Littafan Hausa Novels

Zan rayu da kai Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Zan rayu da kai Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ZAN RAYU DA KAI

 

 

 

 

HOT LOVE STORY

 

 

 

FADEELAH S UTAI

 

 

(Fadeelah Khan)

 

 

 

ELEGANT ONLINE WRITERS

 

 

 

 

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

 

 

 

_________ A hankali ya haura saman kayataccan gadon datake a kwance, kallon yanda ta kudundune yake ,kai da gani kasan bajin dad’in barcin take ba.

 

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya

 

Murmushi ya saki kana A hankali ya fara janye mayafin data rufe fuskarta dashi , kyakkyawar fuskarta ce ta baiyana ta hasken wutar d’akin , inda baisan lokacin da yasaki ajiyar zuciya ba, kana ya shiga janye dogon gashin daya rufe mata gefen fuskarta,

 

 

A hankali tashiga motsawa tana so ta farka, hura mata iskar bakinsa ya shiga yi yana mai sake zubawa fuskarta narkakkun idanunsa masu kama dana mai jin barci.

 

 

 

Jin kamar mutum a kusa da ita yasa ta tashi firgigit tana shirin kwalw ihu yayi saurin Rungumeta tsam a jikinsa, yana mai cewa” shiiii Yan matana nine fa your Uncle”

 

 

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai sake lafe wa Akan faffadan kirjinsa , gawani Sassanyan kamshi daya ke tashi a jikinsa, har yanzun jikinta bai dena rawa ba .

 

 

Sake shigar da ita yayi cikin jikinsa yana mai ci gaba da buga mata bayanta, kana a hankali yace ” nine ko na tsoratar dake ” d’aga masa kai tayi tana mai turo d’an karamin bakinta, ” Am sorry” yace yana mai cirota daga jikinsa .

 

 

 

Zuba mata lumsassun idanunsa yayi yana mai sake ware idanunsa Akan kyakkyawar fuskarta dan yau gani yake tamkar a karawa Jiddeerh kyau.

 

 

 

Sunkuyar da kanta kasa tayi tana mai jin wata irin fad’uwar gaba saboda kallon data ga Uncle d’in ta yana yi mata, janye idanunsa yayi daga gareta kana ya d’ago ta cak tamkar wata jaririya , bai direta a ko ina ba sai a k’ayataccan Falonsu , zaunar da ita yayi akan kujera kana ya wuce in da ya ajiye ledojin daya shigo dasu, a gabanta yazo ya ajiye kana ya wuce kitchen, ita dai binsa take da kallo tana mamakin yanda taga Uncle yana nan nan da ita tamkar wata danyen Gold.

 

 

Dawowa yayi hanunsa d’auke da mug da kuma plate kana ya juye kajin da ya shigo dasu sai kamshi suke , sannan ya zuba Rufaida yoghurt acikin mug d’in, kana ya juyo ya kalli Jiddeerh , mika mata hanunsa yayi A lamar ta zo cike da dauriya ta Mika masa nata, zaunar da ita yayi a kusa dashi kana ya fara bata kazar.

 

 

Girgiza masa kai tayi alamar ta koshi , d’ago kansa yayi ya kalleta kana ya dawo sak Abdallah data sani yace ” kin san bana son gardama ko”

 

 

Ganin dagaske ya koma mata asalinsa yasa ba musu ta bud’e bakinta ya fara ciyar da ita, ganin da gaske ta koshi yasa ya fara bata drinks d’in , goge mata baki yayi kana A hankali yasaki ajiyar zuciya ya dubeta yace ” Jiddeerh” jin yanda ya kira sunanta da Sassanyar murya yasa ta d’ago da kanta tana mai zuba Masa kyawawan idanunta masu matuk’ar Haske.

 

 

 

A hankali ya sauke ajiyar zuciya kana yaci gaba da magana.

 

 

” Jiddeerh tun ranar dana had’u dake a wajen musabak’a naji bugun zuciyata ya karu,nasan cewa tabbas kece Aljanar danake yawan gani a cikin barcina kece wacca kika Hana zuciyata sukuni kece wacca nake buri da son ganinki a zahirance, tun daga ranar dana ganki ban sake ganinki a barcina , nashiga damuwa sosai na rashin ganinki dabanayi, har nake tunanin kodai Aljanune suke so su rudar dani , haka na danne zuciyata ganin bazan iya hakura dakeba yasa nakoma aranar daza ku koma garunku Dan kawai na sake ganinki, ganin kyawawan idanunki yasa na sale tabbatar dacewa ke d’in ce, saboda aduk lokacin dazakizo wajena bana ganin komai naki sai fararen idanunki masu matuk’ar Haske, yanayin maganar ki da kuma shagwab’ar ki su ne suka sake tsundumani cikin soyayyar dana dad’e ina tanadarwa Aljana ta, haka nayi ta bibiyarki ,nasha zuwa garinku dan kawai na ganki . Jiddeerh soyayyar ki ta kusa haukata a lokacin dana ga Kamal yana kallonki kina barci a office d’ina, I luv you Jiddeerh with All My Heart

 

Ina miki soyayyar da ban tab’a yiwa wata ya mace a duniya ba, ba iya soyayyar yan uwantaka nake mikiba A’a soyayyar Aure nake miki Jiddeerh, naji matuk’ar tsoro a lokacin da naga kina kuka dan ance za’a yi mana Aure , zuciya ta ta kusa bugawa duk a tunanina bazakimim Amince dani a matsayin zabinki ba , please Jiddeerh ki tausayawa Uncle d’in ki ki so shi tamkar yanda yake sonki please Yan matana ”

 

 

Sai ga Abdallah tsugune agaban Jiddeerh yana Rokonta Akan tasoshi , kamar ba Abdallah da mata suke rububi akansa ba , kamar ba Abdallah da Amila take zubar da hawaye akansa ba , wai yau shine tsugune agaban mace macan ma yar kauye kamar Jiddo, uhmm so kenan.

 

 

Hawaye kawai Jiddeerh take ganin dakuma jin kalaman da Uncle dinta yake furta mata, itama idan tace bata sonsa to tabbas ta zalunci zuciyar ta, saboda ta dad’e da kamuwa da soyayyar Aljaninta.

 

Da wani irin sauri ta rungume shi tana mai fashewa da kukan farin ciki, sauke ajiyar zuciya yayi yana mai wake matse ta ajikinsa , kamar wani ne zai kwace masa ita .

 

 

Cikin kuka Jiddeerh tafara magana ” I really luv you Uncle nima ina matuk’ar kaunarka , tun ina karama da soyayyar Aljanina na taso, idan na gayawa mero saie Tamin dariya tace aljanine ya Aure ni , nikuma nasan ba wani Aljanin da ya Aure ni , Uncle nima ranar dana ganka banyi barci ba saboda muryanka sak irin tasa,dana rufe idanuna hoton kyakkyawar fuskarka nake gani haka na kwana ina tunaninka , Uncle ina sonka nima “.

 

 

Ta fad’a tana mai sake shigewa jikinsa , fes yake jin zuciyarsa saboda ya fitar da abunda yake hanasa sukuni , gashi kuma Jiddeerh ta dad’a tabbatar masa da soyayyar ta .

 

 

D’aukar ta yayi suka wuce bayi suka d’auro alwala da brush kana ya jasu suka gabatar da na nafilar da na Annabinmu ya koyar damu .

 

 

Bayan sun idar ya dafa kanta yana kwararo Addu’a , kana yayi mata tambayoyi ,inda ta amsa ba ko cin gyara , hamdala yayiwa Allah daya mallaka masa Jiddeerh A matsayin mata , ganin yanda take Hamma yasa ya d’auke yakwantar Akan gadon , rage mata kayana jikinta yayi yasa mata na barci , gabaki d’aya kunya ta rufeta , motsi kasayi tayi saboda sam baya san gardama.

 

 

A wanna dare sai da Abdallah ya nunawa Jiddeerh tsan-tsar soyayyar daya ke mata , yabata kulawa sosai , wanda dakansa ya yayi Mata wanka ya bata maganin zazzabi, da kyar ya samu yaje sallar Asuba saboda zazzabi daya rufeshi shima , yana dawowa yasake janta jikinsa dandanan barci ya daukesu , basu suka farka ba sai kusan karfe goma .

 

 

Ita ce ta fara bud’e idanunta basu shige ko ina ba sai cikin nasa idanun dasuke a lumshe , kallonsa take tamkar wani farin wata , bud’e nasa idon yayi yana mai cewa ” morning princess”.

 

 

Saurin d’auke nata idon tayi saboda matsananciyar kunyar data kamata , saboda tuno abunda yashiga tsakanin ta dashi jiya , dasauri tata shi zata gudu yayi saurin cafkota.

 

 

Fad’owa jikinsa tayi a hankali yashiga rada mata wani abu a kunenta ,gani nayi ta tun tsure da dariya tana mai turesha kana ta ce ” a’a Uncle ni wallahi ban yarda ba ” ta fad’a cike da Shagwab’a .

 

 

Shagala yayi da kallonta kana ya sunkuceta yayi toilet da ita , a tare sukayi wanka kana ya nadota a towel , bai direta a ko inaba sai akan mirror shine ya shiryata cikin wani d’an Ubansun leshi din kin riga da siket ba karamin kyau kayan sukayi mata ba sai ta fito a Amaryar ta tsaf , D’aura dankwalinta tayi ganin ya kasa D’aura mata .

 

 

 

Cewa yayi itama sai ta shirya shi , ba yanda ta iya haka ta shiryashi cikin wani rantsatstsan yadi irin leshin jikinta, tsaf suka fito sai kamshi suke bazawa .

 

 

Shine ya taya ta suka gyara gidan tsaf , sai mamaki take yanda Uncle ke da saukin kai , sha d’aya dai -dai su Auta suka kawo musu breakfast, in da suka ce sun zo basu tashi ba.

 

 

 

Bayan sunyi breakfast din inda Abdallah bai ji kunyar kannensa ba haka ya dinga nunawa matarsa kulawa , su Auta kuwa sai kallon kallo suke .

 

 

Bayan sun gama ya wuce cikin gida yace bari yaje ya dawo , addu’a tayi masa kana ta dawo wajensau Auta , inda suke tayi mata tsiya .

 

Ita dai sai dai tayi murmushi kawai amma sam taki kulasu saboda tasan Auta kad’an take jira .

 

 

Wuni sukayi suna shira a tare suka had’a Abincin rana ,sai kusan biyar sukayi mata sallama suka tafi , in da mero tace gobe zasu wuce da wuri dan haka sukayi sallama tana mai cukasu da goma ta arziki.

 

 

Haka dai rayuwa tayi ta tafiya inda Abdallah yake matuk’ar nuna mata kulawa da tsan-tsar soyayyar dayake gwada mata , itama ba’a barta abayaba wajen kula dashi da jure duk wasu bukatunsa , suna matuk’ar kaunar junansu inda ba karamin farin ciki iyayensu sukayi da hakan ba.

 

 

 

Watansu guda da Aure Allah ya Azurtasu da samun juna biyu , zo kuga murna awajen wannan Ahali ta ko ina samun kulawa Jiddeerh take , bama kamar Abdallah da ko wajen aiki sai tayi masa da gaske yake tafiya, kafin ya dawo kuwa Sai ya kirata kusan sau goma , cikinta yana wata biyar akayi Auran su Auta da Aunty Maryam, ya Khalid kuwa ya dage akan Mero yake so,sai dai muce Allah yabasu zaman lafiya.

 

 

B’angaren Amila kuwa ta rame ta kanjale , saboda duka yan uwa sun gujeta gashi an koreta daga asibiti bayan ta haifi yarta mace tace ga garinku nan .

 

 

 

Wata mahaukaciya na hango akan wata bola ga tulin tsummo kara a gabanta , sai surutu take tana cin kayan dattin bola, koda nasake kallon ta da kyau sai nafa Inna Habi , oh rayuwa kenan koya yayi da kyau zaiga da kyau Allah yasa mufi karfin zuciyar mu.

 

 

 

Cikin Jiddeerh na shiga wata tara ta haifo yaranta yam biyu mace da namiji, murna a wajen Family nan ba’a cewa komai , Jiddeerh taga gata sosai awaje yan uwa da abokan Arziki , in da ranar suna yara suka ci sunan , Abban Jiddo da Ummi , in da ake kiransu da , Ayyan da Ayana.

 

 

 

Bayan suna Jiddeerh ce ta shiga d’akin Abdallah hanunta d’auke da Ya Ayyan bayan ta kuma Ayana ce , inda taci gayu sai baza kamshi take .

 

 

 

Kwance yake ya lumshe kyawawan idanunsa kamar mai barci jin kamshin turaran ta yasashi bud’e ido , ganinta yayi tana kwantar da yaran akan d’an gadonsu kana ta nufoshi tana mai sakar masa wani killer smile, bud’e mata hanunsa yayi , ai kuwa kamar jira take ta shige jikinsa suna mai saki n ajiyar zuciya a tare da ba k’aramin kewar juna sukayi ba , sake rungume ta yayi yana mai cewa ” yau zamu samu little twins kenan ” zaro manyan idanunta tayi tana mai turo masa su ,aikuwa da sauri ya cafki bakinta yana mai sakar mata da wani irin kiss mai matuk’ar tafiya da zuciya …

 

 

 

 

TAMMAT BI HAMDILLAH anan nakawo karshen wannan littafi nawa ,kuskuren dayake ciki Allah kayafemin , Allah yasa mu Ammfana da darussan dasuke cike , subahanakallahumma wabihamdika ashhadu Alla ilaha illa Anta astagafurka wana tubu Ilaik.

 

 

Sai mun had’u a sabin book Dina kamar Haka

 

 

BAKON ZUCIYA

 

 

 

BADAN INA SO BA

 

 

 

FADEELAH KHAN CE

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment