Littafan Hausa Novels

Zafin So Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Zafin So Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Zafin So Hausa Novel Complete

GARGADI:

Bamu yarda wani/wata suyi copy and paste na wannan labarin ba, duk wanda ya aikata hakan mun barshi da Allah mai kowa mai komai.

 

KALAMAN GODIYA:

Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, ka qara tsira da aminci ga manzon tsira annabin mu Muhammad (SAW) tare da alayensa, godiya ga duk kan masoyan mu maza da mata aduk inda kuke, duk da wannan shine farkon rubuta novel din mu nida Hanee, muna fatan ku kasance tare damu a wannan labarin, karku bari a baku labari.

Agolah Hausa Novel Complete

SHIMFIDA

Wannan labarin ya qunshi labarin wata yarinya matashiya wadda ta tashi a cikin gatan iyaye, sai dai kuma kash! Tayi amfani da wannan damar data samu ta hanyar wulaqantar da duk wanda yake qasa da Ita, wanda a sanadiyyar hakan ne zata samu dana sani daga qarshe.

 

‘Yan uwan mu musulmai! Ku sani kar kuga Allah ya baka lafiya, dama, lokaci da kuma dukiya, kayi amfani dasu ta hanyar nuna rashin godiya da ya baka su, ku sani! Akwai dubban mutane da suke neman lafiya, dama, lokaci da dukiya amma basu samu ba, tou dan me kai/ ke kun samu wannan damar sai ku lalata su? Muna roqon Allah daya qara shirya mana zukatan mu, ya bamu ikon amfani da lafiya, da dama da Allah ya bamu.

 

COMING SOON

 

Haneefah and Amrah

Princess

ZAFIN SO

Na Amrah GHW

Da Haneefah NWA

page1⃣-2⃣

 

Tafiya muke nida Hanee ko waige bama yi, da abn yayI nisa ma har gudu muka koma yi duk dan muga mun tarar da wannan hamshaqiyar yarinyar, bamu muka tsaya ba sai bakun wani qayataccen gida wanda da ka ganshi gasan na wani mai muqami ne, a daidai vakin gate yarinyar ta tsaya da motarta qirar range rover ash colour, horn tayi amma shiru ba’a bud’e gate ba, sai bayan kamar minti biyu ta qara wani horn d’in amma shiru gate man bai bud’e gate d’in ba. A fusace ta fito daga mota ko jakarta bata d’auka ba ta bar motar bud’e ta shiga gidan. Koda shigarta ta samu gate man d’in kwance yana rawar sanyi alamar baida lafiya, bata ko duba yanayinshi ba ta d’aga hannunta ta wanke shi da mari, dafe kumatunshi yayi wani zazzafan hawaye na saukar mishi, kafin ya ankara ta qara d’auke shi da wani marin, sai a lokacin tace “kai uban waye da zanyi maka horn har sau biyu amma ka kasa bud’e min gate? Bayan kuma kasan bisa ga d’abi’ata horn daya kawai nakeyi ko sallah kake dole kabarta kazo ka bud’en gate in shigo gida, mtswww wawan banza!”.

Fita tayi bata koma takan motar ta dake waje ba, tayi tafiya mai nisa kafin ta isa inda farfajiyar gidansu take, shiga tayi kai tsaye babu ko sallamah. Ta samu momy kishingide ana mata matsar qafa, fad’awa tayi jikinta tana mayar da numfashi, a firgice momy ta miqe zaune tana fad’in “na shiga uku, auta me ya faru dake na ganki kamar ba’a hayyacinki ba?”. Kyakkyawar budurwar tace “momy wai waye ta kawo mana wancan wawan a gidan nan?”, momy tace “wa kenan?”, a shagwa’be tace “gate man d’in can mana”. Momy tace “ai! Wai baba faruku? Dady da kanshi ya kawo shi wai yana tausayinshi ne, me ya miki ne auta ta?”, “momy wai har sau uku ina horn amma yaqi bud’en gate, motar ma tana can na bari a waje har da key d’in yana jiki ban cire ba tsabar takaici”, miqewa tsaye momy tayi tace “auta! Baki da hankali ne? Baki gudun a sace ta ne? Kin san fa jiya aka kawo ta, waccan d’ayar ma ajiyeta kikayi fa aka sace miki a gidan biki”. Kamar tana jira momy ta gama maganar aikuwa ta fashe da kuka tana fad’in “momy! Yau nice kike yiwa fad’a har da nuna min yatsa? Momy tunda nake baki ta’ba yi min haka ba, a dalilin wancan wawan tsohon gate man d’in? Tou barin je inda yake, wlh sai yabar gidan nan, ko uban wa ya tsaya mashi”.

 

Haneefa Usman

Princess Amra

Princess

ZAFIN SO

Na Amrah GHW

Da Haneefah NWA

Page3⃣to4⃣

 

 

Fita tayi ko dan kwali babu a kanta, bata ko nemi takalmi ba ta kama hanyar d’akin me gadi, ta same shi still yana rawar sanyi wadda tafi yanda tabarshi d’azu. Bara jira komai ba ta fad’a d’akinshi, finciko shi tayi ta jefar waje, ta duba bakin katifar shi taga wata qaramar Ghana most go, dauko ta tayi ta jefa mashi a daidai isowar momy wurin, fitowa tayi daga dakin tace “a dalilinka momy na tayi man fad’a harda nuna ni da yatsa tayi, wlh yau sai kabar gidan nan, tsohon banza zaka nemi takurawa rayuwata, sai ka koma qauye aci gaba da cin tuwon dawa ai, mtsww” taja tsaki tare da barin wurin.

Abn haushi wai momy ta kasa ce mata komai, har tayi nisa da qyar tsohon nan me gadi yace “SAFNA!!! Ni kika wulaqanta haka? Ni kike kira da tsohon banza? Ko da yake banga laifinki ba, laifina ne da na qasqantar da kaina nake bauta a gidanku, hmmm!! Neman halak kenan, insha Allahu yanda na nema gareku kina wulaqanta ni bayan kuma nayi jika dake, ina roqon Allah ya kawo ranar da kema zaki nema a wuri na….” ya qarasa maganar cikin kuka da ban tausayi.

 

Da sauri ta dawo wurinshi ta sake wanke shi da mari tace “ba amin ba tsohon NAJADU!! Allah ya fika, kuma ni bazan ta’ba nema a wurinka ba, babana yana da kud’in da ko bayan ranshi zanci har in kyautar wa mabarata irinka” ta tofar da yawu qasa tace “tir! Da MUMMUNAN FURUCINKA”.

Barin wurin tayi da gudu saboda qunar da zuciyarta ke mata. Momy bata ce komai ba sai bin bayan ‘yarta da tayi tabar me gadi nata goge hawaye. Bayan kamar minti biyu yaja Ghana most go d’inshi ya fita. A hankali yake tafiya dan yana tsananin jin zazza’bi.

 

 

 

Da qyar ya samu yaje tasha ya hau motar qauyensu BAGARUWA, d’an chanjinshi ya biya kud’in mota ya isa. Ya samu Nawwaf na zaune qofar gida ya buga tagumi, koda yaga babanshi tuni ya tashi ya nufI wurinshi ya kar’bi jakar suka qarasa ciki yana mashi sannu da zuwa.

 

Haneefah Usman

Princess Amrah

ZAFIN SO

 

 

Page5⃣to6⃣

Na Amrah

 

 

 

Da shigar shi gida bai jira komai ba ya kwanta kan wata tabarma dake shimfide a bakin qofar d’aki, NAWWAF dai sai bin babanshi yake da kallo ganinshi da yayi sukuku, “Abba sannu da zuwa”, ya ansa da “yauwa NAWWAF, ina umman taka?”,,,,,” tana daga ciki ina jin, Ummah!”, “ga ni nan, zuwa fa, aahhh lale marhaba da mutan birni, sannu da hanya” ummah ta fada tare da fitowa daga daki.

 

Wasu irin zafafan hawaye suka fara ambaliya a fuskar Abbah, duk hankalunsu ya tashi ganin abbah na kuka, a rude NAWWAF yace “abba wai me ya faru ne? Tunda kazo naga kana da damuwa a zuciyarka, ka fada mn matsalarka wlh na dauki alqawari indai ina da maganinta”.

Ummah tace “malan meke faruwa da kai, kuka fa kakeyi, tunda nake dakai ban taba ji ko ganin kayi kuka ba, amma da mamaki sai gashi yau kana yi har idonka yayi jaa”.

 

Sun d’auki tsawon lokaci shiru basu samu ansa daga Abbah ba, jin bashi da niyar basu ansa ne yasa Ummah tayi qarfin halin cewa “ka watsa ruwa malan ka kwaso rana sai kaci abinci”. Baice mata komai ba ya miqe jikinshi na rawa ya nufi toilet. Da gamawarshi ya fito, abinci kawai yaci ya kwanta bacci yayi gaba dashi.

 

NAWWAF duk abn duniya yabi ya dame shi, sai zaman tagumi yake har abba ya farka yaga Ummah zaune kusa dashi tana hawaye, ga NAWWAF ma zaune a gefen Ummah, ganin su cikin wannan halin yasa shi cewa “kuyi haquri, bana son na fada maku abnda zai saku bacin rai ne shi yasa naqi fada maku, amma tunda kuna son ji yanzu zan fada”,,,,,,,,,,nan ya hau basu labarin duk abnda ya faru tun farko har qarshe.

 

Zumbur NAWWAF ya miqe tsaye yace “Abbah ka bar naje Katsina na samu jakar yarinyar nan, wlh sai naci mutuncin ta kamar yanda taci naka mutuncin, kawai qaramar yarinya ta kiraka da tsohon banza, munafuki, Subhanallah! Abbah yau yau din nan zan tafi”. Bai jira komai ba ya tafi dakinshi da nufin canza dressing.

Tsawa daya abbah ya mashi dole ya tsaya, abba yace “na saka ne? Wau kai NAWWAF yaushe zaka rage wannan ZAFIN zuciyar taka ne? Ya kamata fa kasan ka girma, kuma nace kabarta da duniya, duniya zata bida ta, ai laifi na ne da naje gidansu da aiki, kaga inda ace banje ba ai da bazata ci min mutunci ba, amma yanxu da nabar gidan ba shikenan ba? Sai kuma tayiwa wani ai”.

 

Ummah tace “hakane malan, tou amma yanxu idan ka dawo gida ka zauna ya zamuyi da abincin da zamuci? Shi NAWWAF bai iya ko wace sana’a ba, shidai karatun boko kawai ya tasa a gaba, ni fa yanxu kusan shekarar shi biyu kenan da gama degree dinshi, har service ya gama amma babu wani aikinyi kullun sai zaman qofar gida yake, sai matacciyar zuciya kawai”.

NAWWAF da hawaye ya wankeea fuska yace “Ummah indai hakane zan nemi kudi insha Allahu, neman kudi kuma ta tsaftatacciyar hanya, zan nemi halal insha Allahu ko ta hanya mafi wahala ne”.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment