Littafan Hausa Novels

Zan Jiraka Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Zan Jiraka Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ZANJIRAKA

 

 

 

 

 

 

 

Story&writting by

Eesha Alkali

(Mrs aysib)

 

 

 

 

 

Hmmm fans kuna ina nace kuna ina tofah na dawo muku tsaf da zafina.

Labarine wanda ya kunshi matsananciyar soyayya cin amana yaudara da son kai

Soyayya ce mai zafin gaske

 

 

 

 

 

Duk Mai bukatar tallata mata hajarta zata iya tuntubata ta wannan number domin karin bayani masoyana kuma zaku iya ajemin Dm amma game da littafina nagode sosai da nuna kaunarku gareni

 

 

 

 

*Ku kasance da alkalamina ✍🏻✏️domin samun dadadan littafaina ina godiya masoyana*

 

 

 

*HAPPY NEW YEAR 2024 FANS*

*Allah yabamu alkhairin da ke cikinta sharrinta kuma yakaremu dashi*

 

 

 

Bismillahi Rahmanir Raheem

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai

Yadda nafara wannan littafi lpy Ubangiji ina rokonka da kasa nagamashi lpy ✍🏻🤲🏻🙏🏻

 

 

 

 

 

 

 

Page 1️⃣&2️⃣

 

 

 

 

 

—————Yara na hango gurin wata katuwar bishiyar lim sun zagaye mutum wanda hakan yasa bana iya hango komai’ kasancewar bansan mey ke faruwaba kuma inaso na dauko muku rahoto yasa na matsa matsa kusa dan ganin mey ke faruwa.

 

 

Koda nakarasa wata yarinya na hango tsakiyarsu daga gani kasan itace boss dissu, waka suke mata itako sai kwasar rawarta take , suna cikin wannan shirmen nasune wata kawarta ta karaso da gudu cikin filin “Noor kizo inna na nemanki wai zata aikeki bakin kasuwa tace kiyi sauri “

Haushi ne yakama wannan yarinyar da aka kira ta juyo kamar wata zakanya tayo kan kawarnan tata “indo banace kifita harkataba ke matsalata dake munafuka ceh nasan ke kika gayamata ina gurin party shine takeso nabari nadawo gida “

“Wlh tallahi Noor bani bace kawai najene naga ko kinan muyi wasa ashe kinzo nan “ takarasa maganar kamar tayi kuka

“Tau shikenan muje amma wlh mukaje na tarar da kece kika fada mata wani abu wlh saina maki dukan tsiya “ tafada kamar wata mai karfi.

 

Me Debe Kewa Hausa Novel Complete

Koda suka isa gidan Inna na tsaye da dari biyu a hannunta tana jiran shigowarsu Noor d indo “Assalamu Alaikum “ suka fada gaba dayansu kamar munafukai “Nikuwa nagaa lokacin da zaku girma tundazu na aika kiranki dake da yar aiken kunkoma kunyi zamanku Ni kuzo kuwuce kumuna cefane dare nayi “ kudin Noor ya karba ta juya “injin ke kadai zakije?” “Uhm uhm indo muje” “saura kukoma kuyi zamanku wlh sai ranku ya baci “ tajuya ta shige dan madaidaicin dakinsu.

 

 

Inda Allah ya rufa musu asiri sunada gidan kansu da basusan yanda rayuwa zata zo musu ba ,gashi Allah ya azurtata ta da yarinya mara jin magana, Noor farace tass yanayin wahalar da suke ciki ne ya kodeta takoma chocolate color.

 

 

Suna tafiya Noor tace da indo “wai Bala’ayi miki fada a gidaba?”

Murmushin karfin hali indo tayi tace “Noor ynx haka zuwan da nayi gidanku wlh sbd wata magana ne amma kinki ki saurareni!”

Takarasa maganar cikin raunin zuciya .

 

Cikin natsuwa da ba kullum Noor take fidda taba ta kalli indo tace “indo wani lokacin akwai bukatar ka maida kanka wawa acikin mutane nan da kike ganina ina sane da komai dake faruwa dake , nakanji inama inada halin fiddaki acikin wannan azabar amma indo ba hali duka duka shekarunmmu sha uku ne amma har cikin kauye anfara wai har yanzu babu mashin shini amma gara Ni da ake ma kallon karamar yarinya sama dake,nima jiya naji batun aurenki wurin innarsu walida kinsan ba shiri muke dasuba.”

 

 

“Noor banason auren nan “

Tafada hawaye na bin kumatunta

Tsaida tafiyar da suke Noor tayi tace

Indo in sha Allah bazaki wulakantaba na rasa mahaifi kin rasa mahaifiya amma karki damu komai mai wucewane inada tabbacin auwalu zai kula dake dan dama yana sonki kece kike tsoron kulashi sbd iya “

 

Goge hawayen fuskarta tayi tace “nagode Noor da shawarki in sha Allah zan fawwalawa Allah komai” haka suka suka cigaba da tattaunawarsu kamar wasu manyan muatane dan Noor sosai take karantar rayuwa kuma take karbarta duk yadda tazo mata, sun gama cefanensu suka kama hanyar komawa gida auwalu ya tare su a hanya cikin jin zafin taresu da akayi yasa a harzuke Noor tayo kanshi indo ce tace Noor auwalu ne dan lokacin idanun Noor rufewa yayi kan masifa,”kaga malam bawai dan anbaka indo zaka rika taremu a kan titiba kabari intaje gida ka isketa acan “murmushi auwalu yayi dan yasan za’a rina “yauwa gimbiya sarautar mata ayi hakuri wlh bada wata manufa nayiba” yadda yake maganar kamar karamin yaro ne ya ba Noor da indo dariya “tau malam auwalu ango bari na baku wuri kuma kuyi sauri dan Inna na jiranmmu “tafada tareda komawa gefe “dama indo akan maganar auren mu ce shine innata tace nasameki sbd bataso adau hakkin maraya shin kin amince zaki aureni?”

Cikin jin kunya da son auwalu a dankare aranta ya juya da gudu da tafi gurin Noor datake nesa kadan dasu.

 

 

“Harkun gama maganar?”

“Nidai muje tafada cikin yarinta murmushi kawai Noor tayi suka tafi “

 

Koda suka karasa jiki a sanyaye Noor tabama Inna ledar dan tun a kofar gida indo tace tayi gida duk da tasan duka kam yau saita shashi.

 

 

Inna na lura da yanayin Noor amma batace mata kalaba dan Noor yarinya ce wacce bata boyon abinda ke ranta tasan zata fada mata koma menene.

 

 

Daki Noor ya fada sai kuka

“Inasonka wlh inason ka sosai bansan yaushe tayaya a ina wani lokaci bane nidai inasonka haka take kuka kamar ranta zaifita ji take kamar dutse mai nauyi aka aza mata akan zuciyarta,saida taci kukanta mai isarta sannan ta share hawayenta tafito daga dakin,kofar gida ta nufa zata fita tajiyo muryar inna tana magana “Noor ina zakije da mangariba haka?”

 

“Inna zanje gurin Ummie ne “

 

“Tau shikenan karki tsaya wasa Noor kinsan banason hayaniya balle wannan kauyen da aka sakamiki ido ki kama kanki kinji Noor dita kuma Allah ya kawo miki miji nagari kiyi aurenki ki huta “

“hmmm Inna kenan inkika san mey nakeji akansa saikin ce nahaukace “

Cikin zuciyarta take wannan tunanin “maza jeki karkiyi dare dan nasan halinku keda Ummienki “

Murmushi Noor tasakar ma mahaifiyarta kallonta Inna ta tsaya yi dan ita kanta tana yaba irin kyaun da Allah yayima Noor

Noor farace sosai tanada jiki madaidaici dan a iya shekarunta baici ace tanada wannan girmanba shiyasa Inna koda yaushe take taka tsantsan da tarbiyar yarta, duk da Allah ka tsaro gara kasa ido sosai shiyasa ta maida yar’ta kamar abokiyar shawarta amma duk da haka bata bari ta raina taba.

 

 

 

 

 

—Page 3️⃣&4️⃣

 

 

 

*Waiwaye kadan*

 

 

 

 

————-Noor ta kasance marainiya ceh mahaifinta ya rasu tun Inna nada ciki wato mahaifiyar Noor, Dangin mahaifinta ba yadda basuyiba akan abusu ita amma Inna firrr tace ita zata rike yar’ta da hannunta a daliln haka sukace babusu babu Noor dama mahaifinta bawata dukiya ya bariba balle su kula dasu haka kuwa akayi Inna tacigaba da rainon yar’ta Noor, itake fita tayi surfe ko wanki abiyata sannan su samu abinda zasuci cikin ikon Allah,Allah yahadasu da Ummie a wani gidan kara da yake bayansu jininsu ya hadu sosai haddai Noor da kowa natane ba ruwanta.

Noor batasan Ummie nada babban da’ba sbd lokacin ba komai take ganewaba ,ana haka Inna tace da Ummie mey zai hana taso bayan garin ta dawo cikin mutane haka ko akayi Ummie tadawo cikin garin ya kasance gida uku ne tsakaninsu .

 

Haka rayuwa tayi ta tafiyar musu yau da dadi gobe babu ita dai Noor batasan da wata damuwaba sbd lokacin tana yar shekara daya ba abinda ke damunta.

 

Noor batajin magana a kauyensu kowa yasan da haka shiyasa ba mai shiga shirginta tayi zage zagenta bamai kulata balle yajawa kansa zagi inda Allah ya gyara sosai Allah yasa mata tsoron Innar tata ,duk jaye jayen da take bata yadda akawo kararta gida,ahaka take sula tsiyarta.

 

 

Wata rana Noor na dambe bakin gidansu indo kawarta saiga wani matashin yaro da jakarsa ta goyo inka ganshi zaka rantse da Allah bature ne gashi fari ya tara saje a fuskarshi, jikinshi madaidaici dan bazai wuce shekaru 18 a duniyaba ita kuma a lokacin tanada shekara tara a duniya .

 

 

 

Cikin mamaki ya karaso gurinsu ganinsa baisa Noor ta daina zage-zagen da takeba saima karawar da tayi, hakan kuwa ba karamin batama wannan matashin saurayin rai yayi ba,bulala ya gani gefensu kasa yaje ya dauko batare da Noor ta ankaraba,taji saukan tsuma a bayanta haka take dira tana faduwa tana ihu tun tana iya kuka da muryarta har saida muryarta ta dishi sannan ya barta dan inba haka yayi mataba yaga alamar kanta na rawa, “mey ya hadaku” cikin cool voice dinsa Mai dadin sauraro ya fada kamar ana masa dole dan miskilin kwarai ne.

 

 

Nan aka zaiyane masa komai mamaki ya cikashi irin karfin halin wannan yarinyar fadan ma banata bane wacce akama ta hakura amma ita sai masifa take nan dai ya raba fadan sannan ya wucewarsa ko kallon Noor bai sakeyi ba ,ita kuma malama Noor tsoron shi ne falll aranta bata tana gamuwa da wanda yamata kwarjini ba kamar wannan baturen a cewarta.

 

Kowa yaji mamakin Noor sbd duk akayimata saita rama bata bada bashi balle wannan dukan da yayi mata,Noor kuwa data sha jinin jikinta ta tashi tsaye cikin dakiya ta kalli kowa dake wurin yana jiran jin rashin mutuncin da zata tafka masa “tau munafukai sai a watse kuma wlh karkuga ya dakan bance masa komai ba wlh saina dau fansar abinda yayi min da kuna fama da kai kamar kwallon goriba mitttttss”. Taja tsaki tare da juyawa tabar gurin kowa a zuciyarshi tunanin yazata kaya tsakanin Noor da wannan baturen lol 😂 inji Malama Noor.

 

 

Akace laifin dadi karewa saimu hadu a next page domin jin yazata kaya

 

Shin wanene wannan baturen?

Waye wanda Noor keyima matsananciyar soyayya 🤔?

Ina jarumin littafin?

 

Ku shirya wannan tafiyar Dan nasan zata nishadantar da ku masoyana

 

 

Taku har kullum Mrs aysib

 

 

Comment and share my people

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment