Yar Gidan Yaddiko Hausa Novel Complete
YAR GIDAN YADDIKO👩🏻🦱*
*HAZAK’A WRITER’S ASSO*
Mai_Dambuce
Sadaukarwa Ga Aisha alto
*Page 1*
A garin Gumau, gari ne da fulani da manoma ƴan gudun hijira da suka fito daga Jos suke zama, sun fito daga barikin Ladi da Yalwan Shandam.
Garin Gumai wani yanki ne da ya had’a yankoki guda biyu, Bauchi da Jos. Toh duk abinda aka shuka sai Allah ya albarkace shi. Manoman suna noma kabeji, gurji wato cumcumbe. Latass, karasa, dan kalin turawa da ta hausa, kai har doya sunayi, ga masara wanda aka zuwa da manyan j5 ana saya.
Mutanen gumau akwai haɗinkai da taimakon juna.
Wannan knn…..
Hajiya Tabawa wacce yan garin ke mata lak’abi da Yaddiko, tsohuwace mai zuciyar niman na kanta, gata bafulatana ce amma mai zuciyar nima, dukda Y’ay’anta masu kuɗi ne, amma haka bai hanata niman nakanta ba, dan har noma take ga kiwon da take.
Ko maigari a gurinta yake niman aron kuɗi dan ɗan hasafi, duk wani mai ji da kuɗi a garin gumau yasan bai kai Yaddiko ba, dan karamin ɗanta babban ma’aikacene a custom, babban kuwa shima ɗan kasuwa ne,dan har gidajen mai gare shi. Allah ya albarkaci Yaddiko da yara huɗu biyu maza biyu mata sai dai ɗaya mace ta rasu.
Alhaji Imarana shine babba yana bauchi a Ibrahim bako yake da zama, Sai Alhaji Rabi’u yana zaune a abuja da iyalinshi shike karamin ɗanta.
Sai Hajiya Sadika da take aure a jos, da yaranta, sai Hajiya Aisha wacce ta rasu a shekaran da Yaddiko ta tsinci Yar gidan Yaddiko, ta sanadin hatsrin mota ita ɗaya ce aka tsinceta dan motar ta kama da wuta.
A duniya babu abinda Yaddiko ta tsana irin kukan Shatuwarta dan lokacin da aka sameta itace ta amsheta da saran ko danginta zasu tawo nimanta. Har yanzun shiru kake ji. Daukacin mutanen garin gumau suna shakkar jarabar yaddiko da yar gidanta, dan duk laifin da tayi hakuri suke aje gurin mai gari a gaya mishi.
Bagidajiya ce Hausa Novel Complete
Wannan knn bari mu duba yar gidan Yaddiko.
Faran faran kamar mi faret haka take tafiya tare da ɗaga kuran hanyar, sanye take da unifoam ruwan bula. Tsabar niman tada hankalin jama’a take ɗaga kuran.
A gaban Lamiyo mai kosae ta ci birki, kallon dandazon mutanen da suke bin layi tayi ta taɓe bakinta. Da mugun sauri tayi kan kaskon mangyaɗar take duk sukayi baya.
Akwai mai shayi a gurin irin yan nijar ɗin nan ne dariya yayi sannan yace.
“Yar gidan Y
addiko tinkiya sarkin tamɓele.”
Murmushi tayi sabida tana nazarin abinda zata mishi ai tasan nufin maganarshi.
Washe hakorana nayi ina kallon Ila da taburin shayinshi, girgiza kai nayi na koma da baya, na gyara zaman hijabina wanda yake a cukurkuɗe. Sakamakon tauneshi da nake, idan duniya tayi min daɗi.
Da gudu na antayo na dunbuli kosan tare da ture wasu mutanen suka ture taberin ila mai shayi, jin karan kwai kake tassssssss. Na cikawa bujena iska ina dariya,
Ina cikin tafiya, naga babangidan alhaji dauda ya sayo kamu, dama ina cike da ɗan banza da gudu nace.
“Ba burki burki.”
Kafin ya shalake harina tuni na banke ɗan wofi, na cikawa bujena iska.
Har zan wucce sai na hango gwaibar gidansu Ta asibi, kallon katangar gidan nayi na buga tsalle na kama jikin bangon na ɗanne kamar wata yar biri na tsinko, dayawa sannan nace.
“Ta asibiii ki hito gani nan na sace miki gwaiba alkur’anan nayi maganin masu dukiyar ɗan karuna.”
Aikuwa yan gidan suka fito asaba’in na dire abuna na arta a guje duk na zubda gwaibar,
Ban tsaya ba sai makaranta sabida ranar monday ne. Ina shiga naga firifet suna tsaren lati, fuska nayi na shige,” keee ” inji garbebe, turusss nayi na tsaya tare da cin wani burki na juya, tare da kallonshi.
“Zo nan yar kwal uba kinhi sauran yaran ne.”
Taɓe fuskan nayi tare da girgiza kai, nace.
“Ni ba yar kwal uba bace.”
Na faɗi haka tare da murguda ɗan mitsisin bakina.
Kaiiina sukayo, na tarta a guje gurin da ake asanbili na faɗa cikin ɗalibai take na rusa musu jerin gwanonsu ta hanyar zubewa a kasa.
Shiru hedimansa yayi yana kallona, mikewa nayi ina kallon mutanen gurin har da wani bakon da mukayi a makarantar.
Sake bakina nayi ina kallonshi, cike da al’ajabi sabida siririntakar shi, da kuma muninshi.
Gurin hedimansa naje na tsaya tare da rike bakina nace.
“Hedimansa wannan kuma waye kuka jajjuɓo mana mkrnta salon muyi mafarki yo kaga kugun kaman ayiwa sauro zanzaro, ga manyan idanu kamar an watsawa bududdugi barkono a idanu sam bai min ba, gaskiya a sauya shi dan matukar na cigaba da gani hi, kuka zanyi.”
“Kee bana son sakarci tahi maza kije layinki kaji yar koɗar uwa.” tashi nayi na bar gurin ina tura bakina.
Har aka gama aka sallamemu zuwa ajinmu, aji biyar nake.
Malam ayaga lutine ya shigo mana, kallonshi nayi tare da gintse dariyata na kalli katon cikinshi, ya cigaba da dariya a fili.
Cikin fusata yace.
“Shatuwa fito waje.”
Fitowa nayi na tsaya kerere.
Kallona yayi yace.
“Mi yasaki dariya.”
Nuna mishi tumbinshi nayi cikin dariya nace.
“Yaseen idan ka juya baya tamkar an sanyawa agwagwa buje, idan ka juyo tumbinka kamar tsohon kwaton da yagaji da duniya, sannan idan kana magana sai fuskarka tayi tankar kahin hainu.”
“Hhhhhh” yan ajin suka ɗauki dariya har da masu riƙe cikinsu.
“Ya isaaaaaa”
Ya buga musu tsawa.
Kallona yayi cike da bakin ciki yace.
“Amma ke anyi yar jakar uba, yau sai na kankaro miki rahin mutunci.”
Zaro idanuna nayi waje cike da tashin hankali nace.
“Malam ayaga luti, kayi hakuri.”
Fuskarshi ce tasake bayyana ɓacin ranshi yace.
“Kai kasumu jeka karyo min reshe.”
K’in tashi yaron yayi dan zao gwamance dukar malam ayaga luti da jarabar faɗata.
Buga mishi tsawa yayi ya mike yana kallona. Tsaki nayi sannan nace.
“Alkur’an yau hida ga wata nasan zaka zo amsa bahi a gurin ya diko kwarankwatsa sai na hanata baka.”
“Kaii kasumu dawo.”
“Ahe kunsan inna inji ɗiyoyin mayya.”
Komawa mazauni na nayi ina dariya haka ya gama lissafinshi ya fita.
Sai ga sabon malamin nan ya shigo, kallon yanda yar kugunshi nayi yanda yasha zanzaro gashi ya tsuke, amadadin nayi dariya sai na tsinci kaina da fashewa da kuka.
Wiwi kamar wacce akace ga yaddiko zata shura. Mamaki ne ya kama yan ajin, shima malamin duk ya ruɗe, yans tambayana.
“wai ayu kirayin.”
Ji nayi kamar ya kuntuttuma min ashariya nasaka hannuwana a tsakar kaina na fasa ihu, tare da zaman yan bori. Take wani yaro ys fita ta taga ya sheka a guje sai ofishin hedimansa ya labarta mishi yana ganin hedimansa ya tawo ya fita da gudu daga makarantar sai gidan yaddiko.
Tana zaune ta kunna radeyonta sai murzawa) tana kokarin kamo gidan raidiyon bauchi. Da gudu yaron ya faɗa kanta yace.
“Yaddiko kizo maza ga yar gidan yaddiko can tana kuka.”
Ai batasan lokacin da ta wacakalar da raidiyon ba ta finciko hijabinta, daga ita sai ɗaurin kirji. Fayau fayau……
Ina zaune malamai sun kewayeni kai sai ka rantse wani gamo nayi.
Ina jin muryan sanyin idaniyata na kara fashewa da kuka, nace.
“Yaddikona.”
Da sauri ta isa inda nake tace.
“Na shiga uku, ni tabawa Yan nan faɗa min waye yaci mutunci a cikinsu.”
Tana magana tare da watsar da hannunta.
Girgixa kai nayi cikin kuka nace.
“Yaddiko.”
“Na’am Yar nan.” tace min duk ta kagu taji mi yasani kuka,
Kallon Malamin nayi sannan nasake ɓarkewa da kuka nace.
“Yaddiko kintuna da dan kyalla.”
Cikin jimami ta yatsina fuska sannan tace.
“Ayya har yau bani manta mutuwar ɗan kyalla.”
Sharce majina nayi cikin shasheka, na kalli malamin nace.
“Toh yaddiko ni ban taɓa sanin a cikin mutane ana samun masu kama da zuri’ar ɗan kyalla ba, yaddiko kinga yanda suke kama da wancan malamin.”
Lalluɓo haɓar zaninta Yaddiko tayi cikin tsare gida ta ɓan tari goronta ta jefa a bakinta, “kurrsu” ta taune goron sannan tace.
“Yo banda abinki ai da ɗan kyalla da wancar mutumin kamar an zaga kara an karya ke dai banbancinsu wannan mutum ne ɗan kyalla kuma ɗan taure ne.”
“Wallahi kuwa yaddiko, kamar kinsan suna kama da ɗan kyalla har da ramarsu kuma shi ɗan kyalla ai cutar mi ma ya kahe hi?”
“Yo akwai wata cuta ce da ta cuce cutar barbara.”
Nahiga uku yaddiko, dama barbaran akwai cutarhi ce?”
Na tambayeta tare da zare idanuna.
“Awo baki sani ba, toh ki bari idan kika dawo zan faɗa miki.”
Juyawa tayi tabarni a gurin. Haka malamin yafita, bai koyar ba.
………. Ana tashi tara na ɗauki yar jakata da nabarta tun jumma’a na fita.
Dama ni bana zama a tashi dani, ina tashi tara nake gudowa.
Gida na dawo na sauya kayana na sungumi tayana na fita da ita ina garata.
Sai da na shigo maciyar dake gaban unguwarmu na sake tayar tayi kan, Lantana mai ɗan waken hantsi.
Kafin tayar ta isa nace.
“Lantana lantantan, ki kula da ga tayata nan zata ɓari miki da miyar ɗan wakenki.”
Kafin ta ɗauke kwanon miyar tuni taya ta bangaji, miyar ya kware, nace.
“Na rama tunda kika ce min ni hegiya ce ba’a san asalina ba toh ni kuma nasan asalin tayata.”
Zuwa nayi na ɗauki tayar tare da dangwalar miyar na suɗe….
Tattara kayanta tayi sai gidan mai gari.
Ina cikin tafiya na hango, abbasiya da tiren kayan miyarta da gayya na saita tayana na gara shi sai kanta…..
Aikuwa tayi ɓarin kayan miyar. Ina zuwa nace.
“Innarki tace bahin yaddiko bata biya ba, kuna da gadonta.”
Mikewa tayi a fusace tayo kaina na arta a guje, sai majalinsa ɗan izala. Birki naci daga nesa, na tsurawa wani bakon da sukayi ido. Kyakyawa dashi sai yar gemunshi yayi min kama da gemun.
Tauren yaddiko da aka sace, mai suna Sahabi………😹👌
*If i see comments maybe na cigaba*
_Da’iman-Abadan kuyi hkr na dakatar dashi_
*??YAR GIDAN YADDIKO *
*HAZAƘA WRITER’S ASSO*
Mai_Dambu….
_Kuyi hkr na dakatar da Da’iman-Abadan_👏
*Sadaukarwa Ga Aisha Alto*
Page…2
Kasake nayi ina kallon yanda mutumin yake magana, ɗan gemunshi nan sai wani motsi yake, girgiza kaina nayi cikin jin daɗi nace.
“Ahe a cikin mutane akwai masu kama da akuyoyi yo dubi gemun wancar kaman ta sahabi Allah sarki.”
Tattara dukkanin karfina na lafta a guje, ga uban kuran da na tadda. Kallona malam Dalha yayi ya girgiza kai yace.
“Ina ga gidan Yaddiko kuke nima, ga can takadarirrayar jikanta can tana tadda kura.”
Tunda naga ya nuno ni, nayi kwafa a raina nace.
“Nasan za’a rina.”
A nutse na iso gurinsu na kalli malam dalha nace.
“Naga kana nuno ni? Ince dai lahiya? Da fatan ba wani hairrin za’a ƙulla min ba.”
Kallona bakon yayi cike da mamaki, kardai Shatun Yaddiko ce haka.
“Ke tafi can shashasha, baki kukayi daga birni.”
Kamar wacce aka ce min ga baki daga kasar waje na wani washe jajjayen hakorana nace.
“Yo kace baki mukayi daga binni, toh kardai a kintsa musu wani hairrin dan nasan a garin ga banda Yaddiko ba me kaunata duk masu kaunata dan kuɗin Yaddiko suke kaunata, mutum yayi magana Kwarankwatsa idan yazo cin bahi nasa Yaddiko ta hana hi.”
Bai ce komi ba, yace.
“Toh bawan Allah ga Yar gidan Yaddiko nan zata kaiku har gida.”
Mika mishi hannu bakon yayi suka gaisa, ni kuwa na leka hannun cikin katsalanda nace.
“Karka wani bahi cin anci, kawai kazo muje.”
Da mamaki ya kalle ni, ni kuwa sai wani buɗe hancina nake, irin na zama wata a garin gumau.
Cikin daddaɗar muryanshi yace.
“Toh kishiga motar mana.”
Juyawa nayi na kalle shi sama da kasa, nace.
“Yaddiko ta hanani higa motar mutane dan tace yan han jini ne suke cewa a higa motarsu, kagaku biyo ni sannu ahankali zan kaiku Unguwar gabar.”
Gaba nayi abuna shi kuma ya shige cikin motar, ya kalli abokin tafiyar yace.
“Man kaga yanda Shatun Yaddiko ta girma kuwa.”
D’ago kanshi yayi ya kalli mai maganar sannan yace.
“Sai ya.”
Dake yasan halin abokinshi bai kuma cewa komi ba yajasu suka bi bayana.
Wani irin tafiya ake mai cike da abin takaici da ban haushi kamar abin arziki na ɓoye hali, muna cikin tafiya na hango. Audu ya sayo manja a leda, sai sauri yake zai kai a musu abinci nasha gabanshi nace.
“Yawwa nakama ka.”
Zaro ido yaron yayi cikin tsoro yace.
“Shatuwa, kiyi hakuri Iyata ta aikeni nasayo manjan alale ne.”
“Kai tafi can haihaihai, kawai sai na durje bakinka da ka zagen kace min tinkiya.”
Hakuri ya shiga bani, na dalla mishi mari, kafin ya dawo hayacin shi na sami tsakiyar kanshi na zuba mishi rankwashi, sannan na ture shi manjan ya fashe.
Duk dukar dana mishi bai ji zafi ba kamar fashewar manjan na kuwa tsinka a guje, karshe fitowa sukayi a motar suka ɗaga yaron, da yake kuka. Biyanshi kuɗin manjan sukayi.
A can gaba kuwa, ina zuwa dandali naga talatule da tiren gyaɗa, Talle da kwanon dafaffiyar masara, xuwa nayi na tsaya musu nace.
“A bani alkoro ko nayi aikin.”
Banza suka min nasake nanatawa basu kula ni, fakansu nayi na wafauce gyaɗa da masaran wanda yayi sanadin tintsirewar kayansu baki ɗaya.
Koda na isa bakin kasuwa samu nayi ana dambe tsakanin. Hudu da Sanda. Sun yasar da kayansu na talle a gurin, dariya nayi nace.
“Mahaukata yaseen sai na ɗauki, yar yau da kosan rokon.”
Buɗe kayan nayi na ɗiba, aikuwa suka yo kaina na falfala a guje,
Ban tsaya ba sai a gida, nasami bakin har sun iso, ko inda suke ban kalla ba na buɗe gidan na shige abuna.
Kai tsaye bishiyar maina na haye abuna, dan naji kamar Yaddiko bata gida.
A kofar gidan mai gari kuwa, takanas ya tura aka kira Yaddiko ta zauna.
Shiru fadan tayi, Mai gari yace.
“Yaddiko!!! Mutane suna kawo min karan jikanyarki fa, zan koreta a garina dan ta buwayi mutanen gari.”
Shiru tayi sannan tace.
“Toh Yallaɓai ta’adin nawa tayi?”
Nan aka shiga mata lissafi bata damu ba, ta ciro kuɗinsu ta biya sannan ta mike cikin bala’i tace.
“Banda rashin mutunci har nice za’a kawo ni gaban Mai gari toh a kwaryan cin tuwonku dan sai kunzo cin bashi zan. Kankaro muku ɗiban albarkan da kuka min, masu son ganin bayan shatuwa kuwa sunci kaya kurwata kurrrr.”
Kaɗe gyaleta tayi tabarsu a gurin, tayo gida.
…….A kofar gida ta ci birki tace.
“Kaiii Mutanen bauchi da Abuja barkanku da zuwa kushigo sannun Mahar da Najibu.”
Tura kofar gidan tayi, duk suka shigo cikin gidan. Falonta takaisu, nan tashiga hidima dasu.
Ina sama abuna cikin kwanciyar hankali da nutsuwa nake barci a jikin reshen.
Fitowa tayi taga takalmina a kasar bishi, tace.
“Shatuwa, sauko kije gidan Mai tafasa ki amso min nayi dambu ace.”
Leko kaina nayi nace.
“Toh Yaddiko.”
Dirowa nayi na amshi naira hansin ɗinta na fita, ina cikin tafiya muka haɗu da Sahura.
Kallonta nayi na kauda kaina dan ta cika gulma da tsirfa.
Da sauri tayo kaina tana washe hakora tace.
“Yawwa, Shatuwa dama ina nimanki, Da wata labari”
Harara na banka mata. Tare da taɓe bakina nace.
“Munahufa, yau kuma wata haihaihar ce tayi, magana a gabanki har kika zo gayya min.”
Sosa kai tayi alamun jin kunya.
“Hmm dama Sa’aden gidan Tabayye ita min wai Yaddiko tsintarki tayi.”
Taɓe baki nayi, ina kaɗa kai nace.
“Hikenan dama.”
“A’a wai ke baki da asali a titi aka tsinceki gobara ta cinye iyarki da Babanki.”
Juyawa nayi cikin jin haushi nace.
“Wato Sa’aden da take zuwa cin hinkafa a gidanmu hine zata ci amanata, hikenan zan kamata dan kwal ubanta zata gaya min inda taji labarin ni ɗin yar tsintuwa ce.”
Juyawa nayi ban kara cewa komi ba, na dawo gida ina shiga Yaddiko tace.
“Shatu ina tafasar.”
Kallonta nayi na ajiye mata kuɗin na shige gurin dabobinta na zauna. Gaban uwar garke na fashe da kuka sosai.
Dabbobin dake sun san halina zuba min ido sukayi, jikin Yaddiko na rawa tayo garken cikin kuka nace.
“Kyau kinji wai nice yar tsintuwa, na higa uku na lalace. Wai iyata da babana wuta ta cinyesu. Kuma kunsan wacce ta faɗi haka kawata Sa’ade fa.”
Aikuwa dabobbin suka ce min “Maaaaaaa”
Cikin yarda da abinda suka ce nace.
“Wato fansa ya tabbata ga maciya amana ko.”
Aikuwa uwar garke tace min.
“Mahaaaa.”
“Kaiii wankesu kin gama min, komi dole naci kwal ubanta.”
Cike da mamaki Yaddiko tace.
“Wata yar wofi ce tace iyarki ta kone.”
Tura mata baki nayi nace.
“Sa’aden tabayye mana, hi yasa ban sayo miki tafasar ba kawai ki girka musu hinkafa da…”
Rike bakina nayi nace.
“Ki kawo kuɗi naje mahauta na sayo musu nama dan Yaseen baza’a taɓa min, kaji ko zabi ba, dan nayi musu alkawarin kare rayukarsu, kuma da zaran na bari aka yankasu tankar cin amana ce.”
Gyaɗa min kai tayi sannan taciro min jaka guda ta bani tace.
“Gashi ta jaka guda.”
Da sauri na sungumi tayata, na fita ina gara tayar.
Har naje nasayo namar na dawo kawai na ratsa ta maciya, da gudu na shige da tayata kan kayan miyar Nata’alla, tussss suka zubo tare da fashewa.
Kara kaimin guduna nayi naje naja rumfar salele take ya zube akanshi,
Kafin mai kifi ya ankara na jefa mishi tayar a kaskonshi, na arta a guje da laidar naman.
“Kutare mana yar kwal uba, kaii Yar gidan yaddiko kin addabemu”
Inji Nata’alla
A hanyar dawowa na gamu da Sa’ade ta bayanta na shakota nace.
“Dan kwal uwatai hine kikayi gulmata ke nan bazan samu masu faɗa min bane hegiya karamar munahuka, da hegen kananun idanu kamar na y’ayan tsak’a yau zanci mutuncinki yanda ya dace.”
Kamar zata fashe da kuka. Yara sai ce min suke.
“Shatuwa!!!”
Aikuwa kaina yayi gingime. Bansan lokacin da na kifeta da mari, Cikin zubda kwalla tace.
“Ayya shatu kiyi hakuri Innata ce ba lahiya.”
Taɓe baki nayi na tureta na kara gaba abuna.
****
Ina isa gidan mika mata sakon, sallamar mutane yasani lekawa naga mutanen da nayiwa ɓarna a hanyar dawowa tace suka biyo ni, taɓe bakina nayi nace.
“Yaddiko gasu can sunzo ɗaukar fansa.”
“Allah ya shiryeki”
Tace bakinta na ɗaki, Y’an gwabjejjen yafito sabida sallamar da ake, gani ni kuma na haye sama.
Fita yayi yaga yawar mutanen da suka kawo karana.
Mika musu hannu yayi suka gaisa nan yace.
“Lafiya bayin Allah.”
Fitowar ɗan me gemun ya kalle shi alamun tambaya.
Nata’alla ya mishi bayani. Duk bakinsu ɗaya.
Ajiyar zuciya suka sauke cikin gida Ya shigo ya buɗe jakarshi ya fidda kuɗi ya fita kofar gidan ya basu, akan su raba. Tsagal ina sama nace.
“Yaseen sai nasake muku barnan.”
D’ago kai yayi ya tsura min ido ranshi na kara ɓaci, zabga min harara yayi. Ni kuwa na murguda mishi baki.
Lumshe idanu yayi, cike da bakin ciki yau shi ake harara.
Bai ce komi ba ya shige kallona mai gemƴ yayi aikuwa na sauko daga bishiyar na zauna a gaban Yaddiko na fashe da kuka.
Kallona duk sukayi cike da mamaki, kallona tayi a kiɗime tace.
“Keee Yar nan mike damunki.”
Nuna mata mai gemun nayi nace.
“Wallahi, Yaddiko kama yake da Sahabi mijin Kyauu.”
Zaro ido tayi tace.
“Kuma haka ne fa, Kaii Najibu kaji wai kama kake da Dan taurena da aka sace dan shima gemu ne dashi kaman kai, gashi kyakyawa kamarka.”
Amadadin yaji zafin maganar da nayi sai ya sake murmushi yace.
“Yaddiko kina fama da Shatu haka ta girma, dama.”
“Eh wallahi tagirma shekara goma sha ɗaya fa, dan ma bata da girman kashine. Ga bakin mutane dake damunta wallahi duk sun saka mata ido.”
Dariya yayi mara sauti yace.
“Na lura mutane sun sanya mata ido, Shatu amma daga yau ba shatu zan cigaba da kiranki ba sai Ummuna Aisha, zaki bimu binni.”
Matsawa jikin Yaddiko nayi ina matsar kwalla nace.
“Kwarankwatsa bani zuwa ko ina ko Yaddiko.”
“Eh amma ai zamu, dan an kusan bikin Yar gidan Sadika.” tace min.
Gyaɗa kaina nayi ina jan majina tare da tsotse nakan hancina, Murmushi yasake yi, a karo na uku. Mike ɗayan yayi yana yunkurin amai….
Tsaki nayi nace.
“Mai gemu miye sunan wancar.”
“Suna na Ya Najib, shi kuma Ya Maheer, ba mai gemu ba.”
D’aga kai nayi ina kallon sama, sannan nace.
” ai kai sunanka bai da wuya Ya Najib, hi kuma Ya Mayyer toh dama hi mayyer toh kuce mihi mayye kawar wani.”
Juyowa yayi a fusace yayo kaina nayi cinyar Yaddiko…..*?
?
*??YAR GIDAN YADDIKO🏻🦱*
*HAZAƘA WRITER’S ASSO*
Mai_Dambu….
_Kuyi hkr na dakatar da Da’iman-Abadan_👏
*Sadaukarwa Ga Aisha Alto*
Kyautar Farko gareku…
Deejer A Chiroma
Ummu Hajra
Ummy
Maryam Candy
*Da kuma member Musha karatu Mmn Sadiq, Action Lady, Nancy, Da Baby Maryam, Yar Yaddiko tace Mahaaaaa😹*
_Akwai Wacce tayi min sticker na suna jiran Yar yaddiko Ina miki fatan alkhairi nagode_
Page…3
“Kaiii Mahar bana son ɗibar albarka, yarinyar ce xaka nemi murkushewa, gafara can.”
Yaddiko ta tare shi kafin yace zai iso gareni.
Leka shi nayi tare da zaro harshena nace.
“Yo Yaddiko Yaseen sunar mayye fa, kaii gaskiya kice a sauya sunan.”
“Kee tafi can bana son rigima.”
Sauka nayi a cinyarta na shige gurin Akuyoyina dan naji haushi gwaleni da Yaddiko tayi.
Ina shiga ciki naga faratu ta zabga min harara.
“Kwal Ubanca Faratu ni kika harara.”
Kaɗa min wutsiya tayi alamun tayi ɗin, kallon Uwar garke nayi cikin jin haushi nace.
“Yau rahin mutuncinku kaina zata kare.”
“Burrrrrrr.”
D’an maraya yayi min, cikin jin haushi nace.
“Kundun Ubanku, kuma a bakin abincinku.”
Ya Najib na tsaye sai dariya yake yana karawa, ganin na fito a fusace yasashi riko hannuna kwacewa nayi na fashe da kuka.
Ina da wata ɗabi’a shine kishi bana son naga wani ya kwace min abuna ko yakusanci abinda nake so, daga zuwan mayyen can har ya lashe zuciyar Yaddikona.
Rikoni yayi yace.
“Faɗa min mi aka miki.”
Cikin zallar yaranta nace.
“Daga zuwan mayyen can har Yaddiko ta fara min faɗa, bata taɓa min faɗa ba.”
“Toh kiyi shiru, zan baki alawar birni ko baki sone.”
Cikin jin haushi nace.
“Kaga yau har faratu hararata tayi.”
Rike baki yayi cikin dariya yace.
“Amma Faratu bata kyauta bawa Aminiyarsu ba, amma naji kince a bakin abincinsu na rana.”
Gyaɗa kaina nayi, kallona yayi sama da kasa, bani da makusa tsaf nake kamar ba yar kauye ba. Toh taya zanyi kazamta tunda Yaddiko ce ke min wanka, kuma har almiski take ɗigawa a ruwan wankar, Ni ba fara bace ni bakace amma ina da kyau mai shiga rai, gani da gashi har goshina zuwa saje na ya kwanta, sannan bana kitso dan tun ban kai haka ba aka daina min kitso, amma kullum sai Yaddiko ta wanke min gashina ta tufke, sabida gashine dani kamar ɗiyar turawa nan kuwa bakace ni.
Duk wani abu sabon yayi a jikina ake fara gani, sannan yaran gari, kai nifa ba’a gasa dani.
Komawa kasar bishiyar mukayi na zauna ina kallon yanda Yaddikona ke girki cikin gwanancewa da tsafta.
Dariya nayi nace.
“Mai kama da Sahabi, Ina son Yaddikona ta iya girki.
“Hmm Ummu Aisha haka zaki je gidan mijinki ki masa girki mai daɗi ko.”
Washe hakorana nayi, farare wanda kullum sai Yaddiko tasa gawayi ta gurje minshi.
Nace.
“Hmm aure kuma Yar karama dani.”
Basar da zance yayi ya cigaba tambayata a mkrnta nan yaga tsabar surgududu, dan bana fahimtar komi, sai tsabar shiririta da shirme, mikewa yayi sakamakon fitowar Mayye, ɗaga kaina nayi na kalleshi ya zabga min harara, ni kuma na murguda mishi bakina. Nace,
“Kurwata kurrrr, babu mayyen da zai iya cinye ni.” zaro ido yayi ya kaɗa kanshi ya ficce nima na tashi na ɗibo ruwa a gwangwani, sai lokacin Yaddiko tace.
“Shatuwa zoki rike min miyar nan sallah zanyi.”
“Ki jirani nayi sai nazo na amshi girki.”
Kamar da gaske nagama jika jikina na wucce ciki.
Karku damu kanku da sanin irin sallata, dan na doka goshi a kasa yafi sau goma, sannan na kwaɗa sallama nafi. Waje,
“Shatu wannan dai ba sallah kikayi ba. Kwaɗa goshi a kasa kikayi.”
Tace min.
Kamar zan fasa ihu nace.
“Yaddiko sallahce mana, nayi naka’a sama da goma da asuba nayi goma ynx nayi goma, an jima nayi goma.”
Shigowarsu Ya Najib yana dariya yasani cika fam, shikan mayye baikula mu ba yayi shigowarsa, magana yayi min naki kulashi. Sai ya shige falo abin shi,
Ganin ba kowa nasa ludayar miyar na tsamo nama, nasaka a bakina ina tauna tare da yarfe hannuna.
“Sannu ɓarauniya.”
A gigice na juya muka haɗa ido, tura bakina nayi bayan na kumbura shi nace.
“Kurwana kurrr.”
Ban karasa ba yaxo inda nake ya kama kunnena ya murɗa, sai da nafasa ihu, kamar gidan zai tashi.
Da sauri Ya Najib yafito, gani na yayi ina rike da kunnen sai kururuwa nake da birgima, dakyar Yaddiko tashafa addu’a tafito zani a hannu tace.
“Lafiya Najibu.”
“Wallahi Yaddiko ban sani ba.”
“Wayyo kunnena na higa uku nalalace zai kaheni Yaddiko Mayye ne yaja min kunne na.”
Murmushi Ya Najib yayi ya fita waje, dan yaga yanda fuskar Yaddiko yakoma na angry bird.
Zaunar dani tayi cikin ɓacin rai taci ɗammara sai waje.
“Mahar kwal Ubanka wallahi sai na taka har bauchi naje naci Ubanka babu abinda ya dame ni, ɗan banza mugu kashe min ita zaka, Yarinyar da batakai sha ɗaya ba. Zaka murɗa mata kunne ai dole takiraka Mayye, ɗan banza mai kiran mutanen farko ko kunya baka ji ba l, kasa mi yar da batafi hanjin cikinka ba ka murkushe mata kunne, ka cigaba Allah ya bamu yawan rai, dan baka san inda rana zata fito ba kuma ka tattara shirginka kabar min gida.”
Masifa take tana, watsa hannu kamar zata mare shi.
Juyawa tayi fuuuu, abinta.
Boyayyen murmushi yayi tare da cigaba da danna wayarshi.
“Maheer baka kyauta ba, Yarinya ce fa, ka zage karfinka ka murɗa mata kunne.”
“Sai akayi Ya? Kai baka ga irin wahalar da take bawa Yaddiko bane, indai kana son taimakonta toh ka rabata da Yaddiko dan wallahi tsohuwar nan mutuwa zatayi da lafiyarta dan takaicin wancar abar kasheta zaiyi, wai tana sonta so ko shirme. Bana son shiga hurumin da banawa ba, amma matukar kuna son ta kintsu sai ka kaita makaranta, tayi nisa da Yaddiko.”
Zaro idanu Najib yayi cike da tashin hankali.
“Rufa min asiri, kana tunanin Yaddiko zata yarda ta bani Ummu Aishane. Ai kasan abinda bazai taɓa faruwa ba kenan.”
“Zai faru mana. Yanxun muka faɗa da ita, kai dazaka je mata da cewa kayi istahara Yarta tana cikin tashin hankali, idan basu bar garin Gumau ba kasheta Mayyu zasu take zata amince. Dan ko wancan watar sai Abban Abuja yayi maganar rashin dawowarta bauchi, tunda nan da shekaru biyar zai ajiye aiki.”
“Toh Ya zamuyi da Ummu Aisha kenan, dan Wallahi shirme da shiririta take babu wani fahimta.”
Harara ya doka mishi sannan yace.
“Najib kana da kayan haushi malaman da suke zuwa amsar bashi hannun Yaddiko. Sune zasu matsawa jikarta tayi karatu, ina cewa ɗazun fa tace maka daga gidan Mai gari take, taje biyan ɓarnan da wancar gafiyar tayi. Sannan aka idanunka na biya kusan dubu talatin kuɗin ɓarna, shawara kasan yanda zakayi Yaddiko su dawo bauchi.”
Yana gama faɗar haka ya diro akan motar ya shige gidan.
Shiru Najib yayi kuma yana hango gaskiya ziryan amaganar Maheer.
****
Ranar Jumma’a da wuri Yaddiko tayi min wanka, shadda tasa min ruwan hoda na zauna na ɗauko kayan kwalliyata. Man stalle mai gurguwa nake shafawa, sai hodata baɗata jaka, da kwalina gyatuma raɗau. Sai jan bakina magic, wato da na gama shafe jikina da man inda nayi ɗan wake da jikina, sannan na shafe hodar fuskar nan kaman akuya taci gari, sai na ɗauko gyatuma raɗau ɗin nan naja wata taɓarya, nan wai nayi ja gira,
Sannan na ɗauki magic ɗin nan na goga abakina bayan na bishi da bakin gyatuma raɗau, sannan nabi sauran sararin fuskana na ɗiga mishi kwalin.
Wani murmushi na sakewa kaina, sannan na mike nasaka kayan. Fitowa nayi zanje Yaddiko ta ɗaura min kalabina, Najib ya kalle ni, murmushi ƴa sake tare da shafe fuskarshi. Tunda suka zo banda makaranta da nake zuwa wanda shi yake kaini, baya barina fita ko ina sabida niman tsokana da barna. Yau kuma dake jumma’a ce dole ns fanshe kwanakin da nayi bana fita.
Gashin kaina Yaddiko ta fara saka igiya buhu tattaro gashina ta tufke min shi.
“Masha Allah Yaddiko, ashe Ummu Aisha haka take da gashi.”
Dariya nayi wanda yasa laɓɓana lutsawa ciki.
Kalabin ta ɗaura min, sannan na ɗauko gyalena da takalmin robana nasaka na fita a guje.
Garammm nayi karo da shi, komawa nayi zan faɗi yasaka hannunshi ya finciko ni, a tsorace na kalle shi, sai ganin jan bakina da rabin kwalliyata a jikin faran shaddarshi. Kwace hannuna nayi na fasa ihu.
Tare da zubewa a gurin ina cewa.
“Kwarankwatsa sai ka biyani kwalliyata, jibi jan bakina a jikinka Wayyo Allah na sai kabiya ni.”
Tsallaka ni yayi ya wucce abinshi da nagaji da ihu tare da kukan da ba hawaye na mike salin alin na bar gurin.
……..
Dandali na nufa inda nasami dayawan Yan matan sun caɓa kwalliya, komawa gefe nayi ina wani cin magani. Wai ni nan akwai yan binin a gidanmu kar a kawo min reni.
Shiru na zauna naki kula kowa, ina niman hanyar ɓarna. Hango Yar gidan bala kansila nayi tare dasu Sa’ade da sahura, taci gayu da wani kayan ɗiyoyin turawa.
Suna zuwa inda nake suka fashe min da dariya suka wucce.
“Kan buuuu.” nace.
Na mike da sauri tasha gabansu, nace.
“Kunci kanfifirintin kwal ubanku, har nice zakuwa dariya ke sahura munahuka. Ince ke kika kawo min gulmar sa’ade tace min Yae tsintuwa, hegiya munahuka alguguna ɗiyar wofi har hinkafa na baki da jar miya, ranar laraba kuwa. Haiyi da barodi, tare da soyayyar kwai kika ci a gidan mu. Ga dagedage namar da kika ce har kike ce min kinje gidan Bala kansila Innarsu Haira bata kyauta sai mugun rowa, hegiya ko ba haka ba hine zaki min dariya kin janyowa kowa na garin gumau bala’ina.”
Ina gama faɗar haka na arta a guje nayi kan masu sayar da kayan gurin nabi takai abuna,
Duk wanda na samu a hanya, da talle ko garin tuwo tunkuɗe su nake. Ban kyale kowa ba har rumfar masu rake sai da na tunkuɗe musu. Kafin na iso gida,
Tun daga kofar gida na saka hannuna a tsakar kaina na fasa ihu na shiga.
Ina isa tsar gidan na tuma tsalle nayi zaman yan bori na kwanta na fara birgima.
Daga Yaddiko sai Najib suka tawo kaina, a kiɗime suke tambayata lafiya.
D’ago kai na nayi nace.
“Yaddiko!!”
Sai kuka.
“Yo wani ɗan iskane ya taɓa min ke.”
“Yaseen Yar gidan bala kansila ce aka saya mata Kayan turawa hine suke min kallon uku saura kwata, kwarankwatsa na fasa saka wannan kayan, tumbur zan zauna.”
Cire kayana na shiga yi ina wurgi dasu, dagani sai ɗan kamfe. Shiru Yaddiko tayi ranta na kara ɓaci wato gasa za’a fara da Yar Yaddiko toh sunyi karya.
Dan kowa yasanta da zuciyar niman nakanta, shi yasa ake cewa gayawa mai zuciya biki ba mai dukiya ba.
Lalitarta ta ɗaga ta ciro dubu huɗu, ta ce min.
“Kee Shatu mike muje kasuwa na saya miki kayan.”
Kallona Najib yayi ganin yanda na buga wani tsalle, tare da fashewa da dariya.
Takaici ya gama rufe Mayyer, yana ɗaki yaki ma fitowa balle yasan mi mike tattaunawa…
Najibullah Ibrahim……… *👩🏻🦱YAR GIDAN YADDIKO👩🏻🦱*
*HAZAƘA WRITER’S ASSO*
Mai_Dambu….
_Toh banda abinku Yar Gidan Yaddiko ta tsani gasa_
Najibullah Imran shine cikaken sunan Ya najib Mahaifinshi ne Custom, yana zaune a abuja. Autan Yaddiko kenan. Ya najib yana da kanne mata uku, Shamsiya, Sai Samha da Kubra.
Yana karatun degree ɗinshi na biyune a jami’ar khartum nakasar Sudan, shi da Ya Maheer.
A burin Iyayensu su haɗasu auren zumunta, dan za’ayi baikone tare da bikin Yar Hajiya Sadika.
Inda aka haɗa Ya Najib da Binta Yar wajen Hajiya Aisha, sai Maheer za’a haɗa shi da Sailuba Yar gurin Hajiya Sadika, duk sai sun karasa karatunsu za’ayi bikin.
Yanzun ma hutu suka zo shine aka turosu mutafi bikin kafin a fara.
Ya Najib yana da hakuri da kawaici ga kara, shi mutum ne na kowa bashi da wata damuwa, a duniyarshi kuma bai da aboki sama da Maheer, ga rikon addini dan yana daga cikin ɗaliban makarantar gwalaga, matashin ɗan ahli sunnah. Wanda ya haɗa ilimin Addini da na boko. Yabi jikinshi da jininshi ko wandonshi ka kalla zaka tabbatar da haka.
……..Maheer Ibrahim cikaken sunanshi shima jikan Yaddikone, miskili babu ruwanshi da kowa, ba ka taɓa gane gabanshi balle bayanshi, Yana da kane biyu. Ammar da Hafsa.
Ba ruwanshi da shirgin mutane, asalima idan da cinkoso a guri fita yake yi.
Mahaifiyarshi Zainab Yar nabardo ce, babantane hakimin can.
Maheer da Najib suna karatun likitancine, Maheer ta ɓangaren mata da kananun Yara, Najib kuma Likitan zuciya ne, komi nasu ɗaya sai dai banbanci halaya, Maheer yana shan taɓa. Najib kuma ko warinta baya so.
……Hajiya Sadika tana da Yaronta irin marasa jin nan dan yana cikin matasan yan sara suka, Faruq ya addabi Yan unguwarsu kandahar zuwa bakoro dan ma mahaifinshi bai kyaleshi haka ba.
Hajiya sadika tana da yara bakwai Faruq, Sailuba, Alawuya, Habibu, Laweeza, Firdausi, Sai Ahmad.
Yaran Hajiya Aisha kuwa, biyar ne.
Binta, sai Fauziya, Wasila, Nuhu. Da Jamila.
Wannan sune jikonki Yaddikona idan aka tara nidi kuma har da aminaina dan suma na kala musu dangantaka da Yaddiko(😎)
…… “Maza saka kayanki muje ni za’a gayawa zuciya daɗin abin kafin ya zama kansila nan yake zuwa amsar bashina har yau ina binshi dubu goma, ɗan banza hala sai a lahira ya biya.”
Dariya nayi na washe hakorana, saka kayan nayi, zamu fita. Ya Najib yace.
“Ai Yaddiko kika kuskura kika saya mata kayan nan tabbas mayune zasu cinyeta, dan jiya nayi mafarkin indai ba ɗauketa akayi daga garin nan ba. Toh ba shakka turen aljani zasu mata, da kuma nayi istahara sai naga tabbas zasu lashe miki shatuwarki ke burinki bai cika na niman Iyayen….”
. “Kaiii Najibullahi karka karasa, Yar yaddiko kinji abinda malam Najibu ya faɗa muhakura idan muka je bauchi na saya miki kinji Yar nan.”
Komawa gefe nayi na fasa ihu, tare da zuɓewa kasa ina kuka. Mai cika kunne.
“Wayyo na higa uku na lalace, hikenan an fasa min kayan turawa, toh Kwarankwatsa. Tsirara zanyi yawo.”
Daga Yaddiko har Ya Najib sun ruɗe, rarrashina suke amma ina botsarewa.
“Duk wanda ya fasa yawo tsirara a gidan nan ya rena kanshi, idan kin isa ki gwada na gani sai na miki zanen dodo a jikinki.”
Ya buga min tsawa da har gagi, bansan lokacin da na shige jikin Ya Najib ba, tare da sauke bahagon ajiyar zuciya.
D’ago ni Yayi yaga idanuna sun kafe.
D’ago kanshi yayi yace.
“Man ta suma fa.”
“And So what.” ya shige abinshi, ai jin batun na suma Yaddiko ta bishi ɗakin cikin balbalin masifa tace.
“Mahar kaci ubanka wancar katon tsawar da ka buga mata, da izinin waye, munafuki dama kazo kashe min itane..”
Shiru yayi ya juya mata baya, a waje kuwa ruwa, Ya Najib ya shafa min.
“Haba jama’a yarinya karama idan ba’a lallaɓata wata uwar za’a mata, ka zauna kana buga mata tsawa yanzun ga tashin hankali mayu na bin min kurwan yarinya Toh kai Najibu ina zankaita.”
“Eh toh,,, Yaddiko ni a tunanina mu wucce da ita bauchi, a can sai ta cigaba da karatu ba.” Ya ce mata,
Shiru tayi cikin damuwa can tace.
“Wallahi bazan iya barin Yar gidan Yaddiko a wata duniya ba sai dai mu tafi tare.”
Mamakin Hikimar Maheer yayi wato cikin ruwan sanyi yasaka yaddiko ta koma bauchi.
Ajiyar zuciya na sauke, a hankali na buɗe idanuna na kalleshi, shima ni yake kallo. Murmushi ya sake min, tare da ɗagani na jingina a kirjinshi. Bugun zuciysrshi naji wanda yake tafiya da karfi, na juya nace.
“Ya Najib baka da lafiya ne? Naji nan ɗinka yana bugawa.”
Jan hancina yayi yace.
“Kece Sanadin heartbeat ɗina.”
Fitowar Maheer a ɗakin yaxo ya wucce mu, Yaddiko tabishi da cewa.
“Ga mutum har mutum amma zuciyarshi ba taushi.”
“Yawwa Yadikko ya zamuyi da dabobinki sai a kira mahauta su saye.”
“Kut wasu dabobin za’a saida, ba dai Aminan kwarai ba, dabobin da basa munahunci da gulma kullum kaunata suke, hine zaka kira Mahauci yasaya. Naga wanda ya isa Yaseen sai nasaka hi asara kwarankwatsa kaii.”
“Gaskiya Yar Yaddiko ta faɗa bazan iya saidasu ba sai dai mu tafi tare da su ko shatuwa.”
Maheer na kofar gida, yana jin hayaniyarmu bai ɓata lokaci ba ya nufi mahauta, yayi musu talle dabbobin. Aikuwa aka sami har mutane biyu suka biyo shi, muna kan takardamar sai gasu kai tsaye gurin dabbobin suka shiga nan suka gani ciniki ya faɗa, ganin ana fito dasu yasani mikewa.
Wani malalacin kallo ya bini dashi, ya sani tsura mishi ido ba tare da tsoro ba, nace.
“Kayi min rai karka sa ayanka min akuyoyina wallahi na musu alkawarin kare rayukarsu.”
Kallon yayi ya kauda kai, shi kan mamakin yanda nake zaro magana yake.
Zaman dirshan nayi ina kallon awakina ana fita dasu.
Sha kanshi Ya najib ya ji ba daɗi sai da yayi mishi magana, yaki karshe ma fita yayi ya bar gidan Ya najib ya shiga rarrashina.
Zazzaɓine ya rufe ni, ina ji ina gani an saida min dabobbina. Ran Yaddiko ya ɓaci masifar da tayiwa Maheer ba iyaka..
Washi gari haka na tashi dan ko abinci dare banci. Da safe dakyar nayi sallah ina gadon mai rumfar Yaddiko.
Kallon Maheer Najib yayi cikin sannan ya kauda kanshi yace.
“Man, nifa ina da ra’ayin mata biyu.”
D’ago kai Maheer yayi yana kallon shi, sannan yace.
“Miye hujjarka? naga ko Iyayenmu basu tara mata biyu sai kai.”
“Eh toh ta biyun dai bata wani kosa ba, Yar gidan Yaddiko ce dan Allah ya gani zan tsaya mata tayi karatu, kuma zanyi kokarin ganin wani bai shigo rayuwarta ba sai ni ɗaya, wanda da zaran nace ina sonta babu damuwa.”
“Hmmm Yayi kyau Allah yasa mudace.”
Abinda ya faɗa mishi kenan bai kuma ɗaurawa da komi ba.
***
Bayan karyawanmu ne Yaddiko tashiga makota tayi musu sallama, nikam bana hum bana humhum. Haka muka shige mota Yaran unguwarmu sai murna suke. Jaraba zata tafi tabarsu…..
Karfe goma muka shigo bauchi, kai tsaye ibrahim bako muka wucce unguwarsu Ya Maheer.
Gidana ne babba har da part kusan huɗu, ɗaya Part ɗin Abban Bauchi da Iyalinshi, ɗaya kuma na Abban Abuja da iyalinshi, sai ɗaya gidan Maheer da Ya Najib, wanda suma aka raba su, sai Part ɗin Yaddiko.
Sai can wani guri na daban da aka ware dan wasan Yaran, sai kuma wani rumfa da naji kukan dabbobi da gudu nayi gurin, ina lekawa na hango faratu da Uwar garke.
Wani irin daɗi ne ya kamani wani murmushi na sauke musu tare ds kunshe bakina na shige gurinsu ban damu da ɓata gurin ba na rungume Uwar garke nace.
“Yaseen na ɗauka ancinye ku ahe kuna raye, toh maza mu tsaya muyi wakarmu.”
_Salama salam dudum_
Aikuwa suka ɗaga kafarsu tare da gwara gansu ya bada dudum.
_Yar Yaddikonku ce take muku salama salam dudum_
Suka sake haɗe goshinsu ya bada _dudum._
Ni kuwa na samu abinyi ina tikar rawa a tsakiyarsu
_Salama salam Dudum_
💃💃💃💃💃💃💃
_A yanda na tsammata ahe ba haka bane salama salam dudum_
_Dudum_
_Nice me kaunar da gaskiya salama salam dudum_
_Dudum_
_Kaunar ta ratsa jinina salama salama dudum_
_Dudum_
_Duk wani munahuki da d’an bakin ciki Allah kahe mana hi salama salama dudum.”
_Dudum_
“Yanzun zamu sake wakar girgije ruwan gora da fatan zaku tayani.” ” Burr” ɗan Maraya yace min.
Hararanshi nayi uwar garke ta tayani make shi,
Nayi muku wakar kenan.
Aikuwa Yar kyamus ta kaɗa min bindinta.
_Girgije- girgije – girgije ruwan gora arziki na Allah baba yaki dillina inna taki dillana namuje mu taka rawa sai yafi yan Bori._
_Kwal-Kwal-kwal_
Suka buga kofatarsu da kasa,
_Ranar Faratu_
Sai gata tafito ta wani buga kofata a kasa.
_Kwal-kwal_
_Ranar Auren Yar kyamus_
_Kwal-Kwal-_
“Keeeee Fito a cikin dabbobin nan Wallahi kika addabemu zaneki zanyi kuma na saida dabbobin mahaukaciya aljana kawai banda aljana irinki wake saka dabbobi rawa.”
Fita nayi a guje bansan inda zan nufa ba wani lungu na nufa a gidan naje na zauna tare da fashewa da kuka,
Tsaki yayi ya tare da barin gurin.
“Man Ya akayi kuma kaida kace zaka sayar da dabbobin sai kuma gasu a bauchi.”
Najib ya jefa mishi tambayar.
Tsaki yayi ya kaucewa tambayar Najib,
Sider ɗinshi ya nufa bai kuma bin takan kowa ba.
Cikin gida Ya Najib ya shiga, nan yaji Yaddiko tana cewa bata ganni ba fa ina suka kaini.
Maheer ya fito daga wanka kenan Najib ya shiga mishi akiɗime.
“Man Ina shatuwa? Bata cikin gida fa.”
“Ok na ɓoyeta ne?”
Amsar da ya bashi knn,
“Kaii wani irin mutum ne mara adalci Yarinyar da bata san guri ba ta ɓata kace min ka ɓoyeta ne.”
“Ka Najib fita min a ɗaki bana son fitina kaina na ciwo.”
Ran najib a ɓace ya fita daga ɗakin.
Zama yayi ya shafa vaseline ɗinshi, sannan yasaka riga da wando, kananun kaya wando black jeans sai rigar fara, anyi katon hoton G&D.
Takardunshi ya janyo ya fara buɗewa, amna tuna yanda Najib yafita yasashi buga tsaki ya fita daga ɗakin.
Ganin yanda hankalin kowa ya tashi yasa shi, tuna inda na bi da yakoreni.
Dafe goshinsa yayi dan yana sane da lungun baya rasa macizai.
“Kana cikin rayuwar farin cikinka sai an shigo maka da damuwa.”
Lungun ya nufa, anan yasame ni na haɗe kaina da gwiwana ina kuka,
Gefena kuwa wani katon macijine ya fasa kanshi.
Cak ya tsaya yana kallonmu, tabbas idan ya koma baya tunda har macijin ya hangoshi zai razanani macijin ya sareni. Idan kuma ya saka kanshi ina jin motsinsa zan firgita.
Wani tunani ne ya zo mishi, ya koma sanɗa yana bin bango, jin motsi yasani ɗago kaina, ina mikewa Maheer na tsalle gefena a macijin yakai sara.
😂😂😂😂😂😂😂😂😂
*Da fatan kun chashe*
*??YAR GIDAN YADDIKO🦱*
*HAZAƘA WRITER’S ASSO*
Mai_Dambu….
_A gaskiya Na fahimci yanda kuka sakawa Yar Yaddiko idanu toh kuyi ku gama babu wanda zai ci Hinkafa da Jar Miya_
Page….5
Haɗani yayi da bango ya rikeni sosai, ɗago kai nayi zan ɓare bakina naga yanda ya runtsa idanunshi, har jijjiyar goshinsa sun mike.
Sake kai saran macijin yayi yana rike dani, a hankali nace.
“Ya Mayyer, sauke ni.” buɗe idanunshi da sukayi ja yayi ya hankaɗa can na faɗi ya juya ga macijin wanda yake hankoron kai mishi sara na uku, cikin hikima ya cafke wuyar macijin, dan dai naga ya duka, mikewa yayi yana kallona. Aikuwa na fasa ihu na juya a guje,
Daure macijin yayi akafar da ya sareshi yafito a hankali. Sai lokacin Naga mutanen gidan sunfito da gudu na ɗanne Yaddiko, ina niman maɓoya tace.
“Lafiya kuwa! Shatuwa?”
“Yaddiko maciji xai cuna min.”
Rungume ni tayi, zata fara masifa. Ganin halin da yake ciki yasa ta zaro idanunta, tana cewa.
“Kaiii ku kaishi asibiti mana.”
A gigice Hafsat da Ammar sukayi kanshi,, da sauri Najib ya janyo mota har inda yake, ya shiga ya xauna.
Da gudu najib suka fita tare da Ammar,suka nufi asibitin bauchi.
Nikam ina nasan mike faruwa, part ɗin Yaddiko muka nufa da ita, na shige falonta wanda girmanci yayi wani ɗaki biyu. Sai manyan kujeru ga manyan labulaye, tsakiyar an sanya wani jar kafet,
“Yaddikooooooo”
A kiɗime tazo, tace.
“Yar lafiya.”
” Yaseen wannan jar abar tsarkiyar tsoro yake bani.”
Na nuna mata kafet, tsaki tayi tace.
“Ga ɗakinki can, ki shiga. Akwai komi a ciki.”
Ta juya tabar ni a gurin hankalinta yana kan Mayyer, taɓe bakina nayi bayan na kumburashi na shige ɗakin.
Da gadona ɗan karami, komi nawa dai daini ne,
……..A can asibiti kuwa anyi sa’a dake ɗhyaje da macijin take aka duba ruwan alluran dafin kalar macijin, aka mishi sannan suka cire a hakoran macijin, suna mishi dariya.
Ban ɗakin na shiga na karewa ko ina kallo, kafin na shikawa Yaddiko kira.
“Yaddikooooo”
Da sauri tashigo ban ɗakin kallonta nayi ina murmushi nace.
“Kahi zanyi.”
Shiru tayi sannan tafita can sai gasu tare da Hafsat, bayani hafsat tayi min yanda zanyi amfani da komi, ta kai hannunta gashina da na sake shi a kafaɗana.
Koda nagama abuna na wanke na kuma buɗe masa ruwa na kura mishi ido,(😂 Sowiee banyi dan na ɓatawa wani rai ba)
Tsuka nayi nace.
“Hima kahin sai an kai hi, inda zai zauna.”
Bahun wanka na cika ruwa na shiga ciki na zauna, can na sake kwallawa Yaddiko kira, tana shigowa nace.
“Yaddikona ki min wankar mana.”
Soso na taje ta ɗauko min, sannan tazo ta saɓeni, sam ban lura da damuwarta ba, itama kuma bata damu da nasani ba, tana gama min wankar na fito nasaka kayana, na fito falon na zauna ganin nafito ta kama hannuna ta kaini cikin gida, gurin Mahaifiyar Mayyer mace mai kirki da sanin ya kamata. Tana gani na tace.
“Aishatu ce ta girma haka Yaddiko?”
“Eh itace Safiya, Ya jikin yaron nan hankalina yaki kwanciya.”
Duba wayar hannunta Mamansu Maheer tayi cikin murmushi tace.
“Yaddiko da sauki fa tayu zuwa gobe ma su sallame shi, ai yaje musu da macijin kuma an sami maganin gubar.”
Shiru Yaddiko tayi, amma zuciyarta ba haka yaso ba.
Abinci aka kawo mana, tuwon shinkafa miyar ganye, murmushi nayi nace.
“Yaddiko ga abinci nan, ni ba yanzun zanci ba.”
D’aukar abincin akayi zuwa gidanmu, nan Mamansu Maheer kejana da hira, har nasake da ita nuna min ɗakin Hafsat tayi na shige, sannan tace.
“Yaddiko ko zan kaiki ki ga halin da yake cikine.”
Ajiyar zuciya tayi tace.
“Haka yafi.”
Mikewa Yaddiko tayi tasaka hijab ɗinta Mama kuma ta shiga ɗaki ta ɗauko key mota, tace.
Mufito.
Haka muka nufi asibiti, sai kale kale nake, mun same shi yana zaune suna hira da Ya Najib.
Muna haɗa idanun shi ya zabga min harara, ni kuwa na koma jikin Ya Najib na murguɗa mishi baki.
Lumshe idanunshi yayi, kaman yanda yasaba, idan na bashi haushi. Kowa ya gaishe ni ni kuwa na koma jikin Ya Najib ina mita.
“Ya Najib hine ka tahi kabarni? Ni ɗaya na.”
Nuna min gadon Maheer yace.
“Baki gaidashi.” ya faɗa min tare da tsare ni da ido.
Kwal kwal nayi da idanuna ina kallonshi nace.
“Ince muna higowa ya harareni.”
“Toh tunda haka ne babu ruwa na dake, daga yau mun daina abota.”
Juyawa nayi cikin kuka nace.
“Ya jiki?”
Basar dani yayi, kamar bai ji me nace mishi ba, sai da Mama tace.
“Bana son wulakanci tace maka ya jiki kayi banzada ita.”
Taɓe baki Yaddiko tayi cike da takaici tace.
“Zan sami Iro ya shiga tsakanin shatu da Mahar. Dan kiyayyar tayi yawa.”
“Kiyi hakuri Yaddiko nima zan tsawatar mishi.”
Haka muka gama zaman asibitin babu abinda ke haɗani da shi sai harara.
Tunda muka dawo ban kuma damun kaina da naje asibitin ba, har Hajiya Sadika tazo ita da Yaranta marasa kunya, suka shigawa Yaddiko ɓarna da bincike, ni kuwa nace ban iya ji ba.
Ranar da aka sallamo shi suka cika gidan, ni kuwa na tafi gurin dabbobina da nagama share musu ɗakin n Saka musu abinci na fito.
Bishiyar maina gidan na haye, abuna na zauna ina kallon shige da fecce mutane,
Can na diro sakamakon ganin Sailuba, tana barbaɗa abuna cikin abincin da aka bata takai ɗakinshi.
Toh dake bansan kan gidan bs, nayi zamana ina jiran Ya Najib can kuwa sai gasu sun shigo, kowa yafito tarɓansu lafewa nayi jikin bishiyar abuna.
Har suka shige cikn gida sun daɗe a can suka fito Ya najib da Binta, Sailuba da Maheer dan zuciyata bata raya min na kirashi da Yaya ba.
Mikewa zubur nayi ina washe baki nace.
“Ya Najib, karka ci abincin da wancar takai can gidan Yo kwarankwatsa tayi barbaɗe.”
Ina gama faɗar haka nasakai na wucce ina wakena.
Shiru Sailuba tayi tana kwafa, ko raka Maheer ɗin ɗakinshi batayi ba ta juya, riko hannunta yayi cikin miskilanci yace.
“Muje ki bani abinci naci.”
Muryanta na rawa tace.
“Kaje Yaya ni kaina na ciwo.”
Bai damu ba yajata suka shige har part ɗin jikin binta yayi matuƙar sanyi kallonta Najib yayi cikin takaici bayan su Maheer sun wucce yace.
“Meye Ma’anar haka, Yarinyar can bazata yi karya ba, dan na fahimci halinta nima kin saka min abu a abincine.”
Girgiza kai tayi cikn kuka tace.
“Bani da Uwa, sai mahaifi da dangin mahaifiyata, sai kai da kashigo rayuwata wallahi Ya Najib ko cewa kayi bazaka zauna dani kaɗai ba zan zauna na tallabi maraicin Kanena na Iswear bazan iya ciyar da kai wani mugun abu ba dan ina sonka tsakani da Allah ne.”
Bai ce mata komi ba yayi gaba shi kuwa Maheer suna shiga cikin falon ya wucce yabarta Sailuba ranta na kona.
Jin yaki fitowa ya tashi tafita daga part ɗinshi ta nufi cikin gida ranta a ɓace.
Nima da nashiga gidan, tun a bakin kofa, muka gamu da Hajiya Sadika wata uwar harara da tabini dashi ya sani komawa da baya..
Dama gurin Hafsa zan kuma ta koroni, gidan Yaddikona na koma abuna ina shiga nasami Yaddiko sai faɗa take da Yaran sun mata ɓarna, ban kai da shiga ciki ba, baji an fincinkoni an maka da bango ta shiga jibgana, aikuwa Yaddiko ta rufeta da duka itama.
Tana kuka nima ina kuka, sai gashi ya shigo yana zuwa ya zare hannun Yaddiko a jikin Sailuba, ya mai da ita gefe yazo a zare ni daga makura da tayi min, idanuna sun firfito waje.
Jan hannunta yayi suka fita, ni kuma nayi kan Yaddiko ina kuka.
“Yaddiko mu koma Gumau kawai bana son nan ɗin ba daɗi.”
Shafa min kai tayi, ta mike dani sai cikin gida.
……”Miye Hujjar ki na dukan dukan Yarinyar, dan nasan haka kawai baxata faɗi abinda bata gani ba.”
Kuka ta saka mishi tare da mikewa zata bar falon, ya buga mata tsawa.
“Kika kuskura, kika fita baki faɗa min hujjar dukan Yarinyar ba zan karya ki.”
Shiru tayi ta cigaba da kuka, can yace.
“Ainyi na farko kar a kuma na biyu get out.”
Kwanciya yayi akan kujera yana me dafe kanshi…..
***
“Sadika! Dama kin kawo yaranki ne dan su kashe marainiyar Allah, maza ku tattara ku bar min gidan ɗana kafin raina ya ɓaci dake.”
Dake tasan halin Yaddiko ba musu ta haɗa kan Yaranta suka bar gidan.
***
Tsakanina da Mayye ba sauki, dan hantara na yake musaman ya shiga alamarina duk abinda za’a min na jin daɗi ya hana, kitso da banayi ranar da mai kitson su Mama tazo tasa Hafsa ta kirani, ina zuwa tace.
“Zauna maza a kitse kanki nan da bakya son kitso.”
Zaro idanu nayi nace.
“Yaseen da zafi, kuma kuka zanyi. ”
Lallaɓa ni Mama take ina ɓotsarewa.
Kayan ciye ciye aka ciro min, na zauna na fara ci ana taɓa kan na fashe da kuka.
“Assalamun Alaikumun.” muryanshi da bata cika amo ba gauraya falon haɗiye kukana nayi, kallonmu yayi ganin yanda naketa juya kan, ita kanta mai kitson ta gaji.
Zagayowa yayi ya zauna, ya ciro wayar radio ya ajiye a gefenshi, nutsuwa nayi ina ambaliyar kwalla, Mama tace.
“Ina kuka shigane tun safe.”
Karamin tsoka yayi sannan yace.
“Wancar gilgil ɗin muka fita nima mata makaranta dakyar muka samu, Dolphin Maria college. Dakyar suka bata aji shida dan tana gamawa special school kafin Madaki zata wucce Dan mun gama komi da Nafi’u koda bama nan, kinga nan da wata bakwai kenan.”
“Bodin school fa, anya kana da imani kuwa kaida Yaddiko.”
Komawa yayi ya kwanta tare da banka min harara.
Ina ji ina gani aka kitse min kaina, wanda nasakawa Yaddiko rigima a tsafe, dakyar Ya Najib ya lallaɓani ya ɗauke ni muka shiga kasuwar Winti, ya saya min kayan turawa tare da katon Yar baby da tiddy, pink.
Ga chocolat da ya cika min katon leda dashi, tun acan nake ci, har kuma iso gida,
Ganin yanda Najib ke fito min da kayan da ya saya min ga katuwar Yar baby da Teddy, Maheer yasa hannu ya kwashe teddy ya wucce dashi, kuka na fasa ina mika hannuna ya bani teddy na fir yaki kulani, saima wuccewa da yayi dasu cikin gidanshi.
Rarrashina Najib yayi naki shiru karshe, ɗaukana yayi ya kaini gurin Yaddiko, nayi kuka sosai. Haka na hakura, na lura nice baya kaunar nayi farin ciki.
…… Ranar Monday aka bani kayana saka, bakin wando da riga fari. Sai ɗan kwali.
Na fito har cikin gida na shiga sai najine wata iri, naje na karya sannan Mama ta zuba min wani a lunch box, muka fito da Hafsa wacce take aji biyun scndry.
Haɗuwa mukayi dashi na kauda kaina kaman bansan yana gurin ba Hafsa ta gaishe shi, ni kuwa na ɗauke kaina.
Mota muka shiga aka fita damu, ina zaune a baya hafsa na gaba ta juyo tace.
“Aisha mi yasa baki gaida Yaya ba, yana da kirki fa.”
Kwalla ne suka zubo min nace.
“Bansan mi nayi mihi ba ya tsaneni, Yar tsanata da dolina ya amshe fa, kuma duk abinda yasan ina so hanani yake yi koda bashi zai min ba, akan mi zan gaihe hi.”
Dariya take har da rike ciki tace.
“Toh wallahi karki fara magana a cikin class ɗinku dan dariya zasu miki dan baki da shi da sha.”
Shareta nayi, na cigaba da share kwallana.
***
Sati biyu da fara zuwana makarantar boko da Islamiyya suka koma, nan na sami sauki na cigaba da jan faɗa idan muka je islamiyya nice dukar wanca marin wanca cin zara.
Kullum sai a zane ni a aji ko a waje, gashi ina ɗaukar karatun fa, amma naki nutsuwa Yaddiko kuwa bata fasa fita islamiya tana kankarowa Malam ɗiban albarka ba.
Lokacin da mukayi jarabawa aboko na faɗi, sabida point ɗina, haka na mai maita aji.
Ban wani damu sabida bani da kyakyawan tushen karatu. Shi yasa da aka ce na faɗi ban ji komi ba.
Wasa wasa, naki mai da hankali a karatun boko sai da na kusan shekara biyu dukda aji shida aka sani, fa.
A shekaran suka sake zuwa hutu, tunda Ya Najib yazo ya duba takardu na sai kawai ya nima min malamin lesson dan kafin yabar kasan yake son na fara scndry.
Koda aka kawo malamin bana zama zanje fitsari zan je shan ruwa, Maheer da Ya lura da haka sai ya dawo zama a gurin karatun dashi ake tashi. Dan najib Ya koma abuja hutunsu na wata uku ne sabida wani cos da zasu shi yasa., kuma next month zamu gama primary.
Sosai na maida hankalina dan ko gudun cin mutuncin wannan mayye……
Ranar da bani da lesson har murna nake.
…………
*👩🏻🦱YAR GIDAN YADDIKO👩🏻🦱*
*HAZAƘA WRITER’S ASSO*
Mai_Dambu….
*_Masu Yalwata da zunzuruntu ɗaukaka basu cika damuwa da kiran kansu suna dashi ba, sai dai daga mu’amalarsu zaka fahimci haka, Wannan zance nakine Aunty Gimbiya Allah Ya karawa Mai Martaba nisan Kwana Ya kare zuri’arshi da sharrin masharranta Nagode sosai Kina raina_*
Sadaukarwa gareki Aisha Alto.
“`Gabaki ɗaya wannan book ɗin na baki Kyautarshi Aunty Nice“`
*Jamila Safyanu, Maman Ihsan, Asma’u ka’oje, Maman Khairat da sauran Member Taskar Mai Dambu ga shafinku amma gaskiya team ɗin Najibullah nake, Mayyer yaci kanshi😂*
____________*Queen Indo nd Deejah A Chiroma, idanunku yafita akan Mayyer😂*
__________________________________
Page…6
Dake yau babu hegen Iyamurin fita nayi makota, na sami wani yaron Me suna Abbati, ya rakani dajin angasawa. Dan naji wai Sailuba zata zo gidan, ni kuma ina cike da ita kamar Yanda tamin duka shekara biyu baya yanzun ni kuma zan ɗauki fansata….
“Yaseen ni Yar Yaddiko ba gaba da gaba ko tabaya sai an hirya”
Tunda na lura mayyer baya gida sai na sulale muka fita, kallonshi nayi nace.
“Abbati karara nake so zanyi amfani dashi.”
Zaro ido yayi cikin al’ajabi yace.
“Yar Yaddiko! Karara fa, taɓ wallahi bazan iya tsinko miki ba.”
“Dalla can banza kawai nuna min zakayi na tsinko.”
Gyaɗa kai yayi yace.
“Basai munje angasawa ba, nuje bayan house akwai a can”
Aikuwa muna nufi bayan house muna zuwa na samu a kasa laidar da na ɗauko nasaka hannuna ciki na ɗauki kararan nace.
“Hikenan banza matsoraci.”
Bai ce min komi ba, ya wucce muka dawo dan yasan sai na makeshi.
Muna shigowa naga ta sauka a napep dariya nayi, nace.
“Barka da zuwa sansanin Yar Yaddiko.”
Wucceta nayi abuna ko kallon bata isheni ba, har zan k’ule tace.
“Keee Yar tsintuwa.”
Dukda bani da hankali yanzun na fara fahimtar kalmar Yar tsintuwa bata cikin kalma masu daɗi, juyawa nayi, ina kallonta.
Kallonta nayi daga sama har kasa, sannan nace.
“Yo ba gwara ni Yar tsintuwa bace, ke da baki iya zaman gidan Ubanki fa.”
Ina faɗar haka nayi shigewata, gurin Yaddiko, da take sauraran radio, kular gabanta naja naga tuwon laushi miyar karkashi murmushi nayi najuyi miyar karkashin na fice a falon, nasan duk rintsi sai tazo duba mayyer ban wani ji ɗar ba, nage na zuba miyar a matakalar biyun karshe da kuma barandar.
Na koma na ajiye filet ɗin, fita nayi naje na kirawo Abbati, Abdul da Fatu, abokaina ne. Na ɗauko taburma muka zauna muna hira bayan na kwaso musu chocolat biskit, chewgum, da sauran kayan ciye ciyen da Ya Najib ya jibge min sai sabuwar Yar tsanata, wacce nasaka mata suna Yar amana da wata dolina, ire iren wannan abun yasa bana maida hankali a makaranta, bawai dan bana fahimta ba sai dan wasan da yaci raina, kuma ba’a sami wanda zai jani a jiki yasani nayi karatun babu takurawa ba.
Muna zaune sai gata ta ɗibo kwalliyarta tana kareraya, a raina nace.
*Yar wofi aikina na jiranki*
Kallonta mukayi, tare da fashewa da dariya muka tafa, dan na faɗa musu shirina.
Aikuwa muka fara cewa.
“1….2….3….4…”
Yanda take hawa matakalar muke kirgawa, bata kai ga inda ya dace ba, ta juyo ta banka mana harara, tana hayewa, nace.
“Sauka lafiya mai sunan ifiritaiii.”
A fusace tajuyo ai kuwa santsi ya kwasheta, ta rikito daga, sama dai dai shigowarshi gurin kenan.
Mukuwa muka fashe da dariya.
Nace.
“Ni bandamu da sanin asalina ba, da kike ce min Yar tsintuwa, abinda na sani aikina nasan asalinshi dan ba tsintarshi na haka kawai ba, Yaseen kin bugu a mazaunarki da gohinki.”
Juyawa nayi muka tafa ina dariya, ɗago kan da zanyi sai akan fuskarshi.
Ya naɗe hannunshi a kirjinshi, yana kallona. Yanda nake zaro manyan magana,
Tsabar na razana fitsarine ya kwace min, idanuna suka kawo ruwa. Lagwaɓe kaina nayi ina share kwalla,
Bai ce komi ba ya taɓe bakinshi ya wucce bansan lokacin dasu Abbati suka ware ba.
Zuwa yayi ya ɗagota ta kwanta a jikinshi tana kuka, sake baki nayi ina kallonsu.
Sabida ban taɓa ganin haka ba, wuccewa da ita yayi cikin gida, yaje ya jibgeta a falo,
Ya fito ina gurin da ya barni, zuwa yayi ya rike kunnena yace.
“Kafin na miki zanen dodo a jikinki ki nemo broom da ruwa ki wanke min gurinda kika ɓata wawuya jibi fitsari kikayi a jikinki, wai ke kam yaushe zaki yi hankali, bazaki daina aljananci ba ko zan shiga jikinki, yarinya sai kace aljana.”
Duk masifar da yayi min babu wanda ya ɓata min rai kamar aljananci. Sake min kunne yayi na falla aguje nace.
“Kwarankwatsa bazan haire ba, kuma sai na fadawa malamin islamiyanmu ka taɓa ta mace.”
Dafe goshinsa yayi hannunsa ɗaya a waisting shi, yana kallona har na shige.
“Ya Allah” ya furta a hankali.
Ina shiga ciki garammm Yaddiko ta tashi, da sauri. Dakina na shige suma ji kake buuuuuum na rufe kofar na fada ban ɗaki, na cire kayana na wanke jikina. Na fito, tumbur babu kaya, tunda ɗakina ne bana damuwa da ɗaura towel ko zani, wardrop naje na ciro pant ɗina nasaka, sannan na duba kayan da Ya Najib ya kawo min, wani jeans ne dark blue, iyakar shi gwiwa. Crazy ne, da ratsin fari da pink a jikin wando, rigar wando pink mai ratsin fari sai kirjin akasaka patter ɗin jeans ɗin na saka hula na fito abuna.
Jikin Yaddiko naje na kwanta, a nan barci yayi gaba dani,dake na kwanta da tunanin Mayyer zai biyo ni sai gani ina mafarkinshi ya biyo ni da bulala.
Janye ni Yaddiko tayi ta gyara min kwanciya na, ta shige ɗakinta.
Ina cikin barci sai naji ana shafa jikina, tare da zame min wandona gyara kwanciyana nayi tare da tura bakina,ganin ina motsawa yasa aka bari, can da barcina yayi nauyi aka cigaba da haka.
Zame wando akayi na buɗe idanuna a hankali, na kuma rufe.
Ya kai hannunshi da niyar zare min pant aka ce mishi..
“Mallakarka ce ita Yarinyar da kake taɓawa.”
A razane Ya juya Mayyer ne a tsaye a bakin kofar shigowa. Ya jingina jikinshi yana kallon Faruq ɗan Hajiya Sadika.
Saka hannu Mayyer yayi a cikin aljuhun rigarshi ya zaro karan taba, ya kunnata yasaka a bakin shi ya zuketa sau ɗaya sai da ta cinye. Ya yasar da ita ya take filtar ya kauda kanshi.
“Zoka fita.”
Ya faɗa bayan ya sake hayakin tabar ya fita, jikin faru a mace ya mike da sauri sai da Mayyer ya bari ya kusan fita ya dunkule hannunshi ya zabga mishi naushi a fuska.
“Kamar Yanda zan kare mutuncin Hafsa haka zan kare nata, dan tana hannun kakarmu baxan taɓa barin wani ya cutar da lafiyarta ba, Yarinyar da Najib yake adanawa kanshi kazo zaka lalata masa ita, ko Najib ne yaga abinda kake shirin aikatawa iya abinda zai maka kenan.”
Dukan Faruk yake, wanda ihunshi ya taddani daga barci na mike zubur, ina kallonsu ganin wandona asaɓule yasani maza nagyara ina tura bakina zanyi kuka.
Dake bansan Faruq ɗin ba sai ya bani tausayi, na fara matsar kwalla. Ihun faruq da yake ne ya dawo da Yaddiko da ta fita gurin Dabbobina, sabida jiya kwana Faratu tayi tana ihu. Ashe haihuwa ce, ta haifa min yara biyu duk taure ta haifa,
Da gudu tazo tasami dukan da yakewa Faruq dakyar ta raba idanunshi sunyi ja, har sai dasu Mama suka fito suna tambayar ba’asi kamar ya cire zuciyarshi ya fitar waje, cikin konar rai yace.
“Wannan Yaron na kuma ganinshi a gidan nan zan kashe shi. Har lahira,”
Ya faɗa tare da sauke huci, a fusace ya juya cikin gidan ya kwaso kananun kayana har na jikina sai da yasa nacire ya kwashesu kaf ya konasu akan idanun mutane.
Cikin kuka nace…
“Tunda katsane ni ka kahe kawai, kayan da baka saya min ba hine dan bakin ciki da hassada zaks kona min kuma Allah sai ya saka min tunda ba kaine kasaya min ba, shi yasa nake son Ya Najib, dan shi kullum damuwarshi nayi farin ciki, amma kai kullum sai ka sani kuka. Ni mai namaka baka sona a gidan nan.”
Banza yayi dani ya wucce gidanshi riko hannuna Mama tayi cikin damuwa tace.
“Nana Aisha! Rashin kunya kikewa Yayanku, baki san babu kyau ba. Toh ki daina zan saya miki kayanki da ya kona, jikin Nanata.”
Har gidansu ta kaini dan kuka nake sosai, har da shasheka. Ruwan sanyi ta bani nasha sannan na kwantar da kaina a cinyarta a hankali nace.
“Mama to mi yasa ake kirana da Yar tsintuwa.”
Shafa kaina tayi, cikin jin ba daɗi.
Kafin tace wani abu na rigata.
“Toh nima da ina da Mama da Baba bazasu taɓa barina nayi kuka ba ko? Dan nasan Ba Yaddiko bane mamana, amma ina sonta. Sosai”
Daga yanayin magana na ta lura da ina cikin kewar ahalina, kallona take sosai, tana nazarin yanayin fatata da kyauna, sai ta da tsura min ido, ɗago ni tayi cikin nutsuwa. Kantane ya ɗaure dan tana kallon yanayina zai fin kama da Yanki maiduguri, idan tayi dubi da gashina da kuma kalar fatata.
Mai dani tayi na kwanta ta tattara shirmena ta ajiye a gefe ta cigaba da shafa kaina wani barcine yayi gaba dani.
Shigowa Yayi ya zauna kusada ita, kamar bazai magana ba yace.
“Mama! Buk sun karɓe ni zan karasa karatuna a nan kawai. Tunda saura shekara ɗaya da rabi ne. Amma sun kara min wata uku akan.”
“Allah Ya taimaka ya kuma bada sa’a, Sauluba ma tana ɗaki dan tabugu gaskiya.”
Shiru tayi sannan tace.
“Ka rage hantara Aisha, kaga Yau har da wasu maganar da bai dace ba ta tambayeni, haka da kake zai haifar muku da muguwar kiyayya, nasan bata ji amma ka daina nunawa baka son farin cikinta, dan Yau har cewa tayi da ace iyayenta suna nan ai bazasu hanata farin ciki ba, sannan wannan abinda kake mata bazai sa ta daina kiriniya ba, dan yanzun take jin kiriniyar, mafi alkhairi kasan yanda zaka shiga jikinta ka sauyata, ko kuma shi najib ɗin ya shiga jikinta, dan duk kulawar da kuke bata bashi take bukata ba, wanda zai shiga alamarinta take nima ya sauya mata tunaninta da gobenta. Take bukata koda kun kainta kafin madaki, bazaita daina halinta ba. Sai ma karuwa da zaiyi,,,, Sannan mi faru yayi da ka mishi wannan dukar.”
Lumshe idanunshi yayi ya kwanta a jikin kujera yace..
“Nasame shi yana son rape ɗin tane”.
Shiru tayi a tsorace.
“Toh mi zai hana ta dawo nan da zama dan kasan dai ba zai fasa zuwa gidan nan ba.”
Shiru yayi kamar badashi tayi magana ba yace.
“Barta a gurin kakarta gidan ne dai bai isa ya shigo ba.”
Duk abinda sukd faɗa sailuba na jinsu, har suka ajiye maganar suka ɗauko na makarantar Ammar, ban tashi ba sai azhar gidan Yaddiko naje nayi sallah, nasami wasu sabin kayan doguwar riga irin namu, sai riga da skirt duk irin na turawa, na washe bakina nace..
“Yaddiko waye ya kawo min kayan turawa.”
Taɓe baki tayi tace.
“Mahar.”
Ajiye kayan nayi na bar falon na shiga ɗakina, nayi alola na gabatar da sallah yanzun da sauki sallahta ba irinta da bace, ina gamawa na fito na zauna kusada ita, shayi ta haɗa min ta bani, ina ganin sabon gwagwani nace.
“Yaushe Kayan haiyinki suka kare.”
“Ke kan kisha mana Mahar ne.”. Bata karasa cewa shi ya kawo ba, na dire kofin, nace.
“Wallahi har na mutu bazan taɓa cin abin hannunhi ba, tunda baya kaunata, yo wa yasani ko guba yasako dan ya tsane ni naci na mutu.”.
Shuru tayi tana kallona,
Duk da ya saya min kayana da ya kona amma haka bai rage abinda yake min ba, asalima ko waje indai ba islamiya bai ya hanani fita, ni kuma haka da yake min yasani jin masifar jin tsanarshi fiye da komi, dan ko kallonshi banayi.
Kwana uku tsakani, inata fakon sailuba, tana ɗakin Hafsat dan bata komi sai taci ta kwanta, ra shiga ban ɗaki na shiga ɗakin na zuba mata karara a kayanta na ficce a bina……..
*??YAR GIDAN YADDIKO?*
*HAZAƘA WRITER’S ASSO*
Mai_Dambu….
*Wattpad:Mai_Dambu*
_Mommyn Sayeed da Noor, goyan bayan Mayyer fa kike, toha kiyayye Mai nima_😂
*Fatan alkhairi gareku, Ayusha Abraham, Rukayya Umar Mom Nur, Najida, Hafsat Abubakar, Tare da wanda ban kira sunansu ba da fatan zaku cashe a sabon wakarmu mai suna tunkwal a rawan wutsiya😎*
Page 7
Murmushin mugunta na sake lokacin da nafito falon ina, yar tsallen nasara.
Tsura min ido yayi, na ganshi sarai na saka nayi kaman bansan da mutum a gurin ba na fita a gidan, shiru yayi yana nazarin dariyar da nayi.
*Wannan Yarinyar iblishiya ce, sam bata da nutsuwa*
Abinda yayita aiyanawa kenan, can kusan mintina goma da fitata, sailuba ta fasa ihu tana sosa jikinta.
Mikewa yayi ya sameta ta kwaɓe rigarta, tana ihu da hauka.
Komawa yayi da baya yaja mata kofar dan yanda take babu kaya baxai yarda yakai mata taimako ba, gudun faɗawa tarkon shaiɗan.
Fita yayi gurin Yaddiko ya faɗa mata, aikuwa ta taso jikinta na rawa, suka nufi cikin gidan dan Mama bata nan, taje sunar Yar kawarta a Tafawa balewa Estate ita da Hafsat.
Yaddiko na shiga ɗakin, tasameta tumbur tana ihu da sosa jiki, sororo Yaddiko tayi cikin jin haushi tace.
“Ke ! bana son shegantaka mike damunki?”
“Kaikayi Yaddiko! Sosa min baya, wayyo kirjina, nan ba can ba. Na shiga uku na lalace Yaddiko ki taimake ni.”
Toh dake Yaddiko bata kawo cewa karara bane, sai tayi tsaki tare da barin ɗakin.
Kuka tasaka ta ihu.
……Dan gulma sai gani na sake zuwa, yana falo a zaune na shigo. suna magana akan kaikayin nazo ina raba idanun nace.
“Yaddiko mike faru?”
Watsar da Hannunta tayi bayqn tayi tsaƙi tace.
“Wancar shashashar ke mana hauka mana”
Nuna min ɗakin nayi kaman ban da masaniyar komi na shige ciki.
Kaɗa kanshi yayi, yana girmama kundin rashin kunyata.
Ina shiga na ganta gatsuuu kamar gayar tuwo.
Rike k’uguna nayi nace.
“Yaseen ina da maganin kaikayin karara amman sai kin min rawan, asosa.”
Kamar zata tayi hauka ta gyaɗa min kai, nace.
“Toh ai hikenan, amma kisani dole ki min rawa sosai da amshi.”
Shiru nayi na rasa wani waka zan mata kawai nace.
“Kawai ki min rawan kaikayi”
Juyawa tayi tana kallona kwalla na zuba a idanunta ta fara rawan kaikayi.
_Kaikayi-Kaikayi-Kaikayi_
Yo fansa zan ɗauka sai da naga tana kuka wiwi na fecce a ɗakin na kalli Yaddiko nace.
“Yaddiko ki mata a gaji da toka da manja Kwarankwatsa Karara ta kwaso garin hegen Iyayinta.”
Ina gamawa faɗa musu na fita da gudu zuwa gurin awakina,
Ina shiga na fashe ds dariya nace.
“Yaseen na ɗauki fansa, ku tsaya na na baku labarin abinda ya faru.”
Nan na kwashe duk abinda ya faru na faɗa musu, “Sannan zamuyi wakar tunkul tunkul rawan wutsiyarsu.
_Tunkwal – Tunkwal rawan wutsiya kowa ya iya ya huta_
Aikuwa suka zuba kofatarsu a kasa yabada tunkwal tare da kaɗa wutsiyarsu, nan na cigaba da wakata.
_Nima na iya na huta_
Yoni ai ba wutsiyarce dani ba sai na kaɗa musu Yar k’uguna,
_Tunkwal_
_Uwar garke ta iya ta huta_
Sai da tayi tunkwal sannan ta kaɗa wutsiyarta.
_Faratu ma ta iya ta huta_
_Tunkwal_
_D’an maraya ma ya iya ya huta_
_Tunkwal_
_Sangami ma ya iya ya huta_
_Tunkwal_
_Yar Kyamus ma ta iya ta huta_
_Tunkwal_
_Iyale ma ta iya ta huta_
_Tunkwal_
_D’an duna ma ya iya ya huta_
_Tunkwal_
_Talle ma ya iya ya huta_
_Tunkwal_
_Yan biyun Faratu ma sun iya sun huta_
Tsallen sabin jarirai suka min.
_Allah ya barni da ku na huta_
_Tunkwal_
_Allah Ya kahe makiyarmu mu more_
_D’an bakin ciki ya fecce_
_D’an bakin rai ya sheka_
_Mahassada su kone_
_Masu kaunarmu mu so su_
“Toh Aljana Yar madabo zaki zo kiwucce ki sai nakira Mahauta sun yanke min kawunan shaiɗanun dabbobinkin da ba’a cinsu sai kiwo.”
A tsorace na juya, tare da raɓa gefenshi na wucce, rakani yayi da harara. Yana mai buga tsaki.
Oho dai yau mun chashe Yasin ko yanzun na gyagije, kuma na tadda komaɗa.
****
Wato salon fitinata na daban ne, domin lokaci guda, na buwayi kowa a makaranta amma a gida ba’a san da haka.
Cikin ikon Allah dake ta tsaya taga nayi karatu sai gani na gama primary.
Hutun muka sha mai uban Yawwa wanda yazo daidai da saukar Hafsa. Shadda Abban bauchi yayi mana, Mama muka english Wax, Kubra sunzo da Ummansu.
Haka kawai matar tunda suka keɓe da Hajiya sadika ta sauya min fuska, nima bai dame ni ba, duk inda Hafsat saka kafa ina gurin har aka gama hidiman sauka.
A cikin hutun da mukayi har an gama min komi na makaranta, Abban bauchi da kanshi yasami Yaddiko ya faɗa mata, kuka ne baiwar Allah nan ba tayi ba amma ranta ya ɓaci.
Wani tausayina da soyayyata yasa ta mike ta shige ɗakin,
Tana tuno ranar da ta tsinceni, a naɗe da farin towel nasaka yatsana a bakina ina tsotsa, kowa yaki ɗaukana sai ita.
Kwalla ne suka sauko mata tace.
“Ubangiji ka jirkinta min, karɓan rayuwata har nasami iyayen Aishatu, na sauke nauyin dake kaina.”
…….Tunda aka ce mata bodin ne nan tsohuwar nan tasa aka sauke min alkur’ani, tare da bani ruwan addu’o’i ina sha, maganin kambu baka, da na idanu, da na Mayyu duk nashashi.
Duk ban sani ba.
Sai da ana gobe zamu tafi Ya Najib yazo.
A min kitso mai kyau.
Komi am min irin ta yar gata.
A daren da washi gari zamu tafi Yaddiko take faɗa min.
“Shatu za’a kaiki makarantar kwana, kiyi karatu sosai kinji nasanki baki da kwaɗayi don Allah ba ruwanki da abin hannun kowa kinji.”
Jin maganarta nayi kamar saukar aradu.
“Wallahi bani zuwa ko ina, ni za’akai bodin, inda akace akwai aljanu da mayyu wayyo na higa uku na lalace.”
Ai tun a daren na birkita mata lissafi har gari ya waye ihu da kuka nake.
Naki wanka naki cin abinci dakyar nayi sallah.
Fita nayi zuwa cikin gida, nasami mama tana abin karyawa na zube a kitchen ɗin ina kuka nace.
“Mama ki cecce ni zasu kaini bodin wallahi bana so kuma, na rantse zanyi karatu sosai bazan kuma kiriniya ba.”
D’agoni Hafsa tayi itama tana kuka, dan ita sona take.
Fitowa Mama tayi tace hafsa ta karasa aikin.
Rarrashina ta shiga yi, amma ji nake kamar tana sheka min ruwan zafi.
Mikewa nayi na fita da gudu, gurin dabobbina naje na kama uwar garke ina kuka nace.
“Uwar garke sun shiga tsakanina daku wallahi, rabamu zasu ku taimake ni karsu tafi dani.”
Cak naji anyi sama dani, kamshin turarenshi naji na fahimci mayyer ne, hantsilawa nayi na dira, ina gurnani idanuna sunyi wani irin ja, zai riko hannuna nace.
“Don’t dare touch me.”
Sake matsowa yayi yana kallon cikin idanuna, nima cikin nashi na kalla.
Daka mishi tsawa.
“Karka taɓani!!!!! Nace na tsane ka, bana son ganinka, Ya Maheer mi na maka zaka rabani da farin cikina, mi yasa bakawa kowa abinda kake min, dan ni ba yar uwarka bace. Ai dama basai kun kore ni ba, tunda haka Umma Ya najib tace min tsintata Yaddiko tayi Mama hajiya ma tace niba danginku bane, na fita a rayuwarku. Toh zan fita basai ka kaini bodin ba.”.
Riko hannuna Yayi bai kalle ni ba yaja ni har gurin Yaddiko yace.
“Najib yana shiryawa tayi wanka ta karya.”
Saka kai yayi zai fita nace.
“Ya Maheer Allah sai ya…”
Buuuu naji yaddiko takai min duka a bakina, a razane na juya ina kallonta. Na fashe da kuka nace.
“Yaddiko baki taɓa dukana ba fa, Nice Aisharki, Yarki fa, Yaddiko kinga yanda kika fasa min baki, keda baki son ko kuɗa ya sauka jikina, toh shi kenan kina son na tafi makarantar ne.”
Kauda kanta tayi tace.
“Eh.”
“Shi kenan Yaddiko zan tafi, amna ki faɗa mishi bazanyi karatun ba.”
Yana tsaye bai ce cikanki ba yafita.
Wanka tayi min da kanta, sannan na fito nasamu har ta shirya min kayana.
Abin karyawa tabani a baki. Har Ya Najib ya shigo dake yanzun babu wani ɗasawa tsakaninmu dan Ummanshi ta min zagin karen dangi akanshi ni kuma ina da zuciya da kafiya, shi yasa na fita har kanshi.
Fitar da kayana yayi, na shirya tsaf cikin unifaom,
Mama da Abban bauchi, suka fito. Amma Yaddiko taki fitowa, juyawa nayi na kalli kofar gidanta bata fito ba, shiga motar nayi na kwanta tare da kifa kaina a kujeran sai hafsa da ta shigo, kuka nake sosai kamar raina zai fita.
Ina ji ina gani suka fitar dani zuwa Kafin Madaki.
Tafiyar Mintuna arba’in da biyar yakaimu har makarantar.
Har ofishin shugabar makaranta aka kaini, daga nan aka nime metro aka batani da kayana, rarrashi d da nasiha suka min, fushi nayi dasu dan nasan abinda suka min haɗin bakine.
Banyi musu sallama ba na juya nayi tafiyata, nabi Bayan metro. Jikinsu yayi matukar sanyi dan sunsan ban cika fushi ba, amma yau nayi fushin.
Daga hostel ajinmu aka kaini, na zauna.
Malamin dake maths yace.
“Tashi ki gabatar mana da kanki.”
Mikewa nayi cikin dashasshiyar Murya nace.
“I’m Aishatu Imran Gumau.”
“Frm Which School?”
Ya jefa min tambaya,
“Dolphin maria college”
Jinjina kanshi yayi sannan ya ce na zauna ya cigaba ds koyarwashi..
Koda akayi tara ban fita ba, ina zaune sai ga sako wai Ana kiran Aishatu Imran Gumau.
Mikewa nayi, na fita ina tunanin waye ne kuma.
Ina isa naji kamshin turaren Arab perfume.
A hankali na isa gurin cikin rawan murya nace.
“Gani nan.”
juyowa yayi yana kallona, murmushi yayi, ya zauna yace.
“Kinyi kuka dayawa, kina son nima nayi kuka ne?”
Kwalla ne suka sake zubo min daga idanuna, na ɗago kaina ina kallonshi nace.
“Kaiii waye?”
Murmushi yayi sannan yace.
“Nadeem Hamza shira, zaki iya kirana da Ya Nadeem, mi yasa kike kuka.”
“Sabida ya tsanane yasa aka kawo ni bodin, yasa Yaddiko tayi fushi dani, kalli Yanda ta fasa min bakina, ni ma na tsane shi bana son shi, kuma bazanyi karatun ba wallahi.”
Ware dara daran idanunshi yayi cikin mamaki yace.
“Waye haka yayi mana yankar kaunar?”
“Waye banda Ya Maheer, gashi ya rabani da awakaina.”
B’ata fuska yayi irin tawa, kamar zai fasa kuka yace.
“Gaskiya bai kyauta ba, dama ni abokinshine daga yau na daina abota dashi, kuma batun kin bazakiyi karatu ba bai taso ba, Indai kina son mu zama abokai toh kiyi karatu duk weekend zan xo dubaki Yanzun ma zantafi wani gurin ya faɗa min ya Najib ya kawo ki makaranta shine nazo duba ki, kinji kuma na miki alkawarin bazan taɓa barinki kiyi kuka ba, duk abinda aka miki idan nazo ki faɗa min, Aeesha.”
Gyaɗa kaina nayi, duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi yayi, sannan yace.
“Promise me da zakiyi karatu sosai, ni kuma zan baki mamaki a rayuwarki.”
Murmushi nayi cike da farin ciki na gyaɗa mishi kai nace.
“I promise, indai baxaka min faɗs ba.”
Zaro wata yar karamar kwati yayi, ya buɗe tare da ciro wani sarka yasaka min a wuyana, yace.
“kinsan kuɗin wannan sarkan toh ki rike shi sosai, ina son kiyi karatu Ummuna Aeesha.”
Rike sarkar nayi nace.
“An hanamu saka sarka, za’a kwace amma zan rike shi sosai kamar yanda zanyi karatu.”
Mikewa yayi yace zai tafi.
Ina ganin ya shiga mota nima na wucce class.
****
Shigowar Ya Nadeem shira, yasani mai da hankali a karatu, dan duk sati yana makarantar, duk karatun da mukayi sai ya min bitarsu.
Kuma abin mamaki na zamana a makarantar babu me shiga harkatq, kodan satina biyu ne ana niman na uku, ɗakinmu akwai mater ɗina, guda uku sai senior huɗu jimula mu takwas kenan,
Bansan laifin da mukayi ba bayan an tashi mkrnt Yan aji shida suka kamamu suka zane mu, tasss banyi kuka ba, amma nayi marker fuskarsu kuma sai na ɗauki fansa dan bana yafiya…….
*YAR GIDAN YADDIKO*
*HAZAƘA WRITER’S ASSO*
Mai_Dambu….
*Wattpad:Mai_Dambu*
*Wannan shafin na kune.*
*Mommyn Abul*
*Jiddart*
*Idon Kuka*
. *Oum Rahman*
_Ayi rawan tunkwal_
_Kabi kwarewa….Nasara sai tabika_
”’I know not with what weapons World War III will be fought, but World War IV will be fought with sticks and stones.”’
By : Albert Einstein _________________________________
Page.8
Kallon yan uwana da muka ci duka dasu suke kuka, amma niko a jikina. Sulalewa nayi nabar hostel na mike cikin dajin makaranta, tafiya mai nisa nayi na samo karara na juyo abuna yo ko tsoro babu a raina.
Koda na dawo nasami ɗalibai a zazzaune ana hiran irin muguntar da senior suke sai banji komi ba,
Tun a lokacin na ɗiɓe ruwan wanka da nasallah nasami Yaran da muke ɗaki daya nace.
“Kowa taje ta ɗibo ruwan wankanta, don gobe babu ruwa.”
Kallona sukayi cikin renin hankali ban damu ba, na zauna,sai da yamma yayi muka tafi islamiyya, muna dawowa muka tafi evening lesson.
Bayan magariba muka wucce gurin cin abinci, dake akwai mugun kudiri a raina banci abincin ba na tashi,
Bohul ɗinmu dama ya lalace, a rijiya ake ɗiban ruwa. Gugar nace na zuba karara a ciki, sauran nabi ɗakunarsu na zuba musu a cikin bokatayensu.
Na wucce abuna na dawo ɗakinmu kamar mayya. Na zauns tare da buɗe book ɗina ina karatu.
Can sai ga ɗalibai sun dawo, bayan sallar isha na kwanta sai barci.
Assalatun farko naje nayi wanka na. Na dawo nashafa mai na kwanta lokacin sallah nayi na mike nayi dama da alola na,
Can naji an fara layin ɗiban ruwa,
Senior suka gama ɗiba, sannan kowacce taje ta ɗauko towel ɗinta wanda yasha barbaɗen Karara.
Suka nufi banɗaki suna susa jiki sama sama,
Aiku kafin su shiga wanka komi ya lalace, domin kaikayi har a ruwan da suka watsa, sai kuga katuwar budurwa tanq birgima a kasa, shiryawa nayi na fita abuna.
Ko kallo basu isheni ba, na nufi gurin cin abinci. Ranar da yawan ɗalibai basu yi wanka ba, har da yan ɗakinmu da muka dawo bayan an tashi, aka sake zuwa za’a zane mu dan anyi tunanin jenior ne sukayi haka, har ansa wasu jada gwiwa ns mike tsaye nace.
“Nice Na zuba muku karara a cikin bokiti da towel, matuƙar kuka cigaba da zalinci nima bazan fasa ba, dan haka ni ɗaya zan amshi hukuncinku sauran su je ɗakinsu.”
Kamar Mayyu haka suka yo kaina, niko ɗar banji ba.
Bulalar hannunsu suka tawo dashi, duk suka rufa min da duka, banji nayi kuka ba kuma bsn durkusa ba.
Suna gamawa suka ce nayi tsalle kwaɗo, nan ne kan sai da nayi kuka, dakyar suka barni da taimakon metro ɗinmu, ina mikewa nace musu.
“Wallahi kunci bashi sai kun biya.”
Koda muka koma.
Zama nayi naci kuka kamar zan cire idanuna.
Yan ɗakinmu sai rarrashina suke, da dare kafana ya hanani barci.
Tashi nayi na ɗauki farin zanin gado, na baɗe fuskana da farin hoda, bakina na lafta jan baki.
Na nufi ɗakunar kwanarsu, dama mutane biyar ne, kafin na tafi na sami katon itacena na tafi dashi, Senior Devana itace na fara da ita, inda na ɗauki katon itacena na maka mata a gwiwarta.
Tana farka da ihu nasaka hannuna a bakina, nace.
“Shiruuuu.”
Duk wanda ya farka ya ganni ds farin kaya komawa yake, ɗan buuuu sai da na make mata kafa.
Nafice zuwa ɗakinsu Senior karima,itama na mata,
Yaseen duk sai da na buge musu gwiwarsu na dawo ɗaki na kwanta bayan na antaya kashedi da karsu kuma taɓani dan aljanatace tazo ɗaukar fansa.
Ina shiga ɗakinmu naga Yan ciki duk sun mike a tsorace cikin tashin hankali Metro tace.
“Kece kika sake zuwa ko, mi yasa baki da hakuri.”
“Iya jeki kwanta nima na gaji.”
Haka nace mata, sauran na kallesu nace.
“Saura wata tayi gigin magana Yaseen gobe zata rasa kayan zuwa aji.”
*****
Washi gari kuwa aka tashi da labarin Aljanar Aisha Gumau ta ɗaukar mata fansa, Wow lokaci guda na zama cele,😂
Ranar Asabar Ya Nadeem yazo na bashi labarin abinda ya faru, dariya yayi sannan ya ɗaura min da nasiha.
Sosai Ya Nadeem ya ɗauke min kewar Yan gida, sai dai ina yawan tunawa da Yaddiko da awakina.
Ina cika wata ɗaya aka zo mana visit, naso Ya Nadeem su haɗu da Ya Najib da Yaddikona Hafsat Mama dan mugunta Mayyer ko yazo nima ban damu ba, amma bai zo ba har suka tafi can Yamma sai gashi, fushi nayi na tura mishi baki na, tare da kauda kaina kamar zanyi kuka.
Dawowa gabana yayi ya rike kunnenshi, har da mun alamar tsallar kwaɗo.
Dariya nayi na faɗa a jikinshi, nace.
“Yaddikona tazo, ita da Ya Najib da Hafsat da Ya Ammar, shine kaki zuwa ko.”
D’ago ni yayi yana murmushi muka zauna kayan da su Ya Najib suka kawo min na ɗauko nasaka a gabanshi nace.
“Gashi kaci ka kuma tafi da wanda kake so.”
Jan hancina yayi yana dariya yace.
“Wannan dambu Mama ce tayi, sai miyar can Yaddiko tayi miki, wancar kayan chocolat Najib ya saya miki ko, Ina na Ya Maheer.”
Tura baki nayi nace.
“Ko ya kawo min baxan amsa ba, dan bazanci abin hannunshi ba.”
“Sabida Me?”
Ya tambaye ni,
Sake tura bakina nayi cike da kiriniya nace.
“Bana sonshi mana.”
Lumshe idanunshi yayi ya buɗe a hankali ya sauke a kaina, sai na lura da sunyi ja, har eyeball ɗin shi sun tara ruwa.
“Kayi hakuri ai kai kana da kirki.”
Murmushi yayi sannan ya riko hannuna yace.
“Don soyayyar da wani zai nuna miki, toh Bayan wanda maheer zai nuna mikine. Lokacin da Yaddiko ta ɗauke ki, shi ya bada shawaran asa miki sunan goggonshi, sannan shi…”
Tsura mishi ido nayi dan ban fahimci komi ba ɓata fuskana nayi sannan nace.
“Ni dai kadai na min maganarshi kaina na ciwo.”
Mikewa yayi ya wucce gurin motar shi ya ciro min katuwar teddy sak irin wacce Ya Najib ya saya min.
Da gudu naje na amsheta, ina daka tsalle. Jingina yayi da jikin motar, shi kaɗai yasan yanda yake ji da zaran yaga Ina farin ciki.
Sake buɗe motar Yayi ya fito min da kayan da ya kawo min, sannan ya kira wasu yan mata, ya basu kuɗi suka kwashe min har hostel.
Dakyar muka rabu dan shirme nayita mishi karshe aka rabu da kuka….
*****
Sannu sannu bai hana zuwa sai dai a dade ba’aje ba, har mun kusan hutun farko wanda zamu samu a cikin december, murna kaman nayi hauka.
Ranar da muka fara revision kowa yasan ina murna.
Tsabar farin cikin sai da nabi ɗakunar ɗalibai na razana.
Kaii muna fara test, naga point ɗina yana ja, sosai sai na fara rayawa a raina dole ma mayyer ya sake min kurwa.
Da muka gama test Ya Nadeem yazo na kai mishi ya gani, sai da yayi min katon kyauta.
Yace.
“Idan kika yi na farko zan saka Ammar Ya kaiki Yankari.”
Zaro ido nayi sannan na fashe da dariya ina murna.
Bayan munyi tafiyarshi sai ga wasu, senior suka zo zasu kwace min kayan da yabani, kallonsu nayi cikin dariya nace.
“Wannan kayan nawa ne duk wacce taci sunanta gawa.”
Ina gama faɗar haka na wucce abuna ina dariya.
Cikin nasara muka gama exam, nan nabi na buwayi kowa har da senior babu wanda ya iya magana sai da muka gama Exam na sami buɗe abinda Ya Nadeem ya kawo min.
D’an kunne da sarka da zobensu mai kyau.
Ranar Hutu kuwa Ya Ammar ne yazo ɗaukana.
Haka muka tafi dama Yan ɗakinmu ban saba da kowa ba dan ba magana nake musu ba.
Gashi Ya Nadeem bai sake zuwa ba haka muka tafi jikina ba daɗi.
……
Mun isa gida lafiya, aka baje min abinci da kayan makulashe, Yaddiko da Mama.
Haka naci nasha sannan na kwanta na hucce.
Wannan karan babu mayyer haka nasha hutuna sannan aka min sayayya da muka koma aka maidani, wanda nake cike da ɗauki da murna….
****
“Yaya dama akan Maganarsu Sailuba ne naga har yanzun baku sake magana ba.”
Shiru Hajiya Sadika tayi, tana na jiran abinda Alhaji Imran Gumau zai ce.
“Eh Sadika ina sane da komi so nake Yaran su gama karatune sai ayi komi a nutse.”
“Toh shi knn Allah ya nuna mana lokacin.”Tace.
“Amin” yace, suka ɗauko wani hiran nadaban…
*****
Bayan shekara uku da wata shida, wanda ya bani damar kaiwa huɗu, shirme da shiririta ya fita a rayuwata, sai dai bani da hakuri ne har yanzun. Fansa kuwa sai dai ba’a taɓa ni ba.
Tsakanina da Ya Nadeem ba’a magana sai dai ba kowani lokaci yake zuwa min ba, akwai lokacin da Ya Maheer yazo kamar mai ɗaukar wuta, dama nima ban gayyatoshi ba, sai da na gama ɓata masa lokaci naje inda Ya Nadeem yake zama idan yazo, nace.
“Gani malam.”
Kallo ɗaya yayi min ya taɓe baki, tare da kauda kai,, da nagaji ni kuwa na juya abuna ban kuma cewa kala ba, haka kawai zai zo ya baza min mulki, ina dab da shiga aji huɗu.
Mamakine yakama shi lallai kuwa.
Yace a rainshi.
Duk wani alamar girma Ya bayyana a jikina dan nima na zama lady, tunda har boons🙈
Sai dai abu guda ɗaya shine cikon girman yaki zuwa, wato circle dan yar ɗakinmu mai suna Nasiba, ta fara ba ita bs har Zahra da Raliya, ni kuwa har lokacin shiru.
Wata jumma’a mun fito class , kenan ciwon ciki ya fara damuna da mara, dakyar na isa ɗakinmu. Na kwanta, a nan abun yaci karfina tun inayi cikin nutsuwa har na fita hayacina.
Kafin ace an kaini asibitin makaranta, na suma a ɗimauce aka kaini inda aka samin drip da allurai.
Ban farka ba sai cikin dare da sabon ciwon cikin, sosai nake jin abun dole aka kira shugabar makaranta ta kira Ya Najib ta faɗa mishi.
Allura barci yace a min.
…….Washi gari ina barci sai farkawa nayi na gansu shida Ya Mayyer, har lokacin da sauran ciwon.
“Sannu Ummu Aisha, ina ke miki ciwo.”
Kwallar da nake adanasu ne suka sauko nace.
“Cikina da Bayana da….”
“Dalla ya isa haka, sai kace ba mace ba, a haka zaki haihu.”
Kuka nasaka tare da kauda kaina, mikewa yayi ya tattaro kayan aikin da suka zo dashi, Ya Najib ya fita. Buɗe cikina yayi ya ɗiga min gel ya shiga min scanner.
Yana gamawa ya kashe komi ya wurga min tissue.
Gogewa nayi bai tambaye ni ba nima kuma bance komi ba, fita yayi, ban ganshi ba sai bayan wani lokaci sai gasu tare allura yayi min tare da wasu magani,
Sannan ya fita, mikewa nayi naji ni kamar na tsula fitsari.
Kallon Ya Najib nayi nace.
“Ina son zagawa.”
Mikar dani yayi na zauna, sako kafana nayi ina kallon jikar da nayi da zanin gadon jini ne malala, da sauri na koma kai na fashe da kuka ina yarfe , ruɗewa Ya Najib yayi yana tambayana, kasa magana nayi ina leka inda na tsaya, lekawa yayi yaga ɗigon jini.
Sai kunya ya kama shi nima kwanciya nayi na rufe idanuna ina kuka,
Fita yayi ya maw Nurse ɗin magana, ita ta shigo ta gyara min jikina, da yanda zan na amfani da Always.
Sai da suka ga na koma fess sannan suka dawo, bauchi.
****
A can kuwa bauchi bikinsu Ya Najib ne ya taso dan har sai da aka kai ruwa da Ya Maheer yace baya son sailuba, abu ya koma rikici a family.
Sai da Yaddiko ta tsawata masu, sannan ya amince, dan babu yanda ya iya dan cewa sukayi Mama ce take zugashi, abinda yaso kawo rashin fahimta kenan, Yaddiko tayi dagaske a cikn alamarin.
Bikin a saka shi dai dai mun sami hutu, dan haka akayita shirya shirye, duk anko da akayi sai da Mama tayi min, A bangaren Ya Najib har shaddar da Binta zata saka ranar ɗaurin aure ya min.
Ana saura kwanaki za’a kai kaya, Sailuba tazo gidan. Kai tsaye ɗakin Ya Maheer taje.
Baya falo ta shige ɗakinshi, tana shiga taga karamin box ɗauka tayi ta buɗe, taga zobe mai shegen kyau.
Tana cikin kiyasa kuɗin zoɓen ya fito kwacewa yayi yasaka a wardrop.
Kallonshi tayi ganin Yanda ruwake ɗiga a jikinshi, ɗaukar towel tayi ta shiga goge mishi jiki, cikin wani salo, da iyawa tana kara shigewa jikinshi.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kai hannunshi ya amshi towel ɗin ɗin, rike towel ɗin tayi, tana kallonshi.
Fincika yayi ta fado faɗaɗɗar kirjinshi, tana sauke a jiyar zuciya tare da narkewa a jikinshi.
Tureta yayi cikin faɗa yace.
“Gaggawar mi kike, tunda kince ni kike so. Shawara zan baki karki kuskura kice zaki shigo min gida kina barbaɗa min magani dan duk ranar da nasameki dashi ba zan sake zama dake ba.”
Tureta yayi ta faɗi ya wucceta yayi ya nufi kofar fita yace.
“Zaki fitar min a gida. ”
Mikewa tayi ta fita.
****
Kamar mahaukaciya ta nufi gidansu ta zuɓe a jikin Hajiya sadika, tana kuka tsaki faruq yayi cikin jin haushi yace.
“Hala keda wancan jaki ko?”
Gyaɗa kai tayi, cikin jin haushi yace.
“Yarinyar da suka ajiye nake hari wallahi Hajiya sai na farke Yarinyar nan koda zan mutu ne.”
*YAR GIDAN YADDIKO*
*HAZAƘA WRITER’S ASSO*
Mai_Dambu….
*Wattpad:Mai_Dambu*
“`Kyautar shafi gareki Marubuciyar Sarautata Alfaharina“`
*Allah nabaku Kyauta Uwar garke, tunda baku so hikenan sun sheka Lahira*😂
Alhamdulillah😉
Page.9
“Wallahi na faɗa miki, sai na farke yarinyar dan tayi min.” ya faɗa cikin salon yan daba.
“Dalla can ana maganar arziki kana sako na tsiya” inji Hajiya sadika.
Shiru yayi yana cizon lip ɗinshi, irinta rikakkun Yan iska, ya mike tare da buga sowa,
Kallon Sailuba Hajiya tayi cikin nutsuwa tace.
“Miye ya faru?”
“Hajiya nifa ban gane kanshi ba, sai magana yake faɗa min.”
Bakinta ya gaza furta komi sabida tashin hankali. Allah ya gani ta haɗa aurene dan ƙuɗin Yayanta, kuma tasan Mahaifiyar Maheer bata da matsala kamar Hajiya Salma mahaifiyar Najib.
Hajiya Safiya tana da halin kawaici irin na fulanin Katagum, gata da mutunta mutane, uwa uba abinta bai rufe mata idanu ba, shi yasa Hajiya Sadika ta makale mata, banbancinta da Hajiya Salma kenan tana da iko da jin kai, irin na ɗiyoyin sarauta.
Gata da mugun rowa. Abin hannunta ba kowa keci ba, kuma ta maida Alhaji Ibrahim kamar buje, juya shi take son ranta. Sai gashi ɗanta Najib bai ɗauko halinta ba, dan Allah yayi mishi yawan kyauta.
Furza da iska tayi tace.
“Kyale shi, karki damu zanyi maganinshi.”
…..
Fitsarine ya dame ni, cikin dare amma haka na kwanta abuna, dan dole na mike tare da sauka a gadona na ɗauki lenta na na fita zuwa waje bakina dauke da Addu’a.
Nazo zan yanki kwanar da zan yanka na shiga ban ɗakine sai ga wata dirkekiyar kuliya, akan wata yarinya tana lasar jikinta.
Abinda ya fito bakina shine.
“7 A’uzu bikalmatullahi tam……”
Kafin na karasa sai ji nayi kamar an sure ni anyi sama dani aka maka da kasa, mikewa nayi ina kara maimaita.
“K’alu Innalillahi…”
Aka sake sama dani, wannan karon ban faɗi ba, cak na tsaya a iska, idanuna rufe.
A hankali aka saukar dani kasa aka jingina ni da bango, na zame na kwanta. A gurin ban kuma sanin abinda ya faru ba sai bayan kwana uku.
Na farka a ɗakin Yaddiko, Mama tana kusadani, Ya Najib na gefen Yaddiko da take fyace majina tana kuka, dama abinda ta guda kenan gashi nan mayu zasu kasara mata Yar mareniyar Allah.
Gogan na bakin kofa. A tsaye yana kare min kallo.
Nima tunda na tashi nayi mika tare da addu’a nace.
“Mama jikina na ciwo.”
Na faɗa a shagwaɓe. Shafa kaina tayi, tana murmushi tace.
“Sannu dole jiki yayi ciwo Baby, kwana biyar kina barci tunda aka kawo ki daga schl.”
Dafe goshina nayi tare da cewa.
“Washi Allah na, kaina zai fashe.”
Dan jin wani kuwwa, da kararrawa, tare da hayaniyar mutane. Komawa nayi na kwanta tare da lumshe idanuna. Sannu suka dame ni da cewa, na buɗe jajjaye idanuna na daka musu tsawa tare da mikewa a iska.
A razane Mama da Yaddiko sukayi baya, Ya najib yakai hannunshi da niyyar taɓa ni aka maka shida bango.
Naɗe hannun rigarshi yayi, ya shiga karanto, (229:2: bak’ara)
Ya iso har inda nake, kamoni yayi ya danna nida gadon nasake mikewa ya maza ya haɗani da kirjinshi, yana karanto Ayoyin alkur’ani.
Ihu nake tare da kururuwa, dukar shi nake ina cizon shi tare da yakushi bai fasa ba, haka Mama itama ta cigaba dayi. Tana haɗa maganin da aka bani lokacin da Aka kawo ni daga makaranta aka kaini gidan Imam Nafi’u Saɗ’e babban Malami a cikin garin bauchi, kuma yana daga cikin Member na Izalatul Bidi’a waikamatul Sunnah.
Shi ya haɗa maganin da kanshi dake Ya Najib ɗalibinshine yace a na shafa min a jikina kuma a bani nasha.
Mama na mikawa Ya Najib akayi wurgi da maganin, Ya Mayyer bai fasa karatun ba, nima ban fasa ihu ba.
Yana kwafkume dani, can jikina ya bada wani irin zafi wanda kamar zai kona mishi fatarshi dan har ya fara gumi tare da sauke wani irin numfashi, ya mika hannun aka bashi maganin kwara mana yayi har jikinshi, tare da shi. Wani ihu na kwalla tare da mikewa akan iska haka shima da yake rungume dani, aka shiga cewa.
“Maheer kayi mana Illa muma sai mun maka illa, sai mun rama abinda kayi mana kuma kasaka ido sai mun shayar da Aisha jini, kamar yanda ka kona mana abin bautarmu akan Aisha sai mun kona farin cikinka sai mun hanaka sukuni, hahahaha…”
Wani jan hayakine ya fita a bakina da hancina bi ta kofa ya fita da sauri.
Jagwaf muka koma gadon, tare da rungume ni, sai zufa yake fiddawa, tare da ajiyar zuciya kallon fuskana yayi ya kauda kanshi ya maidani kan shimfiɗina, tare da tofa min addu’a. Ya shafe min jikina tass sannan ya fice,
Binshi Ya Najib yayi a baya da sauri yasha gabanshi yace.
“Man!!! Kana son Ummuna Aishane?”
Ya wurga mishi tambayar dan yana son jin amsar da Maheer zai bashi..
Kauce wa yayi ya shige, “Maheer Tambayarka nake kana son Aishatu ne?”
Naɗe hannunshi yayi a kirji, tare da tsuwa najib idanu yace.
“Ka ga wani abune?”
“Na farko awaki daga gumau zuwa bauchi, na biyu tsayawa maciji ya sareka na uku ajite karatu daga Sudan zuwa naija. Ga na huɗu akan idanuna ka sake bada rayuwarka domin ita.”
Shafa kanshi yayi sannan yace.
“Ni banga wani abin ɗaga hankali ba,,,,”
Kamar bazai cigaba ba, yace.
“Abinda zanyiwa Hafsat da Kubrah ne fa nayi mata, Yallaɓe da kishi zai rufe maka idanu. Don ALLAH bani guri na shige.”
Shiru Najib yayi yana bin maheer da idanu, sam bai ga wani alamun so ba, tunda maheer baka taɓa sanin meke cikin ranshi, koda kuwa cutuwa yake yakan aro juriya da hakuri cikin ranshi wanda ko akan fuskarshi baxaka taɓa ganin haka ba.
Sider ɗinshi ya wucce shima yayi wanka da ruwan zafi, sabida buguwar da yayi.
Dukda wanka yake amma sam zuciyarshi ba daɗi, karshe tattara komi yayi ya watsar yafito a bishi.
……
Yana shiga falonshi Ya sami sailuba, kallonshi tayi kamar zata fasa ihu kafin tace.
“Ya Maheer yau saura kwana wata guda bikinmu amma baka min magana akan event ba, asalima idan nazo da zance kaucewa kake, dukda baka sona ni ina sonka haka.”
D’ago idanu yayi ya kalleta sannan ya kauce abinshi, ya shige ɗakin, daga b ban ɗaki ya faɗa,
Koda ya gama, ya sameta a bakin gado. Rike da towel, tana ganinshi ta mike zata isa gareshi ya dakatar da ita, dacewa.
“Ke baki da kunya ne? Ko baki da hankaline, da zaki shigo min ɗaki kai tsaye idan da nafito babu kaya fa.”
Dariya ta saka har da rike cikinta. Rike bakinta tayi sannan ta mike ta nuna shi da yatsa tace.
“Ya Man! Wallahi duk yanda kafito ni bazan damu ba, dan nasan saura kwanaki na zama taka, dan dai baka guri kasaka kaya.”
Tana gama faɗar haka, tafita daga ɗakin.
Tsaki yayi ya shiga shiryawa.
*****
Babu wanda yasake min maganar komawa makaranta, saima kulawar da mama da Yaddiko suke kan bani. Sati na ɗaya sai gashi ya kawowa mama kayan makaranta wai zan fara jibwis, karban kayan mama tayi ta kai min ɗakin Hafsat dan yanzun ina cikin gidane, sabida yawan tashin ciwona Yaddiko bazata iya min ba, sai yace a dawo dani cikin gida.
Tunda wannan abin yasame ni nake keɓe kaina naci kuka sabida ji nake kamar ana gasani da wuta, ko makarantar ma dakyar nake walwala, hankalin kowa yanzun ya koma ga shirin biki har Ya Najib.
Bayan gidanmu nake zuwa na zauna, nayita rizgar kuka sai nayi ya isheni sannan nake komawa cikin gida.
Ana haka wata safiyar Talata aka sami Awakaina duk sun mutu, kamar mahaukaciya haka na koma rashin magana yasake shiga min, sosai.
Bayam faruwan haka ranar ya kaini makaranta, ya ajiye ni ya juya.
Kamar wacce aka umarta na bar gurin na cigaba da tafiya nake, tun daga kofar wambai har gubi dam, Allah da ikonshi ina daf da faɗawq cikin ruwa naji an rikeni.
Juyawa nayi ina kallonshi da jajjayen idanuna na fashe da kuka, nace.
“Baba kabarni na tafi, suna kirana idan banje ba zasu kashe min Yaddikona.”
Jan hannuna yayi har bakin rugarsu,ya kira matarshi Goggo, ya ce.
“Shiga ɗaki ki ɗauko min jakar maganin nan.”
Da sauri tashiga, ta ɗauko jakar zama yayi ya fara rubutu a jikin alo, tun kusan biyar har akayi sallahr magarib ya dawo, ya cigaba da rubutun, bai fasa ba har ya tafi isha sai bayan karfe goma na dare, ya wanke ya haɗa min hayaki. Yasaka ni a ɗaki, ya mikawa matarshi ruwan rubutun ya shiga watsa min,
An ɗauki lokaci kafin ɗakin ya shiga jijjiga, tare da ihuna.
Yaki sauraransu duk yanda suka so suyi magana, bai basu dama ba.
…….
A gida kuwa lokacin ɗauka nayi aka tura Ya Ammar ya gama jira bai gan ni ba, ya dawo gida ya faɗawa Mama.
Kiran Ya Najib mama tayi ta faɗa mishi, lokacin Ya Maheer ya shiga tiyata.
Dole ya jira shi ya fito, kallon juna sukayi lokacin da Ya Maheer ke cire rigar da yayi aiki da ita.
“Man! Ba lafiya fa.”
D’ago shanyayyun idanunshi yayi ya zubawa Ya Najib.
“Umma Aisha, ba a ganta ba.”
“and So what?”
Kallonshi Najib yayi cikin masifa yace.
“Amma kai anyi ɗan kutumar Uba, so Ubanka dan banza mai baki rai kawai.”
A fusace Najib ya fita daga officer ɗin, ya nufi gida.
Abin mamaki yana isa gida yasami har Maheer ya rigashi dan shi ya tsaya a makarantar.
Tsaki yayi, ya shige yasami maheer a tsakiyarsu ya Yaddiko yana kwance, sai ma murmushi yake dokawa.
Ganin yanda Yaddiko ke kuka, ina na shiga.
Fita Najib yayi zuwa B.R.C bauchi, yana zuwa yasami wani class mater ɗinsu ya bashi komi aka kaina, abinda Kabir bundat ya faɗa mishine yasashi sanyi jiki.
“Likita ai ɗan uwanka ya turo min da komi, har ya tura B.A tv kuma zamu cigaba da cigiyarta.”
Koda ya koma gida yasamu Ya Maheer ya fita.
……
Wato ba karamin wahala nasha ba, kafin bawan Allah nan ya rabani da fitinar ba. Sai asuba nasamu barci.
Fita yayi ya gabatar da alola yayi raka’atul fijr a tsakar gidansu, yana idarwa yaga wuccewar katon mage har sau biyu, bai fasa addu’a ba. Karshe dai magen tayo kanshi da gudu, kafin ta isa gurinshi ta kama da wuta, ajiyar zuciya ya sauke tare da mikewa ya nufi masalacin dake rugar.
Ban farka ba sai gurin karfe shida jikina duk ciwo yake, fitowa nayi naga tsohuwar tana dama kunu, tana gani na, na mike ta kawo min buta tace.
“Sannu kin tashi? Ina ke miki ciwo?”
Murmushi nayi nace mata.
“Babu ko ina”
Na faɗi haka ne, dan kar na kara musu ɗawainiyata.
Alola nayi na shiga na rama sallar dake kaina, sannan na ɗan zauna ina tunanin gida, mi xancewa Yaddiko.
Abin karyawa ta kawo min tana mai cewa.
“Allah yasa ki iya cin abincinmu.”
Murmushi nayi na karɓa nace nagode.
A hankali nake shan kunun wanda yaji kayan kamshi, da kosai. (Kusan fulani d son kosai Badake nake ba Ummin Ilham😂 tsarguwa.@com) sosai naci sannan na fito da kayan na wankedan na lura da matar ba dai tsafta ba. Ruwan wanka ta juye min, naje nayi.
Ina fitowa na mai da kayana, Baffa Audu yasami a gaba, har bakin titi, ya tara mana mashin guda biyu. Muka faɗa mishi, dakyar suka kawo mu a ɗari biyar biyar.
Har kofar gida aka sauke mu, lokacin Abban bauchi ya fito shida su Ya Najib zasu koma gidan, B.r.c ance musu an sami wata yarinya sai gamu.
Ina sauka a mashin ɗin, Ya najib ya iso da mugun sauri, ya rungume ni, kuka nasaƙa mishi tare da rike rigarshi.
Gurin masu mashin ɗin Ya Mayyer yaje ya biya kuɗin dan yaga tsohon na kokarin basu kuɗin.
Yace.
“Baba mushiga daga cikin gida.”
Shiga akayi Ya Najib yana rungume dani, har falon Abba.
Zama sukayi aka gaisa, ina ganin mama na koma jikinta ina kuka, bayan sun gaisa kenan sai ga Yaddiko itama tashigo gidan.
“Shatuwa”
Mikewa nayi na kwanta a jikinta, ta rungume ni tana kuka, zama mukayi ganin kukan yaki tsayawa “Dalla kiwa mutane shiru, ƙin cika mana kunne.”
D’ago kai nayi a fakaice na murguda mishi bakina, sannan na juya cinyar Yaddikona.
Gyaran murya baffa yayi, sannan yace.
“Wato wasu abubuwan suna da sila, musaman babin k’addara, yau kwana na biyar da dawowa daga kudu, da shanuna knn, bans cika kiwo waje mai nisa sai dai jiya kiwo ya kaini bakin dam, ina zaune sai naji wuccin wuta yana tunnkaro inda nake kiwo. Ina dubawa sai naga Yarinyar can ne, kallon da nayi mata sai naga kamar tana cikin matukar hatsari, dukda ban basu damar magana ba amma na fahimci kungiyar asiri suke bibiyarta, kuma cikin ikon Ubangiji na kawo karshen zamansu da ita, dan yanda suka ɗaukota. Sunso kasheta ne, ta hanyar saka mata zafi. Sannan ina baku shawara ku daina barinta tana fita da dare ko goshin almuru, dan ko babu matsafa, akwai shaiɗanu.”
“Mungode Baba ALLAH Ya saka da Alkhairi, ynx haka zamu gidan gidan radio ne dan duba wata yarinyar da akace an sameta.”
Nan suka ta godiya, Mama ta kamani muka shiga ɗaki nayi wanka, a nan nabarsu da Baffa.
****
Saka ido sosai akayi akaina, tare da bani kulawa tsakanin Mama Yaddiko Ya Najib.
Bikin da ake tasaka ranarshi har ya iso, ga Umman Ya Najib suma sun tattaro sun dawo, kwanansu biyu da dawowa ta tura Kubrah ta kirani.
Ina shiga, na sameta dasu Hajiya sadika da Yaransu.
Gaida ita nayi ta banka min harara sannan tace.
“Dan Ubanki naji kina shigewa Najib toh kar na kuma ganinki tare dashi, munafuka shegiya tsintarciyar mage.”
Kaina a sunkuye ban ce musu komi ba, har zan fita.
“Ke zo nan kwarkwasa, wani shegene yasaya miki sarkar wuyarki, munafuka ko kin fara bin mazane.”
Inji Sailuba, sunkuyar da kaina nayi ban iya magana ba, sai kwallar da ya ciko min ido, kallonta nayi, na juya nabar musu, falon har zan fita a gidan naga sauran ruwan da sa’idu ya gama wanke motar na ɗauko omo nazazzaga na kaɗa nashiga cikin gidan na watsa a step………