Littafan Hausa Novels

Zakisan Koni Waye Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Zakisan Koni Waye Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

ZAKISAN KONI WAYE

 

®zuwairat(ummu maryam)

1⃣

 

Ahamdulillah. Ya rabbi ya amshi ibadunmu. Happy sallah to all muslims.

 

Ban yarda wata ko wani ya maida wannan novel din document ba saida izinina.

 

Wata babe ce zaune cikin wani katafare falo wanda girmanta zai yi 100by100, fadin tsarin falon is a waste of time amman kuyi imagining kyawun falon masu hannu da shuni, budurwan sai kada kafa take da alaman ba gidan ta bane, kaman mai gidan take jira. Wasu hadaddun designer english wears ne jikinta, sai kamshi take, da ganin ta kaga wayayyun babe masu aji.

Alkawarin Allah Hausa Novel Complete

Bayan kaman minti talatin aka bude kofa, wata kyakyawa babe ta shigo, aikam afusace wacce ke zaune afalon tamike fuskanta daure, ta nuna wacce ta shigo da dan yatsa sannan tace

“wato mimi baki ji ko..” bata karasa ba wacce aka kira da mimi ta tuntsure da dariya sanna tace

“ke uban wacece da zaki nuna ni da dan yatsa…ko kin manta ni fina na fiki tunda ubana ba hannun efcc yakeba..banza karuwa..” bata karasaba taji saukan mari

“dan uwarki ni mate dinkice dazaki gayamin magana?…sau nawa nake gaya maki ki rabu da slim…

.” itama bata karasaba aka dauke ta da mari

“ke har kin isa ki rabani da slim..uban wa ke baisan ke kike binshiba?..kuma kowa yasan duk big boys din abujan nan ke kadai ke binsu …kariya” haba nan suka shake junasu.

 

Sunfi minti biyar suna dukan junansu at the same time suna gayawa junansu bakaken magagganu. Ni kam mamaki nake wanene wannan guy din da kyawawa yanmata ke dukan junansu sabodashi. Fina rike gashin mimi tayi da niyyan janta waje amman weavon din dake kanta ya cire, afusace mimi ta juyo tare da cire designer shoe din dake kafanta ta wullawa fina, da sauri ta kauce ya sami wani katon canema dake jikin bango nan take ta tsage. Itama fina cire nata takamin tayi ta wullawa mimi itama ta kauce ya sami wasu glass decor dake kan dinning nan take suma sauka tarwase, dukkansu babu wacce ta kalli barnan datayi suka cigaba da fadansu fina na cewa

“wallahi bari slim ya dawo….yau sai ya zaba tsakanina dake..” mimi da kanta babu wani gashin kirki kuma fina ta cire karin datayi ta rike a hannunta gam, mimi sai kokarin amsan brazilian hair dinta take tana cewa

“dalla bani weavon dina, don kudinta ya fi karfinki….”

“bazan badaba..ki tsaya ahaka har slim ya dawo ya ga kwalkwalin kanki”. Itama mimi kaman kan fina tayi ta fixge nata karin gashin. Nan take itama kanta ya bayyana. Dukkansu biyu babu mai gashin kirkin amman kansu kyare suke . Da weavon mai suna brazilian hair wanda kudinta yakai 600k suke amfani. Kowannesu klokarin amsan karin gashinta take.

 

Afarfajiyan gidan wani katafaren gate ya bude, wasu manyan motoci kiran bentley guda uku suka shigo gidan, wurin parking suka nufa, suna gama parking da sauri wasu guys guda uku suka fito daga cikin motan gaban at the same time guys biyu suka fito daga cikin motan baya suka nufi motan tsikiya, ahankali daya daga cikin guys din ya bude murfin motan tsakiya. Wani hadadden kafa nagani sannan mai kafan ya fito, wooooow, kawai nace don fina da mimi basuyi laifiba da suke cin abun junansu sabodashi, don guy din tamkar shi ya hallici kanshi, wani suitmai tsada ne kwance jikinshi , ahankali ya mika hannu ya amshi briefcase din dake hannun daya daga cikin guards dinshi sannan ya sakar masu murmushiai bayyana hakora, wow nasake cewa don wasu fararen hakora nagani tare da wushirya tsakiyansu. Nikam ban taba ganin mutum mai kyau har cikin hakoraba don komai nashi wonderful

“alhajis na gode” naji yace, nikam wooow na kara cewa don muryanshi so cool and gentle. Suma guys din murmushi suka sakar mashi, juyawa yayi yafara tafiya, yana daga kai yaga wani range rover sport tare da hummer tsaye, nan take ya hada giran kasa dana sama, don yasan masu motocin. Girman gidan yayi hecter daya, da akwai manyan flat a farfajiyan gidan, amman wanda yafisu girma ya nufa, su kuma guys din sukayi wani bangare daban.

 

Yana zuwa bakin kofan falonshi ya taddata bude, afusace ya shiga falon, adaidai lokacin da su mimi da fina sukayi wa karin gashinsu kacakaca a falon, suna ganin shi kowa yasha jinin jikinshi

“kam babban burouban nan!!!!! ” saurayin ya fada a fusace, wanda yasani rasana don yanda yayi magana sai ya firgita duk wanda ke saurarenshi, yacigaba dacewa

“who the fuck gave you bitchies permission to enter my house? ” dukansu shuru sukayi, ahankali mimi tace

“slim ni kake kira bitch? ” ta fada tana nuna kanta, a fusace yace

“aa sugar badake nakeba da uwarki nake… I said uban waye ya bude maku falona? ” fina na gani ya watsawa mimi bakar magana ta saki murmushi tare da nufoshi tana cewa

” habibi welcome ” harara ya watsa mata tare dacewa

“gidan ubanki nazo? Banza yayan barayi” itama fina cewa tayi

“are referring to me” dan girgiza kanshi yayi sannan yace “da lankwaceccen ubanki nake… Bazaku gayamin ubanda ya baku izinin shigowa gidanaba kafin insa guys dina suci uban da ya haifeku? ” fina tace

“ni na bude”

“who gave you my password? ” ya kara daka mata tsawa

“last weekend da mukazo b day dinka na rike passwords din… Kasan am smart ”

“kika rike passwords dina don in bana nan kizo kiyimin sata ko” ido mimi ta bude

“sata kuma slim… Ni kake cima mutunci haka? ”

“eh mana… Ba sata ubanki yayi efcc suka kamashiba? Nasan ko kin gada?” fina bata kara cewa komaiba ta koma baya, takalminta ta dauka da niyyan sakawa, itama mimi designer hand bag dinta ta dauka, ajiye briefcase dinshi yayi gefen inda yake tsaye tare da harde hannuwanshi kan kirjinshi yan kallon yanda fina ta duka ta saka takalminta, mimi zuwa tayi zata wuceshi, ya fixgeta tare da wullata cikin falon

“where did you think you are going?… Ubanwa kuka barwa gashin doki chan” ya nuna weavon din dake sakar falon sannan ya kara cewa

“in kun bar gidan nan sai kun gama gyaramun falona… Banzaye second hand bitchies” irin fixgan da yayiwa mimi yasa batayi gardamaba ta koma tafara kwace karin gashinta tare da maida tro pillows din da suka wullawa junansu. Magananshi kara batawa fina rai yayi, bata kalleshiba tazo zata wuce inda yake, wani irin damka yayi mata tare da turata baya

“safina kina son nuna min taurin kai ko?… To wallahi in baki gyaramin falonaba dukan tsiya zansa ayi miki kuma kisan nothing will happen ” murtuke fuska tayi kafin tace

” gaskiya ko agidanmu ban aiki so yanzu ma bazanyiba” wani irin dariyan rainin hankali yayi wanda ya kara bayyana kyauwunshi

“ai yarinya kwanda ki fara koya don satan da ubanki minister yayi aka kamashi…bailing shi zai maidaku matsiyata…” bai karasaba ta yaji tace

“dadin abun ba ubanmu kowai ke barawon government ba…. ” dauketa yayi da mari.

” kio ubanki baya magana in inayi balleke….” bai karasaba ya daga kai yaga cinema dinshi fashe, wani ashar ya kara saki sannan yace

” wacece ta fasamin plasma! ” ya fada afusace, fuskan fina murtuke tace

” nice ko abiyakane….tunda kasan ba matsiyaciya bace”

“abinda ya zama dolema..ai comfirm sai kin sa an kawo zaki bar gidan nan” batace kara cewa komaiba ta kira bodyguard dinta dake waje ta sanar dashi yayi amfani da ATM dake hannunshi ya sayo mata the largest plasma.

 

Fina kallon mimi dake tsaye tayi sannan tace

“malama kema ki kisa akawo mashi glass decor dinshi” sai lokacin slim. Ya kalli wurin dinning dinshi yaga barna da sukayi mashi, still cewa yayi sai mimi ta biyashi, itama bodyguard dinta takira yazo. Ciki ta bashi ATM dinta tare da nuna mashi abinda zai sayo.

 

Har lokacin salem bai bar inda yake tsayeba, mimi da fina zuwa sukayi zasu wuce ta inda yake, rike masu hannu yayi tare da kallon fuskan ko waccensu sannan yace

“meyasa kuke fada sabodani? ” dukkansu babu wacce tace komaiba, yacigaba dacewa

” ko dan kudi da neman connection?” ahankali mimi tace

” haba slim why are you saying this.. Kasan ni badan wani abu naka nakesonka… ” itama fina cewa tayi

“kaima kasan i love you” dan tabe baki yayi don yasan karya suke

” naji…amman kuna iya fada saboda security ko wani mara hali? ” dukansu shuru sukayi sannan yakara cewa

“.kuna iya bin mai gadin gidanku gidanshi?…” kaman hadin baki sukace

” i love you!! ” suka juya tare dawullawa junasu harara, shi abinma dariya ya bashi

” naji…muje bedroom dina in nuna maku wani abu” su biyu kallionshi sukayi alaman yana son kwanciya dasu lokaci. Babu kunya fina tace

“gaskiya slim i can’t share you with her” ta fada tana nuna mimi, shidai baice komai ba yacigaba da tafiya dasu har bakin wani katon kofa, daidai wani scanner dake jikin bango ya tsaya tare da dukawa, abun yayi scanning idonshi, nan take kofan yayi sliding gafe daya sanna ya shiga rike da hannun ko waccensu.

 

[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ♥

ZAKISAN KONI WAYE

®zuwaira(ummu maryam)

2⃣

Suna shiga dukansu suka bude baki don tunda suke basu tabha ganin bedroom mai girma da kyau irin nashibha don ana iya gina katon three bedroom flat da filin bedroom dinshi. Sakin hannunsu yayi ya shiga bathroom dinshi ya daure alwallah ya fice daga dakin ba tare daya kallesuba

Bayan sun dawo daga daga masjid direct inda cook ya shirya masu dinner kan carpet suka wuce. Suna cin abinci suna hira, inkazo wurin baka gane waye oga don sai dariya suke.

Around 8pm suka gama dinner still masjid suka koma don sallan ishai. Shidai salem kullum bashi da aduan da yawuce Allah ya bashi mata tagari.

 

Suna dawowa suka zauna tsakar gidan wanda ke da haske tamkar rana. Su shida ne tare da salem su bakwai. Hira suke suna daria, bayan kaman minti 30 daya daga cikin guard dinshi mai suna Jibril yace

“sir in babu abinda zanyi maka ni zan tafi wurin madam,,” dukkansu daria sukayi

“kaji masu iyali” inji daya daga cikinsu mai suna abdul.

“ai sunji dadinsu…inama ni” inji Salem, dukkamsu kallonshi sukayi sanna Jibril yace

“sir ai kai ke bakason auren..don don nasan ko mata hudu kakeso kana iya aurensu rana daya…tunda ga naira ga kudi” dan tabe baki Salem yayi sannan yace

” ai abinda bana so kenan…so nake in aure macen da zata soni don allah ba don connection ko kudinaba” dan daria sukayi sannan daya daga cikinsu mai suna majid yace

“ai sir da wahala ka gane macen dake sonka don Allah yanzu tunda ko wacce mace pretending zatayi tana sonka don abin hannunka”

“kaji problem din” ya fada sannan ya kalli Jibril

” alh Jibril yaushe ka auri matanka” yace mashi don haka yake kiransu ALH kasancewan dukkansu sunje hajj a sanadiyanshi. Ahankali Jibril yace

“Yanzu shekaranmu biyar da aure…dukda dai nasan mata kudi sukeso gaskiya sir banda matata… Don sanda mukayi aure teaching nake a private school kuma albashina 15k.. ” bai gamaba Salem ya kwalo ido waje tare dacewa

“alh Jibril 15k fa kace?:” ya fada with disbelieving voice ” daga mashi kai Jibril yayi tare dacewa

“yes sir.. ” da sauri salem ya sake cewa

“ya mutum zai yi surviving da 15k balle har da mata? ” dan murmushi Jibril yayi sannan yace

“sir shi yasa nace matata is different don a wannan lokacin ita ke karfafa mani gwaiwa…wallahi sir da akwai lokacin da zamu kwana babu abincin kirki…amman she stands beside me with love” duk jikin Salem da sauran guys din yayi sanyi, ahankali Salem yace

“inama ni.. ” da sauri Jibril ya katseshi dacewa

“sir kar kayi fatan shan wahalan da ni da matata muka sha” ahankali Salem yace

“but you have true love..and it’s among what matters most in life…i wish ina iya samu macen da zata soni.. I can do anything for true love..don gaskiya ban iya aure sai na sami true love ” dukkan guys din shuru sukayi suna tunanin maganan ogansu.

 

Few seconds later abdul yace

“sir kaman yanda majid yace da kyar ka gane mai sonka, don ina tabbatar maka babu macen dazata ki ka” yadan tsaya sannan yacigaba dacewa

“sir tunda kana neman true love… Ina da shawara… ” dukkansu harda Salem suka maida hankalinsu kan abdul

“am all ears” Salem ya fada mashi. Abdul shiru yayi ya kasa magana, don yasan Salem baya daukan rubbish,

“kaifa nake jira… ” Salem ya sake cewa. Shuru Abdul yayi for a while sannan yace

“sir abar maganan kawai” don yana tsoron abinda zai faru in har ya fadi abinda yayi niyya

“ai baka isaba… Am listening ” Salem ya ce mashi.

Sadakarwa Abdul yayi yafara cewa

“sir.. Da cewa nayi why not ka dan maida kanka talaka for a while…. ” darian guys din ya hanashi karasa abinda zaice, shi kam salem kallon Abdul yake ba kiftawa, daga kai yayi ya kalli guys din, nan take sukayi shuru sannnan ya kara maida kanshi wurin ABDUL din da yayi tsuru2 sannan yace

“alh Abdul taya zan maida kaina talaka bayan ni ba talakan bane… Please explain your self ” ahankali Abdul ya ce

“sir..ina nufin kayi disguising kanka… I mean kana iya maida kanka taxi driver….” wani irin dariya dukkansu suka sakeyi, banda Salem daya hada giran sama dana kasa, a hankali ya mike ya taka zuwa gaban Abdul sannan ya dafa gaban goshinshi don tabbatar ba zazzabi yakeba. Jiya yayi temperature dinshi normal, shi kam Abdul gabanshi sai disco yake.

 

Salem bai ce komaiba ya wuce side dinshi. Dukkan guys din kallon Abdul sukayi suna cewa

“you fucked up… Yanzu kasa ran sir ya baci…”

Salem kam tunani yake ya sakar wa bodyguard dinshi jiki da yawa tunda abun ya fara kawo raini tsakaninsu…

“wai ni taxi driver…hmmm i will treat your fuckup” ya fada yana bude kofan falonshi, yana shiga agogon hannjunshi ya fara ringing cos waya ce, dan murmushi yayi kasancewan yasan mai kiran don wakan sweet mother ne kawai ke tashi daga agogon hannunshi, ahankali ya yi picking tare dacewa

“good evening first love… ” bai karasaba naji wata irin sweet mature female voice tana cewa

“son ka rainani ko?.. ” da sauri yace

“first love kiyi hakuri…” matan ta katseshi da cewa

“keep quiet silly child…kullum am sorry.. Yanzu where are you?” Salem kan kujera ya zauna yana shafa kanshi irin na mara gaskiya sannan yace

“first love ina ABUJA.. ”

” me ka gayamin da safe? “” matan ta tambayeshi, ahankali yace

” umma cewa nayi zanzo yola yau… ”

“to yanzu a yola kake? ” matan ta sake tambayanshi, dan girgisza kanshi yayi sannan yace

“no… Umma sai karfe eight na tashi daga off… ”

“yimin shuru makaryaci… Nasanj dalilin dayasa bakason zuwa…don’t worry zansa abbanka ya zaba maka mata cikin family ko cikin yayan friends dinshi…. ” sanin halin ummanshi yasa shi saurin cewa

“wayyo Allah first love kiyi hakuri na kusa kawo mata…please don’t talk to abbah.. ” ahankali matan tafara cewa

“love why are you treating me like this?… Ko don ka san you are my only son?…sisters dinka suna chan gidan mazajensu kai kuma bazaka kawo min yarinyaba?… ”

“first love give me a little more time… Inshort ki bani maximum of five months… In ban kawo mataba ki auramin kuturuwa…” darian ummanshi ya katseshi , shima murmushi yayi

“habibi ka maidani kakanka ko..”

“no first love am serious.. Kibani wata biyar kawai…kinji please ”

“naji..amman let your five months be five months..” da sauri yace

“yes umma” dan hira sukayi for about 20 minutes sannan sukayi sallama. Dan ajiyan zuciya ya saki sannan yace

“atleast zan dan huta da fadan mom na wata biyar… ” relaxing yayi yana lumshe ido ahankali yana tunanin ya Allah kabani mata and she will be the luckiest girl.

[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ♥

ZAKISAN KONI WAYE

®zuwairat(ummu maryam)

 

3⃣

 

Su mimi suna ganin ya fita suka kalli junansu sannan suka fara kallon dakin, komai na dakin golden color ne, wani irin makeken gado ne a tsakiyan dakin wanda ke kamada baa kwanvciya samanshi don komai very neat, mimi dan matsawa tayi kusa da dressing mirror taga kayan shafa kaman da mace don ko a mata sai masu hali zasu iya siyan irin kayan shafanshi cos ko su da suke yayan minister basu da yawan kayan shafanshi, perfume kam tamkar nan ake saidasu, itakam fina wani kiofa da aka rubuta my wardrobe ta bude sai taga dakine amman abin mamaki duk girman wurin suturanshi ne shake da wurin, suit sunfi kala dari da hamsin kuma dukkansu designer ne like wise takalma ma basu irguwa suma yawancinsu daga companin prada ne, juyawa tayi ta kalli inda yake ajiye agogo da glass suma sunfi kala 40 suma designer, itama mimi dakin tabi fina, itama tana shiga ta bude baki

” the guy is beyond our expectations..” fina juyawa tayi ta kalli mimi tare dacewa

“ni tunda nake zuwa shopping abroad ban taba ganin boutique dake dauke da yawan designer clothes waje daya kaman na slim ba… Kalli vallantino pijamas.. Babe mu ajiye fadamu waje daya mu dangwali arziki..wallahi this guy is loaded ” murmushi mimi tayi tana tunanin ai ko a ta hudu tana iyan ajiye pride dinta ta aureshi, itama fina tunanin da take kenan don salem ya fi duk yanda take tunani, wata koface suka gani mai cikin wardrobe room din, ahankali mimi ta bude wurin, wani irin wagegen bathroom suka gani,

“shidai slim komai nashi extra large..” inji fina.

 

Girman bathroom din abin mamakine don wani katon swimming pool ne wurin sai wata plasma a tsakiyan ceiling din. Daga gefe kuma wani mirror ne wanda shake yake da bath perfume kala2 sai shower gel suma kala2 , daga dayan gefen kuma wani rank ne mai dauke da towel manya da kanana.

 

Wata kofa suka bi sai gasu a bedroom, wani fridge duka bude sai ga exotic wine amman ba mai giyaba, daya suka dauka tare da cup guda biyu, kan wani mini dinning mai dauke da kujera biyu suka kioma suka zauna suna shan wine din kiowacce tana tunanin yanda zatayi slim ya zama mallakinta.

 

Shidai salem dan tsohon shugaban kasane amman baya cikin yara masu dogara da arzikin iyayensu don yanzu shine shugaban NGO na Africa gabaki daya, shine babba agidansu sai kannenshi biyu mata wanda yansu suna gidan mazajensu.

Salem yana da kirki sosai don duk shekara sai ya biya mutane dari kudin hajj sannan yana da kungiyan tallafawa talakawa a garuruwan arewa sanna duk begger daya cikaro da slim kaman yanda friends suke ce mashi saboda yanayin jikinshi ya warke ko da a gidansu talaucin duniya ta kare. Shidai Salem yana daga cikin the most eligible bachelor da muke dasu a duniya don yan mata da suke sonshi basu irguwa amman abinda basu saniba shine babu abinda yafi damunshi kaman true love.

Bashi da babban aboki sai Khalifa dan governor na garinsu wato Adamawa, sannan ya dauki bodyguards dinshi tankar abokai don yawanshisu zasuyi shekaru daya.

Saidai wani hanzari ba guduba baya tolerating immorality don mutune mai tsanani amman in ka gane zama dashi yana da saukin kai sosai. Yanzu dai he’s 35 years old. Wanna shine short and brief history na Salem.

 

Bayan ya gama waya da ummanshi yayi relaxing, kaman an sunkuereshi ya mike yana cewa

“subhanallahi!!” donshi ya manta da su mimi a bedroom dinshi, da sauri ya kama hanyan bedroom din yana cewa

“those abuja girls with evil character.. ” yana shiga dakin ya hangesu zaune feeling at home har sun kusa shanye wine kwalba daya. Suna ganinshi suka mike tare da nufoshi, kallonsu yayi

” wai ku in dare yayi baku san hanyan gidajenkuba?” yace masu, ahankali mimi tace

“slim ba sauri mukeba..sannan ai dazun kai kace zamuyi maka wani abu ko ka manta?”wani irin kallo ya wasta mata sannan yace

“oh… Na mance,..daman inners dina naso ku wanke min… Amman tunda dare yayi ku tafi” wani irin lustful look suka dinga jefa mashi, yasan maanan kallon amman ya basar yana cewa

“kuyi sauri ku tafi… “mimi da fina kallon junansu sukayi sannan suka nufoshi. Bayanshi mimi ta tsaya, itakuma fina ta zagayo gabanshi, tsayawa takayi daf dashi don boobs dinta yana taba kirjinshi, nan take tsigan jikinshi ta tashi amman sai yayi karfin halin cewa

“meye haka… ” bai karasaba fina ta zagaya hannuwanta biyu bayan keyanshi tare da kai bakinta saitin kunnenshi sannan tace

“sli.. You can have us both… ” tafada muryanta na fita ahankali, itama mimi tafara shafa gadon bayanshi itakuma fina ta kai bakinta saitin bakinshi ta fiddo harshenta ta lasan bakinshi, nan take ya chafke bakinta yana kissing dinta kaman his life depends on it. Mimi sai shafa gefen cikinshi take, with out wasting of time ya fita hayyacinshi, hannuwanshi biyu ya zagaya kugun fina dasu, yana nishi kaman wanda yayi hour daya yana gudu.bai ankaraba yaji hannun fina kan joystick dinshi.

Nan take ya turata tare da ingiza mimi yayi sannan yayisaurin zama kan kujera, mimi da fina kallon juna sukayi sannan mimi tace

“what’s wrong Slim….” ahankali ya daga red eyes dinshi ya watsa masu disgusting look sannan yace

“you both should get out of my house ” dan murmushi fina tayi sannan tace

“common slim… Let’s have fun ” Salem lumshe idanuwanshi yayi sannan yace

“i can’t ” sake kallon juna sukayi snnan fina tace

” haba slim.. You can’t ko you won’t.. Nasan you are not impotent don yanzu na taba joystick dinka. ..” bata karasa ba ya katseta dacewa

” ban taba zina ba… Kuma bazan faraba yau. Kuma ko ina zina nafi karfin inci leftover irinku…so leave my house before I call my guard to force you out…” tsayawa sukayi suna nuna mashi boobs dinsu, afusace ya mike yana tafiya yana rike gaban jallabiyan dake jikinshi don kar suga girmanshi.

 

Wani intercom dake jikin bhango ya dannja sannan yace

“guys come and bundle those second hand bitchies fr… ” bai karasabha kowacce ta dauki hanbag dinta don a ganinsu abun kunyane suna yayan ministers asa bodyguard su fiddasu.

 

Suna fita ya tafi wajen wani cabinet ya bhude ya dauki wata magani, wajen fridge ya nufa ya dauki foreign juice yasha maganin sannan ya koma kan kujera, lumshe ido yayi yana tunanin halin matan yanzu, yanda suka koma basu da wani tunani sai na yin mugun abu saboda connection

“anya mu da bamuyi aureba zamu sami matan aure kuwa..don 99% na matan yanzu are bitchies..ya rabbi ina kara rokonka, yanda ban tabha kusanta zinabha kar kabani mata mazinaciya…ya allah yanda nake da tawakali ka bani mata mai tawakali… Ya azizu yanda nake son talakawa kabani mata waccfe zata soni don ni bha dan wani abu nawaba.. ” haka ya dinga adua kamar yanda ya saba donshi babu abinda yakeso kaman aure cos yana samun matsalan hornyness.

 

Ahankali ya mike yashiga bathroom tare dayin bubble bath sanna yafito sanye da kayan bacci. Kwanciya yayi tare da rage hasken dakin. Har ya mance da maganan da Abdul ya fada mashi.

 

Around 3am yayi firgit ya tashi da adua bakinshi da alaman mafarki yayi, ji nayi yana cewa

“ya Allah ka sauwake wannan mafarkin… Me taxi driver… Kuma ina kuka…” kunna hasken dakin yayi ya dauki wayanshi kaman zaiyi waya kuma kome ya tuna oho ya maida wayan sannan ya mike yashiga bathroom ya dauro alwallah yafara sallan nafila.

[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ♥

ZAKISAN KONI WAYE

®zuwairat(ummu maryam)

 

4⃣

 

Wacegari baiyi breakfast da guards dinshi ba. Aside dinshi yasa cook ya kai mashi abinci, bodyguard dinshi sai tsoro suke don basu san abinda zai biyo bayaba mussanman Abdul don gani yake ya riga ya rasa aikinshi.

 

Kaman kullum yafito, cikin girmamawa sukà gaidashi, ya amsa masu a takaice. Ba kaman yanda ya saba ba.

 

A office kam sai ya tsinci kanshi da tunanin abinda Abdul yace, shuru yayi for a while sannan yace

” it can’t be possible.. It’s only possible in movie “. Aranan baiyi aikin kirkiba don banda tunani babu abinda yake yi Amman abinda yafi bashi haushi shine yanda Abdul ya rasa abinda zaice yayi sai taxi driver. Kaman ya kira Khalid Amman yasan shegenta babu abinda zaiyi mashi.

 

Atakaice dai bayan kwana uku abun ya zame mashi kaman disturbia, don tunda Abdul yayi wannan maganan bai Iya bacci batare dayayi marfarkin yana tukin taxi ba. Wani lokacin ya ganshi zaune cikin mota da wata cute lady amman baya ganin fuskanta, kuma tun ranan yabar zama da bodyguard dinshi balle yakara jin abinda Abdul zaice.

 

Dazun ya kira Khalid yana gaya mashi abinda ke faruwa amman daria ban haushi ya dinga yi mashi yana cewa nasha gaya maka ka bar bari bodyguard dinka suna ganin girmanka don irin wannan amman bakaji. Maganan Khalid haushi ya bashi don basu gama maganaba ya kashe wayanshi.

 

Yau yayi daidai da sati daya da maganan, ji yayi kaman he’s going insane. Bayan ya dawo daga sallan ishai ya zauna falonshi sannan ya kira Abdul,

” meet me now!” Yace MASHI bayan ya dauki wayan.

 

Jikin ba kwari Abdul ya shiga falon kasancewan yasan password din kofan. Da sallama yashiga Salem ya amsa Mashi, bayan ya zauna Salem ya kalleshi sannan yace

” Abdul wane irin charm kasa abakinka kafin ka bani shawaran kwanaki baya?…” Da sauri Abdul yace

“Sir wallahi babu wani asiri…sir am sorry…” Daga mashi hannu Salem yayi sannan yace

“Yanzu ba lokacin bada hakuri bane…inason ka yimin bayanin plan din…” Dan girgiza kai Abdul yayi before saying

“Sir da ka bar maganan kawai…”

“Abdul am not a patient person so don’t play dumb with me…” Ya fada afusace, jikin Abdul na rawa yafara cewa

” sir… Gani nayi tunda kanason samun mata dazata soka don Allah…shine nace ahaka bazaka gane masoyiyarka na gaskiyaba….” Salem ya katseshi dacewa

“Nasan wannan part din…I want you to hit the nail at head and stop beating around the bush” Abdul dan gyaran muryan yayi sanna yace

“Sir cewa nayi kayi pretending kai talakane for a while…” Salem ya sake katseshi da cewa

“Abdul banda abinka kawai daga nayi pretending ni talakane said in gane mai sona?…” Dan girgiza kai Abdul yayi sannan yace

” ai sir ba haka nake nufiba…Ina nufin kayi pretending ka maida kanka taxi driver…. ” daga kai yayi ya kalli reactions din Salem sannan yacigaba dacewa

” na Dan lokaci nasan insha Allah zaka hadu na mai sonka ba don abinda hannunkaba” Salem kura Mashi ido yayi for a while sannan yace

“Yanzu Abdul kasan cikin kasan nan daidaikune basu sanni ba sannan kasan in na fita ko hour day a bazanyiba zaayi kidnapping dina…ko ka manta saboda tsaro nake daku?” Ahankali Abdul yace

“Sir…ai ba a haka zaka fitaba dolene zaka danyi disguising kanka yanda bazaa ganekaba tunda kasan in har kafita a haka ko ba mota babu Wanda zaiyi maka kallon talaka cos everything about you look rich..” Maganan Abdul dariya tabashi don saida yadan dara

“Wai everything about me look rich…” Shima Abdul dan daria yayi, Salem shuru yayi acikin ranshi yana tunanin this might be fun cos sauran sati biyu ya fara annual leave dinshi kuma wata uku zaiyi, da yayi niyyan zaije yola yayi masu sati daya sannan ya wuce San Francisco daga nan ya wuce ummura Amman yanzu zaibi shawaran Abdul at least ko bai samu mataba zai samu more experience akan rayuwa.

 

Kallon Abdul yayi sannan yace

“Alh Abdul wane gari zamu…” Da Sauri Abdul yayi murmushi tare dacewa

“Sir duk garin da kakeso…”

“Ka bar cewa duk garin da nakeso cos kaima you are involved… So ka zabamana inda zamu” shuru Abdul yayi kaman mai tunanin sannan yace

“Sir muje Adamawa garinku tunda suna da beautiful ladies…” Dasauri Salem y girgiza Mashi kai

“Kai alh forget about beauty wane dare jemage bai ganiba…sannan kasan ba disguise ba ko ubanme zanyi bai hana first love sanin ina garin…so choose again” shuru Abdul yasakeyi for a moment sannan yace

“Muje garinmu” kallonshi Salem yayi sannan yace

“Na mance wane garinema?”

“Kano” Abdul ya amsa mashi, I do Salem ya kwalo sannan yace

“KANO?!!”

“Yes sir” Salem shuru yayi kaman mai tunanin wani Abu

“Kaima alh Abdul ina zan Iya taxi a garin Kano tunda ba sanin garin nayiba …wait a second meyasa ka nacewa taxi driving alhalin dakwai wasu aikinyi kaman ….” Sai yayi shuru don baisan example din da zai badaba, cikin zolaya Abdul yace

“Kaman sharan titi…” Dariya suka farayi sannan abdul ya cigaba dacewa

“Ko kwasan toilet….” Bai karasabha Salem ya jefeshi da pillow da ke kusa dashi yana daria, saida suka sami nutsuwa sannan Abdul yace

“Sir abinda yasa ka ga na nacewa taxi driving shine yana bawa mutum daman samun address dinmutum sannan karka damu wurin gane garin cos I will be besides you all through the way”

[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ♥

ZAKISAN KONI WAYE

®zuwairat(ummu maryam)

 

5⃣

 

“Subhanallahi” wata beautiful mata dake zaune balcony din saman bene ta fada lokacin da ta ga abinda ke faruwa cikin tsakar gidanta.

“Inna lillahi waina ilaihi rajuun” ta kara fada tana mikewa tana komawa daga bakin balcony don kara tabbatar da abinda idonta ya gane mata, don akasan benen wata yarinya ce wacce bazata wuce shekara 18 ba ta watsa wani mutum dake wanke wani jeep ruwa ajiki.

 

Afusace Matan tace

“Me nake gani haka…what’s happening?” Tambayan data jero masu kenen Amman yarinyan bata juyo ba balle ta amsa mata sai nuna mutum da ta watsawa ruwan take tana cewa

“Yanzu ya kaji ajikinka?…don dabbanci Ashe karasa abinda zaka wanke sabon murano dina sai detergent?. …” ahankali mutum Wanda zaiyi shekara 40 yace

“Allah ya huci zuciyanki…wallahi car wash ne ya kare…Ku…” Bai karasa ba ta katseshi da cewa

“To sarkin jahilai data kare agidan nan sai ya kare a kasuwa ko?..to wallahi….” Bata karasaba Matan saman bene ta kara cewa

“Wai badaku nakeba?!” Tafada atsawace. Mutum Wanda sai rawan sanyi yake a sanadiyan ruwan sanyin da aka zuba mashi ya daga kanshi ya kalli Matan dake saman bene sannan yace

” Hajiya don na wanke motanta da klin shine ta watsamin ruwan klin din a jikina” yafada kaman zaiyi kuka, Matan komawa baya tayi da alaman kasan bene zata sauko , yarinyan tana juyawa taga babu Matan saitayi saurin komawa cikin don kar matan tarisketa, itama matan sauri take don tasan halin yarta, lokacin daga suka hadu afalo

“Ameera da gaskene abinda umar yafada?” Ta tambayi yarinyan fuskanta babu alaman wasa, Dan matsawa baya tayi sannan tace

“Mummy he wash my brand new jeep with…” Bata karasaba Matan ta sharara mata mari Wanda yasa kunnenta tsaya jin, yarinyan dafa kunnenta tayi tana kuka tana kiran daddy.Matan tacfigaba dacewa

“Maimaita abinda kikace…” Yarinyan batace komaiba sai kiran daddy take

“I said repeat what you said” ta daka mata tsawa, da sauri tafara cewa

“Mommy kiyi hakuri…ruwan klin na watsa mashi…” Wani Marin Matan ta kara mata, wani irin rikitaccen ihu ta saki still tana kiran daddy

“Ameera kika zubawa age mate din ubanki ruwa?..ameera rashin hankalinki ya kai haka? …ni like son jawa zagi a garin?….” Cikin kuka tace

“Ni ba saan ubana bane…” Wani irin mutum duka matan ta kaimata, aikam nan yarinyan ta kwanta kasan ta rolling tana kuka tana kiran daddy na…ihunta yasa wani mutum tahowa daga saman bene da gudu don har neman silbewa yake don sauri

“Ameera daddy meya faru?” Ya tambayeta, tana ganinshi ta tashi da gudu ta fada jikinshi, riketa yayi ya sake cewa

“Ki gayamin abinda ke damunki” dakaji yanda yake magana kasan yana cikin tension kuma kasan bai hada wannan yarinyan da kowaba. Matan bata kalleshiba tashigaba dacewa

“Ameera ba baki nayi makiba Amman ke macece kuma in har baki bar wannan halin ba shi zai jamaki wahala” wani dan saurayi ne Wanda bazai fi shekara 12 ba dake zaune kan dinning da alaman yana homework Yayi saurin cewa

“Mommy jiya ma dan tace ya siya mata Mtn na 1k ya sayo na 5 hundred guda biyu tayi ta zaginshi tana cewa jakki jahili…” Ran Matan kara baci yayi ta nufe, ameera bayan daddy ta boye, shikam daddy ya hada rai sannan ya kara cewa

“Wai me kika yi take dukkanki kaman jakka?” Ya fada afusace, cikin kuka ameera tafada cewa

“Daddy wai dan umar mai wankin mota ya wanke motata da klin na zuba mashi ruwan ajikinshi shine mommy take dukana” afusace babanta yace

“Wai dan ki nunawa mai aiki Laifinshi take dukanki?” Cikin shagwaba ta dagawa ubanta kai, mutumin jiyawa yayi ya kalli Matan , itakam Matan ko kallonshi batayiba ta banbare ameera daga jikinshi zata kara dukanta mutumin yayi saurin rike mata, yana cewa

“Wai meye haka…ki bar dukanmi daughter don ta nuna…” Bata bari ya karasa ba tafara cewa

“Wallahi alh ka barni in hukunta yata tunda bakai zaa zagaba…nice uwa kuma nice zaa zaga..haka wannan yar iskan yarinyan tajtaza zana tattoo kaman wata karuwa amman ka hanani hukunta…” Mutumin Dan daria yayi sannan yace

“Hajiya banda Africa mentality.. Daga tattoo sai yarinya tazama yar iska?..kullum INA gayamiki yarainta ke damunta…watarana ko ance tayi bazata yiba…so….” Cikin fada Matan tace

“Ba wani yarinta…kawai kana goya mata baya..yanzu Aisha bata ganin uban kowa da gashin arziki…to wallahi gidan nan ni dakene..ko ki chanza ways dinki ko kuma in hallakaki dan wallahi bazan haifi yar dazata jamin tsinuwa ba…” Tana kaiwa nan ta hau stairs tabarsu, ameera cikin kuka tafara cewa

“Daddy ka kaini gidan anty Safiya…mommy bata sona” dan rarrashinta daddy yayi sannan ya haura daita dakinta, wani irin harara ta watsawa yaron

” affan zan kamaka” tacewa yaron.

 

Ameera dai irin yanmatan nan ne dabasu ganin kowa da gashin arziki mussaman in kana karkashinsu, daka ganta saika rantse yar barikice don komai nata irin nayan bariki, don har tattoo gareta abayan wuyanta, a bangaren samari kam babu namijin dazai ganta ya kauda kai, amman wulankanci kam kaman daita aka hallinceta don zagi kwando2 taiya kuma dad dinta is hundred percent behind her, kyakyawa ce na gidan karshe . Tana 200 level a b.u.k She’s the first born sai kaninta affan Wanda Sam ba halinsu dayaba

 

♥♥

 

“Ma-mi am going.. Kuma insha Allah in aka bani kudi yay zan sayo maki inhaler dinki” inji wata yarinyan da ke tsaye ratayi da dan tsohon handbag, da ka kanta kasan ba bahaushiya bace, yarinyan tana da kyau Iya gwargwado don bakace, Amman inda zata sami hutu zatayi kyau fiye da yanda take, mata dake zaune kan wata tsohuwar kujera tace

“Tawakaltu…” Yarinyan ta amsa tana rusunawa kusa da Matan sannan Matan tasake cewa

“Ki dawo lafiya” ahankali yarinyan yace

“Ameen mami” yanda take maganan ya nuna tana da respect, dan rungume matan tayi sannan ta fita daga dakin room and parlour, tana fita tsakar gidan naga ashe gidan mutane ne dayawa don dakunan dake gidan zasuyi takwas kuma da ganin duk ciki da falone, wata mata dake wankeke ta gaida cikin girmamawa sai naji matan tace

“Toyin ..zaki tafi” sunan da aka kirata ya tabbatar min cewa yorubace, amsawa yayi sannan ta fita, duk yaran gidan sai bye bye sukeyi mata.

 

 

Abangaren slim kam ana sauran sati daya tafiya yasa aka gyara gidanshi na Kano tare da zuba mashi sabon furniture, awurin parking kayan sawanshi kam suka samu matsala da Abdul, don Abdul cewa yayi dole ya sake siyan kaya Nigeria made tunda dukkan kayanshi designers ne, kememe slim yaki, da kyar Abdul Abdul ya shawo kanshi ya yarda aka kawo mashi kaya daga wani classic boutique suma saida Abdul ya sakasu a cikin washing machine yayi masu wanki kusan sau biyar suka dan koke sannan ya linkesu cikin watan katuwan traveling bag batare da angogesu ba, shikam Salem shuru yayi don Abdul is now the boss kaman yanda yake cewa.

[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ♥

ZAKISAN KONI WAYE

®zuwairat(ummu Maryam)

 

6⃣

 

Sauran kwana uku da tafiya Salem ya tafi yola ya shirgawa ummanshi gaskiya da karya amman ya gayawa abbanshi gaskiyan abinda zaiyi kuma ya bashi full support don abbanshi yafi ummanshi saukin kai.

 

Dukkan guards dinshi sunce zasu bishi Amman yace su zauna su jirashi har yadawo, da Abdul kawai zashi.

 

Ranar Thursday suka isa kano,kuma agidanshi na Kano suka sauka dukda Abdul nada babban gida a kano Salem cewa yayi I need my space.,

 

bayan kwana biyu Salem na zaune yana tunanin anya wannan ba stupid idea bane? Ya zaiyi kamanshi ace yayi descending so low don yana son true love.

“You can just back down” wata zuciya tace mashi

“No..not now.. I know it will be fun” ya fadawa kanshi, yana cikin tunanin ne Abdul yayi sallam yashigo tare da wani good looking guy. Ahankali ya amsa masu sallaman tare da daga kanshi yana kallonsu, cikin respect guy da suka shigo da Abdul ya gaida Salem cos yasan shi waye.

 

Bayan sun zauna Abdul yace

“Sir wannan guy din shine zai dan chanza maka kammanni da cosmetics” kallonsu Salem ya tsayayi for a moment sannan yace

“OK” guy din ya dan runtsuna sannan yace

“Alh zamu fara yanzu” ya fadawa Salem

“OK” ya sake ce mashi. Wata katuwan bag gayen ya dauko ya fiddo wasu abubuwa kaman kayan kwalliya , kallon kayan Salem yayi sannan yace

“Me zaayi da wannan cosmetic din?” Ya tambayi gayen

“Dasu zan dan chanza maka kamanninka..” Ya amsa mashi

“Hope basu da side effects” ya sake tambayanshi, dan murmushi guy din yayi sannan yace

“Not at all sir”

“OK then..let’s begin” Salem yace mashi.

 

Kayan ya kawo gabanshi sannan ya fara dan shafa mashi kayan, Abdul kam zai kallonsu yake, da sun hada ido sai ya galla mashi harara.

Sunfi minti ashirin suna abu daya sannan guy din ya dauko gemu, mara tsawo, kallon beard din Salem yayi sannan yace

“Is this necessary?” Ya tambaya yana kallon gemun with disgust

“Yes sir…wannan zai kara badda kamanninka” Abdul ya amsa mashi, Salem baice komaiba ya mike ya dauki iPad dinshi sannan ya kunna mirror cikin, kallon kanshi yayi, sai yaga an rage mashi haske sosai, amman still duk Wanda yasanshi daya ganshi zai ganeshi, kallon guys din yayi sannan yace

“Zan koma original color dina kuwa?” Daga mashi kai yayi

“Yes sir…da akwai wani makeup remover da zan baka Wanda zakayi amfani dasdashi kullum kafin ka kwanta”

“Are you telling me kullum zaka dinga yaba min wannan abun a fuskata?” Ya tambayeshi sounding so inquisitive,

“Yes sir..kasan in kayi amfani da makeup remover komai zai goge har sai mun sake wani” guy din yayi mashi bayani

“Ni dai babu abinda zai sami fuskata ko?” Ya kara tambayan gayen

“Sir kar ka damu” yakara jaddada mashi. Sannan Salem ya koma ya zauna aka saka mashi gemun. Daya kalli madubi yaga kamanninshi ta Dan sauya.

 

Bayan guy din ya tafi suka fita da Abdul cikin wata old modern Toyota corolla, yana tuki Abdul na nuna mashi gari sannan yana gaya mashi sunayen wuraren.

 

Ko 30 minutes basuyi da fitaba Salem ya sami parking space yayi parking sannan ya kalli Abdul yace

” alh Abdul kadawo driver seat ” kallonshi Abdul yayi yana murmushi sannan yace

“Sir har ka gaji?”

“Yeah” daria Abdul yayi

“Sir a haka zamu samu biyan bukata?” Abdul ya tambayeshi, Salem yayi relaxing tare da lumshe idanuwa sannan yace

“I am excusted.. Inajin kaina yana son iyimin ciwo sannan am not use to hayaniya” ya fada yana mikewa zaune

“Sorry sir very soon zaka dan saba” ya fada yana fita daga cikin motan, zagayawa yayi wurin Salem sannan ya bude motan Salem yafito shikuma ya koma driver seat. Abdul yana tuki yana tambayan Salem sunan inda ya nuna mashi dazun amman yayi banza ya kyaleshi,

Suna komawa gida direct wajen first aid box ya wuce ya Balli aspirin yasha. Sannan ya wuce bedroom dinshi,

 

Aranan duk yanda Abdul yaso su kara fita ko kallonshi Salem baiyiba balle ya bashi amsa.

 

Wace garima makeup artist din ya kara zuwa ya chanza mashi fuska Amman ki fita Salem yayi wai the sun is very hot, sai bayan sallan asar suka fita, suna cikin yawo, mutane sai tsaida taxi suke amman ko kallonsu bayayi balle ya tsaya.

 

Around six Salem ya hangi wata babe tsaye, ta ci gayu cikin fitted gown,gata beauty, Salem kallon Abdul yayi sannan yace

“Alh kalli wata yarinya chan..she look cute” sai lokacin Abdul ya lura da yarinyan.

“Sir ka tsaya kayi toasting dinta mana tunda tayi maka” Salem dan rage gudun motan yayi sannan yace

“Ya zanyi toasting dinta…kasan ban taba woeing yarinya ba..” Ido Abdul ya zaro

“Sir what about all the girls?..”

“Su suke nuna interest a kaina…” Bai gamaba yaga yarinyan tana tsaidasu, Dan murmushi yayi sannan yayi parking yana cewa

“Allah gani gareka” da sauri Abdul yace

“duk inda tace kanuna kasan wurin” yarinyan Dan takawa yayi saitin Salem sannan tace

“Mallam sharada zaka kaini” wani kamshin turare Salem yaji sannan ga muryan yarinyan so melodious

“OK” ya amsa mataa shiga motan tayi suka kama hanya.

 

Da taimakon Abdul suka isa sharada, sai yarinyan ta cigaba da nuna mashi inda zai kaita har suka isa kofar gidansu, 1k ta fiddo ta mika mashi, kallon kudin Salem yayi sannan yace

“Bani da chanji”

“Keep the change” yarinyan ta fada mashi, Dan girgiza kai yayi sannan yace

“No…you keep the money” yarinyan hada gidan sama Dana.kasan tayi

“Malan kallanni da kyau ka kalli kanka wayafi wani bukatan kudin” ahankali Salem yace

“Nafiki bukata… Amman haka nan nakeson bar maki kudin” yarinya tsoki taja tare da wulla mashi kudin sannan tace

“Kaji matsiyaci da iya yii…dalla take your money” tana kaiwa nan ta shige gidansu. Salem kam dariya ya dingayi kaman mara hankali

“Wai kaji matsiyaci da Iya yi” yafada cikin daria. Shima Abdul daria yake, Salem kallon Abdul yayi sannan yace

“Ashe mata sun iya rashin mutunci ” ya fada yana rike cikin don tsananin daria

“Sir indai wulakancin matane kadan ka gani…don wallahi suna dashi kwando2” Salem kara tuntsurewa yayi da dariya

“Ai sai yanzu na lura da haka …anyway nasan wannan adventure namu zai zama fun cos am feeling it already”

[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko:

ZAKISAN KONI WAYE

 

®zuwairat(ummu maryam)

 

7⃣

 

Har suka kai gida Salem bai bar dariyba,

“Ni ake cewa matsiyaci…gaskiyana tausayawa samari marasa money.. Don gaskiya da gani suna shan wulakanci” daria Abdul dake zaune yayi sannan yace

“Ai sir kadan ne wannan..” Dan tabe baki Salem yayi sannan yace

“Amman wasu yanmata basu da tarbiya..haduwa babu kunya babu tsoro ka zagi mutum”

“Ai sir wasu yanmata har marin samarin suke…” Bai karasaba Salem ya katseshi dacewa

“Kai alh Abdul ..ka bar karya mana…daga inasonka sai mari…ya rabbi kasa incikaro da irin wannan wallahi sai na taya ko waye daukan fansa” shidai Abdul daria kawai yayi don yasan irin wahalan dayasha hannun yanmata kafin ya gama degree dinshi yasami aiki a NGO kuma amatsayin bodyguard din Salem.

 

ONE WEEK LATER

 

cikin sati daya Salem ya gane abubuwa da dama game da mata don cikin sati dayan kullum sai yaga cool babes amman duk wacce yayiwa maganan so sai su wulakantashi , wasu har da zagi, Amman abun bai bashi haushi don duk sanda mace ta zageshi ko tayi mashi kallon banza sai ya wuni yana daria don dadin abun yakeji cos yanzu zai gane wacce zata soshi don Allah, yasan duk yanmatan dayayi toasting dasun San koshi waye da gudu zasu amsheshi hannu bibbiyu. Kuma yanmatan rashin kula garesu don fuskanshi da kayanshi mara guga kawai suke kallon Amman dazasu kuramashi ido su kalli agogon hannunshi, Rolex watch ne sannan inda zasu kalli zoben azurfan dake hannunshi costumise ne sannan da zasuyi hakuri su kalli kafanshi designer Prada ne kuma inda zasu kalli.hannunshi da kafanshi fari kal suke kaman ka taba jini yafito abunka da bafulatanin cikin daula.

 

Tunda suka fara fita kullum Salem cikin ciwon kai yake sannan tafin hanninshi yayi ja saboda dan tukin dayake cos rabonda yayi tuki har ya mance sai yanzu.

 

Duk wacce yadauka sai sun biyashi kudi koda yace baya amsa sai sun tillasa shi ya amsa amman suna bashi yana badawa.

 

Kuma wannan fitan ya kara wayar mashi da kai don yanzu yasan yakamata masu hali su dinga Dan fita don hakan zaisa su san halin da talakawa suke ciki cos yanzu ya kara sanin da akwai masu wahalan rayuwa sosai. Kullum sai yafita da akalla raw cash na 1million amman bai dawowa dako sisi saboda duk mai baran daya gani sai yabashi rabonshi.

Tunda yake bai taba fita koda abroad yaji it in dadin da yake ji ba cos he’s having lots of fun. Haka yasan yayi deciding koda Allah yasa ya samu biyan bukatanshi, duk shekara zai dinga dan fita yana ganin abinda ke faruwa.

 

 

 

Ameera ce tsaye cikin wata kayattacen daki, daka gan dakin kasan na yayan hutune, komai na dakin pink sannan ga wata madaidaiciyan plasma jikin bango da decoder, tashar boom TV take kallo don sai wata wakan Stanley enow ke tashi itakuma sai rawanta take, daga ita sai pant da bra sai rasa take kaman ance kiyi rawan zaa baki award. Duk ilahirin jikinta sai shaking yake, bayan wannan wakan aka sawakan sekem aikam nan rawa ya chanza, yanda take rawan tamkar daita akayi rawan sannan kaman itace tayi wakan don babu part din wakan da bata iyaba.

 

Wayan ta dake kan dan mini bed dinta sai ringing take amman bataji, sai bayan anyi mata 3 miss call sannan daga baya taji da sauri ta rage volume din decoder tare da picking wayan

“Babe ya kike?” Daga daya side din akace

“Haba ameera INA kika ajiye wayanki naketa kiranki ba amsa…” Ameera dake nishi saboda rawan datayi tace

” sorry sis wallahi ina nan INA practicing dance step dina ne….” Bata karasaba yarinyan ta tuntsure da dariya sannan tace

“Practicing kaman dole ko kuma ince kaman za a baki award?”

“Dalla malama what’s your reason for calling”

“Daman ummace ta aikeni zoo road shine nace inzo ki rakani?” Ameera kaman jira take

“Yes kizo daman nagaji da gidan nan kuma mom ta hanani fita”

“OK..gani nan zuwa Amman please ki shirya don nasan halinki”

“Don’t worry yanzu nan zan shirya” suka katse wayan. Da sauri ameera tabude katon wardrobe dinta Wanda ke shake da kayan sawanta,wash purple Arabian gown ta fiddo tare da Dan figigin Vail din kayan.

Dagudu tashiga bathroom ta watsa ruwa sannan tafito, cikin sauri ta shirya cikin kayan sannan ta dauko makeup kit dinta ta zauna gaban mirronta ta tsara kwalliyanta looking so breathtaking, sannan ta fesa turuka masu kamshin gaske. Wurin shoe rank dinta ta nufa ta dauki wasu light purple high heels sannan ta zauna bakin gadonta tana jiran zuwan kawarta mai suna zeenat.

 

Batafi minti 20 dazamaba zeenat tazo, taganinta ta window taga batazo da motaba

“Kambu ..badai da motata take son mujeba…” Bata karasaba zeenat tashigo

“Babe ina motanki..” Ameera ta tambayeta

“Tana wurin gyara wallahi…muje da naki…” Da sauri ameera ta girgiza kanta sannan tace

“Babu fuel kinsan daddy yana abuja kuma kona gayawa mom bazata bani ba..so yanzu meye abunyi?”

“To zai mu hau taxi…” Dan table baki ameera tayi sannan tace

“Amman fa kinsan banson hawan public car…mutum na iya kamuwa da wani communicable disease.. Balle bakasan ubanwa da uwarwa suka taba hawaba….” Tunda tafara maganan zeenat ke kallon ta, saida ta gama sannan tace

“Ke dai kullum halinki bai chanzawa…kawai daga hawan taxi sai my kamu da disease?… Dalla taso mu tafi time is not on our side” tafada tana fita daga dakin.

Zeenat kyakyawace Amman ko kadan bata kama kafan ameera ba…Amman when it come to character she’s an angel.

 

Itama ameera fita tayi tabi bayanta Amman saida ta dauki dettol disinfectant spray tasaka cikin handbag dinta.

 

Dakin mom dinta suka tafi tana ganin ameera ta hada giran kasan dana sama, zeenat na shiga dakin ta saki fuskanta, bayan sun gama gaisawa ameera tace

“Mom zan raka Zainab zoo road” Matan shuru tayi kaman bataso sannan ta daga kai ta kalli agogn dake jikin bangon dakinta

“Kunga this is after 4, Ku tabbatar kun dawo kafin 7” da sauri suka amsa

“da yes mommy” sannan suka fita

[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ♥

ZAKISAN KONI WAYE

®zuwairat(ummu maryam)

 

8⃣

 

Suna fita suka tsaida taxi amman mutum in na tsayawa ameera ta kalleshi sannan tace

“Malam ka wuce” mutum kallon ta yayi

“Malama ai bake kika tsaidaniba ” mutum ya amsa mata, ameera tabe baki tayi sannan tace

“Kayita tsayuwa nan” ta gayamashi a tsiwace, itakam zeenat ta saba da halin ameera, mutum ya watsa mata mugun kallo sannan yace

“Shegiya mai kama da aljannu” itama ta kalli mutum Wanda akalla ya girmi ubanta tace

“Shege mai kama da shaidanu” mutum fixgan motan yayi yabar wurin yana cewa

“Banza mara tarbiya” dukda mutumin ya tafi bai hana ameera cewan

“Uwar data haifekace mara tarbiya” kallonta zeenat tayi tare dacewa

“Haba shekira ai wannan mutumin ya girmi daddy fa?..” Harara ta ballawa zeenat sannan tace

“Daddy ki ya girma..don ni kam bai kai ubanaba balle ya girmeshi” Dan tsoki zeenat taja kafin tace

“Wata rana sai kin ja ruwan dafa kanki wallahi…nonsense kawai” itama ameera tsaki taja sannan tace

“Kema kinsan baa haifi mutum ba wallahi..kuma kika kara cemin nonsense sai injuya gidan ubana ai ba dole bane in rakaki” haka suka dan taba chan2 baki kaman yanda suka saba kafin kowa tayi shuru.

 

Sunfi minti ashirin tsaye, duk dan taxi din da suka tsaida sai ameera ta kare mashi kallon sannan tace ya wuce,saida suka tsaida taxi yafi biyar, suna tsaida na shiddan zeenat tayi sauri ta shige.

 

Itakam ameera saida ta fesa dettol disinfectant spray a inda zata zauna, mai motan juyawa yayi ya kalleta, itama ta kalleshi tare dacewa

“Non entity”. Ko kallon zeenat batayiba har suka isa zoo road.

 

Karfe shida da rabi suka fita daga gidan yayan zeenat, dan takawa sukayi kafin su karasa bakin titi, kaman dazunma duk mai taxi din da suka tsaida sai tace suna kama da kazamai ko kuma tace sun cika muni

 

 

 

Salem kam har ya mikawa Abdul car ya daga kai sai ya hangi wasu yanmata su biyu tsaye, maida key din yayi Wanda hakan yasa Abdul cewa

” sir ya akayi kuma” ya tambayi Salem, dan murmushi yayi sannan yace

“Kalli wasu babe chan.bari muje don wancan mai purple gown din tayimin..” Dan daria Abdul yayi sannan yace

” sir ai magrub ya gabato…” Salem ya katseshi da cewa

“Don’t worry…in har suka tsadamu to zamu san gidansu, gobe sai muje”

Rage gudun motanshi yayi lokacin daya kusa zuwa inda suke tsaye, aikam zeenat na ganin taxi sai ta tsaidashi, dadi Salem yaji cikinranshi don ya gagara yaji muryan budurwan dake sanye da purple gown. Yana tsayawa ameera ta zubawa Salem ido, shima zuba mata ido yayi yana kallon ta bako kiftawa, bai ankaraba yaji dayan budurwan tayi saurin bude motan tashiga, itakam saida taga gama kallon Salem sannan ta ja wani irin dogon tsoki tare da kauda kanta gefe

“Please babe ki shigo mu tafi kinga magrub ta gabato” yaji budurwan da tashiga motanshi tace, itakam ameera tafi minti biyar sannan ta bude handbag dinta ta dauko dettol disinfectant spray ta fesa inda zata zauna, Abdul da Salem juyawa sukayi suna kallonta, itama kallonsu tayi da sexy eyes dinta kafin tace

“Malan wannan kallonfa..ko Baku taba ganin disinfectant bane?” Tafada tana gyara zamanta, Salem kam beautiful mouth dinta ya kurawa ido yana imagining yanda zasuyi tasting. Juyawa yayi ya tada motan lokacin da zeenat tace

“Malan GRA zaka kaimu” .

Yana tafiya yana kallon ameera ta mirror, Abdul nuna mashi hanya yake amman dukan hankalinshi ya tafi ga ameera data fiddo iPhone 7 tana danne2, kaman ance ta daga kai, sukayi 4 eyes, wata irin mugun harara ta balla mashi tare dacewa

“Malam ijn idonka yayi maka ya ka ciro mu raba …village monger” Salem sauke idonshi yayi tare da yin murmushi, cikin ranshi yana cewa

” wai ne take cewa bakauye alhalin nasan inda naje aduniya da kyar taje kafin ta mutu”

 

Zeenat matsawa tayi kusa da ameera sannan cikin rada tace

” babe kalli hannun wannan mutumin tare da agogon hannunshi” baki ameera ta tabe sannan tace

“For what?” Salem yaji suna magana ahankali yadan saci kallonsu ta mirror, yaga zeenat nayiwa ameera rada, Amman bayajin abinda suke cewa

“Babe please ki kalla mama”zeenat ta sake cewa ameera, sai lokacin ameera ta daga kanta ta kalli hannunshi.

 

Gani tayi hannunshi farin kal sannan ga Rolex kwance kan fatan hannunshi, baki ta tabe kafin tace

” kilan barawo ne…INA taxi driver INA Rolex watch ” Salem da Abdul Dan kallon juna sukayi dan sunji abinda tace cos baa ahankali tayi maganan ba. Abdul kam murmushi yayi cos yasan they don’t know who they are dealing with.

 

Cikin minti 50 suka isa gra, a wani katafaren gida suka tsaya

“Babe ki shiga gida kawai su wuce dani” zeenat tafadawa ameera,

“Sai munyi waya” ameera ta amsa mata kafin tafita, Salem bayanta yabi da kallo

“Angel” ya furta ahankali

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment