Hafsatu Manga Hausa Novels Complete
Hafsatu Manga Hausa Novels Complete
HAFSATU MANGA
_Yarinyar Kauye_
Wattpad @KhadeejaCandy
Assalamu alaikum Habibaties, fatar duk kuna lafiya 😍 Na sake dowowa da labarin kauye kuma labarin sarauta mai suna HAFSATU MANGA 👌
Labari ne mai cike da kauyanci, ban dariya, sarauta da kuma makirci.
Happy reading 😍
_____________________________________
1⃣
A hakali ta sauko saman Motar fuskarta ɗauke da damuwa.
“Na gode”
Ta furta murya ƙasa-ƙasa kamar mai shirin yin kuka. Dattijon da ta yi ma godiyar ya ciro wata tsohuwar naira ɗari ya miƙa mata yana faɗin
“Karɓi wannan ki siye abinci”
Sai da ta share hawayen da suka zubo mata sannan tasa hannu biyu ta karɓa tana masa godiya
“Na gode Allah ya saka maka da alheri”
“Babu komai Allah yayi miki mafita”
Cewar Dattijon, mutanen da ke cikin Motar suka amsa da
“Amin”
Sannan Dattijon ya tashi Motar suka hau titin unguwar Gada biyu, titin da zai sada su da tsakiyar birnin Gusau.
Da kallo ta bi Motar itacen, hawaye na bin fuskarta, sai da ta daina hango Motar sannan ta maida dubanta gurin manyan gidajen da suke gabanta, wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da kuka mai ƙarfi, kukan da bata san ta ina yake fito mata ba, kukan da ba ta san ranar tsayawarsa ba, hawayen da babu mai share mata su, sai Ubangijin daya ƙaddaro mata rayuwar da ta tsinci kanta ciki.
Ba ta damu da rashin takalminta ba, ta cira ƙafafunta cikin rashin kuzar tana ɗingishi ta nufi wata ƴar kwarkwaɗar data hango wadda ke tsakankanin gida da gida, cikin kwarkwaɗar ta shige ta zauna saman simintin dake gurin sai ta fashe ta sabon kuka muryar a daƙishe saboda majinar data kama maƙoshinta.
Kuka take mai tsuma zuciyar mai sauraro, kuka mai ban tausayi, kukan rashin Uwa da Uba, kukan rashin ƴan’uwa da abokan rayuwa, kukan rayuwar da ta samu kanta da kuma wanda zata zo mata nan gaba, kukan rashin sanin makomarta, kukan baron duniyar jindaɗi, duniyar dake cike da masoyanta da abonkan rayuwarta, lokaci ɗaya komai ya tsarwatse mata ta rasa komai nata, yau gata cikin duniyar da bata san kowa ba.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, na shiga uku na bani na lalace, wayyo ni Allah na”
Ta furta hakan yafi a ƙirga kamin kuka ya ci ƙarfinta, ta ɗauki tsawon lokaci a gurin tana kuka ba tare da kowa ya kula ba, kasancewar unguwar manyan mutane ce, ba kasafai za ka ga mutane a unguwar ba, sai Motacin dake kai da kawo suma kuma ba sosai ba, mutane dake tafiya da ƙafa kuma tsinta-tsinta ne kowa na sha’anin gabansa, ba kowa ba ne zai kula da gurin da take zaune balle har a iya gano da mutun a gurin kasancewar yamma tayi sosai.
Hakan ya bata damar tausayawa kanta, ta ci kukanta har ta gode Allah ba tare da kowa yaji ba.
Kiran Sallah Magariba ne ya saukar mata da natsuwa har ta samu damar jan numfashi ta lumshe ido tana sauraren Ladani tana girgiza kai. Yau Magariba tayi mata ba’a gida ba, wasu zazzafan hawaye ne suka fito daga idonta dake rufe suka gangaro zuwa kumatunta.
A she kayi kuka a kula da kai a baka haƙuri gata ne, ji take kamar wani ya zo ya dafata ya rarrasheta kamar yadda mahaifiyarta take mata a duk lokacin da take kuka, amman ina! Yau ta rasa wannan gatan, lokaci ɗaya haske ya zame mata duhu, fari ya koma mata baƙi duniyarta ta barkace ta zo mata bai-bai, ji take kamar ita kaɗai ce ta rage a duniya, jikinta na bata wani yanayi na daban komai ganinsa take kamar mafarki.
Sai daf da ƙare Sallah Magariba sannan ta fyace majinar data ɓata mata fuska, ba ta damu da share hawayen ba, ta fito daga kwarkwaɗar tana cigaba da ɗingishi.
Hanyar dake damanta ta kallah kamin hagu, sai shawartar zuciyarta take gurin zuwa, ga kanta babu ko ɗankwali, zane da rigar dake jikinta ma ko wanne daban-daban ne kamar wata sabuwar haukaciya.
Cikin unguwar ta kutsa kai, ba dan tasan inda za ta ba je ba, ita dai tafiya kawai take tana kalle-kallen manyan gidaje. Tafiya ta riƙayi har ta kusa kaiwa ƙarshen unguwar bata ga gidan da zata iya shiga roƙon mayafi ba balle abinci, a ƙofar wani ƙaton gida ta tsaya tana ƙare masa kallo, babban gida ne da aka ƙawata shi da ƙwayaƙwan lantarki, a gefen gidan kuma an yi masa kwalliya da fulawoyi masu kyau da ɗaukar hankali.
A tunaninta babu mutane a gidan haka zuciyarta ta nasalta mata, gurin da fulawoyin suke ta nufa, kasancewarsu ba masu tsawo sosai ba, ya bata damar tsallakawa ta shiga ɗan filin dake tsakanin fulawoyin da kuma ginar gidan, zaunawa tayi a gurin zuciyarta cike da rauni da zullumin abunda zai same ta.
Ɗaya bayan ɗaya tunanin ƴan gidansu ya soma dawo mata, nan take kanta ya fara sarawa tana son kuka amman ba hawaye, a haka ta gaji ta kwanta a gurin sauro na bin ƙafafunta da hannayenta, ba a ɗauki dogon lokaci ba bachi ya yi gaba da ita.
Bachinta bai kai na mintuna ashirin ba, aka buɗe ƙofar gidan da ƙarfi, hakan yayi sanadin tashinta a firgice har tana ƙoƙarin yin ihu, a zatonta mutane da suka kawo musu wacan harin ne suka sake dawowa, ɗan bachin da ta yi yasa ta manta da inda take, da sauri ta fito daga cikin fulawoyin tana haƙi.
Daga mai gadin har yaran gidan sakar mata ido suka yi, kowa kallon mahaukaciya yake mata, bama kamar mai gadin da ya haske ta da fitilar hannu.
“Ke bar nan gurin”
Mai gadin ya faɗa a tsawace. A maimakon tayi magana sai kawai ta fashe da kuka ta juya a firgice ta nufi sashen wasu gidajen, ba dan tasan inda zata ba sai dan kawai tayi nisa da gurin da mai gadin yake dan ta tsorata da yanayinsa sosai.
A ƙofar wani gidan ta zauna tana cigaba da kukan, bata tuna ta jefar da naira ɗarin dake hannunta ba, har sai da cikinta ya fara kukan yunwa da ƙishin ruwa a lokaci ɗaya, wani irin murɗa cikin yake mata hanjinta na kukan yuwanwa, ji take idan bata ci abinci a yanzu ba za ta iya mutuwa, duƙawa ta yi a gurin ta matse cikinta ta rumtse ido.
______________________________
Labarin Masarautar Rishim da kuma Kauyen Kufawa. Labarine mai cike da sarkakiya, ban dariya, kauyanci, kurciyar Hafsat, tausayi, tashin hankali da dai sauransu
[2/19, 9:46 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_
Wattpad @KhadeejaCandy
2⃣
Komawa tai can gefe ta zauna hawaye na bin fuskarta, kuka take son yi amman babu muryar kukan saboda rashin kuzari dake tattare da ita. Dama ta fara dubawa kamin ta duba hagu kamar mai tunanin inda zata je. Tana haka aka bude katon gate din take gefenta ta firgita sosai abun ka da bakauye sai kawai ta ranta cikin na kare ta koma can bayan kwarkwadar ta buya tana lekon mutumen daya fito daga cikin gidan ya doshi wata hanyar daban dan shi be ma kula da ita ba. Sai ta tabbatar yai nisa sannan ta fito tana tafiya a hankali sai waige waige take har ta isa bakin gate din, baki sake ta kai hannu ta tura kofar gate din sai ta jita a bude sai dai tai kara lokacin da ta turan din, hakan yasa ta sake arcewa kai kace ma biyota aka yi, babu komai a cikin zuciyarta sai tsoro da fargaba, cikinta kuma dauke da yunwa da kishin ruwa.
Ganin babu sarki sai Allah yasa ta sake komawa duk kuwa da irin abunda zuciyarta take raya mata na cewar kille mata kai za’ayi a wannan gidan dan yai mata kama da na yan yankan kai, a hankali ta saka kanta ta leka harabar gidan, a yadda ta hango compound din sai yasa idanuwanta suka fiffito kamar wata zarrariya baki sake take kallon motocin dake harabar gurin.
Tabbas gidan yan yankan kai ne, haka zuciyarta ke raya mata, sai dai hakan be sa ta zata iya komawa ba tare da ta nemi abunda zata jefa a cikinta ba duk da bata dan inda zata samoshi ba. Kamar ance ta juyo tana juyowa ta hango kofar Kitchen bude sai dai ita din bata iya banbance kitchen ne ko kuma wani abun na daban.
Hango mutum na kallonta ta window yasa ta juyo har tana kokarin faduwa ta fita da gudu tana haki.
“Na bani na lalace wacan aljanin nasu ya hango ne”
Ta fashe da kuka sosai tana gudu iya karfinta duk da babu wani kuzari a tare da ita. Bayan wacan kwarkwadar ta sake komawa ta buya tana kuka babu hawaye, kwarkwada ce dake tsakanin gida da gida baka jin sautin komai sai iskar da ke kadawa, hakan ya bata damar tausayawa kanta da kanta tai kuka iya wanda take jin zai isheta amman ko kadan hawaye be zubo daga idonta ba. Lokaci lokaci tana shafa fuskarta wai ko zata ji saukar hawayen tun da bata ji sanyinshi ba, amman sai taji babu komai.
“Hawayena ma har ya kare… ”
Ta fada tana kara fashewa da kukan still babu hawaye.
YARIMA ZAIN POV.
Tana tsaye jikin fanfo yana wanke hannunsa ya jiyo karar taba gate, hakan yasa shi dagowa ya kalli gurin gate, kasancewar windows kitchen din da kuma dayar kofar duka suna fuskantar gate ne. Yasan Malam Adamu mai gadi be isa dawowa daga aiken da Anty Ummi tai masa ba, to waya turo gate din? Hakan yasa shi maida hankali sosai gurin gate din zuciyarsa cike da son sanin dalilin motsin kofar gate din. Bayan kamar mintuna uku sai aka sake turo gate din, karamin kai ya fara hangowa an ziro ana karewa gidan kallo, kai tsaye ya koma gurin windows yana son tantance abunda yake hangowa tana kallo inda yake sai ta juya ta zira da gudu, shi dai ba zai iya tantance abunda ya hango ba duk kuwa da kasancewar akwai wadataccen haske a ko ina na gidan, mutum ko aljan? Iyakar abunda zai iya tabbatarwa mace ya hango ba namiji ba saboda yawan gashin kanta, kuma karamar yarinyace sai dai idan mutum miyasa be hangota da tufafi complete a jikinta ba, ko dai mahaukaciyace ko kuma aljana haka zuciyarsa take raya masa sai sai tafi raja’a ga cewar aljanar ce ba mahaukaciya ba.
Ji yai bashi da natuwar jiki da ta ruhi har sai ya tabbatar da abunda yake zargi ko ba komai ya kamata ya duba yaga ko minene saboda tsaro ba dan tsoro ba. Ta kofar kitchen din ya fita kai tsaye ya nufi gate din, yana isa ya kai hannu ya bude ya fita waje gaba daya ba tare da fargabar komai ba, cike da natsuwa yake kallon damansa kamin ya juyo zuwa hago, sai dai ko kadan be hango abunda zai sada idanuwansa ga kallon abunda ya gani dazu ba balle kuma har ya sake ganinsa, kamar zai juyo ya koma sai kuma yai gaba kadan ta inda kunnuwansa suke jiyo masa sautin kuka duk da bashi da tabbacin kukan ne. Ba’a iya jin sauwon takunsa balle kuma har mutum ya iya auna tafiyarsa, Yarima Zain irin mutanen nan ne da ba saka ta zuba zance baka saka suna kusa da kai ba har sai kamshin turarensa ya sanar maka da zuwansa, hannayensa duka biyu suna baya har ya karasa inda yake jiyo kukan.
Wannan karon kallon Aljana yai mata dan ta bashi baya ne fuskarta tana kallon karshen kwararo, hakan ya bashi damar kallon bayan kanta da kuma sauraren kukanta, yasan babu abunda zai kawo mutum cikin daren nan kuma a irin wannan gurin ko da kuwa mahaukaciya ce, babu komai a cikin sautin kuka sai.
“Yunwa wayyo yunwa zata kashe ni”
Juyowa yai ya dawo zuciyarsa na raya masa abunda ya kasa natsuwa da shi, miyasa shi kadai ya ganta? Akan mi ya bibiyeta har ya ji tana jin yunwa? Idan be taimaketa da abinci ba mai zai faru da shi? Idan ma da gaske aljana ce mi zata masa?
Har ya dawo cikin kitchen din wadannan tambahoyin ne a ransa, Anty Ummi ya tarar cikin kitchen din tana hada ma yaranta ginger tea. Kallo daya tai masa ta dauke idonta daman tasan yau kanenta baya cikin walwala saboda ta tabo masa inda baya son a tabo masa, bata bukatar tambayar damuwarsa domin hakan ya wuni a gidanta da abarsa. Tsaye yai yana kallon kofar gate din har ta gama hada tea ta mika masa nasa.
“Kamar kana jiran wani”
Ta fada tana kallon gate din ganin yadda ya tattara duka hankalinsa ya maida can. Hannu ya mika ya karbi kofin tea din.
“Maybe…”
Ya fada yana daga kafadunsa tare da tabe baki, sai ya kawar da idonsa daga kallon gate din. Aje kofin yai dan baya jin zai iya shan ginger a yanzu, yana son ya ce Amal ta kawo masa keys din motarsa dake falo kuma yana jin hauyin bude baki yai maganar hakan yasa ya nufi falon da kansa ya dauki keys dinsa ya fita ta kofar falon. Da sauri Anty Ummi ta fita ta kofar kitchen ta zagaya ta nufi inda yake kokarin bude motarsa tun kamin ta karasa ta fara masa fada saboda ranta a bace yake.
“Au kayi fushi kenan ko? Saboda an fada maka gaskiya, kai ba dama a zaunar da kai ayi magana Allah da Annabi? Kanka farau mutuwa da zaka dauki abu ka saka a ranka? Ai ban san son da kake mata ya kai haka ba har sai ka hadiye zuciya ka mutu sai a binneka kusa da ita sannan hankalina zai kwanta”
Tun da ta soma maganar be dago ya kalleta ba har ta gama ta juya ta koma, zaunawa yai cikin motar ya lumshe idonsa yana sauke numfashi a hankali. Ko kadan maganar Anty Ummi bata masa dadi ba, sai dai yasan ranta ne ya bace, kuma bata nufin komai a gareshi sai gyara domin ba zata so wani abun cutarwa ya same shi, ta fi kowa shiga damuwa da halin da yake ciki, shi kuma baya hango abunda take hangowa a matsayen mata a gareshi.
Bayan kamar mintuna biyar zuwa shi da ya tashi motarsa, kamin ya karaso bakin gate din sai ga Malam Adamu ya dawo tare da Farhat Malam Adamu komawa yai gefe ya aje ledodin dake hannunsa ya bude masa gate Farhat kam yin tai yi kamar ba san da mutum a compound din ba ta wani dauke kai ta nufi cikin gidan. Da mugun gudu Zain ya bi ta kusa da ita kamar zai kadeta har sai da ta matsa gafe. Kwafa tai ta nufi kofar falon a fusace.
Anty Ummi na zaune falo Farhat ta shigo kamar an jefota.
“Wallahi Anty Ummi wannan kannen naki bashi da kirki kin ga yadda ya bi kaina da mota kamar zai takani, shiyasa bana son zuwa gidan nan idan yana nan”
Murmushi Anty Ummi tai ta aje kofin ginger dake hannunta ta kama hannun Farhat ta zaunar da ita.
“Kin riga kin san halin Zain amman kullum sai ki tai min complain akan matsalar, yanzu haka it wasn’t intentionally amman kin wani fusata, kina da zagar min dan’uwa a gaban idona, kuma wasu abubuwan rayuwarsa ce amman idan baka saba ba sai ka dauka wulakanci yake maka”
“Wallahi da gangan yai, shikenan dan yana dan sarauta sai ya dinga yi ma mutane wulakanci son sansa, haka ranar fa ina zuwan gidan nan ya dinga hararata”
“No no no Zain amman baya harara haka dai kallonsa yake, maybe ya tsareki da idone ke kuma kika tsargu, amman ni nasan waye kanane”
Anty Ummi ta fada tana dariya.
“Ni dai gashi inji Anty Rukaiya tace wai idan na kawo miki ki kirata kayan mata ne…”
Farhat ta fada tana dankama Anty Ummi bakar ledar dake hannunta.
“Ba sai kin fada min ba, na sani marar kunya, tashi kije kar dare ya miki”
Karanta Littafin Hajiya Gwale Hausa Novel
Anty Ummi ta fada fuskarta babu alamun wasa, Sai ta ta dauki ragowar ginger da Anty Ummi take sha ta shanye sannan ta tashi ta fita tana mata sai da safe.
Babu wani nisa sosai tsakanin gidansu da gidan Anty Ummi amman hakan be hanata gudu ba duk da kasancewar akwai haske a ko’ina. Ko da ta shiga gidansu har haki take saboda gudun data debo, da sanda ta shiga falon sanin cewar Ya Bashir na nan yana jiranta dawowar daman kamin ta fita ya fada mata zai yi magana da ita. Duk da hankalinsa yana gaban Plasma hakan be hanashi fahimtar shigowarwata ba.
“Farhat bana nace ina son magana da ke ba?”
Cak ta tsaya duk wani kuzari nata sai ya yanke, tsoro da fargaba tare da tunanin abunda zata fada masa suka cika mata zuciya lokaci daya. Zagayowa tai gabansa ta zauna tana mai nuna tsantsar ladabi da biyaya a gareshi ta risinar da kanta kasa tana jiran abunda zai fito daga bakinsa.
“Ya kuka da Auwal?”
“Ya na fada mishi sai ya ce dan Allah ka yi masa uzuri har ya dawo dan sunje Abuja gurin wani meeting da sun dawo zai zo ya sameka”
Kai kawai ya daga mata, ta tashi jiki a sanyaye ta nufi dakinta, da shigar ta maida kofar dakin ta rufe ta fada saman katifarta tana sauke ajiyar zuciya, tana mai jin nauyin irin karyar da tai ma Ya Bashir sai dai idan ba karyar ta masa ba ya zata ce masa? Auwal din ne yaki ya fito a duk lokacin da tai masa maganar aure sai ya kawo mata wani uzurin, iya daga kafa tasan Yayanta yai mata kuma ya bata dukan danar data kamata amman ta kasa gane kan Auwal yadda yake ta mata yawo da hankali a duk lokacin da tai masa maganar aure har ta rasa gane kansa, a iya abunda ta sani zuciyarta tana son Auwal sosai kuma bata jin zata iya rayuwa da wani namijin bayan shi, wannan ne dalilin daya hana ta kula kowa a duk tsawon shekaru hudu da suka kwashe a tare, Auwal gwani ne kuma gwarzon da zai iya cinye ko wane irin kambu na masoya a fashen soyayyar irin tarairayar da kulawar da yake nuna mata a waje take fatan samun a gidansa, irin soyayyar da ake a cikin finafinai da littafai take son su yi ita da shi a gidan aurensu, saboda tana gani da tunanin babu namijin da zai iya bata wannan kulawar da soyayya kamar Auwal dinta.
Farhat mace ce da idan tana son abu takan so shi duka, zata iya mutu da sake mutuwa ta kuma sake mutuwa akan Auwal, a shekara hudu nan da suka yi a tare babu wani a cikin familynta da be san da zancen Auwal ba, kama daga kawayenta har makota da yan’uwanta, tun tana makaranta gashi har ta gama tai service be taba maganar aikawa a gidansu ba, duk kuwa da sakancewar yana mata komai daya kamata saurayi yai ma budurwarsa babu abunda ya rage ta da shi, abu daya ne zai tabbatar wa da Farhat cewar Auwal yana da niyar aurenta saboda gabatarda ita da yai a gaban iyayensa shekaru biyu da suka wuce.
Turo kofar da Anty Rukaiya tai ne ya katse mata tunanin da take.
“Kin ce ta kirani?”
A firgice ta kalli matar yayyan nata.
“Ee tace zata kira ki”
“Better”
Tana fadar hakan ta juya ta bar jikin kofar. Farhat kuma ta busar da iskar bakinta tana lumshe ido.
GIMBIYA HAMEEDA POV.
Tsaye take jikin window dakinta,
sanye take da dogowar riga mai ruwan zuma jikin rigar kamar na almiski anyi mata ado da stones masu haske da daukar Hankali, kanta babu dankwali, iskar hadarin dake kadawa yana watsar mata da gashinkai har ya baibaye mata fuska, bata damu da gyarawa ba da alama ma hankalinta kwatakwata baya gurin.
Baka iya banbance abunda take kallo a tsakanin hadarin da soma haduwa tare da iska da kuma sauran taurarin da suke sararin samaniya.
Jin motsin an taba kofar dakinta ne yasa ta sauke kanta kasa tare da kai hannunta ta share hawayen da suka zubo mata, juyowa tai a hankali ta kalli Abida irin kallon nan na neman dalilin shigowarta dakin.
“Allah ya taimakeki naga garin akwai hadari ne shiyasa na shigo na rufe miki kofafin taga”
Cewar Baiwar tana risinawa cike da tsantsan da kai. Ba ce mata komai ba ta taka a hankali ta isa bakin gadonta ta zauna, yatsun hannunta ta soma murzawa sai kuma ta fashe da kuka. Da sauri Abida ta karasa rufe windows da take ta karaso inda take ta risina har kasa tana kallon fuskarta cike da tashin hankali.
“Allah ya taimaki uwargijiyata, mai zai kawo zubar hawaye a fuskarki a yanzu?”
Bata ce mata uffan ba har sai da ta gama kukanta sannan ta share hawayenta ta nufi gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta.
“Miyasa bani da sa ar rayuwa Abida? Miyasa komai na alheri yake tsallakeni ni na mana duniya take juya min baya? Miyasa nake ta rasa abubuwan da suke da muhimmanci a rayuwata?”
“Duniya tai kadan ta juya miki baya Gimbiya Hameeda, komai a yanzu a hannunki yake”
Abida ta amsa mata daga can inda take risine tana fuskarta Uwargijiyarta.
“A cikin gidan nan da duniyar nan Hajiya Yalwa ta tsani kuka da kuma damuwarki data Yarima, zata jure komai amman ban da damuwarki data Yarima….”
Hannu Gimbiya Hameeda ta daga mata daga can gaban madubin da take tsaye tai mata alama da ta fita. Cikin rawar jiki Abida ta tashi ta fice tare da jan kofar dakin.
Zaunawa Gimbiya Hameeda tai tana cigaba da kallon kanta a gaban madubi, tasan babu abunda ta rasa na daga kyaun halitta da sura irin na ya mace, amman miyasa har yanzu Zain ya kasa yi mata irin kallon da take masa na son kasancewa da shi a matsayin miji kuma jagoranta?
‘Kina da gaskiya Abida na fi kowa gata a gidan nan, lokaci yai da ya kamata na daina kuka hakanan ni ma ai na cancanci farinciki kamar kowa, sakacinane yasa Zain ya tsallake ne ya auro yar’uwata, a yanzu kuma da bata raye ni ya kamata ace na maye gurbinta’
Shine abunda take sakawa a zuciyarta a fili kuma sai ta furta.
“Mutuwarki tai min rana Haleema…”
Ta furta tana wani shegen murmushin da ita kadai ta san manufarsa.