Littafan Hausa Novels

Zazzafar Kishi Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Zazzafar Kishi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

ZAZZAFAR KISHI

_labar me ɗauke da makirci _cin aman da soyayya_

 

 

 

 

 

 

*NA*

*ZAINAB HABEEB.*

*MOM ISLAM*

 

 

 

 

*MARUBUCIYR*

 

*ZAINABU ABU*

 

 

*AND NOW*

 

*ZAZZAFAN KISHI!!!*.

 

 

 

*GODIYA ta tabbata ga Allah mad’aukakin sarki daya bani _ikon rubuto muku wanan tak’ai taccen labarin tsira da amincin Allah su k’ara tabbata ga annabi Muhammad ( s. a w).*

 

 

 

*GARGDi* *wanan littafin k’ir k’ira ne bany yishi dan cin zarafin wani ko wata ba in yazo dai dai _da labarinki /labarinka to hasa shene kawai.*

 

 

 

*BISMILLHIR RHMNIR RAHIM*

 

 

*page* 1_2

 

 

📖_____motocin ɗaukar amarya ne sukayi parking a harabar gidan alhaji Yusuf wato mahaifin amarya Afrah.

 

Misalin ƙarfe 8:30pm wata dattijuwar mata da bazata wuce shekara 70 ba ta fito tana faɗin ga amaryar nan fitow…..

 

Kafin tagama rufe baki sega Amarya Afrah lulluɓe cikin mayafi tana ta kukan rabuwa da iyayenta .

 

Riƙo hannun kakarta wato datijuwar nan tayi kakar ce ta dube ta sekuma taji hawaye na zubo mata .

Ma’aikaciyar Gomnati Hausa Novel Complete

Sunata kukan rabuwa babu me bawa wani haƙuri angwayenne suka dubi mutanen da suka tsaya suna jiran amarya ta shiga mota suma su samu su shiga. abokin ango ne yace kaka bawai kun rabu kenan ba ai aure ba mutuwa bace. ita ko kaka tana kukan Afrah zata tafi gidan me mata ne .

 

Riqe da hannun juna suka shige motar daganan suka miƙi hanya se kano.

 

 

Tsakanin zariya da kano babu nisa sosai shi yasa suka isa da wuri .

 

 

Wani gida naga sun dosa gidane me kama da ginin turawa iya tsaruwa gidan ya tsaru ko maƙiyi se haka Horn motocin suka shiga yi .

 

Me gadi ne ya buɗe musu gate ɗin gidan suka shige da shigar su aka fara rangaɗa guɗa.

 

Dangin amarya ne kan gaba se tsirarin dangin ango se kuma ita kanta amaryar .

 

Da sallama suka shiga katafaren gidan da babu abin da babu acikin sa babu ce kawai amma gidan ba,a cewa komai kun gane ai masu karatu.

 

Dakin da yake ƙasa shine nata kujeru ne da mahaifinta yayi mata su kamar ba,a talauci a kasarnan tamu.

 

Direct ɗakin ta aka wuce da ita shima fa ɗakin ya haɗu can tsakiyar gado kawayen ta suka kaita suka daɗa fesheta da turare suka gyarata .

 

Yan uwan Mamin ta ne suka ƙara yimata nasiha me shiga jiki daganan sukayi mata sallam haɗe da ƙawayen duka suka wuce mota .

 

 

Zaune take tana ta tunanin a zuciyar ta kuwa cewa takeyi dama haka akeyi ¿ai na ɗauka zanga kishiyar tawa ta shigo .

 

 

Can misalin karfe 10:30 taji ƙarar buɗe kofar ɗakinta.

Angon ne yashigo shi kaɗai babu abokannashi.

 

Kitchen ya wuce kai tsaye ya ɗauko abinda zasu bukata ya dawo.

 

Buɗe ledar da yashigo da ita yayi kana ya fito da kaza da hollondia babba ya tsiyaya musu lemon ita dai Afrah na cikin mayafin ta .

 

Jitayi an cicciɓo ta kamar baby zaunar da ita ya yi kana yafara bata abaki shima yanaci sun kusa cinyewa ta miƙe tayi brush ta dawo ta zauna tattara kwanukan ya yi, Kitchen yakai ya dawo izinin ta tashi suyi alwala ya bata bayan sun ɗauro alwalr ne yaja musu jam,I suka tada sallah raka,a biyu sukayi kana suka yi sallama ɗaura hannun shi yayi a kanta ya dinga kwararo mata adu,oi .

 

Daganan ya sunku ce ta ya kaita gado lulluɓesu yayi da blanket ,ya fara shafa mata kai kenan sukaji alamun buga ƙofa Afrah ce ta miƙe hankali a tashe ta dubi JABIR nuni yayi mata da takoma ta kwanta.

 

Fita yayi dan yaga wake buga ƙofar yarinyarshi ce da bazata wuce shekara goma ba kuka takeyi sosai.

 

Janyo hanunta ya yi kana yafara tambayarta “meke faruwa¿”.

 

Amsawa tayi da “momyce ta dakeni shi kuma a rauwar shi bayason kukan yara dan haka ya kwantar da ita a kusa dashi aka mance da amarya.

 

 

Washegari Afrha ta yi wanka ta shirya cikin doguwar ,riga irin ta larabawa ba ƙaramin kyau tayi ba tunda asbh tayi angon yai alwala ya fice itama yarinyar ta bishi .

 

 

Washe gari da safe JABIR ya kirawo AFRAH kana ya kirawo MARIYA wato uwar yarannan .

 

Tunda ta shigo take harare harare ko sallama batayi ba kan cinyar JABIR ɗin ta zauna .

 

Magana yafara yimata faɗa faɗa sauka tayi ta fashe da kuka tana cewa “wlh dama nasan tunda kayi aure zaka fara wula kantani.

 

JABIR be kula tabs se fuskar AFRAH da ya kalla yaga bata nuna alamun damuwa ba tunda yafara magana babu me cewa komai har yagama jawabinsa.

 

 

Riƙowa AFRAH hannu yayi suka wuce ɗaki da shigar su yana shirin tura ƙofar sega yarinyar jiya ta dawo ɗauke da abinci a wata kya kayawar kwanukan tangarass miƙawa AFRAH tayi.

 

 

AFRAH ce ta karɓa da fara arata kana tace me sunanki yarinyar ce ta ,ce sunanan BILLY.

 

AFRAH ce tace BAILKISU ko ?eh yarinyar jiya ce jabir kuwa dayaga MARIYA ta kawo wa AFRAH abinci yana ganin kamar har zaman lpy y wanzu a tsakanin AFRAH da MARIYA.

 

Ficewa yayi a ɗakin ya nufi nashi ɗakin abincinta faraci seda ta kusa cinye abincin duka sanan ta ajiye kwanon ta ɗauko ruwa ta kora suka cigaba da hira itada BILLY .

 

 

Bacci ne taji ya kama mata ido miƙewa tayi ta cewa BILLY “kitafi wasa zani in kwanta .

 

 

Tana kwanciya bacci me nauyi ya ɗauketa wani mumunan mafarki tayi .

 

Da gudu ta miƙe ta nufi bathroom ɗinta tayo alwala ta dawo tafara sallah qur,aninta ta ɗauko ta fara karatu.

 

 

Can anjima misalin karfe biyu na rana ta miƙe ta dauki waya takirawo maminta albarka mamin tadinga sa mata sukayi sallama ta ajiye wayar wanna ta kuma yi kana ta shiga kitchen domin ɗaura abinci .

 

Taliya da wake da taji hanta da kifi ta ɗaura bayan wani lokaci ta sauke ta sawa BILLY nata itama tasa nata .

 

MARIYA ce ta aiko a kirawo mata BILLY , BILLY ce da ta kalli yaron da befi shekara takwas ba da taji BILLY ta kirashi da khalifa kace INA zuwa.

 

Shikuwa kalifa yana zuwa gurin momyn shi yace ga BILLY can tana kwaɗyi a ɗakin amarya.

 

Tunda MARIYA taji haka aikuwa ta fice a fusace tace “dan ubanki kashemin ƴa zakiyi da asirinku ¿.

 

 

AFRAH taji zafin maganar kwarai amma haka ta daure .

 

 

Da daddare misalin ƙarfe tara BILLY ce da khalifa suka shigo JABIR ɗin be nuna damuwar shi ba guri n zuwansu .

 

Jikinshi suka haye suna wasa ita ko AFRAH takasa magana wai dama haka auran me mata yake ¿take tambayar kanta ……..

 

ZAZZAFAR KISHI!!!

_labar me ɗauke da makirci _cin aman da soyayya_

 

 

 

 

*NA*

*ZAINAB HABEEB.*

*MOM ISLAM*

 

 

 

 

*MARUBUCIYR*

 

*ZAINABU ABU*

 

 

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

 

 

*AND NOW*

 

*ZAZZAFAR KISHI!!!*.

 

 

 

*BISMILLHIR RHMNIR RAHIM*

 

 

*page* 5_6

 

 

_____ kwanan JABIR biyu a d’akin MARIYA yaune ze dawo d’akin AFRAH misalin 6 o’clock na yamma AFRAH tagama tsararren girkinta tayi had’a kunun aya ,bayan tagama girke ,girkenta tashiga wanka ta dad’e tana wanka .

 

Bayan tafito daga bathroom already tayi alwala zama tayi a kujerar dake gaban dressing mirror d’inta nutsuwa tayi tafara tsara kwaliya bayan ta gama ne taje ta d’auko kayanta atamfa ce d’inkin rigada siket yazauna a jikinta sosai dama AFRAH kyakyawace kamar kasaceta ka gudu wata humrah ta d’auko wace momynta ta siya mata bata ta6a shafawa ba kuma ance mata indai mijin na gida ne zata shafa .

 

Aikuwa AFRAH ta shafa humrar a ko ina na jikinta karfe 6:40 lokacin sallah yayi bayan ta idar da sallaharta ta kuma gyara fuskarta bayan anyi sallahar isha, i .

 

Misalin karfe 9: dai dai taji ana nocking mik’ewa tayi ta bud’e k’ofar JABIR ne yana sanye da shadda me ruwan k’asa shimafa yayi kyau sosai AFRAH data bud’e k’ofar ta koma kan kujera ta zauna JABIR ne yadubi fuskarta yace naga kamar bakiyi farinciki da ,dawowata ba juya idanuwanta tayi kana tace ni na isa tasa dariya .

 

Jiyo kamshin humrar jikinta yakeyi kuma yana jin mutuwar jiki mik’ewa yayi jiki babu k’wari yaje yarufe kofar palon yajanyo hannun ta suka nufi bedroom d’inta tunkafin su isa jikinshi ke rawa suna k’arasawa ya d’auketa ya kaita gado yafara sauya salo itadai AFRAH tarasa yau kuma meke damun JABIR duk yabi ya sauya mata a zafafe ya cire kayanshi yana cikin cire mata nata AFRAH tajiyo alamun buga k’ofa zata mik’e JABIR ya matseta da alamu bayajin bugun k’ofar seda yakoma asalin ango tukun ya sami sauk’i se alokacin abubuwa suke dawo mai gaskiya yayi farincikin samun AFRAH a budurwa samata albarka yashiga yi yana tausaya mata baccine ya d’aukesu se wajen k’arfe hud’u na asbh JABIR ya farka fara tashin AFRAH yayi bud’e ido tayi a hankali ta fashe da kuka d’aukarta yayi ,ya kaita bathroom ya had’a mata ruwan wanka yasata acikin ruwan k’wala ihu tayi seda ta jima tukun ya zubar da ruwan yazuba mata wani tayi wanka kasa taka kafarta tayi seda ya d’auketa tukun .

 

Ya kawota bedroom d’inta ya kwanta da ita kamar baby ya lulu6eta da bargo yatafi sallah itama tayi alwalar nafila tayi sannan tayi sallah ta koma ta kwanta .

 

 

Bacci ne me nauyi ya d’auketa ba ita ta farka ba se wajen k’arfe 10am ganin kayan abinci a dining tayi komawa d’akinta tayi takuma kwanciya .

 

JABIR ne yashigo yana sanye da yadi blue me laushi isowa kusada AFRAH yayi ,yace sannu my only nikuwa nace ina kabar MARIYA¿ koduk cikin angoncin,nne .

 

*Kira gareku y’ammata kar ,rud’in duniya ya rud’eku zubda mutunci babbar asarane dan Allah mu kula ko shekara goma kikayi da aure to wanan tabon, nanan wlh*

 

 

Rik’o mata hannu yayi suna nufi dining AFRAH ce tace naga abinci waya dafa¿ JABIR ne yace nine lokacin kina bacci.

 

Zubo mata abincin yayi ,yafara bata abaki batajin dad’in abinci ta kauda kanta gefe shayi ya had’a mata me madara dak’yar ta shanye suka koma bedroom d’inta .

 

Aranan dai JABIR be fita aiki yanata lalla6a AFRAH kamar k’awai .

 

MARIYA ce zaune kamar ta kurma ihu jiya ta tura yaranta saboda su hana AFRAH sakewa da JABIR segashi cikin dare taji ihun AFRAH tana cewa dan Allah kayi hak’uri .

 

Jitakeyi kamar taje ta shak’e AFRAH ta mutu kozataji sanyi acikin ranta gashi yauma ko fitowa beyiba bare yaje aiki .

 

Zuciyace ta d’ibeta ta mik’e a fusace tanufi d’akin AFRAH tayi sa,a d’akin a bud’e yake ko sallama batayi ba tashige batasami kowa a Palo ba kai tsaye bedroom ta nufa tana tura k’ofar taga abinda yasa takasa tsayuwa AFRAH tagani manne ajikin JABIR kamar ze maidata cikinshi kansu tayi a fusace Allah yasa dukansu da kaya a jikinsu kuma bacci sukeyi.

 

Finciko AFRAH tayi tafara kaimata naushi da sauri ya mik’e yana nuna MARIYA da yatsa yace wlh inbaki ficemin a d’aki ba wlh sekinyi nadamar shigowa .

 

MARIYA ce tadubi JABIR tace munafuki maci amana kunanan kuna cin amana ta .

 

JABIR ne yace menene abin cin amana matatace fa ba zina mukayi ba kuma ba kwananki na d’auka na bata ba AFRAH na tsaye tana jira MARIYA takuma tunkarota ,ta had’a mata jini da majina.

 

MARIYA ce tayi kukan kura ta cafko AFRAH itako ganin ta cafko ta AFRAH ta kaiwa MARIYA, wani wawan mari seda tafarajin jiri na d’ibarta .

 

JABIR ne yadaka musu tsawa yace MARIYA kiwuce d’akin ki galla mai harara tayi kana tace meze hana bazaka fita dani ba kafin takaiga k’arasa maganar ya wanketa da lafiyayyun maruka har biyu dagudu ta wuce d’akin ,nata tanata kuka sosai tana cewa wlh setad’au mataki kowannensu seya raina kanshi akan yayi aure ze cimata mutunci a gaban shegiyar yarinya .

 

Duba number wata k’awarta me duna jamila danna kira tayi daga d’ayan 6angaren jamila tace seyau kika tuna dani ko MARIYA ce tace ke inacinkin tashin hankali dan Allah gurin bokannan zaki rakani jamila ce tasa shewa tace karki damu sedai matsalar kud’i MARIYA ce tace babu matsalar su barin shirya .

 

Bayan tagama shiri tafice daga gidan suka had’u da kawarta suka wuce gurin boka wani jeji ne me uban nisa dukda ana tafiya a moto tofa in akazo kusada jejin sedai a yi parking d’in motar a tafi da k’afa mota bata shiga gurin duwatsu sunyi yawa sosai .

 

Da isarsu suka hango wata bukka ta kara da alamu nanne gidan boka suna cikin tafiya suka jiyo wani irin gurnani MARIYA ce zata tsorata Jamila ta rik’ota suka wuce da baya da baya suka kai gurin bokan daga nan .

 

Yafara yarenshi na hauka kana ya kalli MARIYA yace meke tafe daku kokuma aljani dan biluu yabani labari cewar kishiyace ta matsa miki MARIYA ce ta girgiza kanta tace eh hakane .

 

Boka ne yasa wata mahaukaciyar dariya kana yace mekikeso ayi yanxu MARIYA ce tace inso yazama batada farinjini a gun mijina yazamo ni kawai yake so .

 

 

Bokane yace karki damu buk’atarki ta biya suka had’a ido da jamila suka sa dariya jamila tace aina gayamiki aikin boka babu sauk’i.

 

Wani magani yamik’o musu a wani ganye a k’ulle yabawa MARIYA kana yace kud’inki dubu goma mik’amai kudin tayi daga nan suka taji ya daka musu tsawa yace kufita da baya.

 

 

Bazan sami yimuku typing gobe ,ba sedai zuwa Monday.

 

 

ZAZZAFAR KISHI

_labar me ɗauke da makirci _cin aman da soyayya_

 

 

 

 

*NA*

*ZAINAB HABEEB.*

*MOM ISLAM*

 

 

 

 

*MARUBUCIYR*

 

*ZAINABU ABU*

 

 

*AND NOW*

 

*ZAZZAFAR KISHI!!!*.

 

 

 

*BISMILLHIR RHMNIR RAHIM*

 

 

*page* 7_8

 

 

_____bokanne ya kwala musu kira juyowa suka da baya wani garin magani yakuma basu a k’ulle a leda yace wanan ,na ganyen ki bar6ada mata a cikin abinci wanan na ledar ki wurga d’akinta mijin bazeji marmarin shiga d’akinba MARIYA tsabar murna seda tak’arawa boka kud’i suka nufi inda motarsu take bayan sun fito daga jejin”.

 

Dubu uku tabawa jamila godiya tayi mata MARIYA tawuce gida tana shiga taci karo da JABIR da AFRAH zasu fita rik’e da hannun juna ko kulasu batayi ba ta shige d’akinta shima JABIR d’in baice mata komaiba sukayi fice warsu misalin k’arfe 6 o’clock na yamma segasu sun dawo da k’atuwar leda a hannun AFRAH part d’in MARIYA tawuce samunta tayi tana waya batasan metake cewa ba ta ajiye mata ledar zata juya kenan MARIYA tace ubanwa kika kawowa wanan shegiyar ledar AFRAH bata kulata ba tafice zuwa d’akinta tasamu har JABIR yatafi masallaci domin magriba tayi AFRAH ce ta dora abinci ta shiga wanka a kitchen d’inta MARIYA ce ta fito a hankali tana sand’a ta je d’akin AFRAH tayi sa,a k’ofar d’akin a bud’e take.

 

Alokacin AFRAH bata ma fara wankan ba MARIYA ta wurga barbad’a maganin ,nan a bayan gadon AFRAH ta fice ta nufi kitchen shima tayi sa,ar abincin murfin a goce yake ta barbad’a maganin da ke k’ulle a ganyen ta wuce d’akin ta a hankali.

 

Bayan AFRAH tafito daga bathroom direct kitchen ta wuce ta sauke abincin ta ,ta dawo d’akinta domin shafa mai tana cikin shafa mai taji gabanta na fad’uwa innalilahi tayi taci gaba da maimai tawa acikin zuciyarta jitayi ranta yayi mumunan 6aci alqur aninta ta d’auko tafara karatu daga nan tayi sallah ta zubo abinci auzubillahi tayi tafara cin abincin .

 

Bayan sallahr isha,a JABIR yashigo da sallamar shi yasamu AFRAH ta idar da sallah rungumota yayi, yace my afyy am felling hungry wlh sosai .

 

Da sauri ta mik’e tanufi kitchen zubomai abincin tayi zefara ci tace haba kayi bissmillah mana godiya yayi mata kana yace bissmillahirrahmani rahimm .

 

Daganan yafara cin abincin hankalin shi kwance bayan yagama cine ya mik’e ya had’owa AFRAH shayi da madara yakawo mata dan bata iya cin abinci sosai.

 

Washe gari MARIYA ce suketa zuba shewa da k’awarta jamila MARIYA tace ai wlh jira nakeyi ,inaga ya shegiyar nan zata kasance tana cikin wayar ne tajiyo kamar ana fad’a a d’akin AFRAH mik’ewa tayi da sauri saboda tagano ko aikin boka yafara kutsa kai tayi cikin dakin .

 

 

JABIR ne rik’e da AFRAH tanata kwara amai yana mata fad’a tadena cin abinda zetada mata da zuciya zaro ido tayi sekuma zata juya JABIR yace kodan wahalar datasha ai MARIYA kya temakawa AFRAH koda ruwan zafi ne MARIYA ce tadubi JABIR kana tace wlh batada wanan matsayin dan ubanta shegiya k’ilama cikin shege tayi zatazo ta jona mana a gida .

 

JABIR ne ya mik’e a fusace yace ki iya bakinki waye shegen ,nine shegen ficewa tayi tana masifa .

 

Bayan takoma d’akinta zufa ce ke karyo mata tana tunanin aikin boka yayi yanzu kuma gashi kamar ciki ne da wanan shegiyar ina wlh senad’au mataki .

 

Tana cikin haka k’awarta jamila ta kirata amsawa tayi da ai wlh aikin beyiba kina ganin d’azu dana shiga d’akin a jikinshi na ganta jamila ce ta zankad’o salati tace to kishirya zuwa gobe seku koma to tacewa jamila sukayi sallama ta kifa kanta a gado.

 

Fitowa yayi da ita yasata a mota yayiwa MARIYA sallama suka nufi hospital likita suka fara ganin akayi test d’in fitsari akayi na jini suka zauna jiran sakamako ba,a jimaba sega wata burwa rik’e da sakamakon da fara,a tace congratulation matarka na d’auke da juna biyu na tsawon sati uku murana gurin JABIR ba,a magana itako AFRAH ta jigata ko magana batayi gado aka bata .

 

Kwananta biyu a asibitin amma babu MARIYA babu alamarta ko zuwa batayi ba AFRAH taji sauk’i sedai karfin jiki da babu takardar sallama aka basu .

 

 

Suna cikin mota taga me gwaiba kwalawa mai gwaiba kira tayi JABIR ne yace karki k’ara maiyasa bazakiyi min magana na kirawo shi ba”.

 

Mai gwaiba ne yak’araso yace na ,nawa za,a baki hajiya JABIR ne yakar6e zancen yace kawo ta dubu d’aya mai gawaiba jin cini yazo ya ruga da gudu ya d’auko leda yazuba yabasu JABIR ne ya mik’a mai dubu da ,d’ari biyar godiya yayi mai suka nufi gida .

 

 

MARIYA yasamu a Palo tana zaune dayake d’akin mu had’u a Palo ne kuma palon su d’ayane kowace da kayan kallo a bedroom d’inta .

 

Zaune take tana kad’a k’afa sallama sukayi ko kallonsu batayi ba,bare tasan da zuwansu JABIR ne yace sannu MARIYA harara ta gallamai ta mik’e tayi bedroom d’inta .

 

AFRAH ko da maganar tafi k’arfinta wucewa tayi taje ta cire kayanta ta shiga wanka bayan ta fito ne JABIR ne yashigo ya d’auketa ya kwantar da ita a gado yafara sauya labari nikuma na fito na barmusu d’akin ganin suna harara ta.

 

 

Yaune JABIR ze koma d’akin MARIYA kwata kwata bayason tafiya yabar AFRAH ita kad’i .

 

 

Bayan sallahr isha,I misalin k’arfe tara na dare yashigo da sallamarshi MARIYA ko kallonshi batayi ba tashi tayi zata bar gurin dayake JABIR d’in ba kanwar lasa bane ya rik’ota ta fad’o jikinshi be nuna mata ta 6atamai rai na k’in zuwa duba AFRAH a hospital ba .

 

Cakul kuli yadiga yimata seda tayi ta dariya tukun ya barta”.

 

 

Washe gari MARIYA ta ,tambayi JABIR anguwa tayimai k’aryar zataje gidan su duba momyn ta babu .

 

Bayan ya barta shiryawa tayi ta d’auki isashen kud’i shima JABIR d’in yabata dubu biyar tabawa momynta , tayi farinciki har ,rungume JABIR d’in tayi ta fice ta barshi a gurin yana shirin fita aiki.

 

 

Jamila ce takirawo ta a waya take tambayarta akan ta shirya ?eh tace mata kana ta d’auki hand bag d’inta ta fice a gidan tabar yara da mai ,aikin datasa aka kawo mata .

 

 

Samun jamila tayi kusada layinsu bakin titi suna nufa wanan karon bada driver sukatafi ba motar haya suka dauka akan ze kaisu ya dawo dasu .

 

Bayan sun isa cikin jejin suka duba babu ,boka babu dalilin shi se wasu mata suka gani suna tafiya cikin jejin daka gansu kaga yan gidan masu kud’i saboda sunfi JABIR kud’i shima JABIR d’in nada kud’i amma kana ganin kayan dake jikinsu ,seka rik’e baki .

 

Jamila ce tacewa MARIYA kodai muyiwa wa ,inan mutanen magana ko sunga boka anan gurin .

 

 

MARIYA ce tace dan Allah kiyi musu magana ko lokacin da sukazo sun ganshi, jamila ce ta k’arasa zuwa gurin matan guda biyu da a k’alla sun haifeta tace sanunku dayar ce tace yauwa barka jamila ce tace dan Allah ko kunga boka dayar ce da tunda jamila tazo batayi magana ba tace bokafa ya tashi kuma bamusan inda yanufa ba amma idan kunason aikin hatsabibin,bokan dake can gaba Ku biyomu can zamu tafi…….

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment