Littafan Hausa Novels

Yar Goggo Hausa Novels Complete

Written by Hausa_Novels

Yar Goggo Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ƳAR GWOGGO !!!

 

Takensa(bawa baya wuce kaddararsa)

WRITTEN

BY

SAYYADA ..

 

Book 1

Pg 1&2

 

Paid book 300 ko katin waya ta

Phone number

09021796569

 

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI DA YABANI IKON RUBUTA WANNAN LITTAFIN MAI KUNSHE DA ILIMANTARWA DA NISHADANTAEWA HAR DA FAƊAKARWA.

 

Ƴar Gwaggo kirkirarren labari ne amman akwai darasi aciki banyishi dan muzantawa ba indai yazo dai dai da labarin rayuwar mutum Amin afuwa . sannan yana mana nuni da kada muraina kowa dan bamusan mai zai zama nan gaba ba , kuma mudinga fadin Alkhairi akan mutane . NASIHACE

Sarauniyar Zuciya Hausa Novel Complete

*************************

KAUYEN KUKAWA

 

” Tafe nake ina raira waƙar da jiya mallamar mu ta makaranta ta koya mana…..ji nayi ance iyar GWOGGO!! , najuyo naga wane dan rainin wayonne yake tsokanata yau , akullum inhar nafito sai an tsokaneni ,

 

ashe salisu ne daman shi nazo nema dan na anso kudin KOSAI ” nace kai salisu ina kudin kosai na ” kai kullum in dai kaci bashi bakka biya , to wallahi yau sai kabiyan ” kee Deeje anki abiya tunda ma rashin kunya kikemin , yayi wuce warsa ya barni asaye nace, kan ubannan yau zakasan da Deeje kake, dutse na ɗauko nace, salisu juyo ka gani…. Aiko yana juyowana wulla mai dutse a goshi.. ji kake kauuu.. na ruga aguje..nayi gida abina ,

 

shiko salisu rike wajen yayi yana ihu!! yana aradu zakici ubanki Deeje kuma akudin kosanku innabiya shege nake …. Kan kace kwabo jama’a suntaru sunawa salisu jaje dan kuwa yaji rauni sai jini ke zubowa agoshinnasa gashi yakumbura , pharmacy aka kaishi dan ada katar da zuban jinin, aka wanke aka manne masa bandeji , daga cen yawuce office na iyan sanda mota guda sukayo gidan su deeje .

 

Deeje ko ina shiga gida na tarar Gwaggwa ta gama aiki har abinci an ajiye min nace washh !!! nagaji ,dan ƙaramin madafar abincin mu na nufa na debo abinci na zauna nafara ci …. Gwaggwa ko dajin ana taba kwanuka a kitchen tace” lallai bunsurun gida inna mai kunu!! !yau kwananka ya kare ta dauko katon katako tayo madafar abincin da niyyan rafkamai kawai taga ashe dai Deeje ce….tace ke Deeje wallahi yau da kin ziyarci lahira , ai nadau wannan” bunsurunne ” amman bana hanakinshigowa ba sallama ba.

 

Kofan gida mukaji ana bugawa…. Kamar za a balleta !! Nace bari inleka bazai wuci salisu bane nayi kofan gida, ina budewa ko naga wani dan sanda da katon ciki da kulki ahannu ihuuu nasaka … Gwaggwoo Kitaimakamin zasu tafi dan! i atake nafara fusari a wando dan bana kaunar ganin iyan sanda”

 

yace heeee shut up your mouth … Nace aradu bani bace oga mai tumbi , kana wa Allah ka kyaleni , ya juya yace wa salisu is she d suspect? …

 

Aiko sai ga Gwaggwa ta fito , tace meke faruwa ne ni Hajara me zan gani !! Salisu yace wannan yarinyar ce tamin haka kuma inaso itama ta dandana abinda tamin !! What !!!! Akan wannan yarinyar kasa muka dau rundunan iyan sanda mota guda , hee how old are you ?nace wayyo na shiga uku Gwaggo wai prison zanci har na mutu … Da turanci yafada … Aiko Gwaggo har kasa ta durkusa tana iyallabai kar katafi da jikata wlh bamu da kowa sai Allah… ,

 

Wani daga cikin iyansanda yace cewa akai shekarunki nawa …. Nanko goggo ta tashi tace aiko zatakai shekara goma sha daya …. Yace oga yarinya ce … To me yafaru har kika ji masa rauni haka….nace zuwa nayi na anso kudin kosai, yau kusan kwana uku yaci bai biya ba , shine yace wai inzo da daddare na ansa , shine na masa haka ….salati Gwoggo ta tafara tace….. salisu amanar Allah zakaci wannan yarinyar amanace gareni …tafashe da kuka yace …wlh Gwaggo sharri ta lakamin ba haka akayi ba …. Dan sanda daka mai sawa yace… Wato kune masu ɓata yara ko zakayi bayani ,” arrest him “yace wa sauran iyan sanda atafi dashi .

 

Muka koma cikin gida, aiko cikina yaruɗe nayi bandaki da gudu ….nafito duk na galabaita nace oh ni Deeje yau naga ta kaina… Gwaggwa tace deeje zonan, nazo na zauna akusa da ita ” tace fadamun gaskiya deeje nasan halinki me yafaru dazu da nace ki anso kudin kosai agun salisu ” nace Gwaggwa kinsan halin salisu cewa yayi bazai biya ba shine namai haka, tace” deeje Yakamata kinutsu yanzu kam tun kina ƴar shekara uku kike jawo mun tashin hankali, yanzu Abin ma harda iyan sanda deeje”

 

nace kema kinsan ni bana shiga sabgan mutum amma in aka shiga tawa to bana bari …..nace bari in ɓarza waken ƙosai ko Gwaggwa, natashi nafara aikin wake .

 

****

Washegari da wuri natashi na dau kayan tuyan ƙosai na fitar rumfar da Goggo take tuya! Anan bakin layinmune , na ajiye kayan nawuce na kai markadan wake, nadawo natar da Gwaggwa har ta hura wuta ni take jira , tace sannu deeje, yaukam kin dan jima ko da layine , nace ba wani layi kawai Habibah ce da shege ganda a hankali take nikawa , na ajiye nace zanje na shirya zani makaranta kinsan mun fara jarrabawa , tace to ki hanzarta fah kibiyo ki anshi ƙosan kitafi dashi nace to nayi gida .

 

Bayan nashiryane nayi wajen Gwaggo na anshi ƙosan da kudin mota dan hawan bus , saboda makarantar a bakin gari take “,KUKAWA PRIMARY SCHOOL” makarantar Gwamnati ce tazo tagina mana a ƙauyenmu ( kukawa) karamar garine amman akwai ta da jama’a , sannan ko wacce lahadi muke cin kasuwa har iyan birni suna zuwa cin kasuwan kukawa ba abinda babu daga dabbobi har kayan lambu, kayan miyan gargajiya da na abinci .

 

Bayan muntashi ne muke kokarin shiga bus damanni ba wanda yake iya ja dani , dan kuwa za ayi tashi tashinan hankali, Bus in iyan makaranta ne acikin , zeenatu ce yau aka hankade tafado daga motar wai ai ba gun zamanta bane , inji fauziyya tayi shigewarta ta zauna , aiko nima na hankado fauziyya ta fado kasa dan kuwa ina cike da ita nace , ke wacece da zaki hankade zeenatu bayan tarigaki zama, motar ta ubanki ce !

 

Cikin jin haushi fauziyya ta tashi ta rikoni sai ta jehuni nima , aiko window motan nakama da kafa na hanka ɗeta ta sake fadiwa , haba kowa yasa dariya daman haushi fauziyya kowa yake ji akwai ta da nuna gadara dan wai motar ta mijin yayar tace , tace to wallahi daga yau bazaku sake shiga motar nan ba , dan kuma bata ubanku bace , aka sake kwashewa da dariya , nace ai mu dole ne mushigeta mota kam ta uban kowace ….nan ma aka sake shekewa da dariya, cikin fushi fauziyya tashigo ta zauna harara ta dankamin nima ko na rama dan ba amin inkyale , haka dai muka iso unguwar mu …

 

na sauko nayi gida Salisu nagani a kofar shagonsa yana saye yana kallona yace ke ƴar Gwaggwa!!! Nayi banza dashi yace ” zakishigo hanuna deejee sai kin yabawa aya zakinta ”

 

nayi cikin gida abina , kayan makaranta nafara cirewa nayo madafar abincin ina maganar zuci……”

 

Yau ko me GWAGGO ta girka mana … Naji ance deejee zonan , nace kai sohuwar nan kina da damuwa , nashigo ta nanan a daki tace ” aiko ga abincin ki anan muddin bakiyi sallama ba bazan baki ba ” nace kabdijam da a hanani abinci gara a hanani wanka …komawa kofar gida nayi nadinga tafka sallama harda ta iya shege !!!!! Gwaggo abin ya isheta tafito da wani kwanu a hannu ta wullamin na sunkuya ina dariya tace” deejee naga randa zakiyi hankali ,sai ki wuce kidau abincin kin , aiko da gudu nayi daki na fara ci ina santi dan Gwaggwa gonar iya girkice , sai da nayi tasss da abinci na tashi nayi sallah na koma bacci dan akullum sai nayi bacci bayan na dawo daga makaranta kafin natafi karatun allu ……

 

*********************

Yau take asabar bamu da makaranta kuma duk sanda ba ni da makaranta ninake soya ƙosai Gwaggwa tadinga saidawa , inacikin sai dawa sai ga Auwal yace “mutuniyar kwana biyu kinyi wuyan ganin” nace Auwal kenan bakasan gidanmu bane da zakace nayi wuyan gani ,

 

nacigaba da tuyata yayi murmushi yace “” in dai na biye miki yanzu zamuyi fada”” cen sai Bello yace waike tundazu nake jiranki kizubamin kosai sai kika mikawa Mallam Hashimu alhalin na rigasa mikamiki kudi, to indai za’amin wulakaci adawomin da kudina “”

 

Mallam Hashimu yace “” ayya yaronnan aibansa kamika mata kudi ba shiyasa na ansa amman kayi hakuri””

 

nace baba Hashimu wane irin hakuri kake basa indai bazaijira ba ba a dole sai mutum yayi gaba abinsa , ko kollonsa banyi ba naci gaba da tuyata . “””

 

Yace deejee ni kike gawaya haka ke harkin isa , to bari kiji abinda kikewa wasu su kyaleki ni baki isa ki min ba dan kuwa tattakaki zanyi “”

 

Na mike saye nace kai Bello da kake cewa ni( WACECE) littafin mu na gaba insha Allah. To ni ko nake da usul tunda Ni musulmace ……yace ” yace dalla kan ina asalin yake ! inda asali uwa da uba ake nunawa kinga ko tunda nake da uwa da uba aiko nafi ki asali , ke nunamin naki iyayen”””

 

Cikin harzuka namiki nace Bello har ka isa ka shegantani !!! Aiko ba iyayena to ai da kakata kaganni tunda ko ita ta haifi daya daga cikin su….. Yaushe kashigo musulunci ma da zaka san fari da baki..

 

Auwal ne yace haba Bello menene haka baka ganin yarinya ce mai yasa bazaka kaman kanka ba , deejee dan Allah abr maganan nan haka naga abinnaku yana neman yazama babbba , kudin na cillamasa nace baza a bada ƙosan ba aje anema agaba ,na fara zubawa sauran Gwaggo ce ta iso tana cewa wai hayaniyar me nakeji ne anan Auwal yace ba fa. Komai kawai hirace ,

 

nace a’a Auwal kafadi gaskiya! Gwaggo Bello ne wai dan nabawa baba Hashimu ƙosai wai maiyasa zanyi haka harda shegentani shine nace to bazan sai da masa ƙosan ba .

 

Ran Gwaggo ya mutukar tashi wato dai haryanzu wannan batun ba a daina shiba na shegan ta mata jika to wlh Bello sai ya gane kuransa yau zata nuna masa iyakarsa …..

 

Ta fara tattare kaya ! Nima nafara tayata tace Auwal Auwal ya tayani mukai kayan gida zataje gidan su Bello!! Cikin jin dadi nace to Gwaggo amman araina naso inje ayi wacce za ayi agabana amman tunda za’aje karbomin encina . Har kofan gida Auwal ya rakoni da kaya a zauren ya direminsu , na mai godiya duk da irin abinda nake masa Auwal baya biyemin sai dai yayi murmushi yace yarantace .

 

Gwaggo na isowa gidansu Bello ta hau sirfa bala’i tana ina kuke masu gida da asali ! Mahaifiyar Bello ce ta leko sakar gida tace Gwaggo ne kishigo daga ciki mana kya saya arana !! Gwaggo tace ai bazama ya kawoni ba ina wannan dan naki maikama da inyamuri to wlh ki shaida masa yafita a sabgar jikata inbahaka ba to kararsa zankai ga hukuma !!

 

Allah sarki madam balki tace sai hakuri wo i told this boy not to go carry rigima for me wo Bello zakazo kasameni !!! Aiko Gwaggo tace ninake kariya ( carry) wato bello ne mai gaskiya dan banyi boko ba ( boy ) to wlh ahir dinko nafi karfinku nima jikata ai ƴar boko ce !! “””

 

Madam balki tace NO what I mean kiyi hakuri bazai sake ba , !! Sai ga Bello ya shigo gida yana WHATS going on …. Chakkk ya dakata da ganin kakar DEEJEE!! “”

 

Tace nine goni kon ( going on) to wlh tafadi akanka mara mutunci . Mahaifiyar sa tace yabawa Gwaggo hakuri””‘ yace I’m so sorry Gwaggo tare da rike kunnuwansa .

 

Aiko Gwaggo tasake fusata tace saurayi ( sorry) kuma kul kai ba saurayin jikata nace ko tarasa mujin aure bazata aure kaba . Tashin hankali sun fahimci suhuwar abirkice take bazata fahimce su ba suka fara lallabata ! Da kyar ta tafi tana tafe sai surfa bala’i take har ta iso gida .

 

Inanan zaune ina jiran dawowar Gwaggo inji ya akayi sai ko tashi go ke!!!! Deejee zonan !! Cikin hanzari na iso wajenta ta min wani wawan rankwashi aka wanda yasani kara tare da rike wajen tace ƴar kwal’uba ni zaki maida sakariya ashe soyayya kuke da Bello wai daga zuwansa yace wai ni goni kon ( going on) kuma shi saurayinkine ( sorry) !!! Cikin bakin ciki nace Aradu Gwaggo karya yakemin ni ba saurayina bane sharri ne !!! Kuma sai na mai rashin mutunci .

 

Gwaggo najin nace zanmai rashin mutunci tasan zan aikata tace yauwa DEEJEE “” kintabbata babu wata alakar soyayya ko “” nace eh “”, tace to magana ta wuce daura mana tukunyar abinci !! Kidafa mana miyar bushashshiyar kubewa dan Allah tayi dadi irin na rannan …. Nace to Gwaggo ,fuskata a daure dan har yanzu ban huce ba har sai na zazzagawa Bello rashin mutunci Ni zaice muna soyayya wato hadani da kakata zaiyi na hura wuta nafara girki !!!!!

 

Gwaggo sai cewa take bi ahankali karki ƙone dan takula a daddafe nake girkin har na kammala ina zancen zuci ! Na kagu gobe tayi insami zeenatu infada mata abinda Bello yamin . Ina tashi da safe nayi sallah danko Gwaggo bata tashina wai ai sallah bata hau kaina ba dudu du shekaruna Goma sha daya ne fah ake wannan badakalar . Dumamen da Gwaggo ta ajiyemin ne nagani nace nawasa ruwa nasa uniform na makaranta nabiya na amshi ƙosai da kudin mota nayi gidansu zeenatu.

 

Ina zuwa ko nafara bata lbr abinda yafaru tace “” kina nufin yaci buluss”” nace wlh bai isa ba sai naga wanda zai kwace sa daga tuggun deejee!!! Sukayi dariya suka tafa zeenatu tace kedai muje makaranta kamin sajen Musa ya laka da mana na jaki …. Da sauri suka fito daga gida sukayi wajen BUS Ashe ba agama hallaruwa ba mukane sit muka zauna , Fauziyya ce ke harararmu mukam ko kallo bata ishemu ba dan bamu da lokacin ta mu yau da Bello muke ….

 

Muna isowa makaranta mukayi aji uncle sani ne a aji yace yau ma kunyi late wai ku bakwa tashi daga bacci ne dawuri ..

 

yace oya ON YOUR KNEELS muka fara zuru zuru da idanuwa dan bamu fahimci mai yake nufi ba bulala ya anso a hannun MONITOR yafara zabga mana yace dakikai ku rage sawo nace kunwani sayamin akai sai kace andasa ece ….

 

Aikuwa ranan munci duka nacewa zeenatu wlh makarantar ALLO zan koma Ga karatu ga lada amman boko fah sai cin zali dubi uncle sani da katon kai ga sawo dama ance duk dogon mutum hankalinsa a gwaiwa yake muka fara dariya kasakasa ….

 

Yace Au kunma maidani mahaukaci Khadijah Ibrahim and zeenatu Ismail get up kubiyoni , …

 

Biyoshi mukayi bayan aji yakaimu akwai wani bola mai uban doyi wai mu kwashe nace Alkur’an bazan kwasheba haka kurum cutar ta kamani sai dai akoran yace haka kikace to yauko zakibar makarantar nan office ya nufa yasanar da headmaster ….

 

Sai da yayi ajiyar zuciya yace na gaji da case din deejee nakore ta yafi akirga BUT her grandmother tabani tausayi she explained everything for me wai marainiya ce in aka koreta abun sai yayi yawa …. Daman ba karatun takesoba …

 

Ya aika muzo muna zuwa muka durkusa har kasa muka gaidashi … Yace Khadijah Ibrahim and your friend I’m tired with your Case but zandau kwakkwaran mataki akanku , go to your class..

 

ya zaunar da uncle sani yamishi bayanin komai yanuna masa they’re villages, so they need our help!! Yanzu muna korinsu kaga bamu cimma abinda mukeso ba kakara hakuri Sani ninasan matakin da zandauka …..

 

Muna shigowa aji ana buga bell antashi ba abinda mukayi sai punishment yau jiki yayi tsami !!! Muna dawowa gida nasha magani na kwanta sai bayan la’asar natashi ,liyin su Bello naje akacemin yatafi bautar ƙasa cikin jin babu dadi nadawo gida .

 

TAMMAT TAKU HAR KULLUM SAYYADA

( Ummul ummu Abiha)

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment