Likitan Mahaukata Hausa Novel Complete

Likitan Mahaukata Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

*LIKITAN MAHAUKATA…*

 

“`romantic story“`

 

MRS SADAUKI

 

 

 

FCWA

 

 

*Ina yi ma ɗaukacin musulmi Barka da Sallah, Allah gafarta mana zunubanmu ya karɓi ibadunmu*

 

“`NA JIMA SOSAI RABON DA NA YI LITTAFI MAI ƁANGARE BIYU, WANNAN YA SAKA NA TSARA WANNAN BOOK ƊIN INA FATAN ZA KU KARƁE SHI,AKWAI TARUN DARUSSA A CIKI DA KUMA ƘALUBALEN RAYUWA“`

 

 

 

1_2

 

 

MAROC

 

Kukan jiniyar motar asibiti ce ya karaɗe titin,duk ababen hawa sai darewa suke su na ba motar hanya ta wuce.

A harabar babbar asibiti motar ta tsaya,tuni dama nurse da sauran likitoci su na jiran isowarsu.Gadon asibiti aka saka aka fiddo wanda ya yi hatsarin,mutane da dama suka ɗauki salati saboda abun babu kyawun gani sai jini ke masa zuba.

Alkawarin Macijiya Hausa Novel Complete

Dr Mahamud wanda ya kasance babba kaf a asibitin banda hawaye babu abin da yake,sakamakon Ɗa ɗaya tilo a gunsa da ya ga cikin wani mawuyacin hali.

 

Sam kasa shiga ya yi a emergencyn,kan kujera ya zauna tare da rabka uban tagumi.

Sama da minti talatin kafin nurse ta fito ta yi masa alama da hannu kawai ,da saurinsa ya tashi ya shiga room ɗin.

A kwance ya tarar da Ɗansa rai hannun Allah,hancinsa an saka masa oxigene.

Dr Habib ya haɗiye wasu yawu dakyar ya ce “Dr kamar….kamar dai…. Am… Nace ko ka duba lafiyarsa ƙila kai kafi mu sanin daidai”

“Na ga kamar numfashinsa ya daidaita ,wace matsala ce kuma?” Dr Mahamud ya tambaya idonsa ƙurrr kan yaransa likitoci,duk sunne kai suka yi.

“Kwanyarsa ce ta taɓu?” Ya sake tambaya cike da raunin zuciya,Dr Habib ya ce “a’a yalaɓai ɗaya wajen dai mafi muhimmanci a jikin na..mi..ji!”

Gaban Dr Mahamud ya bada wani ras,a nan take kuma ya daburce ya rasa ma abin da zai ce sai kallon RAJEEB yake bisanin ya yaye zanen da aka rufe shi.

Da kansa ya fara duba Ɗan nasa,can ya sauke numfashi “akwai ɗigo ɗaya na nasarar zai iya warkewa,ya Rahman ina tawasali da sunayen ka tsarkaka ka baiwa Ɗana lafiya” ya na gama faɗar haka sai hawaye sharrr can kuma ya fita da sauri.

 

 

Sai wuraren ukun dare RAJEEB ya farka daga dogon baccin da yake mai kama da doguwar suma.Manyan idonsa ya buɗe dakyar wanda suka yi masa nauyi,bai yi wani dogon tunani ba ya fahimci inda yake wato a asibiti.

Na’urar da ta fara kuka ce ta baiwa likitoci damar shigowa suka duba shi.Abun ƙarin numfashin suka cire masa,bisanin Dr Habib ya fara yi masa tambayoyi “ina yake ma ciwo yanzu?” Bai basa amsa ba sai ma lumshe idonsa da ya yi,”please Raj faɗa mini mana”

“Ina Daddyna?” Ita ce tambayar da ya jefo masa maimakon amsa,”ya na can ya na aiki an samu wata emergency ne” Dr Habib ya basa amsa.

 

 

“Ni na ji sauƙi ku sallame ni please” ya faɗa a shagwaɓe wanda ya saka Dr Habib ɗan darawa ya ce “to shalelen Daddyn a gadon asibitin ma sai an nuna halin?”

RAJEEB ya buɗe ido tare da ɗan hararensa ka na gani ka san su ɗin abokai ne ,”Allah gaske nake rasss nake ji na,in ka fidda kaina da ke mini ciwo” ya yi maganar ne tare da tashi zaune ya ture zanen rufa tare da sauke ƙafafuwan shi ƙasa .

 

 

Suman tsaye Dr Habib ya yi,ya na tunanin kamar ba abokinsa ba ne aka kawo cikin jini ba.

Ihu da kururuwa duk suka cika asibitin,da sauri duk suka fito waje don ganin ikon Allah.

 

Duk yadda RAJEEB ya so ganin wacce ke yin ihun amma hakan bai yiyu ba sakamakon mahaifinsa da ya zo ya ja shi zuwa wani room ɗin.

“Na ji daɗi sosai da na ga ka samu sauƙi,amma don Allah ka kwanta ka sake hutawa”

“Daddy wace ce ke ihun nan?” ya tambaya,cikin jimami ya basa amsa da “wata mahaukaciya ce mai tsohon ciki ban san mi ya kawo ta nan ɗin ba,amma kar ka damu na sa a fidda ta”

Da sauri ya miƙe tsaye ya na mai cewa “haba Daddy ita ma fa mutum ce,a barta ta haihu a nan kamar kowa mana” ya na maganar ne tare da nufar ƙofar fita zuciyarsa na wani irin halbawa wanda bai san dalili ba.

Daddy ya take masa baya,cirko-cirko suka tarar da likitoci a falon asibiti sun saka mahaukaciyar gaba.

 

 

 

RAJEEB ya yi turus ya tsaya waje guda tare da nunata da yatsa ya ce “keeee!?” Sai kuma ya yi shiru zuciyarsa na fat!Fat!Fat.

Ƙarar da ta yi mai tare da ambaton sunansa shi ya saka shi saurin dafe kansa,daga nan bai sake sanin abin da ya faru ba sai washegari.

 

 

Tamkar wani ƙaramin yaro haka ya koma,sam ya kasa samun nutsuwa bai san mine ne haɗin Ɗansa da wannan mahaukaciya ba.Ya matsu ya fito daga toilet ya tambayesa,ya na nan zaune ya fito kuwa.

Ya kalli Daddynsa suka yi ido huɗu,da sauri ya janye nasa ya na jin zuciyarsa babu daɗi.

“Ya jikin naka ? ”

“Da sauƙi alhamdullah!”

“Ina son yin magana da kai” cewar Daddy.

ya ce “to Daddy amma kafin nan please mahaukaciyar nan ta haihu kuwa?”

Shiru Daddy ya yi na ɗan wani lokaci bisanin ya basa amsa da “eh!” Ga mamakinsa fara’a ya ga a fuskar ɗansa,”mi ta haifa? Baby girl ?” Ya sake yin wata tambayar murmushin kan fuskar shi.

“Eh mace ta haifa,amma faɗa mini ina ka san ta ne?”

“Daddy mu je ka kai ni please na ga Babyn” ya yi maganar ya na mai jan hannun mahaifinsa, Daddy bai da wani zaɓi haka ya miƙe suka fita zuwa ɗakin da aka ajiye mahaukaciya.

Su na turo ƙofa Dr Habib ya ɗago kansa tare da cewa “yalaɓai Allah ya yi mata rasuwa!” Dammm! Ƙirjin RAJEEB ya buga,tamkar wani zararre ya yi saurin ƙarasawa ya kama hannun mahaukaciyar ya na cewa “amma ai kin ce za ki faɗa mini wani abu don Allah ki tashi kar ki tafi ba tare da kin sanar da ni ba”yadda RAJEEB ke magana a haƙiƙanin gaskiyar shi ya saka Dr Habib ya gaskata maganar mahaukaciyar,ba tare da ya yi nauyin baki ba ya ce “Ni zan faɗa ma ta bani saƙo” da sauri ya juyo cike da murna ya na cewa “da gaske? Habib da gaske ta shaida ma?”

“Eh ! Tace na faɗa ma SUMARANA za ka gane komi take nufi”

“Eh na gane!” Shi ne abin da ya faɗa bisanin ya ɗauki Babyn da ke wutsilniya.

 

 

 

“Mine ne haɗin ka da wannan mahaukaciyar?” Daddy ya tambaya.

Ba tare da ya juyo ba ya ce “Daddy ni kaina ba zan ce maka ga abin da ya haɗa mu ba,amma zan ce ma ita ce silar hatsarin da na yi”

“Hum!” Daddy ya yi ƙyaci, RAJEEB ya ce “Dr Habib ka cika takardu ni zan ɗauki wannan Babyn riƙo”

Dr Habib ya kalli Daddy bisanin ya ce “ƴar mahaukaciyar? Mike damun ka wai?”

“Barsa Habib ,zan ji da komi”

Cikin ɗan lokaci aka yi ma gawa sutura aka kaita makwancinta,yayin da RAJEEB kuma ya ɗauki Baby ya kai gidansu.

 

 

Zulfa ita ce ƴar aikinsu,asali ma ita ta raini RAJEEB tun ya na yaro.Mace ce mai daɗin zama da son mutane wannan ya sa RAJEEB miƙa ragamar Baby Najma a hannunta,wato ƴar mahaukaciya.Sosai take kula da ita,tun daga ranar kuma Daddy bai sake yin zancen ta ba duk da a gida guda suke rayuwa.

 

 

RAJEEB ya ɗauki son duniya ya ɗora ma yarinyar,cikin ƴan watanni shidda ta zama tuleliya mudul-mudul da ita.Ta yi wayo sosai ,a duk lokacin da ya dawo daga asibiti to sauran lokacin shi na Najma ne.

 

Kwance yake kan capet ya na latsa waya, Baby Najma na gefensa ta na koyon zama haɗi da gwarancin ta.

Zulfa wacce yake kira da Mama ta fito hannunta riƙe da ɗan basket ƙarami “yarona har yanzu ba ka shirya ba ne?”

Da sauri RAJEEB ya tashi zaune ya na cewa “oh! Na sha’afa amma jira ni nan da 10mn zan fito,a sake ma Baby kayan jikinta”

Mama ta ce “ai ba su yi wani datti ba yanzu na saka mata su”

“A’a a canza mata dai” ya faɗa tare da nufar step ,Mama ta ɗauki Baby Najma ta je ta canza mata kaya.

 

 

Su na nan zaune sai ga shi ya sauko cikin shigar fararen kaya, Mama ta miƙe saɓe da Najma suka fice.

Driver ne ya tuƙa su zuwa wurin shaƙatawa da wasa yara,kamar ba gobe haka RAJEEB ke ɗaukar su hoto shi da Najma ita dai Mama na gefe ta na kallonsu.

Har za su tafi gida sai kuma suka nufi bakin Teku ,”Mama ina son zuwa gaɓar ruwa amma ban san mi ya sa Daddy bai so ba,rabo na da na zo nan tun ina primary” cewar RAJEEB ya na waigawa baya inda Mama ke zaune.

“Wurare ne wanda ba a so yara su zo,saboda ganganci da wasu ke yi na cewa sai sun shiga can nesa”

“Ruwa na burge ni sosai Mama,dubi yadda suke gudu” ya faɗi haka ne lokacin da suka fito daga mota su na dosar Tekun.

Shi ne gaba driver a bayansa,har sauri yake wajen shiga kamar wanda ake jira ya na tsoma ƙafafunsa ya ji tamkar ana jansa ƙasa.Drever ne ya lura da haka,da sauri jawo shi ta baya ya na cewa “yalaɓai ruwan fa na da zurfi”

RAJEEB ya ja wata doguwar ajiyar zuciya ya na kallon ruwan,idonsa har wani mas suke masa.

 

 

Baby Najma ta fara kuka,Mama ta bata madara ta ƙi sha sai kukan take kamar ana zarar ranta.

Da sauri RAJEEB ya nufo su”lafiya mine ne?” Ya yi tambayar tare da karɓar ta ya nufi mota da ita,su na shiga ta yi shiru.Da zarar ya fito kuma sai ta fashe da kuka, wannan ya saka a doli suka koma gida.

 

 

 

 

Washegari

Jungum Mama ta yi jikinta cike da kasala, RAJEEB ne ke yi mata tambayoyi “tun yaushe ne zazzaɓin ya sauko mata? Wane irin magani ki ka bata?”

“Cikin dare ne,maɗagar kanta ce ke ɗagawa ta na halbawa da sauri,ban san mi zan bata ba” Mama ta bashi amsa.

Allura ya yi mata ba a ɗau lokaci ba zafin jikin Baby Najma ya sauka sai dai fa ƙwallon kanta tamkar garwashi, wannan ya saka RAJEEB a doli ya tafi da ita asibiti.

 

 

 

Yadda duk ya susuce ya saka Daddynsa duba yarinyar da kansa a matsayinsa na babban likita.

An ɗauki lokaci kafin ya fitar da wasu takardu ya miƙa ma Dr RAJEEB wanda yake Ɗa a gare shi,”hoton ƙwaƙwalwar ta ne,bincike ya nuna ta na da taɓin hankali” Daddy ya faɗa cike da jimami.

Tsabar ruɗewa RAJEEB ya saki takardun, Daddy ya ci gaba da cewa”haƙuri za ayi dama ai ana gadon hauka,bai kamata ka yi mamaki ba”

“Amma Daddy ba ta shayar da ita ba”

“Ko ma dai mine ne Najma mahaukaciya ce” Daddy ya faɗa ya na mai yin gaba.

Sam RAJEEB bai yarda ba,ya ɗauki hakan a matsayin ƙiyayyar da Daddy ke nuna ma ƴarsa wannan ya saka ya sake wasu abitocin da dama sai dai amsa guda ce Najma na ɗauke da ƙwayar taɓin hankali.

 

 

 

Bayan sati biyu

“Ba ka da hankali ko mi? RAJEEB ka san abin da ka ke faɗa kuwa?” Daddy ke tambaya cikin ɗaga murya.

Ya ce “Yes Daddy! Duka shekaruna 25 ne a duniya ban ga wata matsala ba don nace zan sake branche na karatuna ba”

“Zan barka ka yi komi amma banda *LIKITAN MAHAUKATA* wannan impossible ne salon su mayar da kai taɓaɓe-taɓaɓe”

“A’a Daddy kar kace haka don kuwa har na cika takardu gobe ma zan fara,don ba ka san muhimmancin Najma a guna ba ne shi ya sa har ka ke ɗaga jijiyoyin wuya akan nace zan yi karatun da ya shafi matsalar kwanya”

Maruka masu rai da lafiya Daddy ya sauke akan fuskar RAJEEB, bisanin ya nuna shi da yatsa ya ce “kafin ka canza aiki domin neman lafiyar ƴar titi ka je ka fara neman taka lafiyar,ko kuwa haka za ka zauna ba tare da ka yi aure ba? ”

“Banda lafiya ne?” Ita ce tambayar da ya yi,sai kuma Daddy ya yi shiru sam bai so ya faɗi hakan ba.

“Daddy banda lafiya dama shi ne ka ɓoye mini ?” Da sauri Daddy ya ce “lafiyar ka lau,je ka karɓo mini shayi gun Zulfa” ya na maganar ne tare da ƙoƙarin hana idonsa zubar da hawaye,ganin hakan ba zai yiwu ba ya saka shi nufar ɗakinsa ƙwalla na masa zuba.

 

 

RAJEEB ya fita a gudane cikin mota a zuciyar shi kuma sai tunanin yanayinsa da ya canza tun bayan hatsarin da ya yi.Biri ya yi kama da mutum,bai zarce ko ina ba sai Abitibi.Kudin likitar ya fara bincika,har ya kawo da inda aka yi register sunan shi ya na tsaka da dubawa Dr Habib ya shigo.

Idonsa sun kaɗa sun ja ya ɗago su ya ware su akan abokinsa Habib wanda tuni Daddy ya gargaɗe shi akan kar ya saki ya faɗa ma RAJEEB komi,shigowar da ya yi ma don ya ɗauke kundin ne sai dai kash tuni RAJEEB ɗin ya rigaye shi.

 

 

Ɗas ! Ɗas ! Haka hawaye ke masa ɗasa,zuciyarsa na zafi tamkar za ta fashe.

“Ka yi haƙuri Allah bai taɓa jarabtar bawansa da abin da ba zai iya ɗauka ba,duk wani mummuni ya na tare da jarabawa” Habib ya faɗa cikin sarƙewar murya.

Sam RAJEEB ya kasa jurar hakan,bai san lokacin da ya zame jiki ya faɗi ba…..

 

 

 

 

 

 

 

MARAƊI

 

 

 

Wata matashiyar mata ce wacce a ƙalla za ta kai shekaru talatin a duniya,tsaye take ta na zazzaga ma ɗanta masifa tare da dungure masa kai take bisanin ta ɗauki ƴar Babynta wacce ba za ta wuce shekara ɗaya da wasu watanni ba ta goya masa ita a baya.

“Je ka karɓo masara kwano guda ka zo ka surfa,in ka gama sai ka wanke ka kai niƙa”

Kuɗin ya karɓa kafin ya fita ya sayo,kamar yadda ta ce masa haka ya zube masarar a turmi ya surfe.

 

 

Ya na tsaka da wanke surfen Fateema wacce ke goye da bayansa ta tashi da wani irin kuka.

Ya na sauketa ta fara dariya sakamakon tozali da fuskar shi da ta yi,ruwa ya bata ta sha bisanin ya ajiye ta ƙasa ta fara wasa.Abinci ya ɗauko mata ya na mai cewa “Teema zo ki ci abinci” kai ta shiga girgiza wa “in ba ki ci ba to ba zan saya miki cakuleti ba” ya faɗa tare da nuna mata kuɗi,da sauri ta fara ci shi kuma ƙasan ransa ya masa fari ƙal.

 

Bayan ya bata abinci ya yi mata wanka sannan ya ƙara goyata suka tafi kan niƙa.Ya na dawowa ya tarar da Umma ta dawo,yadda take hararensa kamar idonta zai faɗo ya saka Aliyu firgita ya saki robar garin masarar a ƙasa.Garin bai zube ba,sai dai robar ta fashe.

“Laaaa ha ila!” Ta furta tare da nufo shi ta wanke fuskar shi da mari,Teema da ke goye a bayansa ita ta fashe da kuka shi kuma kamar kullum zuciyarsa ce ta sake kumbura ya na jin haushi da takaici da Allah ya basa uwa irin ta.

“Shege ɗan iska,ba a taɓa saka shi abu ya yi daidai ba.Wannan robar da ka fasa sai ka biya ni abata dan ubanka”

 

Abba da ya shigo ya ce “subahannallahi! Saratu wai sai yaushe za ki yi ma kan ki faɗa ne? Kullum zagi mi zai hana yaro ya tandare?”

Wani marin ta sake kifa ma Aliyu bisanin ta baiwa Abba amsa “na je na zaga ɗin,ƙarya na yi ba shegen ba ne? ” Kai kawai Abba ya girgiza kafin ya kama hannun Aliyu.

“Dubi yadda ki ka ji masa fuskarsa duk ta yi ja”

“Ko za ka rama masa ne? Nace ko za ka rama masa ne?” Ta yi maganar ta na wani riƙe ƙugu.

Abba ya yi gum da bakin shi tamkar mai tsoronta,ya kasa cewa komi.Ɗakinsa ya ja Aliyu suka shiga, bayan Saratu ta karɓi Teema.

“Ka yi ta haƙuri Aliyu wata rana sai labari,kar ka taɓa gajiya da yin addu’ar”

“Abba wace ce Ummata ?”

“Za ka san ta,nan gaba ka ƙara haƙuri,duk wani bayani ya na nan cikin wannan akwatin in lokaci ya yi za ka sani”

Aliyu ya dubi akwatin da kallo,ba tare da ya ce komi ba ya sunne kai har yanzu ransa babu daɗi.

 

 

“Ka fito ka hura wutar da zan yi maku girki ko da kaina ka ke so na yi?” Saratu ta faɗa ta na ɗage labule,da sauri Aliyu ya tashi ya fito.

Bakin murhu ya zauna ya na iza itace,bai tashi ba har sai da Saratu ta gama girki.

Shi da Teema ta zuba masu kamar kullum,don sam yarinyar ba ta cin abinci in ba a hannun Aliyu ba.

Su na waje su na cin abinci Aliyu ya fara jiyo sautin murya Saratu a hankali cikin wani irin Yare,kamar an tsikare shi ya je ya leƙa ta window abin da idonsa suka gane masa ne ya sa shi saurin gusawa da sauri zuciyarsa na bugawa.

 

 

Tsakiyar dare

Da kukan Saratu Aliyu ya farka,ya fito tsakar gida.Yadda take furta kalmar ta shiga uku da kuma sunan mahaifinsu ya fahimci abin da ke faruwa.

A nan take hoton abin da ya faru jiya ya dawo masa a kai,duk da ya na da ƙarancin shekaru amma ya na da yaƙini kan mutuwar Abba na da nasaba da abin da ya gani ɗin.

Rasa mi zai yi ma ya yi,kawai sai ya nufi ɗakin Abban.A kwance ya tarar da shi rufe da zane,idonsa ya kai kan akwatin jiya da sauri ya ɗauki akwatin.Ya na jin yadda mutane uwanda suka fi kusa da su suka fara shigowa,da alamu Saratun ta buɗe masu gida.

 

 

Aliyu ya koma can ɗakin Saratu wanda dama a nan yake kwana shi da Teema.Tunanin mafita ya fara ,yayin da a can ɓangaren kuma suke ta salalami dangane da ƙarya da Saratu ke shararo masu.

 

A hankali ya leƙa sai ya ga tsakar gidan babu kowa,inda Saratu ke ajiyar kuɗin adashe ya buɗe ya kwashe su sarai bisanin ya goya Teema wacce ke bacci,cikin ikon Allah Aliyu ya sulale ya bar gidan.

Post a Comment

Previous Post Next Post