Littafan Hausa Novels

Yadda Zaki Gyara Budurcin Ki

Farjin Mace Kala Nawane
Written by Hausa_Novels

Yadda Zaki Gyara Budurcin Ki

 

 

 

 

 

 

 

 

YADDA ZAKI GYARA BUDURCI KI

 

 

MENENE BUDURCI?

 

 

 

Assalamu Alaikum Warahmatullahi wabarakatuhu.

 

 

 

Wannan wani darasine mai muhimmanci da ya kamata mutane su sanshi musamman samari da yan mata, amma da zaran an fara irin wannan sai a kama jin kunya, ko shi mai koyarwar ya ji kunya ya ki yin bayani yanda ya kamata ko su masu sauraro su sa kunya su qi nutsuwa su koya. Don haka ya kamata mu gane wurin neman ilimi ba a jin kunya.

 

 Hanan Hausa Novel Complete

 

Nana Aisha (RA) tace: “Madalla da matan madina wadanda kunya bata hanasu tambaya game da abinda ya shafi addininsu ba. ”

 

 

 

Sannan a wani hadisin Ummu Salamah tace ma Manzon Allah (SAW ) “Lallai Allah baya jin kunya game da gaskiya. Shin akwai wanka kan macen da tayi mafarki?” sai yace “Eh! idan ta ga ruwa (ma’ana idan ta fitar da maniyyi)”. [Bukhari da Muslim].

 

 

 

Indai wurin neman ilimi ne musamman ma na gyaran ibada da rayuwa to ba a jin kunya. Wannan dalilin ne yasa naga ya kamata na yiwa yan’uwana wasu bayanai akan budurci, bayani ba irin na posts na rashin kunya da batsa ba da suke yawo a social network. A’a bayani akan yadda budurci yake da darajar budurci don yan mata su san me suke dauke dashi.

 

 

 

Allah cikin ikon sa da tsari na halitta Irin naSa Yasa kowace mace da budurci ake haifanta, shi ake kira da “HYMEN” A turance.

 

 

 

Ita dai HYMEN wata fatace mai dauke da jini a cikinta tana farjin kowace mace amma ba tada wuyar fashewa. Sannan ba wai hymen bane kadai a cikin farjin mace ba a’a. Akwai fata biyu sune LABIA MINORA da VESTIBULE Su wainnan sune suke farjin mace amma shi ainihin budurcin yana daga ciki, ma’ana kenan sune suke kare miki ainihin budurcin ki na ciki.

 

 

 

Shi wannan zafin da ake ji lokacin jima’i na farko sune suke budewa suke fitowa da jini, Sune idan babu su to zaki ga babu wannan jan jinin a jima’in farko saboda sun rigaya sun narke ne a gabanki, sai ya zamana koda kin yi aure mijin ki ya sadu dake to zai ga baki fitar da jini ba sai ya dauka ko kin taba bin maza ne, bayan kuwa ke baki taba yi ba, kuma mata dayawa suna shiga cikin matsala saboda mazan su suna jin su a bude yayin da suka shiga gidajen auren su.

 

 

 

Sannan su wainnan fatan uku ba makawa idan daya ya yage a cikin su to dukkan sauran zasu yage, don ita ba tada karfi, kuma yawan kai hannu wurin zai bude shi. Mafiya yawan yan mata suna loosing virginity nasu ba tare ma da sun sani ba, saboda wasu abubuwa kamar haka:

 

 

 

1. Guje guje da tsalle tsalle, da tafiya da sauri kamar gudu koda yaushe.

2. Rawa mai karfi ko motsa jiki mai karfi.

3.Bude kafa, ya zamana mace tana zama da karfi sosai, kuma kullum in ta zauna zata bude kafa, bata kama jikinta.

4.Hawa bishiya, da keke, da daukan abu mai nauyi.

5.Tsallake rami mai fadi sosai ko yin abin da zai sa sai ta bude kafanta sosai.

7.Nishi mai karfi.

8.Magana ko ihu mai karfin gaske, don akwai mata shashashai, ita mace tana magana ne with class da kamala irin ta mace.

9.Yawan saka hannu a wurin na rashin dalili.

10.Dadewa ba aure da yawan shekaru ma yana sa mace ta rasa budurcin ta.

11. Mikewa tsaye da karfi, idan zaki mike tsayema ya kamata a matsayinki na macce ko matar aurece ki yishi a nutse balle budurwa da tasan darajar ajiyar ta.

11.Wata kuma budurwar yawan cushe cushe ko matse matsen abubuwa da yawan sit bath ba tada aure zai iya kawo kaucewar budurcinta.

12.Sannan wasa da kansu da wasu mata ke yi saboda matsanancin sha’awa gashi ba su da aure, yana kawar musu da budurci. Dama sauran su.

 

 

 

Kenan dole ne ki fahimci matsayin ki na mace budurwa, kuma ki dauki aniyar gyarawa, Idan ka tattauna da matan aure da dama zasu ce wallahi idan har namiji ya sami mace budurwa to ta riga ta gama amsan ma kanta girma da daraja, kuma duk lokacin da yaso ya ci mata mutunci zata tashi tsaye tace wallahi kasan dai yanda ka same ni, ni ba mutumiyar banza bace, suka ce sai ka ga sun shiga hankalin su, saboda sun San ke mai mutunci ce.

 

 

 

Don haka babu wani dalili da zai sa ki bari ki watsar da budurcin ki musamman ta hanyar zina. Wallahi budurcin ki shine daraja da kimarki a gidan mijinki, Kenan shine yancinki, kada ki sake wani sakaran saurayi ya hure miki kunni ki bashi budurcin ki a bulus, kuma ko nawa ya baki to bai kai ‘dan kadan din sadakin da mijinki ya bada ya auro ki cikin daraja ba, wanda kowa yasan ya bada.

 

 

 

ABIN DA YA KAMATA MAZA SU FAHIMTA SHINE:

 

 

 

Hakika mun san cewa budurci abu ne mai ‘kima da daraja saboda wannan shi yake nuna mace bata taba sanin wani namiji ba, namiji yana farin ciki da murna ace shine ya fara sanin matar sa, amma ina so ku sani cewa Idan ka shigi mace baka ga jini ba, ba yana nufin babu budurci bane, ko yana nufin shikenan ta san namiji ba a’a duk shekarun Mace kuma koda ta rasa budurcin ta to dole a matse take, Saboda babu abun da ya taba bin wannan hanyar. Sai dai kawai babu wannan jinin.

 

 

 

Sannan akwai wacce ma jinin baya fita sai bayan ka gama taje futsari sannan zata ganshi, kenan ba hujjah bane ka rinka yiwa mace wulakanci na cewa wai bata kawo budurcin ta ba, don mace budurwa taste din ta daban yake wallahi.

 

 

 

Mace gaskiya bata ganewa, kuma ba ta sanin lokaci da ta rasa shi, kenan ita ma da tasan bashi to zata zo gidan ka cikin tashin hankali, amma ka same ta a matse da kyar ma wani zai shigeta but still zai canza fuska, tun a daren ma wani zai ce wai ya naga haka?

 

 

 

Zinace zinace ya yawaita yanzu shiyasa maza suka dogara sosai da wannan ganin jinin, saboda suna ganin koda ma ba budurwa bace zata nemi abubuwan matsi ta matse kanta, shiyasa shiyasa an sha fahimtar dasu amma basa samun nutsuwa muddin basu ga jinin ba. Kenan tun da abun ya koma haka dole ne ki bude ido, ki rinka kula da budurcin ki kamar kwai, don gujewa matsalolin gidan aure.

 

 

 

SHIN JININ HAILA YANA BUDE BUDURCIN MACE?

 

 

 

Allah cikin hikimarsa ya kaddara komin girman jinin da ke fitowa yayin jinin hailar mace to baya kawar mata da budurcin ta, duk da dai wasu manyan matan sun ce yana dan bude mace kadan idan ta gama jininta, amma likitoci sun ce baya bude mace, Shiyasa suke bawa yan mata shawarar sanya almiski don wurin ya koma kamar da.

 

 

 

Wannan shine kadan daga cikin bayani akan budurci, amma ban gama rubutun ba, Sati na sama zan yi bayani akan hikimar da yasa Allah yayi budurci. Sannan da darajojin mace budurwa a musulunci, sannan da hanyoyin da mace zata bi wacce kaddara yasa ta rabu da budurcin ta, sannan da bayani akan fake hymen.

 

 

 

Ana so ko da yaushe idan mijinki zai kusance ki yaji ki a matse kike, ba”a son lokacin da miji zai kusanci matarsa ya wuce siririf.

Don haka ya ke da kyau mace ta rika kula da gabanta kar ya bude

Abubuwan da ke matse mace suna da yawa misali

Bagaruwan hausa.

ana dafa ta da ganyen magarya ko ita kadai a rika wanke gaba dashi ko ki zuba a baho ki zauna a ciki da dumin kaman 30mins a kalla sau biyu a sati.

Kanunfari ana dafa shi a sha da zuma da zafi zafi ko ki jika ya kwana da safe ki tace kisha da madara da zuma.

Ana kuma dafa ta a zauna a ciki da dumin ta ko a rika tsarki da ruwan ko kuma a zuba kanun farin garwashi a tsugunna shi ma sau 2 a sati Kwallon mangwaro idan kika fasa zaki ga dan ciki

fari haka, ana busar dashi a daka a kwaba da zuma arika matsi da shi bayan isha’I idan zaki kwanta

bacci ki wanke ko kuma ki dafa dan cikin da bagaruwa ki wuni tsarki dashi ko ki zauna a ciki

n shima a kalla 3x a sati.

Almiski fari ko ja ki daka kanunfari ki tankade yai laushi sai ki kwaba da miskin da man zaitun yawaita amfani dashi na matse mace sosai kuma kullum cikin kamshi….yana gyara macen da ta haihu sosai musamman da jinin haihuwa ya dauke ki fara amfani dashi har ki ar’bain…

Inda wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da

ruwan dumi

bagaruwa

Na tsawon Wata guda sai kuma matsi shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki kuma wannan mun dade dayin bayaninsa

 

KAYAN HADIN

ki daka garin zogale ki tankadeshi.

ki samu man ka danya ( Ana samu a wajen masu maganin gargajiya.

ki samu man zogale ( Ana samu a wajen masu *_Islamic-medicine

ki samu Karo shine wanda ake tawada dashi kuma ana wanke hula dashi ( Ana samun sa wajen masu kayan koli ).

ki samu man shanu ( anansamunsa a wajen masu sa yarda nono).

duk ki hada su wajen daya ki kwaba su suyi kamar sa’oi 5awa zakiga sun hade sai Kiyi Matso dashi kuma Zaki iya rabashi uku gida 3 wato Kiyi matsi dashi Sau uku a cikin sati biyu.

 

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment