Littafan Hausa Novels

Yayi Sake Hausa Novel Complete

Suwaye iyayen Ummi Rahab
Written by Hausa_Novels

Yayi Sake Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

YA YI SAKE

*_BILKISU H MUHD_*

 

 

PHONE

08031307884

 

MARUBUCIYAR LITTAFAN

HUBBAN SHADIDAN

IZZATU

MULKIN MALLAKA

WAYAFI SON TA

KAUNA CE

RASHIN RABO

ILLAR SABO

JINI BIYU

BAYAN KUSKURE

WATA RAYUWA

MATSALAR KAUNA

DAKE NA DACE

KA AURE NI

GORO DA SANKARA

ZUMA DA MADACI

DACEWA

 

 

Page 1

*_BismillahirRahmanirRaheem_*

YA YI SAKE

Wannan yanayin yafi ko wani yanayi sanyata ni shadi,tana mutukar kaunar yanayin damuna,musamman ma yau da hadari ya hado tun safe Kamar wadda za,ayi ruwan sama sai dai har kawo yanzu ruwan bai kaiga sakkowa ba maimakon hakama sai wani daddadan iskar daya maye gurbin ruwan hakanne ya sanya hadarin washewa a sararin samaniya,daidai wannan lokacin tana jikin Inna idanunta a lumshe yayinda  Inna ta kutsa yatsunta cikin gashin kanta Mai tsananin laushi da tsayi tanayi mata wani abu mai kama da susa tanajin dadin yadda take yi Mata.

” Sumayya yau hammanki yayi sati biyar akasar India Ina saran ko yaushe zai iya dawowa.

ambaton hamma da tayi ya sanya sumayya ta zumburo baki hadi da hade rai taja wata yar karamar tsaki.

” Inama kada yadawo yayita zamanshi acan.inna ta Kai mata bugu

” Ja,irar banza.

Gidan Arna Hausa Novel Complete

” To ai Inna kinsan halinsa yana dawowa zai gallabi rayuwata da wannan shegen son girman”Kinga dagani bazan iya jure jin wannan shirmen naki ba,ayi mutum sai shegen son jiki,ko da yake laifin yayanki ne shine ya koya miki.

“To Inna daya koya mini bagashi yanzu yadawo yana hantarataba,” yaga ke bakisan kin girma ba har yanzu” toh daman su wa,anda suka girma hantarar su akeyi,bafa yason ko kadan in rab’eshi yatsaneni dan haka banason kusantar inda yake,

Ke sumayya kada nasake jin wannan furucin daga bakinki

ta mike tana faman tsuke fuska,Inna ta fada cikin daure fuska.

sam Inna bata son laifin hamma koya takawo kushensa sai ta mara mishi baya dakinta ta shige yayin da Inna ta shige kitchen dan dora sanwar dare tana tafe tana faman mita..

Kwance take a tsakiyar gado hoton hamma Wanda ke manne a gefen gado ta kurawa ido tafi maida hankali ga kallon dan karamin bakinsa,ta murguda masa baki kamar tana gabansa,da Allah jishi Kamar wani na Allah,macijin sari ka noke kawai,babu abinda ya iya sai shegiyar zuciya da mosifa fal ciki,duk matar data auri wannan na tabbatar zaben tumun dare tayi ina tausawa wadda zata aure shi,ta Kara nitsewa cikin kare masa kallo,ta tabe baki koda ike nasan ahaka wata zata kwasa ko dan wannan shegen kyawun nasa.

Hamma ingarman namiji ne irinsu ake Kira da jaint dogo ne shi amman ba canba yana da fadin kirji bashi da rama ba kuma shi da kiba fari ne shi kwal tamkar wani balarabe fatarsa Mai kyau ko ina na jikinshi gargasa ne yana da manyan idanu masu daukar hankali hancinsa daidai tsarin fuskarsa gashin kanshi kuwa tamkar na larabawa baki suduk ga laushi babu abinda yafi daukar hankalin mutane sai irin tabon sallar dake goshinsa,hamma yana da kwarjini ba irin mazajennan ne da za,a rainaba Kai da ganinsa kasan tsayayye ne bayason raini miskili ne na ajin karshe bashi da son magana duk maganar da zaiyi Mai muhinmanci ne,gashi da tsurfa komi nasa akyiyade yake mutunne shi ma abocin son ibada Ina ganin hakan nema yasa ko yaushe zaka ganshi a nitse Kai baka Isa ka kawo mishi wargiba gashi ma,abocin son mu,amala da  kamshi,ko da yaushe cikin kamshi yake hatta bacci inzaiyi sai ya feshe jiki da turare sabida yewan ta,ammali da turaren har kamshi ya zauna masa koda bai fesaba ma kamshi yake hatta bakinsa kamshi yakeyi yayin da yake magana,wani lokacin da gangan sumayya ke matsawa kusa dashi idan Yan Shirin sukazo har ta kanyi mamakin yadda yake da yawan yin brush ga in zaiyi sallah sai yadan goga aswaki wannan al,adar ta zame mishi jiki,haka nan itama ya dorata akan abinda yakeyi inko yaga batayi ba ta shiga uku ala dole ta dauki duk wasu dabi,unsa .

Ita kuma sumayya akwaita da surutu ga rawar Kai da tsiwa wannan dalilin ne yasa tasu bata zo daya ba babu abinda yafi bata haushi irin yace zai kwance ta yayi d’ai d’ai da ita ya sanya Mata notinan da zai dinga sarrafata yadda yake so yanzunn c can zata sa masa kuka duk karadin ta da zaran ya dawo gida zakuji tamkar ruwa yacita tana tsoronsa sosai baya barinta tana mu,Amala da kuwa ballantana ta sami sassauci Inna ce abokiyar hirarta itace komi nata shiyasa ma har yanzu bata da wata wayewa sosai ss 1 take a makaranta, a makarantar suma yan ajin wareta sukeyi a cewar su wai ita karamace ba sa,arsu bace ko kuma nace kokarin da take dashine yasa suke wareta hakan bai wani dameta ba sabida mazan ajin suna kulata sannan malamai naji da ita kokarinta bai tsaya a boko kadai ba hatta karatun muhammadiyya ma itadin ba baya bace har ma tayi sauka duk da kananun shekarunta.

Washe gari bayan ta idar da sallah asuba ta mike zata tashi daga kan darduma ji tayi mararta ya wani daure ga wani irin ciwo komawa tayi ta durkusa agun ciwin na cigaba da nukurkusar ta aikuwa ta saki ihu tana kwalawa Inna Kira asukwane ta shigo ta rufa akainta ,ta dagota tambayar ta takeyi amman takasa magana jinta takeyi tamkar zata mutu ciki ta soma nunawa Inna aguje tayi waje kitchen ta nufa ta jiko kanwa ta komo dakin har lokacin sumayya bata daina kukaba ta tallafo kanta ta shiga dura mata.

” Maza shanye zaki Sami sassauci gaba daya ta shanye sai dai babu alamar sauki sai ma gaba da ciwon yakeyi gaba daya ta gama karaya ta shiga maimaita kalmar shahada Inna ta mirgino ta jikinta tayi rubda ciki ta shiga dan bubbuga Mata baya Kamar yadda akewa yara tana tottofeta da wasu ayoyi daga cikin alkur,ani Mai tsarki ahankali ta soma jin dan sassauci har bacci ya dauke ta ahankali Inna ta zare jikinta kitchen ta nufa don Dora musu abin kari

Bashi da burin daya wuce  ace yau sun zauna da ummansa suna hira irin ta da da mahaifiya sai dai bai taba samun hakaba yau ya tabbatar dadewar dayayi basu haduba zai sanya ta nuna mishi kulawa a dokance ya shiga gidan cike da kewar ta

tana zaune da kannensa hira suke sosai daganin shigowarsa tayi saurin mikewa atafe ta amsa gaisuwarsa kuma aciki ta tsiri aikin ba gaira ba dalili,duk sai yaji ransa ajagule Anya ummansa na kaunar sa kuwa idan yayi korafi ace ita bafullatana ce tana kallo ba haka shauran kishiyoyinta keyiwa “ya”yan suba tunda yake da ita maganar minti biyu bata taba hadashi da ita ba,ko su fulanin sundaina irin wannan kawaicin.

Kannensa suka gaidashi cike da farin ciki hadida girmamawa tsabar da ya yo musu ya dire ya fice batare da ya ce komi ba sabida takaici.

dakin hajiyarsu ya shiga uwar gida agun abban su mace Mai dattako da son mutane gata da saukin Kai bata da son hayaniya ta daukeshi tamkar dan da ta haifa ita ke share masa hawaye bakomi yake boye mataba kusan ince ita ce ta raineshi.

Zaune take akan darduma da alama sallah ta idar fuska kunshe da fara,a takeyi mishi marhabun cike da girmamawa ya gaidata” saukar yaushe?,”saukata kenan.” ikon Allah kace kosu Inna basusan da dawowar kaba,lalle yau sumayya akwai murna kenan”.

Sun taba hira bayan ta kawo masa abinci da lemo Mai sanyi,ta numfasa” kashiga gun umman ne? yadan jinjina Kai” nadai ganta a setting room zaune yadanyi shuru zuwa wani lokaci yayinda hajiyar su ta tsira masa ido ta fahimci yana cikin damuwa ta kuma San damuwar har kullim daya ne,” kayi hakuri wataran komi zai zamo labari,kaidai bita a sannu uwace kaji.

” nagode hajiya”.

Mikewa yayi zai fita ta dakatar dashi da fadin” bangaya makaba Abban zainab ya biya mini hajji wannan karon dani za,a” Masha Allah, wannan bawan Allah akwai kokari Allah ya kara arziki. Sai da ya biya dakin haj Aisha ya gaida ta itama Haj Aisha itace amaryar abbansu.

***.          ***

Babu Wanda yaji motsin shigowarsa har yagama kintsa komi na dakinsa ya shiga bathroom yayi wanka bayan ya fito ya sanya kaya marasa nauyi ya feshe jikinsa da turare ya dubi agogon dake manne ajikin bango yanzu lokacin sane na barci idan ko baiyi ba kansa zai yi mishi ciwo duk da yana son ganin sumayya .

Karfe hudu daidai kiraye kirayen sallar da ake yi ne ya farkar dashi asukwana ya shiga bathroom ya goge bakinsa hadida daura Alwala ya bi ta kofar da zai sadashi da kofar gida ta dakinsa batare da an ganshiba masallaci ya nufa.

Rashin jin motsinta ya tabbatar masa da cewar babu lafiya shashinsu ya nufa ya tara’s da Inna zaune tana jin redio Inna ta fadada fara,arta” haba nifa nasan kaine kadawo don tun dazu nakejin motsi”

Samun gu yayi ya zauna yana faman rarraba ido” Inna nadawo ne agajiye shiyasa ban shigoba.tayi murmushi” mutuniyar taka yau ba lafiya koda taji zuwan naka bata da sukunin zuwa balle ta addabe ka.” Ido waje ya ke kallon ta” meke damunta”

“Yau wuni tayi da ciwon Mara tamkar ta mace min agida na tsorata sosai yanzu na dan bata kanwa shine tadan Sami bacci, yayi wani irin zabura” kanwa kuma Inna , innalillahi da sauri ya mike itadai Inna ta bishi da kallo.

Kwance ya ganta tayi ruf da ciki rike da cikinta yashiga Kiran sunanta bata iya amsawaba sai dai gyara kwanciyar ta datayi zuwa rigingine har lokacin hannunta na rike da cikinta sai gashin kanta da yayiwa fuskarta rumfa hannunsa na rawa ya Kai fuskarta ya kwashe gashin daga fuskarta tsohon mintina uku yana kallon kyakkyawar fuskar ta mamaki yake yadda ta K’ara girma jiyayi gabansa na bugawa da sauri,da sauri bushasshen hawayen da yagani a fuskar ta ya tabbatar masa da taci kuka da sauri ya dauke ido daga kanta cike da tunani barkatai ajiyar zuciya take famanyi irin na wanda yaci kuka ya koshi da sauri ya mike ya bar dakin. A harabar gidan sukayi kicib’is da Inna” ya jikin nata,Inna ta tambaya” bata farkaba bacci takeyi.

 

Wani irin rikitaccen mafarki yakeyi cikin baccin sa yaji Kira ahankali ya bude ido tabbas wannan Kiran ba,a cikin mafarki akeyin saba” hamma yaji muryar sumayya ta sake fada zumbur ya mike ya fara shiga bathroom ya

dan goge baki ya fito daga shi sai singlet da gajeren wando.

Rungume ya taddata ajikin Inna tana faman ciccije lebe ” Inna mutuwa zanyi zan mutu,Inna ta dubeshi.” Hafiz yarinyar nan najin jiki harda fa Suma yakamata ayi wani

abu akai,yadan dube ta ta wutsiyar ido tabbas yasan tana da raki sai dai wannan karan da gaske ne abinnata,akwai alamun rudewa afuskar sa ” Inna zata Sami sauki yanzu insha Allah.

muryarsa taji tamkar amafarki sai da ta tabbatar shi dinne ta sake narkewa satar kallonsa ta shigayi azahiri ciwon yadan lafa kodan ta huta da mosifarsa na tashi kiyi wanke wanke share can goge nan jeki sakeyin wanka lokacin sallah yayi maza yi shafa,I da wutili kinyi walaha da sauransu dole ta langwabe ko ya sakar mata Mara tayi fitsari aiko taga tsantsan tashin hankali kwance a fuskar shi ya karaso kusa da ita ya zauna mararta taji yadanyi wani danka aikuwa ta danko hannunsa da karfi yadda zata more muguntar da yakeyi Mata dam yaji gabanshi ya buga sakamakon yanayin daya tsinci kanshi  wannan shine Rana ta farko daya tafarajin hakan  cikin tattausar murya irin na Mai son lallashi.inna Kam tashi tayi ta bar dakin.” Yanzu gaya mini kamar Yaya kikejin ciwon?

bata bashi amsaba dan ya tabbatar da ciwon ba na wasa bane yasa ta dauko hannunsa ta dora a mararta da sauri ya janye hannunsa kamar Wanda wutar lantirki ta jashi ” ina zuwa yace da ita barin dakin yayi sai gashi ya dawo da kayan gwaje gwaje irin nasu na likitoci ta Kara wani langwabe wa ya taimaka Mata ta mike zaune gwaje gwajen daya somayi matane yasata rudewa atunaninta wani mummunan al,amari ne ke shirin faruwa da ita yanzu kam kuka take da gaske ya dubeta akufule” malama bace miki nayi ki rufen baki ba idan baki rufen baki ba yanzunnan zan zurmuka Miki allurar bacci.abinda tafi tsana kenan wato allura aiko babu shiri ta rufe baki har abin yaso ya bashi dariya ya basar.

Yadade yana gwaje gwajen lokaci daya yanayin sa ya sauya,kokadan baiso zata fara jinin al,ada yanzuba yana ganin tayi kankanta dai dai lokacin Inna tashigo yanayin dataga yashiga yasata tambayar sa ita kanta ta rude da yanayinsa.” Hafiz lafiya maike damunta a wahalce ya dubeta” babu wata matsala Inna bara na kawo Mata magani ya juya ya fice gaba daya duk su biyun suka bishi da kallo, sumayya ta dubi Inna,” Inna ko mutanen nasa ne suka motsa inyi ta kaina,Inna tayi murmushi ” lalle kin fara samun kanki kenan,to bara kiji barinki zan dashi yayi Miki lilis” yi hakuri Inna gani nayi duk yabi ya birkice” sai kuma kiyi.

tayi raurau da ido kamar zatayi kuka,” Allah Inna banji dadin dawowar shiba yanzu zai fara tsangwamata.” Kidaina yiwa yayanki mummunan zato kinriga kinsan halinsa yakamata ki daina saka damuwa a ranki don bazai canzaba hali zanen dutse,ta dubi Inna cikin daure fuska,” babu abinda yake dauwamamme wataran dole na bar gidannan sai naga wacca zai nunawa zanen dutsen.” Oh sumayya rigima kenan,to yanzu yakikeson nayi?” Kawai ki sanyashi ya maidani makarantar kwana,tayi murmushi” shikenan zanyi iya kokarina,Inna ta mike bara na shiga na dan kwanta kinsan gobe zani kauye gashi yau sam ciwonki bai bari na rintsaba.

Kicibis sukayi da hamma rike da magunguna a hannu tayi mishi sannu ta shige.

“Taso Kisha magani kallon da ya watsamata ne yasa ta karbi magungunan babu shiri ta afa a baki,tana gama Sha ta juya zata kwanta sam batason ganinsa yayi saurin dakatar da ita gurin kada mata Kai tariga ta gane abinda yake nufi tagama karantarsa Kamar yadda ya karanceta fiyema da inda ta karanceshi ya kafeta da manyan idanunsa hakan ya tilasta Mata sunkuyi da Kai bata iya jurewa kallon wannan mayun idanun nashi,wani irin idone Wanda aduk lokacin da ya kalketa dasu sai dukkan jikinta sun amsa takanji kamar wadda aka tsinkewa jijiya wani irin kwarjini yakeyi Mata ahankali ya shiga fadin” wato ke bakiyi farin cikin dawowana ba ko,ta ware idanu akanshi tana borin kunya shin ya akayi ya ganota.

” Injiwa?bai ce Mata komi ba ya tashi ya fita gaba daya ta ji badadi.

Tun da sassafe Inna ta dauki hanyar kauye gaba daya bataji dadin hakan ba yau tarasa abokin hira zaman kurame kawai za,ayi a gidan mikewa tayi jiki ba kwari ta sabule kayan jikinta ta daura tawul bathroom tashiga sai da tafara yin brush sannan tayi wanka.

Kayan da hamma ya kawo Mata na tsarabar India ta shiga kiciniyar budewa jitayi wani danshi a kasanta ta yi saroro hadida Kai hannu gun dan sanin ko menene jini tagani dumu- dumu a hannunta wata iriyar razana tayi tare da sakin wata gigitacciyar Kara Hamma acikin dakinsa yana sharce gashin kanshi da brush baisan sa adda ya cillar da brush dinba ya nufo dikin asukwane itama daidai lokacin tana kokarin karasowa gunsa cikin rashin sa,a suka yi karo da juna zata fadi yayi saurin rikota jikinta na faman rawa.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment