Littafan Hausa Novels

Yar Zaman Wanka Hausa Novel Complete

Babbar Yarinya By Oum Aphnan
Written by Hausa_Novels

Yar Zaman Wanka Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

YAR ZAMAN WANKA

 

(KWANA ARBA’IN)

NA

 

 

MAMAN AFRAH

 

 

FCW

 

🅿️1️⃣

 

 

Gabaɗaya ta jibge kayan cikin wardrobe ɗinta a kan gado, sai zuba wa take a cikin wata babbar bakkon kai da gani tamkar ƙaura za ta yi, sai da ta kwashi son ranta ta maida sauran. Akwatin ƙarfe ta ɗakko irin tasu ta mutanen da, kayanta ne na fita unguwa ƴan atamfofinta sabbi. Sai zuba kayan take tana ta faman murmushi gabaɗaya wani irin daɗi take ji a ranta

Mijin Buzuwa Hausa Novel Complete

“Yau sai kwanan binni” Inna Azimi ta faɗa tana ƙoƙarin zige zip ɗin bakkon nata, hango sallayarta ya sanya ta dakata da zige zip ɗin ta ɗakko abin sallar tana cewa

 

 

“Kar in je in ke cewa a bani abin sallah dan ni bana son yin sallah sai a kan sallaya ta bare ma su yara da kunya kake bani-bani in da abinka kwa sai dai a ga ka ɗakko” Ta ce tana sanya sallayar ta dannata daƙer ta samu ta shiga saboda cika da bakkon ta yi.

 

 

Wanka ta shiga abin ta, tana ta sauri ta fito, kallon ɗakin kishiyarta ta yi ta yatsina fuska a ranta ta ce

 

” Humm ba zan faɗa miki ba jikata na naƙuda, ba sai dai ki ganni da kayana zan tafi birni in yaso baƙinciki ya kasheki, tun da ke baki da dangi a birni” Ta faɗa har da wani gatsine kamar wata ƙaramar yarinya.Ɗakinta ta shiga sai da ta shafa mai tsaf, ta sanya kwalli sai wani kallon ƙaramin mudubi take tana wani gyagygyara fuska tamkar wata ƴar budurwa. Sai da ta gama tsaf ta ɗakko atamfarta batik a linke a kan gado daman takanas ta fitar da ita saboda ta sanya idan za ta tafi.

 

 

Sanyawa ta yi a jikinta ta ɗakko ɗankwalinta irin na tsaffin nan ɗan kantu mai santsi ta ɗaura har da yi gwaggwaro a gaban goshi, ƙasan gado ta sunkuya ta ɗakko takalminta ɗan madina domin shi ne wanda take sanyawa in za ta gidan biki dan shi ne na ganin sarki, ta fiddo shi ƙofar ɗaki ta ajiye, ta ɗauki silifas ɗinta wanda ta cire duk ya wani tsufa ya katale, ta shiga da shi ɗakin ta sanya a ƙasan gado, madarar turarenta ta ɗakko ta shafa abinta, sai ta kwalbar turaren a ƙaramin aljihun bakkon tana cewa.

 

 

 

“Wannan sai ranar suna kuma zan shaga abuna, yo a kan me zan ke wari ranar suna a raina min hankali ganin daga ƙauye nake” Ta faɗa tana taɓe baki.

 

Sauran goranta ta ɗauko ta ɓantala tana ci ta ƙulle sauran ta saka a ƙaramar jakarta ƴar pos wacce jikarta Sadiya ta bata.

 

 

 

“Yauwa na gama komai bari in je in tambayo Malam, dan ma kar ya ji ya wai dan wallahi tafiya babu fashi” Ta faɗa tana fitowa ta nufi turakar mijin nasu da ke can wajen hanyar zauren gidan.

 

 

Kai da tsaye ta danna kai turakar Malam tana mai cewa

 

“Gafaranmu dai”

 

“Allah mana gafara” Cewar Malam yana kallonta mamaki bisa fuskarsa ganinta da shirin fita dan ya san biki ma sai na wanda yake da kusanci da ita take saka atamfofinta na adakar ƙarfe, hakan na nufin biki za ta ko sanar masa bata yi b ya faɗa a ransa.

 

Inna Azumi kwa sai da ta gama shigowa ɗakin ta lura da Tasalla da ke zaune a ɗakin sai lokacin ma ta tuna Tasallar ce da girki.

 

Wani kallo ta yiwa Tasallar ta ce

 

“Umm in ji mai ciwon haƙori” Ta faɗa tana samun wuri ta zauna. Shi dai Malam har lokacin kallonta yake da mamaki, sai da ta zauna ta ce.

 

“Sannu Malam” Kallonta ya yi tare da gimtse fuska sannan ya ce

 

 

“Yawwa sai ina, dan na san dai zancen gizo bai wuce na ƙoƙi tun da na ganki da shirin fita”

 

 

“Haba Malam, dama magana ce nake so mu yi” Ta faɗa tana kallon Tasalla dan so take Malam ya ce Tasalla ta fita dan bata so Tasallar ta san da tafiyar tafi so sai ta fiddo jakarta ta mata bazata.

 

 

“Ki faɗi abin da ya kawo ki” Cewar Malam yana kallonta har lokacin babu fara’a a fuskarsa.

 

 

Washe haƙuranta ta yi wanda har lokacin da ɗan sauran goron da ta tauna a bakin ta ce

 

“Dama Halima ce ƴar wajen wannan yaro zan je yiwa zaman wanka sai…

 

 

“Zaman wanka kuma Yaushe Halimar ta haihu da har za ki tafi zaman wanka ko faɗa min baki yi ba sai da kika shirya? Shin ma me za ki je ki yi da girmanki da komai?” Malam ya faɗa rai ɓace dan abin ya bashi mamaki bai zaci ma garin za ta bari ba duj tunanisa biki ne za ta je a cikin garin ko wani ƙauyen da ke maƙotaka da su.

 

 

 

Tasalla da farko wani haushi ta ji jin kishiyarta za ta tafi birni, dan duk da sun tsufa amma kishin nan yana nan sabo dal a zukatansu. Amma ganin Malam ɗin ya haƙiƙice sai ta faki idonsa ta yiwa Inna Azumi gwalo.

 

Inna Azumi wani ƙululun baƙinciki ne ya tokareta ganin kishiyarta tana mata gwalo har da ƙunshe dariya.

 

“In kin san wata baki san wata ba wallahi sai na yi kissar da sai ya barni na tafi, shegiya ƴar baƙimciki da bata da kowa a birni bare tasa rai wataran za ta je ta sha miyar ɗanyen kaya (jar miya).

 

“Bata haihu ba fa fama…

 

“Ban gane bata haihu ba wato shi zaman wankan ma tun kan a haihu ake zuwa yinsa?” Malam ya katse ta da tambaya cikin nuna tsantsar mamaki a fuskarsa.

 

“Yau za ta haihu”

 

“Ikon Allah wato dai har ɗan adam ya san ranar da wani zai haihu in ce dai wannan ilimin ubangiji ne, ko su turawan da suka fito da yin hoton ciki (Scanning) Dan a san watanninsa da ranar haihuwar ai ko sun faɗi ranar ba a ita ake haihuwa ba ko dai mace ta rage kwanankin ko kuma ta haura ma amma ke har kin ware ranar da za ta haihu, wallahi Azumi ki fita idona ba na son fitina” Malam ya faɗa yana nunata da yatsansa.

 

Sosai abin ya yiwa Tasalla daɗi, sai ƙunshe dariya taje tana yiwa Azumi kallon ƙasan ido, wannan abu shi ya ƙara ɓatawa Azumi rai sosai take jin kamar ta fashe da kuka.

 

“Haba Malam ai ka bari na mutu kafin ka binne ni” Cewar Azumi a ɗan fusace.

 

“To uwata yi min faɗa ko ki haɗa da duka tun da ke ce mai gidan, kuma ma da kin san ke ce mai gidan ai da baki zo nan neman izini ba da sai ki yi tafiyarki” Malam ya faɗa yana gyara zamansa ya lanƙwashe ƙafafunsa wanda suke a miƙe.

 

Sai sannan Azumi ta gane katoɓarar da ta yi aikuwa da sauri ta ɗan karyar da kai tare da sanyaya murya ta ce

 

“Haba Malamin Malamai, Malamin da ƙauye da rigagen yankin nan ke ji da shi suna alfahri da shi, ni na isa in ja da Malamin da kowa ke girmama shi saboda ilimi da ɗaukakar da Allah ya masa”

 

Aikuwa Azumi ta harbo jirgi tuni Malam ya washe jajayen haƙoransa, cikin jin daɗi ya ce

 

 

“To ai ke ɗin ce Azumi sai kike abu kamar dai ke ce sama da ni amma ai sai ki yi bayani tin farko”

 

Tasalla wani irin takaici ne ya mamaye dukkan zuciyarta dan bata so Malam ɗin ya sakko ba ta so ayi ta gumurzu, har ayi faɗan da Malam ɗin zai hana zuwa birnin duk da ta san har yanzu bata ji an yi haihuwar ba, ta san kawai riɗin abincin birni ne ya sa ta zazzoɗin son tafiya.

 

 

Wani kallo mai haɗe da hara Inna Azumin ta yiwa Tasalla kafin ta juya wajen Malam ɗin ta yi murmushin jin faɗi ta ce.

 

“Wallahi dama ɗazu ne na kira lambar Babar Halimar dan in ji ya suke, to shi ne fa na ji tana ta sheshshekar kuka tana cewa “Inna ki taho idan da hali muna asibiti an kawo Sa’adiyya tana naƙuda idan ya so sai ki nemo izini agun Malam ki mata zaman wanka, kin san dai bata da wata kakar da za ta mata zaman wanka sai ke kaɗai a duniya” Inna Azumi ta faɗi maganad tana share ƙwallar ƙaryar da ta mammatso daga idanun nata.

 

 

“Wato da gasken dai bata haihun ba?”

 

“Haba Malam wai ya kake maida hannun agogo baya ne, na faɗa maka naƙudar take amma kaƙi yarda sai wasu tambayoyi kake min mau kamar tuhuma, ko dan ka ga yarinyar ba jikar ka bace, amma tabbas ka zama mai manta alheri lokacin yaron nan na da rai haka zai kwaso goma ta arziƙi ya zo ya gaisheka duk da ba kai ka haifesa ba amma shi ne yanzu dan ƴarsa za ta haihu zan je zaman wanka kake nuna mata wariyar launin fata?” Ka san dai shi kaɗai na haifa a duniya, shi ma su biyu ya haifa daga ita sai ƙanwarta, kuma wannan ne karo na farko da jikata za ta haihu amma kana ta yalbatsani a gaban kishiya salon wataran a min gori” Ta ce tana fashewa da kukan makirci har da su fatar majina ita ala dole ta tuno da ɗan mata da ya mutu.

 

 

Baki sake Malam ɗin ya ke kallonta, ganin dai ta daddage sai zuba kuka take ya ce

 

“Ku dama mata kowa ya sanku da goranta abin da kuka yiwa mutum, ko goranta masa a kan abin da wani naku ya masa, da zarar abu ya haɗoku sai ku yiwa mutum gori. In ba haka ba daga magana sai ki fara lissafo abubuwan da ɗanki ya mini saboda ba ni na haifesa ba, to indai tafiya birni ne ki je Allah kiyaye Allah ya sauketa lafiya.

 

 

“Haba Malam ba haka nake nufi ba na ga ma har ranka ya ɓaci, kawai ma na fasa tafiya da in tafi kana fushi da ni” Ta ƙara faɗa cikin kissa da kisisina.

 

“Lah babu komai wallahi, ai mu ma maza wani lokacin da namu laifin sai mu hana mace zuwa abin da bai dace mu hana ba, kin ga wannan ai bai dace ko kusa na hanaki ba, wallahi na aminci Allah kiyaye hanya” Ya faɗa yana sanya hannu a aljihu ya fiddo dubu biyu ya miƙa mata.

 

Hannu biyu ta sanya ta karɓa tana ta rafka godiya

 

“Yaushe zan dawo kuma?”

 

 

“Kamar ya yaushe za ki dawo ba zaman wanka za ki mata ba ai zan ce kwana arba’in ne ake zaman wanka ko an canja shi daga haka ne?”

 

 

“A’a ba a canja ba sai dai da yake haihuwar fari ce ana iya ƙarawa ma a yi arba’in biyu wani sa’in ma in mijin mai sakin fuska ne bai nuna alamar gajiyawa ba har arba’in uku ana yi” Ta ce tana ƴar dariya.

 

“Inyeee to abin ya zama hauka kuma ba zaman wanka ba, ke yanzu sai ki yi sama da watanni uku a gidan mutane yo ai har yaron ya fara zama ma, amma ana yiwa uwarsa zaman wankan haihuwarsa ai da kunya ma gote-gote da ke ki zauna a gidan yara har arba’in uku”

 

“Ni fa ba wai cewa na yi zan yi arba’in uku ba kawai dai ina faɗa maka ne abin da ake yi, amma ni kwana hamsin zan yi, sannan jar miya da naman kaza sun ratsa ni” Ta faɗa tana lashe leɓenta dan har yawunta ya tsinke.

 

 

“Ko da na ji, Allah kiyaye”

 

“Amin, amin Malam” Ta ce tana kallon Tasalla da ta cika ta yi fam kaɗan ya rage ta yi bindiga dan baƙinciki.

 

 

“To Tasallele, mu zamu tafi birni sai Allah ya ƙaddara saduwarmu, kike sana’ar man ƙuli na da nake yi dan kar kasuwar ta yi ƙasa ganin ana zuwa nema babu sai mutane su ɗauka na daina yi ne kwata-kwata amma in kina yi da na dawo sai in ɗora daga inda kika tsaya, kuma kowa ya tambaye ni ki ce masa na tafi Kano ta dabo tunbin giwa jikata ta haihuwa zan mata ZAMAN WANKA” Ta faɗa tana dariya, Malam dai kaibya girgiza a ransa yana tunanin ranar da matan nasa za su girma gashi dai sun tsufa amma in suka yi wani abin kamar yaran mata.

 

Haushi ne ya ƙara cika Tasalla wato bayan sana’arta ta waina, hallaw take sana’ar mai da ƙarago ita tana can tana cin shinkafa da miya da nama, har wata ƙwallar takaici ce ta kawo a idonta. Ganin Malam ya kalleta ta daddage ta danne ta ce mata

 

“Sauka lfy”

 

 

“Sana’ar man ƙulin fa?” Ta tambaya da sheƙiyanci.

 

 

“Ba zan yi ba” Ta bata amsa a takaice.

 

“Kin huta” Ta faɗa tana dariya dan ta lura Tasallar ta shaƙa sosai.

 

 

 

“Amma kin san dai yanzu motar kasuwa ta tafi, sai dai ki hau machine ki je Garki ki hau motar Kanon a can ko?” Malam ya katse musu maganar dan ya lura abin na neman zama fitina gwara a rabu lafiya.

 

“Eh dama yanzu mota ai ta tafi dan rana ta yi sosai dan azzahar ma ta kusa hantsi ya dubu luday”

 

 

“Yawwa a gaishe su”

 

“Za su ji” Ta faɗa tana tashi daga zaunen da take ta buɗe labulen ta fito daga turakar Malam ɗin.

 

 

Ɗakinta ta koma ta ɗakko lalle ta sanya a bakkon (Ghana mostgo) Ta ɗaga dakyar ta fito da ita daga ɗakin ta ajiye a ƙofar ɗakin ta ɗakko kwaɗo ta kulle ɗakinta ta sanya mukullan a cikin pos ɗinta. Ƙofar gida ta fita ta sanya Lawwali almajirin Malam ya samo mata mai machine, aka ɗakko jakar za a fice da ita dai dai nan Malam ya fito daga ɗakinsa ya ga Lawwali ɗauke da jakar.

 

“Azumi lafiyarki kuwa?” Ya tambaya da mamaki.

 

“Me ka gani Malam” Ta faɗa cikin nuna rashin fahimtar inda tambayarsa ta dosa.

 

“Wannan jakar ce za ki yi tafiyar da ita, kin shaƙeta da kaya kamar wanda za ki ƙaura can”

 

“Ba fa kaya bane kaɗai Malam har da bargona a ciki ka san lokacin sanyin nan kar inje ina bani-bani a gidan yara gwara na tafi da abuna” Ta faɗa tana murmusawa.

 

“To ai shikenan” Ya faɗa, suka fito tare ta hau machine almajiran Malam na ta ɗaga mata hannu, ta tsakiyar ƙauyen suka bi duk inda suka wuce ana ɗaga mata hannu alamar Allah kiyaye dan an ganta da jaka a gaban machine kuma duk yawanci an san tana da ƴan uwa a birni da yake ma ƙaramin ƙauye ne, tun da a can ne ma ta fara aurenta na fara har ta haifi ɗanta ɗaya tilo kafin ta auri Malam ɗin, da har yau basu taɓa haihuwa da shi ba. Duk inda suka gifta sai hannu ita ma take ɗagawa alamar ta tafi har sai da suka hau hanyar da za ta sada su da garin Garki L.G sanna ta sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ranta fari ƙal tana jin wani nishaɗi dan babu abin da ya fi faranta mata sama da yadda Tasalla ta shaƙa, da kuma yadda jama’a ke ta ɗaga mata hannu lallai zuwa birni da daɗi.Gabanta ne ya bada wani rass tuno da halin mijin Halimar sam bashi da sakin fuska ga rashin ta ido, tunaninta ma yadda zaman zai kasance…

 

 

To fa dandandan dan dan dan dan, ku biyo ni dan jin wannan labari mai cike da barkwanci, shin ya zaman zai kasance tsakanin masu gida da kuma ƳAR ZAMAN WANKA

 

 

 

 

YAR ZAMAN WANKA

 

(KWANA ARBA’IN)

 

 

NA

 

MAMAN AFRAH

 

 

🅿️2️⃣

 

 

Tun da ɗan acaɓan ya kaita tasha, ta biya shi kuɗinsa har gaban mota ya ajiye mata jakarta tana ta zabga masa godiya kamar wanda ya kawo ta kyauta. Mota na cika suka kama hanyar Kano, Inna Azumi ta samu wata tsohuwa mai shegen surutu irinta aikuwa suka rinƙa zuba kamar daman sun san juna, tafiya ta yi tafiya Inna Azumi ta fara gyangyaɗi a haka suka ƙaraso Tashar ƴan kaba ɗan sahu ta samu unguwa uku zai kai ta, suna cikin tafiya ta tuna cewa bata sanar da Mamar Halima ba dan dama ƙarya ta yiwa Malam a kan cewa ta ce ta taho, kawai dai Inna Azumi ta kira su gaisa sai take ce mata suna asibiti Sadiya na naƙuda shi ne fa ta shiryo ta taho ba tare da ta sanar da ita ba.

 

 

Ganin wayar babu caji ta mutu ta taɓe baki a zuciyarta ta ce

 

 

“Yo ya za a yi da ni, ni da gidan ɗana duk da dai ya mutu amma ai babu mai korata daga gidan jikokina, dole na je na tabbatar kar na fara zuwa gidan Halima(Sadiya) Na tarar an bar ta a gidansu saboda wankan jego, ko da kuwa ma hakan ta kasance dole na mayar da yarinyar ɗakinta na mata zaman wanka dan ba kasafai wasu mazan ke son matansu su je gidan iyayensu wankan jego ba” Tana cikin saƙar zucin ta lura sun kusa layin da za a ajiyeta, dan haka ta shiga nunawa ɗan sahun inda zai bi har dai suka ƙaraso ƙofar gidan, idanu ta ƙwalalo lokacin da ta yi tozali da danƙareran kwaɗo a ƙofar gidan ɗan sahu bai ankara ba ya ji ta ce

 

 

“Na shigenge ni Azumi”

 

 

 

“Lafiya dai Baaba” Ya faɗa yana kallonta da mamaki, ganin ta dage sai zabga salati take kamar an ce wani ya mutu.

 

 

“Yo ba dole ba na yi salallami ɗan nan ka ga gidan da na zo a rufe”

 

 

“Haba Baaba ya za a yi da ki taho baki sanar da mutanen gidan ba, gudun haka ne ya sa ake faɗa, gashi na ga da alama ma kamar ba a gari kike ba dan na ga lokacin da kika sauka daga mota”

 

 

“Wallahi kuwa ɗan nan ba a gari nake ba daga wani garin nake, amma na san inda zan same su, mu je tarauni”

 

 

“To Baaba” Haka ya juya kan napep ɗin suna tafiya tana ta faman surutu har suka kawo ƙofar gidan da ta nuno masa zai ajiyeta tun kan su ƙaraso.

 

 

“La’ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W, yau dai na ga ta kaina wannan wane irin abu ne kamar an haɗa baki” Ta ƙarasa faɗa tana tafa hannuwa.

 

 

Ɗaga ido ɗan sahun ya yi aikuwa ya sauke a kan ƙofar gidan ashe nan ɗin ma a kulle.

 

 

“Gakiya Baaba kin taka fawul a ce ko ina babu kowa kamar basa son zuwanki” Ya faɗa yana tuntsurewa da dariya.

 

 

“Kai ɗan nan ka kiyayeni ni nan da kake gani can gidan ɗana ne nan kuma gidan jikata kuma na san inda suke suna asibiti jikartawa za ta haihu zatona duk sun dawo shi ya sa”

 

 

“To ki musu waya mana” Bani sa caji kai bari dai ka ga” Ta faɗa tana fitowa daga napep ɗin ta lissafa kuɗinsa ta biyashi kamar yadda ya faɗa, ya fito mata da jakar kayanta kamar yadda ta buƙata.

 

“Baaba ziyara kika zo ko ƙaurowa kika yi?” Ya faɗa cike da sheƙiyanci lokacin da ya ɗaga bakkon ya ji wani uban nauyi.

 

 

“Ka ji ni da ja’irin yaro to ina ruwanka” Ta faɗa tana juyawa ta shige gidan da ke maƙotaka da gidan Sadiyar, shi kuma ya ja ya tafi yana ta dariya dan hatta yadda take magana dariya yake bashi, ga wani uban gwaggwaronta kamar bututun zuba kalanzir.

 

 

Tana shiga suka gaisa da matar ta sanar da ita gidan Sadiya ta zo a rufe, nan matar ta ce suna asibiti tun da sassafe. Matar ta ce ta zauna kafin su dawo dan ta gane kakar Sadiya ce ta taɓa zuwa gidan sun haɗu lokacin ita Inna Azumin ta zo, cewa ta yi bari ta samu ko almajiri ne ya ɗakko mata jakarta.

 

Imran ne tafe a kan machine ɗinsa roba -roba matashi ne matashi ne dan ba zai haura shekara 26 ba ɗan gayu ne dan yanzu ma yana tafe a machine ɗin sai wani dube -duben jiki yake, lokaci zuwa lokaci yana sanya hannu ya karkaɗe rigarsa duk da ba komai a jiki amma saboda kawai tsabar tsafta da ƙyanƙyami yake karkaɗewa. Imran bashi da son mutane gashi da ƙyamatar ya ga an kusanci inda yake sai wanda ya yi niyya sai kuma wanda jininsa ya haɗu da nasa. Ba ya son duk wani abu da zai shiga tsakaninsa da farincikinsa wato matarsa Sadiya yana son ta sosai saboda auren soyayya suka yi hakan ya sanya ba ya son duk wani abu da zai sa ya yi nesa da ita ko ya nesanta shi da abar ƙaunar tasa. Ya fi so koyaushe idan yana gida ya kasance tare da matarsa, gashi mutum mai yawan buƙata, shi ya sa ko yaya ba ya son wani abu ya haɗashi da Sadiya bare ta yi fushi, idan kuwa hakan ta kasance to ya kan yi iya ƙoƙarinsa ya shawo kan ta dan kar ya rasa biyan buƙatarsa dan bashi da haƙuri ko kaɗan a wannan harkar, sai ya samu matar tasa ita ma mai burin faranta masa bata so ko kaɗan ta hana shi kan ta.

 

 

Ya kusa ƙarasowa gidansa ya hango wata ƙatuwar jakar bakko a ƙofar gidan, cikin mamaki yake kallon jakar da kuma neman dalilin ajiyeta a ƙofar gidansa.

 

 

 

 

Cikin sauri da azama ya ƙaraso har yana neman faɗuwa a machine ɗin dan ba ya ƙaunar abin da zai haɗa shi da kayan wasu, dan shi akwai tsare gidan ko maƙota iyakarsu gaisuwa tsakaninsa da su dama shi ba wani yawan magana yake ba bare zaman majalissa in har ba wurin aiki ya tafi ba to yana gida tare da iyalansa, sai ko idan ya je gaishe da Hajiyarsa. Yana faka machine ɗin ya ƙanƙance idanu yana kallon jakar, kallon da ya mata ma sai ya ji yana tsantsaninta dan sai ya ga duk ta yi wani ƙura, ko kuwa dan bai yarda da jakar bane oho ya ɗago kai yana son gano yadda aka yi jakar ta zo ƙofar gidansa sai ya ji wata murya tamkar daga sama an ce.

 

“Shikenan ma na huta ga Imirana nan” Shiru ya yi tare da runtse idanunsa da ƙarfi, jin an kirashi da sunan da ba ya so kwata-kwata, kuma ma duk duniya ya san babu mai kiransa da sunan nan sai kakar Sadiya wato Inna Azumi ita kaɗai ke kiransa, kuma ya shaida muryarta dan ko daga bacci ya tashi ba zai kasa shaida muryarta ba.

 

 

 

Shi ya rasa me yasa matar nan take son takurawa rayuwarsa, sam ba ya son wannan nuna ƙoƙon usulin da take nuna masa dan yana auren jikarta, shi ko ƴarta yake aure ba ya son takurawa amma ita ta kasa ganewa, sannan duk miskilancinsa na ƙin son magana da mutane sai da ya daure ya faɗa mata cewa Imran ake kiransa dan idan ta kirasahi da Imirana nan ji yake kamar ta kwaɗa masa gudum a kan sa.

 

“Ashe ma kana kusa har nake bin gidan maƙotanku ka ganni nan saukar yanzu tsal ɗin nan” Ta ƙara faɗa tana ƙarasowa wajensa ba tare da ta jira ya ce wani abu ba, cije gefen lips ɗinsa ya yi yana ji da a ce wani ne da ban ba tsohuwa ba yake damunsa kamar yadda tsohuwar nan ke damunsa da sai ya ɗau mummunan mataki.

 

“Eh” Kawai ya ce hakan ma dan ta kasa kunne ne ta gane me ya ce amma da gungune ya yi maganar.

 

“Allahu akbar Imirana har yanzu dai kana nan da wannan mugun halin naka, kai wane irin mutum ne da baka sakewa da mutane ku yi magana ma ta fatar baki kawai ni fa kakar ka ce ba sirikar ka ba” Ta faɗa tana kallon fuskarsa da ya haɗe ta murtuk kamar zai saki kuka.

 

 

“Sauri nake” Shi ne kawai abin da ya ce, shi ma dai da ƙunƙunen ya faɗa.

 

“Oh Allah na shiga aljanna na maƙale, yanzu baka ce min Inna ina wuni an zo lafiya ba sai ka zauna kana min magana kamar mai ciwon haƙori, ko kallon arziƙi na kasa samu daga wajenka”

 

Banza ya mata ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan.

 

Inna Azumi kuwa baki ta taɓe, dan ta lura in ta ce za ta ga yadda take so to zuciyarta sai ta yi bindiga bata samu yadda take son ba, gwara ta lallaɓashi a rabu lafiya, bare ita da ta zo dandalar arziƙi.

 

“Sa’adiyyar ta sauka ne?” Ta faɗa tana kallonsa yana cire kwaɗo daga jikin ƙofar gidan.

 

Bai bata amsa ba a take ta tuna da katoɓarar da ta yu, dan dama Sa’adiyya take kiran Sadiya amma saboda kwainane irin nasa ya ce wai ta fiya ɓatawa mutane suna ganin baya iya faɗar Sadiya sai Sa’adiyya sai take cewa Halima saboda jarabar Imran ɗin dan duk ranar da ta zo gidansa haka zai yi ta mita a ƙunƙunen nan har dai ta ɗan canja sannan ta samu salama.

 

 

“Na ce Halimar bata sauka bane?” Ta gyara sunan dan ta matsu ta ji halin da jikarta ke ciki.

 

” Ta sauka” Ya faɗa a takaice yana tura ƙofar gidan ya shige ya bar Inna Azumi a tsaye baki sake, da ya shige ma sai da ya ɗan turo ƙofar.

 

 

“Yau na ga abin da ya isheni, a haka zan yi har kwana hamsin ɗin, ana wannan zaman doya da manjan, taɓɗi aikiwa duk abin amarya sai an sha manta wallahi ko me za ka yi sai na zaina ZAMAN WANKAN nan dan ban ga abin da zai sanya na fasa ba dan kana wannan fisfigar” Ta faɗa a ranta tana tura ƙofar ita ma ta shiga gidan tare da jan jakarta ta shigar da ita dakyar saboda nauyi, Imran da ya dawo domin ya ɗakkowa Sadiya zani saboda zannuwan sun yi kaɗan yana cikin sanya zanin a leda ya jiyo ƙaran jakar Inna Azumi tana janta ƙiiiii.

 

“Me yasa matar nan ta shigo min da ƙazamar jakarta gidana” Ya faɗa a ransa, ya yi sauri ya fito daga ɗakin ya dawo falo ya sanya hannu ya fusgi labule da ƙarfi ya fito daga ɗakin tare da rufo ƙofar dan ma kar ta yi gigin shigar masa da jakarta ɗaki dan ba ya jin zai iya bacci ma idan jakar tana ɗakin saboda ƙyanƙyami.

 

Baki sake Inna Azumi ke kallonsa har ya gama kulle falon, yana wani ɗaɗɗaga kai kamar ya ga kashi ya ce.

 

 

“Asibiti zan koma” Sai da Inna Azumi ta saurara da kyau sannan ta gane me ya ce.

 

 

“Yo ni ma ina na ga ta zama, ai ba zama wai an ɗaurawa karya zani, mu tafi sabitin in je in gan su dan can ma gidansu na fara zuwa a rufe, na zo nan ɗin ma ashe dai basu dawo daga asibitin ba”

 

 

“Eh” Kawai ya ce dan shi kamar mai ciwon baki haka yake ba ya son magana ko Sadiya sai ita ta yi ta masa hira shi dai sai umm da um, um kawai ko da zai yi maganar ma to ba wata mai yawa ba sai dai kuma ranar da ya ga dama sai ya yi maganar amma ba sosai ba.

 

Yana fitowa ita ma ta fito ya rufe gidan, aikuwa sai ga wani mai napep zai wuce ya tsayar da shi ya ce ya ɗauketa sai ya biyo bayansa.

 

 

“Wannan yaro da mugun hali yake” Ta faɗa tana taɓe baki ta shiga napep ɗin suka bi bayansa. Maƙociyar Sadiya kuwa da ta leƙo ganin Innar bata dawo ba, ganin Imran ya sa ta juya ta koma gidanta dan ita ko gaishe shi ta yi banza yake yi in ma yana amsawa to ita bata ji, sai ma ta daina gaishe da shi ganin rainin wayo da rainin hankalinsa dan ita tana mamakin yadda Sadiya take zaune da mutum kamar gunki.

 

 

Tun da suka fara bin Imran yake zabga uban gudu kamar zai tashi sama, da yake kuma unguwar kwana -kwana ta yi yawa ga ƙurunƙusai sai ya zama na Inna Azumi tana ta tangal-tangal a cikin napep ɗin saboda yadda ɗan sahun shi ma ke zuga gudu abinsa. Inna Azumi hannu ta sanya ta kama ƙarfen napep hagu da dama ta ƙanƙame dan ji take gabaɗaya kamar juyata ma ake yi. Idanu ta ɗaga ta sauke a kan me napep ɗin fa bai wuce shekaru sha tara zuwa ashirin ba, ga wani uwar suma a kan gashin ya yi cibir-cibir har da matajin kai a soke a jikin gashi, ga wani uban kiɗa da ke tashi a napep ɗin tamkar ma kiɗan jijjiga napep ɗin yake.

 

 

“Wai ni kai kwa yaro bahaushe ne?” Inna Azumi da bakinta baya shiru ta tambaya tana mai ƙuga maganar da ƙarfi yadda zai ji..

 

“Ke tsohuwa da wane yare na miki kama”?” Ya faɗa yana sakin wani uban fito da duk ƙaran kiɗan amma bai hana fitowar fiton ba.

 

 

“Ai tambayrka na yi dan na ga alama hausa bara ganka ba”

 

 

“Inyamuri ne ni, ko na miki ne, kina ciki”

 

“Amma wannan yaro an yi shegen yaro yanzu ka dubeni tsofe-tsofe da ni ka ce ina sonka? Amma gidanku ba manya”

 

 

“Sun ƙare” Ya bata amsar yana sanya hannu ya ciro matajin ya ɗan taza kan ya mayar ya soke.

 

“Baby kin yi shiru”

 

 

“Uwarka ce baby, wallahi tsakani na da kai Allah ya isa, ni Azumi na ga ta kaina.

 

“Ba dai shaƙa kika yi ba Hajiya, ban da ƙauyanci dan na ce baby ba wai yarinya nake nufi ba, wasan kaka da jika ne fa”

 

 

“Ƙauyancin uban wa? Na ce ƙauyancin uban wa, to tun kafin a haifi uwar mai sabulu farfela take da farinta” Ta faɗa tana jin kamar ta saki fitsari dan gabaɗaya an dagula mata lissafi ga yunwa ga wani fitsari da ya cika mata mara ga wannan jijjigar da napep ɗin ke yi sai ta ji a ranta ta fara ɗan da na sani kaɗan ba da yawa ba na tahowa ZAMAN WANKA, da tana gidanta da yanzu ta ci ta ƙoshi tana bacci ko kuma tana kama ƴan kuɗaɗenta daga masu zuwa siyan mai da ƙuli amma wani ɓangaren na zuciyarta sai ya bata ƙwarin gwiwa.

 

 

“Kar ki karaya bayan wuya sai daɗi, daga yau ne fa wahala ta ƙare za ki fara cin kayan daɗi” Wani murmushi ne ya suɓuce mata har sai da ta ɗan rausaya kai.

 

 

“Ka daina zabga wutar nan haka gudun ya yi yawa”

 

“Bakya ganin yadda wanda muke bi yake gudu kamar zai tashi sama.

 

 

 

 

 

“Rabu da Imirana mugun hali ne da shi ka yi tafiyarka a hankali ka ji”

 

“In ya ɓace mana ke zaki kaimu wajen da za ku je?”

 

Shiru ta yi bata ƙara magana ba, wata kwana Imran ya shiga dai dai wani gida ya faka machine ɗin ya sauka ya faka machine ɗin ko kallon su Inna bai yi ba ya tura gidan ya shiga.

 

“To ki fito mana tun da mun zo ashe ma babu wani nisa sosai”

 

 

“Nan ne asibitin?”

 

“Asibiti kum?”

 

“Eh mana asibiti za mu je”

 

“Haba Hajiya nan ya miki kama da asibiti nan ai gida ne”

 

“Gida kuma, wai ni me ya sa Imirana ya raina mutane ne haka, ya za a yi ya shige wani gida ya bar ni ko bayani ba zai mini ba” Ta faɗa tana saurin sakkowa daga napep ɗin ta ce mai napep ɗin ya jira ta, a fusace ta tura ƙofar ita ma ta shige tana shiga ta ga wani ɗaki da ke a farkon shiga gidan, bata yi wata- wata ba ta bankaɗa labulen kawai sai ganinta suka yi bakam ta shigo kamar an jefo ta.

 

Wani kallo da Imran ya jefawa Inna Azumi shi ya sanya ta wayance ta ce

 

 

“Ikon Allah ashe ba mu zo asibitin ba, wallahi duk zatona ɗakim haihuwar ne nan” Ta faɗa tana saurin juyawa ta fito da sauri dan shi da wani da alama abokinsa ne ya miƙo wa Imran ɗin zamzam a robar zamzam. Abokin kuwa yadda Inna ta yi ya matuƙar bashi dariya, Imran kwa tsaki ya yi ya fito ya hau machine ɗin.

 

Inna kuwa mai napep ganin ta fito da sauri sai abin ya bashi mamaki har ya so bashi dariya.

 

“Kin masa magana?” Ya tambayeta lokacin da ta fito ta shiga napep ɗin.

 

Inna da gabaɗaya take a ruɗe ba wai kallon da Imran bane ya sa ta gigice ba, abokin nasa ne babu kaya a jikinsa daga shi sai ƙaramin wando wanda ake kira inpant, to har ga Allah bai san ya yi wawan zama ba ashe Inna ta hango abu ya leƙo ta ƙafar wandon wannan ne abin da ya ruɗa ta dan ita yaushe rabonta da ta yi ido huɗu da bananar ma ta manta, dan su yanzu an tsufa, ganin bananar abokin Imran ne ya ruɗa ta, hakan ne ya ruɗa ta ta dawo da sauri har tana neman yin tuntuɓe. Dan da alama ɓa abokin nasa gwauro ne dan ɗakin nasa a bakin ƙofar gidan ne daga ciki kuma tana jiyo hayaniyr mutane daga cikin gidan.

 

 

 

 

” Ashe ruwa zai kama” Ta faɗa dan ta waske amma a ranta sai salati take ko idanu ta rufe sai ta ga abu kawai. Da haka dai har suka iso asibitin bayan sun sha uban gosulo. A wurin da aka tanada dan ajiye napep a nan ya sauke Inna haka ya yanka mata uban kuɗi ta bashi, dan Imran ko tsayawa bai yi ba bare ta sa rai zai biya kuɗin napep ɗin.

 

 

Tana bawa mai napep ɗin kuɗi ta fara sauri-sauri gudu-gudu dan ta tarar da Imran dan machine ana iya zuwa da shi har ƙofar ɗakin da mutum zai je da ke asibitin na gwabnati ne, ashe da ɗan tazara zuwa ɗakin haihuwar dan haka kafin Inna ta kawo ta gama jigata dan ma tana iya hango Imran ɗin da yake wurin babu kwana bare ya ɓace mata.

 

 

“Oh ni da bani da kuɗi yau da na tagayyara, wannan yaro ko kaɗan bai san mutunci ba, uwarsa kwa ba haka take ba lallai albasa bata yi halin ruwa ba, na ɗauka shi zai biya min kuɗin tun da shi ya tsare ɗan sahun amma sai ni na biya, ko ma ya tsaya idan ma ba zai biya ba, sai ya ce Inna ki biya kuɗin amma shiru maƙatau babu niyya wai ango ya kwana da wando” Take ta zancen zuci har ta ƙaraso wurin ɗakin haihuwar.

 

 

 

 

 

Mai son shiga grp ɗin dan samun cigaban buk ɗin ya mn mgn 09030283375

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment