Littafan Hausa Novels

Wata Uwace Hausa Novel Document

Written by Hausa_Novels

Wata Uwa Hausa Novel Document

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Wata Uwace Hausa Novel Complete

 

BY

 

 

 

MOMMYN MUS’AB

 

 

MARUBUCIYAR

 

ASANADIN BOKO

 

 

ƘADDARAR RAYUWA

AND

 

NOW

 

WATA UWACE

 

 

 

HAPPY BIRTHDAY TO ME

 

DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI

 

 

 

 

GABATARWA

 

INA MAI GODIYA GA UBANGIJI DAYA BANI IKON GAMA LITTAFINA NA BIYU NA SHIGA LITTAFINA NA UKU ,NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GA MAHAIFIYYA TA UWA MAI FARAR ANIYA .

 

 

DAUKAR NAUYI

 

 

IMMUNIZATION CARE OF FTH GOMBE

 

1 and 2

 

 

“Yanzu Ashfat bazaki tashi kibawa yarinyar nono ba tanata kuka ,mesa kike hakane wai yanzu sai munir ya fito yazo ya sameki ko ”

 

Tashi tayi tana mutsutsuka ido tana ƙuƙuni tace

 

 

 

“Kai Umma wlh ni gaba ɗaya yaronnan ya isheni shegen tsotso ne dashi kaman me shikenan dan mutum ya aihu sai bazai huta ba yaroba sai kace ɗan mayu ”

 

 

“Ke dan uwarki ɗan nawane dan mayu lallaima yarinyar nan inbama ikon Allah ba ke kin isa ki shayarmun da ɗana shegiya tun dazu yaronnan yake ihu batashi umma dan Allah karta karɓa ta gani”

 

Fadan munir daya shigo ya sameta tanata mita ,Ummace ta miƙa mata yaron dayake ta tsala ihu kaman ransa zai fita ,tura baki tayi ta juya zata kwanta tas tas ya ɗebeta da mari yace

 

“Wlh ashfat idan baki karɓi ɗannan ba saina sanja miki kamanni marar imani kawai na rantse ki fita a idona zan tattakakifa shashasha kawai sokuwa ”

 

 

Hannu ta miƙa ta karɓi yaron tana tura baki tana ƙuƙuni kafun ta ciro nono tasawa yaron a baki ,kamawa yayi da karfi ya zuka aikuwa ta wankawa yaron mari saboda zafin da taji kafun ta daga hannunta munir ya kaimata maruka guda biyu masu rai da lafiya atare suka fashe da kuka ita da yaron duka yasa kafa zai tokareta Umma tace

 

 

Karanta Littafin Asp Zarah Hausa Novel

“Ayya munir ka rabu da yarinyar nan dan Allah sai dukanta kakeyi akan dannan kasani itama dan tane kuma tafika sonshi domin ita ta haifeshi nasiha zakana mata a sannu zata gane ”

 

 

“Umma kirabu da yarinyar nan wlh saina allata akan yaronnan da iyaye basa shayar da zata rayune ke wace irin WATA UWACE Sokuwa kawai zaki bashi yasha ne ko saina makeki”

 

 

Saita nonon tayi a bakin yaron ya kama tana cije leɓe yafara sha sannan munir yasa kai ya fita a dakin ,girgiza kai Umna tayi tana mamakin zamantakewa irin nasu Ashfat gaba daya ta kasa gane musu .

 

 

Abangaren guda kuwa kawayene guda biyu suna zaune a cikin daki akan wani makeken gado daga ganin gidan kunsan sun wadatu da dukiya ,wanda naji tacewa zaliha ce tace

 

“Yauwa shamsiyya bawai kin aihuba saura ki zauna ki yarda ki lalace duk surarki ta lalace ”

 

kallon ta Shamsiyya tayi tace

 

“Bangane karna bari surata ta lalace ba kimun bayani dalla dalla ”

 

“Abunda nake.nufi shine kinga yanzu kin aihu da kanki gabanki ya bude. wannan tsokar ta koma cikin nahaifa dole saikin dage da gyaran jiki koda kinyi gyaran ma bazaki taɓa dawowa daidai ba me yarage a jikin mai albarka ki cemun nono ,Shamsiyya nonon kine kawai darajarki a gun mijinki kinga mijinki soja ne kinsan sojoji akwai su dason hutu matikar kika walaƙanta jikin ki to wlh zaifara bin matan banza kuma kinshiga uku ”

 

 

Shiru Shamsiyya tayi tana nazarin maganar ƙawarta raliya ,tabbas kawarta tayi gaskiya domin ita duk duniya ba abunda abudulwahab yakeso kaman breast nata domin yasha yana faɗa mata ko lokacin da take budurwa ma idan wuna hira kansu gama sai yaɗan dumbula koda zasuyi faɗa sai ya taɓa ,numfashi taja tace

 

 

 

“Gaskiyarki raliya kuma banma an kareba saida kika faɗamun gaskiya nagode dama tun dawowar mu yarinyar tana bacci kinga kafun ta tashi saina sama mata madara pls kimin wata alfarma zan baki kuɗi kisayomun in boye dan yanzu mommy tana ganina kashina ya bushe ”

 

Bakida matsala kikawo insayo miki ”

 

Tashi tayi ta dauko kudi a jakarta ta mika mata ta fita daga gidan tana zuwa wani babban pharmacy taje ta samu likitan tace

 

 

“Barkan kade doctor”

“Barkankide”

 

 

“Yauwa doctor inaso kabani madara wanda zaana bawa jarirai wanda aka haufa dazu ”

 

 

“Ok ina mahaifiyarta ”

 

 

Shiru tayi sannan tace

 

 

“Eh mamar batada lafiya neh bata hayyacinta kuma babu ruwan nono gashi ƴar tanata kuka ”

 

 

“Ok ”

 

 

yace sannan ya tashi ya miko mata ta juya tashiga motar ta ta fita .

 

 

 

Washe gari da safe Umma tana daura karyawa ,jaririn ashfat ne.yake ta tsala ihu tana baccinta Umma kuwa tanata fama da wutar damuwa munir ne ya shigo ya kalli Umma yace

 

 

“Subhanallah ,haba Umma yanzu keda nake ganin ki babbar ma haka zaki dawo kiji yadda yaronnan yake ihu waini in yaronnan ya mutu kam mai zakucemun ne ina ashfat din take ”

 

 

Yafaɗa yana shiga cikin dakin da sauri Umma tabishi domin tasan yanzu zaije ya mammake ta ,aikuwa kaman ta sani tana shiga yana zabga mata mari aikuwa ta firgita ta tashi ta fashe da kuka ya daura mata yaron akan cinyar ta yace

 

 

“Maza kibashi nono yasha yanzu sannan kigama bashi mutafi rigakafi don an fadamun yiwa yaro rigakafi bayan aihuwa zaikareshi daga cututtuka ”

 

 

Itade batace komai ba sai shishitar kukan da takeyi yaro kuwa sai zuƙar nono yakeyi kaman dan…..

 

 

Au fans na manta munir ya hana cewa dan mayu

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment