Gidan Arna Hausa Novel Complete

Gidan Arna Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*GIDAN ARNA*

 

 

*By S-REZA *

*(Writer of Uwata ce sila)*

 

*First class writers asso…*

 

*Kaman yanda na ce muku labarin a kwai kwamgaba-kwambaya to tabbas haka ya ke. Labarin iyayen yaran da kuma labarin yaran wanda shine a salin labarin. Fatan dai kanku ba zai ƙulle ba? Ku dai ku biyo ni ku sha labari..*

 

_Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaban halittu Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama. Ya Allah kaman yadda na fara rubuta wannan littafin lfy Allah kasa na gama lfy. Allah ka amince mini na tura wannan saƙon dake cikin wannan littafin izuga masu irin wannan ɗabi’ar, sannan Allah kasa ya zama silar shiriyar su. Amen Amin._

Aure Uku Hausa Novel Complete

_Sadaukarwa ga Aminiya ta kuma abokiyar aki wato…_ *Chamsiya D Amadu.*

 

*Bismillahi Rahaman Rahim!!*

 

*PAGE 1️⃣*

 

*GARIN JOSS NIGERIA*

 

…Da ƙyar ta iya lalibo kalmar daga bakinta tsabar ɗaci da ranta ke mata duk a kan abin da har izuwa yanzu bata da masaniya a kai, sannan wacce a ke mata abin domin ta itama har yau taƙi sanar da ita komai bare har ta iya kare kanta a kan hakan. ta ce “Da gaske Mama Ashana ce sanadiyar wannan halin da kike ciki? Fauza ta tambayi mahaifiyar ta cike da tsoron jin amsar da zata bata domin kuwa tasan amsar dai ɗaya ce. Wani irin murmushi Anty Badau ta saki sannan ta kunna karan sigarin da ke hannunta ta shaƙi hayaƙin sannan ta ɗaga kanta sama tana kallon rufin ɗakin sannan ta saki hayaƙin daga cikin bakinta izuwa gurin da take kallo ɗin, ta na kallon yadda hayaƙin ke zaga ko ina cikin ɗaƙin sannan tana ƙara jin abubuwan da suka cika mata kai suna bin wannan hayaƙin suna tafiya tasu dudiyar. Sai da Anty Badau tayi haka sau uku kafin ta take sauran karan sigarin da ko rabin sha batayi ba, ta miƙe tsaye ta matso kusa da ƴar tata wacce ta ke tsaye tana jiran amsar tambayar ta. Cikin zafin rai da ɓacin rai a kan wannan maganar da Fauza ta yi yasa ta ce “Nafi ƙarfin uban da ya haifi uban Ashana ma ba ita ba, wallahi bata isa tace itace sanadiyyar wannan halin da nake ciki ba, sai dai ma ni nace ni ce sanadiyar halin da take ciki, kuma karki damu da abunda tamin domin ni ce na bata wannan damar…”Cikin tsawa kai ka rantse ba mahaifiyar ta ba ce Fauza ta katse Anty Badau da cewar “Anty kina cikin hankalin ki kuwa? Kinsan abunda Mama Ashana da Saudat suke shirya wa kuwa da har ki ce kece kika bata dama…kar ki sake kicemin da gaske Mama Ashana ce ta buɗe miki ido kamar yanda Saudat ta ce mini? Kenan da gaske ne Mama Ashana da Saudat sunci galaba a kan ki? “Da sauri Anty Badau ta ce “Karna sake jin wannan kalmar daga bakinki domin kuwa Ashana da ƴarta bazasu taɓa cin galaba a kaina da kuma ke ba, mutuƙar keɗin jininace. “To Anty menene gaskiyar zancen? Fauza ta tambaya tana kafeta da ido tana tsoron jin abunda zai fito daga bakin uwar tata. A zuciya Anty Badau ta ce “Allah ya nuna mini girmanki Fauza, sai na ba mara ɗa kunya. “Zamuyi maganar amma ba yanzu ba labarin yana da tsayi. Anty Badau ta faɗa tana share hawaye domin tuno rayuwar su ta baya.

 

***

Ban taɓa tsanar wata halitta a duniya kamar yanda na tsani Badau da ɗiyarta Fauza ba, wallahi da inada damar da zan iya shafe rayuwarsu a doron duniya to da ba’a kai wannan matakin da muke kai yanzu ba, zan ɗan-ɗana mata wutar masifa da bala’i a cikin gidannan wanda hakan zaisa ta bar gidan da ƙafarta. Cike da ƙosawa Saudat ta ce “Wai mene ne tsakanin ki da Anty Badau ne da har yau kinƙi sanar mini da Komai ne? Wacce mamalakin wannan gidan da har yau kunƙi sanar da kowa ne? Kuma mai yasa a ka sawa wannan gidan irin wannan sunan da kowa yake alawadai da shi da al’ummar da ke cikin gidan? Da sauri Mama Ashana ta kalli Saudat wacce take da buri, fata, muradi a kanta, ta zama magajiyarta a kan wannan sanar tasu, kuma tabbas ta yarda da cewar ta samu magajiya domin kuwa ko a iya yanzu da take yarinya ƙarama tana iya aiwatar da komai kamar dai yanda uwar tata take so. Batare da ta bata amsar tambayar da ta mata ba itama ta watso mata tata tambayar. “Kar ki damu da abunda al’ummar gari suke cewa domin kuwa dare nayi sune suke cika mana gidan, sannan kin taɓa gani wani ko wata sun shigo cikin gidan nan sunyi wata maganar banza a kansa? “A’a “To kawai kema kiyi abunda ke gaban ki. “Mai ya faru tsakanin ki da Fauza? Mama Ashana tayi tambayar cikin nuna son jin amsar ta yanzu-yanzu. Ganin haka yasa itama Saudat ta bata amsar a taƙaice. “Faɗa mukayi”. “Akan me? Ashana ta sake jefa mata tambayar da tasa Saudat ɗin kallon fuskar mahaifiyar tata ganin yanda tayi kicin-kicin da fuska. Babban baƙin cikin Ashana a ce yau Fauza taci nasara a kan Saudat, ko kuma Anty Badau ta ci nasara a kan ta. A komai na rayuwa burninta a ce ita da ƴarta su zama abun kallo a gurin su Anty Badau, tanada buri sosai a kan ƴarta hakanne ma yasa take kula da ita a kan komai na rayuwa, domin kuwa bazata taɓa manta abunda ya faru tsakanin ta da Anty Badau ba.

 

Saudat cike da tsiwa da rashin kunyar da ta gado a gurin mahaifiyar tata ta ce “Muna zaune da su Habib ne tazo take mini gori wai mamarta ce mai wannan gidan har tana cemin sun kusa su koremu daga gidan, shine fa nima nace ai uwarta ce ƴar karere a gidan, kuma mun kusa mu koresu, shine fa ta fara min gori k…” Cikin sauri Anty Ashana ta ce “Ke kuma mai kika ce mata? “Wannan maganar da kika faɗa mini ita fa kawai na faɗa mata shine ta fara kuka ta nufi ɗakin uwarta…Saudat ta ci gaba da cewa… kuma kowa dake gurin sai da ya mata dariya. Mama Ashana ta kwashe da dariya tana kamo Saudat tana saka mata albarka sannan ta ƙara sanar da ita wasu abubuwan da zata dinga sanar mata a duk lokacin da wani abun ya haɗa su. Suna zaune Zee ta shigo ɗakin tana kallon yanda suke cikin farin ciki.

 

***

A shekarun baya da suka shuɗe anyi wasu aminan juna a duniyar bariki kuma ƴan amutu a kan junansu wato Aisha  da kuma badawiya. Su ɗin karuwai ne masu ji da tashin iskanci wanda karankaf faɗin garin Jos da Lagos an san da zamansu. Babu ruwansu zasu iya kwana da namiji ɗaya a gado naƴa. Sun yarda da junansu irin yarda da wani baya aiwatar da komai sai da sanin ɗayan. (A kan ce a bari babu a mana to amma fa tsakanin Badawiya da Aisha a kwai ta mai ƙarfi ma kuwa.. amma dai bari muka ƙarshen abun)

 

A bariki suka haɗu amma idan kaga yanda suke rayuwar su sai ka rantse cewar su ɗin ƴan uwan junane. Kayan sawarsu a haɗe yake, kowacce zata iya amfani da kayan ɗaya, sannan ɗakin kwanansu ɗaya ne, haka zaluka idan sun fita sun samo kuɗi shima kowa yanada ikon yin yanda yaga dama da wannan kuɗin koda kuwa ba tare su kayi aikin ba. Aisha da Badawiya sunyi yawo a gidan karuwai masu tarin yawa kafin suma su zama wasu abun. Wani abu guda ɗaya da zai baku mamaki a kan wannan amintar tasu shine…Basu taɓa zama kowa yaba kowa labarin farkon rayuwarsa ba, sun bar wannan a matsayin sirrinsu. Sannan su basa lesbian kuma basa yarda a yi amfani da su ta baya. (Wannan kenan)

 

Kaman yanda kowa ya sani cewar ita nasara ba’a samunta cikin sauƙi, sannan kuma bata samuwa ga rago. To wannan ne ya faru da su Badawiya.

Forkon shiga harkar sun sha wahala sosai domin a lokacin dukkaninsu sabbin shiga ne, daga Jos suka koma Lagos wanda shima dai saida suka tabbatar da cewar lallai bariki ba sauƙi. Sunada kyu dukkanin su domin kuwa kallo ɗaya zaka musu ka yarda da hakan. Badawiya tafi Aisha hasken fata kuma ta fita tsayi kaɗan, sannan ta fita sakin fuska da saurin yarda da mutane, haka zaluka Badawiya kallo ɗaya zaka mata ka gane cewa ita ɗin ruwa biyu ce. (Ma’ana ba Hausa ba ce gaba da baya ba) Aisha kuwa kallo ɗaya zaka mata kaga cikikkiyar bahaushiya, sannan ita bata da sakin fuska ga saurin fushi, tanada dogon hanci kaɗan sannan tafi Badawiya diri. (Kai abun dai sai Masha Allah domin kuwa su ɗin sun cika matan zamani)

 

Shekara ɗaya a Lagos suka gama gane harka, a cikin wannan shekara ɗayan sun zauna a gidan karuwai ya kai kala shida, tsabar rashin kunyar su da kuma neman rikici. A haka suka samu wani gidan karuwai wanda ya tara ƴan duniya irinsu dama waɗan da suka damasu suka shanye. A wannan gidanne suka ƙara tabbatar da cewar a shefa suɗin basu kai ko ina a wannan harkar ba. Gidan babban gida ne mai ɗauke da ɗakunan mazauna cikinsa. Ko wani ɗaki na ɗauke da sunan mai shi da kuma hoton mai ɗakin da numbar mai ɗakin. Ƴan daudu kuwa sunfi biyar a cikin gidan. Kallon juna sukayi suna jin cewar wannan gidan shine saidai da su. Ai kuwa suka nufi cikin gidan kowacce goye da jakar ta a ba ya (Wannan kenan)

 

***

Anty Badau ta fito daga cikin ɗakinta tana kallon filin tsakar gidan nasu wanda a yau gaba ɗaya bata loƙo waje ba tsabar far gaba. Kafin ta iya cewa komai saiga Amal ta shigo gidan cikin yanayin tashin hankali. Jaka a hannun hagu, sai taƙalmi a hannun dama, tana tafiya kamar wacce taje filin yaƙi. Ba tare da ta luran da sauran ƴan gidan da suna ganin ta kowa ya miƙe cike da mamakin ganin ta ɗin a wannan lokacin ba. Ita kuwa Amal ɗakin uwar ɗakin tata ta nufa kamar zata faɗi. Ganin haka yasa Anty Badau koma wa cikin ɗakin tana bata guri. Bayan Amal ta wuce ne Zee ta miƙe da sauri tayi ɗakin Mama Ashana. Tana shiga bata tsaya wata-wata ba ta sanar mata da cewar Amal ta dawo kuma da a lamar a tsiyace ta dawo domin kuwa yanayin ta kawai zai nuna cewar zuwan banza tayi. Mama Ashana ta rangaɗa wani uban kuɗa suna tafawa da Zee kafin ta ce “Ina Habib ya zo yaje ya jiyo mana halinda a ke ciki. Suka tintsire da dari kafin Zee ta kalli uwar ɗakin tata ta ce “Ashana yaufa gaba ɗaya baƙar munafukar bata fito tsakar gida ba, Alamu dai sunnuna cewar ta tsorata da ke ne. Mama Ashana ta miƙe tsaye cikin farin ciki ta ce “Amal ce matsalar farko a gidannan domin ita ɗin ba ƙaramar mai wayo bace, yarinyar tasan mai take yi. Zee ta ce “Kardai kice tana baki tsoro ne? Murmushi ta yi ta ce “Ki saurari abunda zai biyo bayan dawowar tata, ba dai tana murna akan wannan karan sune suka ci zaɓe ba, to ayi mugani.

 

Amal kuwa tana shiga ɗakin Anty Badau ta jefar da jakar hannunta da taƙalman ta faɗa kan gadon tana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. Koda Anty Badau ta shigo ɗakin kallo ɗaya ta mata tasan cewa a kwai matsala. A fili ta ce “An yanka ta tashi! Tana zaune ita kaɗai a ɗakin tana tunanin abubuwan da suke faruwa a tsakanin ta da yaran ɗakin nata sai taji sallamar ɗaya daga cikin amintattunta “Gafaranku dai masu ƙasar” cewar Habib yana shigowa ɗakin cikin sauri. Ai da sauri Anty Badau ta miƙe zatayi magana Habib ya katseta da cewar “An shiga uku mai zan gani haka wai ni Habiba da yankan ragon laiya, kamar Amal gwarzuwar shekara nake gani cikin wannan lokacin kuma a wannan gidan sannan a wannan yanayin? Ko dai gizo idona kemin ba ita bace? (Habib kenan mai ɗan banzan surutu da iyayi) Yayi magana yana ƙarasawa kusa da Amal ɗin zai tashe ta domin kuwa hankalin sa yayi mugun tashi. “A’a Habib barta ta huta  a gajiye ta dawo. Habib ya kalli Anty Badau da kyu ya ce “Wallahi Anty Badau kawai saboda kece kika ambaci wannan sunan  ba dan haka ba kwaran-kwatsa sai mun baiwa hammata iska a gidannan…ya ana cikin wannan tashin hankalin amma kina sako wani zancen daban, a ce gwarzuwar shekara a gida kuma kina sako wasa. Kafin Anty Badau tayi magana sai suka ji an turo ƙofar ɗakin anshigo babu ko sallama. Tasan idan ba Habib ko Amal ko Fauza ba to babu wani ma’aluƙin da zai iya shigowa cikin ɗakinta a cikin gidan nan koma wacece. Fauza ce ta dawo daga school, batare da ta yi magana ba ta shiga cire kayan school ɗin tana kallon Amal cike da mamakin ganin ta a kwace a gida. Anty Badau ta kafe Fauza da ido tana aiyana wasu abubuwa da dama a kanta. “Anya bazata shigar da Fauza cikin wannan harkar tun yanzu ba, idan har ba so take sunanta ya dishashe a duniyar bariki ba to ya kamata a ce ta daina wahala a kan yaran wasu, kawai tayi amfani da ɗiyar cikin ta domin kuwa Fauza ta haɗa komai da a ke buƙata, matsalar kawai tayi yarinya ne, amma kam bazata tsaya kullum tana kwasar baƙin ciki ba. Yanzu ga Amal da kowa yake mata kallon mai wayo da iya taku da sanin abun da takeyi to itama gashi ta dawo kuma a lamu sun nuna cewar itama ba’a yi nasara ba, ai kuwa idan hakan ta faru to tabbas mutuncinta zai zube. A lokacin da Anty Badau take wannan tunanin a wannan lokacin shima Habib yake kallon Fauza yake aiyana hakan a ransa. A hankali Anty Badau ta ce “Bari dai Amal ta farka muji komai daga gare ta.

 

Fauza ta gama cire kayan jikinta ya rage daga ita sai… Sannan ta shiga tolet ɗin dake cikin ɗakin. Bayan ta shiga dukkaninsu suka dawo da kallonsu izuwa ga junansu, ai kuwa suka haɗa ido kowa ya sauke ajiyar zuciya suna kallon juna. Kallo ɗaya Habib ya ma uwar ɗakina tasa ya gano abun da take aiyanawa. Fauza kuwa tana shiga ban ɗakin ta ƙarasa cire kayan jikinta da suka rage sannan ta kalli kanta daga sama har ƙasa a jikin madubin ɗakin, sai kawai ta fashe da dariya tana tuno lokacin da Amal taci gasar da kuma tafiyar ta da kuma yanzu da ta ganta a gida wai har ta dawo. A fili ta ce Anty Badau kenan wato ku yanzu a tunaninku bansan komai ba ko? To da da yanzu ba ɗaya bane, idan ke kinyi karuwanci a baya kina tunanin kinsan komai to yanzu zamani ya sauya muje zuwa dai naga gudun ruwanku.

 

***

Saudat ta kalli sartakeken namijin da take kan cinyarsa ta ce “Komai da ka ga ina yi to a ankare nake, domin kuwa nasan mai nakeyi. Lokman ya ce “Kinga tashi na kaiki kafin wani yazo ya samemu a haka. Dariya Saudat tayi sannan ta miƙe ta shiga saka kayan makarantar ta ta na cewa “Tsoro kake ji ne? Bai bata amsaba ya shige toilet yana sakar mata murmushi. Da sauri ta fito daga cikin motar Lukman ɗin domin kar wani ya ganta, ai kuwa tana sauƙa yaja motar tasa ya bar gurin da gudu. Tsayawa a ƙofar gidan nasu tayi wanda a kullum kwanan duniya kafin ta shiga cikin gidan sai  ta tsaya ta kalli sunan gidan nasu dake manne a bagin mashigar gidan. A gidan a ka haife ta, sannan a gidan ta girma, amma kullum tana mamakin irin gidansu, kullum idan zata shiga gidan sai ta karanta sunan gidan nasu kafin ta shiga, kullum tama kin komai na cikin gidan nasu, gida sai ka ce hotel harda suna a saman gida.Yanzu ma a fili ta karanta sunan gidan… *”GIDAN ARNA!.* Ita har zuwa yanzu ta kasa gane mene ne ma’anar Gidan arna?

 

Tana shiga gidan ta tsaya tana kallon mamaki ganin yau kusan kowa yana gida. Bata tsaya magana da kowa ba ta nufi ɗakin mahaifiyar tata cike da mamakin ganin yau kowa na gida abunda bata saba gani a gidan nasu ba. Tana shiga ɗakin taci karo da Zee zata fito daga ɗakin. “Saudat an dawo daga school ɗin? “Eh na dawo Allah yasa dai a kwai abinci a gidannan? Zee ta ce “Ai yau dole ma kici abinci harda nama da laimon kwalba domin kuwa Amal ta dawo gida. Chak Saudat ta tsaya da ƙoƙarin cire kayan da take yi tana mamakin wai Amal ta dawo “Gwarzuwar shekara ce ta dawo gida? Cewar Saudat cikin dariya? “.

Post a Comment

Previous Post Next Post