Littafan Hausa Novels

Bagidajiya ce Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Bagidajiya ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

Bagidajiya ce Hausa Novel Complete

Bismillahir~ rahmanir~ raheem

 

 

___________________________

 

 

1️⃣&2️⃣

 

 

 

 

*Kauyen fallankin malam yahaya*

*Zuntu*

 

 

Wani irin gudu takeci uwa rainta zai fita,sakamakon ganin ‘yan kungiyarta suna dab da shigewa rutsutsin wajen gonakin.kwalla ma daya daga cikin su kiratakeyi da karfi, hakan yasa suka dakata da tafiyan.

Har ta Karaso cikeda haki

“K’ure dadi nine zakuyiwa wulakanci ko?,wato da bansauriba tafiya zakuyi kubarniko?”

 

“Laa bahaka bane indo kinsanifa sarai lokacin birek gajerene…gashi munada yawa masu cin gwavan inba muje da wuriba za’a iya komawa aji ,ko masu gonan su zo”

 

“Wooo, kahe da sunhememu…hanzarta mu higa layi yanda akasa ba ,kasan gonan nan akwai hi da hammatsi” tafada da lalataccen hausan ta na gidadawan ‘kauye

Layi maza uku sukayi agabanta sai rahane kawarta ta biyar sauran mazan abayansu

A hankali take tafiya sadaf sadaf cikeda tsoron karta taka kan maciji…har suka iso fili suka fito sosai iya ganin ka mai cikeda bishiyoyin mangoro da guava

Daf undo tahaye nagovan tana watse masu suna watsawa abuhu

 

Dagacan nesa wani mutumi dake gyangyadi karkashin bishiya da zugegen dorina a gabansa, ga dukkan alamu maigadin wajen ne,ya hango su a hankali yashiga sad’ad’awa wajenda suke,karaf kan idon indo,dirkowa tayi akan bishiyar jikake tif!

 

Hada baki sauran sukayi suna fadin “lafiya?”

Ai yankan hanya tayi da gudu tana gayamasu cikib waka faditake”ga mai gona ga mai gona nan…Wanda yakalla banyafeba”.

Haba kafa mai naci banvakiba,shimako maigadin yadade masu baya .gudu sukaringayi tun suna jin nishad’i har indo tafara kuka ,tuni a hanyar sun zubarda buhun goban amma mutiminka yaki daina binsu, har suka shiga filin makarantan yana binsu.daidai nan aka kada kararrawa na komawa aji, ai dagudu suka hade da yara kowa yayi ajinsu.

 

Koda maigadi yaga sun tsira ,takaicin gudun da yayi yakeyi,atake yayanke shawarar tafiya ofishin malamai yakai kararsu

Duk ko malaman suna nan…

Discipline master ne yamike cikeda fushi yacewa mutumin “yi hakuri malam ,yanzu duk sun gama shiga aji don haka muje inzaja iya ganesu a tsintosu”

 

“Tabbas zangane ,wannan mai muryar chanisawan(yana nufin indo)

 

Aji aji yaringa zagawa dashi ,har sukazo js 3 anan tun kafin sushigo yayi idobiyu da idon indo ta windown ajin ,ido ranbadadau da kwalli. Daganinta kaga Mara gaskiya.

 

” malam itace wagga”yanuna ta da yatsa da sauri

Malamin bai wani damuba don yasan indai indoce zata aikata abunda yafi haka

 

“Fito gaban allo kowa yaganki barauniya,ina sauran?” Cewar discipline master.

First Ramadan with Habibi Hausa Novel Complete

Ganin ba matsera yasa tafito tana muzurai,kyar tayi da ido ma en ajin

“K’ura dadi,lafazi,rahane….kai nagaji dakiran sunayenku,malamai ai he kuhito ko”

Ba arziki suka yo waje ,don sunsan inya zakado su zafa adake sun,sukuma bi hanya itama ta narka.

dukansu saida suka fito malamin ya mikama maigona bulala yazanesu…haba kura dadi yafara gaba shine dama bai tsoron bulala, sauke masa da yafara yi ,azabar dukan yagigitashi kwara ihu yakeyi iya karfinsa,tuni idon indo ya raina fata,baya taringa yi har tajingina da gajeran windon ajin basu yi auneba saidai sukaji dirkanta cikin gonakin bayan ajinsu,kalkalawa tayi da gudu ‘yan ajin akasa sukabita amma haka suka kare gudun su suka dawo don tab’ace masu.

Dabalain gudu tashiga gidan,mama na tsugune tana wankin waken alala bataji shigiwarta ba saidai taga giftawarta tayi ciki da roban waken.

Mikewa mama tayi tana tafa hannu tareda sallallami

“Auta wa kuma kika tono yau ?ina makarantab?kifito inji nace”

 

“Alkur’an mama banfitotwa sukamani….ke makarantan ma anbari daga yau…yasin yau ban kwanan garin nan tunda kowa ya tsaneni”

 

Shigowa dakin tayi ,taciro ta a bayan kofan.

“To kwantarda hankalinki kimun bayani sosai”

Hmmm inazuwa ” randa tanufa ta dibi ruwa a mod’a tashiga kwankwa’da daga nesa kanajin karan wucewar ruwan.tana gama sha ta suri buta taje bakin vandakin gidan ta tsula fitsarinta yako gangaro wajen dakin yaya(kishiyar mamanta)ta kakkabe jikinta tashigo daki.

Mama nanan zuru tana jiran fitowa r ta, zama tayi kan tabarma gefen mama tayi gyaran murya tasoma koromata bayani

 

“Mama ina gonan gobannan danake kawo maki kinaci ,kina tond’e baki?todai yau dubunmu tacika dinko su rahane yau sunkade har buzunsu da duka….”

 

“Ke tsaya auta menene na duka kusiya Abu da kudinku?”

 

“Tab lallai ma to debosu mukeyi ,hannu nki ana ke hin dauka kudi muke basu to yasin yau ban zaman garin nan Zaria ba nufa gidan anty,bazan zauna me gari yazo akamoniba,dama gashi da jikakka tsakanina dashi….ki tashi ki shirya mun kaya don alkuran akazo kamani zance kece barauniyar zaunen ,akama dake…”

 

“Auta nice barauniyar ?to ba inda zaki kijamasu magana ,acan su basu saba da hayani yaba ,unguwarsu na natsatsune”

 

Geiwoyinta tasa a kasa tana rokonta “mama nice fa autarki indo,zakiso akashani,ji nake idan na kara kwana ajalina kekira ,konafada ruwa ko rijiya…

 

…..to shahararriya fito ki wanke fitsarin da kikayi ….ace kaf ,kafin gidannan kin karyesu da fitsari?komai nagida kin lalaceshi ,mudai anhaifo mana annoba”

“Bani bace annoba sunusi danki shine annoba”buge bakinta mama tayi,tasoma ba yaya hakuri

 

” yimana shiru baqar algunguma…ba kece kikajaba,to maza sata tawankemun kofar daki don bazan dauki cin kashiba”Tsidik tayi mata a gaba

“Ninan na isheki ,kuma tunda kika zagi uwata abakin wankin fitsarin kofar dakin ki”

Tayi shigewarta muryan daki tahaye gado,masifa taringa yi kamar zata ari baki tagaji tafita ,don takaici ya hana mama bintu magana.saida taji tsiyar ya kwanta,tashiga tasameta tayi daidai a gado tana barci hankali kwance.daka Mata duka tayi acinya

“Jai’rah tashi ki hada kayan ki kitafi zarian,konaji kunne na kwana biyu”

Aidasauri tafigi Ghana mustgo tagaudanna kayanta acikin.taje tadako tsaminta tadan gurza Vaseline guburi guburi,tayafa kanannadadden mayafintada kila baitava ganin iron ba a rayuwar sa

“Mama na shirya sallameni,karsu taso makarantan” tsaki tayi ta kwanto hannun zani taciro Dari biyar tabata,tashi ga rumbu ta jibgo kayan tsaraba irin nasu na ‘yankauye tabata takai masu.mai baro tafita tanemo ya kwashe kayan ta suka tafi tasha,saida tajita a motar Zaria .kuma tacika sun hau kwalta tafara jin daidai a ranta”cab ai Yaseen sai na huta na watanni zandawo lokacin komai ya lafa…,”tunanin rayuwar ta data gudanar a garinsun yasoma dawowa kwanyarta,tartar………

 

 

#vote

#share

#comments

[8/19, 10:09 AM] Haisahhtttttt💅🏻: 👠👠💅🏻BAGIDAJIYACE👠👠💅🏻

 

 

 

 

*©️HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

*(Home of peace, joint entertainment to educate and enlighten our readers)*

 

 

 

 

Wannan pajin nakune kuyi duk yanda kukaso dashi,,, kawayena,aminan arziki,abokan tsegumi da dan gulma🤪

Aisha Abubakar musa(mrz zuntu)

Zainab Isah (hajiya babba)

 

 

 

Written by✍🏻

Hassenart Mohammed😘

 

 

Littafan marubuciyar:-

 

-RAYUWAR AFREDARH (Endless love)

 

-QASAITATTUN MATA

 

-RAMUWAR GAYYA (The shaded blood)

 

_And now_

 

BAGIDAJIYACE

 

 

*littafina dashi da ramuwar gayya,dukna kudine#200na mtn ake biya ta wannan number 09065990264 inkuma vip kikeso zaki turo #300 👷ace tabiya na ramuwar gayya kuma #100 zata biya VIP #200 𣁈ajiya daure rage ciki kibiya ba tsada bane gareshi da zaisa sai anfita maki dashi kina jira aturo kisamu, inmai turowa hidima yasha masa kaifa🙃😏*

 

 

 

___________________________

 

 

3️⃣~4️⃣

 

 

Wani handsome sojane fari tar kyakyawa ajin farko sanye cikin farar T-shirt da gajeren wandon kakinsu, nagani tsaye acikin filin wajen training din ‘yan Navy acikin makarantar NDA ta kaduna,gadai dukkan alamu dalibin department dinne .waya yakeyi cikin natsuwa…ayanayinsa da yanda yake harhad’a maganarsa zakagane shid’in bamai cika son hayaniya bane,da yawan surutu….

daidai nan wata matashiyar inyamura takaraso wajen dayake itakuma cikin complete shigan uniform dinsu na navy,amma tana d’auke da alamar ‘yan shekaran farko,acikin collegin.

 

Tana ganin sa ta fara feck call,”hello my friend,can u hear me?…eh I told u what man can do,a woman can do beyond… Letz…”rashin sani kenan donko

Awani bala’in zuciye yaje ya shaqota ya jefata cikin wani tabon jar kasa mai dauke da ruwa kimbul,tako fada ta fuska, ji kake facccch!, yayi saurin bin bayanta kafin ta dago yataka keyarta fuskarta dakanta yalume cikin ruwan jar kasan mai kamada yanbu na training dinsu.haba wutsil witsil takeyi da kafa kamar kifi, tana kuka amma bakaji saima ruwan dake shigamata ta hanci da baki,adole tai shiru cikin sadakar da cigaban rayuwa.shikan gogan ko a jikinsa saima yacigaba da wayarsa.

 

Da sauri wani matashin sojan ya ‘karaso wajen dasuke,rai a ‘bace ya saita cinyar kafar da ya daura akanta ,ya kaimasa tokari da sauri yad’an goce, cikin sauri yayi azamar janyota ya watsar gefe,sannan ya soma magana

“Farouk yaushe kazama maras imani ?,kashata zakayi komene,jibe tafa wannan tama suma…taimaka mukaita asibiti”

 

“…kai baka da hankali,nine zanyi punishing mutum kuma inzo inkaishi inda zai samu relieve?… Bayan rashin kunyarda victim din taimun?Towaima me ruwan ka dani da zaka daka tar dani eyee haidar?,kamata yayi kabarni inbata lesson tukuna,i want to confirm her that,what man can do, a women can never ever do…even if they can die and resurrected hundred times,so now banwaje mtseww”

bai jira tacewarsaba ya ja tsaki ya bar wajen.girgiza kai aliyu yayi ,yakira juniors dinsu dasuka zo wucewa yasa suka taimaka suka dauketa zuwa asibitin cikin makarantan.

 

 

 

**********

 

Indo kam an sauka a tashar kofar doka cikin zeetown lafiya, mai Babur tayi kiran sa tayi masa kwatancen inda zai kaita ,yadaukar mata buhun tsara barta,yasa agaba , tsohon Ghana must go dinta abaya sannan itama tahaye bayan.tiiiiiiii haka yakwasheta har GRA .daidai kofar wani gida dayafi duk sauran gidajen gurin tsaruwa ya ajeta ,taciro #200 tabasa yanda sukayi ciniki,kamar mumina Wanda tasaba biyar masu ocada hakkinsu,yo ehmana matarda saidai ta dirka tafalla a guje tace inkanada zarra kabiyota ka amsa?!

 

Tadad’e tsaye kafin tasami almajiri tarokesa ya shigar mata da kayan.

Tundaga bugun gate d’in, gatemen din su kasan sunyi ba’kin mahaukata.

Don haka dasauri nakusada kofar ya bude cikeda fushi dafatan kama kowaye ya Zane….ganin ta yasasu saranda don yasan watan aikin su ya tsaya,baxai taba manceta da balainta ba,sakin baki yayi galala yana istigfari aransa inyayiwa Allah laifine ,donko hadaka da indo gida daya babbar jarabawace…”

Bai ida zancen zucinba yaji takarashe hankado gate din ji kake,garararaf to ufo ciki abunta,a firgice ya juyo yana kallonta

“Malam inkagama kalle kallen ba yaro waje yahuce,haba mutum haka sai kallon tsiya ba aiki?, Sam anty bahuyi sahan mai gadiba…wannan ai shai yarinka koron masu bakin alkhairi”

Fuuuu tayi ciki da katon ghana mustgo dinta akai.

Dasauri ya amshi buhun hannun almajirin,yabi bayanta dashi don Sam baiso yazama na farko dazasuna soma rikici.

 

 

Babban kofar dazai sadaka da asalin cikin gidan tashiga kai tsaye,tasoma kwarara sallama

“Assalamu alaikum sallama nake,gaba kuwa gaisheku take,ina antyn tambayrku nake”

“Barkanki da zuwa…anty na ciki” taron masu aikin suka hada baki wajen bata amsa.

Cikeda fargaba daya daga cikin housemaid din ta amsheta da Jakarta ,har cikin falon.

ACikin falon ,Hassana da Husseinane zaune akan kujera Hassana game take a laptop dinta Hussaina na charting da wayarta ta like kunnenta da earpiece, sai Ahmad dan karamin kaninsu dabazai gaza 10years ba,dake kan dinning yana shan Golding morn.ga karan t.v dayacika falon ,din haka Sam basu ji shigowar taba saidai sukaji dirkan buhu akan center Carpet din ,take kurar kuka da barkonu yatashi alamun sun fashe ta cikin buhun.daidai nan indo tasoma magana

“Kai dan uwarku bakuga muhane bane hiyyeee”

Ai tari suka dauka atare,don Hassana harda hawayen azaba don direct yawuce mata ta kofofin hancinta.

dasauri tarufe laptop dinta tabar shinan tahaura sama da gudu,sauran ‘yan uwannata suka dafe mata baya

 

Tsaki tayi tasama kujera tabaje tanajiran azo atarbeta,shiru har kusan Rabin awa. Sannan ne Hassana tadawo falon,tasungumi laptop dinta tanufi hanyar komawa dakin su

 

“Ke ina uwartakune,ne ne?”

“Kai indo kin cika fitina to tana dakin abbey kuma har yanzu ba tafito ba tukun, sai kijira in akayi azuhur zasu fito ai”

 

“Caftsi,kenan zaman cikin nan zantayi?,aiko na gaji saidai ko naje dakinku najirata….yaa shafii kafii” takarashe maganar ta tareda yunkurawa tayi hanyar wajen steps din.Ai azabure Hassana tayi ciki da gudu kamar wacce ta ga horror, tashige dakin su tamurza key da sauri.

Jingina tayi da jikin kofar tana hakiiy.

 

“Ke lafiyarki kuwa?” Hussaina takaraso tana tambayarta

 

“Inafa lafiya, laluwa bala’i zata shigo mana daki”bugun kofar suka somaji da karfi

“Mtseww to meye ?,ke wannan tsoron ne zaisa tarainaki….kina ganinta da lodin kayannan ,kinsan tafiyanta ba yanzuba…kuma kinsan abbey baison hayaniya ,ji yanda take bugun kofa?” Janyeta tayi ajikin kofar tamurza key din ta bude tashigo,duk suka koma gadon su suka zauna

 

“Ke to meye na guduwa ,harda sa makulli saikace kinga mu da fatalwa?”

Hussaina ne tasoma magana cikeda kambamawa

“Wanemu anty ayeeshar…jakadiya er saleh,sa baki dariya sai yak’e ,kowa yace zaiga dariyansa ya mutu ,margamargan dutse kinfi gaban aljihu….barkanku da zuwa bakin zuntu”………..

 

” aiho ai na aza baku marhabin danine ,dasaina koma inda nafito “.

Allahumma ameen, Hassana tace a hankali

 

” wanemu anty ,salan kija mana fushin ummy….ai murnar ganiki muke…(ta waigo da fuskarta wajen Hassana) ai ma ringa samun dadadan labaran ban dariya awajeta ko !”

 

Gyada kai tayi kawai batace komaiba.turo kofar akayi,ummyne da abbey suka shigo yi mata sannu da zuwa,din dinki shigewarta

 

“Barkaana ,barkaana daganinku mutanen zuntu…kun iso lafiya?”

Dadyne yake magana tareda tafa hannu wa fuskarsa cikeda fara’ah

 

“Barkankadai alhajinsu ‘yan biyu…munsameku lafiya”

“Lafiya klou,ya wajen su mama….Hassana yabakusata tai wankaba”ya tambaya cikin sigar tsokana

 

” yoooh inbanda abinka alhj yazasu martaba ni ,haikashe fatsima uwarsu?…dadai itane zasu bata…to kusani matsayin mu daya da fatsime dan iyayen Ku,gatanan tsaye Ku tambayeta “tafada tana zazzare ido kamar uwarsu

 

” ayi hakuri dai ranki yadade…kuruciyace”abbah yafada cikin sugar zolaya dafatan kwantarda tarzoma

 

“Hmmm…wai ina mutumina ne aliyu haidara,hoja mazan hwama” tafada tana washe dafaffun hakoranta

 

Ummyy ta amshe maganar”Nana aisha tashi muje dakina …sweetheart kubiyota da Jakarta…aliyu na makaranta ,but munasa karan zuwansu a satinnan”

 

“Eyyah Allah yakawoshi lafiya donjin gidannan nake uwa maka barta dabayanan” tafada tana karkade ‘Yar zaninta tamike tabi bayan ummy ,Abby ma yafita.

 

 

 

 

#vote

#share

#comments

[8/19, 10:10 AM] Haisahhtttttt💅🏻: 👠👠💅🏻BAGIDAJIYACE👠👠💅🏻

 

 

*©️HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

*(Home of peace,joint entertainment to educate and enlighten our readers)*

 

 

This page ix wholly dedicated to my besty Hameedart 🥰

Allah yabama mamanki twins,anty habiba saura karkice ameen🤩🤩

 

 

 

Written by

Hassenart

 

 

 

Littatafan marubuciyan:-

 

-RAYUWAR AFREDARH (Endless love)

 

-QASAITATTUN MATA

 

-RAMUWAR GAYYA (The shaded blood)

 

And Now

 

BAGIDAJIYACE

 

 

*Wannan littafin na kudine only #200 VIP #300 , idan kinbiya na ramuwar gayyya kibiya #100 vip #200. Hanzarta kibiya kudinki kafin nagama*💃💃💃

 

 

5️⃣~6️⃣

 

 

*WACECE INDODO*

 

 

Indo Aisha diyace ga mal.abdullahi da mal.binta

Mal.Abdullahi asalin su fulanin usulne ‘yan asalin garin zuntu a wani ‘kauye da ake kiransa fallanki,babansa ,shi yakafa kauyen sunan shi mal.yahya ,amma shidan kauyen gabane ana kiran kauyen *fallankin sab’a dutse* to lokacin da ya bar kauyensu da matanshi ,sai yayi ‘yar madaidaicin gidansu suka zauna anan.

sai ya zamana infulani sukazo wucewa zasu sauka awajen sudanyi bukkansu na wucin gadi sutashi wasu su tsaya,ahaka waje yayi tayawa har yazama gari ana cemasa fallankin mal.yahya.

 

Mal.yahya yana da matan aure hudu dayara Ashirin da uku ,Ashirin da daya matane biyu maza Abdullahi da Abdussalamu

 

Lokacin da yaran shi maza suka fara tasa wane yadaukesu yakaisu almajiranci abdullahi aka kaisa Zaria ,shi kuma abdulsalamu yafi kusa akabarsa a soba .

 

Abdullahi Dane mai hazaka saida yayi sauka sau uku da tishi ,abdulsalam baiyi dayaba. adon haka sai yafara sana’arn dinkin hula anan cikin Zaria ung. Albarkawa tunda ba halin komawa yabar dan uwansa bai dawoba,yina sana’ar sa yana karatun littafai don sun zama gardawa.Ahaka wata rana wani alhj Ilu dake sayan hula a wajen sa yayi masa tayin makarantan boko ,bai wani musaba don yana da sha’awar karatun dama can,yaroki mutumin da yazo ya rokar mashi malamin su in ya amince.

 

Bai sha wani wuyaba sakamakon toshe masa baki da kudi dayayi.

Damakarantan yaki da jahilci yasoma, daganan yawuce secondary yafara daga form 1 har 5 .lokacin har yafara sana’ar yadiddika da dinka Manyan riguna yana saidawa attajirai da masu sarauta duk da taimakon wannan alhajin

 

Koda yagama sakandire makarantan gaba yanema yasamu yayi diploma daganan karatun ya tsaya ,saboda hura masa wuta a kauyensu da akayi da yayi aure a lokacin tuni abdussalami yayi aure matansa biyu da ‘yaya rututu.

 

Alhaji Ilu mai gidansa yasama da maganar, yagayama duk matsalar da yake ciki,kwantar masa da hankali yayi sosai yakarba takardunsa yasamar masa aiki a wani babban kotu dake a sabon gari.yakuma wanke ‘yarsa bintu yabasa da kyautar gida.

 

Hankali kwance yake gudanar da rayuwarsa arziki na kara bunkasa har suka hayayyafa a lokacin da binta tahaifi yara biyune Fatima da ameena danginshi nacan suka matsa sai ya auri ‘Yar uwansa yahadasu inbahakaba,’yan Zaria zasu kwashe arzikinsa inya rasu,binta tanada sanyin hali batada hayaniya samsam .

 

Bata matsa masaba ya auro matarsa kuluwa amma ana kiranta yaya yabarta acan fallankin bayan ya Gina gidansa me kyau acan.

 

Tunda binta tahaifi ‘yarta Rahma haihuwar ta tsaya mata.bare kuma yaya da ko b’atan wata bata tab’a yiba.

 

Tuni fatima da amina sun girma har anyi bikinsu ameena a tudun wada tayi aure da yaranta uku dayake gwarne takeyi itakuma fatima tabiyo mamansune danta kenan daya alokacin sunansa Aliyu a hanwa suka fara zama da mijinta cikin danginsa.

Itakuma rahma ansamata rana da wani dan Abuja yazo bautar kasa makarantarsu,suka hadu

 

Sai a wannan lokacin ne ciki bul ya bayyana ajikin mama binta daabokiyar zamanta yaya .

 

Akuma wannan lokacin ne mal.yahya Allah yayi masa rasuwa.

 

Suka d’ibi jiki aka tafi gaisuwa bayan an share zaman makoki an raba gado mal.abdullahi yayi shirin komawa Zaria ,nan enuwanshi suke shaida masa wasiccin babansa dayayi akan yadawo fallanki da iyalansa da zama.

 

Yayi kukan bakin ciki bintama tayi ai wannan shi ake kira karkon kifi daga cikin gari sai dosun kauye?

 

Adole yakara fadin gininsa yayi masu wadataccen gini na sumunti ,yaje wajen aikin su aka bashi transfer yadawo kotun zuntu.

 

Basudawo fallanki da zamaba saida sukajira akayi bikin rahma acan zarian amarya tatare agidan mijinta a abuja

 

Anan fallankin tahaifi ‘yarta aishatu danginta nacan nakiranta indo,itama yaya tahaifi danta namiji ana kiransa sanusi,sa’annine indo da sanusi wata biyu sanusi yabata.itakuma lokacin Fatima tana goyon ‘yan biyunta sunba indo wata hudu.

 

A lokacin da indo da sanusine suka isa shiga makaranta babansu yasakasu a primary din cikin garin zuntu,kullum in zaije aiki zai tafi dasu.in lokacin tashi yayi yaje yadaukesu su wuce gida,a kullum cikin kawo masa kararta ake yau taci abincin wane,gobe ta Zane wane, tankwalace original duk jarabawa ita ke daukan na baya.ancancanja makarantu ba adadi amma Sam ba abunda ya sauyata nadaga kokari ko kawo kararta kan yaran mutane

 

Dama kuma tunda indo ta taso , tun bata wuce shekaru ukuba tayi tanbari a unguwansu to, cizon yaran jama’ah iyaye na ganin ta ,suke dauke yaransu su Goya, ga rigima.

 

Watarana ne anty Fatima tazo garin da ‘yan biyunta,shikenan tunda yara sukazo garin suka daina shan ruwan garin ko anbasu sai sun amayar,A lokacin basufi shekaru biyar ba,take suka fara rama.da tana kawaici ne saboda alkunyar dake tsakanin ta da maman matsayin ta na ‘Yar fari ,bata ko kula ‘yayanta bare ita kanta.gashi basuyi sa’ar kishiyar uwaba don Sam harsuzo sutafi daga gaisuwa ba maganar da zai sake hada su.

 

Ganin ‘yayan mutane na Neman halaka abanza ,ai ba arziki tazari keyn motarta taje nemo masu ruwan roba a cikin gari,don tasan ruwan rijiyar garinne badadi kuma ita bazata iya basu narafiba.

Cartons 5 tasiyo dasu caprison datarkacen chocolate takawo masu. Aikoba ajimaba ,yara suka murmure suka saki jikinsu.

Saidaime?tunda indo ta kyalla ido taga ruwa ,tashi ga jida ,tana bama yaran makota da almajirai kwaf daya, saida takrar da duka ,itace kwabin wasan kasa dashi ,tajika jiki ta bannatar.

tun Fatima na kawaici harta kare dai ta tsawa tar mata.

Haba dan fadarda taima ta keda wuya ,tasami karkashin inuwa tamike kafa ta runtse ido taringa kwarara ihu iya karfinta,kaf saida ta tada hankalin gidan,kowa yazo lallashinta sai aga ido a soye ba d’igon hawaye.

 

Tun safe har karfe biyu tayi zufa sharkaf ,kowa dayagaji dole suka shige daki suka barta ,harsaida tayi su amai sannan bacci ya sureta a wajen.

 

Fatima da yaran ta kam tundaga lokacin suka fara ganin babi babi na izaya,shiga dubu fita dari saita jibgesu,don dole ta tattara kawunan ‘yayanta suka koma inda suka fito.

 

Haka rayuwa tacigaba da gungurawa ,har indo suka shiga shekaru takwas,nan akeyinta

Don ita gabadaya tatasone tsundum cikin ‘yan kauye bata San komaiba daga zuwa dandali sai taya kawayenta Fulanin dasuke zama a kauyen kiwaon shanayensu.

Tsabagen karfi dajin naci tuwon dawa na kangare har siyanfada takeyi.

 

Za’ai girkin engayu adakinsu zata fitar suyi musaye da ‘yayan makota wai bata iya cimarba ,itadai tasha fate da sugar ba manja,dan gauda,tukurkusu dadai sauransu don haka tataso kakkaura gidirgir kakkarfa da karfi kamar shara’a uwa wani namijin

 

Tunda yaya tahaifi da namiji bayan dogon zangon da ta kwashe ba haihuwa ,shikenan gori ya ishi mama binta ,wai sune da gida ,waye waye……

 

Wataranar sallah ce kaf yaran mama sunzo da yaransu duk mazajensu suka kawosu,basuyo abincin sallah ba saboda nisa amma sun kawo buhunhuna da gallons na mangyada da manja da komai namahadin girki.

 

Mama wayayyiyace don haka dasauri tadaura babban tukunya taraya masu girki dayaji tsokokin kaji,tahada masu lafiyayyen kunun aya dayaji madara ta aika akaje zuntu aka nemo mata kankara tasaka aciki

Ta wanke lafiyayyun plates ,warmers da spoons tagoge ,tazuba komai tashimfeda dardumanta na alfarma datayo a saudiyya tashirya masu komai a falonta

Suka baje kwansu da kwarkwatansu,sukaja gara cikeda barkwanci da wasa da dariya kamar zuri’a daya

 

Takaici kam habaici dayada magana mama sun shata, ko kusa taki ko zuwa su gaisa saboda bakin ciki

 

mazan da zasu tafi,kowa da kudinshi na albarka,Rafa Rafa sule yaya ba tasamu ba,yooo basuma San da itaba.

 

Fitonsu keda wuya tajawo murhu tahada wutankara tafara mulla tuwo,tana wake wake: “duniya rawar ‘yan matane na gaba yakoma baya”

Sarai sumama sun gane mai take nufi amma bawanda yatankata

Cikin sa’a saiga daidai daita tashigo a keken almajiran gidansu data ara

 

“6ii6itttttttt!!!

abani waje kar nayi 6anna,akaudakaya harnayi kutubal dashi alkur’an…..”

Hango yaya tatakarkare tana tuka tuwo,kawai sai ranta ya kissima mata ta roreta da fada

 

Kewaye ta da murhunta tashiga yi da keken “agafara ba birki Yaseen”wani gigir,gigir tashiga yi da kan keken kamar zata duro ta jikinta,raba mata hankali yasoma yi jiri nadibanta,ga hucin tuwo,ga wuta gakeke da ke wuliwuli akanta.

 

” ke dan iyayen ki bar nan” tafada tana zare idanuwa

 

“Hajiya nakwalla shugaban aiki maza tukesa Tass,din vamusan guda…don dole ki tuke katon tukuny mu danna …..wooooo ‘Yar aiki ke daya daya dagake saidanki sanusi mai kan jaki…..kinaji zaki kwashe ki kawo mana”

 

Yo kanta tayi dagudu zata daketa ,tako zille ta watsar da keken ckan tukunyar ,yako 6are cikin wutan,ji kake cuuuuiuuu!!!

 

 

“Wayyo jama’a gudunmawa ta shekarmun da tuwo” tasa hannu aka tana kwarara ihu ,cikinta ba kululu na azababben yunwa.

 

Lankwashe murya indo tayi sannan tayi maganar da karfi ,yanda kowa zaiji a aza indon keda gaskiya

 

“Wayyo yayan mu saida nace maki ba burki ….kiyi hankuri bari naroko maki abincin en birni dakin mamanmu” tadaddalo mata ido tana mata gwalo da dariyan sak’e

 

“Saidai ki roko wa uwarki dinmu bamuyi gadon rokoba” tanayi tana matsowa kusada inda take

 

Tsalle tayi taje kofar fita waje”haba Yar tsohuwa ,tarrr nake kallon ki…..kije jira zamanku da yunwa dan aradu babana yau famfo zammai ga abinci gida baxai asaran kudi yabakiba……hahhhhh yau wata zataga malaikan mutuwa azzallaruruwa me wukaken azaba kala dubu”tafalla aguje tabar gidan

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment