Littafan Hausa Novels

Yadda Ake Tsara Budurwa A Waya

yadda ake tsara budurwa a waya
Written by Hausa_Novels

Yadda Ake Tsara Budurwa A Waya

 

 

 

 

 

 

 

 

YADDA ZAKA SA MATA KAUNAR KA TUN DAGA NESA

Bari kaji yadda abin yake ;A matakin farko kana bukatar ka san abinda yake burge ‘yan mata da kuma abinda suke so tukunna. Ah’ ah ha ! Kwantar da hankalin ka kaji mana ! Kaa ga! duk ba maganar kokarin ka a makaranta bane ,ko sai Mahaifin ka ya zama wani sannan a soka. Wohoho ! Dadina da kai gajen hakuri ! Nace maka ba sai kayi quru ka sayi Mashin ko Mota ba.

yadda ake tsara budurwa a waya

To waima bari in tambaye ka. Gayu nawa kasha gani basu da ko sisi amma ‘yan mata sun makale musu? Ah toh! Ka ganima ko! Ai na fada maka babu mummuna a Maza !!! Bari kaji sirrin …

Abinda zakayi tashin farko da ka hangeta shine.

Bazawara Ce Ita Hausa Novel Complete

Amma kafin ka tunkare ta ya kamata kasan wadannan sharuddan kamar haka

-Mace bata son matsoraci ko wanda ya cika fariya ko mai girman kai

-Mata basa son namiji mai yanga duk sai yabi ya gundure ta , ah ‘ eh mana ,kana yanga tana yanga me kenan akayi?

– mace tafi son wanda baya jin kunyar fada mata duk wani motsin sonta dake zuciyar sa

– kuma mata basa son hauragiya da harigido ,saboda haka ka natsu ka fuskance ta

– mace tana son namijin da yasan darajar mata ,kaga kenan kar ka kuskura ka bata labarin cewa wai mata dayawa suna sonka amma ka wulakanta su saboda ita da zarar taji haka to kashin ka ya bushe koda ta amsa tana sonka,

-Sannan kar kaje kai tsaye kace ‘Ina sonki’ ai sai ka firgitata, ana buqatar abinnan da turawa suke kira ‘Introduction’ kaga zaka tanaji yan bayanai masu ma’ana kenan wanda suka dace da ita domin ba sakin baki zakayi ka rinka zuba kamar kanyar da ba dadi ba.

– kuma ka nuna mata kasan darajar kanka ,don haka kar ka kuskura ka roqe ta ta soka sai ta raina maka wayau ko kuma ta ja maka aji sosai kafin idan kaci sa’a ta amince ,idan kuma ba’ayi sa’a ba to kuma. abin dai ba’a cewa komai.

Alhamdulillahi kaga ‘yar halak gata can kamar tasan muna nan . Maza tashi ka sameta kaga yadda zata amsa maka…. Ah! ah! me nake gani haka ? Haka zaka tafi da fuskar shanu kamar an maka mutuwa? Dawo! Dawo! Zo in koya maka yadda ake murmushi da irin salon tafiyar da ake yi idan za’a tun kari Budurwa , kwantar da hankalin ka ai ba wahala, yanzu duk zaka iya kafin ta kara so.

Ko baka kalle ni ba zaka iya insha Allahu !yadda ake murmushi shine.

 

KALAMAN SACE ZUCIYAR MACE A FARKO

 

SIRRIN YADDA AKE SACE ZUCIYAR BUDURWA DUK GIRMAN KANTA DA KUMA JAN AJINTA!!! Sanin kowa ne jindadin rayuwa sai mutum ya sami irin Macen da yake so sannan zai gane a dadi yake ko a wahala. Ta yaya zaka shawo kan macen da kake so ka rayu da ita?

 

To dakata! Ita dai mace da kake gani, daga ‘yar shekara 1 zuwa 100, ma’aunin tunaninsu daya ne. Harshenka da kwakwalwarka, makamai ne masu karfin da har yau mace bata mallaki garkuwar kare hare harensu ba. Idan kana so ka sace zuciyar.

budurwa da kalamai, wadanda zasu ratsa ta duk jikinta su sami tabbataccen wajen zama a zuciyarta ya zamana ba mai fada mata taji in bakai ba, koda kuwa iyayenta ne, to kalmomi ne guda bakwai 7 zaka kiyaye. Dasu mace take jin lallai ta sami masoyi

 

matukar taji su cikin bayanan ka da kake mata. Mace tana so taji wadannan kalamai ta bakin duk namijin da ya tsaya a gabanta domin neman soyayyarta. Kuma dayawa daga matan basa gane ya akai ka iya sace mata tunani da zuciya. Karkayi kasa a gwiwa, daka ga mace kana so kai tsaye ka tunkare ta ba da wata fargaba ba. Kana zuwa, dama fuskarka a sake take kamar kaga…

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment