Littafan Hausa Novels

Wata Rana Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Wata Rana Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

WATAN WATA RANA

 

 

 

 

 

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

P.M.L.

 

 

 

_Writings by:_

 

 

*Fadeelah (FaShuNa)*

*Faridat Musa*

*RØØKÏÊY KÆXS*

*princess Eshat Aysm*

*meryerm Abdool*

*Husna Bauchi*

 

 

 

_*Muna yiwa yan uwa barka da sallah, Allah yamaimaita mana na bad’in ba d’ad’a Ameen*_

 

 

 

 

Page 1–5 *FaShuNa*

 

 

 

 

Adaidai titin Amadu Bello way,wata mota k’irar 4matic black colour da gudu tazo ta wuce, tsabar gudun datake bakace yarinya ce k’arama take wannan gudun ba, sai kayi tunanin masu tseran motone, Allah ne kad’ai yasan inda baiwarsa ta nufa sai kuma ni mai suburbud’omuku labarin, muje zuwa.

 

 

Awani katafaran gida abakin gate, ta tsaya ta nafaman hon d’et d’ettttttt, Allah Allah take abud’e mata tabar gurin ko hankalinta zai kwanta.

 

Da sauri Malam Idi mai gadi yabud’e mata get d’in, k’arfin halima yakeyi d’an yasoma yafi k’arfinsa tsabar tsufan dayake dashi.

 

Mijin Bazawara Hausa Novel Complete

Bai k’arasa bud’ewaba tai shigewarta saura kad’an ta bugesa, shikansa parking d’in motar datai ba a dai-dai tayishiba, da gudu tafito tai cikin gida, tabar Malan Idi rik’e da baki.

 

 

Malam Idi har tashige cikin gidan yana kallanta, aransa yana tunanin wannan hali ba halin _AIDA_ bane yarinya mai hankali da tunani yace tai wannan shigowar, yadda take ganin mutuncinsa da girman tsufansa tazo wucewa bata gaisheshiba, inbanda k’addara mai zai kawo Aida baiwar Allah gidannan tabar iyayanta, kyakkyawar yarinya mai hankali, anbata mata rayuwarta, amma yana fatan *WATAN WATA RANA* zata daina abinda takeyi tadawo hanya madai daiciya kullum addu’arsa kenan Allah yashirya baiwar nan taka Aida,Yana rok’on Allah karya d’au ransa batare dayaga shiryuwar Aida ba.

 

 

Toh Malam Idi irin wanna soyayya da kake nunawa Aida komeye dalili? muje zuwa.

 

 

 

Tana dosar cikin falon, taji gurnanine ketashi tsabar masha’ar da ake aikatawa, matane suke aikata alfasha,wa’iyazubillah Allah kashirya dukkan musulmi gaba d’aya, ka karemana zuri’armu, Ameen.

 

Ita kanta Aida ta tsani tashigo ta tarar da irin wannan acikin falon amma yazatayi bata da damar hanawa.

 

 

Wata hamshak’iyar matace azaune tana kallan kowa daya bayan daya, sai wata yarinya wacce bazata wuce 11 years ba tana mammatsa mata k’afa, ita kuma sai faman shashshafata takeyi, tana ganin Aida tai saurin ture ta, yarinyar tafad’i ta bugu da gefan kujera.

 

 

Da saurinta tace “Aida ta meya sameki naga ranki ab’ace wanene ya b’atamiki rai? yaga ba dai daiba”, tajanyota kan cinyarta fad’an waye.

 

 

Jitake da Aida sosai dan tasha bak’ar wuya kafin tasameta shiyasa take lallab’ata bata son bacin ranta dan akwaita da shiga rai, shiyasa suka lak’anta mata ‘Yar baiwa.

 

 

Da kyar Aida tabud’e baki tayi magana, “wannan yar rainin hankalince Aifat wai ni zataiwa Yar uwa ta had’ani da wata k’azama! to tasani daga yau munyi hannun riga da ita bani babu ita”.

 

 

Tunda tafara maganar harta gama Hajiyar babba ita take kallo, magana Aida ita kanta abin saurarace balle ka kalleta, fara ce amma ba sosaiba akwaita dacikar gashin gira da ido hancinta mai kyaune, kanta cike yakeda gashi,gawani dimple daya kara mata kyau.

 

 

Kowane lokaci intana magana Hajiya babba tana kallanta dan tana yawan burgeta, takance dama itace da kyan Aida wai kubundu kenan

 

 

“Haba Aida mene na damuwa akan Aifat tasamu wata, shine zaki wani bata ranki rabu da ita ga yaranan kala-kala acikin gidannan sai wacce kika zaba kika darje, ko kuma gani kinsan tuntuni ina kwad’ayin na muganmu tare “tafada tare da marairaice wa kana kallan fuskarta kace buhun kwakine yadoso gun tsabar muninta.

 

 

 

Wani abune ya tsayawa Aida azuciya dan bak’in ciki,tace ” nagayamiki Hajiya bana son irin wannan abun itama can Aifat d’in damuke tare da itace sanadiyar shigowata cikin harkarnan ita tab’atan rayuwata ta rabani da iyayena da ‘yan uwana ta kawoni cikin wannan k’azamar rayuwar, yanzu inna mutu mezan cewa Allah awannan yana yin danake ciki “tafashe da kuka mai ban tausayi.

 

 

 

Wacece Aida?

Kuma meye dalilin shigarta neman mata?

Kuma wacce Aifat?

 

 

 

 

Kubiyomu kusha labari

 

 

 

 

 

 

FaShuNan kuce

 

WATAN WATA RANA

 

 

 

 

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

P.M.L

 

 

_Writing by:_

 

*Fadeelah (Fashuna)*

*Princess Eshat Aysm*

*Faridat musa*

*Rookiey kaxs*

*Meryerm Abdool*

*Husnah Bauchi*

 

 

 

Page 6 –10 *Princess Eshat Aysm*

 

 

 

 

 

 

 

*WACECE AIDA?*

Y’ace ga Malam Audu, Mahaifiyar ta MAIRO amma tana k’iranta Inna ta taso cikin gata da kulawa kasancewar ita kad’ai suka haifa.

Malam Audu talakane sosai Kayan Miya Yake D’an Sara Yana Siyarwa, saidai yanada wadatar zuci, talaucinsa bai hana yabaiwa y’arsa ilimi ba.

 

 

Yauma Kamar Kullum Tafito Zata Makaranta Lokacin Tana Primary 5, Ta Karya Kwana Zata Shiga Kwanar Gidansu Aifat, Taga Mutum Agabanta Yana Murmushi.

Ta Watsa Mai Harara Tace “Malam Kamatsamun Na Wuce”

Yagyara Tsayuwa Yace “ke Kullum Saikinbiya ta gidansu Aifat Ne? Nasan Ita Take Saku Latti.”

 

 

Takad’amasa Idanuwanta Dasuke Kusan Sumar Dashi Tace “Ahseef don Allah kamatsamun nawuce”

Baiyi Musuba Yabata Hanya Tawuce, Yabita Da Kallo Yana Murmushi.

 

 

Ahseef Yarone Matashi D’an Kimanin Shekaru 20, Allah Yajarabceshi Da Tsananin K’aunar AIDA Tun Tana Y’ar Mitsitsiya.

Mahaifinshi Alhaji Sagir Yanada Dukiya Daidai Gwargwado.

 

 

Ahseef Yaron Kirki Kullum Zaka Ganshi Tareda Mahaifin Aida Ko Agida Ko Akasuwa Sun Shak’u Sosai, Kullum Adduar Malam

Audu Baiwuce Allah Yabaiwa Aida Wannan Yaron ba.

 

 

Aida Kuwa Batada Mak’iyin da Yawuce Ahseef Arayuwarta.

Duk Randa Yamata Magana Ji Takeyi Kamar Yana Watsa Mata Wuta Duk da Lokacin Batasan So ba, Balle Tagane Sonta Yakeyi! Itadai ji takeyi Tsaneshi Kawai.

 

 

 

Tana Isa Gidansu Aifat Tagaida Ummanta Tawuce D’aki, Tasamu Ko Shiryawa Batayiba.

Duk B’ata Lokacin Aifat Akan Kwalliya Yake K’arewa Kamar Wacce Zata Canza Kamanni.

 

 

Aida Tad’anja Tsaki Lokacin da Take Zama, Aifat da Tun Shigowarta Tagane Tana Cikin damuwa tace “Waye Yatab’amun ke?”

Saida Tad’an Sake Jan Tsaki “Tace Wallahi Banason Ganin Ahseef D’innan, Amma Kullum Saina Ganshi.

 

Aifat ta yatsuna fuska tace “kimanta dashi yafiye kallo dayawa, ni wallahi idan naga kina kulashi haushi nakeji”

 

Aida tamik’e tace “kinga lokaci yak’ure, narasa mawa kike wannan kwalliya da baya k’arewa, kefa kyakyawa ce kidaina b’ata lokacinki wajen fente fuska.”

 

 

Aifat tayi dariyar jin dad’i domin arayuwar ta ba abunda tafiso kamar kace mata ita kyakkyawace.

 

 

Sai kusan 8am suka isa skul.

 

 

 

 

Ahseef tun shigewar Aida yatsinci kanshi cikin farinciki, kai tsaye gidansu Aida yanufa.

 

Bayan sun gaisa da Inna Mero yashige wajen Malam Audu a kasuwa.

 

 

Aida yarinyace kyakkyawa mai hazak’a, tanada hankali ga nutsuwa, tasan darajar mutane tana girmama na gaba da ita, akasin k’awarta.

Shiyasa tazamo abun alfahari ga kowa.

 

 

 

 

 

Aifat itama tanada kyau amma batakai Aida ba, sai shegen rawar kai da son kyawawan k’awaye.

 

 

 

 

Muje zuwa!!

 

 

……………….,…………………………….

 

Malam Audu dayake ta shirya kayan miya akan table yace “Ahseef ya maganar karatun naka?

Haryanzu ba’a samu admission d’in bane?”.

 

Yace “ansamu Baba sai farkon month d’in dazamu shiga zanfara zuwa.”

 

“Au to to Allah yasa a fara a sa’a.”

Yace “ameen”.

 

Shiru sukayi natsawon mintuna, Ahsif yace “Baba ina neman wata alfarma”

 

Malam Audu yabar abunda yakeyi yana sauraronsa.

 

Yad’an sosa k’eya yace

“Ina neman alfarmar kabani Aida amatsayin wacce zata zamo matata anan gaba, wallahi ina masifar sonta zankula maka da ita kamar yadda take samun gata awajenku, katausayamun kayimun alk’awarin aurenta”

 

Malam Audu yayi matuk’ar jin dad’in wannan zance saboda yadad’e yana fatan haka aranshi.

 

Yace “kaikuwa Ahseef Aida k’aramar yarinyace ai”

 

Ahseef yagyara zama “yace Baba ba lallai sai yanzuba zanjira ta girma tsawon lokaci”

 

 

Malam Audu ya fad’ad’a fara’arsa yace “yace Allah yasanya alkairi zanyi shawara da mahaifiyrta”.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Aha!! Love you all my fans.

 

Princess Eshat dinkuce

Faridat Musa

 

WATAN WATA RANA

 

 

 

*®pure moment of life writer’s* *(p•m•l)*

 

 

_writings by:_

 

 

*Fadeelah (fashuna)*

*Princess Eshat Aysm*

*Fhareedat Musa*

*Rookie kaxs*

*Maryerm abdool*

*Husnah bauchi*

 

 

 

*Dedication this page to all writer’s ubangiji ya k’ara had’a Kawu nan mu*

 

 

 

*Page 16–20 by HUSNAH ABUBAKAR BAUCHI*

 

 

 

 

Aida da Aifat sun kammala karatun su na secondary school Aifat kullum burinta bai wuce taja hankalin Aida suna gudanan da alfashar su tare ba amma ina Aida har yanzu takasa canja rayuwar ta domin Aida yarinya ce abar alfahari ga iyayan ta abar alfahari ga Malamanta abar a fari acikin dangi a kullum tana alfahari da kanta cox tun taso warta iyayanta suke shimata albarka,

 

 

*WATA RANA*

 

 

Aifat da Aida suna zaune a gidan su Aida a cikin d’akin da Aida ke kwana Aifat ta dubeta k’asa da sama tace

 

“Aida kallo ki mace har mace amma ace kin kasa gane yanda rayuwar nan ta dosa yanzu Aida kallo yanda rayuwa ta ta canja a cikin d’an k’aik’anin lokaci a yanzu Aida ina da dukiyar da zan iya siyan mota kuma bada ga hannun iyayena suka fitoba kinga wayar nan dake hannun mu a yanzu ba abun dabaza ki koya a cikin taba Aida inason sonki da alkairee ne kallo fa yanzu irin surutun sawa ma Aida ga garki suke ni kuma fa in naga dama a yau sai na siye suturun da zan shekara ina sawa Aida ki bud’e wayar nan zakiga komai a cikin ta ita kad’ai ta isa ta miki bayani ba sai na tsaya b’ata lokaci na ba”

 

 

“Aifat na fad’a miki idan su ummah sukaga wayar nan kwace wa zasuyi yanzu haka duk kud’in da muke samu da kuma suturan sawa wallahi bana sasu suna ajiye bakiga bani amfani da suba ne?”

 

 

“Kai Aida wallahi kina bani mamaki yanzu ace keda d’akinki ke kad’ai amma baza ki iya adanan phone a cikin saba ni a gaskiya Aida ban san irin wannan abun dakike”

 

 

“Hmm! Arfat Kenan baki san halin Ummah da Abbana bane shiyasa kike fad’in haka amma ba komai phone nasan yanda zanyi da ita karki damu”

 

 

“Ok ko kefa na bud’e miki WhatsApp nasaki a wani group namu na manyan Mata k’arfe 8:0pm ki bud’e data naki zamu tattauna wata magana”

 

 

“Ok to”

 

 

“To ni zan wuce My Aida dan Allah karki kasa kallon abin dake cikin wayar nan dan in kin kalleshi saki fi gane yanda harkai tamu take tafiya”

 

 

“In Allah ya yarda zan kalla Aifat sai kin jini”

 

 

“Yauwa My Aida”

 

 

Rik’e suka fito da hannun juna Ummah tana kitchen tana fama da itace d’anye sunk’i kama wa idonta sai zubda ruwa yake muryar Aida da Aifat taji suna cewa “Ummah” fitowa tayi daga kitchen d’in tana cewa “Aifat har kin fito ne?”.

 

“Eh wallahi Ummah naga dare ya fara kar a nemeni a gida”.

 

“Eh kuma haka ne da gaskiyarki ki gaida min da Maman ki”.

 

 

“Zataji Ummah sai da safe”.

 

 

“To Allah ya tashemu Aifat Allah ya bar Ku tare de wannan k’awancan na ku abin sha’awa”

 

 

“Ameen Ummah”su biyun suka amsa a tare Ummah tai murmushi ta koma kitchen, ita kuma Aifat ta fita daga gidan suna d’aga wa junansu hannu, ba gida ta wuce kai tsaye ba, gidan wata Hajiya ta wuce, wacce zamu iya cewa itace silar sa Aida a hanyar bin manyan Mata domin kuwa ta dalilintane Aida tafara zuwa abuja da Lagos,

 

 

_______________________________

*WAI SHIN WACECE AIFAT?*

 

 

Aifa y’ace a wajan alhaji Amadu mai kananzir Alhaji Amudu mutum ne mai son duniya Dan baya kula da tarbiyar y’ay’ansa shi dai ya samu kud’i kawai ya kashe su a banza da wofi yana da yara maza biyu sai ta ukunsu itace Aifat, Maman su itama macece mai son duniya amma bata samu miji mai sake mata aljihuba dan haka tasha alwashin yarinyar ta sai ta zama tauraruwa domin duk burin Halima akan Aifat ya k’are d’an su Babba Abdullahi, yarone mai hankali da nutsuwa shine mai kula da shige da ficen Aifat amma Maman shi tace bata son sa ido, Dan haka ya fita harkan ta badan ransa ya soba Dan yana lura da irin lalacewar da k’anwar tasa tayi tuntana ‘yar shekara 11 amma yana magana Mama zata haushi da fad’a da yaga abin yafi k’arfinsa sai ya tattare nasa ya nasa yabar musu gidan ya koma can wajan yayan baban sa da zama ita kuma Mama tak’ara d’aure wa y’ar tata gindi, Dan haka Aifat bata shakkar fita daga gida a duk lokacin da taso fita.

 

 

*WANNAN KENAN*

 

 

 

Bayan fitar Aifat daga gidansu Aida, Aida ta shiga kitchen ta taya Maman ta aiki bayan sun gama suka d’aura alwala sukai sallah suna kan daddumar da sukai sallah basu tashi ba har Abba ya shigo da sallamah suka amsa masa tare da yi masa sannu da zuwa, Ummah ta tashi ta d’ebo masa ruwa kamar yanda ta sab’a bayan yasha yace,

 

 

 

“Arfat alhmdulillah yaunce Ranar da zan fad’a miki buk’ata ta a gareki wanda ina fatan baza ki bijire ma Umurnina ba, Aida ina fatan kin san Ahseef?”.

 

 

“Eh Abba na sanshi”.

 

“To alhmdllh dama ya zomin da buk’atar Neman Auran ki kuma na amince masa amma munyi da iyayan sa akan sai kin kammala karatu zan sanar dake to gashi yau Allah ya kawomu Ranar da kika kammala karatunki, kuma gama karatun ki yayi daidai da samun aikin Aheef Dan haka yanzu ke kawai muke jira muji ta bakin ki”.

 

 

 

Hawaye ne suka fara zarya akan kumatun Aida ta kasa cewa uffan, sai hawayan dake bin kumatunta Ummah ce tace.

 

 

“Ke Aida Lafiya daga miki magana zaki fara yi wa mutane kuka ba tambayar ki akeyi bane”

 

 

Aida dai ko kallon inda suke batayiba ta tashi da gudu ta wuce d’aki.

 

 

“Wai ne yarinyar nan take nufi kenan ?” Inji Abba Ummah tace “abarta mugani zuwa gobe muji me zata ce” “to Allah ya kaimu goben amma karma ta kuskura tace min bata son Ahseef Dan wallahi baza ta miyar dani dattijon banza ba” .

 

 

Ummah tace “insha Allahu hakan baza ta kasance ba”.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment