Littafan Hausa Novels

Alkawarin Macijiya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Alkawarin Macijiya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

ALƘAWARIN* *MACIJIYA*

 

 

_DAGA_ _AIƘALUMAN))_

 

*Sajida Faɗima*

( *Gimbiyar dashen* *AIIah)*

_TARE_

_DA_

*Fatima Abdullahi* **Shadai*

( *Zahra T. Fresh)*

 

*DASHEN AIIAH* *WRITER’S* *ASSOCIATION*

 

 

_BISMILLAHIR_ _RAHAMANIR RAHIM_

 

 

*PAGE 1 & 2*

 

 

_KANO_

*Ƙauyen makoɗa))*

 

A hankali ta buɗe mayafin da ke rufe a fuskarta, da _BISMILLAH!_ ta sauka daga kan gadon da take, ɗakin take ƙarewa kallo ta ko’ina murmushi take ita kaɗai a zuciyarta ta furta _Ma Sha AIIah!_ “gaskiya iyayena kun fitar dani kunya a cikin wannan garin nasan duk faɗin garin nan babu wacce ɗakinta ya kai nawa haɗuwa da tsaruwa nasan yanzu na musu zarrah ta ko’ina, dan nasan babu sa’a ta acikin su dole ni ce nomba ɗaya a wannan ƙauyen ni ce sarauniya.

Fyaɗe Romantic and Sympathetic Hausa Novel 

AIIah ya saka muku da aIkhairi iyayana da kuka fiddani kunya, AIIah na gode maka, su Lami da a ke mana gori idan mun hau mata gado ku sauka karku karya min gado don kaf cikin ku babu wacce zata samu kamar gado na dan a burni a ka sai min shi,uhmmm! Lami lokacin ramuwa yazo dole na rama abinda ki ka yi min lokacin auren ki AIIah ya kaimu gobe yasin idan kika zomin gida baza ki haumin gadona ba, nima daga birni a ka sai min shi kuma nawa yafi naki tsada da kyau ai wallahi duk wacce tai min rashin mutunci lokacin auren ta to ga lokacin ramuwa ta yazo”.

 

 

Jamila tayi nisa cikin tunanin da take dan kuwa duk wannan maganganu da take yi acikin zuciyarta take yin su.

Ɗakin ta shiga zagayawa tana dariya ta taɓa wannan ta taɓa wancan

 

“wai yanzu wannan ɗaki na ne?

In yi abinda nake so babu mai hanani kuma fa duk abinda nake so shi zanci? Gaskiya aure ya yi arayuwa babu mai hanaka baccin safe ai, wallahi tunda yanzu na yi aure sai lokacin dana gada ma zan dinga tashi daga bacci”

Cigaba ta yi da surutanta sai da ta yi mai isarta kana ta nutsu ta dawo kan gadon ta zauna tana maida numfashi.

 

Magana tafara tana kallon ƙofar shigowa.

 

“Jamilu daga raka abokai shuru har yanzu baka dawo ba? Karfa ka manta nifa amarya ce yau a ka kawo ni gidan ka, ya kamata ka dawo kabani kazar amarci na wacce a ka ce tafi ko wace kaza daɗi haka dai naji amare suna faɗi koda gaske ne AIIah masani amma har ga AIIah na kosa naci kazar amarci na don AIIah Jamilu kai sauri ka shigo”.

 

Jin alamun kamar za’a shigo yasa Jamila saurin gyara zamanta, mayafinta ta ɗauko ta rufa sai da ta sake feshe jikinta da turare kamar yarda Inna Luba ta gaya mata idan zai shigo ta feshe jikinta da turare.

 

 

Shuru-shuru Ango Jamilu bai shigoba can kuma taji a na buga ƙofar kamar za’a ɓallah saboda tsabar bugu mamaki ne ya kama Jamila tasan wannan bugawar bana mai hankali ba ne, “wani wawan tsaki ta saki kana ta nufi ƙofar tana mita ƙasa-ƙasa ta yarda babu mai jinta…..

Tsaye ta yi a bakin kofar kamar baza ta buɗe ƙofar ba gashi daga waje kuma ba’a fasa bugun ba cikin masifa Jamila tace “waye! Wai don AIIah? Irin wannan buga ƙofa haka sai ka ce yaƙi”,cak aka tsaya da buga ƙofar ahankali ta buɗe ƙofar wayan babu kowa har waje taleƙa amma babu mutum babu alamar kowa tsaki taja tatura kofar ta dawo ciki tana masifa, zamanta ke da wuya aka sake buga ƙofar har bugun yafi na ɗazu wannan karan Jamila ƙofar tabi da harara.

 

 

 

***********

“To! ƴan’uwa abokaina na gode sosai da haɗin kan ku a gare ni naga masoya sosai a wannan biki nawa AIIah ya saka da aIkairi gobe idan AIIah ya kaimu lafiya sai kunzo cin taliyar amarya amma fa karku zomin gida da sassafe dan bada wuri zamu tashi daga bacci ba dan ni sabon ango ne”,Jamilu ya ƙarasa maganar yana yi musu murmushin tsokana.

 

 

Aliyu da yake gefansa ya kaima sa duka da hannu yana ce wa “to mara kunya ai sai kagaya wanda bashi da mata irin su mudi amma ba muba da fatan kagane ko” ya ƙarasa maganar yana nuna Mudi da hannunsa, shi dai Mudi sai dariya ya yi musu, don shi mutum ne wanda surutu bai dame shi ba.

 

“To! Ya isa abar maganar haka ni fa ba haka na ke nufi ba Aliyu naga kamar ka yiwa maganar tawa wata fahimta to koma dai menene ai nima yanzu mai gida ne ai, bara na barku haka ku gaida gida sai mun haɗe da safe nabar amaryata ita kaɗai a ɗaki nasan tana can tana jirana AIIah yasa dai ba ta yi fushi ba da ni ba”.

 

Cewar Jamilu wanda yana magana yana ɗaga musu gira.”

 

Nan abokai kowa da abinda yake faɗa ca sukai masa sai tsokanar sa suke kowa da abinda yake gaya masa, shi dai Jamilu dariya ka wai yake musu sallamah suka yi wa juna kowa ya nufi hanyar gidan su masu aure suka nufi gidan matansu marasa aure suka nufi gidan iyayansu.

 

Tafe yake yana gyara babbar rigarsa babu abinda yake sai murmushi ya ƙosa ya ƙarasa gurin Amaryar sa, tafiya yake yaji kamar ana binsa abaya cak ya tsaya da tafiyar ahankali ya juya ganin mai binsa koda ya juya baiga kowa ba da kewa ya yi ya ciga da tafiyar sa yana sauri yana waiwaye kamar zai arce da gudu tumtuɓe ya ci da wani ƙatan dutse sai ji kake ya zube ƙasa tum.

 

 

Cigaba a kai da buga ƙofar Jamila daga zaune tace “wai don AIIah waye! Wannan? ƙofar a buɗe take idan mutum zai iya shigowa to, _Bismillah_ ni dai wallahi bazan tashi ba haba matsalar zama a gidan surukai kenan duk subi su takura maka daga kawo ni yau har na fara fuskantar rashin mutunci da rai ni ko uban me zan musu oho koda yake inaga yara ne amma ai na buɗe banga kowa ba ɗazu to, ko bugawa suke sai su gudu to koma dai menene yasin bazan tashi ba in dai ba angona bane ya shigo kwayi ku gama Jamila bata da lokacin ku.”

 

 

 

*ASTAGFIRULLAH* *WA’ATUBH ILAIHI*

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment