Littafan Hausa Novels

Watan Ramadan Hadissan Barka da Shan Ruwa

Ramadan Day 1
Written by Hausa_Novels

Watan Ramadan Hadissan Barka da Shan Ruwa

 

 

 

 

 

 

 

“Manzon Allah S.A.W yace kaji tsoron Allah duk inda kake, kuma ka biyar da kyakkyawan aiki a kan mummuna, domin ya shafe shi, kuma kayi hulda da mutane, da hulda kyakkyawa”.

“Manzon Allah yace hakika Allah ya hukunta a kyautata akan dukkan komai, idan zaku yi kisa, to ku kyautata abin kisan, Idan za ku yi yanka, to ku kyautata abin yankan, kuma lalle dayanku ya wasa wukarsa, kuma lalle ya hutar da abin yankansa.”

Ramadan 2023 Dates, Images, Pictures and Quotes

“Manzon Allah S.A.W yace Wanda duk ya kasance yayi Imani da Allah, da ranar Lahira, to ya fadi alhairi, ko kuma yayi shiru.”

 

“Imanin dayanku bazai cika ba har sai yaso ma dan uwansa abinda yake so ma kansa”

 

Watan ramadan

“Manzon Allah S.A.W ya ce Yana daga cikin kyawun musuluncin mutum ya bar abin da bai dameshi ba”

 

“an gina addinin musulunci akan abubuwa guda biyar; ka shaida babu wani abinda ya cancanta a bautawa in banda Allah, kuma Annabi Muhammad manzon Allah ne, ka tsaida sallah, kuma ka bayar da zakka, kuma ka ziyarci dakin Alllah, kuma ka azumci watan ramadana”.

 

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment