Littafan Hausa Novels

Wata Hanya Hausa Novel Complete

Maganin Karfin Maza
Written by Hausa_Novels

Wata Hanya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

*WATA HANYA*

 

1

 

Ayeesha Abdulkareem

*(Indo ce..)*

 

 

ELEGANT ONLINE WRITER’S.

 

Bismillahir-rahmanir-rahim.

 

 

 

 

Fatima ce ta kalli Shukriya gami da cewa “Yau kuma me ki ka zo mana da shi?”

cike da rawar kai da gigi ta ce “DOUBLE TWO STAR”

Fatima ta mai-maita cikin sigar tambaya. Shukriya ta ce “Mamaki ki ke?”

Fatima ta ce “Tarar Aradu da kanki ne yake bani dariya, in banda abinki meye garin-gaɗinki da Double Two Star? to ma wane labari za ki kawo akai?”

Dole Ki So Ni Hausa Novel Complete

murguɗa baki ta yi gami da cewa “Ina ruwanki? ki bari na gabatar da ke sai ki fara yi min tambayoyi, ba dan ke zan yi labarina ba kuma na makara yau dan haka in kin shirya saurara ki yi min shiru”

Fatima ta ce “Allah ya shirya ki”

gyara zama ta yi sannan ta fara da cewa “Assalamu’alaikum Barkanmu da Safiya, ina fatan kowa da kowa ya na lafiya, ni ce HAUWA’U IBRAHIM wadda ku ka fi sani da SHUKRIYA, aikina shine kawo muku labarai masu sanya nishaɗi daga wannan gidan Radio namu me Albarka, to yau na zo muku da magana akan wannan cibiyar kasuwancin ta DOUBLE TWO STAR tambaya ɗaya zan yi zuwa biyu duk wanda ya amsa min ya na da kyauta”

Fatima ta ɗan yi gyaran Murya sannan ta fara cewa “Assalamu-alaikum Masoyanmu, gigi da rawar kai na Abokiyar Aikina Shukriya ya sa ta manta ba ta gabatar da ni ba dan haka zan gabatar da kaina, Sunana Fatima Usman ina tare da ita domin sanya ku nishaɗi, to Malama Shukriya wace tambaya za mu amsa akan Double Two Star?”

murmushi ta yi sannan ta ce “Kowa ya buɗe kunnuwansa, Menene Ma’anar Double Two Star?? wasu sukance ƴan huɗu ne masu wannan kasuwanci wasu kuma sukance ƴan biyu ne wasu su ce mutum ɗaya ne, to menene asalin gaskiyar? duk wanda ya ban amsa ya tabbatar ya bani kyakkyawar hujjar da zan yarda”

Fatima ta ce “Gaskiya Shukriya wannan tambayar taki akwai ruɗani a ciki, amma dai bari mu fara amsa kira”

bayan ta ɗauki kiran sallama mutumin ya yi kafin ya ce “Ina ganin dai Double Two Star ɗinnan yana nufin su huɗu ne”

Shukriya ta ce “Bani hujja, Ka taɓa ganinsu ne su huɗun?”

ya ce “A’a amma dai sunan ya yi kama da hakan”

dariya ta yi kafin ta ce “Madallah da kasancewa tare da mu sai anjima”

kiran da yake shigo ta amsa gami da amsa sallamar da aka yi, ” Ƴan biyu ne domin Kuwa mutane da yawa ma haka suke cewa”

Shukriya cikin fara’a ta ce “Masha Allah, to malam ko zan iya samun hujjarka?”

ya ce “To ni da ban taɓa ganinsu ba ta ya zan tabbatar?”

tuntsirewa ta yi da dariya gami da cewa “Wallahi kuna sa ni nishaɗi, wato ba ka tabbatar ba amma ka faɗa cikin ƙwarin guiwa to muna godiya malam Idris”

Fatima ta ce “Wallahi ku shirya sosai dan yau Shukriya ta yi shirinta, nima nan na kasa gane bakin zaren, to ku ci gaba da dagewa saura mintina goma sha-ɗaya suka rage mu dena karɓar amsoshin nan mu ci gaba da kawo wasu labaran”

 

da kira ya katse da wani ya shigo, duk yadda mutum ya yi ƙoƙarin nuna gaskiyarsa akan abin da ya faɗa sai Shukriya ta ce ya faɗi.

Fatima ce ta ce “To Shukriya tin da duk sun kasa bamu amsa ke sai ki gaya mana meye gaskiyar?”

Dariya ta yi sosai kafin ta ce “Nima ban sani ba na yi tunanin akwai wanda ya sani ne sai ya sanar min”

Fatima ta yi dariya gami da cewa “To masu sauraronmu kun ji dai halin nata yau ma dai kamar ko yaushe ta yi muku tambayar da ita kanta ba ta da amsarta, fatan hakan ya na sa ku nishaɗi sosai da sosai”

 

Fiddausi ce ta ce “Wai Umma ƙa’ida ne sauraron wannan mashiri-riciyar?”

Dariya Umma ta yi gami da cewa “Ke? wallahi ba shiririta take ba ta na sa mu nishaɗi sosai ba ni kaɗai ba ma mutane da yawa a hakan suna sonta kuma suna sauraronta, kin ga da na samu na ɗauki lambar ta-ta na ajiye ai da na kira nima wataran a ji muryata a gidan Radio, bare ace na amsa tambayar dai-dai kin ga ai ba magana”

Ma’aroofa da ta fito daga ɗaki yanzu ta nemi guri ta zauna gami da cewa, “Kuma wallahi nasan amsar kawai nai muku shiru ne, kuma ba zan faɗa muku ba”

da sauri Fiddausi ta ce “Dan Allah Anti ki faɗa mana, haba dan Allah”

“Idan ma na gaya muku amsar da za ta baku itace, kun faɗi, dan haka ba za ku ji a bakina ba”

Umma ta riƙe haɓa gami da cewa “Iyye!!” ci gaba ta yi da cewa “Ku ji min ƴa da sababi? wato aiki a gidan masu kuɗi ya koya miki wani faɗin rai na daban”

murmushin takaici ta yi gami da cewa “Ku ne dai ku ka kaini, yau da wuri zan tafi Fiddausi ki yi sauran aikin gidan”

Umma ta ce “Ai shine ɗan rufin asirin namu, ni dai dan Allah kar ki yi abin da za su koreki ki jaza mana”

miƙewa ta yi ta shige ɗaki gami da cewa “To”

 

09:22pm.

Mommy ce ta ajiye Carbin da ke hannunta sannan ta miƙe, gyara zaman baƙar doguwar rigar da ta ɗora akan atamfar da ke jikinta ta yi sannan ta nufi falon ƙasa.

“Inna!!! Inna!!!!”

kira take ƙwalawa Inna lokacin da take ƙoƙarin zama akan ɗaya daga cikin hamshaƙan kujerun falon.

Cikin Sauri ta fito ta na cewa “Gani nan Ƴata, ina kicin ne”

“Ba kya gajiya da ɗora tukunya da saukewa ne wai?”

“To ai Hajiya gani na yi ba ni da aikin yi shi yasa naje ina yiwa Saurayina girki”

Murmushi Mommy ta yi gami da cewa “Dama kiranki na yi mu yi muhawara”

Inna ta ce “Sun kusa dawowa ne?”

Mommy ta ce “Haka nake gani, waye zai fara shigowa?”

Shiru Inna ta yi ta na nazari na ɗan lokaci sannan ta ce “Fara faɗe”

Mommy ta ce “Um,um”

Inna ta ce “Toh, kawai dai na ce Shahzain”

Mommy ta ce “To mu jira”

Tana rufe baki su ka yi sallama, mutum biyu ne maƙale da juna ɗaya ya ɗafe jikin ɗaya dukansu da kyar suke tafiya, da sauri Inna ta ce “Na faɗi ba dai-dai ba ko?”

Mommy ta ce “Menene hakan kuma?”

ShahZaib ya ce “Bacci ya yi ji shine ya kasa tafiya, kin ga da zanin goyo ma goyashi zan yi”

Mommy ta yi dariya gami da cewa “Allah ka shirya min”

Sallamar da aka yi ce ta katse musu maganar, cikin ƙasaitaccen takunsa na kamala ya ƙaraso fuskar nan tashi a murtuke, mazauni ya yi wa kansa a kusa da Mommy gami da cewa “Sannun Mama”

Murmushi kawai ta yi ba tare da ta amsa ba ta maida hankalinta kan Shahzaib ta na cewa “Shi kuma Shahzain yana ina?”

Shahzain shigowarsa kenan ya yi saurin cewa “Gani ta nan Ummi Ya-Ya ya barni da gyarawa motoci zama ne”

nannauyar ajiyar Zuciya ta sauke tare da furta

“Alhamdulillah” a cikin ranta, gyara zama ta yi kafin ta ce “Ayya! ba rabon wani abu yau, ai kuwa akwai wani abu na musamman da na ajiyewa me bacci sai gashi kuma ya yi bacci ba rabonsa”

kafin ta rufe baki Shahmeer ya dawo kusa da kafaɗarta ya maƙale idanunsa fiƙi fiƙi ya ce “Ai ban kai ga yin baccin ba ko kuma ince har na ma tashi”

Inna ta kwashe da dariya ta na cewa “Allah ya yi miki Albarka kin yi min maganinshi”

Kallo ya ƙare mata kafin ya ce “Baby wai ya akai yau ba ki yi kwalliya ba?”

ta ce “To ai dare ya yi”

ya ce “To na ji, yanzu dai ba wani abu na masoya da ki ka ajiye min?”

za ta yi magana Shahbeer ya katseta da cewa “Na gaji da jin maganar soyayyar nan taku ku yi min shiru”

Shahmeer ya ce “To Almasifatu”

Shahzain ya ce “Ya zageka”

Da sauri Shahmeer ya ce “Rufan asiri me ya kaini? a’a kar ma ka ƙara faɗe”

Mommy ta ce “Ya kamata ku ajiye wannan maganganun ku ci abinci”

kallon-kallo su ka shiga yi wa juna kowa jiran amsar da ɗan-uwansa zai bayar yake.

Shahbeer ne ya miƙe gami da cewa “Ba fa daɗewa mu ka yi da fita ba, sai da safenku, idan kun ci abincin sai ku zo ku kwanta”

miƙewa su ka yi su duka suka mara masa baya.

 

Inna ta ce “Ya tabbata dai ba za su ci ba kenan, ai ko Auta ne ya ce ba ya ci ba lallai su ci bare goga me haɗaɗɗiyar fuska kamar wani bujimin sa”

Mommy ta murmusa gami da cewa “Fuskar ce kawai a haka, a zahirance Shahzaib yafi kowa faɗa a cikinsu shi kawai kwarjini gareshi, yanzu duk ba ma wannan ba Inna, na ga yau kamar ba sa walwala sosai anya kuwa ba wani abin?”

Inna ta ce “Allah ne ya sani, ko za ki tambayo su ne?”

Mommy ta ce “Idan ba su yi niya ba ba za su faɗi komai ba, amma dai mu bari sai gobe”

sashin su Shahbeer.

suna shiga falon Shahmeer Shahzain Shahzaib suka baje akan kujerun falon, Shahbeer kuwa takaici ya hana shi zama.

Shahzain ne ya ce “Amma da wannan tsayuwar kai kawo ɗin ai da zama ka yi ka huta ko ka je ka kwanta”

“Do Allah kar ka ƙara yi min magana yau idan ban tambayeka ba”

jan bakinsa ya yi ya tsuke dan kuwa ba zai iya jayayya da Shahbeer ba.

Shahzaib ne ya yi ƙwafa kafin ya ce “Boss, ka barni da komai a hannuna dan Allah wallahi ɗauka ɗaya zan yi masa haƙuri da shi ba abin da zai amfana mana”

Murmushi Shahbeer ya yi ya ce “Barshi ya jaraba, baisan ba’a taƙun saƙa da ni bane, ba na jin duk abin da yake taƙama da shi, ku barshi ya yi iya yinsa kawai”

Shahmeer ya ce “Boza! wato sunan nashi ma da ka ji kasan ba Albarka a ciki”

Shahbeer ya ce “Surutun ya isa haka, ku zo ku yi bacci”

 

washe-gari.

Momi ce ta yi sallama a falon nasu, Shahzaib ne ya amsa gami da cewa “Ayi haƙuri Umma kin ji mu shiru ko?”

“Shi yasa na zo da Kaina”

ta faɗa tare da yiwa kanta masauki.

gaisheta su ka yi ta amsa cike da so da ƙaunarsu, ci gaba ta yi da cewa “Jiya a kan tsini kake Inya!”

ba tare da ya kalleta ba ya ce “Ummi Jiyan fa ta wuce”

“Amma ai abin da ya faru bai goge daga cikin tunaninku ba, Shahmeer gaya min me ya faru?”

Shahmeer ya ce “Ta yuwu shi da Zuciyarsa su ka yi faɗa dan mu ba mu san abin da ya faru ba”

Za ta yi magana Shahzaib ya ce “Mama Shayi dan Allah”

miƙewa ta yi tare da cewa “To, bari na sa a kawo muku ni zan fita gurin masu jirana”

“a dawo lafiya”

Shahzain ya amsa.

ta na fita Shahzaib ya ce “Mu na bari ta sani shi kenan za ta ƙara ɓata min rai”

Dariya Shameer ya yi ya ce “Ni Shahbeer ne ma ya bani dariya wai jiyan fa ta wuce sai ka ce ba ta sani ba”

Shahzain ya ce “Na rasa ma meke damunta wallahi, lamarin dai sai addu’a kawai”

Sallama aka yi a falon hakan ya sa su ka yi saurin gimtse bakunansu gami da har-haɗe fuska, cikin sanɗa ta ƙaraso dan kuwa mugun shakkarsu take, dire tray ɗin hannunta ta yi a ɗan fizge ta ce “Ina kwana”

Shahzaib ya ce “Auta ana gaisheka ”

Inna ce ta ƙaraso ta na cewa “Ina ruwanki da gaida waɗannan ƴa-ƴan? ki tsaya iya ajiye tray ɗinki sai ki kama hanya ki yi waje”

Shahmeer ya ce “Ya za ki ce haka Baby, yarinya da ƴar tarbiyarta ta gaida mutane sai ki ce haka?, wai ma a ina ki ka samota ne?”

Inna ta ce “Ai gani na yi ba kasafai ake gaisheku ku amsa ba, ka ga da ta gaisheku ku nuna mata ko in kula ta ji ta tsani kanta ai gwara ta yi muku shiru, ka ganta nan sabuwar me aiki aka kawowa Hajiya yanzu ina nunnuna mata abin da ya kamata ne ”

Shahmeer ya ce “Allah sarki, kuma kin ganta dai a haka kamar gaske”

maida kallonsa ya yi kanta gami da cewa “Ke Beauty kalar kyau ya sunanki ?”

jikinta ya gama ɗaukar kakkarwa cikin rawar baki ta ce “Ma’arufa”

ya yi dariya gami da cewa “Inya ka ji wani suna”

kallonsa Shahbeer ya yi ya kauda kai ba tare da ya yi magana ba.

Shahzaib ya ce “Abin da ya shafemu shi muke yi a zaman da mu ka yi nan amma ka biyewa wani shashanci”

kallon Ma’arufa ya yi ya ce “Ke ja saɓa Dallah”

da sauri ta fice har ta na ƙoƙarin yin tuntuɓe.

Inna ma hanyar fita ta nufa tana mita “Ai fa ku ba dama a raɓeku a ji daɗi shi yasa dai nake son masoyina.”

 

 

 

 

MOONASH

Alƙaluma Biyar

daga ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS.

 

Aisha I Yahya (Shaahd)

SARƘAƘIYA

 

Aysha Abdallah (Ayush)

BARRISTER SHAHEEDA

 

Ayeesha Abdulkareem (Indo)

BAYA BA ZANI

 

Maimunat Abdullahi (Maimoon)

BANI DA HUJJA

 

Nazeefa Nashe (Jikar Nashe)

ZUMUNCIN ZAMANI

 

 

Duka waɗannan littafai biyar duk guda ɗaya NAIRA 200 ne kacal, ga me buƙatar VIP NAIRA 300 ba yawa.

dan neman ƙarin bayani ku nemi wannan lambar, 0907 988 5632

 

 

 

Takun ce dai wato *INDO CE..* Wannan karon ma na zo muku da wani ƙayataccen labarin, salonsa daban ne kar ku bari a baku labari, ku biyoni a sannu don jin yadda usulin lamarin yake.

😍

[14/12/2022, 9:44 am] +234 902 685 6699: *WATA HANYA*

 

2

 

Ayeesha Abdulkareem

*(Indo ce..)*

 

 

ELEGANT ONLINE WRITER’S.

 

 

 

Tsaki Shahzaib ya yi ya ce “Allah tsohuwar nan da abin takaici take.”

Shahmeer ya ce “Da alama dai kishi kake malam.”

Shahbeer ne ya katsesu da cewa “Jayayyar taku ta gado za ku fara yi ko?”

shiru su ka yi kowa ya yi ƙas da kai dan yadda ya haɗe rai ƙiris yake jira, dariyar Shahzain ce ta sa Shahmeer ɗagowa yana zabga masa harara, Shaahbeer ya ce “Sai na ce ku ci abincin kuma?”

“Wannan Mutumin fa ya fiye tsayayya”

Shahzain ya faɗa lokacin da ya zame daga kan kujera zuwa kan carpet.

Shahzaib ya ce “Amma ai kai ma ya kamata ka c..

katse shi ya yi da cewa “Double Two Star Rice Company zan je tare da ɗayanku, biyu kuma su je Double Two Star Oil, ina fatan kun gane”

da sauri Shahmeer ya ce “Shi kenan, dama dai in anga zara za a ga wata Dan haka ƙafarka ƙafata.”

Shahzain ya ce “Ba wannan maganar, ban yi niyar zuwa Oil Company ba dan haka sai ka san ƙafar wa za ka kama.”

a tsawace Shahbeer ya ce “Ya isa!!, Maudu’in Muhawara na kawo muku ne?”

Shahmeer ya ce “A’a Wallahi YaYa, kawai dai kasan halin Autoci sai Addu’a.”

ya ce “Shahzaib da wace mota ya kamata mu fita?, Jariri (Shahmeer) saura idan kun tashi fita ku tsaya ja-in-ja akan wanda zai ja motar, idan duk ba za ku iya ba sai ku nemi direba.”

Kallon-Kallo Shahmeer da Shahzain su ka yi, Shahzain ya ce “Ka ga shi kenan an raba gardama.”

Shahmeer kuwa harara kawai yake bin Shahzain da ita.

 

Shukriya ce zaune ta tara littafai kala-kala a gabanta daga ta ɗauki wancan sai ta wurgar ta ɗauki wannan. Mami ce ta shigo ɗakin tare da sallama, da sauri Shukriya ta amsa ta ci gaba da cewa “Mami kaina duk ya ɗau wuta karatu nake yi.”

“Karatu ki ke yi ko kuma hargitsa littafai?”

“Ohh Ai dubawa nake yi, ke dai zauna kawai Mamina.

“Lamarin naki ya fara bani tsoro Shukriya kina zaunenki lafiya me ya haɗaki da ƴan-kasuwa kuma?”

Zaro ido ta yi gami da cewa “Me??”

Mami ta ce “Ba ma ki san kinyi ba ko?, labaran nishaɗi fa kawai ki ke yi da amma sai na ji kin fara sako wasu mutane a cikin lamarinki, Duniya fa a sannu ake binta kar ki je garin ɓarin bakinki ki janyo mana wahala. ”

iska Shukriya ta furzar gami da cewa “Ohh, sai yanzu na gane nufinki Mami, to ai hakan ma yana ɗaya daga cikin nishaɗina.”

“Ba haka bane”

Mami ta faɗa tare da tsareta da ido.

Gyara zama ta yi gami da dai-daita nutsuwarta dan ta lura Mamin ba da wasa ta zo mata ba, cikin nutsuwa da son kwantarwa Mami hankali ta ce “Mami ba komai fa, su fa kawai ƴan-kasuwa ne kuma hakan zai temaka wajen saninsu a Duniya wanda bai sansu ba ma zai sansu kin ga ai banyi laifi ba ko?, ni fa Mami tsakani ga Allah ina son sanin abubuwa da dama akan Double Two Star ɗinnan sai dai bansan ta ina zan fara binciken ba.”

“Hmm ni dai wannan duk ba abin da ya dameni bane kawai fatana ki kula da kanki kar ki shiga rayuwar wanda bai shiga rayuwarki ba.

gyaɗa kai ta yi gami da cewa “To, in sha Allah zan kula.”

 

“Shahzain gaskiya kai ne za ka ja motar.

Shahmeer ya faɗa ya na haɗe fuska alamar da gaske yake.

Shahzain ya ce “Madalla Sannunka, ai kuwa sai dai kowa ya zauna a gida.”

Shahzaib ne ya sosa ƙeya gami da cewa “oh ni ɗannan wallayi ni bacci-bacci ma na ke ji kamar ba zan iya jan mota ba nima”

Shahbeer ne ya shiga rarraba musu Zaratan Idanunsa ya na binsu da kallo me kama da gargaɗi, cikin sauƙi duk suka shiga taitayinsu, miƙewa ya yi ya kwaso makullan motor har guda huɗu ya cillawa kowa ɗaya, a ɗan tsakaice kamar yadda ya saba magana ya ce “Kowa ya ja da kansa, kuma kar wanda ya shige min hanya ko na ganshi ya na bin bayana.”

daga haka ya yi hanyar da za ta sada shi da babban Falo, bin bayansa su ka yi dukansu Shahmeer sai tilliƙa dariya yake.

Inna ce kaɗai a Falon ta na kallo, kusa da ita Shahmeer ya zauna ya na cewa “Sweethear!!”

murmushi ta yi gami da cewa “Angona na kaina an samu fitowa?”

Ya ce “Ƙwarai kuwa Masoyiya yanzu za mu fita don Allah ki kula mana da Mama.”

Ta ce “In Allah ya yarda kuwa, Allah ya tsareku ƴaƴan-nan ku yi ta addu’a dai.”

Shahbeer ya ce “In sha Allah, Ina Mommy take?.”

“Ta na sashinta.

Ba tare da ya ce komai ba ya nufi sashin nata ganin haka ya sa duk su ka bi bayansa, sallama su ka yi mata sannan suka ɗau hanya.

 

“A’ah Sannu da dawowa Ma’arufa yarinyar kirki, dama kuwa jiranki muke ta yi, mun rasa me za mu girka ne ko akwai ƴan canji a gurinki?”

Umma ta faɗa cikin fara’a tana bin hannun Ma’arufa da Kallo.

cike da takaici Ma’arufa ta zauna sannan ta ce “Ai kuwa ba ni da ko sisi.”

Umma ta ce “Innalillahi!! Allah ka rabamu da babun nan, gashi Ma’arufa da ke kaɗai muka dogara Allah gatanmu ke gatanmu, yanzu me za mu ci kenan?”

Ma’arufa ta yi ƙasa da kai Zuciyarta tana ƙuna, ba ƙaramin raɗaɗi take ji ba idan ta ji Umma ta na cewa itace abar dogaronsu, wai sai yaushe za su zama ƴantattun mutane kamar kowa? menene ya jaza musu wannan ƙasƙantacciyar rayuwar?, kafin wannan ma yanzu wace hanya za ta bi wajen samar musu da abin da za su kori yunwar cikinsu?.

“Aunty Yaushe ki ka dawo?”

Fiddausi ce ta jefo mata tambayar bayan ta yi sallama.

“Yanzu na dawo, na yi sa’a Wannan Tsohuwar ta gidan ta bari na tawo da wuri ina ta tunanin ko kun ci abinci ma yau?, sai yanzu kuwa Umma ta ke gaya min ba ku yi girkin ba, don Allah ki je kantin Garo ki ce ya bani rancen kayan abincin zamu biya shi gobe ko jibi ko lokacin da mu ka samu.

“Ba zan yi musu ba dan ba mu da yadda za mu yi sai hakan” Fiddausi ta faɗa tare da juyawa ta nufi hanyar fita.

Umma ta ce “Allah Sarki Ma’arufa da ba ni da ke da ban san yadda zan yi ba.”

miƙewa Ma’arufa ta yi ta shige ɗaki dan kuwa irin Magan-ganun nan na Umma ƙuntata mata suke yi sai ta ji Zuciyarta ta na raya mata abubuwa kala-kala.

 

ɗaya bayan ɗaya su ka yi parking sannan su ka nufi hanyar cikin gida, Shahmeer ne a gaba a cewarsa ya ƙagara ya je ya ga masoyiyarsa, cakk ya tsaya da tafiyar sabi da wani mugun gani da idonsa ya yi, ido suka zubawa Mutumin da ya ke shirin fitowa daga gidan cikin mamaki.

rai a ɓace Shahzaib ya ce “Alhaji Basiru Boza!!! a matsayinwa? da wane nufin ka shiga wannan gidan ?.”

cikin Duniyanci Alhaji Basiru Boza ya ce “A matsayin babban baƙo a wajen Hajiya A’i, Mahaifiyarku itace tai min baki akan wata rana dole sai na zo na nemi temakonku to kuma sai gani yanzu, nasan ba za ku tsaya ku saurareni ba shi yasa na yanke hukuncin haɗuwa da ita, da na yi niya ko a gidana ko a wani guri da bai shafeku ba zan iya haɗuwa da ita amma da na ga abin duk na gida ne sai na ce gwara na yi takakkiya na zo har gidan naku, magana ce me muhimmanci dan haka ku shiga ciki za ta gaya muki.”

daga haka ya raɓe ya wuce ko waiwayensu bai ƙara yi ba.

 

cike da zafin Zuciya Shahzaib ya ce “Kayyasa!! lallai akƙwai baƙin bala’i walla..”

a tsawace Shahzain ya ce “Kulll, kar na ƙara jin kalmar bala’i a bakinka”

Shahzaib ya ce “Amma ai ka ji abin da ya ce ko?, wai har ma tutiya ya ke zai iya haɗuwa da Ita a wani gurin, Mahaifiyarmu ce fa!, wannan fa cin mutunci ne da zubar da kima”

Shahbeer ya ce “Ƙarami, mu je ciki do Allah.”

raɓewa su ka yi gefe shi kuma ya shiga gaba.

 

Mommy ta miƙe kenan da nufin komawa Sama ta ji sallamarsu hakan ya sa ta fasa tafiyar ta na murmushi ta ce, “Sai yanzu ake ganinku?.”

ko kallon inda take Shahbeer bai yi ba, da yake da umarninsa suke aiki su ma ba su saurareta ba suka wuce sashinsu.

Komawa ta yi ta zauna “Yasalam” ta faɗa gami da dafe kai.

Inna ta ce “Tirƙashi, Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke duka, yau gashi kema kin jawo ruwan dafa kanki.”

Rintse ido ta yi da ƙarfi gami da girgiza kai ta ce “Na san dama hakan za ta faru dole, amma me yasa?”

Inna ta ce “Allah dai ya kiyaye na gaba, yau dai kuwa wannan Mutumi ya gama lalata miki farin ciki, amma da bai zo a irin wannan lokacin da ya san za su iya dawowa ba.”

cike da damuwa Mommy ta ce “Inna ki yi shiru Don Allah surutun naki ƙaramin zafin yake.”

Inna ta ce “Na ma yi ai, ni madafa ma zan tafi.”

 

A sashin su.

Shahzain ne ya ce “lallai ashe watan targaɗa duk wani abin da mutumin can yake taƙama da shi ya kama”

Shahmeer ya ce “Wallahi ɗari bisa ɗari ina bayanka, wannan fa babba ƙalubale ne a garemu”

Shahzain ya ce “Shi yasa lamarin yake ɗaure min kai, na rasa wane baƙin tsafin ya yi wa Mommy da har take zama ta saurareshi”

 

Mitar abin da ya faru suke yi cikin ɓacin rai gami da damuwa, Shahbeer kuwa ko uffan bai ce ba.

Shahzain ne ya ce “Inya, (Shahbeer) magana fa muke ta yi amma ka ƙi cewa komai ka biye wa wannan karen.”

Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce “Ta yuwu shi Karen idan nace ya yi shiru ba zai ƙara magana ba.”

Shahmeer ne ya gyara zama kafin ya ce “Ni dama nasan surutan nan namu duk ba wanda ya hau ƙa’ida, faɗa mana me ya kamata mu yi? umarninka kawai mu ke jira.”

shiru ya yi na ɗan Lokaci sannan ya ce “Umma ta na buƙatar Zuwa Saudi Arabia don gudanar da ibada”

murmushin farin ciki ne ya baiyana akan fuskar Shahzaib, ya lumshe idanunsa gami da cewa “Ka yi kyaun kai YaYa, kafin ta dawo mun gama yarfa masa rashin mutunci.”

murmushin gefen baki Shahbeer ya yi kafin ya ce “Cikin hanzari nake son ayi hakan.”

 

 

 

MOONASH.

Daga Ƙungiyar, ELEGANT ONLINE WRITERS.

 

 

BANI DA HUJJA

Maimoon

 

BRR SHAHEEDA

Ayush

 

SARƘAƘIYA

Shaahd

 

ZUMUNCIN ZAMANI

Jikar Nashe

 

 

WATA HANYA

Indo ce..

 

 

*ALBISHIRINKU Masoyanmu, yanzu dukan littafan nan sun dawo kyauta za ku sha karatunsu ba tare da kun biya ko ficika ba, ina fatan hakan zai sa ku farin ciki, Much Lve😘*

 

 

 

 

 

*INDO*

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment