Littafan Hausa Novels

YADDA ZAKI KULA DA MAI GIDAN KI DOMIN MALLAKE SHI

Written by Hausa_Novels

YADDA ZAKI KULA DA MAI GIDAN KI DOMIN MALLAKE SHI

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

YA AKE TASHIN MIJI DAGA BARCI.

 

LALLE WANNAN YA KAMATA MATA KU LURA.

Saboda rashin iya tashin miji a barci yanasa

miji ya tsani matarsa……

Tashin miji daga bacci suna dayawa.

Ga daya daga ciki.

 

Lokacin da kika iso daf da gadonku zaki hau gadon ne a hankalii.

sai ki kwanta a kan qirjinsa a hankali.

ki komar da kanki ki kwanta.

lalle tabbas zai ji numfashinki.

sai ki dan dago kisa bakinki daidai kunnensa kidan hura iska kadan nan take zaidan motsa yana bude idonsa sai ki sakar masa murmushi.

Saiki sakar mashi murmushi kikai Bakinki anashi kiyimasa.

 

“”hot kiss ”” kadan sai ki fara magana kamar

haka “”dear lalle barci yai dadi sannu farincikina nazo tashinka ne, “”Sweety nah karka makara pls tashi muje toilet.

kina magana irin ta mata masu iya sarrafata.

kina gama magana saiki tashi ki riqe hannun abinki, ki rakashi har toilet tabbas zai biki kamar raqumi da akala amma karki tsawaita ku wuce tacan ba ruwana.

 

Amma fa ki tabbata kin rigashi yin wanka kafin

kizo tashin sa, Yana bude idanu zai ganki tsafta.

tauraru, wannan kyan zai zauna mishi a kwakwalwa bazai rinka mantawa da keba koda yana zaune a office ne.

 

WACE SHIGA YA KAMATA KIYI A GIDANKI.

Yar uwa kizama meyin dressing kala-kala karki

nacewa kwaya daya kullum English dress kamar wata ba saban ba,a’a karkade kunnen ki kijini.

 

Yau inkika zama Baturiya, to gobe ki zama Balarabiya a wajen dressing.

jibi kuwa nemo fakistan dinki damammu kisa ki zama indiya.

 

shigar hausa kuwa karki bari a barki a baya don yanzu akwai dunkuna damammu na daukar hankali..

 

gata kuwa ki canja kizama beyarabiya, yi kokari kiyita rikida kamar wahainiya kullum kita bashi mamaki,bawai dressing daya ba wanda kullum zaishedaki dasu.

 

Ko tunanin ki zaiyi da wannan shigar zai ganki a kwakwalwarsa saboda ita yake gani kullum.

karki bari ogah ya fita yaga wata da shigar da ke bakyayi har yayi mata kallon da bana shari’a ba.

 

Yar uwa bude idonki karki bari a barki a

baya.

 

SIRRIN KALLO

 

Kallo wani abune mai saurin isar da sako

musamman a wajen masoya ko kuma

Ma’aurata.

Yawancin mata suna da wani matsala wacce itace ke sawa bayan anyi aure sai yaji matar tana fita masa a rai a hankali a hankali.

Tun kafin auren mace bata iya bude idanuwanta ta kalli saurayinta saboda kunya, idan aka tashi

kallonsa to kallo na daban take mai to wannan kallon da take masa na kunya yana da tasiri kwarai da gaske a wajen namiji.

Akwai sinadarin da yake kunshe

cikinsa.

Da yin aure sai kaga mace ta canza, wannan kallon da ake masa lokacin samartaka yanzu an daina.

Kallonsa takeyi kamar yadda take kallon kowa.

Kallo yana da nau’I iri iri.

Anaso mace ta dingayiwa mijinta kallo na

musamman, kallo na ‘kauna, da soyayya hade da daukar hankali.

Matan da suka amsa sunan su mata, sune masu kallo iri-iri kuma kowanne akwai manufarsa:

 

Akwai kallon ‘NAYI KEWAR KA’,

ka jima a office, yana ganin wannan kallon yasan yayi laifi zai fara rarrashin ki.

 

Akwai kallon ‘INA ALKAWARI NA’…, yana gani ya sani, idan alkawarin bai cika ba zai sake miki wani alkawarin hade da ban hakuri.

 

Akwai kallon ‘BANI DA LAFIYA’ a nan zai fara tambayar ki mai ya sameki? Kinsha magani?

Akwai kallon ‘KAYI MUN LAIFI’, ka ‘bata min, zai fara baki hakuri.

 

Akwai kallon ‘FARIN CIKI DA NISHADI’, a nan zakiji yace menene labari yau naga nishadin yayi yawa.

 

Akwai kallon ‘GODIYA’ a nan Maigida zaice

kinfi haka duk abinda nayi miki ban biyaki ba,da dai sauransu.

 

Akwai kallon ‘INA DA BUKATAR KA’ idan ya gani yasan me kike nufi.

To Allah yasa mijinki mai karantar kallon kine.

Ameen.

 

Akwai salon KALLO da yawa wanda mace ta nan kawai ya isa ta isar da sako ba sai tayi magana ba, ko da kuwa za tayi maganar, ya zamo kallon ya riga maganar isar da sako.

 

TO YA ZANYI IN KALLI MAIGIDANA?

A koda yaushe mace idan zata kalli mijinta ya kasance kada ta bude idonta gaba daya, tayi ‘kasa dasu kamar mai jin bacci, ta rinka lumshe su, tana sarrafasu yadda ya kamata, musamman in an sami mai manyan idanuwa ce, sannan mata ku dagye wurin sanya kwalliyana gyaran idon mace kallon zaifi dakan zuciyar Maigida, Kuma kada ki ‘kurawa Maigida idanu kai

tsaye, bance kada mace ta kalli mijinta ba.

About the author

Hausa_Novels

Add Comment

Leave a Comment