Aameenat Bazawara Hausa Novel Complete
AAMEENAT (Bazawara)
Littafin Haɗaka ne
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER’S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER’S
PAGE 1
Bismillahirrahmanirrahim
Kaiwa Waccan Tsohuwar Bazawarar Abincinta, Fati ta faɗa Gami da gyatsine Fuska, Umaima ta ƙyalƙyale da dariya sannan ta ɗauki ɗan Abincin ta nufi Ɗaki da shi.
Aameenat Ta na zaune ta zuba Tagumi ta na jiyo su amma ba ta da bakin cewa ƙala.
A can gefe Umaima ta ajiye Abincin Sannan ta ce “Ga shi nan in za ki ci”
rausayar da kai tayi sannan ta taso zata ɗauka seda tazo gaf da Abincin Umaima tayi maza ta ɗauke tana cewa “Ahayye ƙwalelanki ƙaramar bazawara”
“da kin zauna a gidan miji ai da kinci” Fati faɗa tana ya mutse fuska, dariya suka kwashe da ita suka tafa.
hawayen da suka cika mata Ido ne suka samu damar gangarowa fuskarta wani kallo Umaima ta watsa mata sannan taja Fati suka fice suna waƙe waƙen su na fitsara .
Doctor Nawal Hausa Novel Complete
wani sabon kuka ta fashe dashi tana cewa “kacuceni bazan taɓa yafe maka ba azzalumi”
ganin kukan baze amfane ta ba yasa ta tashi ta nufi ɗakin wanka ruwa ta watsa ta fito ta shirya cikin doguwar riga Abaya yaluwa taji duwatsu masu sheƙi da walwali tayi kyau sosai madubi ta kalla wasu hawaye masu zafi suka fara gangarowa da sauri ta kauda kai tana tauna laɓɓan ta kafin ta tashi ta nufi ƙofa Mama ce tace ” zawar zawar ce yau tafito kenan” “haba kekuwa Mama ba dole a fita neman bazawari ba”
dariya Su ka sa Kafin Mama ta ce “Allah ya raka taki gona” Aaminat ta murmusa ba tare da ta yi magana ba ta yi hanyar fita, a ƙofar gida ta coge ta na leƙawa, kasancewar yamma ce ga iska na kaɗawa a hankali a hankali ya sa yanayin ya yi mata daɗi sosai, yaran layin da su ke Ƙwallo ta ke kalla, a zahiri idanunta su na kansu amma a cikin ranta tunanin Yau da Goben Rayuwarta kawai ta ke yi, “Wace irin Rayuwa ce Ƴan Adam su ka ɗorawa kansu??, ba sa tunanin ita Ƙaddara ba kai kake tsarawa kanka ita ba??” tunanin da ya fi yi mata yawo kenan, ta na cikin tunanin ta ji saukar Ƙwallon a Fuskarta, ta yi baya cikin sauri gami da dafe fuskar tata, hawayen azaba ne su ka fara tseren zubowa kan kumatunta, yaran su ka yo yuuu akanta wasu suna “Don Allah ki yi haƙuri” wasu kuma su na cewa “Wallahi Walid ne ya jefo miki ita” Goge hawayen ta yi ta ɗago fuskarta ta na kallonsu, murmushi wanda ke ƙara nuna zallar haƙurinta ta yi kafin ta ce “Na haƙura” Sauran su ka Ɗauki Ball ɗin su ka koma wasa. Abdulkareem ne ya tsaya Ya na Kallonta cike da tausayawa, “Yaya Aamimat!” ya kira sunanta cikin sigar Tambaya, cikin sauri ta zuba masa idanu, sai a lokacin ma ta san ya na gurin domin kuwa a kowacce daƙiƙa tunani ne tsarin rayuwarta, “Abdulkareem sun ci gaba da wasan ba kai” ta faɗa ta na masa ɗan murmushi wanda ya ke bala’in sumar da Zinariyar Zuciyarsa “YaYa Aameenat ban ji daɗi ba, wallahi dan dai Walid Ƙaninki ne kuma ba’a shiga faɗan dangi banda haka da sai kinga yadda zan yi da shi, don ni da a raina ki gwara a mutu har liman, ban damu da rashin kunyar Yayyensa Ƴan Matan nan ba” Ita har ga Allah ya takura mata, don kuwa ganin tsaurin idonsa ta ke yi ta yadda ya ke iya zama ya na tsara mata kalamai kamar irin Namiji Ɗan 35-37 Years ɗinnan, ashe nan Bai fi 20 Years zuwa 21 22 ba, yadda ya ke iya jefa ƙwayar idonsa a cikin nata ya fi komai bata takaici, shi don bai sani bane amma ba ƙaunar ganinsa take ba. Jin ta yi shiru ya sa shi yin dariya ya ce “YaYa Aaminat haƙurinki ya na bala’in Taɓa Zuciyata!” ya ƙarasa maganar gami da ɗora ɗan yatsansa akan Ƙirjinsa saitin Zuciyar tashi, haɗa hannunta ta yi guri ɗaya alamar roƙo, cikin sassanyar muryarta ta ce “Abdulkareem don Allah ka koma ku ci gaba da ƙwallonku Me yasa sai ka dame ni ne???” “Ba na gajiya da kallonki ne” lokacin da ya yi maganar ya juya mata baya har ya ɗanyi tazara da inda take, ta saki baki ta na kallon bayansa, ɗan ƙaramin tsaki ta ja kafin ta juya ta koma ciki aranta ta na cewa “Ciki ba daɗi waje ba daɗi Abdulkareem ka fiya shiga rayuwata, Mara kunya da tsayayyun idanunka”
Ta na shiga Mama dake shara ta ce “A’ah Zawar me mu ka samu ne naga kin shigo baki na motsi??, ko mun yi sabon kamu ne??” Girgiza kai ta yi alamar “a’a” ta ratse ta shiga ɗaki, Mayafinta ta fizge ta jefar sannan ta shiga gyara ɗakin, daga fitarta har Su Fati sun yi abinda su ka saba, sun yi wa ɗakin batsa batsa, ta na aikin ta na Tunanin Kamal wanda ta kasa mantawa dashi, zuwa yanzu ita kanta shaida ce WATA TSIYAR A Jinin Ɗan Adam take, Ba ta taɓa tunanin haka za ta gindaya tsakanin Rayuwarta da Kamal ba.
hawayene suka fara sunturi a kuncinta sosai take sheshshekar kuka tana girgiza kai, jiri ne ya fara ɗibarta tayi saurin dafa bango ta na ambaton Allah, a daddafe ta iya ƙarasa sharar dan ta zamar mata dole, fita tayi tsakar gidan ta fara haɗa kwanuka domin wanke su ba tare da ɓata lokaci ba ta kammala wanke wanken ta shiga ɗaki ta saki labule domin bata son yin kaciɓus da samarin gidan dan kuwa basason ganinta guri tanema ta zauna tana jen carbi.
dariyar da taji ce tasa ta ɗagowa Umaima ce da ƙawarsu Nafisa da Fati suke mata dariya
“Oni ƴasu dama haka zawarci kebsa bawa ladabi”? Nafisa faɗa tana riƙe haɓarta wani murmushi Fati tayi sannan tace “to zawara se a bawa ƴan mata waje ko, ta baro gidan miji ta zo ta dami mutane”
bata musa ba ta tashi ta nufi ɗakin Umma, duk da ta san balalle ta barta ta shigar mata ɗaki ba kai a ƙasa ta ƙarasa kofar ɗakin, Umma ta watso mata harara gami da cewa “Sannu Aameena karki shigo min ɗaki, ki ɓata min, ɗakin naku aikin me yake yi??” “Su Fati ne a ciki” Umma ta ce “Ai ba ƙarfinki su ka fi ba, ni dai ba a ɗakina ba, yanzu na gama share shi” jiki a sanyaye taja ƙafafuwan ta tanufi kicin, karo taci da Umar ya shigo ta sunkuya tace “Ya Umar ina wuni” be ko kalleta ba ya wuce abin shi hakan yayi mata ciwo sosai Amma inda sabo ta saba haka ta tura ƙofar kicin ɗin ta shiga ta zauna tare da saukar da wata ajiyar zuciya yunwa takeji gashi babu da mar dafa abinci domin in mutan gidan suka sani baza taji da daɗi ba. rabonta da abinci tun karin safe ta galabaita sosai dankuwa duhu duhu take gani..
Rai a ɓace ya shiga gidan bebi ta kan kowa ba ya nufi ɗakin su “Abdulkareem”! tafaɗa cikin kwantar da kai batare da ya juyo ba ya tsaya cak bece ko mai ba a hankali ta ƙarasa inda yake ta ɗan shafi gefen fuskar shi tare da hura mai iska da bakin ta batare da ya ɗagoba yace “Ummi ina jin bacci” “maza kaje in katashi ka sanar min da wuri don rabonka da abinci ka daɗe, ka fi ganewa tsalle tsalle” be ce komai ba ya cigaba da tafiya murmushi tayi tare da bin ɗan na ta da kallo tana sa musu Albarka tare da addu’ar Allah ya ƙara haɗa mata kan su mazan da mata ya tsaresu daga sharin magauta.
ɗakin wanka ya shiga yawatsa ruwa ya na fitowa ya nufi firji gorar ruwa ya ɗauka ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya gami da dafa ƙirjinsa….
CommenT
Shere FisabilillaH
© INDO CE & AUTAR JARUMAI