Littafan Hausa Novels

Zazzafar Kauna Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Zazzafar Kauna Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

ZAZZAFAR KAUNA

 

*FREE BOOK*

 

*CHAPTER ONE*

 

 

 

 

 

Page_001

 

 

___K’arfe 7pm ne na daren ranar juma’a, tana zaune kan er kujerar dake gaban mudubin ta hannun ta rik’e da waya er k’arama wadda wasu ke kira da rakani kashi, sassanyan murmushi ke tashi daga kyakykyawar doguwar farar fuskar ta, tana nan zaune har zuwa lokacin da wata mata wadda kana ganin ta kasan mahaefiyar tace, saboda tsananin kama da suke yi, ta yaye labulen d’akin ta lek’o tana kallan ta

 

“AYRAH wae har yanzu jiran Abban kike?” Murmushi ne ya sake wanzuwa akan fuskar wadda aka kira da Ayrahn wanda hakan ya bawa dimple d’in dake gefen kowanne kumatun ta lotsawa sosae sannan tace cikin muryar ta me dad’in saurare

 

“Ehh Umma..” ta6e baki Umma tayi tace

 

“Ae se kiyi ta jira..” daga haka ta saki labulen ta koma tsakar gida. Tana nan zaune bayan wajen minti 10 ta jiyo sallamar mahaefin nata daga tsakar gidan su, seta ajjiye wayar da sauri akan gadon sannan ta mik’e ta yaye labulen d’akin ta fito, hasken farin wata da kuma na k’wan fitilar da suka kunna ya sanya ni ganin kyakykyawar fuskar ta da har zan iya kwatanta muku ita, matsashiya ce er kimanin shekaru 19 doguwa ce fara sosae, me idanu manya manya da dogon siririn hanci, se d’an k’aramin red lips d’in ta, sanye take cikin doguwar riga bak’a babu d’an kwali a kanta dan haka ta yafa mayafin doguwar rigar akan ta

Kayar Ruwa Hausa Novel Complete

“Abba sannu da zuwa..” ta fad’a tana neman waje ta zauna

 

“Yawwah Ayrah” Abban ya fad’a yana neman waje ya zauna sannan da murmushi kan fuskar sa ya sake kallan Ayrahn bayan ya amsa sannu da zuwan da Umma ke masa

 

“Toh in gyara zama dae in sha labarin karatun kin nan, dan da alama akwae magana a bakin ki” murmushi ta sake yi sannan tace

 

“Abba ae tun d’azu kae nake jira nazo muku da wani babban albishir” Umma ta kalli Abba tace

 

“Ahh toh, tun d’azu tak’i fad’a min abinda yake ta sanya ta murmushi tace seka dawo..” Abba ya maeda duban sa kan Ayrah yace

 

“Toh muna jin ki, Allah yasa alkhaeri ne” gyara zama tayi daga inda take zaune sannan ta fara magana har lokacin murmushi yak’i barin kyakykyawar fuskar ta

 

“Abba na had’u da RAJ..” ta fad’a da mad’aukakin murmushi akan fuskar ta, cikin rashin fahimta dukkan su suka kalle ta, seta d’an tsaya itama tana kallan su kafin tace

 

“Raj fa nake nufi, Umma Raj d’ina fa, kun tuna?” ta fad’a tana d’an murmushi dan ita in dae akan Raj ne bata da wata kunya, kallan juna Umma da Abba suka yi kafin Abba ya runtse idanun sa sannan ya fara k’ok’arin magana

 

“Umma cewa yayi ma na fad’a tun wuri Abbun sa zasu zo wajen Abba” Ayrah ta fad’a kafin Abban ya fara magana, Umma dake lura da yanayin Abba ta furta a hankali tana kallan sa sosae

 

“Abban su lafiya dae koh?” jinjina kae yayi kafin cikin er dakiya ya furta

 

“Kina nufin Raj d’an gidan Kabeeru..?” seta jinjina kae cikin jin dad’in yadda Abban ya gane maganar ta ta tace

 

“Ehh Abba, bama mu ta6a tunanin..” d’aga mata hannun da Abba yayi ne ya sanya ta dakatawa daga fad’in maganar da take k’ok’arin fad’a, ta cigaba da kallan yadda lokaci guda k’wayar idanun sa ta sauya, haka zalika Umma ma tak’i kallan ta, seda Abban ya sake runtse idanun sa sannan ya bud’e ya fara fad’in

 

“Kar ki sake min maganar sa ko maganar wanda ya shafi ahalin su gaba d’aya..” Abba ya k’arasa maganar idanun sa na sake yin jawur, cikin rashin fahimta take kallan Abban nasu, ta kuma kalli Umma sannan tace a d’an rud’e

 

“Abba ko dae ka bayar dani ne ga wani bansani ba? Abba cewa nayi fa Raj ke so azo a nemar masa aure na..”

 

“Ayrah..ki tashi ki bar wajen nan idan baso kike zuciya ta ta buga ba” Fararen idanun ta dake d’auke da bak’a sid’ik d’in k’wayar idanu ta d’aga ta sake duban mahaefin nata, take wasu k’walla suka tarar mata tana jin yadda k’irjin ta ke bugawa da k’arfin gaske, “me yake faruwa ne?” ta tambayi kanta

 

“Abba Raj ne fa, Abba Raj dae wanda ka sani fa, akan sa nake magana..” Abba ya runtse idanun sa yana jin wani irin zafi a cikin ransa cikin 6acin rae ya furta

 

“Ki saka a ranki in dae ina raye, har abada ba zaki ta6a auren Suraj ba” da wani irin razana ta d’aga ido ta kalli mahaefin nata, tana jin yadda kalaman nasa ke sauka a cikin kunnuwan ta kamar saukar mashi, kafin takae ga cewa komae ta sake jiyo Abban nata yana fad’in

 

“Ki kawo koma waye a fad’in garin nan gaba d’aya amma dae_dae da minti d’aya kada ki sake ki yaudari kanki kiyi tunanin zan aura miki Raj, bama Raj ba duk wani daya dangance su bazan ta6a aura miki shi ba” kuka ne ya k’wace mata babu k’ak’k’autawa tana jin wani iri a rae da zuciya har ma da gangar jikin ta, a hankali taja k’afafun ta da rarrafe ta k’arasa gaban mahaefin nata ta rik’o k’afafun sa sannan ta fara magana cikin kuka, kyakykyawar fuskar nan ta ta tayi jajir

 

“Abba..ka tausaya min, Abba ka taemakawa zuciya ta, Abba ko da wannan ce zata zama alfarma ta k’arshe da zaka iya yi min a rayuwa Abba kayi min ita don Allah” ta k’arasa fad’a tana sake fashewa da wani sabon kuka, a hankali Abba ya zame k’afafun sa bugun zuciyar sa na k’aruwa ko ba’a gwada shi ba tabbas yasan ciwon sa na dab da tashi, ya d’an runtse idanun sa kad’an sannan ya fara k’ok’arin tafiya, ta sake rik’o k’afafun nasa tana kuka kamar wadda ranta ze fita

 

“Abba ina k’aunar Raj, zuciya ta zata iya bugawa idan kace zaka rabani da shi, Abba kace wani abu don Allah” juyowa Abba yayi yana kallan ta kana a fusace yace

 

“Ko mutuwa zaki yi ba zaki ta6a auren Raj ba..” daga haka ya wuce d’akin sa, mik’ewar da Umma tayi ne ya sanya ta d’ago fuskar ta da tayi jajir tace

 

“Umma ya zaki tafi ki barni cikin duhu, Umma me Raj ya muku da Abba zece bazan aure shi ba, Umma Raj fa ko har yanzu baku gane wanda nake magana akansa ba.. Umma kiyi wa Abba bayani don Allah” ta k’arasa maganar sanda wani kukan yaci k’arfin ta, ko kallan inda take Umma ba tayi ba ta wuce cikin d’akin da Abba ya shiga.. A hankali ta cigaba da rera kukan ta, seda tayi me isarta sannan taja k’afafun ta zuwa cikin d’akin ta har lokacin hawaye yak’i dena sintiri akan kuncin ta, wayar ta dake ajje ta d’akko ta danno wata number ta kira…

 

 

 

… A hankali ya sako k’afafun sa farare tass dake cikin takalmin wanka, seda ya cire su daga k’ofar toilet d’in sannan ya sako kansa zuwa cikin kyakykyawan bedroom d’in, k’arasawa yayi bakin k’aton mudubin sa ya sanya hannu ya d’auki comb ya fara taje sumar kansa data sha gyara sosae, banda ruwan daya ta6a ta a gyara take tsaf se tashin k’amshi me dad’i da take yi, yanayin yadda yake d’auke da towel ne ya sanya ni ganin yadda k’ak’k’arfan jikin sa yake, dogo ne me k’ak’k’arfan jiki, fari ne sosae wanda hakan ya sanya bak’ar sumar dake kan k’irjin sa ta bayyana kan ta sosae kan farar fatar sa wadda ke kwance luff luff kamar wadda ake kwantar da ita da Comb, yana da dogon hanci me tsayi, fuskar sa d’auke da bak’in sajen daya zagaye bakin sa, ringing d’in da yaji wayar sa nayi ne ya sanya shi sakin wani k’ayataccen murmushi ya ajje comb d’in kan stool d’in sannan ya mik’e ya k’arasa inda wayar ke ajje ya d’auka kana ya zauna ya jinjina da pillown dake kan tank’amemen gadon sa kana ya kara wayar a kunne bayan ya d’aga, da kukan ta ya fara cin karo cikin wayar, seya mik’e zaune yana bud’e manyan idanun sa yace

 

“Subhanallahi..Ayrah meya saki kuka?” ya fad’a cikin kulawa, cigaba da kukan tayi kamar ranta ze fita, daga inda yake zaune kuwa yana jin kamar ana watsa masa dalma ne, mik’ewa tsaye yayi ya murza goshin sa da d’ayan hannun sa yana lumshe idanun sa har lokacin bata bar kukan ba, ya kuma yin k’asa da muryar sa yace

 

“Ya isa haka don Allah, ya isa haka, pls kiyi shiru ki fad’a min why are u crying..” ya sake fad’a cikin rarrashi

 

“Raj..” ta fad’a cikin kukan, ya lumshe idanu yana jin muryar ta ta har cikin gangar jikin sa

 

“Na’am.. Ayrah, pls menene Uhmm?” daga inda take zaune ta d’an lumshe idanu tana sassauta kukan ta koma sheshshek’a se can ta fara magana tana yi tana d’an aje ajiyar zuciya

 

“Abba ne..”

 

“Me Abban yayi?” ya fad’a yana jin yadda ya k’agu yaji abinda ya sanya ta kuka haka

 

“Abba yace bazan aure ka ba.. Raj meka yiwa Abba?” cikin rashin fahimta ya sake bud’e manyan idanun sa kana yace

 

“Ni kuma?” kamar tana gaban sa ta jinjina kae, kafin yace komae kuma ta sake cewa

 

“Na yarda da kae Raj, kawae ka fad’awa Abbun ku yazo wajen Abba, ina tunanin be gane Raj d’in da nake nufi ba..” neman waje yayi ya zauna kafin yace

 

“Ohk..In Sha Allah, yanzu dae ki dena kukan kinji? In Sha Allah ni naki ne kema kuma tawa ce kinji?” jinjina kae tayi ba tare da tace komae ba, se kuma can tace

 

“Ehh..”

 

“Oh yah Smile..” ya fad’a daga inda yake yana d’an murmushi, goge fuskar ta tayi sannan ta d’an yi murmushin me d’an sauti wanda tasan hakan ze faran ta masa

 

“Awwnnn That’s my girl..yanzu dae ki aje waya kiyi bacci zan je na samu Abbu da wannan maganar.. I luv u..” ya k’arasa fad’a idanun sa a lumshe, itama nata idanun ta lumshe kamin tace

 

“Tohm..” Tashi yayi ya k’arasa shiryawa cikin wata bluen shadda dan babu k’arya yayi missing manyan kaya, ba tare da ya d’ora hula akan sumar kansa ba ya d’auki wayar sa har lokacin be dena mamakin dalilin da yasa Abban nata yace haka ba. Kae tsaye parlourn k’asa ya sauko cikin nutsuwar data zame masa jiki, dae_dae lokacin da wata farar mata wadda ak’alla zatayi shekaru 45 zuwa 50, kyakykyawa ce kamar yadda d’an nata yake, tana sanye cikin wata atamfa me kyau d’inkin riga da skirt, jera warmers d’in data fito dasu daga kitchen akan dinning take, ta kalle shi da murmushi kan fuskar ta sannan tace

 

“Ka k’araso ka fara cin abinci koh?, semu zauna mu samu muyi hira..” d’an murmushi ya saki kad’an kamin ya shafa sumar kansa yace

 

“Tohm Ummee.. Amma inaso ne muyi wata magana me muhimmaci..” ya fad’a yana d’an lumshe manyan idanun sa kad’an, dae_dae lokacin Ummee ta gama jera kayan data fito dasu seta k’araso inda yake tsaye tace tana murmushi

 

“Shikenan Raj, ni dama daga yadda na ganka nasan akwae magana a bakin ka” shima murmushin ya maeda mata sannan dukkan su suka wuce zuwa cikin k’aton parlourn daya k’awatu da had’ad’d’un kujeru, suna zama Alhaji Kabeer ya shigo cikin d’akin da sallama sanye cikin manyan kaya da babbar riga, dukan su suka amsa masa ya k’araso yana kallan su su duka kuma a lokaci guda yana amsa sannu da zuwan da suke masa, akan kujera ya zauna, yayin da Raj ya sauko daga kan kujerar yana shirin zama a k’asa Alhaji Kabeer yace

 

“A’ah kayi komawar ka ka zauna, yau ae hira zamuyi..” murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa seya koma ya zauna yana kallan Alhaji Kabeer yace

 

“Barka da dawowa Abbu..”

 

“Barka kadae Raj”

 

“Ko dae a kawo maka abincin nan ne?” Ummee ta fad’a tana kallan Abbun, girgiza kae yayi kafin yace

 

“A’ah fara kawo min dae juice na sha..” mik’ewa Ummee tayi ta wuce inda ze sadata da dinning area, yayin da Abbu ya dawo da duban sa kan Raj yace

 

“Ya hanyar dae? Kuma ya karatun?”

 

“Alhamdulillah Abbu..ina tafe da wani albishir fa..” ya fad’a da murmushi kan fuskar sa, dae_dae lokacin da Ummee ta k’araso hannun ta d’auke da juice d’in ta ajjiye sannan ta fara k’ok’arin zubawa a cikin tambulan

 

“Toh ko zamu bari mu fara cin abinci?” Abbu ya fad’a yana kar6ar juice d’in da Ummee ta mik’a masa kana ta nemi waje ta zauna, hannun sa ya kae kan sumar kansa ya d’an shafa sannan yace

 

“A’ah Abbu.. Na k’agu na sanar daku ne..” Ummee ta kalli Abbu tana murmushi tace

 

“Ae kawae ka k’yale shi ya fad’a dan tun d’azu ya kasa komae har abincin ma shima beci ba..”

 

“Ohk ina jin ka..” Abbu ya fad’a yana kae juice d’in bakin sa

 

“Abbu na samu matar aure..” dukkan su suka kalle shi cike da mamaki da kuma farin ciki duka a lokaci guda, mutumin da suka san kwata kwata baya kula wasu mata amma yau shine ke fad’in ya samu matar aure? Toh ta yaya?

 

“Wacece wannan Raj?” Ummee tayi k’arfin halin fad’in haka, wani k’ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace bayan ya lumshe idanun sa ya bud’e

 

“Ayrah..”

 

“Wacece Ayrah?” Ummee ta fad’a tana kafe shi da idanun ta

 

“Ayrah dae wadda kika sani Ummee, kada kice min har kin manta ta, Ayrah dae tawa wadda kika sani..” k’warewar da Abba yayi ne ya sanya su duka suka kalle shi, babu k’ak’k’autawa ya shiga yin tari sosae, da sauri Raj ya mik’e ya isa fridge ya d’akko ruwa ya kawowa Abbun, da k’yar ya iya kar6a yasha ruwan, ya shiga sauke ajiyar zuciya kamar wanda yayi gudu

 

“Sannu Abbu..sannu..” shine abinda Ummee keta maemaetawa amma Abbun bebi ta kanta ba ya kalli Raj yace

 

“Ya..akayi ka had’u da ita?” yayi maganar a rarrabe yana kallan Raj, sosae Raj ke binsa da kallo yana so ya gano abinda ya sanya shi lokaci d’aya ya zama wani iri

 

“Abbu..”

 

“Ya akayi ka had’u da ita? Ko dama kuna tare tsawon lokacin nan?” Abbu ya katse masa maganar da yayi niyyar yi, girgiza kae Raj yayi har lokacin idanun sa nakan Abbu

 

“Tun wuri ka rabu da ita Raj, ka rabu da ita dan auren ku baze ta6a yiwuwa ba, tun wuri ma ka cire ta a ranka zefi maka..” Abbu ya fad’a yana mik’ewa yayi hanyar d’akin sa, da kallo yabi Abbun sannan ya maeda duban sa kan Ummee yana jin yanda k’irjin sa ke bugawa

 

“Ummee..” ya fad’a yana kallan ta, seta mik’e kawae tabi bayan Abbun a ranta tana sak’a yadda zasu 6illowa al’amarin, lallae idan ba suyi wasa ba suna cikin matsala.. Runtse idanun sa yayi har lokacin yana jin yadda bugun zuciyar sa ke k’aruwa, me yake faruwa ne? Yakae wajen minti 5 zaune a wajen yana sak’awa da warwarewa sannan ya d’auki wayar sa ya lalubo number ta ya danna kira. A 6angaren ta kuwa har lokacin tana kwance kan madaedaecin gadon d’akin, kanta d’ore akan pillow hawayen da suka k’i tsayawa se zuba suke akan pillown, kanta babu d’an kwali hakan ya bawa sumar kanta damar bajewa akan pillown, dae_dae lokacin da kiran wayar tasa ya shigo wayar ta yayi dae_dae da lokacin da Umma ta yaye labulen d’akin ta shigo, ringing d’in da taji ya sanya ta kallan wayar, Ayrah ta tashi zaune tana kallan Umman lokaci guda tana maeda duban ta kan wayar

 

“Mik’omin wayar..” Umma ta fad’a tana mik’a hannun ta, lumshe manyan idanun ta tayi wasu hawaye masu d’umi suna zubowa akan kuncin ta, ganin bata da niyyar mik’o mata wayar ne yasa Umman ta k’arasa da kanta ta d’auki wayar ta kashe ta gaba d’ayan ta sannan ta kalli Ayrah data fashe da wani irin kuka tace

 

“Kiyi shiru ki dena kuka, ki tsaya ki saurare ni, base kin tada hankalin mu muma mun tayar da naki ba..” kafin Umman ta kae k’arshen zancen ta Ayrah tace cikin kuka tana girgiza kae

 

“Umma meyasa haka? Shin baku san wanene Raj ba? Baku san halin sa ba? Ko kuwa iyayen sane baku sani ba..” K’arasawa Umma tayi ta zauna akan gadon kana ta kamo Ayrahn cikin jikin ta, bata fara magana ba seda taji ta fara sauke ajiyar zuciya, sannan ta kama dogon gashin Ayrahn ta d’aure a tsakiyar kanta kana ta fara magana a nutse tana jin zuciyar ta na mata wani irin zafi…

 

B’angaren sa kuwa runtse idanun sa yayi bayan ya sake kiran layin Ayrah yaji shi a kashe, yaja wani dogon numfashi sannan ya mik’e akan k’afafun sa yana daedaeta nutsuwar sa a ransa yana jin ya zama dole yasan aenahin abinda yake faruwa kafin k’wak’walwar sa ta tarwatse, dan kuwa tabbas akwae rina a kaba, me yake faruwa haka?…..

 

 

 

 

 

_*TUSHEN LABARI*_

 

 

 

 

ZARAH AUTA (Mhiz Innocent)

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment