Wa Ya Kashe Rukayya Hausa Novel Complete
WA YA KASHE RUKAYYA*?
*DAGA ALƘALAMIN*
*FIDDAUSI SODANGI*
*Bismillahirrahmanirrahim.*
*Godiya ga Ubangijin mu Allah daya bani ikon fara rubutun nan lahiya, ina rokon Allah yasa in ƙare lahiya ba tare da wata matsala ba Ameen*.
*Wannan labarin kirkirarre ne, banyi shi dan cin zarafin wani ba ko wata, idan yayi shige da labarin rayuwarki ko naka ina niman afuwa hasashe ne da kuma aikin alƙalami wanda yafi na takobi*.
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
1 Ƴar gata
2 Aliya
3 Waheeda
4 A zumuntar mu
5 Real Amani
6 Kwadayi mabudin
7 wahala.
8 Jawaheer
9 Ni da surukata.
10 Makira.
11 Ruguntsumi.
12 Gimbiya Ameenatu
13 Mugun tsartse.
14 Muhibba.
15 Dan hakin daka raina.
16 Zamani.
17 Mugun makoci.
18 Har a zuciya.
19 Kai ne gatana.
20 Maryama.
21 Kaine sanadi.
22 Kaddara ta riga fata.
23 Aminiyata ce.
24. Gobara daga kogi
25. Wa ya kashe Rukayya.
1️⃣
Sararin samaniya ya haɗu ya yi bakikkirin sai cida a ke yi alamun da ga yanzu zuwa kowani lokaci ruwan sama zai iya saukowa, wannan dalilin ne ya sa jama’a kowa keta koƙarin kimtsa kayansa. Lokaci ɗaya ruwan saman ya sauko da ƙarfi haɗe da iska mai ƙarfin gaske. A dai-dai wannan lokacin kuma Mero ke cike da alhini game da abinda likita ya gaya mata akan tilor ƴarta wacce ta sameta bayan shekaru masu dama da auranta. Wata biyu kacal da haihuwar ɗiyarta Allah yaiwa mijinta rasuwa ya tafi ya barta da kyakkyawar ƴarta mai kama da larabawa kasancewar ta buzuwa daga ita har mijin nata.
Juyin Rayuwa Hausa Novel Complete
“Allah Sarki Zainabu ni kam yanayin ki ya daɗe yana bani mamaki da tsoro, yawan kuka ba gaira ba dalili gashi ba ki rabo da zazzabi, duk yara sa’anninki ƴan wata shidda zuwa bakwai sun fiki gwaɓi da walwala ke kam sai laulayi kamar mace mai sabon ciki”.
Cike da tausayawa ƴar tata wacce ke kawance bisa gadon Asibiti da karin jini a hannunta ta ke maganar tana sake matsawa jin ƴar kamar zata mai da ta cikinta.
“Shin Mero ki kwantar da hankali ki yi shuru haka nan tunda ta samu bacci karki tada ta, kema ya kamata ki runtsa haka nan jibi idanunki duk sunyi luɓu-luɓu”.
“Anna kalli tafin kafarta yadda ya yi, kalli kafar ma da hannun yadda suka kumbura suntum”.
*****
Wata galleliliyar mota ce ta shararo da gudun tsiya kamar zata tashi sama duk da ruwan saman da ake shatatawa kamar da bakin ƙwarya. Titin ya yi shuru ko mota ɗaya babu kasancewar hanyar by pass ce gashi kuma dare ne.
“Kaii! Wallahi mun daɗe bamu halarci party da ya yi daɗi irin na yau ɗin nan ba, wai kunji ƙuguna kuwa wlh kamar zai balle Allah dai ya sake maimaita mana”…….
“Ni fa Ahmad ne ya bala’in bani haushi da kwazzabar tsiya duk ya ishemu mu taho bayan duka-duka yanzu ƙarfe sha biyu da rabi kuma fa ina ga wlh sai an kwana ana chashewa gaskiya Ahmad kana takura rayuwarmu wlh”.
“Kai….ni….duk kun…ishe ni da su…ru..tu, Ahmad bani kwalbar nan inɗan….ƙara korawa wlh biyu-biyu…na…ke…gani….ina jin motar nan kamar a sama ta ke gudu…wai kunsan a nawa nake tafiya kuwa…..hahahhah! Wlh a ɗari da sittin nake tafiya ga ruwan….saman nan daɗi su su su hahahahaha! Wlh mota da ɗadi”.
“Kambu, gaskiya Amal ƙaramar ƙwaƙwalwa gare ki duka abinda muka sha bai taka kara ya karya bafa amma wai har kinyi sama haka, gaskiya Ahmad ka karbi motar nan karta jefa mu a rami”……..Ba ta kai ga rufe baki ba motar ta fara tangal tangal tana wani irin ƙugi alamar mai tukin ta yi kokarin kaucewa abu da kuma kokarin taka burki a lokaci guda. Kiiiiiiiiiiiiiiiiiiii kuuuuu……Motar ta kwace a yayin da ta daki wani abu kuma taci gaba da tafiya da su ba tare da sarrafawar matukiyar ba.
Cikin hukuncin Allah motar ta tsaya da kanta a lokacin da matukiyar motar ke ƙarasa wartsakewa daga mayen da ta ke ciki.
In banta salati babu abinda sauran ke yi gaba ɗayansu hantar cikinsu ta kaɗa cikin tsananin kaɗuwa suke kallon juna cike da rudani ko wanne jikinsa na karkarwa.
Namijin cikin sune ya yi ta maza cike da ƙarfin hali yace “Ina ganin fa kamar mun bige mutum ne”.
Ya ƙare maganar cikin rawar murya yana zaro ido.
Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan cewa “mene??”
“Da gaske naga kamar abu muka bige amma ban tabbatar da meye ba kamar dai mutum mu koma baya muga menene”.
“Mene? Gaskiya baza mu koma ba kawai mu wuce tunda dai babu wanda ya ganmu haka kawai mujawa kanmu, to idan kuma mutum ne fa dole fa sai yan sanda sun shigo maganar gaskiya mu tafi kawai, Amal tada motar nan mu tafi kawai”.
“Gaskiya Rahma ta faɗi wlh mu tafi kawai kar mujawa kanmu abin magana, ya iyayanmu zasu ji ace munje party mun bige wani? Wama ya sani ko ya mutu kawai mu bar wajan nan”.
Cikin rawar murya mai tukin motar wacce suke kira da Amal tace “Kuma kunsan bazan iya tahiya ba tare da naje naga abinda muka bige ba gaskiya bazan samu natsuwa ba harsai naje na gani” daga haka ta tada motar ta juya suka koma baya, tun kafin ma su ƙarasa isa fitilar motar ta nuna masu abinda ke gabansu.
A tsorace suka firfito daga motar cike da fargaba ba tare da sun ƙarasa ba.
Ahmad ne ya kuma yin ta maza ya nufi wajan yana taku a hankali bakinsa ɗauke da addu’a cike da fatan Allah yasa bata mutu ba.
A hankali ya ƙarasa tare da leƙa fuskarta. A tsorace ya kai hannu saitin hancinta ya tattabata inda ya tabbatar da cewa lallai ta mutu dan sam bata numfashi.
“Innalillahi wa inna lillahi raju’un!”
Abinda ya ke ta maimaitawa ke nan tare da nufar su Amal wayanda suke kallonsa ko kiftawa babu suna jira ya ƙaraso ya gaya masu me ake ciki.
“Ƴan mata muna cikin bala’i azal ta faɗo mana wlh macece muka bige kuma ta mutu”
A rikice suka haɗa baki wajan sakin ihu “Wayyyo Allah mun shiga uku.”
Hannu Ruky ta ɗora bisa kai ta fashe da kuka tana faɗin “sai da nace maku kar muje party nan kar muje ni jikina bai bani ba amma ku ka ki yanzu ga irinta nan ai”……Laila ce ta katse ta da fadin
“Dan Allah Ruky kiyi mana shiru muji da abinda ya dame mu ko ni mai miji bana abinda ki ke wlh”.
“Yanzu meye abin yi”
Amal ta tambaya tana kallon fuskar Ahmad.
Rahma ce ta yi saurin cewa “kawai mu wuce tunda ba wanda ya gani”
A’a gaskiya ni ina ganin mu ɗauke ta muje mu binneta.
Ahmad ya faɗi da iyakar gaskiyar shi.
“Mene? Gaskiya bakada hankali Ahmad kawai sai mu binneta babu wanka ba sallah? Ni wlh bama zan iya taba gawar ba tsoro na ke ji kadai sake tunani”.
“To Amal mi kike so muyi ne ni wlh duk na rude tunani na ya kulle”.
Laila tace “me zai hana mu ɗauke ta daga titin mu jefa ta a dajin can ina ga sai yafi kunga dai muna ta bata lokaci kar wata motar tazo ta iske mu danma dai dare ne gashi ana ruwa jibi yadda muka jike fa sharkaf”.
Ruky ta buga tsalle tace “wallahi tallahi ni dai bada ni ba, wannan zunubi da yawa ya ke ta yaya zamu wurgar da ita ko binne ta ba gara mu tafi ba wasu su tsince ta nidai gaskiya kuzo mu tafi”.
Haka sukai ta jayayya daga karshe suka kama gawar suka jefar a dajin tare da kokarin juyawa zuwa wajan motarsu.
WA YA KASHE RUKAYYA*?
*DAGA ALƘALAMIN*
*FIDDAUSI SODANGI*
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
1 Ƴar gata
2 Aliya
3 Waheeda
4 A zumuntar mu
5 Real Amani
6 Kwadayi mabudin
7 wahala.
8 Jawaheer
9 Ni da surukata.
10 Makira.
11 Ruguntsumi.
12 Gimbiya Ameenatu
13 Mugun tsartse.
14 Muhibba.
15 Dan hakin daka raina.
16 Zamani.
17 Mugun makoci.
18 Har a zuciya.
19 Kai ne gatana.
20 Maryama.
21 Kaine sanadi.
22 Kaddara ta riga fata.
23 Aminiyata ce.
24. Gobara daga kogi
25. Wa ya kashe Rukayya.
2️⃣
Kukan jariri suka fara jiyowa daga cikin dajin wanda yasa su tsayawa cak daga tahiyar da suke a ta ke suka fara kallon-kallo zuciyoyinsu na bugawa cike da fargaba.
Amal ce ta fara nufar dajin kai tsaye ba tare da tace dasu komai ba, suma rufa mata baya su kai zuciyoyinsu na bugawa ba ma kamar Rukayya da ke ji kamar ta kurma ihu ta arta a guje.
Baby ce wacce bazata wuce wata shida ba nannade a zani tana ta tsala uban ihu tana wulla ƙafa da hannu ruwan saman ya jiƙata sharkaf gwanin ban tausayi.
A hankali Amal ta kai hannu zata ɗauke ta tana sake haske ta da fitilar wayarta da ta kunna.
“Amal! Badai ɗaukar ta za ki yi ba? Dan Allah ki rufa mana asiri kizo mu wuce, ki ka sani ko aljana ce?”.
Rahama ta ƙare maganar tana zaro ido.
Ba tare da Amal ta kulata ba ta ɗauko babyn haɗe dayin bisimillah.
Gaba ɗaya kallon babyn suke yi babu mai bakin magana.
Ahmad ne ya yi karfin halin cewa “Amal me yasa?
Tace “Bangane me yasa ba, so ku ke mu barta ta mutu? ko ban faɗa ba dai kunsan cewa uwarta ce muka kaɗe ta mutu har lahira muka yar da ita, to kuma sai mu bar ƴar kuma ta mutu itama? Gaskiya bazan iya tafiya in bar yarinyar nan ba”.
Sororo suka tsaya suna kallonta da mamaki ruwan saman na sake yi musu duka.
Haka sukai ta jayayya amma Amal ta kafe kai da fata akan ita baza ta bar ƴar nan a nan ba sai dai su tafi da ita. Daga ƙarshe ma da suka nace akan barin ƴar sai cewa tayi su tafi kawai ita zata zo da kanta idan ma su suna tsoron tafiya da babyn ne. Haka dai suka gama jayayyar suka nufi mota tare da babyn dan kuwa Amal tafi su kafiya da naci.
*****
“Annah! Annah!! Annah!!!”
Firgigit ta farka daga baccin da ya ɗauketa bata shirya ba tana gadin uwar da ƴar.
“Annah ina Zainabu ban ganta ba”
Ta ƙare maganar a ruɗe cike da kaɗuwa.
“Bangane baki ganta ba Mero ita Zainabun allura ce da za a ce ba a ganta ba?”
Matar da ke gadon kusa da su ce tace “ni fa naga wata nurse ta ɗauke ta ina ganin wani abin zasuyi mata kila dan taga kuna bacci ne bata tada ku ba nima cikin bacci na buɗe ido dai-dai lokacin tana barin ɗakin”.
Hankalin Mero dai bai kwanta ba nan ta bazama niman ƴarta abu kamar wasa karamar magana ta zama babba.
***
Kai tsaye Danƙareren gidansu suka nufa wanda mallakin mahaifin Rahma ne ya mallaka masu suke zama a ciki tun fara karatunsu har zuwa yanzu da suke matakin ƙarshe. Ƴan aiki har uku ya aje masu suna ɗawainiya da su.
A palo suka baje inda Amal ta cirewa baby jikakkun kayan jikinta ta naɗeta da tawul tana ta jijjigata amma still babyn kuka ta ke jikinta na rawa tana ta jera attishawa akai-akai.
“Ƴan mata yanzu ya zamu yi da babyn nan kenan? Ni ina ga yunwa mafa ta ke ji gashi dare yayi ni banma san meye abinda zamu iya mata ba yanzu”.
Ahmad yayi maganar yana kallon Amal wacce ta hakikance akan babyn.
Kallon shi ta yi da kyau tana bata fuska tace “Wanka zan mata da ruwan zahi nasan danai mata bacci zatai da safe sai mu kaita Asibiti”.
“Wai ke Amal kina da hankali kuwa? Taya zamu iya rainon ƴar yarinyar nan makarantar fa? Kuma ma duka duka nan da wata shida zamu gama gaba ɗaya sai muyi yaya da ita kenan? Hutu ma fa za ai da zaran an gama exams to wa zai tafi da ita gidansu a cikinmu? Mu ce kuma a ina muka samota?”
“Ke Rukayya nifa bance kowa ya so yarinyar nan ko ya ɗauke ta ba, ni ina sonta kuma ni zan tafi da ita gida kar wanda ya sake magana akan babyn nan ya isa haka nan kowa yaje ya kwanta gobe mu kaita Asibiti”.
Haka suka watse kowa ya nufi ɗakinsa Ahmad ma ya nufi site dinsa da ke ta waje.
Bayan sati ɗaya tuni dukkansu sun bala’in shakuwa da babyn nan wacce suka sawa suna Amatullah bayan tayi kwana uku a Asibiti saboda zazzaɓi mai zafi daya kamata a sakamakon ruwan saman da yai mata duka inda likita ya shaida masu cewa yarinyar sikila ce, gaba ɗaya sun tausayawa Amatullah in da suke ta tattalin ta da nuna mata kauna idan zasu tafi makaranta sai su barwa masu aikin nasu su tafi inda suka shaida masu cewa babyn Laila ce ta ɗauko abarta tunda sun san Lailar tana da aure.