Littafan Hausa Novels

Kyandir Romantic Love Story Hausa Novel

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace
Written by Hausa_Novels

Kyandir Romantic Love Story Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

Kyandir Romantic Love Story Hausa Novel

( _Mai Hasken Banza_)

 

_A Romantic Love story_

 

*Free Book 1*

 

Page 1️⃣-2️⃣

 

WRITTEN BY

 

AMINA UMAR FARUQ

_Kwantagora_

 

Marubuciyar

*DA SANNU*

*ZUCIYATA CE*

*AFSANA*

*KYAUTAR ALLAH CE*

*HASKE BAYAN DUHU*

*ZAUJUN MAJNUN part 1*

*TAWAKKALI*

*ZAUJUN MAJNUN part 2*

*TASEERI*

and now

*KYANDIR*

( _Mai Hasken banza_)

 

*GODIYA*

Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.

 

_*SADAUKARWA GA*_

Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.

 

*_KYAUTA_*

Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad’an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu, dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na ‘DAYA ina fatan zaya nishad’antar daku ya ilimantar tareda fad’akardaku”

Jikar Iya Hausa Novel Complete

“Domin kuwa yana dauke ne wata iriyar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al’ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, taba zuciya inda wani shahararran me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*, sai gashi kwatsam yafad’a matsananci so da kaunar *’YAR* me gadin company sa,wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma bawanda ta tsana duniya irin wannan mutumin, aha! shin yakuke ganin tafiyar zata kaya?..hmm!, Akwai rikici hadeda chakwakiya is a very Romantic love story fa hhhh! akwai shanawa sosai, so kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha’allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna masoyana.

 

_*TUKUICI*_

Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.

 

*_TSOKACI_*

Wannan labarin ‘Kir’kirarran ne banyishi dan cin zarafin “wani ko wata” ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d’aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.

 

*_GARGAD’I_*

Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.

 

✍🏼

_Bismillahirrahamanirraheem!_

 

_KNT 6:30 PM SATURDAY_

 

“””””‘Yammace sakkali ta ranan asabar wanda yakasance lokaci na tsululun damuna, dan hakan akoda yaushe garin cikin hadari yake, kamar yanzuma wani irin gagarumin hadarin ne yahad’u agarin knt._

 

“Wato kwantagora kenan kwari makwanci rikici kwarin da ba ruwa yaci mutum lol…..aha kirarin garinmu kenan”, dan karkuce ai yan garinmu” marikita ne, sannan harda cin muta ne” ake to ba haka bane ahaaa lol!._.

 

“Dan haka sosai hadarin yake sake had’uwa, yana sake rikita garin matuka wanda yake kuma bazaranar bada ruwa ako da yaushe”,

 

Hakan yasa “kowa kagani sauri yake ya’isa gida dan kar ruwan ya’iskesa awaje”, dan haka garin yarikice da hayaniya sosai musamman hayaniyar ababen hawa wato mashina da motoci.

 

“Gudu kawai suke akan titi cikin saurin dan suga sun isa gidajansu dan kar ruwan yaduke su”, haka nan suma masu tafiya da kafa sosai suke sauri dan suga sun isa gida, “harda masu had’awa da gudu duk dan suga sun isa gida batareda ruwan yasauko ba”.

 

Acikin masu tafiyar kafan ne na hango wata yarinya wacce baza akirata doguwa can ba, sannan kuma baza ace da’ita” gajera ba tana dai tsaka tsaki, sanye takeda nikaq irin wanda baka iya ganin koda kwar idon mutum, da dogon hijab baki da yasauka har ‘kasa yarufe kafarta dayake sanye da safa baka, da takalmin roba me kyau fari da baki.

 

Dan hakan yasa babu abinda zaka iya gani ajikinta, kasan cewar hatta da hannunta data fito dashi tacikin aljihun hijab din duk sanye suke cikin safa, kallo d’aya zakai mata kagane cikin biyu dole zata kasance daya daga ciki wato ko dai d’alibar islamiyya ko kuma malama, kuma gadukkan alama daga islamiyyar tafito zata gida.

 

“Tafiya take ahankali cike da tsanani nutsuwa da kamala me matukar daukan hankali, tafiya take tamkar batason taka ‘kasa wanda idan ka kalleta sai karantse tafiyace tashiga d’aki bata zuwa gida ba, da alama hadarin bai dameta ba kuma ga dukkan alamu bata’ki ace ruwan yasauko ba, to amma kuma itama wai saurin take ta’isa gidansu, kamar yanda mutane keyi dan kar runwa ya’isketa ahanya shine take tafiya kamar bataso.

 

“Ahankali ta tsaya bakin titi cikin kamala domin ta tsallaka, cike da nutsuwa tafara waigawa gefen hagunta wanda tanan ababan hawan sukafi yawa, sannan ta waiga damanta inda taga wata tsohuwa rikeda sanda da kwano ahannunta, alamar dai almajirace ta taso daga gurin bara kuma itama tsallaka titin zatayi, saidai jikinta sai rawa yakeyi idan tayi yinkurin tsallakawa sai ta dawo da gudu saboda ganin yanda ababan hawan suketa gudu sosai akan titin,

 

“Ko kad’an babu alamar zasu dakata ta tallaka ga yamma tayi gakuma hadarin sai sake had’uwa yake, dan haka tayi tsaye jikinta sai aikin rawa yake.

 

Hakan yasa wannan yarinyar tamatsa kusa da’ita tareda dafa kafad’arta, ahankali cikin wata irin murya me dad’in sauti tace iya kema tsallakawar zaki?….da sauri cikin rawar murya tace “e…hhh! “yar nan, dan Allah taimaka mun ki tsallakar dani kinga yamma kuma idan duhu yayi bana gani sosai gashi hadari yarikice gari, idan har ruwan nan yadake ni kuma zazza’bi zanyi kinji?…

 

tace to ki kwantar da hankalinki” yanzu zamu tsallaka insha’allah! sai kin kai gidanki cikin d’akin ki” sannan ruwan nan zaya sauko da izinin Allah kinji?…tace to “yar nan Allah yasa hakan, to ameen iya bari mu tsallaka.

 

“Rufe bakinta yayi daidai da lokacin da ababan hawan suka d’an tsagaita, hakan yasa takamata suka hau kan titin danufin su tsallaka, saidai suna kai tsakiyar titin sai tsohuwar tazube kasa yayinda jikinta yadauki wani irin kyarma cike da tsoro, sakamakon zaninta da yatad’eta hakan ne yasata tafaduwa bashiri cikin sauri yarinyar nan tabita tareda rikota, tana fadin Subhallahi! sannun iya” kiyi ahankali kinji?…

 

yauwa sannu yar nan, iya ina fatadai bakijin ciwa ba?…da sauri ta amsa da a ah “yarnan banji ciwon komai ba, kedai kamani kid’agani mubar titin nan kar wani abin yasame mu, ina nufin kar mota ko mashi su bigemu “su wuce kuma sai kiga baza’ai komai ba.

 

Tunda kinsan shi talaka baya abakin komai musamman agurin wasu masu kudin, ko kad’an basa tausayin talaka arayuwar su” sai kace sune sukai kansu atalauci sukuma sukai kansu amasu kudi, sai suyi tafaman kyamar talaka.

 

“Cikin wani irin murya me nuna rashin jin dad’in hakan dayake kasan cewa tsakanin talaka da me kudi, tace haka ne iya” saidai kuma sun kyamaci talaka abanza tunda bashi yai kansa matalauci ba, kuma bazaya ta’ba dauwama atalaucin ba sannan kudin dasuke takama dasu Allah yagadama yabasu bawai wayonsu bane ko dabararsu bane yabasu, sannan suma bazasu ta’ba dauwama da kudin ba domin yana iya amsa daga garesun yaba “wani wannan duk cikin ikonsa ne.

 

Idan kuma har “yabarsu dashi to karsu” manta “mutuwa tana nan zuwa agaresu komai dad’ewa zata daukesu, batareda sun tafi da ko sisi ba ko?…”tace kwarai kuwa yar nan wannan magana taki haka take tace yauwa iya” to kin gani, dan haka kar ki damu babu abinda zaya same mu” da izinin ubangiji lafiya lau zamu tsallaka titin nan, batareda ko kwarzane yasamu jikin mu ba takarashe fadi tareda kokarin d’agata ta tashi.

 

“To kuma adai-dai wannan lokacin ne, wasu jerin gwanon dalla-dallan motoci na zamani sukaci wani uban birki ajejjere, wanda kad’an yarage basu bugi junaba wanda inda hakan yakasance kuwa, to dako ba karamin barna za’aiba tayanda ko wace mota zata samu mugun rauni, gashi ko kallo daya zakai motocin nan kagane tsadaddun gaske ne.

 

Domin kuwa akalla kowace daya kudinta zayakai naira miliyan dari da wani abu, yayinda zasunkai guda goma saidai mota ta biyu duk tafisu kyau da tsada domin kuwa royl roys ce wacce kudinta naira miliyan dari biyu da hamsin ne.

 

“Agaskiya motocin sun amsa sunasu motoci sun kuma ci kudinsu domin kuwa sunada matukar kyau da daukar hankali, musamman dasuka kasance kalar daukar ido wato baki sai sheki sukeyi suna daukar idon me kallonsu, ga lambar su me kyau da sha’awa wadda aka rubuta da manyan harufa kamar haka *T R TAFIDA 01* har zuwa *T R TAFIDA 07*, yayinda sauran ukun kuma lambarsu daban.

 

“Kai daganin motocin zakasan cewa kodai wasu shahararran kusashin acikin gwamnati ne aciki, ko kuma wasu hamshakan yan kasuwa ne aciki wanda yasuka amsa sunansu yan kasuwa, irin wanda ake damawa dasu acikin harkar kasuwanci na yau da kullum.

 

Aiko dai hakan ne domin kuwa cin birkin da motocin sukai ne, yasa acikin motar nan tabiyu wacci tafi sauran tsada wani hamshakin matashin d’an kasuwa ne, zaune akujerar baya ahankali yad’ago dakai daga karatun jaridar daily trust din dayake,

 

“aikam take kyakkawar fuskarsa ta bayyana me cike kwarjini da haiba wacce ke dauke da dogon hanci da d’an karamin bakinsa da yaketa tsotsa tamkar yana tsotsan minti, tareda zagayayyan sajansa daya kwanta luffff!, had’eda d’an gemunsa da yawancin samarin yanzu suke yayin bari saboda passion.

 

Duk dacewa fuskar babu fara’a hakan bai hana bayyana cewa shidin kyakkawa ne ba ajin farko, shidin ba fari bane sannan kuma ba baki bane wul wato dai irin kalar nance me matukar tsada wato chocolate color, irin me shaini din nan ne me matukar kyau datsari atakaice dai yanayin fatar nashi tamkar irin mutanan nan dasuka kasance ruwa biyu,

 

wani abin mamaki kuma shine gashin kanshi acukurkude tamkar na fulani sai sheki takeyi alamar tanasamun gyara, to saidai kuma ba abin mamaki bane domin kuwa idan ka kalleshi da kyau yana matukar kama da irin fulanin nan da’ake kirada sullu’bawa, masu su’bul da abin wani lol.

 

“Sanye yakeda wani irin royal blue yadi me tsananin kyau wanda ko ba’a fad’a makaba kasan tsadadde ne, sai akai mashi dinkin zamani irin wanda akema ratsi dawani color yadi, dan haka nashi sai aka ratsa yellow yadi hakan yasa dinkin yai matukar kyau da tsari,

 

wanda yafito da tsantsan kyawunsa hadeda zubin halittarsa me daukar hankali, domin kuwa kirarsa irinta cikakkun mazan nan me masu yawan matsa jikinsu, dan haka dukkan damtsam karfi sun d’an fito tayanda yasake fitar da kyansa na asali, yayinda dogon hannunsa dake kwance da lallausan bakin suma yake daure da agogon gwal, wanda ko ba’a fad’a maka ba kasan tsadadde ne kafarsa sanye da fararan takalmi half cover masu kyau da daukar ido yayinda kunnasa ke makale da bluetooth wanda yasake fito da gayunsa.

 

“Kai atakaice dai matashin nan yahad’u kwarai da gaske, kallon d’aya zakai masa kagane jin dad’i da kwanciyar hankali had’eda nutsuwa su riga sun gama samun gurin zama ajikinsa tin tsawon wani lokaci, akalla zayakai shekaru talatin da biyar aduniya *TAUFIQ RASHIDI TAFIDA* kenan hamshakin matashin me kud’i ne sosai da gaske, kasan cewarsa d’an kasuwa ne da sunansa yafantsama ako’ina daga gida nageri har zuwa kasashan waje yayinda yakasance daya daga cikin kusa acikin gwamnati da ake matukar ji da alfahari dasu akan aikinsu.

 

“Ahankali yamutsa beauty fice dinsa, tareda juya brown din kwayar idonsa me tsanani kyau da d’aukan hankali tareda saka marajin magana natsuwa, sannan da kyar yamotsa d’an karamin bakinsa me dauke da kyawawan lips dinsa wanda yake pink pink black black wanda hakan yahad’u yabada wani irin kala me kyau da tsari, dai-dai lokacin da direbansa wanda yakasance dan sanda kokarin bude motar yake zaya fito, da alama yanasan gani meke faruwa ne.

 

“Cikin wata iri yar cold voice me cike da izza da isa hadeda zallar takama irin tawasu masu kudi sannan yace sajan labaran yake faruwa ne?….cikin rawar jiki yace yallabai ban saniba shine nakeso nafita naduba, yace ok pls kayi sauri namatsu mu isa gida because of nagaji sosai wlh I need to rest sosai, so kaje kaduba pls come back quickly ok?….da sauri yace to yallabai tareda nufar gurin.

 

“Yayinda shikuma yakalli d’an t-v dake manne amotar wanda yaketa aiki shi kad’a, ba tareda ana kallon shiba tsaki yaja mtsw! tareda d’aukan remote din t-v yakashe dai-dai lokacin da d’aya daga cikin tsadaddun wayoyinsa tayi kara, cike da isa yakalli wayar sunan da yagani yabayyana akan screen din wayar ne yasashi sakin kayataccan murmushi.

 

“Hankali kamar bayaso yafurta my first love saida yabari ta tsinke sannan yakira cike da shagwa’ba yace Oh! my lovely Momma sauran kad’an nakaraso naji d’umin jikin, u know I really miss u so much ba?….banji me tace” ba saidai naji yasake cewa yes! Momma I know, ok gani nan karasowa insha’allah yai kiss din wayar tareda sakin murmushi yace byeeee!, sannan yakashe wayar tareda ajiyewa yad’anki jaridar yacigaba da dubawa.

 

“A tsakiyar titi kuwa sakamakon ganin wannan tsohuwar da wannan yarinyar tsugunne akan titi, yasa da sauri direban motar farko yaja birki wanda hakan ne yasa dukka sauran motocin suma cin birki bashiri wanda kad’an yarage mugun hatsari ya’afku.

 

“Hakan ne yasa direbar motar farkon yayi kokarin fitowa cikin sauri dan yaimasu magana lafiya suka tsaya akan titi, to kuma sai yafasa saboda ganin wannan da’aka kira sajan labaran har yariga shi nufar gurinsun.

 

Yayinda ya kallesu cikin fad’a yace malamai lafiya ku ka tsaye akan titi haka eye?…ko ku kafine?…,to ai koda kun kasance makafi bazakuzo kan titi ku tsaya ba tunda ai bagurin tsayuwa bane ko?…

 

“Daga iyar har yarinyar” babu wanda yabashi amsa ko d’aya acikin tambayoyin da yajero masu, asalima sai kokarin d’aga “iyan da yarinyar takeyi” inda idonta yasauka akan lambar motar hakan ne yasata cikin alamar bacin rai tafurta uhum! aidama sai “shi d’an raini hankali kawai, da sauri iyar tace yar nan “wanene fa?….

 

cike da nuna alamar takaici tace” iya wani banzan “mutum ne da baya kaunar *TALAKA* arayuwarsa”, shiyasa nima duk duniya babu mutumin dana tsane irinsa”, iya banason “mutumin nan ko kad’an” cikin d’an bacin rai iyan tace yarnan nima banasan shi” tunda baya kaunar mu *TALAKAWA*,

 

amma yar nan baki ganin yanada dalilin dayasa yake ‘kin talaka?…. a ah iya bashi da wani dalili, tace to yarn nan kin sanfa muma *TALAKAWA* bamuda dama haka kawai sai kiga munajin haushin me kudin, da sauri tace iya duk da hakan bashida wani dalili kawai dai shi dan yaga yanada kudi ne shiyasa, tace to yarn nan amma naji ajiki kamar yanada dalilin,

 

tace humm! iya kenan kedai karkiyi kokarin karesa” agurina domin ni bazaya ta’ba fari agurina ba saboda natsane shi wlh, takarashe fad’a tareda kokarin kama iyar tamiki wacce tasaki murmushi me cike da ma’ana wanda nikam banshi ma’arsa ba.

 

“Shiko sajan labaran tunda yaga ko suwane sai yakoma da sauri ya fadawa ubangidansa, cewa yallabai ai wasu” banzayan talakawa ne suka tare mana hanya, cikin tsanani fushe yad’ago yallesa yace dalla gafara kaje kace subamu hanya zamu wuce, idan kuma bazasu bamu hanya ba kafad’awa sajan iliyasu yabita kansu muwuce ko mun “takesu mun take banza, kuma babu abinda za’ayi kaji ko?…cikin rawar jiki yace to yallabai tareda komawa gurinsu”.

 

“Yace dalla gafara malamai kuyi sauri kuwuce kubamu hanya muwuce kunji ko?…dai-dai lokacin da tad’ago iyan, wacce cike da mamaki tace kai yaro yanzu sai kubi takanmu kuwuce?… itama yarinyar jin abinda yafad’a ne yasata cewa kinji ko iya mutumin fa bayada mutunci, sannan tad’ago kai dasauri ta watsa sajan labaran din harara ta cikin nikaq din,

sannan cikin bacin rai tace ah! ba oganka yace” idan bamu wuce ba kubi takanmu kuwuce ba kuma baza’ai komai ba ko?…

 

to bazamu wuce din ba dan haka sai kubi takanmu kuwuce tunda mudin *TALAKAWA* ne abin banza, da idan an takamu antake banza bakuma za’ai komai ba ko?…..ido direban yazaro cike da tsanani tsoro saboda jin abinda tafad’a, aransa kuma yace innalillahi! ya’akai “taji abinda yallabai yafad’a”?…

 

alhalin bayanshi babu wanda yaji abinda yallabain yafad’a, to kodai ba mutane bane?…aikam take zuciyarsa tabashi amsa da tabbas wayan nan ba muta ne bane aljanu ne, kai bakaga yanda sukai tsaye akan titi ba hankalin su kwance, aikam zuciyarsa nagama fad’a masa hakan yaji cikinsa yai wani irin ‘kululuuuuu! cike da mugun tsoro ya kalleta tareda had’iye miyau jikake ‘kutttt!, cikin bala’in tsoro had’eda rawar murya yace……

 

Aha

 

To muje zuwa ne?….hummm! idan naga ruwan comments zan cigaba, idan ko naga sa’banin haka tsaf zan ajiye alkalamina aha.

 

_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya ‘kayyu mu.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment