Littafan Hausa Novels

Mannubiya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Mannubiya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MANNUBIYA

O 1

NA

Humayrah Bulama

 

 

Daga k’ungiyar ELEGANT ONLINE

 

__________________

 

A shekarar 1990, A garin Kano.

 

A hankali yake tu’kin motarsa k’irar Daewo Nubira.

 

Kamar ba Ya so ya k’arasa inda

Zai je saboda yanayin tuk’in na sa daya ke yi a gefen titi a hankali, a hankali.

Sannu sannu Bata hana zuwa… in ji malam bahaushe don

A hakan ya samu ya k’arasa gidan shi dake unguwar sharad’a. Ko da ya k’arasa bakin gate din bai yi horn ba sai da mai gadin da kan sa ya ji tsayuwar mota ya lek’o

Kasaitar So Hausa Novel Complete

Tukunna ya koma da sauri ya wangale gate d’in Madaidaicin flat house d’in. Jikinsa na rawa

Sakamakon ganin uban gidan nashi ne ke tsaye a waje.

 

Ko da ya shiga ya k’arasa yayi parking

Kashe motar kawai ya yi ya d’aura kanshi a jikin sitiyarin motar ba tare da ya fito daga motar ba.

 

 

Yafi minti talatin a haka yana tunani shi ka’dai Kafin tashi d’aya gaban sa ya yanke ya fa’di.

Ransa ya sake b’aci

Sakamokon Jin fitowar ta .

Ko ba a fadi mishi ba ya San Khadijah ce ,tunda basu da me aiki a gidan daga shi sai ita sai mai gadi Wanda yake musu har wankin kayansu da guga.

 

 

Shiruu kawai ya yi yana jin ta ta rufe k’ofar parlourn data bu’de ta fito ta tunkaro motar Da yake ciki a zaune.

 

As he expected, tana zuwa

Ta banka’da k’ofar motar da k’arfi.

 

Ko sannu da zuwa babu

Cikin fushi ta ce “Shine sai da ka kira Abba ko? Cin fuska da

rashin adalcin da ka kusan aikatawa bai isheka ba.

 

Shine an kashe magana an gyara komai zaka wani wuce ka kira Abba, Me kenan kake so

Yanzu? So kake ya goya maka baya ko me?”

 

Bata jira Jan numfashi ba a hassale ta d’aura da cewa

“Tou bari kaji ,Ko ya Goya maka baya abinda kake so ba zai tab’a faruwa ba Wallahi, Tunda in kana tunanin Abba yana bayan ka ni kuma daddy yana baya na. Ta k’arashe maganar Tata cikin tsananin bacin rai da takaici.

 

Tun lokacin data iso ta fara magana Shima ya Ha’de rai ,

Fuskar nan tamau kamar bai tab’a dariya ba.

Ba tare daya kalle ta ba

ya zare key d’in motar

Ya d’auki abubuwan buk’atar shi ya mik’e ya fito daga motar.

Ko kallon inda take bai yi ba

Ya fara k’ok’arin wuceta .

 

Da dan karfi Sannan da sauri

Ta rik’o hannunshi

Cikin tsananin bacin rai ta ce

“IMAM ,Wallahi na fi k’arfin ka wulak’anta ni ,

Ai so ba hauka bane,bar ganin wai Ina sonka

Wallahi idan baka janye maganar nan ba zan maka abinda sai ka yi daka sanin ha’duwa da ita kanta khadijar zan Baka mamaki zan sanyaka ……..”

 

“Sannu Uwarsa”

 

Suka ji Muryar Abba daga sama

Wanda ba su san lokacin daya shigo ba

ta daki dodon kunnuwansu .

 

Tabbas ,ta sha jinin jikinta amman sam

Kishi da Bak’in cikin da yake a kwance a kan kyakkyawar farar fuskarta be Kau ba Sannan zuciyarta banda turnik’i da tafarfasa ba abunda take yi.

 

Ganin yanda Abban ya kafeta da idanuwa yana me

K’arasowa inda suke ne

Yasa ta d’an sunkuyar da kanta k’asa da sauri kuma ta cikawa

Imam din hannu .

 

Abban yana k’arasowa

Imam ya durk’usa har k’asa ya gaida shi ,bayan sun gaisa

Ya ‘dora da cewa

“Abba ai da ka bari mun k’araso

Don Yanxu nake shirin in yi wanka mu karaso wajen naka.”

“kada ka damu ai

Babu nisa Kuma Ina buk’atar yin tattaki din dama”

Haka kawai Abban yace Yana kallon khadija wadda take gaishe shi “ ina wuni”

Cikin d’an russunawa .

Bai amsata ba,ya juya ya bi bayan Imam

Wanda ya juya ya nufi k’ofar parlourn nasu da d’an sauri yana ce wa “Bismillah Abba. Da kansa Imam ‘din ya shiga ya kawo masa lemo mai sanyi da ruwa sai ‘d’an snacks a Gefe.”

Dan khadija Bata riga ta shiga parlourn ba .

 

Tabbas yanda taga abba tasan ba ze bi bayan ta ba

Sannan ba

‘daga mata kafa

Zai yi ba yau ,kuma tasan Abban nasu

Baya tolerating nonsense da tirjiya .

 

Zata iya cewa Bata tab’a ganin soyayyar ‘ya da uba irin ta Abban ta da sister din ta ba Amman tunda tayi mishi lefi ya fita harkarta

Ya yafe ta

Yanxu hatta ita kanta Bata San inda yayar ta ta take ba .

 

Ayanxu

Tsoron ta daya

Shine

kar ya goyawa Imam baya kuma ya turje Akan se ta bi ta yarda da abunda Imam din yake so

Dan inde haka ta faru

Tou wallahi ta shiga ukun ta .

 

Ko da ace ba Imam ta aura ba ,

Bata jin zata iya zama da kishiya ,

Ballantana kuma Imam din ne ,

Ayanda take masifar sonshi

Bata Jin xata iya jurar ganin wata ‘ya mace a matsayin matar shi bayan ita .Watan ma kuma Khadija ,

Yarinyar data san yana tsana nin so

Domin ko

Satin daya gabata

Haka ya fito kiri kiri

ya ce mata albarkacin sunan su yaxo daya ne yasanya

yake mata raha

yake dan kulata

 

…….

Tasan rashin shigarta Akan lokaci

Ka iya sake hasssala Abba,don haka ta yi ‘ko’kari ta tsayar da kukan nata da kyar

Ta goge hawayen ta

Ta nufi parlour itama .

 

Abba yana zaune a kan kujera

Imam a gefen shi

A zaune a kasa

 

A

Haka ta shiga ta samesu ,

Dan haka itama ta karasa ta zauna a kasa dayan gefen kafar Abban.

 

 

Ba tare daya kalleta ba yace

‘’Se yanzu kika ga daman shigowa kenan ‘’

Be Bata damar cewa komai ba

Ya sake cewa

‘’Inaso ki nutsu kiji abunda xan fada miki yanxu

Na farko shawarace

Na biyu ma kmr shawarar ce

Na uku kuma umarnine

Kuma dole kiji, Sannan kiyi .

 

Still be dau lokaci ba ya daura da cewa

‘’In mata uku Imam yace xe k’aro baki da hurumin shiga Kice A’a ‘’.

‘’Ki zauna a matsayin ki

Sannan ki yiwa mijinki biyayya ki bashi goyon baya ,

Ni ma a matsayina na mahaifinki

Kiyimin biyyayya ki yi abunda nace ‘’.

 

‘’Khadija,!

Imam ze Kara aure

Banason in ji wata matsala ta kuma kunno Kai daga gareki

Har ayi auren nan a gama

Ina ba haka ba Wallahi …..’’

 

Kukan data rushe dashi kmr Ana yanka ta ne yasa duk suka xuba mata ido kawai ,

Suna kallon ikon Allah .

 

 

Cikin kukan tace

Haba Abba

Ko

Wata na biyu ban gama rufawa a cikin gidan nan ba

ace za ayimin kishiya

Kuma Kuce inyi hakuri inyi shiru ?,

Shi meyasa ba zai hakura ba ,

Daddy fa yace be yadda ba bayason ya sake Jin maganar.

 

Cikin katse ta Abban yace

‘’That was when daddyn besan cewa ita wachchar khadijan ya fara so ba

Kuma itace budurwar sa tun asalin farko ba ,

Bari kiji tun Kafin shi Daddyn ya fara maganar ku ke da Imam

Already

Imam yayi min maganar khadija ,

Maganar aurenki ce ta sanya ya daga kafa

Dan haka yanxu Banga dalilin da zai sanya ya fasa aurenta saboda ke a karo na biyu ba Wallahi ‘’.

 

 

Cikin kuka tace

‘’Abba har fa ciki ta zubar

Kuma tsabar cin fuska

Har gidan nan ya kawo min ita

Lokacin

ko sati biyu ban yiba

a chan boys quarters din akayi jinyar ta

Saboda Bata da kowa ,

Taya za a hadani kishi da wadda ta gama shigomin gida ta San sirrina

Wadda Bata da iyaye

Me yawo a titi suna tallan Nono

…..’’

 

‘’Ya Isa haka ,khadija ‘’!

Abban ya daka mata tsawa cikin tarar numfashinta

 

Kafin yace

‘’Tashi ki tafi ki bani guri ‘’

 

Zata yi magana ya kuma daka mata wata uwar tsawar dan haka taja ta mike ta wuce ta shige daki tana wani irin kuka .

 

Ko da ta shiga dakin ma

ta jima

tana kukan Kafin daga karshe ta

Yanke shawarar Neman

‘Larai ‘

 

Saboda ta Lura Hatta mahaifiyarta ita ma bayan Abban take bi .

Iyayen ta sunada matukar kawaici

ta San Imam baya son ta

Biyayya ce ta sanya ya aureta,

Shiyasa su kuma iyayenta baxasu taba goyon bayan ta ba

Saboda

Gudun Samun matsala da

‘family frnds ‘d’in nasu .

 

Shiyasa gwara ta nemawa kanta mafita

Tun Kafin kawaicin fulanin iyayenta ya cutar da ita .

 

A nata lissafin

kamata yayi a ce an barta da Imam ta juyo da hankalinshi gareta ,

Bawai a hadata kishi da wata chan daban wadda zata zo ta lalata komai ta kuma janye mata hankalin masiyo ba ….

 

Khadija Tana shigewa ciki

Abba ya dan gyara zama ya kalli Imam kafin yace

‘’Naji Khadija ta fadi wani Abu wanda ban san dashi Akan khadijan da kake son ka auro ba

Ina fatan zaka cemin ba Dede bane ba .’’

 

Lumshe idanu Imam yayi

Kafin ya shafa farar fuskarshi

da tafin hannunshi ,

wanda tayi jajir zuwa yanzu tsabar shiga tashin hankali .

 

Abba. Is his only hope yasan shi kadai ze iya convincing su daddy su barshi ya auri khadija.

Abunda yaketa tsoro dama shine

kar su san kaddarar data afka wa khadijan dan yasan Muddin suka sani da wuya Abban shima ya yarda

 

Seda yaji Abban ya sake cewa

‘’Imam ,kayi shiru ‘’

 

Tukunna Ahankali ya bude idanunshi

Cikin sanyin jiki yace

 

‘’am Abba

Kmr yanda na gaya maka

Khadija Bata da kowa

Ita da Y’ar uwarta na sani tun farko suna kawo mana Nono office

Se kuma wani Uncle din su data taba hadani dashi

Wanda suke a gidanshi ,

A halin yanzu

Shima ya rasu

Kuma dama

matar tashi azabtar dasu takeyi

Tun a lokacin dayake a raye ma .

 

Shiyasa

Yana rasuwa ta tartara ta barsu ta yi gaba .

Su sunce

min Uncle din nasu da Baban su kawai suka sani

Ba su taba xuwa garin suba bama su dan garin ba har Baban ya rasu yanxu gashi shima kawun nasu ya rasu .

Shiyasa tun a lokacin naso in auri khadijar saboda itama yayar ta miji ya fito mata ta auri wani me mata uku da yara ashirin a layin nasu Amman yace ba zai rike Khadijah ba

 

Nasan zaman ta ita kadai akwai hadari

Shi kuma Daddy ya dage Akan sede ayi auren mu da Khadija tunda an Riga an gama magana

 

Ko uzurina be tsaya yaji ba

Gani yake yi kamar turjiya nake shirin mishi

Shiyasa na hakura

A wannan lokacin

kmr yanda kace inyi hakurin .

 

Itama ba yadda Banyi da ita Akan ta biyo ni ba Amman tace Zata iya zama ita kadai

 

Ni kuma abubuwa sun sha min Kai

A wannan lokacin

Ga hidimar biki

Ga aiki

A wannan tsakan Kanin ne aka samu wani Mara Imani yaje yayi mata fyade

Sam ba laifinta bane

Saboda seda tayi kwana biyu a asibiti Batasan ma a ina kanta yake ba

 

Tun daga lokacin naki amincewa taci gaba da xama a gidan ita kadai

Laifina daya dana kawota nan

Nasan be kamata in kawota nan ba

Tunda gidan aure na ne

Amman banida choice

Tunda su daddy baxasu Bari in Kai musu ita Chan ba

Ba tare da sunsan wacece ita ba

Gashi cikin data samu ata dalilin kaddarar data afka mata

Yaxo da matsala

Ana yin sati biyu ta fara bleeding muna xuwa asibiti ya zube.

Ga rashin lafiya ga rashin safety da shelter,

Shiyasa na kawota nan ita da nurse

Kuma

tunda khadija tayi bincike ta gano asalin gaskiya ta fatattakesu

Se da nayi kwana uku tukunna na nemota da kyar ‘’.

 

Shiruu ya danyi Kafin ya daura da cewa

‘’Dan Allah Abba ka duba Lamarin nan

Mu taru ni da Kai mu ceto rayuwar baiwar Allah ‘’.

 

ya karashe maganar cikin hade hannuwanshi kamr xe fashe da kuka .

 

 

Numfashi Abban ya fesar

Bayan dogon Nazari

 

Kafin ya kalli Imam din yace

‘’Zan ha’daka da driver gobe

ku je ayi duk wasu gwaje gwaje da suka kamata

Allah ya sanya alkhairi

Allah yayi maka albarka ,

Zanyiwa daddyn naku magana

Karka damu ze fahimta .’’

 

 

Wani tsananin sanyi ne ya lullube Imam ,har seda wasu hawayen farin ciki suka wanke mishi fuska .

 

Murmushi kawai Abban yayi ,

Daga haka ya mike da shirin tafiya .

Tsakanin uba da ‘ya se Allah

Yasan abunda yayi

Yake kuma shirin yi

Tabbas shine Dede ,

Amma kuma a take tausayin ‘yar shi se ya lullubeshi ,

Dan Tabbas yasan tunda har Imam ya rufe ido ya sake mishi zancen wata

Bayan ya aura mishi ‘yar shi

Ko watanni biyu ba a rufe ba ,

Tou fa ba karamin so yakeyiwa

Wachchar bafulatanar me tallan Nono ba .

 

Har ga Allah

Da ya ji shiru bayan wata daya da auren su Imam din

ya dauka ya hakura ne ,

Ashe abun yananan .

Tabbas rayuwar ‘yar shi khadija

Tana cikin garari .

Saboda tun shekara daya da ta gabata

A lokacin da aka fara maganar aurensu har kawo yanxu

Be taba ganin digon son ‘yar tashi a cikin idanun Imam ba .

 

Daddy is his best frnd

Tun yarinta ,Ba da ban haka da yanda yaga Daddyn ya nace da son yaga ya kulla aure a tsakanin su ba

Da babu dalilin da zai sanya ya yarda da auren khadjan shi da

Imam,

Tunda ya San

ba sonta yakeyi ba .

 

Yana fatan su samu su da sasanta ya so ta wata rana

Tou

Yanxu kuma gashi xe auri wadda yakeso .

Fatanshi daya Allah yasa khadijan tayi hankali ta kwantar da hankalinta tayi biyayya ta zauna lafiya

Watakila ta samu matsugunni a xuciyar mijinta

In ba haka ba kuwa

Bayajin tanada rabo a xuciyar Imam ……..

 

 

An dan Kai ruwa rana Kafin

Daddy ya yarda aka daura auren khadija da Imam a cikin sati daya ,

Ba kalar haukar da Khadija batayiba

Har kalanzir ta Barba’da a gidan yana bacci

Lokacin ana ‘I gobe ‘daurin auren

Allah ya taimaka

ya ji warin kalanzir din ya farka da wuri .

Yana xuwa ya tarar da ita tana kokarin kyasta ashana

Da kyar ya samu ya karbe

Yana jefar wa ta rarumo wuka,

Ganin fa dagaske kishi ya haukatata in ya barta kashe shi zatayi

Ne

Yasa ya fincikota dakyar ya fitar ya saka ta a mota .

 

Iyayenta kamar iyayenshi ne

Dan ze iya cewa

Shi da ‘dan uwanshi especially ma shi in particular kusan a hannun maman ta ma ya girma

Amman ya kamata a takawa haukar ta burki

Tun Kafin tayi ‘barna .

 

 

Ba dan yaso ba

Haka ya Kai ta gidansu ya fadawa su Abba duk abunda takeyi mishi

Har kokarin kashe shi data fara yau dinnan .

 

Sallamar shi kawai Abba yayi

Bayan ya bashi hakuri

Daga haka ya wuce ya barta a wajen su Abban don yace a bar mishi ita .

 

A tunanin ta fada kawai

Xa ayi mata

Daganan a maida ita

A ranar

Amman se taji Abba ya Hana

ya Hana ma a Barta fita ko kofar gida .

Tana ji Tana gani haka aka daura auren Imam da amarya Khadija .

Ba abunda yafi daga mata hankali irin yadda Abba yace

‘’baxata koma Kwata Kwata ba ‘’

Gashi auren datayi hauka akai ya Riga ya Kara

Dan haka

A take ta fara data sani

Hankalin ta ya sake tashi

Dan gani tayi

kmr ma ta bawa Imam damar cin

amarcin shi hankali

Kwance .

Ko sati ‘daya Ba ayi ba ta fita a haiyyacinta

kamar mahaukaciya haka ta koma

 

Ba da ban larai datake Bata Baki da mahaifiyarta ba

Da tuni ta xauce

….

 

 

Seda ta sha wahala ta fita a haiyyacinta tukunna

Dakyar su mama mommy daddy suka takurawa

Abba ya Kira Imam yace ya xo ya dauketa .

A Lokacin khadija amaryarshi Watan ta daya

Har da ‘dan cikinta

…..

 

 

Tare da Larai suka koma gidan nata

saboda itama a lokacin an dan samu matsala da ita a kauyensu

Taki ta koma

 

Ba karamin mamakin yanda khadija ta chanxa lokaci guda Imam yayi ba

 

ba kishi ba hauka Sannan taja abokiyar zaman ta a jiki kmr zata cinye ta dan so ,

Cikin jikinta kuwa ko ita uwar iyaka yadda zata kula dashi kenan

Komai

Nan nan. Ko abu me nauyi Bata ta’ba Bari ta dauka ,

Bata girki su sukeyi ita da larai

Ko ruwa taje tafasawa haka khadijan zata amshe

Ita ko larai wata ta tafasa

Ta Kai mata har daki

 

 

Wani

Abu da Imam yayi noticing

Shine

kullum fuskar khadija uwar gida

da idanunta a kumbure suke

Yayi tambayar duniya tace mishi kawai ciwon ido ne yake damunta .

A yadda suka hade kansu gidanshi kullum cikin xaman lafiya da lumana

Shiyasa ya kauda duk wasu negative thinking

Ya rungumi matanshi .

 

Shima a bangarenshi

yana ‘ko’kari Sosai wajen Kwatan ta adalci

Shi kan sa yasan yana namijin ‘ko’kari wajen ganin yayi adalci a tsakanin matan na sa

Duba da yadda yakeji game da ko wacce a cikin zuciyar sa

 

A yadda uwar gidan sa take kula da amaryar

Ya kamata ko Albarkacin haka ne

Ace taci

ta samu guri a zuciyar sa

Amman har gobe ya kasa bata

Ko da kaso daya a cikin Dari na zuciyar sa .

Saboda

Amaryar ta riga ta hade ta mamaye gaba daya kaso Dari din

Itace zuciyar tashi ma gaba daya .

 

Amman kuma dukda haka

sam baya Bari a gane

Yana iyakar bakin ‘ko’karin sa sa wajen boye hakan.

Abu daya yake yi wasu lokutan yake tonawa kam sa asiri ,

 

Kasancewar sa mutum me masifaffen kishi yasa yadda yake kishin amaryar su kansu su larai sun fahimci baya yi wa uwargidan ta sa .

 

Tsananin kishin sa ya San ya ko abokan shi ba ya Bari su gaisa da amaryar sa ,

In xa a fita ya dinga gyara mata xaman hijabinta yana rufe koina

Ko

Gaisuwar me gadi in ta amsa se ta hadu da fushin sa na en kwanaki .

Sa’banin

yanda yakeyiwa uwar gidan sa .

 

Shiyasa ko ba a fa’da ba ko ya boye su sun Riga sun sani

Ba tare da shi kanshi yasan sun gama gane wa ba ……

 

 

Cikin khadija amarya yana wata biyar Imam ya tattara gaba daya dukiyarshi ya damkawa babyn

Mace ko namiji be damu ba kawai de shi yasan ya gama yanke shawarar in aka Haifa mishi baby na farko a rayuwarshi to ya bada komai nashi .

Khadija har kuka ta dinga yi Akan ya janye wannan ‘kudiri nashi

Dan xe janyo mata bakin jini ,

Amman furr yaki

 

Daga karshe de ya tilasta ta ba yadda ta iya tayi shiru

Sannan

suka tsaya akan cewa

Maganar zata tsaya iyaka su biyu ,

In ta haihu shi zai ci gaba da kula da dukiyar har se yaron ko yarinyar ya Kai minxalin aure tukunna xa a damka mishi komai

 

A cewarshi a yanda ya fada mata

Saboda farin cikin Samun haihuwa ne Shiyasa ya shirya hakan a ‘dan shi na farko

Kuma ko da ace uwar gidan shi ce ta Haifa tou hakan zai yi .

Amman a cikin xuciyarshi

Har ga Allah yayi hakan ne saboda tsananin so da kaunar da yakeyiwa amaryar tashi ,

Saboda yanda yake sonta ya kwallafa rai a kanta haka yake ji da cikin jikinta kmr ranshi .

 

 

Wani sabon abu

daya fara lokacin da cikin yakai wata bakwai shine

Rashin godewa abunda su larai sukeyi ,

Duk irin ‘ko’karin da sukeyi da khadija se ya Dena gani ,

Ko maganinta ne Bata sha a kan lokaciba

Ranar se anga abun mamaki

Ya dinga masifa har washegari .

 

Kuma inde khadija tayi missing magana tou it’s either wachchar khadijan girki take mata ko wani Abu makamancin haka

 

Ganin rigima Tana shirin fara kunno Kai yasa ita da kanta amaryar ta kar’bi magungunan nata daga hannun abokiyar zaman nata Akan zata dinga sha dakanta

 

Dan ita kanta abubuwan da Imam din yakeyi Bata Jin da dinsu ,

Duba da yanda su khadijan suke namijin ‘ko’kari wajen Bata kulawa Amman Sam baya gani.

 

Abunda Imam yake yi Akan cikin nan zaka dauka akanshi aka fara haihuwa a duniya ,

Abu daya da uwar gidanshi tayi shine

Kauda Kai

Ta dauke kanta

Ta rufe idonta

Sam ta’ki yarda ta biye mishi,

Kuma

Sarai tasan da maganar yanda ya bawa ‘dan cikin khadija dukiyarshi kakaf Amman shima Bata ce ‘kala ba ,

Ita yanxu babbar damuwarta

Shine yanda har yanzu ta gagara daukar ciki,

Dan haka ta du’kufa addua

Ta bar Imam yanata kinibibin shi

‘Kar’kari in yace batayi wa khadija Abu ba

Ta bashi hakuri

A wuce wajen

Ko yana mita bata biyeshi .

 

A kwana a tashi ….

edd din khadija ya cika har ya wuce

Amman Sam

Bata jin ko alamun labour

Dan haka

Suka nufi asibiti .

 

suna xuwa a gwajin farko

aka fahimci

Babyn babu rai yama dade da mutuwa dan har kmr ya fara dagargajewa .

 

Sumewa Imam yayi a wajen da Jin wannan mummunan batu,

Dan xe iya cewa be taba shiga tashin hankali kwatankwacin wannan ba .

Har aka yi aikin aka gama aka cire babyn aka mata wankin ciki be farfado ba .

 

A tare sukayi jinya a asibiti

Dan ba kadan ba jinin shi ya hau

 

A bangaren khadija ma abun ba sauki

Dan bayan kwana biyu dayi mata wankin ciki

Yayarta ma ta rasu

ta sanadiyyar haihuwa data xo yi

Duk su biyun itada yaron ba Wanda yayi

Rai .

Shiyasa gabadaya khadijan ta kuma burkicewa

Badaban karfin Imani ba da tuni ta xauce

 

Imam ma yana nan

Kullum kuka

Seda mamanshi ,

Yahanasu ,

Ta tsawatar mishi ta nuna mishi ya rungumi ‘kaddara tukunna dakyar da taimakon Allah da addu’o’i ya dan dawo Dede .

Ko a gidan nashi ma

se da aka kwashe duk wasu belongings na babyn daya kashe uban kudi ya ware daki guda ya jibge

Tukunna

aka samu sa’ida

Dan haka xe shiga dakin ya rungume Kayan Yaron yayita uban kuka kmr wani karamin Yaro abun tausayi

Dama shi tun yana Yaro yanada masifar son yara

Shiyasa ya kwallafa Akan cikin jikin khadija masoyiyar shi , sai de kuma

‘Kaddara ta riga fata ………..

 

 

Bayan wata uku ,

Kmr ha’din Baki a lokaci daya duk su biyun suka samu ciki

 

Sede edd din uwar gidan ya fi na amarya

Ita zata fara haihuwa da sati biyu

Daganan amaryar ta haihu …

 

Murna wajen imam ba a magana

Amman kuma duk yanda yaso ‘boyewa

kowa ya San yafi yin farin ciki da cikin amarya .

 

Uwar gidan itama ciki gareta wannan Karon

Shiyasa aka ‘karo me aiki

me xuwa da tafiya

Suka hadu itada

Larai

Sukayi ta kula dasu

 

Kmr yadda Imam yayi wanchan Karon haka yayi wannan ma

Ya kwashe komai ya damkawa dan cikin khadija .

 

A nan ne kuwa yaga bacin ranta

Dan burkice mishi tayi tace bazai yiu ba

Ai itama yayar Tata ciki gareta .

 

Har kuka tayi mishi

Tace kar ya zama cikin Masu zalinci mana ,

Tunda take da khadija ba ta taba cutar da ita ba

Abunda takeyi mata ko yayar ta Allah yaji ‘kanta Bata yi mata

 

Taya xeyi mata haka

Ita kam babu ruwanta kuma in ya matsa se ta je ta samu su Daddy ta fadi musu

ba da ita xa ayi wannan zalincin ba ….

 

Yanayin yanda cikin khadija yayi tsini kmr wanchan Karon na farko

Yasan inshaaAllah namiji zata kuma haifa

Sa’banin

na uwar gidan sa daya bi jikin ta Sosai yasa tayi kiba

 

Shiyasa ya yanke shawara

Ya samu khadija ya lalla’bata

Akan ya fasa bada duka dukiyar

Instead ya rabata gida biyu

Sannan

Duk wadda ta haifi namiji a tsakanin su

Tou shi za a bawa

In kuma duk suka haifi maza tou se a rabata gida biyu a bawa kowa kashi daya

Kuma shi zai ci gaba da kula da ita ne

Har se Yaron ya kai eighteen years tukunna ze damka mishi abunshi

 

A wannan Karon ma

Yayi mata bayanin dalilin shi nayin hakan

Na cewa Yaro namiji kuma nafarko ya kamata a bashi support sosai

Sede ita khadija Sam Bata fahimci fa’idar yin hakan ba ,

Tun ba ma yadda ya ware ta ita kadai ita da take amarya ya gayawa ba

A ganinta kamata yayi ya hade su duk su biyun ya yi shawara dasu ,

In ma hakan ne decision dinshi tou ya gaya musu a tare .

 

Ganin da ta yi ranshi ya soma baci da tirjiyar ta ne ya sanya kawai ta hakura ta rabu dashi ,

Amman har ga Allah a chan kasan ranta addua takeyi Allah ubangiji ya sa uwargidan ta haifi namiji.

Sarai tasan tana fahimtar wasu abubuwa na bambanci da Imam yake nunawa a tsakanin su

Amman dukda haka ta kauda Kai kamar bata san me ke faruwa ba ,amma fa tasan ko zuciyar gwal gareta muddin akace sun haihu tare in ita ta haifi namiji aka bata rabin dukiya

Tou fa

Zaman lafiyar ta da abokiyar zaman na ta Wanda take matukar Jin dadi xe iya tabuwa ,

Ita kuma Bata son abunda xe hada ta da abokiyar zaman nata

Dan ta yi mata abunda baxata taba mantawa ba

Yanda ta kula da ita da ‘dan cikin ta a kwanakin baya

Ba ko wa ce zata iya yin hakan ba ,

Ko dan uwanka na jini iyakar abunda ze yi maka kenan.

 

A bangaren Imam Kuwa

Yasan yanason khadija da cikin jikin ta fiye da komai a rayuwarshi

Fiye ma da rayuwar tashi ,

Amma babban dalilin shi daya sanya yake son bawa babyn ta rabin dukiyar sa

Shine

Be san gawar fari ba

Be San lokacin da zai mutu ba ,

babban tashin hankalin shi shine ,rayuwar da khadijan ka iya shiga ita da babyn su in baya raye

Yasan su maman shi zasuyi kokari Amman ba kamar yadda shi xeyi in yana raye ba .

Uwar gidan shi yasan tanada gata er Masu kudi ce ,

khadijan shi itace abar tausaya wa

Gata ita ba karatu ba .

Shiyasa yake kokari yake trying anything possible yaga ya Gina ta ta xama standard

Tunda ba a San gawar fari ba

…………

 

 

 

A kwana a tashi ..akace ba wuya a wajen Allah

 

domin Watan haihuwa ya Kama ,

Har satin edd din uwargida ya shiga .

 

Sam abubuwa basu tafi a yadda Imam ya tsara

Ya kuma yi xato

ba ,Domin amaryar mace ta Haifa

Uwar gidan shi kuma ta haifi namiji .

Wan da

Sam be yi zaton hakan

Ko tsammani ba .

 

A ranar da suka haihun ma baya nan

Yayi tafiya abuja ,

Kafin ya tafi sai da ya kai amaryar

aka tabbatar mishi se nan da two weeks edd dinta xe cika

A Yayin da ita kuma uwar gidan taketa fama da labour tun wayewar gari,

Dan haka ya bar musu duk abun bukata

Yace xasu dan fita shi da khadija su siyo ragowar Kayan baby

Da ga siyayyar ne suka biya asibitin,

Yaji dadi kuwa

Da Jin bayanin doctor

Wanda yake ce mishi

Se nan da sati biyu xa a yi expecting haihuwar Tata .

Saboda shi sati daya kawai xaiyi ya dawo

Kuma yafi son amaryar tashi ta haihu yana kusa da ita .

Dan haka ya maida ita gida

Cike da farin ciki ,

Yayin da ita kuma ta ke ta faman kumbure kumbure Tana mishi wa ‘a zin ya dinga adalci.

 

Cike da fatan alkhairi

Da kuma tsananin kewar khadija ya tafi ,

Tare da fatan yana dawowa ita ma inshaaAllah zata haifa mishi sanyin idaniyar shi .

 

Sede kuma

Yana tafiya itama amaryar ta fara Samun contractions ,

Dan haka akayi asibiti dasu duk su biyun.

 

Suna zuwa akace

Sai de ayi wa amaryar cs dan baxata iya haihuwa da kanta ba ,

 

Ba tare da Bata lokaci ba

Su Daddy da Mama suke cike takardar amincewa aka shige dakin tiyata da ita

 

Itace kuwa ta fara haihuwa

Aka ciro mata babynta mace katuwa

Tubarkallah ,

larai ce ta mikowa su mommy da suke a waje

Yarinyar

Wadda sukayi tsananin farin ciki da gani ,

Basu gama murna ba

Likitan ya fito musu da kyakkyawan Yaro me tsananin kama da uban shi

Dan wajen khadija uwar gida .

 

Kowa in ya kalleshi se ya ce MashaaAllah

Saboda tsananin kyawun Yaron ……

 

A ranar Imam ya biyo flight ya dawo

A hargitse

Da ‘doki

…..

 

Tun a Chan ya gama yanke shawarar fasa bawa dan gidan uwar gidan ta sa Rabin dukiyar sa

Da tunanin neman wata mafitar tunda ba kowa ya san da zancen ba dama …..

 

 

yana xuwa daya dauki yaron yaji duk duniya ba abunda yakeso sama dashi

Dan har kuka yayi tsabar farin ciki

 

Wata irin soyayya Allah ya dasa mishi ta Yaron

Me tsayawa a rai ,

yana son itama dayar yarinyar da aka Haifa mishi amman ba kmr Yaron Ba

Domin wannan Yaron is very very special and dear to him

Wani irin kalar so kauna da tausayi na Yaron yake ji suna ratsa dukkan ‘bargo jini da tsokar dake jikin shi .

…..

 

Beyi tunanin su maman sa sunsan maganar alkawarin daya dauka na raba dukiyar shi biyu ba ,

Seda yaji tayi mishi maganar.

 

Ashe wannan Karon ma uwar gidan ta sani kuma ta gaya mata

Tun farkon sanin xancen

Da tayi ,

Sarai maman nashi ta fahimci son Kai yake shirin yi

Ta kuma ji haushi

Duba da yadda ya yanke shawarar a cikin amaryar na farko ba tare da ya tuntubi kowa ba ,

Shiyasa yanzun tace wa uwargidan ta yi shiru ta barta dashi xatayi Maganin shi .

 

Yaso ya Zille ,

Tabbas yanason ‘danshi fiye da komai

Amman kuma still yana duba khadijan shi

Yaso ace ita ta Haifa mishi wannan babyn

da tuni ya bayar willingly without thinking twice.

 

 

Ganin khadijan nashi da maman shi

Sun fara ganin kmr dama ba adalci yaso yi ba

yasa kawai ya hakura ya bayar da rabin dukiyar tashi a danshi

Ba dan yaso

…………

 

 

Wani ikon Allah

 

Tun daga wannan lokacin abubuwa suka sauya ,

Gabadaya soyayyar Imam ga Khadija tayi rauni ,

tama Lura kmr haushinta yake ji

dan

Ko kusa dashi bayaso taje .

 

Itama uwar gidan nashi ba wani sake mata yakeyi ba ,

Amman de ya fi tsanar amaryar akanta .

 

Inde kaga yana dariya tou ya dauki babies dinshi ne

Amman baya ga haka ba shi da wata walwala .

 

Tashi daya

ya dawo wani iri mur’da’d’den mutum abun tsoro ma

Dan har ga Allah itakam amaryar zuwa yanzu ya fara bata tsoro .

Ga

Hantara kyara da tsana wadda yake gwada mata kiri kiri.

Ga wani irin masifaffen kishinta da yakeyi ,Ko dan yasan ya dena Bata attention maybe Shiyasa yake tunanin zata kula wani a waje .

 

Gaba daya tashi daya duniya tayi mata zafi

Da ga khadija se larai ne Kawai take dasu ta ke dan hira dasu ta ji sauki

 

Se ko er jinjirar yarinyar ta

Wadda ta Lura

‘Kiyayyar da Imam din yake mata ta fara shafar yarinyar da Bata ji ba Bata gani ba .

Kafin ya ‘dauketa sau daya

Ya dauki dan uwanta sau ashirin .

Bata da yanda zatayi

Tunda bama tasan laifinta gareshiba

Ballantana ta gyara ,

Shiyasa ta dukufa addu’a

Take kuma ‘ko’kari wajen holding kanta together ,

Amman fa ko ba ka santa tun farko ba

Kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin tsananin tashin hankali .

 

 

………..

 

 

 

Bayan shekaru talatin ….

 

 

 

‎Open this link to join my WhatsApp Group:

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment