Littafan Hausa Novels

Yarima Junayd Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Yarima Junayd Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

YARIMA JUNAYD

 

 

Na

Jiddah S Mapi

 

*Chapter 1*

 

*_Arewabooks Jiddasmapi_*

 

 

~Yarima!!! Yarima!!! Yarima!!! Ka rike hannuna zan faɗi, sulɓi yana jana banaso na faɗi acikin Ruwan nan, Yarima!!!! Da sauri a farka yana furta “Innalillahi wa inna ilaihiraji’un” ganin yadda ya saki yarinyar ta faɗi a cikin ruwan, a ƴan kwanakinnan wannan mafarkin ya dameshi, baya taɓa kwanciya ya farka lafiya sai yayi mafarkin yarinyar da ko fuskarta baya gani, kafafuwanshi ya sauke daga kan Bed ɗin a hankali ya miƙe yana yamutsa fuska, Lips nashi wanda yake Red Color ya tura na kasan cikin bakinshi yana tsotsa, wannan ɗabi’arshi ne, saida ya mike na zuba mishi ido, wani Dogo ne yana da ɗan kauri, Hancinshi nada tsayi sosai, sai bakinshi dayake ɗan karami, idanunshi na gani irin na Turawa kwayan cikin idon Brown color, manyan ido ne mai ɗauke dogayen eyelashes Wanda yake baƙi sosai, gashin giranshi baƙi ne sosai shima a tattare, kanshi kuma yanada suma kuma yana samun gyara sosai, fari ne sosai, fuskarshi ɗauke da kwantaccen saje wanda yakara fito da asalin kyawunshi, Rigan dayake jikinshi ya cire nan na hango faffaɗan kirjinshi wanda yake cike da kwantaccen gashi, hannunshi ma yana ɗauke da gargasa, a hankali yafara cire kayan jikinshi.

Kwarton Hajiya Hausa Novel Complete

Saida ya cire komai kafin ya ɗau wata ƴar karaman Towel datake shinfiɗe a gefen Gadon da alama an ajiye mishi ne domin hakan, Cikin ɗakin nagani, gadon silver color ne, anyi mishi ado da pink ɗin Kayan sarauta, gadon kaɗai abun tsayawa a kalla ne, balle kuma Mirror da Drower da sauran kayan da suke relative da gadon.

 

Cikin ɗakin kana gani kasan wannan ɗakin Sarauta ne domin an ƙayata shi da kayan ado na sarauta masu kyau da ɗaukan hankali.

 

A hankali yafara takawa zai shiga Toilet ɗinshi dayake haɗe da Bedroom ɗin, Handle ya murɗa yaji an rungumeshi ta baya, lallausan hannunshi wanda yake fari yasa ya riko hannunta, Fuskarta tasa a gefen wuyarshi tana gogawa tana dariya, wata kyakkyawan matace zata kai shekara 25 tana da kyau sosai, tayi Dressing cikin Atamfa sannan ta ɗaura bakin Alkyabba akai, hulan alkyabban tasa wanda yakara fitowa da farin fatar sosai.

 

A hankali ya zameta yana ɗan murtuƙe fuska, rikeshi tayi tana fuskantar shi hannunta kuma ta zagaye Waist ɗinshi dashi, ɗauke kai yayi yana kallon gefe, Towel ɗin tafara warwarewa da sauri ya rike hannunta yana girgiza mata kai.

 

“Why” tayi maganar tana kallon cikin idonshi, zame hannunta yayi daga jikinshi ya juya zai shiga yayi wankan shi, kara rungumeshi tayi ta baya tana ƙankameshi, cire hannunta yayi ya ture ta sannan yashiga toilet ɗin ya rufe, Bayanshi ya haɗa da jikin kofan yana kallon cikin kyakkyawan Toilet nashi, komai da komai akwai aciki, kama daga kan sabulu shower Jel da turaruka ga brush da makilin, cikin Toilet ɗin ma abin tsayawa a kalla ne.

 

A hankali yafara takawa har zuwa wurin da jaccuzzy yake, ruwan zafi da na sanyi ya tara, cire Towel ɗin yayi daga jikinshi ya zauna acikin jaccuzzy yanajin ruwan yana bin jikinshi, kunna shower yayi Nan ruwa yafara tsiyaya a kanshi, lumshe ido yayi yanajin nutsuwa yana shiga jikinshi.

 

Ya kai akalla minti 30 kafin ya mika hannu ya ɗau sabulu yafara gogawa a jikinshi, sanyin daɗi yaji a jikinshi domin sabulun yana ɗauke da sinadarin Menthol, Saida ya goga kafin ya kara kunna shower Nan yayi wanka, ya zura dogayen kafarshi zuwa waje ya ɗau Towel ya Kara ɗaurawa a waist ɗinshi, sannan ya ɗauki wani karami daga gefe yafara goge tulin sumar kanshi wanda suke a kwance.

 

Cikin takunshi na kasaita da isa da nuna shi ɗin jinin Sarauta ne yafara tafiya har ya buɗe kofa, Kamar koda yaushe Lips nashi na kasa ya tura cikin bakinshi yana tsotsa, ganinta a ɗakin ta ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya tana latsa waya yasashi kawar da kanshi yana nufan inda zai zauna ya shafa mai.

 

Wasu lotions da creams da kuma Body kulacca ya ɗauka ya buɗe, drayer ya ɗauka ya kunna yana busar da gashin kanshi wanda yake a jike, Saida ya bushe kafin yafara shafa lotions ɗin yana kallonta ta cikin madubi, a hankali ta taso cikin takunta na kasaita da nuna itama jinin Sarauta ne ta karaso wurinshi, Lotion ta matsa sannan ta goga a hannunta a hankali tafara bin jikinshi da shafa, shiru yayi mata har ta gama yana kallonta ta madubi.

 

Taje gashin kanshi tayi sannan tayi mishi style dashi, murmushi ta sakar mishi tana ɗaga hannunta sama Alaman kayi kyau, Cikin fishi ya tashi zai tafi da sauri ta riko hannunshi.

 

“Haba yarima na kasan fa bazan iya jure fushinka ba, wallahi bada sona na jima a can ba nasan Kanada bukata ta amma ai bazan bar aiki saboda kai kawai ba…

 

Fizge hannunshi yayi dama yasani Ruma bazata taɓa canja hali ba, kullum batada lokacin shi, ga kishi ga isa ga gadara da raini, shi kaɗai take ɗan shakku a gidan amma ko me martaba baya faɗa mata tayi me kyau tayi, dole sai abinda ranta yaso shi takeyi.

 

Rigan Shadda yasa wani ash color sannan yasa wandon, ya ɗau alkyabba ya ɗaura a sama, ba karamin kyau yayi ba da shiga irin ta sarakai, bakin glass yasa a fuskarshi sannan ya ɗau turare mai daddaɗan kamshi ya feshe jikinshi dashi, saida ya gama ya kalleta, tasan me yake nufi, wayarshi ta mika mishi, sannan ta riko hannunshi suka nufi hanyar fita.

 

A ranta tana cewa “wannan da yana magana da ko nashiga uku, Gara da Allah ya toshe bakinshi da ya daɗe da sakina”.

 

Falonshi suka wuce wanda yake cike da kaya irin na sarauta, komai na falon Purple ne, da fari, harda flowers Wanda suke cikin tukunyar flower, Shima flowers ɗin suna bada wani sihirtaccen kamshi na Musamman, wasu bayi ne su biyu ƴammata suka durkusa kasa suna gaishesu.

 

“Gaisuwa gareki Gimbiya Rumasa’u Mai martaba yana jiranku a fada, muna gaishe da Yarima Me jiran gado”

 

Kallon banza tayi musu kana cikin isa da gadara ta ɗaga musu hannu, cigaba sukayi da tafiya, suna wuce part part, ɗaki ɗaki na cikin gidan, Da fari wani Babban falo suka shiga Yarima ya durkusa kasa haka itama Ruma, Wata mata ce wacce bazata kai shekaru 50 ba, amma zata wuce 48 kyakkyawa ce fara sol tana da kiɓa, jikinta sanye da Atamfa tayi ɗauri irin na matan sarki, murmushi tayi ta amsa gaisuwan, A hankali yarima ya mike yana shagwaɓe fuska, gabanta yaje ya zauna ya ɗaura kanshi a cinyarta yayi kamar zaiyi kuka.

 

“Haba Junayd meyasa bakason cikin mutane ne? Meeting ne fa zakuyi dasu me martaba, kuma kasan dolene ka rinƙa Attending ɗin komai daya shafi sarauta a gidannan ko?”

Shiru yayi yana lumshe ido, Ruma chatting ɗinta take da friends nata na school, Kallonta Matar tayi tace “zo ki ɗau mijinki ku tafi kafin Mai Martaba yayi fushi”

 

“To Ammi” tafaɗa tana ci gaba da danna wayar, gaban Ammi tazo ta riko hannunshi, lumshe mata ido yayi yana kwaɓe fuska, a hankali tace “tashi muje sauri nake kuma wallahi Zan tafi school Ni banson rigima”

 

Ammi shiru tayi dan tasan kaɗanne daga cikin aikin Ruma ta juya ta tafi, yanzu ma dan Mai martaba ne yace suke idan ba haka ba bazata je ba.

 

Tashi yayi yana yiwa Ammi Bye Bye, suna fita tayi tagumi a fili tace “Yaushe ne zanji muryan ɗana? Yaushe Allah zai buɗe maka baki Babana? Yaushe zaka fara magana kamar yadda mutane suke yi?”.

 

“Ammi ki daina sa kanki a damuwa Hamma Junayd ai zaiyi magana tunda ba haka aka haifeshi ba”

Wani matashi ne wanda bazai wuce shekara 20 ba, kana ganinshi kasan kasan Junayd ne domin kama sosai ya bayyana a fuskarsu.

 

“Auta har yaushe ne hakan zai faru? Ina kwaɗayin ganin wannan rana”.

 

“Ammi banason ganinki cikin damuwa dan Allah ki daina banaso” yafaɗa yana gyara igiyan wandonshi, yana kama da Junayd sosai saide yafi Junayd yarinta da kuma fara’a.

 

“To Safwan zan daina”

Wurinta yazo yayi mata kiss a gefen fuska “that’s my Mom Haka nakeso naji, yanzu yimin dariya kaɗan nagani”

Dariya Ammi tayi dama idan Safwan yana wuri dole kayi dariya.

 

“Ammi na shirya zan tafi school nifa Ammi nafison Aure akan school ɗinnan gashi Abba ya dage sai nayi school so nake naga nima inada yaro”.

 

Cikin kunya Ammi ta kauda kanta, Yaro Babu kunya haka ko kaɗan?

Yasani shiyasa yayi dariya kawai yafita.

 

Suna fita suka shiga ɗayan ɗakin dayake gefen na Ammi, A hankali Suka durkusa suna gaida matar datake kwance tana cin Tufa, Hannunta ta ɗaura akan Timtim ɗin dayake tsakar falon, Bayi guda uku ne suke matse mata jikinta, biyu kuma sunayi mata fifita, kallon su Ruma tayi tace “Sannunku sai yanzu?”

 

Dariya Ruma tayi tace “Fulani Ai kinsan Yarima da rashin saurin shiri, shi ya daɗar damu”

 

Dariya tayi tace “nasan halin ɗan nawa”

Yarima murmushi kawai yayi mata yasa hannu ya ɗau Apple guda ɗaya a hankali yafara tauna yana kallon Ruma datake cigaba da Chatting ɗinta, mikewa yayi saida ya ɗan Taɓata kafin ta mike tana yamutsa fuska, fita sukayi matar tanayi musu murmushi.

 

A bakin kofa suka haɗu da wani matashi zai kai 26 year Yana ganinsu yanemi canja hanya, Yarima ne ya riko hannunshi, ya juyo ya kalleshi, gira ya ɗaga mishi Alaman ina zaije?”

 

Sosa Kai yayi yace “ina kwana Unty Ruma”

 

“Lafiya kalau Munir ya kake?”

 

“Ina lafiya”

 

“Ina kwana Hamma Junayd?”

 

Kallonshi yayi sama da ƙasa yanajin wani warin kayan shaye shaye yana tashi daga jikin Munir ɗin, kallon tuhuma yayi mishi kafin a hankali ya matso da fuskarshi wurin bakin Munir ɗin, tabbas yasha abu ba hancinshi ke mishi gizo ba, sakinshi yayi yabar wurin ranshi a matuƙar ɓace.

 

Binshi tayi baice komai ba, har suka isa fadan mai martaba, gaisuwa sukayi mishi, Dogarai suka fita a fadan, Babban fada ne na zamani, an ƙayata shi da kayan kyale kyale na zamani, sarki dayake kishingiɗe akan Kujeran sarauta ya ɗago yana kallon Junayd, nan naga kama sosai a tsakaninshi da Junayd ɗin, mikewa yayi yaje ya zauna a gefen Babanshi, wani kyakkyawan darduma ne aka shimfiɗa a tsakar falon, tareda Timtim irin na sarauta kallon Junayd yayi yace “Yarima? Me ya sameka ka ɓata rai haka?”

 

Turo baki yayi gaba yana kallon ƙasa, hannunshi mai martaba ya riko yace “banson abinda zai taɓa ka faɗamin meya sameka?”

 

Biro ya ciro a aljihun riganshi yafara rubutu, saida ya gama ya mikawa mishi

_muneer bai daina shaye shaye ba Abba, gaskiya sai an kara yimishi faɗa tunda yaƙi jina_”

 

Numfashi mai martaba yaja sannan yace “Nasani bai daina ba amma na rasa yadda zanyi dashi saide hakan bazai hana nayi mishi faɗa kuma na hukunta shi ba”

 

Murmushi Junayd yayi saboda bayason yana ganin Kanin nashi acikin wannan hali na shaye shaye, waya ma martaba ya ciro ya danna Number ɗin muneer “ka zo Fada”

 

Muneer dayake kwance a gefen Ummanshi jin mai martaba ya kirashi yasa ya kalli Umman nashi cikin Ɓacin rai da hura hanci yace “Umma kin gani ko? Yanzu yaje ya haɗani da mahaifina nasan faɗawa Abba yayi ina shaye shaye wallahi Umma bazan yadda ba, Ni kaɗai ne a gidan? Ni kaɗai ne?”

 

Murmushin gefen baki tayi, hannunta tasa ta shafo kanshi tace “Kada ka damu Ɗana ka tashi kaje kaji kiran da yayi maka, barni dasu zanyi maganin kowa a gidan”

 

Tashi Yayi dan yasan Umman nashi zata iya komai, ɗakin mai martaba yaje yana hararan Junayd har ya zauna a gefe ya dukar dakai yace “gani”

 

“Kana ganin abinda kake ya dace?”

Shiru yayi, cikin tsawa mai martaba yace “kai ba magana nake maka ba?”

 

“Ayi hakuri Abba zan daina”

 

Ganin ran Abba zai ɓaci ne yace “tashi kafita” fita yayi, Ruma ce ta duka tace “Yallaɓai nikam zan wuce domin inada class”

 

“Kenan class nata yafi mata kiran Mahaifina?”

 

Takalmi tasa sannan tafita a ɗakin, Mai martaba ya kula da halin daya shiga “Ka daina damuwa Komai yayi farko zaiyi karshe kuma ko ba komai ai Ruma kanwarka ce tunda mahaifinta ɗan uwana ne”.

 

Shiru kawai yayi ranshi in yayi dubu to ya ɓaci, ko a wurin kwanciya ba kulashi take ba, sai kishi kamar Hauka, gashi Allah yayi shi Mabuƙaci ne sosai, yanada karfin sha’awa sosai, ya ma rasa yadda zaiyi da Ruma.

 

 

_Wannan littafin na kuɗi ne ku biya 300 kacal tanan 6037523268 Hauwa Shuaibumapi Keystone Bank, ku turo katin shaidan biya ta nan 08144818849, masu kati zaku iya turawa ta nan 08144818849 MTN 300_

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment