Littafan Hausa Novels

Doctor Nawal Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Doctor Nawal Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DOCTOR NAWAL

 

*Alƙalamin*

 

 

*Zainab Muhammad (Indian Girl ce)*

 

 

 

*Wannan littafi na kuɗi ne dan Allah dan annabi sisters da zarar free page ya ƙare ki biya ki karanta*

 

*Ba tsada sauƙi na Allah rangwami na ma’aiki naira 500 kacal ne ba bu tsada ƴan uwa*

Payment

9042626462

Zainab Abubakar Umar

Opay bank

Shaidar biya ta wannan number 08143907733

 

*Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeni ta wannan number 08143907733 nagode*

 

FREE PAGES

 

1-2

__________________________________________ Santala santalan fararen ƙafafunta waɗan da suka sha jan lalle da baƙi wanda yai matuƙar daɗa ƙawata ƙafar tata, a hankali ta ziro gaba ɗayan jikinta ta fito daga motar.

 

Masha Allah tsarki ya tabbata ga ubangijin halittun wanda ya halicce mutum da aljan mala’iku dabbobi da tsirrai sammai da ƙassai, ya halicce wannan kyakykyawar halittar mai matuƙar kyau kwarjini da haiba.

 

Fara ce doguwa mai ɗan jiki, fuskarta ta haɗu ta tsaru tamkar itace wadda ta zauna ta tsara kyan da kanta.

 

Bakinta ɗan ƙarami idanunta dara dara masu haske tamkar madara hancinta dogone mai tsine shape ɗin sa mai matuƙar kyau,girarta zara zara mai kuan shape gishinta lulluɓe da gashi baƙi mai santsi da sheƙi wanda hakan ya tabbatar da yawan gashin dake kanta.

Yawon Ta Zubar Hausa Novel Complete

Shape ɗin jikinta irin shape ɗin nan ne na coca cola shape,dukiyar fulaninta kuwa masha Allah sun yi dai dai da tsarin halittar jikinta.

 

Sanye take take cikin riga da sket na atamfa wanda su kai matuƙar yi mata kyau suka amshi jikinta ta ɗora wata blue ɗin riga irin ta ma’aikatan asibiti sannan ta ɗora mayafi ta yane kanta,hannunta da ƙafafunta sun sha jan lalle da baƙi wanda yai matuƙar hi mata kyau.

 

Doctor Nawal kenan shahararriyar ma’aikaciyar asibiti ta ɓangarori biyu *Medical doctor and surgeos* ma’ana kwararriyar likita ta fannin lafiya da bada magani kowane iri,sannan kuma *Psychiatrists* kwararriya kuma a fannin marasa lafiya masu fama da taɓin hankali.

 

Kai tsaye cikin asibitin ta nufa mai suna *Arab helping hospital* hannunta ɗauke da jaka wadda muhimman abubuwanta ke ciki, office ɗinta ta nufa wanda a ƙofar shiga aka rubuta *special doctor* wato likita ta musamman.

 

Key ta sa ta buɗe ta shiga, tsaf office ɗin yake a gyare cike da tsafta.

 

Kai tsaye ta nufi kujerar da aka tana da dan zamanta ta zauna tare da ɗora jakarta akan table ɗin gaban kujerar, takardun kan table ɗin ta shiga ɗaɗɗagawa tana dubawa can ta ɗauko wani file ta shiga karantawa.

 

File ɗin wata yarinya ce ƴar kimanin shekaru 10 wadda aka kawota asibitin sanadiyar fyaɗe da wani wanda ba a san shi yai mata da kyar da taimakon Doctor Nawal aka karɓeta domin bata taimakon gaggawa saboda yai mata illa sosai.

 

“Ya ilahi Allahumma ajirni fil musibat, ya ubangijin mu ka bamu ɗauki game da waɗannan mutane ɓata gari”

 

Ta furta da zazzaƙar muryarta cike da damuwa.

 

Ɗaukan file ɗin tai tare da yin hanyar fita daga office ɗin,tsayawa tayi taiwa ƙofar key sannan ta juya da zummar barin wajan.

 

“Doctor wajanki fa na zo kuma gashi nagama kin fito daga office ɗin”

 

Taji an faɗa daga bayanta,a hankali ta juya ga mai maganar.

 

Doctor Fauzan kenan kwararran likita a fannin *Ophthalmologists* kwararran likita a fannin ido.

 

Doctor Nawal tai ɗan murmushi sannan.

 

Tace”To Doctor Fauzan gashi kuma zan shiga duba patiens ɗina ne”

 

Doctor Fauzan ya yarfar da hannu baya.

 

Yace”Ok ba damuwa idan kin dawo zan dawo”

 

Doctor Nawal Tace”Ok no problem bari naje”

 

Doctor Fauzan Yace”A dawo lafiya”

 

Ta amsa da Allah yasa sannan ta shige ta tafi.

 

Ɗakin da aka kwantar da majinyaciyar da akaiwa fyaɗen ta shiga,zaune ta sami mahaifiyar yarinyar a kusa da ita tana bata abinci a baki da cokali.

 

Sallama Doctor Nawal tai ta shiga fuskarta ɗauke da fara’a ganin yarinyar zaune har tana cin abinci.

 

Amsa sallamar mahaifiyar yarinyar tayi tanawa Doctor Nawal murmushi.

 

Ƙarasowa Doctor Nawal tayi ta zauna bakin gadon sannan suka gaisa da mahaifiyar yarinyar.

 

Doctor Nawal tana murmushi.

 

Tace”Amma naji daɗi dana sameki a haka Allah ya ƙara sauƙi”

 

Mahaifiyar yarinyar ta amsa da ameen ita kuma yarinyar taiwa Doctor Nawal murmushi.

 

Mahaifiyar yarinyar Tace”Doctor mun gode sosai da taimakon mu da ki kai, kin ceto rayuwar ƴata nagode sosai kema Allah yai miki me kyau a rayuwarki”

 

Sosa goshi Doctor Nawal tayi kafin.

 

Tace”Ba komai ai aikin mune taimakawa wanda yake cikin wani hali da bashi taimakon gaggawa kuma wallahi yarinyar ta ban tsoro dan tasha wuya sosai ,addu’ar ki kuma nagode sosai da ita”

 

Babar yarinyar Tace”Ai nice da godiya,eh wallahi ai ta wahala”

 

Doctor Nawal tai murmushi sannan ta ƙara yiwa yarinyar sannu ta fice bayan ta sake duba lafiyar yarinyar.

 

Haka tai ta shiga ɗakunan majinyatan na asibitin tana duba lafiyar su, a gajiye ta koma office ɗinta tana ɗan runtse ido ga yunwa da take ji domin ba tai break fast ba ta fito dan ta matsu ta zo taga patiens ɗinta dan yarinyar ta bata tsoro.

 

Tana hanyar komawa office ɗinta ta haɗu da Doctor Fauzan dan haka suka rankaya gaba ɗaya zuwa office ɗin nata, suna zuwa ta buɗe suka shiga ta zauna akan kujerarta shima ya zauna.

 

Lumshe kyawawan idanunta tayi kafin.

 

Tace”Yawwa Doctor ina sauraranka kace kana son za muyi magana”

 

Duk idanunta a rufe take maganar.

 

Sauke gwauran numfashi Doctor Fauzan ya yi kafin ya fara mana.

 

“Doctor na san cewa yanzu baki da wani buri sai wanda ba a rasa ba tunda har kika zama babbar likita kamar haka”

 

A hankali Doctor Nawal ta buɗe idanuwanta ta sauke su akan Doctor Fauzan.

 

Tace”Hakane Doctor, amma mene ya sa ka faɗi haka?”

 

Murmushi Doctor Fauzan ya yi sannan.

 

Yace”Doctor maganar gaskiya sonki nake kuma da aure”

 

Ɗan zaro idanu Doctor Nawal tayi kafin.

 

Tace”Amma Doctor nagode da soyayyarka gare ni sai dai gaskiya ni yanzu ba aure zan yi ba”

 

“Amma mene ya sa kika ce ba zaki aure yanzu ba?”

 

Doctor Fauzan ya tambaya.

 

Doctor Nawal ta matsa ƴanyatsunta na hannu suka bada sautin ƙasss.

 

Tace”Zan yi aure Doctor amma ba yanzu ba kuma ba a irin wannan lokacin ba domin ni gaskiya a yanzu babu maganar aure kwata kwata a information life ɗina”

 

Jinjina kai Doctor Nawal ya yi.

 

Yace”Na ji kuma na fahimce ki kuma zan jira ki zuwa duk lokacin da kika shirya”

 

“A’a Doctor karka bar sona yai girman da ba zai ciru ba a zuciyarka saboda ni ba zan yi soyayya ba a halin yanzu kuma kar nan gaba aje a samu matsala”

 

Doctor Fauzan Yace”Insha Allahu ba zan gaza da soyayyarki ba zan cigaba da dakonta har zuwa san da zaki amsheni”

 

“Doctor ba zaka gane bane, abinda nake so ka sani shine ubangiji shine ya tsara mana rayuwa da abinda zai faru da rayuwar tamu sannan a ko da yaushe fa ƙaddara tana iya sauyawa”

 

Doctor Nawal ta faɗa cikin sanyinta.

 

Doctor Fauzan ya sauke numfashi mai zafi sannan.

 

Yace”Insha Allahu ƙaddara ba zata sauya ba,kuma zan jira ki zuwa lokacin da duk kika shirya fara soyayya da yin aure”

 

Doctor Nawal ta dafe kanta a ranta tana furta oh my god,a zahiri kuma murmushi tayi wanda iyakar sa fuskarta.

 

Tace”Shikenan Doctor Allah ya bada juriyar yin hakan”

 

Doctor Fauzan ya amsa da ameen sannan ya miƴe yai mata sallama tare da fatan alkairi ya fice ya koma office ɗin sa.

 

Wata doguwar ajiyar zuciya Doctor Nawal ta saki lokacin da Doctor Fauzan ya fice.

 

“Oh ni ɗiyar Daddyn mu,mutum ana nuna masa gaskiya yana take ta”

 

Ta faɗi haka a zahiri.

 

Jakarta ta ɗauka dan ta wuce gida dan yunwa take ji kuma ta gama aikin da ya kamata tayi yau a asibitin.

 

Sai da ta kulle office ɗin sannan tai hanyar fita domin isa wajan motarta,tunda ta fito suke gaisawa da sauran likitoci da nurses harta isa wajan motarta ta shiga.

 

Tayarwa tayi sannan tai reverse ta fice daga asibitin cike da kwarewa a tuƙi, tuƙi take a nutse har ta isa gida.

 

Horn taiwa mai gadi ya buɗe mata ta shiga sannan ta sake nufar wani get ɗin tai horn wani mai gadin ya buɗe mata ta shiga, paking space ta nufa tai paking sannan ta ɗauki jakarta ta nufi cikin gidan.

 

Falo ne babba wanda aka ƙawata da kujeru masu matuƙar kyau sai tv plasma babba dake manne a jikin bango sannan sauran tarkace na falo sai dinning area wajan da ake cin abinci sai ƙofofi masu kyau na glass.

 

Kai tsaye ƙofar tsakiya ta nufa nan tabi wasu matattakalu masu kyau da ƙayatawa bayan ta shanye su ta tura ƙofar glass ɗin ta shiga, wani falon ne wanda ya fi wan can haɗuwa yai kyau matuƙa ya ƙayatu da kayan alatu na more rayuwa.

 

Tana shiga folon ba kowa nan ta shiga kwalla kira cikin muryar shagwaɓa.

 

“Ammi! Ammi!! Ammi!!! na dawo kina ina”

 

Ammi ta fito daga ɗakinta tana kallon Doctor Nawal.

 

Tace”Ke dai Nawal wallahi Allah ya shiryeki yarinya kin girma amma sai kace ƙaramar yarinya?”

 

Doctor Nawal ta daɗa shagwaɓe fuska kafin ta tawo tai hug ɗin Ammin tana.

 

Cewa”Kai Ammi aini ganina nake tamkar Jawad da Juwaida har ma na fi su in dai a gabanki ne”

 

Ammi ta ɗan ture ta daga jikinta.

 

Tace”To Allah ya shiryeki yaran ƴan shekara 3 kice kin fi su to Allah ya shirya ki ya yaye miki”

 

“Ameen Ammina, Ammi yunwa fa ƴar Babynki take ji”

 

Doctor Nawal ta faɗa tana shafa lafaffan cikinta wanda tamkar bata taɓa zuba masa abinci ba.

 

Ammi ta ɗan harareta sannan.

 

Tace”To ai ke kika jawa kanki yunwa tunda nayi nayi ki tsaya kiyi break fast ko ki tafi dashi amma kika ce ke tafiya zaki kina da patiens”

 

Doctor Nawal ta langwaɓar da kai kalar na abin tausayi kafin.

 

Tace”Sorry Ammi wallahi yarinyar ce taban tausayi sannan ta ban tsoro rapine ɗinta aka yi akai mata illa sosai da kyar aka ceto rayuwarta”

 

Ammi cikin tausayi da jin labarin yarinyar da Nawal ke bata.

 

Tace”Allah sarki, Allah ya saka mata ai yanzu abinda yai yawa a gari kenan sai dai addu’a kawai”

 

Doctor Nawal Tace”Ameen Ammi amma duk da addu’a da za ai ai ya kamata a dinga hukunta duk wanda ya aikata”

 

“Hakane kam domin da za su ga ana santencing ɗin su da sun dena”

 

Ammi ta faɗa.

 

Doctor Nawal Tace”Hakan shine dama ya kamata, Amma yanzu dai Ammi a taimakwa da Nawal da abinci idan taci sai a cigaba da maganar”

 

Murmushi Ammi tayi halayar Nawal ɗin na barkonci yana burgeta ga wasa da dariya ita dai ai nishaɗi.

 

Ammi Tace”To ai naga kin manta da abincin shiyasa nima na manta”

 

Nawal tai raurau da ido kamar za tai kuka cike da shagwaɓa.

 

Tace”Ah haba Ammi ni ba mantawa nai ba kin san ni dai wani lokacin akwai zuba, amma yanzu a taimaki ɗiyar Daddy”

 

“Ke ko Allah ya shiryeki”

 

Ammi ta faɗa tana dariya sannan ta nufi kitchen,kitchen ɗin yai matuƙar haɗuwa sosai gashi cike da kaya.

 

Plate Ammi ta ɗauka ta zuba mata jallop ɗin macroni wadda taji kayan kifi da kayan haɗi sai ƙamshi take, sannan ta ɗauki spoon ta ɗora ta fice.

 

Akan dinnig ta ɗora sannan tai kiran Nawal da ta ƙaraso wajan dinning ɗin,bayan ta zo ta zauna nan Ammi ta haɗa mata tea ta saka sugar kawai domin Nawal bata shan shayi da madara sannan ta zuba mata soya soyen su kwai da dankali.

 

Nan Doctor Nawal tai bismillah ta fara ci a hankali,duk ikirarin yunwar da Nawal take bata da ci domin spoon 5 taiwa macronin sannan ta ɗanci soya soyen ta shanye tea ɗin.

 

Hamdala taiwa ubangijin daya halicceta sannan ta miƴe ta shige ɗakinta da Ammi itama tunda ta gama seving ɗinta ta shige ɗakin yara domin ta linke masu kaya da aka kawo daga wanki.

 

Ɗakin nata tsaf yake a gyare tamkar ba a taɓa shiga anyi wani abu a ciki ba,komai na ɗakin pink and milk color e wanda yai matuƙar daɗawa ɗakin kyau.

 

Kai tsaye jakarta ta ajiye sannan ta rage kayan jikinta ta ɗaura towel ta shiga toilet dan ta watsa ruwa,toilet ɗin shima a gyare yake sai ƙamshi yake gaban mirron dake banɗakin mayuka da sabulai da turaruka na wanka da wanke kai masu ƙamshi da tsada.

 

Bayan kamar 10 minute ta fito ɗaure da towel hannunta kuma wani tana tsane jikinta da gashin kanta daya zuba a kyakykyawan gadon bayanta har zuwa wajan booty ɗinta.

 

Kai tsaye wajan wardrobe ta nufa ta ɗauko wata Yellow ɗin doguwar riga ta sanya sanna ta yane kanta da ɗankwali rigar,rigar ta matuƙar yi mata kyau abinka da farar mace kuma kyakykyawa.

 

Wayarta ta ɗauka a jakarta sannan ta fice zuwa ɗakin Ammi dan ta san yanzu ta gama shirya kayan yaran,zaune ta sami Ammi bakin gado da waya a hannunta alamar waya za tai.

 

“Ammi bari naje ɓangaran granny”

 

Doctor Nawal ta faɗa tana kallon Ammi.

 

Ammi Tace”A dawo lafiya a gaisheta”

 

Doctor Nawal ta amsa sannan ta fice,bayan ta bar ɓangaran su ta nufi ɓangaran granny wato kakar su.

 

Tana cikin tafiya wayarta ta shiga rings ta duba dan ganin mai kiran *Sis Leema* akan screen ɗin wayar,murmushi Doctor Nawal tayi har sis ɗin tata ta ƙosa ganin bata ganta ɓangaran granny ɗin ba sannan ta ɗaga wayar…

 

 

 

*Comments and Sharhi*

 

*Shares saboda girman Allah

 

DOCTOR NAWAL

 

*Alƙalamin*

 

 

*Zainab Muhammad (Indian Girl)*

 

https://www.facebook.com/103637491942644/

 

*Wannan littafi na kuɗi ne dan Allah dan annabi sisters da zarar free page ya ƙare ki biya ki karanta*

 

*Ba tsada sauƴi na Allah rangwami na ma’aiki naira 300 kacal ne ba bu tsada ƴan uwa😀😀*

 

Payment

9042626462

Zainab Abubakar Umar

Opay bank

Shaidar biya ta wannan number 08143907733

 

*Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeni ta wannan number 08143907733 nagode*

 

 

 

FREE PAGES

 

3-4

 

__________________________________________ Daga can ɓangaran Leema ta fara magana.

 

“Sis Doctor wai yau ina kika shige ne ko baki daqo daga asibitin ba?”

 

Dake haka suke ce mata sis Doctor ko suce sis Doctor Nawal.

 

Murmushi Doctor Nawal tayi wanda sai da dimples ɗinta suka loɓa kyanta ya sake fitowa.

 

Ta ce”Wallahi na dawo gama ninan na nufo ɓangaran Granny ɗin”

 

Tana jiyo shewar Leema domin su na matuƙar son su zauna da ita saboda labaran ban dari da sa su nishaɗi da take,kafin kuma Leeman.

 

Ta ce”Yawwa mutuniyar sai kin ƙaraso”

 

Doctor Nawal ta amsa da to sannan suka kashe waya.

 

Doctor Nawal tana ƙarasawa ɓangaran Granny tai knock da sauri Leema ta miƴe domin ta san ba zai wuce Doctorn gidan su ba.

 

Buɗe mata tayi Doctor Nawal ta shiga fuskarta ɗauke da murmushi.

 

Duk ƴan matan gidan suna zazzaune wasu a ƙasan kafet wasu a kan kujera.

 

Yusra,Feena,Zee da Leema,duk kyawawa ne dake hakan familyn suke amma ko ƴɗanyatsar ƙafar Doctor Nawal basu kama ba a kyau.

 

“Allah ya biya Doctor ɗin mu”

 

Ƴan mata suka faɗa cike da farin cikin ganin Doctor Nawal.

 

Itama Doctor Nawal cike da farin ciki ta ƴarasa inda suke tana.

 

Ce wa”Allah ya biya ladies ɗin familyn Arab”

 

Suka sheƴe da dariya sannan Feena.

 

Ta ce”Ameen ameen Doctor familyn Arab”

 

Nan ma dariyar su kai cike da nishaɗi.

 

Yusra ta dubi Doctor Nawal.

 

Ta ce”Doctorn mu yau da wane labari aka zo mana?”

 

Zee Ta ce”Eh nima abinda nake jira na tambayeta kenan”

 

Leema Ta ce”Ni duk na fiku ƙosawa yasin”

 

Doctor Nawal ta gyara zama dake a ƙasan kafet ta zauna,sannan ta canza fuska zuwa ta tausayi.

 

Zee ganin yana yin Doctor Nawal ya canza yasa.

 

Ta ce”Sis Doctor lafiya? Meke faruwa naga yana yinki ya canza?”

 

Duk ƴan matan suma su kai jigum suna jiran jin amsa daga bakin Doctor Nawal.

 

Ajiyar zuciya Doctor Nawal ta sauke sannan ta rafsa tagumi da hannu bibbiyu.

 

Ta ce”Ai yau labarin tausayi zan baku”

 

Suka kalleta ba su yi magana ba dan sun ƴosa suji ta fara labarin.

 

Doctor Nawal ta tuntsure da dariya sannan.

 

Ta ce”Munafukai kowaccenku jira take taji labari”

 

Suma dariyar su kai dan abin suma ya ba su dariyar sun natsu suna jiran jin labarin abin dariya.

 

Feena Ta ce”Allah Sis Doctor yau jamana aji kike da labari”

 

Doctor Nawal ta kalleta tai murmushi.

 

Ta ce”To ba zan ja maku aji ba naga kun matsu kuji”

 

Zee ta langwaɓar da kai Ta ce”Allah Sis Doctor duk kin sa jikin mu yai sanyin jin kin ce labarin abin tausayi”

 

Leema tai dariya sosai ganin yadda Zee tai ita a dole suna jiran jin labarin abin tausayi.

 

Doctor Nawal tai gyaran murya.

 

Ta ce”To za a fara”

 

Ƴan matan suka daɗa gyara zama.

 

Nan Doctor Nawal ta fara basu labarin yarinyar da aka kawo masu ita asibiti anyi raping ɗinta da yadda su kai mata illa da irin wahalar data sha.

 

Sosai Zee da Feena suke kuka suna gyaɗa kai kamar ƙadan garu.

 

Doctor Nawal Ta ce”Ku nima fa sai da nai kukan da ina mata aiki abin ba kyan gani”

 

“Allah da na ƙarasa zama barrister ɗin nan da sai na tsaya mata an bi mata haƙƴinta”

 

Zee ta faɗa tana goge hawayen da suka ɓata mata fuska.

 

Feena Ta ce”Nima Allah kuwa ba dan na kusa gana karatuna ba da aikin law ɗin zan koma”

 

Leema ta sheƙe da dariya

 

Ta ce”Ƴan iska iyayen imani,Allah nima ta mugun ban tausayi yarinyar”

 

Yusra itama da kwalla ya cika mata ido.

 

Ta ce”Wallahi mutane ba su da imani wannan matsalar ta yi yawa a duniya”

 

Doctor Nawal tai ajiyar zuciya jin furucin kowannan su.

 

Ta ce”Wallahi nima sai da nai wannan tunanin nace da Sis Zee ta gama karatunta ta fara aiki ita zata tsayawa yarinyar nan”

 

Leema Ta ce”Eh wallahi”

 

Nan suka cigaba da tattaunawa akan maganar kowacce jikinta a sanyaye.

 

Granny ce ta shigo falon ta ɗau wanka da atamfa fuskarta saye cikin glass tsohuwa fara kyakykyawa ƴar wanka da ita.

 

Ta ƙaraso cikin falon tana magana.

 

“Iyayen surutu har kun cika min falo zaku zo kusan hawan jinin da baku sawa iyayenku ba”

 

Ta ƙarasa faɗa tana zama a ƙan kujera.

 

Leema Ta ce”Yo ai naga azziƙi ne ma a zo ind kake a raya shi”

 

Yusra Ta ce”A to faɗa mata dai tsohuwa sai surutu”

 

Dariya Granny tayi kafin.

 

Ta ce”Subhanallahi kaji yara har kura ce zata cewa kare maye gaku masu shegen surutu”

 

“Allah sarki ƴar baiwar Allah Nawal nice saliha a ciki”

 

Granny ta zaro ido waje da.

 

Ce wa”Wace salihar? Amma an cuci saliha wallahi”

 

“Ai Granny duk ciki sis Zee ce saliha itama ɗin amma wani lokacin gwanace”

 

Feena ta faɗa.

 

Granny Ta ce”Eh gwara gwarn dai amma kar ɗinku sai du’a”

 

Shigowar Yayan su yasa ba su sake magana ba ya nemi waje ya zauna,Nawal dake itace uwar tsokana ita ta fara.

 

“Allah dai ya biya Ya Hafeez yau dame kuma aka zo?”

 

Ta faɗa tana mai da kallonta gare shi,su kuma sauran sun zuba ido suna son jin amsa dan akwai su da son jin labari.

 

Ya Hafeez ya zubawa Doctor ido yana kallonta hutar sonta na daɗa ƙaruwa a zuciyarsa,ya sauke ajiyar zuciya sannan.

 

Ya ce”Ni ban zo da labari ba”

 

Sai suka cuccuno baki jin ba labari.

 

Granny Ta ce”Bar shashashai iyayen son jin gulma dan munafurci ne”

 

“Kai Granny Allah ya raba mu da gulma da munafurci”

 

Yusra ta faɗa.

 

Leema Ta ce”Yawwa ƴar uwa faɗa mata dai”

 

Ita kwa Zee ba tace komai ba kawai kallo take bin su da shi.

 

“Bari na tashi na tafi na barwa wannan ƴar tsohuwar mai farin gashi falonta”

 

Doctor Nawal ta faɗa tana miƙewa tsaye.

 

Ya Hafeez ya kalleta kafin.

 

Ya ce”A’a ina zuwa kuma”

 

Ɗan yatsina fuska Doctor Nawal tayi sannan.

 

Ta ce”Wallahi zan ɗan je na kwanta ne domin yau jina nake a gajiye dan ma ina son ganin sisters ɗina ne shiyasa”

 

“Amma kuma sai da na zo na zauna ai hirar dani sannan zaki tafi?”

 

Ya Hafeez ya faɗa yana wani langwaɓe kai kamar yaro.

 

Doctor Nawal Ta ce”Ya Hafeez kayi haƙuri ai in Allah ya kaimu gobe ranar hutu ce ina jin ba zan je hospital ba hira zan zauna musha”

 

Ya Hafeez Ya ce”To shikenan Allah ya kaimu”

 

Duk suka amsa da ameen suma suna miƙewa za su bi Doctor Nawal kowa ta wuce ɓangaran su.

 

Har sun kai bakin ƙofar fita su ka ji Ya Hafeez yana ce da Granny.

 

“Granny gobe ne fa mutuminki zai dawo daga India”

 

Duk sai suka ja suka tsaya jin cewar takurar su zai dawo.

 

Ita kuwa Doctor Nawal wata irin bugawa taji ƙirjinta ya bayar sai ta shiga furta innalillahi a zuciyarta kafin tace musu ita ta tafi ta wuce.

 

Suma kowacce ɓangaransu tayi zuciyarta na cemata dama karya dawo.

 

 

*Waye iyayen su Doctor Nawal?*

 

Alhaji Arab Ashrab haifaffan ƙasar labanun ne balarabe mai matuƙar kyau,matarsa ɗaya Hjy.Fateema wadda auran zumunci akai musu itama mai kyau da ita.

 

Aiki ya dawo da su nigeria ƴaƴansu 6 Umar wanda shine babba,sai Usman,Saratu,Muhammad,Nafisa, sai ƴar autar su Haleema sun taso cikin so da ƙauna da kulawar iyayen su.

 

Sun yi ilmi sosai na addini dana zamani wanda a yanzu kowannen su yana da aure kuma zaune suke a family house ɗin su wanda kowa ɓangaransa daban.

 

Alhj.Umar yana da matarsa ɗaya Hjy.Suwaiba da ƴaƴa Fiddausi wadda itace babba an mata aure tana da ƴaƴa itama,sai Zulaihat itama an mata aure da ƴaƴanta sannan Sadiya an mata aure itama da ɗanta ɗaya,sai autar su Husna domin shi duk ƴaƴansa mata Allah ya bashi.

 

Sai Alhj.Usman shima da matarsa Bilkisu da ƴaƴansu Kairat itace babba tayi aure a abuja da ƴaƴanta,sannan Ruhaima itama tai aure da ƴaƴanta sai Nabil wanda bai yi aure ba yana ƙasar india yana karantar soja wanda yama kusa kammakawa, sannan Fa’za itama an mata aure sai kuma Zainab (Zee) wadda daga kanta mahaifiyarsu bata sake haihuwa ba.

 

Sai Saratu wadda itama take aure amma a gidan suke zaune da mijinta mai suna Alhj.Bashir da ƴaƴansu Faisal wanda yai aure da ƴaƴansa sai Nusaiba itama tai aure sannan Yusra sai autan su Kaleed.

 

Sai Muhammad da matarsa Hjy.Aisha da ƴaƴansu Nabeela dake auran ɗan uwanta Faisal da ƴaƴansu,sai Isma’il sannan Nawal wadda taci sunan kakar su Fateema sai Kausar sannan Jawad da Juwaida ƴan biyu.

 

Sai Nafeesa wadda itama take aure tana zaune a gidan da mijinta Alhj.Kabir da ƴaƴan su Abubakar wanda yai aure da ƴaƴansa sai Hafeez wanda bai aure ba sa’an Nabil ne sai Haleema (Leema)wadda taci sunan autar su mahaifiyarta sa’ar su Nawal sannan autar su Hidaya.

 

Sannan Auta Haleema itama tana zaune a gidan da mijinta da ƴaƴansu Ruƙayya an mata aure sai Nafeesa (Feena) wadda taci sunan yayar mahaifiyarta sai Zuhra.

 

Alhj.Arab Ashrab ya haɗe kan ƴaƴansa ne a gidan gaba ɗaya har matan bai yadda su fita a gidan ba.

 

Duk yawanci ƴaƴan familyn auran zumunci akai musu kuma suna zaune lafiya amma ba a gidan suke zaune ba kowanne da gidan sa.

 

Doctor Nawal Zee Leema Yusra Feena duk sa’anni ne kuma sune ƴan mata yanzu a familyn suna matuƙar ƙaunar junan su.

 

Ya Hafeez yana ƙaunar Doctor Nawal amma ya kasa tunkararta ya faɗa mata ya bar abin a zuciyarsa.

 

 

Wannan kenan *Arab Ashrab family* kenan family mai abin burgewa.

 

*Cogaban labari*

 

“A’a Feena yane naganki da damuwa bayan da farin ciki kika bar ɓangaran nan?”

 

 

Feenat ta zumɓuro baki kafin, Ta ce”Mammy ashe wai wannan mutumin ya kusa dawowa?”

 

 

Hajiya Haleema bata gane wa take nufi ba, Ta ce”Ban gane wa kike magana a kansa ba Feena?”

 

 

Feena Ta ce”Mammy Ya Nabil fa”

 

Feena ta ƙarsa faɗa kamar za tai kuka.

 

Hajiya Haleema ta riƴe baki da, Ce wa”La’ila Feena ɗan uwanki ne fa”

 

“To Mammy dan ɗan uwa nane sai ya dinga takurawa mutane?”

 

Hajiya Haleema ta riƙe baki, Ta ce”Wuce ki bani waje mara kunya ba dani ba”

 

Feena ta wuce ɗakinta tana ɗan dariya dan Mammy ta bata dariya.

 

***

“Auta lafiya na ganki haka bayan ba haka kika fita ba? Me yake damunki?”

 

Hjy.Bilkisu ta faɗa tare da zubawa Zee idanu.

 

Zee ta sauke ajiyar zuciya ta kalli mahaifiyarta kafin, Ta ce”Wallahi Meema ji nake kamar kar yaya ya dawo”

 

Cikin zaro idanu Hjy.Bilkisu, Ta ce”Subhanallahi Auta mene naji kina faɗa? Saboda me zaki wa ɗan uwanki wannan fatan?”

 

Zee ta sunkuyar da kanta ƙasa, Ta ce”Meema kin san fa halin yaya da takura yanzu da ya dawo zai hana mu sake wa da ya aka cika balle yanzu da ya zama cikakken soja”

 

“Kar na sake jin wannan maganar a bakinki idan ba haka ba ranki zai ɓaci”

 

Hjy.Bilkisu ta faɗa cikin ɓacin rai.

 

Da sauri Zee ta tashi ta isa kujerar da take ta durƙusa da, Ce wa”Meema dan Allah kiyi haƙuri idan har na ɓata miki rai”

 

Hjy. Bilkisu Ta ce”Shikenan amma karki sake”

 

Zee Ta ce”Insha Allah”

Nan kuma suka cigaba da hira.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment