Littafan Hausa Novels

Yadda Naci Kanwar Abokina

Siffofin Mace Mai Ruwa
Written by Hausa_Novels

Yadda Naci Kanwar Abokina

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Yadda Naci Kanwar Abokina

 

Lokacin da suka sauko downstairs,gaba ɗaya kowa Ya hallara akan dining suna Yin break fast,ƙarasawa Su kayi Bayan sun gaishe da kowannansu,Kowa saiyi Mata Ya jiki Yake yi,Taji daɗin yarda Suka nuna damuwa akanta,kusa da oummansu ta xauna,Jahad ma ta zauna a gefenta,a dai dai Lokacin Azmee ta dawo hannun ɗauke da wasu kayan abincin data ɗauko a kitchen,A saman table ɗin Ta ajiye tray ɗin,Atare Sehrish da Abu suka ɗago ido suna kallonta,fuskarta ta kumbura idanuwanta sunyi jawur kamar wadda tasha kuka,a gefen fuskarta hada gurjewa,fatar wurin ta tattare,Abu batayi mamaki ba,don kuwa ta gane cewa Itace ɗin tazo mata da suffar mage a daren jiya,Ga alamu nan Sun nuna,

Zagayawa tayi wurinsu Sehrish,plate biyu ta ɗauko ta zuzzuba masu abinci,tare da tura masu agabansu,Jahad ta hauci,Sehrish kuwa ƙin cin abincin tayi,Miƙewa Tayi daga saman chair ɗin,

Yadda Naci Maryam Hausa Novel

“Ina zaki je”?omamnsu ce tayi magana ganin ta miƙe,
Daƙyar ta iya cewa”Kitchen zanje,”ta ƙarasa maganar tare da kama hanyar zuwa kitchen don ta shirya mashi breakfast ɗinshi,tun da ta fara jin sauƙin jikin nata,

Shaf shaf Ta shirya mashi asaman ƙayataccen tray,Ta wurinsu ta gifta cikin main palour,Upstairs Ta haye lokacin data ƙarasa part ɗin nashi tana ƙoƙarin Shiga,tajiyo muryoyinsu suna magana Shi da Omar,
“The same fa irin message ɗin da aka turomin Ni da Abba,da farko da abba ya nuna mun saƙon nayi tsammanin ɗaya daga Cikin friends ɗinshi ne,Aka samu wani Yaron Ya ɗauki wayar mahaifinshi Ya rubuta jagwalgwalon,Amma daga baya dana ga saƙon sai abun Ya tsaya mun araina,kuma sai gashi kaima An tura maka,to wai wanene da wannan aikin”?Yayi tambar yana kallon Sgr,dake a gefenshi,
“Am confused Omar,Nagaza fahimtar me aka rubuta ajikin message ɗin nan,abu 2 nake hasashe akan saƙon nan,kodai ƙaramin Yaro ne Ya rubutoshi,ko kuma wanda baya acikin hayyacinsa,Amma abunda yafi ɗaure mun kai shi ne,Taya akai wanda ya turo saƙon Ya samu special line ɗina,Wanda bakowa ne yasanni dashi ba,”ya kai ƙarshen maganar yayin da idanuwanshi ke akan Omar,

Kafin Omar yace wani abu,Sehrish Ta katsesu da sallama,Atare suka ɗago suna kallonta,
Ƙarasawa tayi gaban table ɗin dake agabansu,ta sauke trayn asaman shi, kafin ta ɗan ɗago tare da kallon Marshal Omar,murmushi ta samu akan fuskarshi,
‘Ina kwana Ya omar,ka tashi lafiya,”
“Lafiya Lou Sister,Ya jikin naki”?
“Da sauki ya omar,”_
“Allah ya ƙara maki lafiya,”
“Ameen ngde,”ta amsa mashi,
Cike da Zolaya ya nuna kayan abincin data ajiye masu”Nawa ne ko nashi”?
Duƙar dakai ta ɗanyi tana murmushi
“Naku ne,na kawo maku,”
“Kinsan da zuwana part ɗinshi ne,”?
“A’a,”tayi maganar tare da satar kallon Sgr,Ya tsareta da blue eyes ɗinshi,duk saita shiga kame kanta,
“Ya akai naga ka tsareta da ido?faɗamun menene sirrin kallon nan”yayi maganar yana ɗage mashi gira,da sauri Sehrish Ta juya ta kama hanyar fita ɗakin,
“Kallon Ya isa haka,Its better ka kame kanka malam,saura ƴan satittika,Ka sakar mashi Ƴar shi,Ka koma U.s wurin Eva nasan har yanzu tana jiranka,”
Ɗaure fuska Sgr yayi”Omar bana son wannan joke ɗin,idan kaga nabar ƙasar nan,ƙafata ƙafarta,zan tafi tare da ita u.s don taci gaba da yi mun aiki acan,”
Harararshi Omar yayi”Sannu ko?masu aikin dake garemu a U.s fa,Sallamarsu zaka yi ne”?
“Aikinta daban nasu daban,”
“Kana nufin aikin gyara shimfiɗa”?dariya ce ta kufce ma omar,hakan ba ƙaramin hasala shi yayi ba,
Ganin ya 6ata rai yasa shi cewa”Shikenan nadaina,yanzu dae bari nayi serving ɗinmu ko?nasan kana jin Yunwa,”
Yayi maganar tare da kai hannu yana buɗe warmer,
Sehrish kuwa Bayan fitarta daga part ɗinshi,jiki asanyaye take tafiya,maganar da taji su Ya omar nayi akan saƙon nan ya tsaya mata aranta,Taya akai aka tura masu message iri ɗaya,Amma ita saƙon nata bada new number bane,ta layin Amrish ne,kuma a iya saninta Amrish bata da Number ɗinsu Ya omar,balle ace itace ke tura masu saƙon dagangan,to kodai ta yarda wayarta ne?wani yaron ya tsinta Yake tura masu saƙo,Can kuma ta tuna abunda Sgr yace da Special line ɗinshi aka tura mashi saƙon,Wanda ba kowa ne keda shi ba,

Ƙarasa Zancen zucin tayi a lokacin data sauko palour,bata koma dining ɗinba ta wuce bedroom ɗinsu tana zarya acikin ɗakin nasu,

*Amrish*

lokacin data juya izuwa cikin gidan A sukwane ta faɗa falon,da gudu ta nufi wani Corridor,Gidan Yana da girma sosai,tana da tabbacin cewa anan downstairs Suka rufe shi,haka ta dinga bin ɗakunan dake a gidan kaf tana bincikasu,Tasha wahala sosai,Ga uban gumi data haɗa,fuskarta sai naso take yi,A ƙarshe data gaji ta shiga ƙwala mashi kira ko Allah zaisa Yaji kiran nata Ya amsa mata,
“Junaid!Junaid”tamkar maƙoshinta zai 6allo waje saboda yarda take 6are baki wurin kiran sunanshi,

A galabaice Amrish tayi ruku’e hannunta dafe da guiwowinta,Sae faman haki take yi,runtse idanuwanta tayi gam,yayin da take tariyo ɗakunan data bincika a ƙalla sun kai ɗaki takwas masu zaman banza wanda ba’a amfani dasu,zurfin tunani ta shiga,nan take wani abu ya faɗo mata aranta,Acan backyards ɗin gidan Akwai wani munafukin ɗaki,Wanda tun tana yarinya hajiya Sarat ta hanata shiga ɗakin,ko wurin ɗakin taje saita tsawatar mata,tunda take ita dai bata ta6a gani an buɗe ɗakin nan ba,Akan idanuwanta,Kamar an daina amfani dashi amma akwai wasu surruka da aka 6oye acikinsa,Shiyasa aka hanata zuwa,

Cike da ƙwarin guiwa Amrish Ta miƙe,ta juya tare da kutsawa Can ciki,Ta ƙopar baya ta fita,tsayawa Tayi tana kallon Girman ginin,A hankali ta aza idonta kan ƙopar ɗakin dake fuskantar backyard din,Wani ƙaton ƙwaɗo ta gani an garƙame ɗakin dashi,Wanda duk bala’enta bazata iya cire wannan makullin ba,tsabar baƙin ciki kamar ta haɗiyi zuciya a wurin nan,Gashi window ɗin ɗakin sunyi nesa can sama,matsawa tayi jikin ƙopar ta kanga kunnanta,hannu tasa tana ɗan kwankwasa ƙopar ko zata ji motsinshi,Amma shiru babu wani alamun akwai mutun,cike da takaici ta juya zata bar wurin kenan idonta ya hango mata ɗigon Jini a ƙasan wurin,har sai da ta dafe saitin zuciyarta saboda faɗuwar gaban da taji,wannan Yasa ta ƙara yarda cewa Akwai mutun a cikin ɗakin,tabbas Sun shiga dashi cikin ɗakin,da gudun gaske ta koma cikin gidan,akwai wani ɗaki dake jingine da wannan ɗakin dake a backyard ɗin Amma shi yana fuskartar Cikin gidan,ranta na bata cewar Zata Samu window ɗin ɗakin ta cikin ɗakin dake acikin gidan,cike da sa rai Amrish ta faɗo cikin gidan,gudu gudu sauri sauri Ta shiga ɗakin,kamar Store ne na ajiyar buhun hunan kayan abinci da jarkokin Mai,A jikin ƙopar store ɗin ta samu Key ɗin ɗakin,hannunta na kerma ta murza key ɗin ɗakin,kafin ta hankaɗe ƙopar ta shiga,Gabanta sai faɗuwa yake yi tsoranta kada Mommynta ta dawo,dan Wlh har kashe ta zata iyayi,Dama tasha faɗa mata cewa ita bata damuba don ta rasa ba,ba ɗigon Imani azuciyarta,Kamar arniya hake take,

Ajiyar zuciya ta sauke Lokacin data hango Window mai girman gaske Duk da akwai net ajikinta,Amma batayi nisa ba,in har ta taka wani abu zata Iya hangen abunda ke wakana acan ɗakin bayan gidan,Ga uban duhun da ke cikin ɗakin,Bazata Iya hango abunda ke aciki ba,da gudun gaske ta juya tabar store ɗin,kitchen ta nufa Ta ɗauko wuƙa lafiyayya,Kafin ta ƙarasa saman hannun kujera inda ta ajiye wayar junaid ta ɗauketa,dama ita waya koda security torch ligh na kawoka,Don haka ta kunna fitilar wayar,Ta nufi store ɗin a hanzarce,Rufe ƙopar tayi bayan ta shiga,gaban waɗannan jerin Jarkokin man ta nufa,da yake Allah yayi mata ƙarfi,ɗaukar jarkar Tayi tajata izuwa gaban window ɗin,Sannan Ta hau saman jarkar,Iya idanuwanta ne suka kai Wurin net ɗin tagar,

Wuƙar hannunta ta sanya,ta dinga caccakata jikin Ragar,nan take wurin ya lomatse,Gagara wuƙar ta shiga yi tana Yanka Ragar,har sai da ta cire Rabinta,Tukunna Ta saki wuƙar kasa,Haska wayar tayi tana leƙen ɗakin,Saboda tsabar duhun ɗakin fitilar wayar tayi mashi kaɗan,Amma a haka tadinga ƙura ido tana kallon abubuwan dake cikin ɗakin,Wato wasu tsofaffin makamaine aka ajiyesu acikin ɗakin,ga wasu tuluna kamar na ruwa,A jikin bangon ɗakin Ƙwaryoyi ne aka ratayasu,Samansu an rufesu da faifai,ta kasa ganinshi,har sai da ta fidda rai,tana ƙoƙarin janye wayar ta bar wurin,kawai ta hango ƙurar dake danƙare a ƙasan ɗakin tana motsi,nan take gabanta Ya faɗi Rass,lokaci guda ta gane cewa mutunne kwance ƙasan ɗakin,yayi buɗu buɗu da ƙura,nan take zuciyarta ta karaya batasan Lokacin da ta fashe da kuka ba,Don tana ji aranta cewa Shi ne,Batasan taya zata Iya taimakonshi ba,tunda alamun sun nuna cewa babu ƙwari a jikinshi,balle ya iya takowa wurin Window ɗin Ya biyo ta ciki,tunda tagar tana da girma,

Tana cikin wannan Yanayin,Hawaye shaba shaba akan fuskarta,karaf kunnuwanta Suka jiyo mata dirar Mota a cikin gidan,Zo kaga tashin hankali,A firgice ta duro daga saman jarkar,saboda tsabar ruɗi anan tabar wayar Junaid ƙasa, ta rarumi wuqar data wurgar,ta ruƙota a hannunta Da gudu ta rufe ɗakin,Ta nufi kitchen,ƙiris Ya rage ta shiga kitchen ɗin,Muryar Hajiya sarat ta katse mata hanzarinta
“AMRISH”!a gigice Amrish Ta juya tana kallonta,Material ne ajikinta,Ta kashe ɗaurin kallabin nan na rashin mutunci,hannunta ruƙe da hand bag ɗinta,
Wani irin fitsari ne ya matsi amrish,Sai faman haɗiyar yawu take yi,idanuwan nan wuri wuri dasu na mara gaskiya,
“Naga kamar bakiyi farin ciki da dawowata ba ko”?
Shiru bata amsa mata ba,
“Ko har yanzu fushin kike yi dani ne”?nan ma shiru Amrish bata Amsa mata ba
Sai lokacin Hajiya sarat ta lura da wuqar dake hannunta,cike da mamaki tace”Ke!me kikeyi da wuqa a hannunki?Ya akai naga hawaye sharkaf akan fuskarki?wai meke faruwa ne”?
Ajiyar Zuciya Amrish ta sauke,Daƙyar ta iya buɗe baki tace”Albasa nake yankawa a kitchen,ina girka abinci ne,saboda Yunwa nake ji,”ta ƙarasa maganar tana shafa cikinta,
Dariya Saratu Tayi”Manya Na girki,kinga yarda kika canza kamanni?Sai kace bada Gass kike girki ba?Yo wanna ae koda murhu kike girki baza ki yi irin wannan galabaitar ba,Fuskarki ta ca6e sosai kamar ma hada kwalliya kikayi ga janbaki nan dama dama har akan kumatunki”Tana magana tana dariya,
Murmushin yaƙe Amrish tayi tareda sanya hannu tana goge zufar goshinta,Ba ƙaramin daɗi taji ba,Ganin bata Ganota ba,
“Nasan ban kyauta maki ba,Nayi maki alƙawarin zamu fita shopping,Banji daɗi ba daughter,Wani emergency call ne aka yi mun Shiyasa na fita batare dana sanar maki ba,”
“Kada ki damu mommy,Ni yanzu ma ta cikina nake yi,bari na shiga na ƙarasa Yanka Albasar,”
“Okey,Zan shiga ciki na ɗan watsa ruwa,inaso na kwanta na huta,don wlh na gaji,Amma idan na tashi,Zuwa anjima kaɗan sai mu fita Shopping ɗin”
“Toh mommy,A huta Lafiya,”daga haka ta shiga kitchen ɗin,Hajiya Sarat kuwa Upstairs ta wuce,

Ajiyar zuciya Amrish ta sauke,A dole ta ɗauko albasa ta shiga yayyankata,can kuma ta ajiye yankar albasar,ta soma zarya acikin kitchen ɗin tana tunanin Ta yadda za’ae Ta taimaki Junaid Ya koma wurin Iyayenshi,In ba haka ba kashe shi zasu yi,in ma basu kashe shi ba,Wannan daƙyar zai kai labari,

Tunanin kiran Sehrish Tayi a waya,Domin kuwa Ta haddace numberta,Babbar matsalar shi ne Babu wayar da zata Kirata,Wayar Junaid akwai security,duk ta gaza samun natsuwa,a ƙarshe ta ajiye yankar Albasar,ta fito daga kitchen ɗin ta nufi upstairs,A bakin ƙopar ɗakin mommy ta tsaya,tura ƙopar ɗakin tayi a hankali ta leƙa,bata same ta aciki ba,amma taji saukar ruwa alamar wanka Take yi,

Jiki na rawa ta shiga cikin ɗakin cike da fargabar karta kamata,handbag ɗinta ta buɗe anan ta samu wayoyinta guda biyu,ƙaramar nokia da kuma Infinix,duka ta haɗa wayoyin,Sannan ta ɗauki key ɗin ɗakin data gani saman side drawer,fitowa tayi daga cikin ɗakin,Ta garƙame Hajiya Saratu da mukulli,gudu gudu sauri sauri ta sauko downstairs,tana ƙoƙarin kunna ƙaramar wayar kenan,Infinix ɗin hannunta ta soma ringing,ƙura ido tayi tana kallon Sunan daya bayyana akan screen ɗin wayar,Daddyn Amrish,
Maimaita sunan Tayi”daddyn Amrish!”da mamaki akan fuskarta,
“Dama amrish nada uba,”ta tambayi kanta sai kace ba ita bace Amrish ɗinba
Picking call ɗin tayi tare da kara wayar akan kunnanta,
“Kina jina saratu,Wlh karki kuskura kibar yaron nan araye,Don na lura Yaya bazata ta6a bari A ɗauki fansa akanshi ba,Abunda nakeso dake shine,ki ƙwaƙule mashi idanuwanshi nasan zaki iya,Sannan ki binne mun shi da ranshi in bai mutu ba,”
Wata irin zufa ce ta wanke mata fuskarta,Lokaci guda tsananin tsoro ya bayyana akan fuskarta,mutumin bai jira amsarta ba,Yaci gaba da magana duk a tunaninshi da Saratun Yake magana,
“Banaso Ya wuce Yau araye,Kawai ki aiwatar da abunda nace maki,”a gigice Amrish tayi rejecting ɗin kiran,don bazata juri bata lokaci ba wurin sauraron munanan kalaman mutun daya kira wayar,Amma fa tajima tana nanata sunan da Mommynta tayi mashi saving a wayarta,wai daddyn Amrish,A rasa wa za’a sanya ma suna daddyn Amrish sai wannan Mugun,me kashe ƴa’ƴan mutane,

Dogon tsoki Taja,taso ace zata Iya buɗe infinix ɗin don tayi bincike akan wayar,Sae dai kash akwai security ajikin wayar,ƙaramar wayarce kaɗai babu security ajikinta,Call log ta shiga tare da dialling number ɗin Sehrish ta danna mata kira,Sai faman tsuma take yi,don ta qagara Sehrish ta ɗaga kiran ta sanar da ita cewa Yayanta na a gidansu,Suzo su dauke shi,

Almost 3 times Kiran nashiga,amma Sehrish bata ɗaga ba,sakamakon Wayarta dake a silent,tana cikin aljihun doguwar rigar Jikinta,
A ruɗe amrish ta shiga faɗin”Nashiga Uku!Sehrish dan Allah ki ɗaga kiran!Ya zanyi in bata ɗaga ba,Yanzu idan suka kashe shi fa,Wayyo Allah na,”tana cikin wannan zullumin,

A can ɗakin Hajiya saratu kuwa,tana fitowa daga toilet,daga ita sai towel ɗaure a chest ɗinta,kaitsaye ta nufi handbag ɗinta donta ɗauki wayarta,tana zura hannu taji wayamm babu wayoyinta,Zazzage kayan cikin jakar tayi nan ma wayaam babu su dagaske dai an ɗauke mata wayoyinta,da farko tayi tunanin cewa ko a wurin meeting ɗin da taje ne aka dauke mata waya,Amma daga baya kuma sae ta tuna cewa tayi waya acikin mota lokacin da take shigowa cikin gidan,kodai Amrish ce ta ɗauke su!Nan take gabanta Ya faɗi rass,Sae lokacin ta tuna da wayar Junaid data bari asaman gadon,itama wayar babu ita,tun lokacin da tashigo ɗakin tayi noticing ɗin hakan amma bata kawo komai aranta ba,saboda ranta ya bata cewa ko ba anan ta ajiye wayar tashi ba,

A hargitse ta nufi ƙopar da dukkan ƙarfinta tasa hannu ta tura ƙopar,aikuwa taji an rufeta da mukulli,bubbuga ƙopar tashiga yi tana ƙwala mata kira
“Amrish!Amrish!wlh karki kuskura kice zakiyi mun bincike acikin wayata!kizo ki buɗe ƙopa tunkafin in buɗeta dakaina,”
Ƴan hanjin cikinta ne suka kaɗa lokacin da tajiyo Muryar Mommynta,.
Tabbas in bata yi hanzarin kawar da junaid daga cikin ba,su duka biyun zasu iya rasa ransu,
Duk da halin da take ciki hakan bai hanata mayar ma mommynta martani ba,.
“Wlh bazan buɗe ba mommy,Allah ya kamaki,Yau saina tona maki asiri,”
Kamar ƴar dambe haka Hajiya saratu ta dinga bubbuga ƙopar,
“Amrish wlh idan har kika kuskura kika tona mun asiri,Saina kashe shi acikin gidan nan,”ita duk a tunaninta Amrish a iya binciken wayarta ta tsaya batasan cewa ta gano inda suka 6oye shi ba,
Ganin taƙi zuwa ta buɗe mata ƙopa yasa ta nufi cikin ɗakin tana neman ɗayan key ɗin ɗakin,Gaba ɗaya ta hargitsa ko’ina,
Amrish kuwa yatsun hannunta na kerma Ta shiga ƙoƙarun rubuta ma Sehrish saƙo,Bayan ta tura mata text message ɗin,ta jefar da wayoyin saman Sofa,dabara ce ta fado mata,In har ta shiga ta cikin tagar dakin nan data cire ragarta,Zata Iya ƙoƙarin ku6utar dashi,

Da gudun gaske ta koma Store ɗin nan,Ta janyo jarkar man zuwa saitin tagar,ta haye samanta,hannuwanta ta sanya da dukka ƙarfinta ta ƙarasa yayyaga ragar jikin tagar,dama ta tsufa sosai daga taja saita kece,gaba ɗaya ta yakice ta,saukowa tayi daga saman jarkar ta dauko wayarshi da tayi wurgi da ita a ƙasa ɗakin,ta kunna torchlight ɗinta,Sannan ta koma saman jarkar,Da ƙarfin gaske ta kutsa kanta Cikin tagar,ba ƙaramar wahala tasha ba,Saboda girman jikinta don ma Allah yasa Tagar tana da girma,tana jin sauran ragar dake agefe da gefen tagar tana kartar jikinta amma haka ta jure,gaba ɗaya ta rubza cikin ɗakin,ta faɗo ƙasa timmm cikin ƙurar nan,duk ta 6ata mata fuska,A galabaice ta ɗago tare da sanya hannunta,Tana kakka6e ƙurar dake akan fuskarta,ɗago da wayar hannunta tayi tana haska ɗakin,Ga tsoro ga furgici,miƙewa tayi tana haska ƙasan ɗakin har Allah yasa ta gano inda yake kwance,numfashinshi na fita sama sama,zubewa tayi saman guiwowinta,Ta sanya dukkan hannayenta tare da ɗago dashi,yayi buɗu buɗu dashi,ƙurar duk ta rufe fuskarshi,har cikin hancinshi,baka iya ganin komai daga fatar jikinshi,fashewa amrish tayi da matsanancin kuka,kamar ranta zai fita,ya raunata sosai,Alamun sun nuna cewa yana akan hanyar gangara,daƙyar zai iya rayuwa,rungumeshi tayi ajikinta yayin da zuciyarta ke bugawa,Tunawa da Mommynta yasa Ta yunƙura tare da ɗaukarshi asaman kafaɗarta,Yayin da hannunta ke ruƙe da wayarshi,miƙewar da zatayi kenan hasken fitilar hannunta ya hasko mata Wayarta dake dadda6e da ƙura,bata bi ta kanta ba,don a halin yanzu tafi buƙatar Rayuwar Junaid,Ita dai koda gawarshi ce takai masu su ganshi,dole ta tagar ta fara turashi kamar tsumma haka ya faɗo ƙasan ɗakin,ita ma ta biyo ta window ɗin, a hanzarce ta ɗauke shi,saman kafadarta ta kama hanya,fitowa tayi daga cikin ɗakin ɗauke dashi,Ƙura duk ta buɗesu,musamman shi,kamar dodo haka ya koma,ya rame ya shanye ya bushe Ya ƙanjame bawan Allah

Adai dai Lokacin Hajiya saratu ta samu ɗayan mukullin ɗakin dake a cikin drawer chest,jinjina kai tayi tana huci tamkar zakanya haka ta Nufi bakin ƙopar,Ta murza key ɗin………

*Masu buƙatar karanta Abban Sojoji har zuwa Takun ƙarshe yayi mun magana Ta Layina whatsapp kawai 08103884440*

*Ayi hakuri da wannan*

*_MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_*

*DOMIN. DAWO DA MARTABAN NONONKI*

Shin ko kinsan nono yanada matukar muhimmanci a wajan mai gida ,? Shin ko kinsan babu abunda namiji yafiso yafi daukar hankalinahi kamar cikar k’irji , ? To nono shine babban Martaban mace a wajan mijinta , don babu namijin da zaiso mace mai yakunannen nono kamar silifas ,wannan yasa Nazo maku da sahihi kuma ingantaccen maganin nono Wanda bashida wata matsala hadin gargajiya ne , acikin lokaci kalilan zakisha mamakin yadda nononki zai ciko sosai Wanda wannan cikowar ita zata bashi damar da zai tashi sosai ta yadda kema zaki Shiga cikin jerin mata masu aji agaban mazajensu ……..kedai hanzarta ki nemi mmn Yusuf mai kayan mata yar mutan sokoto zaki samu ingantattun kayan mata masu tafiyar da hankalin maigida…….don neman Karin bayani 07069711327 ……

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment