Littafan Hausa Novels

Aure Uku Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Aure Uku Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

AURE UKU.

By

CHUCHUJAY

EPISODE 1⃣

 

KIRIKIRI MAXIMUM PRISON LAGOS STATE NIGERIA.

A kullum zaryarta zuwa prison ɗin yana mutuƙar bata mata rai ,

Bata jin wani tausayi ko rashin jin daɗin abunda yake faruwa da shi duk da irin ɗinbin san da tayi masa a baya,

Ta sa a ranta akan cewa kaddarar sa ce,duk wani wanda zai nuna mata rashin dace wa akan bibiyar sa Ya bata takardar sakin ta Kallansa kawai take sannan bata sawa a ranta domin ta gama yarda da yarda ɗan Adam yake da hallayyarsa,

Badriya Hausa Novel Complete

Cikin handcuff Dukkan hannayen sa biyu Haka aka rako sa ,kallan sa kaɗai yakan sa mata faɗuwar gaba ,hakazalika a yanzu haɗa ido kawai da tayi dashi sai da Taji mumunar faɗuwar gaba Ta kawo mata ziyara,

Abubuwan da suka faru tsakaninta dashi take suka fara tariyo mata ,danne su tayi dan tafiyar su babu abinda ya haifar mata sai tashin hankali da dana sani,

Kallanta ta mayar gareshi dan ta gama yarda a yau sai tabar kirikiri da sakinsa akanta,

Glass Mai Kauri ne tsakaninsu Wanda yake ɗauke da bulloli Shida,telephone ɗin dake sakale a gefenta ta ɗauka ta kara a kunne yayin da shima yayi halkan,

 

Magana ta fara “Hafiz nazo ka bani takarda ta dan Allah mu daina bata lokacin juna kodan zaman mu na farko kan ka chanja Mai ɗan dadi duk da yaudara ne, ka sakeni dan koda ace huƙuncin ka ba kisa bane ta hanyar rataya ,koda kuwa ace za’a cire duk wani charges akan ka,Hafiz bazan taba sake zama da Kai ba.

Kukan da yasa shine abunda yayi mutuƙar bata mamaki,tasan wanene hafiz mutum ne Mai mutuƙar juriya da jarumta ,amma a yau yana mata kuka dan kawai tana masa maganar Ya sake ta,

Shiru tayi tana Mai jin kukan nasa ta cikin telephone ɗin a yayin da yake ratsa dukkan wani sasshe na jikinta,

Ina ma hafiz bai zabi tarwatsa rayuwarsu ba ,ina ma ba’a kamasa da laifuka mafi munin wanda aka kamashi dashi ba,

Ina ma!

Tana kokarin cire telephone ɗin dan bazata iya cigaba da jin kukansa ba ta tsince muryarsa yana cewa”UMAIMAH dan Allah dan Annabi kar ki takura mun na sake ki,ni mutum ne Mai laifuka da dama a wajen ubangiji, kila yamun Rahma sakamakon mutuwa da zanyi a matsayin mutum mai Aure,”Ke mutuniyar kirkice UMAIMA ,a dukkan rayuwata ban taba Auren mace Mai kamala da haƙuri ba kamar ki,ke maratussalaha ce ,ke macece yar Aljanna,Mai tausayi da jin kai,dan Allah UMAIMAH kimun wannan Alfarmar guda ɗaya duk da kuwa ni Azzalumine a wajenki.

 

Bata san lokacin da ta kwace da wani irin kuka ba Mai mutuƙar cin rai,

Take duk ikirarin da take na rashin jin tausayinsa Ya kau dan ta tabbata koda a ce babu soyayyar sa a tattare da ita tasan tabbas yana da soft spot a wani gurbi na zuciyarta,

Tana kokarin cire telephone ɗin yace”UMAIMAH bana so na mutu,Ina mutukar tsoran zuwa na haɗu da mahaliccina,bana so umaimah ,Ina san na rayu na dai dai ta tsakanina da ubangijina na rayu da ɗana wanda shi kaɗai Allah Ya bani,sannan babban farin cikina ta tsatsanki Ya fito,”Amma kash kaico na ,bani da wata damar ,nayi wasa da wadda Allah Ya bani ,nayi fatali da kyautar ni’imar da yayi mun saboda san zuciya da kwaɗayin duniya wanda a yanzu Ya kaini Ga dana sani,

UMAIMA gobe za’a rataye ni ,gobe zan mutu,babban tsorona kenan,a razane nake da Ya zamana nasan ranar mutuwa ta.

 

Shiru tayi tana Mai kallan sa ta glass d’in da Ya rabasu,hannunta tasa ta dafa glass ɗin a dai dai inda Ya ɗora hannunsa ,

A hankali ta shafa tana Mai tuna yarda ya nuna mata soyayya kamar zai cinyeta a wata biyu na Auren su,

 

Lumshe idanunsa yayi wanda suka faɗa saboda tsantsar masifa yace”kar ki bawa ABDALLAH labarina idan Ya girma,bana san yasan babansa failure’ ne a rayuwa sannan na yarda da zaki bashi tarbiyya Mai kyau,kar ki barshi Ya rabi dangina dan na bar miki shi halak malak,dangina ba mutanen da zanyi Alfahari dasu bane Kema kin sani sune mafarin jefani cikin wannan masifar,ina so idan da dama ki raini ABDALLAH Ya zama cikakken Mahaddacin Qur’ani ,Ya zama malami akasin mahaifinsa,”

Idan Kinje gida a side drawer dake gefen gadona na aje cheque na milliyan goma ,ki ɗauka ki juya ma ABDALLAH ,wallahi tallahi ba ta hanyar banza na samesu ba,kuɗi ne masu tsafta babu gurbaci a cikinsu,

Kisa Abdallah yana mun Addua ,Kema idan har da dama zan samu a gurinki bazan ki ba, duk da nasan abun zaiyyi wuya duba da yarda na cutar dake a rayuwa.

Ina mai mutuƙar baki hakuri akan ki yafe mun,Allah Ya baki miji Umaimah wanda yake salihi, Ina Mai miki addua ki Auri miji nagari ba irin mazajen da kika AURA GUDA UKU BA.

Allah Ya haɗa fuskokinmu da Alheri.

Nagode Allah yayi miki Albarka.

 

A Yarda ma’aikatan suka kawo sa haka suka ƙara tasa keyarsa dan komawa da shi kurkukun da suka dauko shi,

Buga glass ɗin tayi wanda hakan yasa shi tsayawa,ma’aikatan basu ja ba dan sukan bawa wanda yayi expire dama duba da duniyar ma barinta zaiyyi baki Ɗaya,

 

Roban take away ta ɗauko daga jakarta wanda bata san dalilin da yasa ta zo dashi ba,ɗaya daga cikin ma’aikatan ne Ya zagayo Ya karba,Ya juya zai tafi tace masa”ka faɗa masa Na kawo masa favorite dambun naman kazan da yake so sannan ni na soya,sannan insha Allahu indai na dena masa Addua to numfashina ne Ya yanke daga jikina,sannan zai Alfaharin abunda zai tafi Ya bari.”

 

Wani irin kuka ta fashe dashi a yayin da taga yana mata murmushi lokacin da aka aika masa da Saƙonta,da sarsarfa ta tashi tabar gurin tana Mai Kallan yarda aka maidashi har a lokacin murmushin na akan fuskarsa,

 

Kuka take sosai a motarta tana Mai jin wani irin zafi a cikin kirjinta,tabbas rayuwar Hafiz babbar Aya ce ga mutane .

 

WACECE UMAIMAH ?

 

DR UMAIMAH USMAN BULAMA,

Ƴa ɗaya tilo a gurin Amaryar Alhaji usman bulama,

Alhaji usman bulama mutumin Zaria ne wanda zama Ya kaishi garin ADAMAWA YOLA garin FULANI tushen kunya,

Alhaji Bulama sharraren mai kuɗine wanda ake lissafawa a cikin dumbin masu kuɗin duniya ba kasa kawai ba,

Architecture ne wanda Allah ya habaka a hanyar domin irin tsabagen basirarsa,

A irin buɗin da Allah yayi masa har Construction company (BULAMA CONSTRUCTION COMPANY) ne dashi wanda suke samun kwangiloli masu dama wadda sai da rabanka ma suke karba.

 

Matan Alhaji bulama biyu,hajiya zuwaira itace uwar gida wadda ta haifa masa yara huɗu dukka maza babu mace ko daya.

 

Mutane kance soyayya da sa rai da yayi ga ɗiya mace ne ya sashi ƙarin mata amma a zahiri kuwa ba haka bane,

Soyayyar Bafulatana Nana Surbajo dake yawan kawo nono Companin sa ita tayi masa mugun kamu duk da kuwa yanayi kamar bai taba kula da ita ba a yayin da ita bama tasan yanayi ba duba da shi ɗin mutum ne da ganinsa sai ka cike Paper.

Da yake Allah Ya kaɗara matarsa ce bai kasa a gwiwa ba wajen bincike akanta inda Ya gano daga rigar da take yaje ma iyayenta da maganar Aure tun kan Ya furta mata soyayya.

Iyayenta ba masu tsaurin ra’ayi bane dan haka suka bashi dama Ya nemi soyayyar nana surbajo duk da yarda danginsu suka masu Cha akan zasu bama dan yankan Kai diyarsu tilo.

Ba wani wahala Ya sha ba Ya samu Auren surbajo wanda kwata kwata baiwa uwargida zuwaira daɗi ba amma babu yarda zatayi da yin Allah dan haka abun ya kullu yarda Allah yaso.

 

A shakara Allah Ya Azurtasu ɗiya mace wadda taci suna UMAIMAH,sosai Alhaji bulama yayi mutuƙar murna wadda tasa shi fitar da zakka Mai mutuƙar tsoka,

 

A duniyarsu ta shahararrun masu kuɗin babu wanda bai san da samuwar UMAIMA ba da kuma irin Adadin ƙaunar da yake mata dan baya iya boyewa,

Wannan ƙaunar da yakewa UMAIMAH ba karamun damun hajiya zuwaira take ba da yayanta uku, cikin yaranta Abubakar,usman,umar,Aliyu,Abubakar babban danta ne Kawai yake jin Umaimah a cikin zuciyarsa kamar uwa daya suka fito amma sauran kuwa ba karamun saka masu kiyayyar umaimah da uwarta tayi ba.

 

A haka umaimah tayi ta girma cikin soyayya da kulawa duk da kuwa irin tsangwamar da take sha gurin uwar gidan Alhaji bulama da yaranta uku,

Tun kafun tasan menene kiyayyar har ta fara ganewa tasan mema kiyayyar ke nufi.

 

A lokacin da ta shiga shekara goma sha biyar Allah yayi ma mahaifiyarta rasuwa sakamakon brain cancer da ya sameta,babu irin kudin da Alhaji bulama bai kashe ba dan kawai Nana surbajo ta warke amma abun yaci tura,

Tun rasuwar Nana surbajo Umaimah ta ci buri kuma ta sawa ranta sai ta zama surgeon,

Da wuri ta fara makaranta sabida irin kaifin kanta,tana da shekaru goma sha biyar ta kammala karatun secondary school ɗinta ,

A shekarar da ta zagayo ya kai ta harvard university inda ta fara karatunta na liktanci,

Babu irin kauɗin da hajiya zuwaira batayi ba akan Kai umaimah Harvard da akayi amma yayi kunnen uwar Shegu da ita, umaimah na shekara ta uku a Harvard mahaifinta yaje Ya ɗaukota,

Bata tambayesa dalili ba d’an tasani idan da wanda yake san cigaban ta bai wuce shi ɗin ba sannan ta yarda duk wani decision da zai yanke akanta mai kyau ne.

 

Bayan dawowarta Nigeria tayi mutuƙar mamaki da taji wai ansaka ranar Aurenta da Habib Aliko yaran Aminin Daddynta,

Koda Daddynata yayi mata magana akan Aurenta da Habib nuna wa tayi duk abunda Ya yanke akanta dai dai ne muddin karatunta bazai tsaya ba,

Tasani Daddynta Ya chanza amma bata saka wa ranta komai ba,baƙaramar rawa Hajiya zuwaira ta taka na wajen Auren Umaimah da Habib d’an ita ta haɗa komai.

 

Yaya Abubakar kaɗai ke bata baki yana Mai nuna mata Auren ma ba matsala bane sannan bazai shiga rayuwar karatunta ba tunda Daddy Ya jaddada ma Habib d’a mahaifinsa kan zata cigaba da karatun ta and baya buƙutar su ɗauki nauyi zaiyyi komai,

Haka nan ya Auri Habib inda Ya ɗaukota daga garin adamawa ya kawota kano,

DE ta samu a TURKISH MEDICAL SCHOOL inda ta dora daga inda ta tsaya.

 

Tun ranar da aka kaita gidan HabIb tasan ba mijin Arziƙi bane ‘dan a buge ya shigo ,bai tsaya anan ba kuma a ganawarsu ta farko raping ɗinta yayi wanda yaji mata ciwo sosai,tashin hankalinta bai fara ba sai da tasan Habib manemin mata ne sannan kuma ɗan giya ,bata sanar da kowa ba take zaune dashi a Haka musamman da taga yarda Daddynta ke mutuƙar yaba hankalinsa ‘dan munafukine na masifa saboda baya taba nuna shi ‘dan iskane gaban iyayenta,a Haka har rabo Ya shiga tsakaninsu ta haifa masa yaro na miji wanda yaci suna NAMEER,

NAMEER na da shekara ɗaya Habib ya saketa sakamakon dawowa da yayi gida a buge suna zaune da NAMEER a falo ‘dan kawai tayi faɗa da mita akan Ya daina shigo musu gida muddin giya bata sake sa ba,

Cikin maye Ya mata saki uku wanda a musulunci ma ta saku,

Daga baya Ya dawo yayi ta naci akan shi bai saketa ba amma Daddynta yayi masa koran kare sannan Ya ƙwaci NAMEER ɗin da Ya kwallafa rai akai wanda mahaifin Habib bai jaba ‘dan baya san alaƙarsa ta baci da Alhaji Bulama.

 

Kamar wasa bayan iddarta Daddy ya sake introducing mata BILAL shima dai yaran Abokinsa,

Abun ne Ya dameta duba da Ko Auren ta na fari bata gama Alhini akai ba amma wai Daddyn Ya kawo maganar Auren ta da wani,wanda shima kamar Habib ba sanshi take ba,

Kuka ta ɗingawa Abubakar Akan ita bata san Auren Bilal ‘dan Auren ma bata so baki daya ,she’s just 21 amma ace wai har Zatayi Aure na biyu,

Baki abubakar yayi ta bata akan zai je ya samu mahaifinsu yayi masa magana,

Koda yawa Daddyn nata magana sai cewa yayi Ai hajiya zuwaira taje wajen malaminta dake mata Addu’a Ya tabbatar mata muddin Umaimah ta zauna babu Aure zata lalace kuma babu wata nasara da zata tabayi a rayuwa shi kuma bazaya taba barin ɗiyarsa tilo guda ɗaya ta tagayyara ba,

Ƙara yarda yayi da Lallai daddy yana san umaimah to extent that yama rasa inda zaisa Alƙibilar tunaninsa,’dan ko shi da yake ɗan Umma yasan maganar ta ba dai dai bane duba da kalar tsanar da take wa UMAIMAH ɗin ,kawai dai tace tana so ta bar mata gida,

Kara bawa umaimah hakuri yayi a karo na biyu inda ta yarda da Auren BILAL wanda yake da mace ɗaya,shima kuma mazauninin garin kano ‘dan Haka Ta dora karatunta inda ta tsaya.

 

Duk da tarin kuɗin mahaifinta hakan bai hana kishiya da miji da uwarsa galaza mata ba,gida ɗaya suke baƙi dayansu,

Karatun ta ne basu so amma kuma babu yarda zasuyi dan basu suke ɗaukan nauyin Karatunta ba sannan yarjejeniya ce akayi Mai zaman kanta,a Haka tana wannan rayuwar ta sake samun ciki cikin shekarar su ta biyu da Aure duk da bata so ba amma Haka nan Ta ɗauki dangana,

Duk wani wulakanci da take gani gidan Bilal dannesa tayi Ko yaya Abubakar bata faɗawa ba ‘dan faɗan ma is pointless ‘dan tasan babu mai duba mata kar ma ace Daddy zaice kawai Zaman Auren ne bata so.

 

Hankalinta ta mayar kan karatunta wanda take samun nasarori sosai a ciki,gefe guda kuma tana kula da NADIYA yarinyar da ta shiga tsakaninta da BILAL Yar shekara,

Saukinta kawai NAMEER YARO DAN SHEKERA UKU a lokacin yana gurin Matar Yaya Abubakar “Sadiya” wadda ke nan cikin mansion d’in Bulama ‘dan bai yarda Ko wanne ɗan sa Ya fita da iyalinsa daga gidan ba ,duba da gidane duniya guda.

 

 

 

CHUCHUJAY ✍🏽

To Be continued.

[10/21, 8:53 PM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU

 

BY

 

CHUCHUJAY✍🏽

 

EPISODE 2⃣.

 

Idan kana bibiyar labarin Rayuwar Umaimah zakace Shin dama masu kuɗi ma suna samun kalubale a rayuwarsu duk da kuɗinsu?

 

Zaka na tunanin tayaya Umaimah zata jure dukkan wannan Abun bayan mahaifinta sharararen Mai kuɗi ne!

 

Abun ba Haka yake ba,sau da dama kana da kuɗin da komai amma muddin Allah bai so ba baza ka ji daɗi ba tawani bangaren ,Ya ‘dan ganta da kaddarar ka,

 

Auren dake tsakanin umaimah da bilal bai wani lasting ba saboda irin sharrin da suka haɗu suka haɗa mata,

 

Tana kwance kan Gadonta tana bacci ta tsinkayi hayaniyar mutane akanta,koda ta farka mijinta da mahaifiyarsa da matarsa ta gani a gefenta sai gefe guda wani ƙato da bata taba gani ba a rayuwarta kwance kan gadanta!

 

A ranar suka mata wulakancin da ta kasa mantawa a rayuwarta wato kazafun zina wanda ya Kai har bilal Ya ke tantamar kasancewar Nadiya yarsa ,duka bilal yayi mata sosai da belt wanda sai da Ya farfasa mata jiki kana ya sake ta saki biyu,

 

Abu na farko kenan da yaje kunnen Alhaji Bulama wanda yayi mutukar harzuƙashi,

 

Kuka sosai umaimah Take masa tana Mai masa rantsuwa akan bata taba Aikata zina ba hasalima ita bata san mutumin da ta farka ta gani a gefenta ba,

 

Mahaifin bilal Ya kira wanda baida masaniyar Mai ke faruwa saboda Ya rabu da mahaifiyar bilal,

 

Kwata kwata Alhaji bulama bai tsaya yi masa da sauƙi ba saboda yarda ranshi Ya baci,hakuri Alhaji muntari Ya bawa Daddy saboda shi bai masan wainar da ake toya wa ba,

 

Gudun kar zumuncinsu ya lalace yasa Alhaji Bulama yace masa zai bincike sannan yana so Ya fitar da hannunsa akan duk abinda zai biyo baya dan muddin Ya gane bilal ne baida gaskiya sai Ya ɗauresa.

 

 

 

DNA Ya fara sawa akayi conducting akan Nadiya da bilal wanda Ya fito 99% positive,

 

Da bincike yayi bincke aka gano haɗine na matar bilal da mahaifiyarsa ,baki ɗayansu Alhaji Bulama Ya daure a yayinda yasa a bawa bilal mugun kashi ladan dukan da yayi wa yarsa sannan yamasa haramiyya da NADIYA.

 

 

 

Haka nan ta cigaba da zama a kano ‘dan karasa karatunta wanda a lokacin tafi yinsa cikin kwanciyar hankali ,

 

A shekarar da ta gama karatunta ta haɗu da Hafiz matashin Mai arziki wanda haduwar farko Ya nuna mata soyayya ,ita macece da bata taba soyayyar ɗa namiji ba sai akan Hafiz ,

 

A hankali soyayya Ya kullo tsakaninsu inda baki daya bata ganin aibunsa musamman da yasan tana da yara biyu Ya amince da daukan su idan sukayi Aure ,

 

Da kalamai masu daɗi Hafiz yasa umaimah ta saki jiki dashi sosai,

 

Bayan ta gama karatunta ta samu licence na fara Aiki takai Hafiz gidansu a matsayin mijin da Take san Aure,

 

Kiranta Daddynta yayi Ya zaunar da ita Ya tambayeta akan gamsuwarta da Hafiz sannan Ya jaddada mata shi bazai sake ce mata ta Auri kowa ba idan tana so ma zata iya cewa bata so baki ɗaya bazai ce mata dan me ba,

 

Nuna masa tayi ta gamsu da hafiz wanda shima a hankali bayan binciken da yayi akansa Ya bada yardar sa akan Aurensu,

 

Da shagalin Aurenta da shagalin murnar samun aikinta Alhaji Bulama Ya haɗa mata gagarumun biki .

 

Kamar yarda Hafiz yayi mata Alƙawari kuwa Haka Ya ɗauki Nameer da Nadiya matsayin nashi,

 

Lagos suka wuce tare duba da yarda kasuwancin sa Ya tarkata chan,inda ita kuma ta fara aikinta cikin kwanciyar hankali.

 

 

 

Soyayya suke gwanin ban sha’awa a gidan Wadda tayi lasting na wata biyu kacal,

 

Hallayyarsa bata fara fito mata ba sai bayan dawowarsa daga wata tafiya da yayi zuwa indiya a lokacin da karamin cikin Abdallah ,babu kalamai masu daɗi Ko zama suyi hira mai sanyaya zuciya ballantana akai Ga mu’amala ta Auratayya,

 

Wasa Wasa tun abun tana ɗaukarsa wasa Har ya fara wuce tunanin ta,

 

Haka take dannewa tana koƙarin nuna masa kulawa amma hantara da kyara babu abunda baya mata.

 

 

 

A cikin gidansa akwai ɗaki guda wanda bata taba shigansa ba hasalima bata san dashi ba sai ranar da Yayi wata dawowa gida cikin dare a lokacin watan Abdallah biyu.

 

,tana jin shigowarsa ta tashi ta fito dan jin dalilin da yasa bai shigo da wuri ba,tayi mamakin ganin yarda Ya dana wani katon photoframe dinsa ,boyewa tayi ganin bangon Ya buɗe Ya bayyyana kofa,

 

Binsa tayi a baya a hankali ta shiga ɗakin itama,

 

Mamaki tasha sosai lokacin da ta ga wasu kayan tsubbu da pads na mata a jere a saman wani table,ba sai an faɗa mata ba tasan ɗakine na tsubbu,

 

Saurin komawa tayi da baya ta koma ɗaki jikinta na faman rawa musamman da taji yana faɗin zai kawo musu jarirai biyu kamar yarda yayi wa King manta Alƙawari.

 

Komawa tayi ta kwanta kamar tana bacci,

 

Dama bai kwana a ɗakinta a yanzu ‘dan Haka ta saka key ta koma ta kwanta tana zulumi,Allah yasa Nannyn su NAMEER na tare dasu kuma suna kulle ɗaki,fargaba da tsoro sune kawai abunda Ke fama da ita,shekarar ta a lokacin Uku da Hafiz duk da fizge fizgensa bata taba sanin money ritual yake ba,juyawa tayi ta kalli jaririnta Abdallah tana ayyanawa kilan ma da Abdallah cikin jariran zai bada.

 

Tunanin barin da tayi farkon Aurensu tafra wanda tasha mutuƙar wahala duk da karamin cikine amma bata kawo komai ba musamman lokacin da ta tsincesa yana waya akan cikin wanda ya mata karya da Auntynsa ce.

 

Tafiyar gaggawa ta kirkira zuwa Adamawa wadda ko sanar mashi ba tayi ba,sallamar nannysu tayi ,a ranar da suka je adamawan da dare Ya kirata yana tambayar tana Ina ,karya ta masa tace taje kano ne karbo wasu takardu,sabida abin bai gabansa bai tambayeta abunda yasa ta tafi bata faɗa masa ba sai cewa yayi ta ɗauke Abdallah suje south Africa zai zo Ya samesu,

 

Batayi magana ba wanda dalilin hakan yasa shi buga mata wata uwar tsawa ,

 

To kawai tace masa ta kashe wayanta,

 

Bataje gidansu ba ,gidan kakanninta da Daddynta ya ƙera masu taje,

 

 

 

A ranar da safe ta tashi da labari Mai mutukar gigitarwa ,wai an kama Hafiz sannan ane neman iyalansa ‘dan case ɗin da aka kamasu babba ne kuma mutum ɗaya daga cikinsu da hannun matarsa wanda Hakan yasa ake nemansu ,

 

Lokacin ta gane mai yake nufi da su tafi south Africa,

 

A ranar ta san wanda ta Aura,Ashe Hafiz babban ɗan yahoo ne wanda suke bada jinin mata da jirirai ‘dan shi kam matansa biyu Ya bada umaimah ɗince yake ma san da bazai iya bada ta ba da ɗansa wanda dalilin hakan yasan asirinsu tonuwa,

 

Bai tsaya anan kaɗai ba harda safarar mutane wanda matar ɗaya daga cikinsu ke musu safara da yawancin yara da mata,ba ma nan kadai ba har Arm Robbery sunayi,

 

Tasha kuka sosai sosai lokacin da tagane wanda take so jabu ne,

 

He was lowkey ‘dan duk binciken da mahaifinta yayi akansa bai gano wani nakasu nashi ba ,

 

Kawai an samu labarin shi ɗin marayane mara uwa da uba wanda Ahalinsa suka banzatar daga bisani kuma bayan wani Alhaji Ya jashi lagos yasashi kasuwancinsa wanda hakan ya habbakasa .

 

Ashe akasin Haka ne money ritualist ne,

 

Bayan zama da akayi a kotu da binciken da akayi akan umaimah aka yanke masu hunckin kisa ta hanyar rataya.

 

 

 

 

 

 

 

BAYAN SHEKARU BIYU.

 

CITY TEACHING HOSPITAL ADAMAWA STATE NIGERIA.

 

7:30 am

 

Cikin taƙama da kwarewa take takowa cikin harabar asibitin a yayin da wani Nurse ke riƙe da jakarta,

 

Idan akace maka tana da Yara uku zaka ƙara tsayawa ne ka Kalle ta da kyau har ka ƙaryata Mai faɗin maganar,

 

Asalin Umaimah irin matan nan ne wanda sukayi kyawu irin na fulani har zuwa jikinta, bata da ƙiba amma ba Haka ke nuna bata da ƙira ba,

 

Kirar jikinta ita ake kira kalangu,a fuskar ta babu abunda zai fara ɗaukar maka ido kamar sexy eyes ɗinta masu kama da tana jin bacci,

 

Zuwa Ga maidaidacin hancinta Mai ‘dan tsayi sai cute lips ɗinta pink,

 

Ba tada yawaitar sakewa saboda irin abubuwan data fuskanta a rayuwarta ,kullum idan zaka ganta serious face ɗinnan ce kawai a fuskarta ,tsakaninta da colleagues ɗinta abunda Ya shafi aiki amma Babu alaƙa ta abota,mutane da dama akan gulmarta suke asibitin ,wasu suce girman kai ne ke ɗawainiya da ita ‘dan tana ɗiyar Mai kuɗi wadda komai take so zata samu wanda sukance aikinma saboda shi ta samu saboda connection ‘dan tana cikin manyan surgeons na asibitin.

 

Abun Ɗaya da basu sani ba shine da kuɗi nasiyan komai da batayi Aure uku ba,

 

A rayuwarta mutum ɗaya ta taba ƙawance da itama shekarar da take harvard suka haɗu HINDU duk da shareta da take bai hana HINDU tusa Kai rayuwar umaimah ba a yayin da ta sake mata duba da lokacin tana da ƙaracin damuwa ‘dan rashin mahaifiyarta yayi ƙaranci saboda yarda mahaifinta ke nan nan da ita,

 

 

 

Kai tsaye Cabin ɗinta ta nufa ‘dan Ko karyawa batayi ba,

 

Aje jakan nurse ɗin yayi kana yace”Dr Bulama,akan matar da za’ayiwa operation ɗin appendix ɗinnan yan uwanta sun saka hannu and kamar yarda kika faɗa yayi severe Dr Jabir yace Ya kamata ayi aikin da gaggawa ‘dan shi yama sa hannu”

 

 

 

Dago Kai tayi ta kalli nurse ɗin tace”nurse farouk patient ɗina ne Ko na Dr Jabir mene Ya saka yasa min hannu?

 

Kara haɗe rai tayi tana Mai jin haushin yarda Dr Jabir ke mata katsalandan a aiki,

 

 

 

Shiru nurse ɗin yayi bai ce komai ba ‘dan yana tsoran fadar abunda zai bata mata rai Cos she’s short temper wani lokaci musamman gareshi wanda tunda tazo suke aiki tare,amma sau da dama shi zai fadi alkhairinta saboda tana masa,

 

Katse masa tunani tayi ta hanyar cewa”so ka tura mun detail ɗin patient ɗin,”?

 

Kaɗa kai yayi Kafun yace “yes doctor”

 

 

 

Jawo laptop ɗinta tayi tana faɗin “and I’m hungry jezzz!”

 

Juyawa yayi yana faɗin bari naje na kawo miki breakfast,

 

Saurin tafa hannu tayi alamun ya tsaya Kafun tayi saurin tashi tana cewa wait this is serious we Are going in for surgery now,

 

Yanzunnan akai ta OR yanzun nan and i need the team available ASAP.

 

 

 

Da sauri Nurse ɗin Ya fita ganin yarda ta fadin maganar ba Wasa.

 

 

 

Koda taje operation Room already team ɗin na nan,hannunta da tayi sanitizing ta miƙa aka samata Hand Gloves Guda biyu,kana ta juya aka sa mata rigan operation then aka ɗaura mata face mask.

 

 

 

Bayan gama operation ɗin cikin sa’a tana fitowa bayan tayi disposing Hand gloves ɗinta da face mask,ta juya zata tafi taji tayi gware da mutum papers ɗin hannunsa sun zube ,

 

Sorry kawai tace ta wuce ba tare da ta bawa wanda tayi gwaren da ba last kallo.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

CHUCHUJAY

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment