya tashi ko?” Kallon kumatun nata Anum tayi cikin raunatacciyar murya tace “Ummu ce ta mareki ko?”

Jannat ta gyaɗa kai kana tace “karki damu idan Ummu ce zatayimin abinda yafi haka tunda yanzu ina tare dake, amma bata tunanin rayuwar Hajna?”

Sosai takaici ya kama Anum sbda a halin yanzu zuciyarta ta fara bushewa sam bata tunanin wata Hajna tunda dukkansu abin a taimaka musu ne, amma yanzu kam kanta take tunani, “ki mance da Hajna”

 

Anum ta faɗa.

“Toh shikenan, dama shawarar itace kinga yau baki da gurin kwana, sannan a gidanmu ma ba lallai su yarda mu kwana a tare dake ba, amma da zaki yarda da nayiwa ƙanwar momyna magana ta ɗaukeki aiki duk wata kina turomin da kuɗin cikin account ɗina, sai mu dinga tarawa har ya isa wanda za’ayi miki aiki, wlhi har makaranta zata saki, matsalar ɗaya ce dole ki kasance a suffar mace saboda wlhi mijinta baya ƙaunar namiji a gidansa, akan hakan matarsa ta tsayar da aihuwa, yaransu biyu Jumayma da Arshi, hamshaƙin mai kuɗi ne sannan kuma dole ƴan aiki tare da yaransa suke kwana, amma fa ansha kawo masa ƴan aiki wlhi yana korarsu dan ranar da naji ƙanwar momyn tana faɗa ƴan aikin da aka yi musu korar kare sunkai su ashirin”

Anum ta zaro ido kafin tace “Anty Jannat gaskiya bazan iya ba, saboda daga lokacin da suka tabbatar da ni MATA MAZA ce kinsan na shiga uku, inaga nikam kasheni zeyi kamar inda Ummu take buƙata”

Jannat ta toshe mata baki, tare da cewa “haba kisa, shidai ya kasance mai baƙar zuciya ne, dan wlhi nima nan da kika ganni ko gidan bana zuwa saboda akwai ranar da Arshi tayimin leifi na duketa bakiga ɗan dukan ba wlhi yana shigowa ya tambayeta tace nice, kawai sai nayi tsuru-tsuru, gashi sangameme ya tako har inda nake zaune saman kujera ya shaƙemin wuya, yace min, wai su biyun sune rayuwarsa zai iya kashe kowa a kansu in kiyaye,

Sosai hantar cikin Anum ta kaɗa, cikin karyar zuciya Anum tace “tunda kince yaran basu da kunya aiko dai bazamu shirya ba, Gara na shimfiɗa kwali na nemi gurin kwana ko a gefen titi”

 

“No ki bari muje a gyara miki gashin bakinnan, saboda nikam bazan iya ganinki cikin damuwa ba”

Jannat ta faɗa tana rausayar da kanta.

Sosai tausayin Anum ɗin ya kama Jannat,

Shiru ne ya biyo baya na ƴan wasu lokuta kafin Jannat tace “bazaki kwana akan titi ba, zan tafi dake gidanmu zuwa gobe da Asbha kafin su momy su fito sai muyi shawarar abinda ya dace”

Tabbas Anum tana jinjina tausayi tare da jarumtaka irin na Jannat sbda tasan idan har iyayen Jannat ɗin suka samu labarin Jannat ɗin ta kwana tare da Anum tabbas zata fuskanci mummunan hukunci, domin mutane da yawa suna suffantata da namiji, ita kuma Anum ɗin abinda bata taɓa kawowa kanta ba kenan, tana sawa a ranta koda yaushe ita mace ce, “toh” Anum tace dan itama kanta ta fara tsoron kwana a titin.

“Inda abin zai kasance, tunda tsakaninki da gidanku akwai nisa sosai gashi har an fara kiran sallah, zan fara shiga gidanmu, sannan da zarar na shiga zan yaudare mai gadi akan yazo ya dubamin wani abu acan baya, kinaji nace “subahanallah sai ki shigo a hankali ki ɓuya gurin motocin Dady, nikuma zan zo sai muyi shawarar inda za’ayi ki shiga ciki”

Anum ta kalli Jannnat dake ta faman kawo musu mafita, kafin tace “Nagode anty Jannat Ubangiji ya saka miki da alkairi”

Jannat ɗin ta miƙe tana cewa “karki damu fatan nasara zakiyi mana”

Suka fara tafiya riƙe da hannun juna, koda suka fito bakin titi da yake gidansu Jannat ɗin dole sai sun tsallaka titi, mutane sai kallon Anum sukeyi, wasu na tsokanarta wasu na nunata da yatsa, daga Anum ɗin har Jannat ɗin sunji zafin hakan, musamman ma wacce abin yake a kanta, cikin tausasa murya Jannat tace “Anum daga yau karki sake yawo babu hijabi kinji?”

Anum ta zura hannayenta cikin aljihun wandonta kamar dai inda maza sukeyi kafin tace, “anty Jannat tun ina ƙarama Ummu ta sabarmin da rayuwa a haka, wlhi rannan da na kwatanta sanya hijabi jinayi ya shaƙemin wuya sai naji sam babu daɗi dole na cire”

Jannat ta zaro ido tare da cewa “aiko inhar bazaki dinga saka hijabi ba wlhi duk gidan aikin da za’a kaiki matsala zaki samu indai ba aikin gida kamar mai gadi da dai sauransu zaki samu ba”

 

“Anty Jannat wlhi dan kawai kar inyi miki musu ne, amma duk sanda na kalli kaina a mirror sai tausayin kaina ya kamani, duk da nasan saɓo nakeyi nakance, mai yasa Allah bai dauki rayuwata ba tun inda jaririya, dan bana raye babu wani ƙalubale da zan fuskanta musamman ma ga mutane uwa uba harda mahaifiyata”

 

Jannat ta dafe kanta, kana tace “idan har bazaki godewa Allah da baiwar da yayi miki ba wlhi bazaki godewa azabarsa ba, inaso ki sani kefa da ranki da lafiyarki sannan zaki iya yin komai na aiyuka banbancin halittace ce dake, ƴar uwarki fa? da yanzu zakiga ana wasa da dariya da ita yanzu zata juye kamar ba ita ba?”

Anum tace “inayiwa Allah godiya, kinsan sharrin zuciya babu abinda bata aiyyanowa ɗan adam musamman ma idan yana fuskantar tsangwama da tsana..”

Isowarsu bakin get ɗin gidansu Jannat ne yasa dukkansu yin shiru tare da kallon juna,

Jannat takai bakinta dai-dai saitin kunnen Anum, kome ta gaya mata oho naji Anum ɗin tace “toh”

Anum ta koma can baya Jannat ɗin taje kusa da get tayi nocking lokacin har an fito sallahar magriba, “waye” mai gadi ya faɗa, “Nice haba malam Lado ka buɗemin mana”

Ƙaramar ƙofar ya buɗe kafin ya washe haƙora yana cewa “aiko Hajiya jannatu ki shirya karɓar faɗa daga gurin Hajiya domin kuwa tun tuni take sababi” ya ƙare maganar yana tafa hannu, taɓe baki tayi tare da nuna shi da yatsanta kafin tace “ni dan Allah karka dameni ka matsamin in wuce”

Tai maganar tana gyara ɗan siririn mayafin dake a kafaɗarta, da sauri ya bata guri ta wuce, da sauri ta nufi can bayan ɗakin mai gadin gurin ya kasance da kyawawan flowers masu kyau da ban sha’awa, tsala ihu tayi tana cewa “Lado dan Allah zoka taimaka min Please bansan meye a gurin ba” yana tafe yana jin radio yana cewa “kedai Hajiya wani lokacin idan kina abu sai kace ƴar yaye, ke da zaki wuce ɓangarenku mai ya kawoki ɓangare na, koda ya iso gurin tana tsugunne kanta a ƙasa, ƙarar horn ɗin motar dadynta da ta karaɗe musu kunnuwa ne yasa tai saurin dafe ƙirji tare da waro ido sbda gabaki ɗaya zuciyarta ta tsinke ta riga ta gama rayawa a zuciyarta Dady yaga Anum angama shikenan kashinta ya bushe….!

 

Mai kuke tunani Anum zata samu damar shiga gidansu Jannat kuwa?

Idan masu gidan da Ummu take suka dawo ya zatayi?

Ya kuke tunanin Arshi zatayi bayan babu kowa a gidan sai ita kaɗai?

 

Amsarku tana cikin littafin NISAN KIWO

 

Drop your comments saboda ku samu update akan lokaci, and then karku manta kuyi following account ɗina a arewabook

 

Mom Islam 08141799224

NISAN KIWO

 

Chapter 2🫰

 

https://arewabooks.com/chapter?id=652a963c3827a31172060506

 

cikin ɗaga murya akace “hahahaha bazakuje ku shirya ba, gashi Aljani ɗan ƙarami harya shirya?” Momy da Dady suka ruga da uban gudu, kai tsaye ɗakin farko na momy suka shiga, sukayi tsuru-tsuru, ko wanne da abinda yake saƙawa a ransa, Muryar Anum ta katsesu, dan sun haɗa baki da Jannat tace “ta rama mata dukan da Dady yayi mata ta hanyar firgitasu” aiko Jannat taje window ɗin momy ta sake sauya murya tace “hahahaha ku kaɗai muke jira saboda Aljanu sun taru a can inda kuke cin abinci bil adama ne kawai babu, ado zakuyi irin na bikin bil adama saboda muma munsha kwalliya” cikin sauri Dady da momy sukayi zigidir kafin…!

 

Please kuyi following account ɗina arewabook domin samun new update

 

Post a Comment

Previous Post Next Post