Littafan Hausa Novels

Wata Kishiyar Page 54 Hausa Novel

Written by Hausa_Novels

Wata Kishiyar Page 54 Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

 

 

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

 

 

Wattpad @MaryamahMrsAm

 

Page 54

 

Washe garin ranar tun goman safe Bala ya sake zuwa, yau ma wuni sukayi dai suna ta tattaunawa duk dai akan Asma’un ne har kuma yamma Bala beyi shirin tafi ba seda Bashir da kansa ya tambayeshi wai ba yace aiki ne ya kawo shi ba yaushe ze fara.

Abinda Zuciyata ta zaba Hausa Novels

Cikin kame kame Balan yake ce masa

“Eh daman aikin na kwana daya ne mun gama kawai dai ina so na huta ne. Ni na gaji da zaman gida ma mu fita waje mu sha iska kuma ita wannan matar daman haka take bata dafa abinci ne?”

Shiru Bashir yayi masa harya qaraci surutunda yayi shiru, be haqura ba bayan wani lokaci ya sake ce masa su fita waje dole ya takurawa Bashir din seda suka fita wajen suka saka kujeru suka zauna.

 

Basu jima a gurin ba motar makaranta ta sauke yara, gaba daya suka gaishe su, Bala ya kamo hannun Abdallah yana cewa

 

“Abdallahn Mami an dawo kenan. Ya naganku a school Bus ina Mamin taku?”

“Daman a school bus muke dawowa” Abdallah ya fada yana shigewa cikin gida yabi bayan yan uwansa.

 

“Wai mutumin ta dena dakko yara daga makarantar kenan?” Bala ya fada yana yar dariyar nan irin ta wanda yaso munafunci akayi sa’a ko kallonsa Bashir beyi ba hankalinsa yana kan wayarsa da yake dannawa.

 

Kusan minti talatin wata hadaddiyar mota Toyota latest model Baqa ta kunno kai cikin layin, daga Bashir har Balan da ido suka bita harta tsaya a daidai qofar gidan Ma’u, seda aka kwashi yan mintina kafin qofar ta bude ta zuro fararen qafafunta da suka sha Jan lalle sukayi shar dasu ga wasu hadaddun takalma na yan gayu masu tsinin dunduniya data saka.

 

Lokaci daya ta fito gaba dayanta, tana sanye da straight gown ta Ash din Leshi tayi daurin nan nata na tsokano sharia kunnenta saqale da AirPod tana murmushi da alama waya takeyi ba tareda ta kalli ko ina ba ta qarasa bakin qofa ta kwankwaso Amnah tazo ta bude tareda karbar jakar hannunta suka maida qofa suka rufe.

 

A tare Bashir da Bala suka sauke wata Ajiyar zuciya. Shi Bashir tashi ta ganin Asma’u ce ita kadai ta fito daga motar saboda yanzu har fargaba yake yaga sabuwar mota me kyau a layin tunda Asma’u ta fara kule kulen nan idan yaga mota ta shigo zuciyarsa ta ringa lugude kenan harse yaga wanda yake cikinta sannan hankalinsa yake kwnaciya.

 

Bala kuwa tsabar yanda Haduwar Ma’u ta tafi dashi ne se bude baki yake amma ya kasa cewa komai harta shige gidan se ya sauke ajiyar zuciya ya waiwaya yana kallon Bashir yace

 

“Kaga wata Arniyar mota Alaji ga kuma hadaddiyar mata ta fito daga ciki kai ina ma ace na samu irinta ai wallahi komai ma zan iya bayarwa indai zan mallaki wannan”.

 

“Asma’u ce fa” Bashir ya fada yana jifansa da wani kallo, Bala kuwa ko a jikinsa sema tabe baki da yayi yace

 

“Ita dinfa, Allahna tuba ni ko Asma’u na samu ai da mugun gudu zan karbeta dan ni nasan darajar irinta. Ai wallahi ban taba sanin kai lusari bane se randa kace mun ka saki Ma’u, yo Allah na tuba ko yankar naman jikina zata ringayi ai zan jure kai in fita ma a kalleni ace ga irin matar da nake aure ma ai martaba ce”.

 

Sakin baki kawai Bashir yayi yana kallon Bala daya dage yana rattabo magana, Lusari daya kira shi ma be dame shi ba kamar jingina kansa da Ma’u da yayi. A mugun fusace ya shaqo wuyansa jin yana ci gaba da maganarsa yace

 

“Idan ka sake hada kanka da Matata sena yanke maka harshe…”

 

“Malam tsohuwar matarka dai ko ka manta ka sake ta ne, kuma wallahi dan dai bazata saurareni bane amma duk da haka ma bari kaji sena gwada sa’a ta waya sani ko rabo na ne ya rantse Allah ya matse ka ka saketa” Bala ya fada yana banbare hannun Bashir daga wuyansa.

 

Tsabar mamaki Bashir daskarewa yayi a gurin be dawo hayyacinsa ba seda Bala ya kusa barin layin ko kafin ya yunqura ma ya bace masa.

Naushi ya kaiwa Iska cikin azababben kishi da fushin da suka turnuqeshi.

 

Kenan angiza me kantu Bala ya ringa yi masa yana nuna masa aibun ta yana qara kambama masa laifuffukanta har seda ya rabu da Ma’u shine yanzu ze zo yana cewa idan ya sameta shi baze rabu da ita ba. Wai ma ina hankalinsa yake da duk be taba lura da hakan ba se yanzu?

 

“Kaico na dana zama me daukar zugar was akan iyalina, kaicona ni Bashir da na fifita lalataccen Aboki akan masu gaya mun gaskiya” ya fada yana dafe kansa.

 

Cikin gidansa ya koma suka hadu da yan biyu zasu fita da gudu ya kauce musu yana binsu da kallo cike da tausayin kansa.

 

Haka kawai ya raba musu kai ya saka suna rayuwa tsakanin gidaje guda biyu. Shidai ya yarda da qaddara ce ta gifta data tilasta rabuwarsa da Ma’u kuma Allah kadai yasan hikimar sa tayin haka. Baze sare ba yanzu nema ze daura dambar gyaran kuskurensa ya kuma maido da Asma’u cikin rayuwarsa kota halin qaqa.

 

Dakinsa ya shiga ya tarar da Amirah tayi daidai akan gado tana sauke numfashi, fuskarta ya kalla kafin ya kalli qasan Tiles yaga amai ne a Gurin. A mugun fusace yace mata

 

“Ki tabbata kafin na shiga na fito kin gyara gurin nan yanda kika tarar dashi idan ba haka ba na lahira se ya fiki jin dadi yau a gidan nan” yana gama fada yayi gaba ze shige bandaki ya jiyota cikin kuka tana cewa

 

“Nifa bani da lafiya, zuwa ma nayi na gaya maka shine amai ya kamani gaskiya bazan iya tashi bama bare na gyara guri”.

 

“Ko mutuwa kike kina tashi se kin gyara gurin nan, duk gidan nan nan gurin ne yayi miki kama da kizo ki zuba qazantarki? Amma karki kwashe ki jira na fito na tarar dashi a nan” ya shige Bandakin ya barta a gurin.

 

Yanayinsa da ta gani tasan tabbas ba tausaya mata zeyi ba idan ya fito din, haka ta tashi ta dakko tsintsiya da abin kwashe shara ta debe kafin ta debo ruwa da mopper ta gyara gurin se haki takeyi tana gamawa ta wuce dakinta ta ta fada kan gado kawai ta fashe da kuka.

 

Wannan masifa har ina? Ace kana da ciki amma banda hantara da kyara ba abinda yake shiga tsakaninka da uban cikin se baqin rai to ko ana so ko ba’a so seta haife cikin nan sedai baqin ciki ya kashe mutum.

 

Bashir kuwa yana shiga ruwa ya sakarwa kansa ba tareda ya cire kayan jikinsa ba. Kalaman Ba ne suke masa yawo a kwakwalwa suna barazanar fasa masa ita.

 

Shi Bala zece yana son matarsa? A yanda ya dauki Bala ya zata ko mutuwa yayi se inda qarfinsa ya qare gurin kare masa martabar gonarsa amma se gashi da ransa rabuwa kawai sukayi yana iqirarin idan zata so shi ze aure ta gaskiya dole ya koyawa Bala hankali ta yanda ba matarsa ba ko wata can a gari aka saka baze sake sha’awar cewa ze aureta ba.

 

Tsabar yanda kansa ya dauki zafi haka ya fito jikinsa na digar da ruwa ya manta da kaya a jikinsa seda ya kai tsakiyar dakin kafin ya ja tsaki ya koma ciki, wanka ya sakeyi ya fito.

 

A gurguje ya shirya, gidan Musa yake so yaje yanzu yana buqatar wanda ze fadawa abinda yake ransa ko zeji dadi.

 

Sanda ya fito bebi takan Amirah ba, a bakij qofa ya hadu da Jafar ya taho da paper bag a hannunsa suna zuwa kusa yaji qanshin Snack be bata lokaci ba ya miqawa Jafar din hannu ya kuwa bashi ya tsaya kawai yana kallonsa.

 

Meatpie ne guda uku manya a ciki, se ya zaro daya ya miqawa Jafar din Murya a cunkushe yace masa

“Dakko mun Exotic ne sanyi” Jafar ya kwasa da sauri ya wuce Kitchen kafin ya dawo har Bashir ya kunna mota yana bashi kuwa ya qara gaba.

 

Yana tafe yana cin Meat pie yana kora lemonsa can qasan zuciyarsa kuwa yama rasa wanne tunani ze kama yayi a haka ya qarasa gidan Musa ya tarar be taso daga aiki ba se ya kirashi a waya yace masa yana hanya ya kusa qarasowa dan haka ya jira shi.

 

Seda sukayi sallar Magriba sannan suka shiga gidan. Musa na tattare kayan da suke kan kujera yace

“Se haquri Engineer kasan gidan Gwauro ko ina ma zubarda kaya muke tunda bamu da masu tattare mana”

 

Bashir dai yaqe yayi har Musa ya gama ya dakko musu ruwa da Lemo da Abincin daya taho dashi ya zauna se ya kalli Bashir da yayi shiru ya zubawa guri daya ido yace

 

“Yadai Bash naga kayi shiru ko dai jikin ne har yanzu?”

Numfashi Bashir ya sauke yana gyara zama yace

“Musa akwai matsala ina jin kamar kaina ze fashe wallahi damuwa tayi mun yawa”.

 

Musa daya debi abinci ya kai baki yayi saurin hadiyewa yana kallon Bashir ya gyara zama yace

 

“Wace irin Matsala kuma Bashir meya faru?”

 

Ba bata lokaci Bashir ya shiga lissafa masa abinda ya faru tun daga kan dalilin sakin Ma’u har zuwa yanayin da ake ciki a yanzu haka da maganar da Bala ya fada masa. Musa da tuni ya sume a zaune yana kallon Bashir seda ya kai aya kafin yaja numfashi ya dire yace

 

“Gaskiya Bashir ka tafka wauta qundumemiya ma kuwa kai wa yace maka ana rabuwa da matar fari, matar dakuka sha wahalar ku tare sannan yanzu ka saketa akan wata can da ka ganta rana tsaka Bashir ka rabu da matar ka uwar yayanka gaskiya ka bani kunya ka kuma bani mamaki tsahon lokacin nan ace baka tare da Asma’u amma baka gaya mun ba.

 

To ni yanzu me zanyi maka ma ai ka riga kwabarka tayi ruwa sedai na baka haquri kawai Allah ya kawo maka dangana amma duk macen dakayiwa haka ka sake ta akan yar uwarta mace gaskiya da wuya tayi haquri ta sake dawo maka dan ka rigada ka nuna mata iyakarka ka nuna mata cewar waccen ta fita martaba da mutunchi a gurinka to zaman me zata sakeyi da kai?”

 

“Haba Musa kaida nazo neman mafita a gurin ka ya zaka ringa magana haka?

Dan Allah ka taimakamun ka bani magita ina son matata bana so na rasata” Bashir ya fada kamar me shirin saka kuka.

 

Musa kuwa Ido ya saka masa yayi tagumi yana kallonsa har yayi ya gama sannan yace

 

“Kanaji ko shawarar da zan baka kawai ita ce ka tafi malam ka gwada sa’arka, wani girman kai duk ba naka bane yanzu dan ka rigada ka kwafsa yawwa kaje ka sauke kai qasa ko roqeta in Allah ya soka ta haqura ta dawo maka shikenan amma dai Asara kam ka tafka wallahi”.

 

Haka suka rabu da Musa ya koma gida yana sake tunanin abinda ya gaya masa kuma ya tabbatar hakan shine mafita dole ya nemi yardar Asma’u dan baze tsaya yayiwa kansa salalan tsiya ba.

 

Ya tarar da Amirah na fama da kanta tayi amai ta galabaita kamar bazata kai ba, dole ya dauketa suka tafi Asibiti saboda yanayin jikin dole se gado aka bata. Seda ya biya duk abinda ya kamata kafin ya barta ya tafi gida da yaje be tarar da Yaran ba Aliyu ne kadai yace sauran suna gidan Mami. Be damu ba yayi kwanciyarsa, dan yanzu yafi samun kwanciyar hankali ma idan suna can saboda anan sun ringa tsokanar Amirah ita kuma tayi ta sababi tanazage zage.

 

Washe gari ya kamata ya koma aiki haka ya tattara ya fita seda ma ya kusa isa ya tuna da Amirah dake Asibiti be biya ya dubata ba bare ya kai mata abinda zata ci duk da dai Asibitin suna bada Abinci.

 

A waya yayi order abinci ya basu Adireshin Asibitin dan baze iya komawa ba, haka ya wuni sukuku a gurin aiki se sannu ake masa dan duk a zatonsu jikin nasa ne har sannan be gama warwarewa ba haka ya tashi kai tsaye ya wuce Asibitin dan duba halin da Amiran take ciki.

 

Da kuka haiqan ta tareshi tana masa qorafin baya sonta be damu da ita ba tunda ya banzatar da ita a Asibiti be sake bi ta kanta ba. Ganin mitar bame qarewa bace ya tafi ya barta dan abinda yake kansa ma a yanzu ya isheshi bayay buqatar qarin wani abun kuma.

 

Ya isa gida ya kasa tsaye ya kasa zaune. Tunanin yanda ze tunkari Ma’u yakeyi, meze ce mata? Ta yaya ze tunkareta?

 

Wayarsa data dauki qara ce ta katse masa tunani, shnan Dada da ya gani ya sakashi dagawa da sauri.

 

Bayan sun gaisa take ce masa

“Bashir Ashe Amirah bataji dadi ba har tana Asibiti?”

 

“Eh wallahi Dada jiya da daddare ne zuwa yau amma gobe ma zasu sallameta ai” Ya fada yana mamakin waya kirasu ya gaya musu bata da lafiya.

 

“Toh ai shikenan Allah ya bada lafiya amma ya kamata ta samu wani babba a kusa da ze ringa kula da ita saboda yanayin jikin kaga tana da zafin laulayi dole seta samu mataimaki”

 

“To ai anan din ma ba abinda takeyi tun tana da lafiyar ma se shirme kawai ta iya” ya fada a hasale

 

“Haka za’ayita haquri dai, seka turo da kudin jirgi na wanda ze zo ya tayata zaman dai, ya bangaren su Asma’u kuwa in ce dai abubuwa sun dai daita ko?”

 

“Hmmmm” kawai Bashir ya fada daga nan sukayi sallama dan besan me ze ce mata ba ma, qarin haushin sa ma wani da tace za’a turo ya taya Amirah zama in dan ta shine a barta ta gane kurenta wallahi haka ba yadda ya iya ya turawa da Naziru kudin dan yana tunanin Fainusa za’a turo ko banza gidan ya samu kulawa ai.

 

Shiru ya sakeyi yana tunani, kiranta zeyi ko kuwa kawai zuwa zeyi suyi magana fuska da fuska?

 

Yanke shawarar ya fara kiranta yayi a waya nan da nan yayi Na’am da wannan shawara ya shiga loda lambar wayar Ma’u da ya dade da haddacewa ya dannan mata kira.

 

Seda tayi ringin harta katse bata dauka ba, be haqura ba ya sake kira nan ma bata daga ba seda yayi mata kira uku ana hudu ta daga cikin muryar nan tata me sanyi tayi masa sallama.

 

Shiru yayi, ta sake maimaita sallamar se kawai ta kashe bayan data ja qaramin tsaki. Be sare ba ya sake doka mata kira, cikin dan fada fada ta daga wannan karon tace

“Waye wai? An kira ni kuma anqi ayi magana” jin ya sakeyin shiru ta sake kashe wayarta shi kuwa tsabar mamakine ya daskarar dashi wannan karon, kenan ta goge lambarsa ma kai ko ta goge ai bazata ce bata gane lambar akai ba shi Ma’u zata ce waye sannan ta kashe masa waya???

 

ASMA’U

Wato  wata irin sabo da shaquwa da ban taba tsammani ba ya ringa shiga tsakanin na da Yusuf. Zuwa yanzu idan muka wuni bamuyi magana ba ji na nakeyi kamar bani da lafiya.

 

Dukda ba wata doguwar magana mukeyi ba amma duk sanda ya kirani seya gaya mun maganar da zatayi Rugurugu da zuciyata ta tsaya mun a zuciya har zuwa sanda zamu sake magana.

 

Aikina kawai nasa a gaba gefe ina kurbar madarar soyayya a ruwan sanyi wadda har yanzu ni ban yarda wai ina son sa bane,kawai ina jin dadin magana dashi na kuma dauke shi kamar wani Aboki ne domin dai so dayane kuma Bashir nayi wa shi.

 

Daren yau ina zaune nayi daidai a qasa ina duba wasu takaddu dana taho dasu daga office, gaba daya na gaji, Allah Allah nake na gama na kwanta na huta ga yara da suka isheni da hayaniya na korasu daki dan gaba daya yanzu kusan rayuwarsu a nan gidan sukeyinta tunda Bashir ya kwanta rashin lafiya suka dawo kwana anan gidan Aliyu ne kadai yake komawa se fa Jafar wata rana idan yaga dama ya bishi su tafi gida.

 

Wayata da na saka a chaji ce ta dauki qiwar in tashi na dakko tasaka na barta tayi tayi harta katse dan kanta idan na gama na kira dan nasan baze wuce Yusuf ba ko sabon Mayen daya maqalemun Hayatuddeen.

 

Jin ana ta kira ba qaqqautawa ya sakani jan tsaki na miqe na jawota, lambar Bashir ce, na tsurawa wayar ido ina so na gano dalilin da ze saka Bashir kirana a waya yanzu to qila yace Yayansa su tafi gida ko amma me yasa baze kira Aliyu ba tunda yana da waya ko Amna se ni ze kira?

 

Ina wannan tunanin har kiran ya sake katsewa wani ya shigo sena daga na saka a kunnena tareda yin sallama. Shiru naji anyi, na cireta na duba dan na tabbatar ko kiran katsewa yayi amma naga sakannin suna tafiya na sake maimaita sallama naji ba’a amsa ba se kawai naja tsaki na kashe.

 

Ta yuwu ma bani ze kira ba ko kuma besan kiran ya taho bama gaba daya ina qoqarin ajiyewa se ji nayi ta sake daukar qara alamar shigowar wani kiran hakan ya tabbatar mun da yana sane kenan wulaqancin nasa ne ya motsa dan haka na gyara zama tare da dagawa nace

 

“Wai waye ne yake kira ana magana kuma anyi shiru? Idan baka da abin fada ni ina da aikin yi” na sake kashe wayar.

 

To haka kawai ze ringa kirana yamun shiru me zan masa, ni kadai nayita mita ina ci gaba da duba takadduna can jimawa se shigowar saqo naji nayi banza da wayar ban tashi dubawa ba seda na gama abinda nakeyi kaf na je kwanciya dan har na manta ma seda na janyo ta zan saita Alam kafin naga saqon akan wayar se na bude na fara karantawa kamar haka.

 

“Zuwa ga Ma’una. Nasan ni mai laifi ne a gareki kuma na karbi kuskurena da hannu biyu sannan a shirye nake da karbar ko wanne irin hukunci daga gareki in har hakan ze saka ki huce daga abinda ya faru.

Kiyi haquri mu komawa kyakykyawar rayuwar da muka faro ko dan saboda so da qaunar da yake tsakanin mu.

Bashir”.

 

Dogon tsaki naja bayan dana gama karanta saqon nasa nan take na goge. Ashe ma nayi haquri ne mu komawa rayuwar mu, juyawa nayi na kwanta ina rufe idona na tashi na zauna ina sake tuna dalilin daya saka Bashir yimun sakin wulaqanci.

 

Akan Mace fa, me daura zani da dan kwali Macen ma yarinyar dana raina da hannuna harta zama abin sha’awar daya gani ya aura ya hadamu zaman kishi da ita a saboda ita ya kassaramun rayuwa ya hadani da zawarci shine yanzu saboda tsabar rashin kunya ze turo mun wannan saqon yana tunanin wannan ya isa ya wanke tarin laifin sa a gurina kenan? Lallai ba shakka ya dauke ni sakarya.

 

Baccina na kwanta, washe gari da wuri muka fita tun a hanya kuwa na kaftawa yaran warning akan kan kar wanda ya sake zuwa ya kwanar mun a gida kowa ya zauna a gidan ubansa. Idan taqamarsa su to yanzu na rigada na saki zuciyata ko da su ko babu su a tare dani babu abinda ze chanza daga walwalata. Na barsu a hannun ubangiji nasan ze kulamun dasu.

 

Sau kusan hudu ina ganin missed calls dinsa a office dinma amma naqi dagawa to me ze gayamun wai? Ko kuwa ni din an gaya masa sakarya ce da zezo yana wani kirana a waya kuma na kulashi.

 

“Ko dan darajar so ai zaki iya saurar sa Ma’u” wata zuciya ta raya mun se gashi yau nida kaina na qundumawa wannan zuciya tawa me qoqarin tsayawa Bashir zagi, ban haqura ba na janyo wayata na goge lambarsa daga ciki sannan na dora layin akan tsarin da kiran baquwar lamba baze shiga ba sedai naga missed call ni na kira dan idan ma nayi blocking nasa ze iya chanza lamba ya kira amma yanzu kuwa koda ace ze sake lamba dari bazata taba shigowa ba.

 

Ina shirin tashi Yusuf ya kirani. Duk wunin ranar bamuyi waya ba saboda ya gaya mun tun daran jiya daman yana da Meeting se sanda ya samu sarari ze kira shine se yanzu.

 

“Nayi fushi” ya fada bayan da muka gaisa.

“Me kuma ya faru? Kai da waye zakayi fushi?” Na tambaye shi dai dai sanda na shiga motata.

 

“Badai se yanzu kike tashi daga aiki ba?” Yusuf ya tambayeni sanda yaji na kunna motar, seda na mayar da wayar jikin sipikar motar kafin na amsa shi da cewa

 

“Wallahi se yanzu, kwana biyun nan ayyuka ne suke yi mun yawa shiyasa nake dadewa a office”

 

“Gaskiya aikin nan yana wahalamun da mata ya kamata na dauki mataki akan sa fa, ko dai a rage yawansa ko kuma suyi asarar haziqar ma’aikaciya wadda mayar da kamarta se an duba”.

 

Murmushi nayi ina ci gaba da tuqina nace

 

“Naji kace kayi fushi, me akayi maka ne?”

 

“Oh tambaya ma kikeyi? Kece mana. Gaba daya yau ko kirana bakiyi kinji ya nake ba ko da yake daman ai baki damu dani ba, ni kadai nake damuwa dake idan banji lafiyarki ba amma ke nasan ma mantawa kikeyi dani idan ban kira ba”.

 

Yanda yayi maganar ne ya bani dariya har seda na dara kafin bace

 

“Haba dai waya gaya maka ban damu dakai ba?”

“Ni na ga haka da kaina amma ki fada naji idan kin damu dani din”

 

“Na damu da kai mana ko ban fada maka ba kaina ai ka sani” na sake fada. Seda yaja wani murmushi kafin yace

 

“Na dai jiki kawai amma ni banga haka ba. Kinga ni ina sonki amma nasan ke duk duniya ma baki da maqiyin daya kaini yanzu”.

 

“Haba wacce irin magana ce wannan Yusuf? Taya zaka ce bani da maqiyi kamar ka yaushe na gaya maka haka?”

 

“To idan ba gaskiya bane ki fada da bakinki cewar kina sona mana sena yarda” ya sake fada yana yin qasa da murya kamar me rada. Ba tare da tunanin komai ba nace

 

“Ina sonka mana Yusuf kaifa dan uwa…..”

 

“Karki qara komai kin rigada kin gama magana ai tunda har kika furta kina sona da bakin ki yanzu zan kira Alhaji Qarami na gaya masa. Daman yace na nemi soyayyarki shi kuma ze tsaya mun da izinin Allah a wannan karon sena sameki Asmyta” Yusuf ya katse ni ciki tsananin murnar da muryarsa ta kasa boyewa.

 

Be barni nayi magana ba ya kashe wayar, mamaki da dariya suka kamani duka lokaci daya. Wai da girmana da komai Yusuf yayi mun wayo dukda ni bada wata manufa na fadi Ina son sa ba kawai dai na fada hakan ne jin yanda yayi magana bawai dan har cikin zuciyata abin da yake raina kenan ba.

 

Tuqina naci gaba dayi hankali kwance harna isa gida. A bakin qofa na tarar da Bashir a tsaye ya harde hannaye da alama ni yake jira, na gama daidaita fakin kafin na fito fuskata a sake na shiga gaishe shi ina qare masa kallo yanda naga gaba daya ya zabge yayi baqi kamar wnada yayi jinyar shekara daya.

 

“Bari na shiga sena turo maka yaran seda fa na gaya musu su ringa zama a gidan ubansu amma saboda rashin ji irin nasu shine suka taho Yi haquri yanzu dana shiga zan tattaro maka su kuwa” na fada ina qoqarin wuce shi na shiga gida seya dakatar dani da cewa

 

“Ba gurinsu nazo ba Ma’u gurinki nazo ina so muyi magana”.

 

“Toh gurina kuma?” Na fada ina kallonsa da mamaki, be amsani ba na ci gaba da magana ina cewa

 

“Kaga yanzu na dawo ko sallar magriba banyi ba ga gajiya na kwaso, idan ba abin sauri bane ka bari ko zuwa gobe Juma’a da wuri zan taso ko kuma Weekend ma kawai kaga ina gida se muyi maganar”

 

“Maganar sauri ce Ma’u, na kiraki a waya ma bata shiga na tura miki da saqo duk babu amsa” ya fada yana tsatstsareni da ido. Ko a jikina, gaba na sakeyi ina cewa

 

“Koh? Qilan saboda idan banyi saving lambar ba kira baya shigowa ne, to tunda kace abin sauri ne bari idan na dan huta zan aiko yara se su gaya maka” na fada ina tura qofa na barshi a tsaye.

 

Har qarfe tara na gama cin abinci kenan sega Abdallah wai Abbi yace yana jirana. Da mamaki na kalle shi nace ina Abbin yake dan nifa shaf na manta da mun hadu da wani Bashir ma har munyi magana ban qarasa cika da mamaki ba seda Abdallan yace mun wai ai yana qofar gida tun dazu ya saka kujera ya zauna.

 

 

Haka na saka dogon hijabi ba na fita saboda dai wulaqanci babu kyau. Yana nan zaune kamar wani sabon Almajiri na zauna a Empty kujera dana tarar ina cewa

 

“Kasan shaf na manta ma da munyi magana, koda yake ban zata zama kayi ba tunda nace idan na gama zan aiko yara su kiraka ai”.

 

Zamowa qasa naga Bashir yayi kamar wanda yaje neman gafara a gaban Dada ya kama qafata na janye ya riqe qasan hijabina yana cewa

 

“Ma’u haquri nazo baki akan abinda ya faru tsakanin mu. Wallahi nayi nadama, sharrin shaidan ne ya angizani kuma na gane kurena na yarda idan babu ke a tare dani rayuwa ta bazata taba cika ba. Dan Allah ki yafe mun ki Yi haquri mu koma wa auran mu nayi miki alqawari baza kiyi nadamar komawa zama dani da dan nasan kina sona nima ina sonki zamu ci gaba da zaman mu cikin aminci kamar yanda muka faro shi”.

 

Ido kawai na saka masa ina kallon wannan wasan kwaikwayo har ya kai qarshe kafin na miqe ina cewa

 

“Ka tashi dan Allah ko da yake kai naga baka tsoron kaga hotonka a Ticktock yanzu idan ba haka ba meye na durqusa mun. Asma’u ce fa Bashir daka danqara mun har saki biyu saboda matar so ka kuma bani rana daya tak dana tattara inawa inawa na bar maka gida har ka manta wannan shine zaka zo kana durqusa mun wai nayi haquri na komawa auranka?

 

To bari kaji, shi son da kake iqirarin a koma Saboda darajar sa daga sanda ka tsinke igiyoyin auran nan suka tattaro Son gaba daya sukayi awon gaba dashi, dama ai saboda auran ne ko tunda babu shi kaga babu sauran wani so tsakani na dakai, ko da kaga ina gaisuwar mutunci dakai darajar zuri’ar da take tsakanina dakai ne amma badan haka ba kai Bashir baka isheni ni Asma’u kallo ba ka sani.

 

Ada tabbas na So ka amma a lokacin da bansan menene So ba ba ayanzu da na hadu da limamin So ya fayyace mun shi na gane ma’anarsa ba. Dan haka idan kana mafarkin ni zan komawa auranka to ka tashi dan kuwa tamkar a baka tsinke a ce ka zunguro sama ne kaga kuwa wannan abu ne da baze taba yuwu ba kayi sake Bashir nayi maka nisan da har abada bazaka tarar dani ba”

 

ina gama fadar haka nayi shigewata gida na barshi a tsaye zuciyata kuwa yanda take bugawa ina tsammanin wanda yake tsaye kusa da ni ma ze iyajin bugunta.

 

A karanta da haquri, wani qundumemen uzuri ne ya taso mun beyond my control

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment