Nufin Allah Hausa Novel Complete
NUFIN ALLAH
*Paid book:500*
*Chapter 1*
_Free page_
Misalin ƙarfe biyar da rabi shida saura na asuba, kyakykyawar baƙar budurwar ta isa ƙofar gidan Hakimin garin giwa. Mai suna Alhaji Haruna Musa giwa, wanda shine Hakimin garin kuma aminin mahaifinta marigayi Malam Mahmuda. Tana kuka wurjajan ta ci burki daga bakin zauren shiga gidan, tana faman raba idanu jin sautin karatun da ke fitowa daga masallacin kusa da gidan.Da alamu lokacin ake sallar asubi a masallacin,sai ta dawo da baya tana zama akan dakalin ƙofar gidan.Kuka sosai take yi iyakan ƙarfinta,baƙin kyakykyawar fuskarta gaba ɗaya ya tasa idanunta sun kumbura domin tun cikin dare take aikin kukan tashin hankalin halin da Innarta ke ciki. Tana nan zaune tana sharan hawaye da sauke ajiyar zuciya, su Hakimi suka fito daga cikin masallaci. Tun daga nesa yake hango wata da jan hijab zaune bisa dakalin ƙofar gidan nasa, hakan ya sanya shi ɗaga ƙafa yana riga Yaransa isa ƙofar gidan domin zuciyarsa na gaya masa cewa ba lafiya bane.
Mannubiya Hausa Novel Complete
“Najmatu lafiya, ko jikin Mairo ne ya sake motsawa kuma? Hakimi Alhaji Haruna Musa giwa ya furta hakan, a lokacin da ya isa wajen dakalin da take zaune akai ya fahimci cewa Ƴar amininsa ce zaune mai suna Najma. Wacce ya kira da Najma tayi saurin dubansa wasu hawayen na zarya akan fuskarta,taja ajiyar zuciya tana faɗin “Jikin ne Baba Hakimi, kwana mukai bamu runtsa ba.Yanzu haka na baro tana jin jiki.” Ta kai ƙarshen maganar tana rushe masa da kuka mai motsa zuciyar mai saurarenta. Hakimi ya ja salati yana faɗin, “Subhanallah!” Ya waiwaya bayansa yana yafuto ɗansa Auwalu da hannu, wanda ya tsaya suna magana da wasu samari. Ganin Hakimi na kiransa ya sanya shi isowa da sauri yana faɗin, “Baba gani.” Hakimi ya dubesa da zallar damuwa akan fuskarsa ya ce, “Maza shiga cikin gida ka ɗakko mukullin mota ka fito mu wuce asibiti, jikin Mairo ya sake motsawa.” Auwalu ya ruga a guje zuwa cikin gidan yana jan salati a zuciyarsa, domin suna tsananin son Inna Mairo da ganin mutuncinta.
Cikin hanzari ya fito daga cikin gidan hannusa riƙe da mukullin motar Hakimi.Ya isa garejin gidan ya fiddo motar, Hakimi ya shiga gaba yayinda Najma ta shiga baya tana faman jan ajiyar zuciya.
Kamar yadda Najma ta sanar da Hakimi Inna Mairo na tsananin jiki, a haka suka sameta. Da taimakon Auwalu da Najma suka kamota zuwa mota, suka wuce da ita asibitin zaɓawa dake garin. Taimakon gaggawa aka bata har aka samu ta dawo hayyacinta.Likitan da ya dubata ne ya basu tabbacin cewa rashin shan magungunanta akan ƙa’ida shike maido da komi baya, don haka dole a kula da sayensu akan lokaci da zaran sun ƙare. Ya kammala dukkanin jawabinsa sannan Ya rubuta musu wasu magungunan kala biyu, Ya ce idan ta shayesu bata ji daidai ba su wuce da ita babban asibitin koyarwa dake shika domin ta samu ganin babban likita. Hakimi sukai godia bayan sun amsa takardan maganin. Najma da sai lokacin hankalinta ya fara kwanciya, ganin Inna ta dawo hayyacinta. Sai ta kama hannunta suka fito daga ofishin Likitan, wanda duk yawancin sanda za a kawo Inna Mairo shi ne ke dubata, kuma shi ne babban likita baki ɗaya a asibitin Zaɓawan.
Suna tafe cikin mota don komawa gida Hakimi na mitan yadda ƴan uwan Inna Mairo da matar mahaifinta da suke kira Gwaggo suka juya mata baya. Ya cigaba da faɗin, “Yanzu saboda Allah Mairo idan su sun yanke zumunta dake sai ke ki biye musu ki daina zuwa inda suke? Karki manta fa kece ƙaramarsu Mairamu, duk yadda zasu gujeki su juya bayansu gareki don sun yi arziƙi, ke bai kamata ki yanke zumunta dasu ba. Ina giwa ina kaduna da za a ce kin yanke dukkan alaƙa da ƴan uwanki, kin zaɓi ki cigaba da rayuwa cikin tsananin maraici da ciwan zuci?” Ya dakata da maganar zuciyarsa na shiga ƙunci mai yawa, domin yana tsananin jin ciwon yadda Ƴan uwan Inna Mairo duka biyu suka wofintar da ita tun bayan rasuwan Mahaifinsu. Inna Mairo dake sauraren Hakimi ta kasa magana sai kuka, kukan da ke tasowa tun daga ƙarƙashin zuciyarta yana ƙona ruhinta.
Sanin da Hakimi ya yi Inna Mairo har da ciwon zuciya ke barazanar kamata,sai ya koma yin rarrashi da nusar da ita illar yanke zumunta koda ace an yanke maka, kai ance ka sadar ga wanda ya yanke maka ɗin. Har suka isa ƙofar gidan Inna Mairo Hakimi nasiha yake mata cikin rarrashi, Inna ta dinga saurarensa kalamansa na ratsa zuciyarta da sake raunatata.
“Najma kamata ku shiga daga ciki,zuwa anjima Auwalu zai je ya samo magungunan da aka rubuta ɗin. Mairamu Allah ya ƙaro afuwa, ki daina sanya yawan damuwa a zuciyarki domin kin fi kowa sanin cewa ba a son mai hawan jini na yawan tunani da sanya damuwa a rai. Musamman ke da zuciyarki ke barazanar kamuwa.Na horeki da ki daina sanya yawan tunani ki maida dukkan lamuranki zuwa ga Allah. Na sani ke ɗin mai tawakkalice amma ki ƙara ninka jururiyarki domin shi komi na rayuwa NUFIN ALLAH ne Mairo, yadda duk Yaso haka yake kasancewa. Allah zai baki lafiya ya kuma ganar da ƴan uwanki da Gwaggo cewa sun yi kuskure, sun kuma ci amanar dattijon arziƙi marigayi Alhaji Muhammad da basu rungumi wasiyyarsa sun riƙe amanarki da ya bar musu ba.” Hakimi ya dakata da maganar yana kallon Inna Mairo da hawaye ke gudu akan fuskarta, ta gyaɗa kanta murya a shaƙe ta furta, “Na gode Hakimi, Ubangiji ya biya maka buƙatunka na alkhairy duniya da lahira. Allah Ya duba gaba da bayanka Ya albarkaci zuriyya.In Sha Allah zan yi ƙoƙarin ganin na rage yawan damuwar.” Ta kai ƙarshen kalamanta lokacin da Najma ta zagayo ta buɗe mata murfin motar ta fito. Hakimi ya sake mata fatan samun sauƙi yana jin tausayinsu ita da Ƴarta Najma na sake mamaye zuciyarsa. Tabbas Ya yi rashin amininsa mai ƙaunarsa, Yana kuma jin cewa kulawa da Iyalinsa tamkar tilas ne a garesa domin ba zai iya zuba ido rayuwar su Inna Mairo ya tagayyara ba. Shiyasa tun bayan rasuwar aminin nasa Malam Mahmuda shi ne yake ɗawainiya da su Inna Mairon,bai taɓa gajiyawa ko gazawa ba,da taimakon Ubangijinsa yake musu komi.
Najma a hankali take takawa hannunta riƙe dana Inna Mairo har suka dangana da cikin gidan nasu, wanda ginin ƙasa ne da ya samu aka filascesa da siminti.Tsakar gidan ma an filascesa babu ƙasa sam a tsakar gidan,ko’ina fes yake don suna da tsanani tsafta da kula da muhalli.
Ƙaramin ɗakin nasu mai ɗauke da falo da ɗakunan bacci biyu a jere suka buɗe, Inna Mairo ta zame hannunta daga na Najma tana nufan hanyar ɗakin baccinta.Najma tabi bayanta da kallo tana mata sannu cike da tausayi. Inna Mairo ta amsa ba tare da ta waiwayo ba, don burinta shi ne ta dangana ga tsohuwar katifarta ta yi kukan da take riƙewa na tunawa da gwarzon mijinta da Mahaifinta da suka kwanta dama. Domin tabbas da suna raye da sun share mata baƙin ciki mai yawa na rayuwa,da bata yi kukan rashin gata ko makusantar da zata kwanta a kafaɗunsu ta yi kuka ba. Sai dai dukkanin gatan nata sun ƙare, ta rasa uwa tun tana tsummar goyo. Gashi yanzu ta rasa miji da uba,duka sun tafi sun barta cikin wannan duniyar mai cike da tarin rikita-rikita da ruɗin zuciya.
Ta kifa ciki tayi kuka mai yawa har Najma dake zaune a falo ta zabga uban tagumi, sai da ta jiyo sautin kukan da Innar ke yi. Ta nufo cikin ɗakin baccin Inna Mairo a rikice, tana mai durƙushewa a gaban katifar da take kwance ta ce, “Inna lafiya, jikin ne? Don girman Allah Inna ki tausayamin ki daina sanya damuwa a ranki, domin ke kaɗaice kika rage gatana a yanzu. Sannan lafiyarki ita ce abinda tafi komi muhimmanci.Ki dubi girman Allah karki bari lafiyarki ta salwanta akan baƙin cikin waɗanda basu san ma kina yi ba.” Najma ta ƙare maganan tana riƙo hannun Inna Mairo ta saki kuka mai ban tausayi, hakan ya sake karya zuciyar Inna Mairo.Ta riƙe hannun Najma da kyau tana faɗin, “Ba don su nake wannan kukan ba Najma, ina kokawa ne don rashin Mahaifinki da nawa.Tuni na daɗe da cire damuwar su Gwaggo a cikin zuciyata,na danne dukkan ƙawazucinsu a raina.Bana ganin laifin su Yaya Kabeeru, laifin Gwaggo nafi gani Najma domin na san ita ce tayi musu katanga dani, ta kuma hana su raɓemu sabida da tsananin ƙiyayyarta garemu ni da Mahaifinki.” Inna Mairo ta dakata da maganar zuciyarta na mata wani irin suya, ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta da ke mata wani irin zafi. Ganin hakan ya sanya Najma taya ta dafe wajen tana mata sannu cikin tsananin jin tausayin Innartata.
Sun ɗauki lokaci a haka hannunsu na dafe da ƙirjin Innar,kafin ta zare hannun Najma tana faɗin, “Tashi ki kunna wuta ki ɗaura abin karin kumallo Najma.” Najma ta jinjina kai tana tashi tsaye ta zare hijab ɗin jikinta, idanunta akan Inna ta ce, “Sannu Inna, bari in je kicin ɗin in ga ko akwai ragowar gawayin da za a iya kunnawa.” Daga haka ta fito daga ɗakin cikin takunta mai cike da nutsuwa ta halitta. Na dinga bin budurwar da kallo, wacce zata kai shekaru sha bakwai.Ina yaba kyawu da tsarin halittarta,domin babu ƙarya Allah Ya yi mata baiwar kyawu da cikar halitta mai asalin fisgar hankali. Baƙace sosai amma kyakykyawar da aka ƙera halittarta tamkar ita tayi kanta. Tana da tsayi matsakaici ba mai yawa ba, sannan tana da gaba da baya wanda suke a cike. Musamman ƙirjinta da yake a tsaye cir! Da cikakkun dukiyar fulani.Dogon hanci gareta har baka,sai manyan idanu farare tas! Masu turawan ƙwayar ciki baƙi siɗik! Ɗan ƙaramin bakinta so cute da cinkusassun gashin giranta baƙaƙe siɗik! Sun fi komi ƙawata kyawun fuskarta. Bata da jiki kuma ba za a kirata siririya ba, sai dai a kirata mai murjajjen jiki.saboda fatar jikinta a cike yake da tsoka babu alamar rama ko siranta a tattare da ita. Koda ta nufi cikin kicin ɗin kai tsaye wajen robar da suke zuba gawayin ta nufa, ganin akwai ragowarsa da ɗan yawa ya sanya ta ɗakko murahun gawayin guda biyu ta zuzzuba wanda zai isheta amfani. Bayan ya ruru ne ta ɗaura ruwan wanka a guda ɗaya, ɗaya kuma ta ɗaura ɗumamen ragowar tuwo miyar kuka da suka ci a daren jiya suka rage.
NUFIN ALLAH
*Paid book:500*
*Chapter 2*
_Free page._
Kafin ruwan ya tafasa tuwan ya ɗumamu Najma ta kammala sharan ɗakinsu, wanda ba wani girma bane da shi. Bayan ta haɗa musu shayi ruwan bunu(ruwan lipton), ta juye ɗumamen a kula ta nufo ɗakin Inna Mairo da shi. A falo ta aje komi ta nufi bedroom ɗin wajen Inna Mairo, ta sameta a kwance har lokacin tayi lamo akan katifarta tana faman zurfafa tunani. Cikin sanyin murya Najma ta zauna daga bakin bed ɗin tana faɗin, “Inna na kammala, ga ɗumamen da ruwan lipton can a falo. Inna Mairo ta muskuta ta tashi zaune tana sauke manyan idanunta da Najma ta gada a kanta, ta sauke numfashi a hankali ta ce, “Sannu Najma da ƙoƙari, Allah ya yi albarka ya zaɓa muku mazajen aure na gari.” Najma da tuni ta gane jam’u da Inna Mairo tayi tana nufin ita da su Luban gidan hakimi take wa addu’ar, sai ta kauda kai tana amsawa a zuci. Inna Mairo ta cigaba da cewa, “Da zaran mun kammala karin kumallon sai ki bani ruwan wanka, watakila idan nayi naji ɗan ƙarfin jikina.” Najma ta murmusa ta ce, “To Inna!” Daga haka suka fito zuwa falon da Najma ta shareshi tsaf, ta goge yagaggen ledar tsakar ɗakin. Suna cin abincin suna taɓa hira akan ciwon Inna Mairo da irin yadda ake samun kuɗin sayen magungunan da ƙyar.Ba don Hakimi ba da tuni watakila Innar ta mutu,sabida rashin gata da wanda zai tsayawa lamuransu har ya ɗauki nauyinsu. Ba kuma don Innar ta rasa Ƴan uwa ba, sai don Ƴan uwan nata sun gujeta sun juya mata baya shekaru kusan bakwai kenan rabonta dasu.Tsakaninta dasu sai dai aiken kayan abinci da zanin sallah da suke mata duk shekara, amma baya ga haka babu mai takowa inda take domin sunyi arziƙin da suke ganin tamkar ci bayane su tako ƙauyen garin giwa su ce suna da ƙanwa bare har su ga halinda take ciki su tallafa mata. Wani irin abu mai ɗaci ya tsayawa Inna Mairo a maƙoshinta, lokacin da ta tuno zuwan Gwaggo na ƙarshe garin giwa, bayan rasuwar marigayi Malam Mahmuda. Najma ta kwashe komi ta kai kicin ta aje, ta ɗauki bokiti ta ɗebowa Inna ruwan zafi ta surka, ta kai mata banɗaki don tayi wanka ko zata ji daɗin jikinta kafin Baba Hakimi ya aiko da magungunan da zata sha.
Ɗakinta da ke kusa dana Inna ta shiga ta share tare da gyara shinfiɗar lafaffiyar katifarta, wacce tun ta makarantar kwanan da suka yi ne ta dawo da abin ta tana kwanciya akai. Gefen katifar ta samu ta zauna ta sauke numfashin a hankali, zuciyarta na kwaɗaita mata son jin asalin tarihin Innarta da yadda aka yi ta auri Mahaifinta Malam Mahmuda. Tana matuƙar son sanin musabbabin da Gwaggon kaduna take nuna wa Inna ƙiyayyar da har ta kai ta rabata da Ƴan uwanta, ta hana su raɓeta ko ita Innar ta rabesu. Tana nan zaune tana zurfafa tunani har ta ji shigowar Inna ɗaki alamun ta dawo daga banɗaki yin wanka, tayi saurin tashi ta fito tana faɗin, “Inna har kin fito?” Inna Mairo ta dubi tilon Ƴarta da take duba ta ji sanyi a ranta ta bata amsa da faɗin, “Na fito Najma, ke ma sai ki je ki yo wankan kafin asan abin yi zuwa rana ko?” Najma ta jinjina kai tana faɗin, “To Inna, amma ina ga da rana ɗinnan da wuya mu samu abin girkawa domin babu sauran kayan abinci sun ƙare.” Inna Mairo tayi shiru, kafin daga bisani ta dubi Najma tana faɗin, “To shikenan Najma, Allah zai rufa asiri. Ina ga Hakimi ya shafa’a ne ba a kawo kayan abincin wannan satin ba.Ki yo wankan ki fito akwai ɗari biyar sai ki je ki auno mana garin kwaki muyi kwaɗonsa da ƙuli muci kawai.” Najma ta jinjina kai cike da gamsuwa da maganar Inna ta ce, “To shikenan Inna, bari in je in yo wankan.” Ta nufi ƙofar fita daga ɗakin ta bar Inna Mairo da bin bayanta da kallo, tana mai jin matuƙar tausayin Najmar na danne zuciyarta.A kullum ta tuna cewa Najma ita kaɗaice a gareta, kuma bata da sauran dangin uba a raye da zasu tallafeta sai ta ji hankalinta ya sake tashi. Domin ita kanta ya ta ƙare da nata Ƴan uwan bare har ta sanya ran watarana zasu tallafesu ita tilon Ƴar nata Najma. Ta ɗanɗana zafin rashin Ƴan uwa ko Ƴar uwa shaƙiƙai da bata da su, ta san zafi da illar hakan ga duk wanda ya taso cikin tsangwaman Ƴan uban da kansu ba a haɗe yake ba. Ta san illar ƙiyayyar matar uba, domin shi ne silar shigarta duk wani halin ƙuncin da take ciki a yanzu, bayan ƙasa ya rufe idanun Abbah da gwarzon mijinta Malam Mahmuda. Domin a lokacin Abbah na raye duk irin ƙiyayya da jin zafinta da Gwaggo ke yi, bata iya nuna mata wani abun sabida shakkar idanunsa. Amma tun daga randa ya kwanta dama, ta sake gane irin ƙiyayyarta da ke zuciyar Gwaggo, wanda bakomi ya sake assasa ƙiyayyar ba sai mugun riƙo da Gwaggon ke da shi.
Inna Mairo ta faɗa ɗakinta don shafa mai ta sanya kaya, tana yi zuciyarta na sake tariyo mata da irin rayuwar da tayi a garin giwa ,tun daga zuwanta tana amarya, har kawo yau da wanda ya yi silar zuwanta garin bashi a raye. Ya tafi ya barta da tarin kewa da ƙuncin zuciya, Ya barsu a lokacin da ita da tilon Ƴarsa ke matuƙar buƙatar kulawarsa. Hawaye masu tsananin zafi da sam bata iya riƙesu a duk lokacin da tunaninsa ya bijiro mata suka silalo daga idanunta,ta kai hannu ta sharesu tana jin ƙunci mai yawa na sake mamaye zuciyarta. Cikin sanyin jiki ta kammala kintsa kanta ta sanya riga da zani na wata atamfar chiganvy, wanda ke ɗaya daga cikin irin zannuwan da ake aiko mata dasu daga hannun Ƴan uwanta su Yaya Kabeeru.
Najma wanka tayo ta shirya kanta cikin wata doguwar rigar atamfar roba, kalar atamfar ja ce da ta haska baƙar fatarta mai laushi.Fuskarta ya yi fayau babu ɗigon kwalliya illa tozali da ta zizarawa fararen idanunta, waɗanda ke da wani irin haske da ƙyalli tamkar ruwan hawaye na taruwa a cikinsu. Gashin kanta sassalka irin na asalin fulanin da ta gado wajen Inna, ta ɗaureshi a tsakiyar kanta kafin ta ɗaura ɗankwalin kayan nata. Lokacin da ta fito daga ɗakin ta samu Inna Mairo zaune a falo, ta nema waje ta zauna daga ƙasan ledar tsakar ɗakin ta ce, “Inna na kammala shirin, bani kuɗin siyan garin kwakin in je in dawo kafin rana tayi.” Inna Mairo ta dubi Najma tana yaba kyawunta, wanda ta gado a wajenta. Baƙar fatarta ce kawai na Malam Mahmuda, amma kyawun fuskar da surar jikin duk nata ne, domin babu inda Najma ta barota a kamanni sai bambamcin kalar fata kawai. Ita Inna farace tas! Wacce a kallo ɗaya zaka gane cewa jinin fulanice sosai. Ta miƙa hannu ta ɗakko naira ɗari biyar ɗin da shi kaɗai ya rage musu a gidan ta miƙawa Najma, ita kuma ta sanya hannu ta amsa tana miƙewa tsaye ta tashi ta nufi ɗaki don ɗakko hijab.
Lokacin da Najma ta dawo ta samu Auwalu ya kawo ma Inna magungunanta, sai dai ba a samu guda ɗaya ba sabida tsadarsa. Ta dubi Inna a lokacin da take mata bayanin ta ce, “Yanzu Inna to ya za a yi kenan?” Inna Mairo tayi murmushin ƙarfafa guiwa ta ce, “Allah zai kawo yadda za a yi Najma, ni burina ma mu sake samun jarin da zaki cigaba da toya ƙosannan tunda sana’ar ya amshemu dashi muke samun na rufin asiri.” Ta kai ƙarshen maganar da sanyin murya. Najma ta jinjina kai ta ce, “To Inna ina zamu sama jarin? sai dai idan za a sake ɗaga wani abin a siyar ko?” Inna ta ɗanyi jim…Kamar ba zata tanka ba, sai daga bisani ta bai wa Najma amsa da faɗin, “Najma na yanke shawaran mu sai da katifar ɗakin Malam tunda babbace zata yi daraja.” Najma da zuciyarta ke sake raunana ta dubi Inna ta ce, “Hakan ya yi Inna, Allah sa tayi darajar da za a samu jarin mai ɗan kauri.”
Inna Mairo ta amsa da cewa, “Ameen Najma, idan kin kammala ayyukan zuwa anjima sai ki je gidan Adama dillaliya ki yi mata maganar katifar.” Najma ta ce, “To Inna!” Daga haka ta zare hijab ɗin jikinta ta nufi kicin don haɗo musu kwaɗon garin kwakin. Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala yin kwaɗon wanda yaji ƙuli dasu tumatir da albasa da ta yankasu gunin sha’awa a ciki, ta juyosa cikin baban faranti ta nufi ɗakin Inna dashi. Ta samu Inna ta shige ɗaki don yin sallar azuhur, hakan yasa ita ma ta fito ta ɗauki buta ta nufi bayi don kama ruwa da ɗauro alwala.
Bayan sun idar da sallar ne suka haɗu suka ci kwaɗon cikin kwanciyar hankali. Najma ta ɗebo musu ruwan rijiyarsu mai daɗi suka sha suka yi hamdala,sannan ta ɗakko ma Inna magungunanta ta sha.
Suna zaune suna ɗan taɓa hira Najma ta dubi Inna Mairo ta ce, “Inna don Allah ki sanar dani tarihinki dana aurenki da Babana, ina son sanin dalilin ƙiyayyar da Gwaggon kaduna ke miki.” Ta dakata da maganar tana duban fuskar Inna Mairo don ganin yadda ta amshi maganarta. Inna da idanunta ke kan Najma tuni ta haɗe fuska, tana mata wani duba na mai yasa kike son sani? Kafin ta buɗe baki ta ce, “Najma sau nawa zan sanar dake babu ruwanki da sai kin san abinda ya faru? Ki rufe wannan maganar bana sonta.” Najma da zuciyarta ke matuƙar son sanin cikakken tarihin Innarta da yadda aka yi aure ya wanzu tsakaninta da mahaifinta, sai ta narke murya tana matso hawaye ta ce, “Don girman Allah Inna karki gwaleni a wannan karon, wallahi ina matuƙar son sanin cikakken asalina da tarin yadda aka yi kika auri Babana? Ki taimaka ki sanar dani tarihin rayuwarki ko na ƙaru da wani abin.” Inna Mairo ta jinjina kai cike da jin tausayin Najma, don ta san tana son jin tarihin baya ne ko zata gano ita ce mai laifi ko Ƴan uwanta su Yaya Kabeeru da suka wofintar da rayuwarta. Ta dubi Najma tana bata tabbacin zata sanar da ita tarihin rayuwarta baki ɗaya, da yadda aka yi Malam Mahmuda ya yi nasarar aurenta, har ya ɗakkota daga birni ya kawota ƙauyen garin giwa. Ta muskuta tana gyara zamanta sosai, ta fuskanci Najma da tayi zuru tana sauraren jin cikakken tarihin rayuwar Inna Mairo da Mahaifinta Malam Mahmuda.
NUFIN ALLAH.
*Paid book:500*
*Chapter 3*
_Free page_
*WAIWAYE…*
Inna Mairo ta dubi Najma da take sauraren jin ta bakinta, ta saki murmushi mai faɗi kafin ta fara da faɗin, “Kamar yadda kika sani Babanki Malam Mahmuda haifaffan nan garin giwa ne.Ya taso cikin maraicin rashin iyaye,don Ya rasa iyayensa tun yana ƙarami.Hakan yasa ya taso a hannun ƙanin Mahifinsa mai suna Malam Lawal, Malam Lawal Malamin addini ne mai karantar da almajirai karatun addini anan babban zauren dake gidansa.Kasancewarsa Malamin addini ya sanya Babanki ya samu ilimi mai zurfi na addini a wajensa.Musamman karatun qur’ani da yafi zurfi a cikinsa, har ya kai ga haddacesa tun yana da shekaru goma sha biyu a duniya. Malam Lawal bai taɓa haihuwa ba, hakan ya sanya ya rungumi Babanki tamkar shi ya haifesa. Ya bashi dukkanin gata da kulawa, sannan Ya sanya shi a makarantar boko sabida bai yadda da zama cikin jahilci ba. Tun daga kan matakin primary Malam Mahmuda bai tsaya da karatun boko ba har sai da Ya kai matakin diploma,inda Ya yi karantun diploma ɗin nasa a jami’ar Ahmadu Bello dake zaria. Ya karanci fannin Business ne, don shi yafi sha’awar Ya zama ɗan kasuwa ba ma’aikacin gwamnati ba.Bayan Ya kammala karatun diploma ɗinsa ne Ya tattaro Ya dawo gida giwa, Ya cigaba da sana’ar yin ɗinkinsa na maza da ya ƙware akai. Don tun yana matakin sakandiri yake koyan ɗinkin har Ya ƙware, Ya mallaki keken kansa Ya buɗe shago anan zauren gidan Malam ɗin Yana sana’arsa. Sosai kuma yake samun rufin asiri da ɗinkin, domin Ya yi ƙwarewar da har daga birni yake samun ɗinkuna. Bayan Ya dawo gida ya cigaba da sana’ar ɗinkinsa ne, sai kuma tunanin son zurfafa iliminsa a ɓangaren addini Ya shigesa. Ya samu Malam Lawal Ya sanar dashi buƙatarsa, shi kuma sai Ya ji daɗi tare da bashi goyan baya har Ya yi masa alƙawarin danƙashi wajen wani babban amininsa wanda yake shi ma babban Malami ne garin kaduna. Malam Mahmuda ya yi farin ciki mai yawa, daga ƙarshe suka rabu da Malam ɗin akan cewa zai yi magana da aminin nasa mai suna Malam Muhammad Kabeer Dukku.Kwanaki biyu bayan sunyi maganar Malam Lawal ya kira Babanki ya shaida masa cewa ya fara shiri, don kuwa Malam Muhammadu ya yi na’am yana kuma maraba dashi a matsayin sabon ɗalibinsa. Kamar da wasa maganar tafiyar Malam Mahmuda karatu ya tabbata, ya yi sallama da dukkanin abokanansa su Haruna ɗan gidan Hakimi, da sauran abokanansa da suka tashi tare. Ya kama hanyar ya bar garin giwa bisa jagorancin Malam Lawal da matarsa Hanne da suka yi masa rakiya, suka kaisa har rigasa gidan babban aminin Malam Lawal ɗin…..
Inna Mairo ta ɗan dakata tana duban yadda Najma ke saurarenta da dukkanin nutsuwarta, ta lumshe ido kaɗan tare da sake buɗesu akan Najma ta ce, “Kin san waye wannan Malamin da aka kai Babanki wajensa?” Najma tayi saurin girgiza kai alamun bata sani ba,hakan ya sanya Inna Mairo yin ƙaramin murmushi tana mai cigaba da faɗin, “Ba kowa bane sai mahaifina Malam Muhammad Kabeer Dukku. Shi ɗin ɗan asalin garin Dukku ne dake ƙaramar hukumar jihar Gombe. Bafulatani ne sosai domin uwa da ubansa duk fulani ne, neman karatun addini ne shi ma ya kawosa garin kaduna daga Dukku. Daga nan ne Ya ji daɗin zama har Ya fara sana’ar sai da zaruruwan ɗinki, yana kuma taya Malaminsa noma da kiwo. Sannu a hankali har Ya yi ƙarfi Ya buɗe ƙaramin shagon saida kayayyakin ɗinki a Kawo, gefe guda kuma yana kiwon kaji idan sun isa ci Ya fitar Ya sayar. Cikin hakan Ya haɗu da Gwaggo Hauwa,wacce take haifaffiyar ƴar cikin hayi rigasa ce. Bayan sunyi aure sai buɗi ya yi ta samuwar masa, samunsa na sake bunƙasa har ya kai Ya buɗe babban shago anan kawo. Shakerarsu biyu da aure aka haifi Yaya Kabeeru, bayan shekaru uku kuma aka sake haifo Yaya Ali. Daga nan sai haihuwar ta tsayawa Gwaggo, sai da ta share shekaru kusan takwas ta sake haifo ƴa mace. Sai dai ko kwana jaririyar bata yi ba ta bar gidan duniya, daga nan ne kuma Gwaggo bata sake haihuwa ba,har kawo yanzu da shekarun tsufa suka risketa.Abbah kamar yadda muke kiran mahaifinmu, Ya auro mahaifiyata ne bayan kusan shekaru talatin da aurensu da Gwaggo. A lokacin su Yaya Kabeeru har sun zama samari sun kammala deegree ɗinsu, don Abbah bai yi wasa ba wajen basu ilimin zamani dana addini. Hankalin Gwaggo ya tashi matuƙa da wannan ƙarin aure da Abbah Ya bijiro dashi.Ta dinga shuka tsiyataku kala da kala amma hakan bai sauya komi ba,don Abbah koda wasa bai ji cewa zai fasa auro Innata ba. wacce ya ganota a can Kaita mahaifarsa.Marainiyace da bata taso a hannun iyayenta ba duk sun rasu, ta taso ne a hannun wani ƙanin Babanta anan kusa da gidan Iyan Dukku, wato mahaifiyar Abbah kenan. Bafulatanace ita ma,uwa da ubanta duk fulani ne.Tausayin maraicin da take ciki da gallazawar da ake mata a gidan riƙonta, ya sanya mahaifiyar Abbah mai suna Iya bai wa Abbah ƙwarin guiwa akan Ya auri Innata mai suna Maryam. Ta kuma ƙara da kwaɗaitar dashi cewa watakila ya samu wani rabon,tunda haihuwa tuni ya ɗaukewa Gwaggo. Lokacin da aka yi bikin haukane kawai Gwaggo bata yi ba, sabida tsananin zafin kishi kamar yadda Iya ke bani labari. Malam bai aje Innata Mairo gida ɗaya da Gwaggo ba, sai ya kama mata haya a wata unguwa da ake cewa hayin banki. Wata ɗaya da auren Innata ta samu ciki, murna a wajen Abbah ba a cewa komi. Iya ma dake can Kaita da labari ya je mata murnar tayi sosai, tana taya shi addu’an Allah ya bashi ɗiya mace,don Iya na matuƙar son ƴaƴa mata domin ita Allah bai bata ba. Duka yaranta uku maza ne, Abbah kuma shi ne babba a cikinsu, sai ƙanninsa biyu Mansur da Salihu. Waɗanda suka rasu suna ƴan samari dasu, sun rasu ne sakamakon haɗarin mota da ya ritsa dasu akan hanyarsu ta komawa makarantar kwana da suke yi a bakori.Sai ya zamana Abbah shi kaɗai ya rage wa Iya, baya ga shi bata da kowa sai ƴaƴan ƴan uwa da take xagaye dasu.Abbah Ya yi juyin duniya ta dawo wajensa da xama taƙi, ba kuma komi ya sanya hakan ba sai rashin kirkin Gwaggo. Don ko kaɗan bata mutunta Iya da duk wasu dangin Malam,ƴan uwanta da ƴaƴanta kawai take gani da mutunci take kuma so. Gwaggo ji tayi kamar ta mutu don baƙin ciki, lokacin da maganar samun cikin Innata ya risketa.Ta sake ninka tsanarta da jin kishinta mai zafi a zuciyarta,duk da cewa ba gida ɗaya suke ba.Amma hakan bai taɓa sanyaya zuciyar Gwaggo ba,kullum cikin nuna kishi da ƙiyayyar da take wa Innata take. Tasha faɗi akan kunnuwar Abbah cewa ta tsani Innata, kuma ba zata taɓa son duk wani abu da zai fito daga tsatsonta ba. Malam ya yi nasihan ya yi faɗan ya yi rarrashin har ya gaji ya zuba mata ido, sai dai fatan shiriya da yake nema mata ba dare ba rana. Sabida a cewarsa zafin kishinta har ya yi yawa,dole a dinga roƙo mata sassauci a wajen Mahaliccinta. Da cikin Innata ya isa haihuwa ne Iya ta haɗo kayanta daga Dukku ta dawo kaduna, don Allah ya ɗaura mata son Innata tare da jin tausayin maraicinta. Daren ranar wata juma’a naƙuda ya kama Innata,kafin asuba an haifoni bayan Inna tasha matuƙar wahala.Ana murna ta sauka lafiya sai kuma jini ya ɓalle mata,kafin aje ga asibiti rai ya yi halinsa ta amsa kiran Ubangijinta.Faɗin irin tashin hankalin da Malam ya shiga bazai misaltu ba, hatta da samarin ƴaƴansa su Yaya Kabeeru mutuwar ya jijjigasu.Don duk irin ƙiyayyar da Gwaggo kewa Innata tana kuma cusa musu ra’ayin su ƙita,hakan bai yi tasiri a zuciyarsu ba sabida Innata bata taɓa yi musu koda kallon banza bane.Duk sanda zasu je wajen Malam idan yana gidanta,kyakykyawar tarba suke samu daga gareta.Take aka yi mini huɗuba da sunan mahaifiyata Maryam, bayan an kammala zaman makoki ne sai Iya ta tafi dani Dukku. Don ta ce bata amince a bai wa Gwaggo ko dangin uwata riƙona ba,tunda ita ma Innata marainiyace a cikin rashin gata ta rayu bare ace zasu iya riƙeni. Gwaggo kai tsaye dama ta ce ba za ta taɓa riƙon Ƴar kishiyar da kowa ya shaidi irin soyayyar da Abbah ya nuna mata,sabida ya aurota tana a ɗanya sharaf ɗinta. Iya ta tattara komi nawa muka wuce garin Dukku, na fara rayuwa a hannunta cikin tsananin gata da kulawa.Kusan koda yaushe Abbah na kan hanyar zuwa dubani,domin dukkanin soyayyar da yake wa Innata Mairamu sai ya koma kaina. Baya iya sati biyu bai je Dukku ya ga lafiyata ba, kuma baya zuwa hannu rabbana sai ya yi mana siyayya mai yawan gaske. Wannan sunturi da Yake yi a kaina da yadda ko a gaban Gwaggo ne Yake nuna tausayina da yake ji a cikin zuciyarsa, sai hakan ya haifar da ƙiyayyata a zuciyar Gwaggo. Ta juyar da dukkanin ƙiyayyar da take wa Inna zuwa kaina, bata taɓa yin kara tabi Abbah Dukku don ta dubani ba ko sau ɗaya.Wannan rashin karan da ƙiyayyar da take nuna mini akan idanun Iya idan munzo kaduna,sai ya sake haifar da rashin jituwa a tsakaninta da Iya. Sabida a lokacin duk wani mai son ganin ɓacin ran Iya to ya gwadamin rashin ƙauna, ko nuna min halin rashin kirki.Na taso da tsananin kyawu da shiga rai, sabida babu inda na baro kyawun Innata na asalin fulani. Jajir nake ga gashi har gadon baya, a haka na taso ina samun tattali da kulawa wajen Iya, wacce bata taɓa bari nayi kukan rashin uwa ba.Hasalima ita na taso na sani a matsayin Innata, sai dana fara girma nayi wayo har na shiga aji uku a primary, sannan Iya ta sanar dani cewa ita Kakata ce,Innata ta rasu tun ranar da ta haifeni. Sam banji komi a raina ba lokacin da take faɗa mini hakan, domin ni ita na taso na sani a matsayin uwata. Ban fara kukan rashin gata da rashin uwa da nayi tun ina tsummar goyo ba sai da Allah ya ɗauki ran Iya, a lokacin ina aji biyu na sakandiri. Nayi kuka kamar zan zautu sabida ita ce kaɗai gatana, da ita na rayu nayi sabon da bana iya ɓoye mata dukkanin abinda yake damuna. Ita kuma bata gajiyawa wajen yi min dukkanin abinda nake so matuƙar baifi ƙarfinta ba.Ban saba da Yayuna su Yaya Kabeeru ba, domin basa zuwa inda muke ni da Iya sai in wani abu ya faru, ko sallah tazo haka sai zo gaisheta.Sai kuma idan Abbah ya taso su a wasu lokutan, to shine zasu zo tare da shi. Amma baya ga gakan takanas dai su taka suje Dukku basa yi,musamman da ya zama sun kama aikin gwamnati a lokacin.Kuma dukansu ba a garin kaduna suke aikin ba, Yaya Kabeeru na NNRA Abuja ne.Wani abokin Abbah ne ɗan siyasa ya amshi takaddun Yaya Kabeerun Ya samo masa gurbin aiki wajen,wanda babban waje ne da ake biyan albashi mai tsoka matuƙa.Idan ba Ƴaƴan manya bama ba a cika bai wa wasu gurabin aiki a wajen ba, sai masu ƙafa da hanya kamar yadda ya kasance da Yaya Kabeerun. Shi kuma Yaya Ali ya samu aikinsa ne a gidan gwamnatin Kano, yana lallaɓawa da albashinsa yana kuma neman scholarship don yana da burin son fita waje ya yo masters deegree ɗinsa a can. Rasuwar Iya shi ya janyo mini dawowa hannun Gwaggo da zama,dawowar da ya zame mini tashin hankali da jefa rayuwata cikin ƙunci mai yawa.Domin Gwaggo ta amshi riƙona ne don babu yadda zata yi,s
abida Abbah ya nuna bashi da wata mai riƙe masani, don haka dole in dawo ƙarƙashin kulawarsa tunda gata a raye matsayin matarsa. Tunda na dawo kaduna wajen Gwaggo ban taɓa ganin soyayyata a idanunta ko kan fuskarta ba, kullum na kalli idanunta tsanata nake hangowa a cikinsu. Abbah bai ɓata lokaci ba wajen nemo mini gurbin karatu a wata private secondary school, na cigaba da zuwa makaranta inda aka aje a JS3.Fara zuwa ta skull ɗin ne ya rage min ƙuncin da nake ji na xaman takura da bautar dani da Gwaggo ta fara yi, kuma da zaran na dawo daga boko ƙarfe huɗu zan shirya na wuce zuwa islamiya.Islamiyar a nan kusa damu ne bamu da nisa sosai,hakan yasa da ƙafa nake gangarawa na je.Bana shigowa gida sai ƙarfe shida na yamma,sai ya zama bani da wani lokacin kaina in ba alhamis da juma’a da bana zuwa islamiya ba. Shi ma kuma a ranakun Abbah ƙarfe huɗu yake baro shagonsa a Kawa,Ya dawo gida don karantar dani wasu littafan addinin. Duk wannan rashin lokacin da bani dashi, hakan bai hana Gwaggo nemo hanyar da zata cigaba da bautar dani ta ƙuntata mini ba.Sai ta koma tashina a bacci tun ƙarfe huɗu na asuba,a lokacin zan yi mata duk wasu ayyukan bautar gyaran ɗaki da wanke-wanken kayan da muka ci abincin dare. Ni zanyi abin karin safe kafin in tafi school, sabida tun a Kaita Iya ta horar dani ɗaura sanwa. Don ta sha ce mini Mairona iya girki shi ne martaba da adon mace, don haka ki dage wajen ganin kin iya sarrafa hatsi kar ki zama mai son jiki ta wannan fannin domin ke mace ce aure zaki yi. Hakan da Gwaggo ta gane ina da bai wa ta fannin iya girki,sai ya sanya ta sallami mai aikinta wacce dama Yaya Kabeeru ne ya ɗaukar mata ita, Ya ce lokaci ya yi da xata fara hutawa tunda sun kawo ƙarfi.Abbah bai san duk halin da nake ciki ba, don ta iya takunta a gaban idanunsa bata nuna min rashin ƙauna sosai. Sannan shi ba mazauni bane a kasuwa yake yini a shagonsa, sannan tun asubahin farko yake ficewa zaure don bai wa almajiransa karatu. Ba zai shigo gida ba sai anyi sallar asuba ya jasu jam’i, hakan ya sanya har in kammala dukkanin bautar da nake yi bai ma sani ba. Ina cikin wannan rayuwar aka kawo mahaifinki Malam Mahmuda Najma, na dawo daga makarantar boko na cidda mun yi baƙi ashe mahaifinki ne da ƙanin ubansa Malam Lawal da matarsa. Na gaidasu na wuce ɗakina da yake can ciki,bayan na sauya kayan jikina nayi shirin islamiya kamar yadda na saba yi.Na ci abincin rana da shi kaɗai Gwaggo keyi don dole tunda ina skull, na gabatar da sallar la’asar na ɗakko jakata na fito don tafiya islamiya. Anan na tadda baƙin da muka yi suma suna haramar tafiya, Abbah ya shigo har falo suna gaisawa da Inna Hanne. Na yi musu fatan sauka lafiya na fice don tafiya makaranta, a zaure naci karo da wani kyakykyawan matashin saurayi baƙi sosai dashi. Amma yana da kyawun fuska da suran jiki sosai,na wuce ina ayyanawa a zuciyata cewa tare suke da baƙin Abbah kenan. Bayan magriba mun kammala cin abincin dare tare da Abbah, wanda lokuta da yawa tare muke cin abincin dare dashi. Muna yi yana lallaɓani da yi min nasiha akan inyi haƙuri da rayuwa, da kuma duk halin da zan tsinci kaina a ciki. Ina matuƙar jin daɗin irin ƙauna da shaƙuwar dake tsakanina da Abbana, wanda hakan ne ke daƙile kaso mai yawa na jin zafin ƙiyayyar da Gwaggo ke mini, da kuma yadda sam babu shaƙuwa tsakanina dasu Yaya Kabeeru. Don ko sun zo gida tsakanina dasu gaisuwa ce kaɗai, baya ga haka basu taɓa jana a jikinsu sun nuna mini kulawa ko ƙauna ba.A matsayina na ƙanwarsu mace tilo da suke da ita, sam basu taɓa nuna min cewa suna maraba dani a matsayin ƙanwa garesu. Bayan mun gama cin abincin muka taɓa hira har aka kira sallar isha’i, Abbah Ya je sallar isha’i Ya dawo ne.Ya taramu ni da Gwaggo ya yi mana bayanin cewa ya samu baƙon ɗalibi da xai riƙa ɗaukar karatu a wajennsa, sai dai wannan ɗalibin yasha bambam da sauran ɗalibansa.Don shi wannan a matsayin ɗa yake a wajensa, sabida haka anan cikin gida za a riƙa zuba masa abinci sau uku a rana kamar yadda su Yaya Kabeeru zasu ci idan suna gari. Sannan yana da hurumin da zai iya shigowa ciki idan yana buƙatar wani abu ko don gaisawa da Gwaggo,Ya shaida mana cewa sam bai yi masa shamaki da hakan ba, matuƙar mu’amalar da zai yi a cikin gidan ba zai wuce tsakanin babban falo zuwa kicin ba. Muka yi shiru ni da Gwaggo muna sauraren jawabin Abbah, yayinda zuciyata ke hasaso mini cewa, ba kowa bane baƙon Abbah sai wannan black beauty ɗin matashin dana gani a zaure ɗazu. Gwaggo ta jinjina kai bayan ta gama jin jawabin Abbah, sannan ta buɗe baki ta ce, “Abbansu yanzu don kawai an kawo saurayi ɗan amininka shi ne har zaka bashi damar shigowa cikin gida ya yi mu’amala kamar yadda su Kabeeru zasu yi? Kana ƙoƙarin nuna cewa zaka daidaita matsayinsu kenan ko me?” Abbah ya dubi Gwaggo cikin nuna rashin jin daɗin maganar da tayi ya bata amsa kai tsaye da faɗin, “Hakane zan daidaita matsayinsu ne Hauwa, don inda kara ɗan da yake a matsayin ɗan aminina to nima yakamata na ɗaukesa matsayin ɗane.Don haka ki iya harshenki akan furta kalamai marasa kan gado akan Mahmuda, sannan zuwa da safe zan gabatar muku dashi..