Meerah Hausa Novel Complete

Meerah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MEERAH

 

 

NA

 

 

MAMAN AFRAH

 

FCW

 

DEDICATED TO AMEERA ADAM

 

Gajeran labari

 

 

*Barka da sallah Hajiyata Allah sa an yi mai lada, alkairin Allah ya kai miki a duk inda kike ftn nasara da gamawa lafiya🙏*

 

Page 1 & 2

 

 

Tun bayan da suka gama waya da mai gidanta Alhaji Mubarak ta fara jin ciwon mara kaɗan-kaɗan. Duk da ya sanar da ita yau zai baro wurin aikinsa Abuja ya taho wajensu Kano amma a mota zai taho, haka yace mata amma kuma wasa yake mata dan lokacin ma yana shirin shiga jirgi, hakan ya sanya ko da suka yi wayar bata faɗa masa cewa tana jin ciwon mara ba duk da kasancewar haihuwar fari ce za ta yi, dan kar hankalinsa ya tashi.

Yarima Junayd Hausa Novel Complete

Haka ta cigaba da daddaurewa dan bata so a fahimci halin da take ciki, saboda kishiyarta Hajiya Zainab da babu wani abu da ta tsana sama da wanann cikin da ke jikin Ummusalma.

 

A hankali Ummusalma ta tashi domin shiga bayin da ke cikin ɗakin nata, amma me sai ta ji mararta ta wani irin hautsina mata a take ta fara jin wani ruwa ya fara fita daga jikinta.

 

Cikin ƙarfin hali da na zuciya ta kama gadonta da hannu biyu ta ƙanƙame jin tafiyar ta gagareta sannan tsayuwar ma na neman gagararta, pant ɗinta ta cire ganin naƙuda ce ta zo mata gadan-gadan. Duk abin da take Hajiya Zainab na kallonta ta tsakanin labule, dan tana shigowa dama ta mata laɓe dan sanin halin da take ciki, dan tun da ta fahimci kishiyar tata ta kusa haihuwa shikenan take laɓewa tana son sanin lokacin da za ta haihu dan ta ɗaukawa kanta alƙawari duk runtsi duk wuya sai ta yi sanadiyyar abin da za a haifa, tun da ita da ta sha wahalar mijin tun bashi da shi bata haifa ba to yanzu kuwa da ya samu arziƙi babu wata mace da za ta zo ta haifa masa ɗa idan ya mutu a raba gado su kwashe a zo a bar mai kaza da kai da ƙafa!

Ameera Adam

 

 

NA

 

 

MAMAN AFRAH

 

FCW

 

DEDICATED TO AMEERA ADAM

 

 

*Barka da sallah Hajiyata Allah sa an yi mai lada, alkairin Allah ya kai miki a duk inda kike ftn nasara da gamawa lafiya*

 

 

page 3 & 4

 

 

Ganin halin da Ummusalma ke ciki, Hajiya Zainab ta lallaɓa ta fito daga sashen kishiyar tata, ɓangaren masu aiki ta nufa tun daga bakin ƙofa take faman ƙwallawa mai aikinsu Iya Lamura kira, da hanzari Iya Lamura ta fito har tana neman faɗuwa, saboda kowa tsoron Hajiya Zainab yake saboda masifa da ƙiyayya ga na ƙasa da ita ko kaɗan bata son talaka, kamar dai bata yi rayuwar talauci a baya ba. Kuɗi ta miƙa wa Iya Lamura ta lissafa mata kayayyakin da za ta siyo a kasuwa, tsohuwar ta juya ta tafi, Hajiya Zainab ta ƙarasa wajen sauran ma’aikatan ta musu kashedi a kan kar wanda ya fito daga ɓangarensu na ƴan aiki cikin girmamawa suka amsa mata, ta kamo hanya ta fito tana kissima irin ta’a sar da za ta yiwa abin da Ummusalma za ta haifa dan ko ɗigon imani babu a ranta. Tana ji a ranta ba gudu ba ja da baya dan da hannuwanta za ta sanya ta murtsuke ɗan har lahira, dan ma ta san Iya Lamura na taimakawa Ummusalma kasancewarta dattijuwa shi yasa ta aiketa kasuwa, su ma sauran ta hana su fitowa ne dan kar su san mai za ta aikata su san yadda suka yi wajen faɗa a zo a kawo wa Ummusalmar ɗauki, ƙwara idan ta aiwatar koma me zai faru ya faru dan ta gwammace ta ƙare rayuwarta a gidan kaso! A kan ta bar abin da kishiyarta za ta haifa da a doron ƙasa.

 

 

Sai da ta tabbatar babu wanda ya ganta kama daga cikin masu aikin gidan maza masu ban ruwan fulawoyi da dai sauran ma’aikatan gidan. Ɓangaren Ummusalma ta shiga ta rufe, bayan ta shiga falon ma ta rufe ta sanya mukulli, bedroom ɗin ta nufa aikuwa tun kan ta ɗaga labule ta fara jiyo nishin Ummusalma ƙasa-ƙasa, bankaɗa labulen ta yi a kwance a ƙasa ta ga Ummusalma tana ƙoƙarin kai hannunta kan mudubi za ta ɗauki waya amma ciwo ya hanata. Wani murmushi Hajiya Zainab ta yi, ta sa hannu ta ɗakko wayar ta danne makunnar har sai da wayar ta mutu sannan ta ajiyeta a kan mudubin tare da ajiye wani ƙyallen tsumma mai naɗe da wani abu da ta shigo da shi a hannunta, ta haɗa da tata wayar da kuma gabaɗaya mukullan da ta ciro waɗanda ta rufe ƙofa ta ajiyesu a kan mudubi, ƙofar bedroom ɗin ta rufe ta sanya mukulli ta kulle ta cire mukullin ta haɗa shi da sauran da ta ajiye.

 

 

 

09030283375

[22/04, 8:05 am] Ameera Adam MEERAH

 

 

NA

 

 

MAMAN AFRAH

 

FCW

 

DEDICATED TO AMEERA ADAM

 

 

*Barka da sallah Hajiyata Allah sa an yi mai lada, alkairin Allah ya kai miki a duk inda kike ftn nasara da gamawa lafiya🙏*

 

 

Page 5 &6

 

END

 

 

Ummusalma da ke ta jijjiga kai saboda tsabar azabar naƙuda , ba ta yi yunƙurin yin komai ba saboda bata da ƙarfin aikata komai, addu’a take ta yi a zuciyarta a kan Allah kare ta daga sharrin matar nan da ita da abin da za ta haifa.

 

“To ƴar matsiyata, wato ke mai ciki wacce za ta fara haifewa Alhaji ɗa a gidan nan ko, to yau za ku baƙunci lahira daga ke har abin da za ki haifa, dan sai kin haife a gabanki zan kashe abin da kika samu sannan ke ma na aika ki, ba ɓata lokaci in ya so daga ƙarshe in ƙare sauran rayuwata a gidan yari na san dai ko iya hakan burina ya cika dan ban bar ƙwan Alhaji a duniya ba, yadda ba na haihuwa haka shi ma ba zai ga ƙwansa a duniya ba.

 

 

In ban da ma butulci irin na ɗa namiji mu sha wahalar rayuwar talauci tare amma yanzu dan ya yi kuɗi ya mini kishiya har za ta haihu ni ina zaune basho” Ta faɗa tana doka wani uban tsaki tare da samun wuri ta zauna a bakin gado.

 

Ita dai Ummusalma sai murƙususu take, dan ta san dai duk cikin abin da kishiyar tata ta faɗa babu wanda zai gagara ta aikata dan rashin imaninta ya zarce hakan ma. Wata uwar harara Hajiya Zainab ke aikawa Ummusalma da cikinta da ya gama sakkowa ƙasan mara dab yake da isowa duniya, cike da muguwar tsanarta da abin da za ta haifa. Baki Ummusalma ta buɗe ta shiga karanto addu’o i cikin ɗaga murya jin ciwon da ya wuce hankali da tunaninta. Ganin hakan ya sanya Hajiya Zainab ta tashi tsaye ta buɗe ƙofar bayin ɗakin ta dawo ta kama ƙafafun Ummusalma ta jata ƙiiii har cikin bayin saboda tsabar rashin imani bata dubi halin da yarinyar ke ciki ba.

 

 

Tana shiga da ita bayin ta wani warɓar da ita gefe, sai numfarfashi take tana jin azaba kamar za ta mutu amma Hajiya Zainab bata tausaya mata ba. Tana tsaye a kanta ta ga wurin ya buɗe tana iya hango sumar ɗa, wani irin baƙinciki da kuma baƙin kishi ne ya turnuƙe ta tana jin kamar ta yi bindiga ta fashe dan hakan zai fi mata sauƙi sama da halin ɓacin ran da take ciki, na mugun abin da idanunta ke yin tozali da shi yanzu.

 

Wani irin durƙusawa ta yi a gaban Ummusalma ta sanya hannu cikin rashin imani ta danna saman cikinta, wata azaba da Ummusalma ta ji sai da numfashinta ya ɗauke ya dawo, kamar wanda aka hankaɗo ɗan sai gashi ya sunɓulo a ƙasan tiles ɗin bayin, lokaci guda mabiyiya ta faɗo, cikin zafin nama Hajiya Zainab ta sanya hannu ta fisgi ɗan da hannu ɗaya, aikuwa hakan ya sa shi sakin kuka da bai yantsara ba tun farko, tana ɗaga shi ƙafafun suka ware aikuwa idanunta da na Ummusalma da ke kwance suka sauka a kan al’aurar jaririya ƴa mace ce.

 

“A yau kika sauka a duniya, a yanzu za ki koma ƙiyama idan kin je ki jira zuwan gyatumarki dan kuwa ita ma yanzu zan aiko da ita ” Cewar Hajiya Zainab cikin kaushin murya. Tana gama faɗar hakan ta dangwarar da jaririyar a inda ta ɗauke ta, cikin jini ga cibiyarta nan a jikinta fitowa ta yi daga bayin cikin ɓacin rai fa raɗaɗin zuciya, duk abin da take Ummusalma na gani sai dai bata da ƙarfi ko kaɗan banda idanu da numfashi babu abin da ke motsi a jikinta, dan danne mata cikin da Hajiya Zainab ta yi ba ƙaramin jigata da azabtuwa ta yi ba.

 

Har tuntuɓe ta yi wajen ɗakko ƙyallen zanin da ta ajiye a kan mudubi ta yi, warware abin da ke ciki ta yi, ta nufi bayin gadan-gadan Ummusalma da ke kwance ga jaririya na tsala kuka ta ɗaga idanunta da ke zubar hawaye ta sauke a kan sharɓeɓiyar addar da ke hannun Hajiya Zainab sabuwa dal sai sheƙi take dan ko gida babu a jikin addar. Kiran sunan Allah Ummusalma ta shiga yi a kan ya kawo musu ɗauki dan ta san cikin mintuna ƙalilan za ta gama musu aiki ba imani ne da ita ba.

 

Hajiya Zainab kwa wani murmushi ta yi ganin burinta na dab da cika, haka ta ɗaga addar cikin rashin imani ta saita cikin jaririyar da niyyar lumawa, hakan ya yi dai dai da ƙaran buɗe ƙofar da aka wanda ko ƙaran mukullin basu ji ba, sai dai turo ƙofar kawai suka ji, Hajiya Zainab da sauri ta juyo daga cikin bayin idanunta suka sauka a kan mai gidan nata wanda ya yi amfani da mukullinsa wajen buɗe ƙofar, riƙe yake da bindiga ya ɗana kunamar bindigar zai harba.

 

“To marar imani kina cakawa ina fasa kan ki wallahi!” Ya faɗa yana ƙarasowa cikin ɗakin.

 

 

 

Hannunta ne ya shiga karkarwa hakan ya sa ta saki wuƙar hannunta, cikin tashin hankali, abu ya haɗe mata goma da ashirin gashi bata cika burinta na kashe Ummusalma da ƴarta ba ga kuma asirinta ya tonu. Ummusalma kwa godiya ta shiga yiwa ubangiji da ya kawo musu mai cetonsu.

 

*Bayan kwanaki uku.*

 

Ummusalma na gani sanye da wani rantsatstsen leshi ta sha ɗaurin ɗankwali tana riƙe da jaririyarta tana bata nono ga ƴan uwanta fal falon ana ta hira. Hajiya Zainab kwa a ranar da abin ya faru Alhaji ya mata saki ɗaiɗai har uku dan cewa ya yi ma sai ya maka ta kotu saboda yinƙurin kisan kai amma Ummusalma ta hana shi, ta hanyar roƙon arziƙi a kan ya barta da halinta da ma sakin da ta jawa kan ta.

 

Ranar suna yarinya ta ci sunan Aisha ana kiranta da MEERAH haka ta taso cikin gata da kulawa tare da tarbiya daga iyayenta.

 

 

 

Ƙarshe

 

Tammmat bihamdulillah A nan na kawo ƙarshen wannan gajeran labari nawa wanda na yi shi dan taya Hajiyata AMERA ADAM murnar ƙaramar salla ta shekarar 2024 Allah maimaita mana amin.

 

MAMAN AFARAH 09030283375

Post a Comment

Previous Post Next Post