Littafan Hausa Novels

Zawarcin Aliya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Zawarcin Aliya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Bisimillahir Rahamanir Rahim*

 

 

 

 

 

 

 

_Dasunan Allah me rahama mejin k’ai , tsira da Aminci su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad s.a.w

 

 

 

*Albishir ga masoyana nadawo daga hutun da natafi , dafatan zaku ci gaba da bibiyata kamar a baya . Ina fatan littafin ya nishad’an tar daku ya Kuma fad’akar daku tare da amfanar mu baki d’aya Nagode Masoyana kuci gaba da bibiyar ‘Yar mutan Kanawa

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Page* 1&2

 

 

 

 

 

 

 

Wata had’add’iyar mota ce tayi parking a harabar wani k’aton Shopping Mall , sai da tayi wajen Minty 15 da tsayuwa sannan aka bud’e wajen me zaman banza , wata matashiyar budurwa ce me kimanin shekara 26 ta fito cikin shiga ta alfarma , daga b’angaren direba Kuma wani jibgegen Alhaji ne bak’i gajere ya fito sai faman muzurai yake , kallon matar da sukazo da ita yayi yace ” Gimbiyata ai basai na shiga ba kawai ki shiga kid’auko duk abinda kikeso kibiya tunda atm d’in nawa Yana wajen ki , ya mutsa fuska tayi sannan tace ” haba Alhaji Wada kamar ya in shiga ni kad’ai ? Saboda me kai bazaka taho mushiga tare ba ? …

 

 

Sakayya Namiji Hausa Novel Complete

Alhaji Wada yashiga gwale ido Yana muzurai tare da kallon ta yace ” *Aliya* Amman tun kafin mutaho sai da na sheda miki bazan shiga gun shopping ba zan jiraki a motar , Kuma kika amince da hakan to Dan meyasa zaki canza magana ? Aliya tace ” kwantar da hankalin ka badai saboda kar aganka bane a gayawa wannan masifaffiyar matar taka ? To natanadar maka abin kare kai , face mark ta ciro cikin jakar ta ta mik’a masa . Alhaji Wada ya tamke fuska Yana muzurai tare da cewa ” haba dai Angaya miki saboda wata mace zanji tsoro har na rufe fuskata ? Kawai bana ra’ayin shiga irin wanan wajajen ne , Aliya ta tamke fuska itama tana cewa ” anshi ka saka tun Muna sheda juna don wlh tunda har muka zo sai ka shiga ka d’aukar min kwadon Shopping , ganin Aliya ta tamke fuska yasa Alhaji Wada ansar Face mark da sauri yasa , don tabbas Abinda Aliya ta fad’a gaskiyane . Don yanajin tsoron magul mata kar agansa a gayawa Falmata , shikuma Yana bala’in tsoron ta gashi Kuma Yana mutuk’ar son Aliya….

 

 

 

Haka suka jera shida ita Aliya sai Hira take masa wacce baya fahimta saboda tsananin fargaba…..

 

 

 

 

 

Hajiya Falmata wai yaushe kayan da mukayi order zasu iso ? Wacce aka Kira da Falmata ta yatsina fuska sannan tace ” kedai bari Hajiya Zainab kinsan wani lokacin Order takan yi one month bata iso ba , Amman nasan suna hanya Nan ba da jimawa ba , Hajiya Zainab tace ” dama a ciki akwai Abinda nake buk’ata saboda zanyi amfani dashi , Hajiya Falmata tace ” karki damu duk abinda akeyin order akwai a wajen wani Shopping Mall da nasani , in kin shirya sai na rakaki muje kisiyo Abinda kikeso kafin wancan su iso , Hajiya Zainab tace ” ai ni yanzu ma a shirye nake kawai tashi muje don inason amfani da abin sosai , Hajiya Falmata tayi dariya tace ” da wurwuri haka to bari in d’auko mayafina sai muwuce , Nan ta mik’e ta nufi b’angaren bedroom d’inta ,…..

 

 

 

 

 

Aliya tunda suka shiga wajen shopping tafara jidar kaya tamkar zata bud’e sabon shago , tun Alhaji Wada na zuba mata ido har karshe yace ” haba Aliya wannan kaya da kike d’iba duk amfani zakiyi dasu ? Aliya ta kallesa tare da turo baki tace ” haba Alhaji na sai kace talaka ni a ganina ko duka kayan wajen nan na d’iba zaka biya kud’in batare da kayi magana ba , Alhaji Wada ya d’an sassauta fuska yace ” hakane Gimbiyata Amman ganin kayan nayi tamkar sun yi miki yawa , Aliya tace ” bawani yawan da sukayi tunda kasan dai dole zanyiwa kowa na gidan mu tsaraba , zaro idanuwa Alhaji Wada yayi tare da maimaita kalmar kowa na gidan su tabbas Aliya bata da hankali , wannan bataliyar yaran gidan nasu tace kowa sai tayi masa tsaraba Ina kanta , shi ba fitar kud’in ce zata damesa ba kawai Yana fargabar had’uwa da Wanda yasan shine saboda gudan agayawa Hajiya Falmata , don wannan wajen Shopping d’in Nan k’awayen Hajiya Falmata sukafi zuwa siyayya , har ita Hajiya Falmatar Yana kawo ta wajen don duk abinda ake buk’ata akwai , Aliya ce ta katse masa tunani da cewa ” nagama d’aukar wa yaran gidan mu yanzu saura Baba Shima yace in yo masa leda guda tasa , Alhaji Wada yace ” kiyi hak’uri mutafi in yaso zuwa dare sai mudawo kiyi masa nasa siyayyar , Aliya ta zaro idonuwa tace ” sokake na kwana a zaure , ai Wanda na maida kayan da na d’iba duka in d’auki iya na Baba , kafin Alhaji Wada yace wani Abu tuni ta wuce tafara d’ibar kayan da Baban yace yanaso…

 

 

 

 

 

Su Hajiya Falmata suna tafe a motar suna hirar su wacce duk akan mazajen su ne , Hajiya Zainab tace ” kinsan Wai dangin mijina suna Nan sun bashi wata yarinya budurwa wai ya aura , wani wawan burki Hajiya Falmata ta taka a tsakiyar titi saura k’iris ta had’a accident Allah ya tsare , duban Hajiya Zainab tayi sannan tace ” kina nufin kicemin Wai kishiya suke so yayi miki ? Hajiya Zainab tayi wani malalacin murmushi sannan tace ” emana wai tunda bazan haihuba sai inbawa wata waje tazo ta haihu , Hajiya Falmata ta danno Ashar sannan tace ” lallai baki uban suba ne shiyasa suke son yi miki wannan haukar , nifah wlh natsani kalmar kishiya bare Kuma ace za’ayiwa wata wacce nasani , a gaskiya kina da hak’uri Hajiya Zainab don inda nice da tuni anyi angama , Hajiya Zainab tayi murmushi sannan tace ” ai Nima ba hak’urin nayi ba kawai Ina shirya yadda zanyi musu ne Amman kema kinsan wacece ni akan Alhaji , Hajiya Falmata tayi murmushi sannan tace ” yanzu naji batu ki shirya Abinda zai basu tsoro yadda ko akan wata bazasu k’ara marmarin yin hakan ba , don wlh ni ko ji nayi Alhaji Wada zai je dangin sa hanawa nakeyi saboda ma kar yaje yaga wata banzar , saboda haka kina kallo ko zuwa gidana basayi saboda sun San halina , Shima Wanda ya ajiye nin tsorona yakeji bare Kuma su , haka suka ci gaba da tattaunawa har suka k’araso wajen shopping sukayi parking sannan suka fito , idanuwan Hajiya Falmata ne ya sauka kan motar mijinta Alhaji Wada , don duk inda taga motar Alhaji Wada sai tagane koda anjera su da yawa iri d’aya , cikin zuciyar ta tace “to shikuma Alhaji me yazo yi Nan ? tasan dai in shopping zaiyi tare suke zuwa shida ita Amman bata sani ba ko wani abokin nasa ya rako , haka suka nufi k’ofar shiga ciki tana nazari……

 

 

 

 

 

Aliya sai da ta d’aukar wa Baba kaya masu yawan gaske harda Wanda baice dasu ba , tana tafe Alhaji Wada nabin bayan ta da kwandon kaya , tamkar ance masa ya d’aga idanuwan sa ya kallo wajen shigowa ya hango Hajiya Falmata da Hajiya Zainab sun shigo , Nan take hantar cikin sa ta kad’a wani fitsari ya d’igo masa a wando , da sauri ya saki kwandon siyayya yayi baya da gudu yashige wani lungu , …

 

 

 

Aliya ta juyo a fusace jin tana magana ba amsa , wayam tagani ba Alhaji Wada sai kaya a zube a k’asa , duba kayan tayi taga duka kayan da ta d’ibane , wata uwar Ashar ta danno tare da cewa ” ni Alhaji Wada zai tozarta ? Wato saboda na takura ya shigo shiyasa yakemin wannan iskan cin har da zubarmi da kaya , sunkuyawa tayi ya shiga tsince su tana sawa a kwandon , dai dai lokacin su Hajiya Falmata suka k’araso wajen , k’amshin turaren Alhaji Wada taji ya daki hancin ta Nan ta Kuma baza ido tana kalle kalle , aikuwa tayi tuntub’e da Aliya wacce take sunkuye tana d’ebe kaya tana masifa , koda taji an bigeta da sauri ta d’ago tana duban Hajiya Falmata , kallon kallo suka shiga yiwa juna Aliya tana tuna a Ina tasan fuskar matar . yayin da Falmata keyiwa Aliya kallon raini , ganin kallon da Hajiya Falmata keyi mata yasa itama ta tamke fuska sannan tace ” baiwar Allah icen da kika bige dashi baiji miki ciwo ba ko ? Hajiya Falmata ta yamutsa fuska sannan tace ” baijimin ba saboda nid’in ba wacce irin wannan icen zaijiwa ciwo bace , Aliya tace ” zai iya jimiki ciwo mutuk’ar kika Kuma tuntub’e dashi , aikin banza kawai taja tsaki tare da sunkuyawa taci gaba da d’ebe kayanta , tana gamawa ta juya zata bar wajen atm d’in Alhaji Wada dake hannun ta ya fad’o , sunkuyawa tayi zata d’auka itama Hajiya Falmata ta sunkuya don d’auka don ko a bacci take aka tashe ta tasan wannan atm d’in na mijinta ne , dukan su hannun su ya sauka kan atm d’in Hajiya Falmata har rawa hannun ta yakeyi tanajin kirjin ta na bugawa , meye had’in Alhaji Wada da wannan Yarinyar ? Wato har matsayi gareta a wajen sa tunda gashi atm d’in sa ma Yana hannun ta , tabbas yau sai Yarinyar Nan tayi nadamar zuwan ta duniya da Kuma sanin Alhaji Wada.

 

NEWER

ZAWARCIN ALIYA HAUSA NOVEL COMPLETE

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment