Littafan Hausa Novels

Yar Mijina Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Yar Mijina Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Yar Mijina

 

*( Love, Funny, Romantic)*

 

**Page-002**

 

*Writing By*

__(Asma’u Aji Ibrahim)__

*Asmeety*

 

 

 

**Elegant online writer’s**

 

_Littafin SASEEN na kuɗi ne _

Reglr group ₦500

Vip group ₦1000

Special ₦1500

Account Number:( 3055025223) Polaris Bank

Name: (Asma’u Aji Ibrahim) . Send a credit card 07089540330 Airtel or 07047201029 MTN send Advice to this number ( 07089540330 Whatsapp)

 

 

 

 

**El-Yakubh House**

 

Baba ne suke zaune a Masalacin dake kofar gidan inda Liman akasa ranar auren Amman shida Ameena Abbi, Dad, Uncle, Abbu sai y’an anguwa da kawun Meena sai baffan ta da dai sauran su inda akasa ranar auren 2month (wata biyu) kenan

Baasan Maci Tuwo Ba Hausa Novel Complete

a gida kuwa Mama ce suda Ammi, Ummu, Auntie sai Mom sai Kuma dangin Mama inda aka kawo kayan lefen Meena basu Wani jima ba suka watse kowa ya tafi gidan sa inda aka bar Auntie Fauziyya wato kanwar Mama suna wasu tattaunawa akan yanda za’a shirya auren

 

A hankali ta bude get din gidan tana leka ko zataga mutane amma babu kowa hakan ba karamin dadi taji ba ta shiga tana fadin”yawwa nagode Allah da yasa wannan jarababben Mai gadin baya kusa” sanda take tana nufar kofar mashigan falo , Mai gadi da ya fito daga bandaki ya hangota tana sanda girgiza kansa yayi yace “wannan yarinyar Mai shegen wayon nan ko” a jiye butan hannun sa yayi yabi bayan ta Shima yana sanda Meera na kokarin shiga falo Mai gadi ya kamo hannun ta yace”wana kama yanzu” murmushi tayi tace “aa kayi hakuri dan Allah baba tsoho kadda ka gayawa Mama rufamin asiri” manna mata yayi ya fara shiga falo kamo hannun sa tayi tana cewa”haba tsoho na kana son nafasa auren na kane?”

manna mata yayi zai shiga tace”shikenan yau dai wani ya rasa ice ream ” aiko da wuri ya juya yace”haba matar ai baza muyi haka dake ba ”

Kau da kanta gyafe tayi tace”aa ajedai a fada yau dai ni kadai zansha abina”

“Haba matar ai kya ta daban ce kinji” murmushi tayi tace”to kayimin alkawarin bara kafada ba?”

“nayi alkawari habibiya ta” hannu tasa ta ciro da roban ice cream guda biyu ta Mika masa tace ” ajiye mana a cikin fridge naka anjima musha kaji?” “To y’ar lelen Baba” daga haka ya karba yayi hanyar dakin sa ita Kuma ta shige falo tana dube dube

Idanun tane suka sauka kan kyawawan akwatuna masu kyau kala 5 a jere a falon murmushi tayi tace “ayya Sweetheart akwatunan sunyi kyau” daga haka ta shige bedroom tana shiga ta Sami Meena tsaye gaban Mirror tana taje dogin gashin kanta

Murmushi Meera tayi tace”Uhmmm Amarya ansha kyau” manna mata Meena tayi taci gaba da tashe kanta

ganin haka yasa Meera yin murmushi tace”haba Sweetheart maye yayi zafi harda fushi ”

“Babu ” cewar Meena tana ciro da kaya a wardrobe

Meera ganin da gaske Meena tayi Mata fushi yasa ta rungume ta ta baya tace”Am so sorry dear please”

Zame jikinta Meena tayi tana kallon Meera tace”nifa banayin ki fa”

Murmushi Meera tayi tace “haba auntie naaaa” harara Meena ta galla Mata ta bugi bayan ta tace”Shegiya bakyajin magana ko?” “Aww zafi fa Auntie Meena” tana rungume ta tace”da gaske?” Meera tana zunbura baki tace”eh mana” tashi Meena tayi tana Shirin ta buge Meera

ganin haka yasa Meera tashi ta gudu zuwa bathroom tana dariya

itama Meena dariyar tayi tana girgiza kai

 

Da Daddare kuwa suna zaune kan draining table suna cin Abinci

Meera kallon Mama tayi taga ko kallon ta batayi tunda ta shigo dazu ko magana taki tayi Mata Hakan yana damin ta Amma sabi da tsoron Mama da take ji ta kasa cewa komai tayi shiru har suka gama cin Abincin Mama bata ce da ita ko ci kanki ba

suna zaune a falo kallo suke gabaki dayan su Mama kallon Meena tayi tace “Meena tashi kije ki dauko min waya ta a bedroom”

“To ” cewar Meena tana tashi da sauri Meera tace”zauna bara naje na dauko” tashi tayi ta nufi bedroom din Mama

bayan ta dauko wayan ta kawo Mata ta zauna gyafen ta tace”Mama ta nasan fushi kikeyi dani ko? Please Stop it Mom wllhy banason fushin nan naki yana sani damuwa please just finished Me” kallon ta Mama tayi ganin har hawaye take yasa ta bugin bayan ta tace”Stop crying idan kika bari hawayen ki suka zubo bazan daina fushin ba” aiko da sauri tasa hannu ta goge tana murmushi tace “Kinga na goge wllhy”

“Good girl” cewar Mama tana rungume ta

Baba da Meena murmushi suke suna kallon su

 

Bayan sun shiga daki wayan Meera ce tayi ringing tana dubawa taga Zee picking call din tayi tace “Zee yah?”

“Lafiya ba Lau ba” cewar Zee

“Kamar ya akwai wata damuwar ce?”

“Eh Amma na solver komai”

Numfashi Meera taja tace”maye ya faru tukunnan?”

Zee tace”ai wancan yarinyar ce taki shiga boss ya Kai ta gida sai da tasa na kira Dad din ta kafin yazo ya dauke ta suka tafi”

Saki Meera taja tace “bansan meyasa ba just kawai naji na tsani yarinyar Wallahi Yarinya sai shegen tsiya haba”

“Sai ayi hakuri ko?”

Murmushi Meera tayi tace “ai dole ne ya na iya”

A haka sukayi sallama kowa ya kashe wayan sa

 

 

** Junaid House**

 

Bayan sun gama cin Abinci kowa ya nufi bedroom din sa haka Shima bedroom din Ammi ya shiga ya same ta tana zaune a bakin bed tana rufe Al Qur’an zama yayi gyafen ta yana kwantar da kansa a kan shoulder din ta

Murmushi Ammi tayi tace “You tried right?” gyada Mata Kai yayi yana lumshe Sexy eyes din sa

Shafan Kansa tayi tace “bara ka tambaye mu wata nawa akasa ranar auren kaba?” Zunbura baki yayi kamar Wani karamin yaro “Uhmmm” kawai yace

Girgiza Kai Ammi tayi tace “2 Month aka sa hope you like it?” Gyada Mata Kai yayi kafin ya Mike yayi Mata sallama ya nufi bedroom din sa

 

 

 

 

**Na, ima side**

Zaune take bakin bed tana cije lips tace”shittt hmmm!! dole zanyi duk yanda zanyi a fasa auren nan sabida Amman nawa ne ni kadai Wallahi” Murmushi Auntie tayi tana dafe kafadar ta tace”Don’t worry Daughter nima Ina bayan ki kiyi koma maye idan har Kinga hakan zai gamsar dake”

juyowa tayi tana kallon Auntie tace”Auntie inason Amman tsosai inason sa har cikin Raina Auntie You Help Me?”

Murmushi tayi tace “Yes of course idan shine hanyar samun farincikin ki kinji”

Rungume ta tayi tana murmushi tace “shiyasa ako da yaushe nake Kara godewa Allah daya ban Uwa Mai son ganin farinciki na Love you”

“Love you too goodnight” murmushi tayi tace “good night” daga haka Auntie ta fice daga dakin Na, ima tana tunanin ta yanda zata taimakawa Y’ar ta domin Samin abinda take so

 

 

 

** Ashraf Side**

 

Kwance yake yasa laptop ya gaban sa yana aiki wayan sa ce ta dau kara daukan wayan yayi yana kura masa ido

ganin Mai Kiran nasa yasa shi yin picking jiyayi ance”Haba Sweet aiko babu alwala akwai wanke fuska haba Ashraf meyasa kake min haka meyasa kake wulakan ta ni sabida inason ka shine kake yimin wulakanci?”

Shiru tayi tana jiran amsawar sa ji tayi yace “Finish? If you finish tell me”

“Yes I’m finish but…..kafin tayi magana ya kace wayan yana Jan tsaki

 

**Da Washe Gari**

 

Kwance yake idanun sa a lumshe suke kamar mai yin bacci ji yayi anfado Kansa an rungume sa dan karamin Kara yasa yana fadin “Ashh!!”

Dagowa tayi tana kallon sa ta kyalkyale da dariya tana yi masa kwakulkuli Murmushi yayi yana kamo hannun ta dariya take tana fadin “Papa get up” Bude sleeping eyes din sa yayi yana kallon y’ar karamar yarinyar da Bata wuce shekaru bakwai ba (7 years) a duniya ba kallon jikinta yayi yaga tana sanye da kayan baccin da ta kwana dashi ganin hakan da yayi ne ya tabbatar masa da cewa taki Yarda kowa yayi Mata wanka tashi yayi da ita a jikinsa yayi hanyar toilet yana zuwa ya hada ruwan dumi yayi Mata wanka tas ya fito da ita zaune ya Sami Ammi tana jiran fitowar su tana ganin su ta saki Murmushi tana kallon y’ar karamar yarinyar tace” tunda Papa yayi Miki wanka sai kizo na shirya ki kadda Shima yayi latti ”

“Okay Grandma” kamo hannun ta Ammi tayi tana kallon Amman tace”Wannan yarinyar bansan mai yake damin taba tunda ta fara zuwa Kids Place ta canza ” Amman kallon yarinyar yayi yana nazari can Kuma sai yace”Sabida bata Saba da wajan bane Ammi”

Numfashi Ammi taja tace “Maybe Amma inaganin akwai dai Wanda basa Shiri da ita a wannan wajan dan kullum idan tazo sai yace Matar batada mutunci tana yi Mata tsawa kasan Kuma Granddaughter babu abinda yake Bata tsoro kamar tsawa ai ” gyada Kansa yayi

Kallon yarinyar Ammi tayi tace”Khushi tell Me wacece Matar da kike yawan surutu akan ta maye sunan ta Uhmmm?”

Cikin murya irin ta yara tace”Wai Auntie MEERA!!”

“Ikon Allah” inji Ammi tana kamo hannun ta tace”Muje na shirya ki” fita sukayi

Amman binsu yayi da ido har suka fice daga dakin

Toilet ya koma domin yin wanka

 

 

 

**El-Yakubh House**

“Kya kijira ni gani nan zuwa kibani 50mnt ” tana gama fadin haka ta dauki Jakarta da laptop din ta sai key din Motan ta ta fice a falo ta Sami Mama da Meena suna tsaye tana ganin su tace” Lafiya dai nagan ku a tsaye haka?”

Meena ce tace “Eh Lafiya Lau ”

“Meera ki raka Meena z…….Mama Ina Kuma zan raka ta?” Ta kwabce Maganan tana turo baki harara Mama ta dalla Mata tace”gidan Uban ki Shegiya Mara kunya kawai ” tana kallon Meena tace”Meena oya ku tafi naji Kuma kinyi Mata Wani Abu ko da gunguni kikayi naji labari idan kinzo gidan nan sai naci Uban ki” tana nuna Meera da yasa “To Mama sai mun dawo” cewar Meena ita ko mutuniyar ko uppam Bata ce ba tayi hanyar waje tana turo baki

 

A hanya kuwa ko kallon inda Meena take taki yi tana tukin ta “kinsan inda zamu ne?” Cewar Meena tana kallon ta

Manna mata Meera tayi taci gaba da tukin ta jan bakin ta Meena tayi tana kallon duniya

“Ina zankai ki?” Yanda tayi maganan yaso ya bawa Meena dariya Amma dan gudun matsifar Meera haka ta hadiye dariyar ta tace” Junaid Gold Company Wanda yake Western” juyowa tayi ta kalleta tace”Amma Meena maye zakiyi acan Kuma?”

“Bakisan cewa yaron gidan zan aura ba?”

“No bani da labari ai” cewar Meera

Murmushi Meena tayi tace “To yanzu dai kinji ai”

“Amma maye zai Kai ki can Kuma?”

“Eh Mahaifiyar sace ta kira Mama wai aiki yayi masa yawa idan babu damuwa naje mu gaiza mu fahimci junan mu wai”

“Kwal Uban can” Wani kallo Meena tayi wa Meera tace “Amma Meera Mama bata hana ki irrin wannan zagin ba?”

“Idan mun koma ki fada Mata Ok?” Tace tana Mata Wani irrin kallo “wai in Banda rainin hankali bama shi zaibar aikin sa yazo yaga Matar da aka nema masa ba Kya zakije gun mijin da aka nema Miki sai kace Kya Zaki aure shi haba Kai Ina” tana bugun Stalin Motan cikin jin haushi tace”Wallahi da nasan wajan sa Zaki Allah koya Mama zatayi bazan rakaki ba sai dai ta dake ni yafi Wallahi da Wani ido zai kalle mu yace ita da kanwar ta ta rakota sunzo Kai” kasa karasar da maganan tayi duk haushi ya kamata ita dai uwar hakurin shiru tayi tana kallon Meera a haka har suka isa Company

suna zuwa kuwa suka shiga ciki bayan sunyi Parking Motan su a Parking Space

Suna shiga ma’aikatan Company suka tarbe su Daman an sanar musu da zuwan su waje Mai kyau suka ajiye su kafin 30mnt har an cika gaban su da kayan motsa baki kala daban daban tabe baki Meera tayi tace “duk da Hakan dai baka burge ba” kallon ta Meena tayi tace “Haba Meera yanzu idan suka jiki fa ”

“Suwa kenan?”

“Ma’aikatan mana”

“So What Dan sun jini Mtswwwwwww” taja saki tana tashi tsaye

“Ina Kuma Zaki ”

Kafin Meera ta bawa Meena amsa Wani Dan saurayi ya shigo yace”Kuyi hakuri fa Oga yana dan Meeting after 30 minutes zai fito sorry kujira sa yace”

” A a babu damuwa zamujira” inji Meena

“Yawwa Kinga ko Daman ba son ganin sa nake ba Kinga fita na”

“To ni kadai zakibari kenan?”

“Eh kijira sa ba?” Tace tana fita daga dakin

Girgiza Kai Meena tayi tace “Allah ya shirye ki Meera”

 

Tana fita ta fara yawo a cikin Company babu inda bata zaga ba Wani Office ta hango Wanda kyaun sa yaja hankalin ta Murmushi tayi tace “dole zan shiga cikin Office din nan nagani”

Tana kokarin shiga Office din dai dain Shima Amman yana kan fita hannun sa rike da Cup Wanda yake dauke da Tea a cikin ya juya yana yiwa Ma’aikacin sa magana ita Kuma Meera tana kokarin Sanya wayan ta cikin Jakarta sukaci karo nan Tea din ya zubu jikinta Kara tasa tana fadin”Kan Uban can……..

 

 

 

 

*More Comment*

*More Typing*

*Share fisabidillahi*

 

**~~No Editing Sorry pleases~~**

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment