Littafan Hausa Novels

Yadda Naci Maryam Hausa Novel

Sirrin mata
Written by Hausa_Novels

Yadda Naci Maryam Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

Sani ɗakinsa ya nufa kai tsaye yana shiga ya kulke kwanciya yai a kan gado yana dariyar mugunta ,magana ya fara a tsanake kamar da mai sauraransa a ɗakin.

“Raliya kiyi haƙuri kin kai ni bango ne shiyasa ba ke ba ce bana so halinki ne bana so, da ba haka kike ba Raliya lokaci ɗaya kika canza hali nayi iya haƙurin da zanyi da ke Raliya amma kin ƙi gyarawa sai kace wacce a kaiwa auren dole, naga auren soyayya mukai da ke, koda da yake baki da lefi Kaka ce mai lefi ita ya kamata ta gaya miki gaskiya tanuna miki yarda zaman aure yake amma sam Kaka bata san lefin Raliya koda da kwayar zarrah, AIIah na tuba kayafemin idan a kace da Raliya zan ƙarashen zaman aure na har a bada ai dana ce ban zo duniya a sa’a ba, dan abin idan ya isheni guduwa zanyi na bar garin kowa ma ya huta koda labarina babu mai ji sai naga da uban da za tai zaman auren haba dan AIIah kowa na auren ya samu farin ciki amma ban da ni? ga mace iya mace amma babu gyara kullum saidai ta zauna kamar jaka babu wanka babu wanki, kai tur da hakinki Raliya.”

Yadda Naci Yayata Hausa Novel

Sani ya ƙarashe maganar yana numshi manyan idanuwarsa masu kama da mai jin barcci.

 

Raliya saida taci kukanta ma ishi kana tai shuru ganin babu mai lailashin ta, tsaye ta miƙe tana karkaɗe jikinta nan ta shiga doka uban wata hamma ga barcci ga yunwa da take ji, dube-dube ta shiga yi a kitchin ɗin ko zata samu abin sakawa a bakin salati amma wayan babu komai ni kuwa nace Raliya baki girkaba taya zaki samu bawan naki ya gaji da girkawa, nan ta shiga hurgi da kaya ƙasa sai faman huci take kamar zakaiya, a hankali ta bar kitchin ɗin ta dawo Faloh ta zauna, a ƙasan kafet, kallon ƙofar ɗakin Sani tai ganin ta a kulle yasa ta doka wani uban tsaki tare da wata muguwar harara, a haka har barcci ɓarawo ya kwashe Raliya a zaune.

*WANNAN KE NAN*

( _Washe gari da safe)_

Da huri Sani ya bar gidan dan yace sam baya so su haɗu da Raliya kwata-kwata baya san ganinta, saida ya fara biyawa gidan Kaka kana ya huce Office ɗin sa.

Su Zakiyya an zama ƴan gari dan ta fara zuwa makaranta idan ta tafi tun shida na safe sai shida na yamma zata dawo gida makarantar boko ce da isilamiyace a haɗe, Sani yai mata hidimar makarantar komai da komai Zakiyya tana waya da su Innarta da Malam ta wayar Kaka dake Hajiya Fulera tabawa Kaka numbar Inna tun randa ta kawo Zakiyya gidan.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment