Alkawarin Allah Hausa Novel Complete

Alkawarin Allah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

ALK’AWARIN ALLAH

 

_HUGUMA_

 

0️⃣1️⃣

 

 

“Allah ya taimakeki” lafazin da ya shiga kunnenta kenan,lafazin da a bakin mutum daya take jinsa,furucin da ko mutuwa tayi ta dawo bata jin zata kasa tantance daga bakin wanda yake fitowa dare da rana,a hankali ta waiwaya fuskarta qunshe da murmushi,yana tsaye daga bayanta kamar koda yaushe,wannan annurin data saba gani kan fuskarshi kowanne lokaci na nan shimfide saman fuskarsa,kwarjini cikar zati da haiba cakude saman kyakkyawar fuskarsa,batasan me ya shigeta ba,sai taji bacin rai ya sauko mata a take,b’acin ran daya sanyata ta dinga ja da baya,ja da bayan daya zama silar data soma ganinshi dishi dishi,yana tsaye hannayenshi goye a k’irjinsa,dubanta yake ba tare daya tsaidata ko yace mata komai ba,saidai annurin fuskarshi ya ragu cikin kaso d’ari zuwa kaso ashirin cikin d’ari.

Mummunan Zato Hausa Novel Complete

 

A firgice ta farka,sa’annan tayi zumbur ta miqe tayi zaman dirshan saman gadon nata,dukka hannayenta ta sanya ta dafe kanta dasu bayan ta dora gwiwar hannunta saman cinyoyinta,gashinta mai tsaho da sulbi ya sako ya rufe fuska da hannayen nata gaba daya,inda zaka ga fuskarta a sannan zazzafan hawaye ne ke layi saman kuncinta,inda ace tana da iko data hana kanta mafarkinsa,da ta isa data hanashi bayyana a duniyar mafarkinta,sam ko kusa ko alama bata da buqatarsa a duniyar mafarkinta kamar yadda bata da buqatarsa a zahiri

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” idan ka kasa kunnenka da kyau zakaji tana fada cikin muryar kuka.

 

Ta jima cikin wannan yanayin kafin ta iya lallashin zuciyarta,kanta ta dago sannan ta sanya hannayenta guda biyu ta tattare gashinta baya ta daureshi,kyakkyawa kuma sassanyar fuskarta datayi jajur ta kuma tasa saboda kukan data yi ta fito fes duk da qarancin haske da d’akin keda shi,a hankali ta zuro qafafunta qasa sannan ta yunqura ta miqe,kai tsaye ta nufi wata qofa dake kallon gadonta ta murda ta shige.

 

Mintuna biyar kyawawa tayi ta fito daure da alwala,ta bude ma’ajiyar kayanta ta fidda after dress da hijabi ta sanya,sannan ta nufi wani kebantaccen waje dake daura da gadonta tahau saman abun sallar dake shimfide a wajen ta kabbara sallah.

 

Ita kanta batasan adadin lokutan data kashe zaune saman abun sallar ba,don sam bata marmarin sake komawa barcin da tayi mafarkinsa a ciki,saidai shi bacci ba wanda yafi qarfinsa,saboda haka sanda yazo yayi awan gaba da ita bata shiryawa hakan ba,sai jingina da tayi da jikin gadon,carbin hannunta kuma ya silale ya fadi nan saman dardumar.

 

******* **** ********

 

Qarfe takwas na safiya ta kammala shirinta tsaf,tsaye tayi kawai tayi gaban mudubin tana qarewa kanta kallo,tayi kyau iya kyau,irin kyan nan mai sanyi,saidai wasu abubuwa da suka soma mata yawo akai take suka d’auke duk wata sauran walwala da taketa yunqurin d’orawa fuskarta,qarar kira daya shigo wayarta yaso janye hankalinta,saita zubawa wayar dake gefan mudubin ido tana kallonta ba tare data tabata ba gudun zuciyarta na qaruwa,bata kuma da niyyar hakan ma gaba daya,har ta qaraci b’urarinta ta katse,tamkar mai jira kiran ya katse din kuwa tayi gaggawar surar wayar ta kasheta gaba daya sannan ta jawo locker din madubin ta jefata ta maidata ta rufe.

 

Cikin kasala kamar wadda tayi wani babban aiki ta koma da baya ta zauna gefan gadonta tana ci gaba da kallon fuskarta cikin mudubi,ko kad’an bata qaunar ta raba wani abu ajikinta da zai sata tayi kyau,don dai kawai bata k’aunar bata ran anty zubaida ne,amma da bata ga dalili ko alfanun kasancewarta a haka ba.

 

“Auntyyyyy….” Muryar huda ce ta ratsa kunnenta,firgigit tayi tana dubanta kafin ta samu qaqaro murmushi wa fuskarta

“Anty ina kwana”

“Lafiya huda ta,kin shirya kenan?” Ta furta tana janyo yarinyar kusa da ita tana gyara mata daurin jelar rigar makarantar dake jikinta

“Ummi tace ki fito karmu makara”

“Muje na gama ai,fitowa kawai xanyi” ta fada tana miqewa,ta qarasa ma’ajiyar jakankunanta ta ciro daya daga ciki da zata dace da shigarta,sannan ta dauko wata daban ta zuge,ta fiddo da tarkacen ciki ta maida wadda zata fitan da ita sannan ta kama hannun huda suka fice.

 

A kitchen suka tadda anty zubaida tsaye tana shirya lunch box din huda,sanye take da rigar bacci da qaramin hijabi,kallo daya anty zubaidan tayi mata ta karanci yanayin data shiga,don haka bayan sun gama gaisawa ta shigar da qorafinta

“Yauma kinyi halin ne?” Murmushi kawai tayi wanda ya fito da ciwo tun daga zuciyarta zuwa labbanta,maimakon ta amsata saita shigo da wata maganar

“Yanzu anty dan Allah ta yaya zanci gaba da kwanciya kina tashi kina girki bayan kula da uncle aby da kike?”

“In kinason komawa kitchen sai kiyo qoqarin maida mode dinki yadda yake…..” Cikin seriouse ness ta waiwayo tana dubanta

“Cikin shekaru biyu mun soma yin nasara shahida….saidai bansan meke neman tarwatsa nasarar da muka samu muka yi ta tsahon shekara biyun ba” ta fada cikin nuna damuwa,shuru shahida tayi tana k’okarin kokawa da damuwar data taso mata,tun lokacin data san cewa suna rayuwa ne ashe cikin gari d’aya da anwar bata sake samun peace of mind ba,murmushin yaqe kawai ta jefi anty zubaida dashi,don bata son dukkan abinda zai sake jagula nutsuwar da take ta yunqurin samarwa kanta,shuru ne ya ratsa tsakani,ganin bata da niyyar magana anty zubaidan ta saki hannayenta tana dauko lunch boxs din huda ta miqa mata gami da cewa

“Shikenan,ku wuce ku karya karku makara,amma dai…..kota halin qaqa karki bari abinda ya riga ya gabata a rayuwarki ya bata future dinki,koda anwar ko babu ki baiwa kanki qwarin gwiwar xaki rayu,rayuwa mai inganci….”

“Zan rayu babu shi ne anty rayuwa mai inganci,babu batunshi ma cikin babin rayuwata” ta fada wani radadi na tasowa tun daga cikin zuciyarta har saman fuskarta,murmushin da ita kadai tasan ma’anarsa anty zubaida ta sako,shahida mutum ce me confidence,tana da qwarin gwiwa saidai har zuwa yau kaman hakan yaqi tasiri ga wannan lamarin,duk da koda yaushe tana yunquri da fadi tashin baiwa kanta wannan qwarin gwiwar,da idanu ta bisu har suka fice daga kitchen din ita da huda sannan ta saki ajiyar zuciya tana yiwa deejan addu’a a fili da zuciyarta.

 

Suna gama karyawar abby ya fito,sanye yake da jallabiyya,mutum d’an kimanin shekara arba’in da takwas,mai cikar kamala da fara’a,cikin girmamawa shahida ta gaidashi,ya amsa fuskarsa qunshe da fara’a yana fadin

“Teacher uban karatu….baku wuce ba kenan?,hala yau keda dalibar taki tare zakusha bulalar latti” murmushi ta fidda,tana mamakin abbyn sau da dama,wuta ne shi a wasu lokutan,amma wani lokacin yafi xuma dad’i

“Yanzun nan zamu wuce abby” ta fadi tana sab’a jakarta

“Gwara kam,don qila hadi(mai adaidaitan dake kaisu makaranta)yana waje yana jiranku na sanshi da himma” dai dai sanda anty zubaida ta fito daga kitchen din sukayi mata sallama suka wuce.

 

A bakin k’aton gate din *NOOR INTERNATIONAL ACADEMY* ya saukesu

“Daganan zan kai adaidaitan wajen gyara….amma zanyi qoqari in sha Allahu na dawo na d’aukeku”

“Karka damu,yauma muna shirye shiryen wasu abubuwa da za’a gudanar a makarantar,ina zaton ma zamu d’ara lokacin tashi,zamu bi ta haya mu koma”

“To na gode,amma du da haka idan na gama akan lokaci zanzo” bata sake ce masa komai ba ta kama hannun huda suka ratsa gate din makarantar zuwa ciki.

 

Dukansu ita da hudan sashen ‘yan nursery da primary suka nufa,saboda a nan ne deejan ta zabama kanta ta koyar,duk da tarin ilimi da Allah ya bata,wanda tana da cikakkiyar damar da zatayi lacturing amma bisa wani dalili nata ta zabi koyarwa a qaramin mataki na ‘yan nursery da primary,tun daga bakin section din yara ke gaidata cikin nuna qauna da soyayya,yayin da ita kuma take amsa musu cikin fara’a da jansu a jiki,sai da zata shiga staffroom sannan suka rabu da yaran,suka wuce azuzuwansu ita kuma ta shiga ofishin malamai.

 

Office ne madaidaici mai girma da tsari,duk da girman office din su uku ne kacal a ciki,makaranta ce da kallon farko.idan kayi mata zakayi tsammanin private ce irin mai tsadar nan,saidai sam ba haka abun yake ba,makaranta ce da wani shahararren d’an kasuwa ya ginata saidai akwai sa’ido da kulawar gwamanti akanta,duk da cewa shike dauke da duk wani nauyi na makarantar,kama daga school unifoarm,littafan karatu,abincin da yaran zasuci na break da dai sauran dukkan wasu lalurori,aqidarshi ce haka,yakan gina makarantar a duk inda yaga hakan ya dace,ya kuma hada hannu da gwamnatin garin donta tayashi lura da makarantar,bawai lura na su bada wani abu ba,a’ah,tsarin gudanarwa tsaro da sauran abubuwan da ya kamata,kusan kowacce qasa dake africa ya gina makarantu d’aya,saidai a inda makarantun suka fi yawa a nigeria ne yankin arewa,duk dalibin dake karatu cikinta yana farinciki haka iyayensa farinciki da kasancewar dansu a cikinta,saboda ta tsaru da tsari mai kyau,hakanan tana da dukkan wani qualities da akeson makaranta dashi.

 

Hidaya kawai ta samu cikin office din tana hada littafan dalibai da tayi marking,da alama tana da ajine qarfe takwas,murmushi suka yiwa junansu

“Kinso makara yau malama shahida”

“Yau da gobe hidaya….” Ta fada tana zaman kan kujerar teburinta.

“Sai Allah…” Hidayan ta qarasa mata kana ta gyara yafen mayafinta

“Mun tashi lpy….”cewar hidaya

“alhmdlh….mun godewa Allah”

“Ma sha Allah….zan wuce aji don Allah idan kausar ta iso kice mata ga kayan nan ta duba”

“Babu damuwa” cewar shahida,tana kallon hidaya ta bude office din ta fice sannan ta maida qofar ta rufe musu,saita maida kanta a hankali ta kwantar saman teburin dake gabanta,idanunta a lumshe,batason tuna komai,batason tunanin komai,tanason ta saita kanta kafin lokacin shigarta aji yayi,don nan da minti goma sha biyar periode dinta zai shiga.

 

***********************

 

“Dukkanin takardun na cikin wannan file din,sauran takardun da za’ayi amfani dasu a d’akin taron ma gab suke da kammala,na shiga dakin buga takardun na musu magana sunce nan da mintina goma da izinin Allah….engine ne yaso basu matsala” mutumin d’an kimanin shekara arba’in dake zaune saman d’aya daga cikin qawatattun kujerun dake shirye a qayataccen office din ya fada,yana bayanin ne ga dogo kuma tsayayyen matashin dake tsaye tsakiyar office din yana kai kawo a hankali,hannunshi riqe da dan madaidaicin glass cup,yayin da d’aya hannun nasa yake riqe da wata zungureriyar takarda yana dubawa,sanye yake da suit masu azabar kyau da d’aukar idanu,wankan tarwada ne shi,dogo wanda ke tafe da tsaho da kuma ‘yar qiba kadan,wadda kai tsaye ba zaka kirata da qiba ta zahiri ba saidai ace murjewar jiki,doguwar fuska gareshi wadda take cikakka,lumsassun idanu mai kama da wanda kejin bacci,saidai da girmansu idan ya budesu sosai aduk sanda yaso hakan,bashi da cikar gashin gira can,saidai gashin idanunshi a cike suke,siraran labba masu taushi,da qawataccen qasumba da aka gyarata aka rage mata yawa da fadi,ta zagaya ta hade da habarsa da kuma qasan hancinsa,kanshi saisaye ne wanda ya qawata fuskarshi saboda gyaran fuska da aka yi masa,kana kallonshi kasan tsafta hutu da iya dressing sun kama gida a wajensa,kana kallonshi kasan ba ma’abocin fara’a bane,sosai ya bada hankalinsa kacokam kan takardar hannunsa da gani kasan abune mai muhimmanci yake dubawa,yayin da ta wani b’angaren daban ya bada hankalinsa ga wanda ke masa bayanin

“Ina imran?”

“Yana sashen aje tsaffi da sabbin qarafa” kai ya gyada yana ci gaba da takawa sannu a hankali,har yanzu hankalinsa na kan takardar hannunsa

“Amma ba tuni na bada umarnin a cire wancan a sanya sabon da mukayo order ba?”

“Sorry sir…..engineer din ake dako,yaudai yayi alqawarin zuwa ya hada” ya fada cikin nuna tsantsar ladabi,bai sake cewa komai ba har na tsahon wasu mintina,sannan ya isa gaban teburinshi ya aje kofin hannunsa,ya taka zuwa gaban matashin dake zaune ya bude files din dake gabansa ya sanya takardar ciki ya rufe,sai a sannan ya dubeshi

“Karku wuce qarfe biyu ba’a gama kammala komai ba,bana son delay….”kafin ya gama fada qofar office din nashi dake aiki da lantarki ta bude da kanta,wanda hakan ke nuna muhimmin mutum ne zai shigo ciki,don ba kasafai take budewar da kanta ba sai bayan sakatariyarshi ta sanar masa ya bada umarni sannan ta bude din.

 

Dukkansu maida idonsu sukayi kan qofar,tun kafin ta qarasa shigowa ya fahimci wacece,hakan ya sanya ya maida idanunsa kan yaqub,don bashi da tabbacin yanayin da zata shigo dashi,don haka ya sallameshi

“shikenan….zaka iya tafiya” a bakin qofar sukayi clashing da ita tana shigowa,cike da girmamawa ya rusuna yana miqa mata gaisuwa,kaman yadda aka saba haka ta amsa a daqile,cike da izza,shan qamshi taqama da isa,yaqub ya wuce ita kuma taci gaba da takowa cikin office din.

 

Fuskarta qunshe da murmushi,hakanan idanunta na kan fuskarshi,taku take d’ai d’ai harta kusa cimmasa,yayin da shi kuma yake kallonta yana nazarin shigarta,babu laifi shigar tata tayau,doguwar riga ce mai wrapper,saidai kuma gajeran hannu ce,tayi rolling mayafi qarami a kanta,high hill ta saka a qafafunta,hannunta ba komai daga waya sai key din motarta

“It seems kamar bakayi farinciki da ganina ba M.A” ta fada a shagwabe tana kallonshi

“Uhummm….who told you?”

“Ba kowa….kawai yau nayi missing ganin cute face dinka,ka fita tun da sassafe ban samu ganinka ba,me yasa baka yi break fast ba yau a gida?” Takawa yayi zuwa d’aya daga cikin kujerun wajen yayiwa kanshi mazauni,itama yayi mata nuni da yatsa yana nufin ta zauna,sai data zauna sannan yace

“Me yasa zaki fito a irin wannan lokacin?” Farrr tayi da ido,tana jin wani dad’i na ratsata,a duk sanda ya nuna kulawa a gareta takanji babu ya ita a fadin duniya,sai data saki murmushi sannan tace

“Kai kadai na fito don na gani,kasan bazan iya wuni ban ganka ba” shuru yayi yana dubanta,can qasan ranshi yana jinjina wanne irin so nafisa ke masa?,kalamanta sunyi shigen kama da na wata,wadda ya soma qoqari da kokawar badda ta daga ranshi a yanzun da takeson taso mishi,don ko kusa bashi da sha’awar hakan,itama kallonshi take,tasan cewa wannan plan din nata ya d’anu,tanason dukkan wasu kalamai nata da yanayin kulawa yayi kama dana waccar da tasan ta taba wanzuwa cikin rayuwarshi,duk da tana baqinciki da cewa kwaikwayonta shine zai sama mata wani gurbi data dauki tsahon lokaci tana neman samu a zuciyarsa,duk da irin baqin fenti da qin jini da yayyabe tarihinta a zuciyarsa,amma duk da haka kishinta take fiye da komai a rayuwarta

“Naso na iso tun dazun sai aka samu akasi” ta katse kallon kallon da sukema juna,dan muskutawa yayi kadan,cikin muryarshi dake nuna halayyarshi yace

“Akasi?,name fa?” Sai data d’an jaa fasali sannan ta sake cewa

“Wallahi wasu ‘yammata ne suka so yiwa motata b’arna…”

“Me ya gamoki dasu?” Ya tambayeta kai tsaye yana ci gaba da dubanta,kafad’a ta daga sannan tace

“No,karka damu,na musu uzuri saboda a make suke,kana ganinsu kasan sunsan sirrin shan syrup,har zan hadasu da police sai kuma na wuce don bai kamata na b’ata lokacina akansu ba” sexy eyes dinshi ya lumshe gaba dayansu,yana jin wani abu mai ciwo na sauka saman zuciyarshi kamar ana d’iga masa wuta,wani boyayyen murmushi ta saki sannan cikin shagwaba tace

“Karka damu nawan….ba abinda ya faru dani,am safe…” Bude idanun nasa yayi kaman zai kalleta saiya kalli wani sashe na daban,yana sauke ajiyar zuciya a boye,a duk sanda yaji ko yaga labari irin wannan babu wadda yake tunawa sai ita,hakanan haushi tsana da qyamarta yakan sake ninkuwa a ransa.

 

“Yaya” ta kirashi tana son kauda damuwar data ziyarceshi,tunda haqarta ta cimma ruwa

“Yaune fa zamuje yaya?,don Allah karki sake cewa kana da wani uzurin”

“Saura minti goma sha biyar mu shiga meeting….saidai bayan mun kammala kuma” ya fada yana miqewa a hankali kai tsaye ya wuce bandakin dake cikin office din nashi ta bishi da idanu tana tantamarsa.

 

A hankali ya tura qofar bandakin sannan ya maidata ya kulle,gaban dan fanfon dake maqale a bango mai hade da madubi dake manne a samanshi ya isa,yasa dukka hannayenshi ya dafe sink din tangaran dake qasan famfon,qirjinsa na zafi haka zuciyarshi,ya jima a haka kanshi a duqe yana kokawar maida yanayinsa yadda yake sannan ya dago yana duban kanshi a madubin kamar baisan halittar kansa ba saiyau,maganganu yake da zuciyarshi,magana yake gayawa kansa wanda shi kadai yasan meke kai kawo a ranshi harna tsahon wasu lokutta sannan ya zare ‘yar samam suit dinshi ya daura alwala bayan ya tattare dogon hannun ta ciki,sai daya saka dan qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida rigar ya fito.

 

Da sauri ta jiyo a firgice suka hada idanu dashi,tana tsaye gaban wani dan qaramin akwatinsa da ake budeshi da lambobin sirri,wanda ta budeshi ta kuma soma fiddo wasu kayayyaki dake ciki,dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida kan d’an akwatin dake zaune dirshan daga can wani saqo na office din,baya taja cikin rawar murya muryarta can qasa tace

“Am sorry” baice mata uffan ya taka a hankali zuwa wajen,inda ta janye jikinta ta rabe a bango,ya durqusa ya dinga daukan kayan d’aya bayan d’aya yana maidasu muhallinsu,duk abu guda idan ya dauka yana jin kaman yana qarawa zuciyarsa nauyi ne.

 

Har ya saka wani abu ya sake cirosu ya kalla,suna nan kamar yadda ta bashi su,hatta da ledarsu itace dai wadda ta qullesu a ciki,d last thing data bashi a tarayyarsu,da hanzari ya maidasu ya rufe sannan ya sauya lambobin sirrin ya miqe zuwa gaban teburinsa ya amsa wayar daketa burari,sai daya kammala a nutse sannan ya aje,ya kalli nafisa data tsarki kanta tare da ala wadai da shegen qwaqwqwafinta da yakeson ya bata mata dukka plan dinta

“Ki wuce gida,saina qaraso” daga haka ya soma diban wasu files,dai dai sanda P.A dinshi ya shigo suka soma yunqurin barin ofishin,hakan ya sanya dole tabi bayansu jiki a sanyaye,a wajen elevator suka rabu,su suka hau wadda zata kaisu third floor ita kuma tayi qasa don barin companyn.

 

 

*GA MAI BUQATAR WANNAN LITTAFI ZAI BIYA NAIRA KACAL 200 YA SAMESHI,WANDA KE BUQATAR DUKKA ZAFAFA BIYAR DUN KUWA ZAI SAMESU NE AKAN FARASHIN NAIRA 500*

 

Post a Comment

Previous Post Next Post