Hausa Novels Littafan Hausa Novels

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Karin hips
Written by Hausa_Novels

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Na Feedohm

1 to 2

البسم الله الرحمن الر حپم

Lumshe Ido yayi sannan ya budesu tar bisa kan wata karamar yarinya dake zanen yar galala ….

Fito yayi da bakinsa a hankali ….da sauri yarinyar ta kallo sama tana murmushi tare tsalle tana daga mashi hannu …

Iska ya huro mata …sannan ya daga mata hannu ….itama hannun ta daga mashi ….

Wata tsohuwa ta fito daga wani karamin gida wanda duk unguwar babu talaka sama dasu ….

Meenalle …Meenalle. ..ta fara kwada kira ….

Yar karamar yarinyar ta juyo da sauri tana bata fuska …cikin shagwaba tace …..Kai kaka ke kullun sae ki batawa mutun suna …nasha fada maki Meenal fa ake cewa? …

tsohuwar tace …to naji sarkin hakuri zo muje ki sayo mana kwaki ko bakijin yunwa?

Saman benen ta kalla. ..har yanzu yana tsaye ita yake kallo …daga mashi hannu tayi tare da langwashe kai …sannan taja hannu tsohuwar suka koma gida ….

Kudin ta karbo sannan ta sako hijab ta fito …tana zuwa bakin kofa taja birki tare da dafe kirji ….hal ka ban tsoro …ta fada hakoranta waje …

Hararanta yayi…ke kuma sarkin tsoro ko …ya fada yana gyara mata hijab dinta …

Kai …aikena fa akayi …ta fada tana neman cire agogon dake makale a hannunsa …

Hannunsa ya janye don karta bata mashi…sannan yace …Me zaki sawo?

Baki ta tabe tana kokarin wucewa sannan tace …kaini Kaka tace kabar sawo man komae ..wae ku yan yankar kaine …kuma tace wae kaina zayayi tsada …

Dariya ya sake a hankali kafin yace mata. ..ni kuma kakata tace man indae mace na yawo to kasa ake rufeta …ya fada idonsa na kallonta …

Ido ta waro cike da tsoro …da gaske Mai kamshi?

Ganin ta tsorota ya saka yace ..eh mana ai bana so a rufeki shiyasa ma nace ki fada man in sawo maki …

Kamar jira take ya rufe baki tayi saurin mika mashi naira hamsin din da ta gama nannadewa …

Amsa yayi ..yace me zaa sawo. ..

Kwaki na talatin sae sukari na ashirin …ta fada a hankali ..

kai ya girgiza kana ya tafi. ..har yayi nisa ta kwala mashi kira…ya juyo. .tace …Dan Allah kace a maka arha ..kuma kayi sauri kar kaka tace na dade …

Kai ya daga mata sannan ya tafi ..

Baifi minti goma ba ya dawo rike da manyan ledoji. ..tana hangoshi ta tareshi tana dariya …

Duka ledojin ya mika mata ya juya …tayi saurin janyo hannunsa ..to ka tsaya mana na duba inda canji ba sae ka bani ba …ta fada tana bata rai ..

Dariya ta bashi sossae ..ya dawo suka shiga zauren gidan …

Zama tayi kasa ta zazzage kayan tsaf …ido ta waro lokacin da ta daga katon gwangwanin madara ..tace …Nawa ka sayo wannan …ta fada tana kallonsa ..

Naira biyar …ya ce idonsa yana kallon karamin bakinta …

Uhmm saura arba’in da biyar kenan ta fada …biscuit ta cigaba da fitowa da chocolate sae ledar cos cos da sugar sae lemuka kala kala …duk wanda ta daga sae ta tambayeshu kudinsa …daga wanda zayace biyu biyar sae na biyar ….har ta fito da tiyar garin kwaki …

Wannan nawa yake? …

Kura mata ido yayi ..sannan yace …wannan a shagon wani abokina ya bani su …

Dariya tayi kana ta maida kayan tana kallonsa …to bani canjina …ta fada lokacin da ta gama maida kayan …

Ido ya waro …wane irin canji kuma?

Harara ta balla mashi …sha biyar mana. .ba yanzu mukayi lissafi ba naira Talatin da biyar ka kashe …

Murmushi yayi ..ya lalubi ajihunsa …babu ko naira 500 bare kananan canji. ..

dubu daya ya mika mata …ta make kafada …ni canjina zaka bani ….ta fada a shagwabe

Dukawa yayi dae dae tsawonta ….kiyi hakuri Meenatou …banda canji…kinji. ki bari anjima zanyi canji sae na baki ….

aa Ni dae ban yarda ba ….muje a canzo su …ta fada. .

To naji shiga da kayan sae ki fito muje. …ya fada idonshi a lumshe …

Ka gudar man da canji …tace

Hannunta ya kamo …baran gudu ba ….ya fada har lokacib idonshi a rufe …

Shiga gidan tayi tana waigenshi …aje kayan tayi ta fito da gudu …kaka nata kiranta. ..amma ce mata tayi ….Kaka Kawata ta mutu ake kiranmu muyi mata addua ….

​Feedohm

.
💧💧 SIRRIN ZUCI……

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Na Feedohm

3 to 4

Suna fitowa daga zauren Gidan …dae dae lokacin mota ke horn kofar gidansu ….da sauri ya kalli motar sannan ya kalli kofar get din …babu alamun mai gadi zaya bude ….hannunsa ya zame ya nufi kofar zaya bude …

Ka tsaya wallahi duk wayonka bara ka gudar man da canji ba …ta fada lokacin da ta bishi da gudu …

Murmushi yayi a ranshi yace …Meenatou kenan ….

Gate din ya bude sannan ya matsa jiki. motar …na ciki ya rage glass din dauke da faraa …yace

Ma’aruf …ina mai gadin ne …

Lumshe ido yayi wanda ya zame mashi dabi’a sannan yace …wallahi ban san inda ya tafi ba …amma ko ma meye na tabbata baya kusa. …ya saka hannun ya bude motar ….

Dae dae lokacin Meena ta iso gurin tana sheshsheka ….

Hararanshi tayi …sannan tace ..wallahi yau ko’ina zaka shiga sae ka bani canjina dan ba asi ta yayeni ba …na gaji mutun sae wayau ..dama ranar nan na biyoka canjin Biyar baka bani ba to yau sae ka hada man da ita …don na gaji da wahala. ..ta karasa maganar kamar zatayi kuka

Mutumin yafito cikon motar dauke da murmushi …ya dafa kanta yace …Mamata canjin nawa zaa baki ?

Dariya tayi kana tace …Abba canjin sha biyar ne biyar din wancen satin dana biyoshi amma ya gudu wae bayya da canji …..Au na manta Abba Ina wuni…

Dariya yayi yace …dama mamana ina zaki tuna idonki ya rufe da kudi …Ma’aruf bawa mamana canjinta….

Murmushi ..yayi yace ..Wallahi Abba banda canji kuma kasan halin Meenatou …

Shima dariyar yayi yace …Mamana bata da wani hali mara kyau …mu shiga gida sae yasamo Maki Canjinki ko mama..nima na gaji da cinye maki kudi kullun ….

Dariya ta sake tana kallon Ma’aruf din …hannunta Abba ya kama suka shige ciki…

Da Sauri ta karbe kayan da wata kyakykyawar mata ta fito dashi daga kitchen …sake mata tayi tana murmushi …

Yau Mamanmu ce a gidan mu …Ta fada tana dauke da murmushi. ..

Meena tayi dariya sannan tace …Eh man ae mai kamshine ya cinye man kudi naira ashirin har da ta rannan …

Dafe kanshi ma’aruf yayi …sannan yayi sama da sauri yana fadar ..Wayyo Meenatou kamar na cinye maki Million bara dole na samo maki canjin ki yanzu. .

Matar tayi dariya tace …Sae kuwa ka biya mamanmu canjinta yau ….zo kici abinci kafin. ya samo maki ….

Girgiza kai tayi tana murmushi…na koshi..

Abba ne yace. .. ai kuwa na kusa batawa da ke mamana

Da Sauri ta matsa kusa dashi …Abba me nayi …

Matar ta tareta tace …da bakicin abinci kullun a gidansu Mai kamshi ..

Ido ta waro …In ci abinci ku sayar dani ?

waye zaya sayar dake …inji Abba ..

Ni dae ba ruwana …ta fada sannan ta fara kwalawa Ma’aruf kira …Matar ta nuna mata inda yake …

Ta kuwa shige dakin da sauri …lokacin da kyar ya samo naira sha biyar …ya mika mata …sae da kyar ya samu ta karba shima da kashedin da ta gansho sae ya biyata ko kuma ta cire mashi agogo …

To kawae yace mata don so yake ta barshi da wannan masifar canji ….sae da ya hada mata da sweet sannan ta tafi tana mita..

Bayan ta fita ya dafe kai. ..sannan ya kwanta saman gado…shi kanshi yasan yau duk inda ta ganshi sae ta nunashi tana binshi canji …iska ya huro …sannan yace …yau ba abunda zaya saka na fita indae ban samo naira biyar ba ….idonshi na lumshe fuskar dauke da murmushi …bacci ya daukeshi ..

••°°

Kunnenta Kaka ta rike …wane shegene ya kiraku kuyiwa gawa addua …

Ido ta waro …wallahi Allah kaka wa …

Bakinta ta buge….rufe man baki ke yanzu ko dabbobin gidannan ai sun bar kama rantsuwarki ..

Baki ta turo waje …tana kefta idanuwa …

Ma’aruf kika bawa kudin ya sawo maki ko? ….ta tambayeta tana kallonta

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
*Feedohm*💞.
💧💧SIRRIN ZUCI……

💞

Na Feedohm💞

4 to 6

Ido ta waro waje …Hauka nake da zan bashi…ae in fada maki kaka wani shago naje mai saukin tsiya komae naso naira biyar suke sayowa ..su fa ko daga kasar Dandiyana suke siyo kayansu …ta karashe maganar hakora bude ..

Gwagwanin madara ta dago tace ..naira nawa kika sayo wannan ? …

Shiru tayi tana tunanin nawa ma Ma’aruf yace mata …da sauri tace Naira biyar …ta fada tare da nunota da hannu …

Kwafa tayi sannan ta fito da wata naira biyar din ta miko mata …kije ki sayo man irinta karba. ..

Babu tantama ta karba ta fice da gudu …daga zaure ta tsaya tana hangen saman benen gidansu Maaruf …ganin baya nan ya saka ta sake murmushin jin dadi tare da fadar …Allah ya soni da yanzuma sae yaci zalina. ..ta nufi babban shagon dake unguwar …

Cikin saa tana zuwa taga gwangwan madarar jere …ta washe baki sannan tace a miko mata …aka saka mata a leda …ta fito da naira biyar ta mika mashi ..

Mai shagon ya karba yace mai zaa baki da wannan …

Rufe ido tayi sannan tace a hankali ..Mai kamshi Ma ya iya cuwa cuwa ashema har da canjina yace naira biyar to bara na koma ya jama kanshi sae ya fito man da kudina …?

Sanna ta nuna wani karamin sweet aka miko mata …ta juya …mai shagon yace ke kawo kudin madarar mana ..

Wani kallo ta mashi sannan tace ..wanda na baka fa ..

Yaushe kika bayar …ya tambayeta …

Malan Dallah biyar din da nabaka fa ka miko man canjin alawa ko bashi kake bina ..

Tsaki yaja ya fizge ledar sannan ya nuna mata hanyar fita ..fice ki bawa mutane guri ..sakaran banza ..Ubanwa ke sayar da katon Gwangwanin peak naira biyar ..fice dallah …

Kuka ta sake gurin …wallahi ba inda zanje sai kun biyani kudina ai bani nace ka tambayeni me zaa bani da biyar din ba …gashi ka saka na kashewa kaka kudi kuma ka hanani abunda na saya .kuma dazu anan aka sayeta naira biyar din …ni sae ka bani kudina kuma wallahi baran sake siyan komae ba anan …

Cikin tsawa yace …zaki fice ko sae naci ubanki anan …kaga marar kunyar yarinya

Tsaye tayi gurin taki wucewa sae da ya dauko bulala ya biyota a guje sannan ta wuce tana kuka …..

Tana shiga dakin ta fada saman cinyar kaka tare da sake kukan da babu digon hawaye ko kadan a idonta ….

Cikin kula tsohuwar tace….Me kuma ya faru Meenalle. ..

Kafa ta fara haurawa tana fadin …ba kudin da kika aikeni bane naje shagon da zan saya babu sae na fito wata akuya ta fizgesu daga hannuna …

Murmushi tsohuwar tayi ..duk da tasan karya take….kuma ta tabbata bara ta kashe kudin ba ..sae dae ko faduwa sukayi …

Ta shafi kanta …to yi shiru mana Aminatuta …dan akuya ta fizge biyar ba sae kiyi hakuri tunda kin san dae baran maki fada ba …banda abunki nima na wuce irin akuyar data fizge naki ta fizge hannuna …yi shiru Meenalle share hawayen mana …

Kin shirun tayi sae ma sabon salon turje turje da ta sake ta hambare duk inda taso ido rufe kuma ko hawaye babu ….

Saukar tsintsiyar kwakwar da taji a kafarta ya saka ta bude idonta da sauri tare da kallon kafarta. ..ganin ledar garin kwakin Da Ma’aruf ya sayo mata ta fashe gashi duk ya zube a kasa ya saka ta gane bannar da tayi ….

Lokaci guda ta tuno da zafin tsintsiyar kwakwar kaka ta zuba da gudu ta fice daga gidan …

Tana jin Kaka na kiranta amma bata tsaya ba ta fice daga gidan …

°°••

Tulin kayan wankine jibge gaban Yar mashiyar budurwar da bata wuce shekara 17 ba ….ta saka hannu tana daga kayan a yatsine tana kauda fuska gefe …
.
Wata mata ta fito daga wani karamin daki …tace Haba luba kiyi sauri ki wanke mashi mana su zaya saka …

Yatsina fuska tayi tace …ni gaskia innarmu baran iya wankewa baba wannan kayan ba …kaya sae wari suke …ga kudi a kai mashi wanki ….ta mike tsam ta shige daki …

Ficiciyar Sallamar Meena ne ya katse mata hanzari …

Matar ta kalleta da faraa ….Su Aminatu ne a gidanmu …

washe baki tayi tana fadin ….Eh Man inna ..fada mukayi da Kaka na taho nan …Mamata tana ciki? .ta tambayeta.

Tana ciki Aminatu…..

Da gudu ta fada dakin tana kwalawa Mamanta kira ….ta zaune saman darduma tana addua ….ta juyo tana kallonta har ta karaso …bata tsaya gurin mamar ba ta wuce gurin wani dan karamin tebur ta dauki ayaba ta saka baki tare da lumshe ido ….da sauri ta budesu tace ..mama karki ga na rufe ido ba fa ki dauka wani abu ..ni ba Mai kamshin unguwar mu ba.. nake kwaikwayo kawae nayine naga ko zai man kyau …kinsan dazu sae da yaci man zalin biyar muka rabu …shi wannan shegen taurin bashine dashi kamar babansu Luba .. ….

*Feedohm💞*.
💧💧 SIRRIN ZUCI….

💞

Na Feedohm💞

7 to 8

Sallamar babansu luba ce ta katse mata sauran maganarta …..da sauri ta koma bayan mamarta….

Ya shigo fuska daure …Idonshi na kan Meena …ya Nuna Nuna mamar da Hannu cikin daga murya yace …Banda iskanci Rabi kina ji ina kwala maki kira kikayi shiru …

Dukar da kai tayi …tace wallahi Malan banji ba kayi hakuri …

Yace …baki ji gidan ubanwa ba …sau nawa ina kiranki dan rashin mutunci har muryata ta dashe ..

Meena tace. . .to tunda bata ji ba kuma ba shikenan ba . kai babansu Lubar nan ka cika masifa …ko dan baka da ko sisine ? ….

Mamar tayi saurin zaunar da ita tare da buge mata baki ….

Girgiza kai yayi yana fadin …owo Rabi har kin haifi diyar da zata fadawa mijinki magana ..to nima ina da yaron da zai mata dan banzan duka ….ya fice daga dakin
….Dafe kai tayi idonta cike da hawaye tace …Nashiga Uku Aminatu waya ce ki zo gidannan …ba na hanaki zuwa ba …kinga yi maza ki fice ki koma gidan Kaka yanzun nan ….

Ai kuwa da gudu ta fice dae dae zaune Musa( _babban dan Malan_)Ya shigo rike da wata doguwar bulala ..tayi saurin boyewa bayan kaure. ..yana shigewa gidan ta fice da gudu ta koma gidan Kaka …..

••°°°••

Wallahi Malan Kaka ce ta aikeni shi yasa na makara …tafada tana daga hannu …

Babu Abunda Ya dameni da wadda ta aikeki ita bata san lokacin Islamiyya ba …?

Tace .. Lah Malan ai lokacinsu babu islamiyya ta tsofa ba ..

Yace Aminatu Abubakar ki matso ba bugeki ki shiga aji …don yau ba wani da uzurinki da zan karba ….

Matsowa tayi …yana daga bulalar ta matsa da sauri..hannu ya saka ya fizgota tare da zuba mata bulala a baya. ….wani tsalle tayi ta shiga cikin babbar rigarshi ta aza mashi cizo a kirji …..

kokarin fiddota yake amma taki sakinshi …da kyar ya samu ta fito lokacin ta sake mashi cizo yafi 5 .. shi kadae yasan azabar da yake ji …idanuwansa sunyi jawur. ..yana ganin ta fito ya shige toilet din makarantar da sauri ya cire rigar …duk inda ta cijeshi ta fasa shi …wani karamin kwalla ya goge tare da yi mata Allah ya isa …duk islamiyyar babu mai son dukan Meena saboda irin wannan abun shima yau tsautsayi yasa Headmaster yace yayi taren yan makara …

Sae da ya gama kananan kwallan shi sannan ya fito daga toilet …Headmaster ya ganshi yace …Ustaz Har ka gama dukan yan makaran ..

Harara ya balla mashi ya wuce office abunshi ….daga cikin office din yana hango Meena nata wasanta …Allah kadae yasan iya Allah ya isar da ya ja mata …bai kuma fita ba har aka tashi …

••°°°••

Ganin motar gidansu Ma’aruf ta fito ya saka ta karasa gurin da sauri tana washe baki. ..

Abba ta gani ciki …yana ganinta ya sauke glass din …ta gaidashi …ya amsa mata cikin Faraa .

Abba kaga Mai Kamshi har yau bai biyani bashina ba …ta fada tana bata fuska ..

Dariya yayi yace …to ae mamana Mai kamshi baya lafiya. ..

Ido ta waro …me ya sami Maikamshina ? ta kareshe maganar kamar zatayi kuka. ..

Murmushi yayi ya fito daga motar tare da jan hannunta suka shiga gidan …Mamanshi bata falo suka wuce dakinshi ….yana kwance yana bacci …tana hangoshi ta janye hannunta daga Hannun Abba ta duka kusa da gadon da yake …tana kallon fuskarshi …fita Abbah yayi …
Hannunsa ta damke tana kallon fuskarshi .sajen dake kwance a fuskar ta taba …..Mai kamshi …ta fada a hankali …

Idonsa yana rufe amma ba bacci yake ba ….ta kara kiran sunanshi. ..ganin bai amsa ba ya saka ta sake mashi kara dae dae kunnenshi …

Da sauri ya bude idon yaji karar har cikin kanshi …dariya ta sake …sannan ta shafi wuyanshi …saurin dauke hannunta tayi tana kallonshi shima ita yake kallo ..

Mai kamshi jikinka Zafi ..ta fada kamar zatayi kuka ..

Daga mata kai yayi tare da lumshe ido …itama idon ta lumshe sannan tace. ..Amma mai kamshi wannan ciwon naka har da taurin bashi ke kara mashi yawa …

Dariya ta bashi yayi saurin janyo drawer dake jikin gadon ya fito da sabuwar naira biyar ya daura mata a hannu …

Baki ta washe tace. ..ka gani ko Mai kamshi yanzu ko mutuwa kayi babu bashin kowa akanka …lokacin guda idanunta suka ciko da kwalla tace …kuma ko bana so ka mutu Mai kamshina …ta fada lokacin kwallar ya gangaro kumatunta …

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
*Feedohm*💞
💧💧SIRRIN ZUCI…..

💞

Na Feedohm💞

9 to 10

Zaune ya tashi tare da janyota ya zaunar da ita bisa cinyarshi ya share mata hawayen

Yace …ai mutuwa dole ce Meenatou ..

Girgiza mashi kai tayi ..aa ni bana so ka mutu …

Shafa kanta yayi yace …to kiyi addua meenatou Allah ya bamu tsawon kwana kinji ko …Na furta maki Sirrin Zuci …mai dadin saurare…

Film din dake kunne a dakin ta maida hankali gareshi …..zuwa can ta mike tana washe baki …tace Mai kamshi kaci abinci …

Film din ya kalla shima ciki wata budurwace take bawa saurayinta abinci abaki …murmushi ya sake ya girgiza mata kai alamar aa …

Ta fice …zuwa can sae gata da abinci cikin Plate ya kalleta da mamaki yace …ina kika samo …

Baki ta washe gurin Mamanku naje nace zaka ci abinci ta bani …

Zama tayi saman cinyarshi …tare da debo abincin a spoon ta mika mashi …ahankali yace ..bana cin abinci da spoon sae da hannu Meenatou
Ido ta waro ..Kai mai kamshi dazu dana zo cizon malan na taba hammatarshi kuma wari take ….

Lumshe ido yayi ya bude …wani abu ya tokare mashi makoshi baya kaunar Meenatou ta taba wani namiji duk da tana karama ….

Shiga toilet ki wanke hannun ki fito …ya fada a hankali …

Sae da ta bashi abinci sannan ta fice …ya bita da kallon ….gida ta koma ta sakewa Kaka kusa sae tazo ta gaido mai kamshinta baya da lafiya …

Da farko kaka cewa tayi bara tazo ba amma da taga masifar ba mai karewa bace ta ziro Hijab ta biyota …

Mamar Ma’aruf taji dadi sossae sanna ta kara son Meena a ranta …haka shima Ma’aruf murmushi kadae yake yi tare da lumshr ido har suka tafi ….

Kasancewar an koma Boko kullun kafin ta tafi makaranta sae ta shiga ta ganshi …ta bashi abinci .. sannan take wucewa haka idan ta dawo sae ta shiga ta bashi abinci ko da kuwa zata dade bata dawo ba to zaya jirata ….Abincin Rana tare suke ci …tana bashi tana ci …amma da anzo gurin nama nanne zancen zai canza salo …don sae taci Yanka 4 kafin ta bashi guda …idan kuma kazane to sae ta cinye tsokar sannan tace ya gashi ya cinye …sae dae kawae yayi murmushi. yace ya koshi. ..haka zata sake mashi kuka sae yaci …hakanan zaya danci abinda zai iya ya bar sauran kashin …Har Allah ya bashi lafiya ….

••°°

Kaka nidae wallahi wannan wanke wanke wanken yayi man yawa …ta fada cike da shagwaba …

harara ta dalla mata …sae ki nemi wanda zaya tayaki …

Sallamar Ma’aruf ce ..yasa ta sake Murmushi tana cewa …Yauwa Maikamshi zoka tayani mu gama na fada maka wata magana
Kaka tace ..bara ya tayaki ba dan kaniyarki ….Ma’aruf ko za zauna ka kyaleta …ta shimfida mashi tabarma ..

Murmushi yayi yace …barta na tayata Kaka naga kayan sun mata yawa ita kadae. ..

baki ta washe …Yauwa mai kamshina ..kayi wanke wanke sae in maka dauraya nafi iya dauraya kai kuma kafi iya wanke wanke …

Yana wankewa tana daurayewa har suka gama ..kaka na kallonsu cike da fata kala kala aranta ….

Bisa tabarmar ya koma ya zauna …zonan Meenatou …ya fada a hankali. ..

Kusa dashi ta koma ta zauna ta harde kafa tana kallonshi ….

Wani karamin zobe na gold ya fito daga cikin jikkanshi …ya zura mata a hannu …

Kallon zoben take ..tana kallonshi ..ni ka sawo mawa ?

Daga mata kai yayi …ta kare washe baki tace …. don kar na fadawa kaka kace idan aikeni na dinga karbowa kyauta a shago …

Ido ya lumshe sannan yace aa …kinsan Zuciya ?

Lallae ma Mai Kamshi tun muna primary one muka ganin zuciya ….

Yace Good …to ki aje wannan itace zuciyata …

Dariya take har da kwalla …kai kuma wannan itace zuciyarka …to nima bara na baka taea zuciyar …ta kwance dankwalinta ta zare ribbon din dake kanta ta mika mashi …

Amsa yayi yana daga shi …sannan yace na meye wannan …

Hararanshi tayi sannan ta saka hannu zata fizge ….to bani abuna tunda baka so …

Aa sorry Meenatou ina so mana …wannan shine zuciyarki ?

Eh man mamana ta bani shi da sallah …ina sonshi …

cikin jikkarshi ya saka sannan ya mike ya ma kaka bankwana ya wuce ..

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI…..

💞

Na Feedohm💞

Senator Son Hausa Novels Complete
11 to 12

Wani karamin yarone ya shigo office din headmaster yana kuka rike da ya gaggen littafi …

Ustaz ya kalleshi Yace..me ya faru kake wa mutane kuka…

Yaron yace .Meena ce ta yaga man littafi …

Wani wahallalen miyau ya hade tare da shafa kirjinsa …sannan yace …Jeka Allah ya saka maka …ya juya yaci gaba da duba lttafin dake gabanshi …

Wani sabon malamin da bai dade da zuwa ba ya kalli Ustaz yace ..Haba ustaz wane irin Allah ya saka mashi …ya nuna yaron tare da fadin ..jeka kirata. .

Bai fi minti biyu ba ta shigo da uwar sallama. …Sabon malamin ya ce ta rage tsawonta …

Zama tayi tsakar office din ta mike kafa ….tsawa ya daka mata. ..babu shiri ta yi kneeldown din …Kallon Ustaz tayi tace …Ustaz Dan Allah kayi hakuri shi ya fara daukar man goriba ya cinye ..

Da sauri Ustaz ya juyo yace. .Meena Abubakar bani na kiraki ….ya kakkabe riga ya fice daga office din …
Sabon malamin ya bata punishment din wanki toilet din makarantar duka tare da share ko wane glass. …tana kuka ta gama ko aji bata koma ba ta wuce gida …

Sae da ta bari lokacin tashin malamae yayi saboda suna tsayawa meeting kullun …lokacin mangrib tayi kowa na sauri yaje masallaci sannan ta nufi hanyar islamiyya. ….tun kafin ta isa ta cika jikkarta da duwatsu …

Wani lungu mai duhu ta samu ta shige wanda ta san dole tanan sabon malamin zaya wuce …Cikin saa sae gashi ya taho kanshi na kasa yana tafiya ….katon dutse ta samu ta saita keyarshi ta jefa mashi ….dafe gurin yayi ya juyo yace …Uban waye ke yo jifa …bai rufe baki ba ya kara jin wata a goshinsa har sae da jini ya zubo ….

Tana ganin ya dafe gurin da sauri ta fito daga maboyarta ta kukan kura tayi ta shige cikin rigarshi …rudashi tayi ta dinga sake mashi cizo tare da yakushi ta ko ina …

Da kyar ya samu ya babbareta …tare da zubawa da gudu …don duk tunaninshi aljanace ….

••°°°

Ustaz ya kalleshi cike da tausayi yace …Malan isiya sae naji headmaster yace ka samu hadari jiya a hanyarka ta komawa …

Sosa kai yayi yace …wallahi kuwa Ustaz ina saman mashin wani mai mota ya bangajemu …

Meena dake tsaye ta kalli ustaz tace. .Malan meye hukuncin mai karya…

Dan wuta …ya bata amsa don yanzu tsoronta yake ji …

to Malan isiya ma dan wutane …jiya gabana akayi …wata aljanace ta rotsa mashi cizo sannan ta shige a rigarshi ta yakusheshe ta ruga …

Wata dariya Ustaz yake har da dafe cikin sannan ya kalli malan isiya da sae yanzu ya gane wannan shegiyar yarinyar ce ta masa rashin mutunci …

Ustaz yace. …Malan da mai motar ya bugeku sae ka fada kan aljanar ?

Shiru yayi …yana nan tsaye kuma duk yaron da yazo wucewa to Meena zata tareshi ta bashi labarin malan yayi karya yace hadari yayi alhalin aljana ce ta shige rigarshi ta yakusheshi …wani ma har yadda aljanar tayi masa take nuna masu da bango …. yana tsaye da uwar palasta a goshi …cikin dubara ya sulale ya fice daga islamiyya….Tun daga lokacin malan isiya bai kuma dawowa ba …

••°°°••

Mai kamshi ina irin wannan alawar daka sawo man jiya …ka tunata …ta fada rike da hannunshi tana murmushi …

Daga mata kai yayi …na tunata ..

Yauwa to ita zaka kara sawo man …ta mika mashi wata rabin naira biyar …

Dan Hararanta yayi …waye zaya amshi wannan rabin kudin ?

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment