Littafan Hausa Novels

Uwar Ta Gari Ce Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Uwar Ta Gari Ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

UWAR TA GARI CE?*

(MAI TAKEN)( RAYUWAR SA’ID)

 

 

Hafsat Ibrahim waziri

{Ummu Azaan}

Princess ɗin Dashin Allah

 

DASHIN ALLAH WRITER’S ASSOCIATION

 

 

 

Yanda zan fara rubutun nan lafiya, ina rokon Allah dayasa in gamashi lafiya, sannan kuma abinda ke ciki na kuskuren Allah ya yafe mini dana rubuta. wanda na faɗa daidai kuma Allah ubangiji yasa masu karatu su amfana dashi Allah jabu Ameen

 

 

 

PAGE 1

 

 

 

Dasunan Allah mairahama maijin ƙai

 

________Babban gida ne tanka meme, mai ɗauke da ɓangarori daban-daban na sashen mutane goma sha takwas. Gidan babba ne sosai dan ya haɗa ne tun daga kan kakanni, ƴaƴaye da jikoki. Har ma da tattaɓa kunne,

 

 

Kauyen JAMTARI kauyene da kuwa ya sanshi wanda yake yana ɗaya daga cikin ƙanana ƙauyukan da ke cikin Garin Adamawa……

Gidan Malam Abubakar Akawu, tunda daga kwanar da zata sadaka da gidan zakaji hayaniyar daketa faman tashi kasan cewar babban gidane mai dauke da al’ummar Annabi da dama aciki, hakan ne yasa na kasa tantace hidimar aure akeyi a gidan,? Ko dai hidimace irin na yau da kullum?

Karsashi Hausa Novel Complete

Tabbas wannan hidimar.na aure ne dan gashi sai gini akayi a cikin gidan,

 

wani shashi ne dake can bangaren gidan ta karshen, na hango wata Mata wacce bazata wuce shakaru ashirin da biyar a duniya ba, kana nagin ta kaga ba fullatanar jeji, dan ko yanayin shigar tama ya babban ta dana sauran mutanen gidan, fara ce tas saɓanin sauran mutanen gidan da suke bakake sosai, tsaye take a bakin kofar tana, kallon mutanen dake shige da fice daga gidan kallo ɗaya zaka mata ka fahinci cewa tana cikin da Muwa da kewa, tayi nisa sosai atunanin da takeyi, taji yaron da bazai wuce shekaru 3 ba yana faɗin, Nenne Nenne, a hankali ta Juyo da kanta tana kallon shi ta sauke wani buyayyen Ajiyar zuciya Tare Da sake mai Murmushin da ya sake fitar da ainihin kyawun fuskarta, cikin harshen fullancin ta ce” Noi Ahmadu? (Yaya ne Ahmadu) nuna mata ɗaki yayi yana cewa, ɓilgel ɗo woka,( yaro yana kuka) ajiyar zuciya ta sake saukewa a hankali, sannan ta kalli cikin ɗakin nasu, eh kuka sosai jaririn da bazai wuce wata biyu a duniya ba, yake yi yana cilla kafafunsa tare da rufe ido irin yanda jarirai keyi,

 

Shiga cikin dakin tayi tana faɗin waɗu muyal, (yi hakuri) ta karasa ta dauke shi ta zauna tare da fara basa nono, nan take yayi Shuru ya fara sha dama yunwa yake ji, tana zaune tayi shiru.

 

Taji ana sallama Wata ƴar budurwa ce tayi Sallamar hannun ta sauke da kaya ta kalli Nenne, da itama ita take kallo suka sakarwa juna Murmushi, dan shine maganar su saboda acikin su babu mai jin Yaren wani dan haka da sun haɗu da jama’ar gidan Murmushi ne kawai a tsakanin su,…..

 

Karasowa budurwar tayi dukda tasan Nennen ba jinta zatayi ba, ta ce”

Wannan kayan kine shi zakisa gobe a wajen buɗan kan matan yaya, tana gama faɗa ta mike ta fita, nenne dai da kallo ta bita dan bata ma fahimci me take nufi ba, saboda bata jin hausa ko da bani ruwa ne,, Sabilida basu dade da dawowa nan ɗin ba, kuma a iya zaman da sukayi, bai isa ace ta fara jiba,,

 

Tana zaune tana kallon yakan, taji an sake yin sallama, Assalamu alaikum, Wasallam yauwa nastu(yauwa shugo) ta faɗa tana daga kayan daga kan hanya, dan ya zauna

 

Shigowa yayi ya zauna, Ahmadu dake kan gado yana wasa, ne yazo da gudu yana faɗin Baba, ya rungume ɗan matashin Wanda a shekaru bazai haura ashirin da tara zuwa talatin ba, bakine shima waluk tamkar sauran jama’ar dake gidan kallo ɗaya zaka masa ka fahimci shi ba bahaushe bane kuma ba bafulatani bane, Yare ne shi MARGI,

 

Murmushin karfin hali yayi yana kallon matar sa uwar ƴaƴan sa abinda alfaharin sa, wanda yakejin zai iya bada rayuwar sa akan ta, ko ɗan halakcin da mahaifinta ya masa, da yanda ya rikeshi tsakani da Allah har ya zama mutum…

 

To amma taya shi zai fara faɗa mata, wannan maganar ne? na cewa mahaifinsa na kokarin yi masa auren mata uku nan da kwana uku, ajiyar zuciya ya sauke a hankali, yana kallon ta, cikin harshen fullancin ya ce” Hauwa’u Noi( Hauwa’u yaya? ) itama a hankali ta kalli sa ta ce? Wala ko ɗume (babu komai) ta sauke Kai daga nan babu wanda ya sake yin magana a cikin su,… har ya gaji da zama ya fita dan ya kasa gaya mata maganar auren dama shi ya kawo sa, ita dai Hauwa’u batasan hidimar da akeyi a gidan ba, dan tunda suka zo bata sake fita ba, kuma babu wanda yazo dan ya sanar da ita,

 

 

Can kicin gida kuwa hidimar auren Umar akeyi gadan gadan babu kama hannun yaro, ƴan uwa da abukam arziki sai shige da fice akeyi, a kirka wancan a sauke wannan,

Haka suma masu ginin gidan sai aikin ginin sukeyi, babu wasa dan ayi agama da wuri, Sabilida jibi za’a gama komai…

 

 

 

DA DADDARE

 

Hauwa na zaune akan tabarma ita da ƴaƴan ta tana rike da jaririn ta a hannu, tayi shiru tana tunanin rugarsu dan ba karamin kewar ƴau uwan ta takeyi ba, tana cikin tunanin ne

 

Taji jama’a na ayyiriri yiriri, haya niya natashi ko ta ina,… sam itama kam ta saka gane wannan wani irin gida ne, tunda sukazo kullum sai anyi biki ta faɗa a cikin ranta.

 

 

Wata kila su kuma haka sukeyi, ta sake faɗa a fili, Assalamu alaikum , sallar goggo rabi ya dawo da ita daga tunani, ta Juyo tana kallon ta

 

 

cikin harshen fullancin suka gaisa sannan Goggo rabi ta sami waje ta zauna. Shuru tayi na ɗan wasu lokuta dan bata san ta ina zata fara ba, Hauwa’u ce ta ɗan kalle ta cike da jin kunya, ta ce” noi?( Yayi) hmmm Goggo rabi ta sauke ajiyar zuciya, cikin harshen fullanci ta ce” Hauwa’u ina fatan dai kinsan abinda ke faruwa agidan nan ko? Cike da mamaki Nenne ta Kallon ta, tana girgriza kai alamar a’a

Ajiyar zuciya Goggo rabi ta sakeyi tana kallon ta tare da nazarin ta da kyau,

Ta ce” dama bakisan Umar shine zai kara aure ba? A mugun gigice Hauwa’u ta ɗago kai tana kallon Goggo rabi, da itama ɗin take kallo, a hankali Nenne ta sauke kanta kasa, maganar ƴar Uwar ta, A’i na sake dawo mata, nan take idon ta ya ciko da hawaye, shikenan hamma ya dawo cikin ƴau uwan sa zai manta da ita,

mai gida ba cefe Goggo rabi ta faɗa tana mikawa Nenne hannu ta bata Sa’id, Babu musu Nenne ta dauke shi ta miqa mata yaron, rawa Goggo rabi tawa yaron kaɗan ta dakata, tana kallon faskar ta, ta dauki lokaci taba kallon nata, kafin ta juya baya ta saki murmushin da ita kadai tasan ma’anar sa, sannan ta Juyo ta fuskanci Hauwa’u, cikin ƙontar da murya ta ce” Kiyi hakuri da abinda zance Hauwa’u, amma maganar gaskiya zan faɗa Miki a wannan gidan kowa baya sonki, duk da abinda kuwa mahaifinki yayi wa Umar, yanzu ma sun barki kina zaune anan ne dan sanadiyar Umar, amma da zarar yayi aure zai manta dake, keda yara ki. Sabilida su yaren basa taɓa auren wani yare sai nasu, kuma ina me tabbatar miki da Yana auren su matan zasu iya kashe ki keda yaran ki ma… ta meke tsaye tare da, dafa kafaɗun ta ta ce” ni tamkar ƴar uwa, nake a wajen ki shi yasa nake faɗa miki, abinda za’ayi gobe kigaya masa cewa kinason ki koma gida idan ya yarda kuka tafi shikenan, idan muku bai yarda ba, ke kice ,zaki koma gida idan yaga kin tafi zai fasa auren su ya biki, kinje? To Goggo yauwa janwala, (Saida safa)

 

Goggo rabi ta fita, ta na fita ta sake wani kayataccen Murmushi, tana faɗin Hauwa’u bazan taɓa bari ki zama ɗaya daga cikin mu ba, sannan wannan dukiyar da kukazo dashi, gaba ɗaya sai ya zama nawa, tana gama faɗin haka ta nufi bangaren ta tana Murmushi.

 

 

 

 

Bayan minti biyar har yanzu Nenne na zaune a inda Goggo rabi ta barta, tana tunanin rayuwar da sukayi a rugarsu da irin sadaukar War da tayi ta aure hamma Umaru wai amma shine yanzu kuma yake kokarin saka mata da sakeyin aure, lumshe idanun ta tayi a hankali ta furta, baffa am,

 

Sallamar Umar ne ya katse ta daga tunanin, tayi saurin share hawayen ta, ta daga kai tana kallon sa, babu ko kiftawa ido..

Shi ko Umar ganin kallon da take mai ne yasashi fahimtar lallai a yanzu tasan komai, jikin sane yayi sanyi sosai har ya rasa abinda zaice, yayi Shuru kawai yana kallon ta, kasa kasa zuciyar sa kuma cike yake da fargaban abinda zai faru….

Hamma yaushe zamu koma wajen su Baffa? Dam kirjin Umar ya buga, me take nufi da yaushe zasu kuma? Ko dai da gaske taji maganar auren da za’a yimai ne?

Saurin kallon ta yayi Cikin ƙontar da murya ya ce” kiyi hakuri Hauwa’u Nima ba’a son raina bane,zanyi wannan auren ba, Zanyi ne kawai dan tilas tawan mahaifi na, wannan al’adar mune dole sai nayi mata uku, dake hutu, na sani Hauwa, ku ba’a muku kishiya to amm…. Shuru yayi dan jin yanda sautin kuka ta ya fara tashi da karfi,

 

Kuka sosai Hauwa tasa, dan Allah ma ya sani tana son sa sosai kuma bazata iya zama da kishiyoyi har hudu, ba dan su a rugarsu can cikin jeje ba’a mata biyu ma, balle har hudu..

 

A hankali ya tako inda take zaune, ya fara rarrashin ta, amma sam taki dena kukan,

Miƙewa tsaye yayi ya kalli Ahmadu dake ƙonce har yayi bacci, barin kaishi ciki, itadai Nenne bata ce komai, ba Ta shunguna itama ta dauki karamin ɗan ta dake kuka, tana jijjaga sa, tana kukan itama.. Umar kuwa yana kai ahmadu dakin ya fito Cikin tausayin ta dayaji yana neman kamashi ya fita daga gidan zuciyar sa duk babu daɗi inama ace mahaifinsa zai iya cenza hukuncin na sai ya ƙara aura,…

 

Haka nenne ta Konta zuciyar ta na sake tunano mata maganganun Goggo rabi, dan santa aka faɗa mata tun daga rugarsu, da ta tuna irin wahalar da ita da mahaifin ta suka shi akan sa, zata sake fashewa da kukan tana dana sanin matsawa da tayi na sai sunzo, yaga ƴan uwansa…..

 

 

Washegari da safe kukan Nenne ne ya tashi Umar daya shigo da asuba yana ƙonce yana bacci bude ido yayi ya kalli ta, tana durkushe tana kukan a hankali take finda sautin kukan, tanayi tana jan zuciya

Nenne ya faɗa yana mikewa zaune, Nenne noi? Cikin kukan ta fara magana, mi yiɗi mi hota sare on(inason zan koma gida ne) zabura Umar yayi ya tashi zaune, yana kokarin yi mata magana amma

Tayi saurin cewa hamma Dama an faɗa min tun a gida idan na yarda muka dawo nan Shikenan zaka manta da ni, sannan kayi aure matan ka kuma su kashe Ni nidasu Ahmadu, tana maganar ne tareda fara tattara kayanta dana yaran tana kulle su cikin ɗan kwalin ta. Da jajayen idanun sa wanda a yanzu suka rikede dan tsaban tashin hankali da jin maganar da take ciwa, ya kalle ta cikin harcen fullanci, da Muryar sa mai nuna rauni da tsoro ya kira sunan ta, Hauwa’u, Cak ta tsaya da tattara kayan dan jin muryar da ya kirata dashi, amma bata ɗago kai ta kalle sa ba,

 

 

 

Ganin bata ɗago ba ne yasa shi sake kiran na ta, Hauwa’u, dage jajayen idanun ta itama tayi ta sauke su akanshi, baki ya buɗe Zai mata magana amma kan yayi maganar tayi saurin katsashi da cewa, he’i banni hamma

(ya isa haka hamma ) Ta karashe maganar tana daure ɗankwalin, ta mike ta dauki zanin goyo, ta daura, dan Allah Hauwa’u, kiyi…… a zafafe ta Juyo tamkar zaki cikin daga murya ta ce” ya isa haka, ya isa ta Juyo, ta dauki wandon Ahmadu dake shanye ta nade..

 

 

Umar da mamaki ya hanashi ko mutsawa yana tsaye yana kallon ta wai mesa sameta ne?.., ganin da gaske tafiyar zatayi, dan yaga ta gama tattara komai, yasa shi buɗe baki ciken harshen da takeji kuma take iya magana dashi kuma yasan tabbas zata mahimce maganar da zaice ɗin, ya ce, Hauwa’u a dillan amma a anda a dillata be ɓingel ko gotel, (Hauwa’u zaki tafi amma ki sani bazaki tafi da yaro ko ɗaya ba) da sauri Hauwa’u ta ɗago kai tana kallon sa tamkar idon ta zai faɗi, Batareda tayi magana ba ta nufi gado inda yaran ke konce suna bacci, ta tsaya tana kallon yaran kaunar su na ratsa zuciyar ta tareda ɓargon ta da sassan jikin ta, yana shiga a hankali ta zame ta zauna a ƙasa tana sake ci gaba da kallon nasu, tana kuka kasa kasa, sun dauki lokaci sosai ahaka, kafin ta mike cikin dakiya da nuna halin ko in kula,

 

Ta dauki Sa’idu wanda a yanzu ya farka daga bacci, yana wasa tafara takowa a hankali, har ta karaso daf dashi, ba tare da tunanin komai ba, ta mikamai shi tare da faɗin, Nima mahaifiyar su ce,

 

Dan haka dole Nima inada hakkin tafiya da ɗaya, daga cikin su, damo a jogamo hama , (gashi nan ka rigeshi a wajen ka) shine naka… ta ajjiye mai shi a hannu.

Ta tsunguna ta sauki kullin kayan ta, ta kama hannun Ahmadu, ta juya zata tafi, taji Ahmadun ya fara kuka yana miƙawa baban sa hannu, tare da faɗin Baba yana ƙoƙarin ƙwace hannun sa daga cikin nata dan son zuwa wajen mahaifinsa, amma sam ta ki sakeshi saima jansa da take da karfi, har suka fito tsakiyar gidan, suna fita tsakiyar gidan taga ilahirin jama’ar dake gidan mata manya da yara sun fito suna kallon su, kowa nason yin magana Ammu babu wanda ya iya fullanci, acikin su sai Goggo rabi….

Umar ɗin ma baya jin kowani yare sai fullanci Kasancewar ba’a wajen su ya girma ba, haka dai suna hakura suka tsaya suna kallo

 

Umar kam mamaki ne haɗe da tashin hankali, ya hana shi koda ƙoƙƙaran motsin kirki dan bai taba tunanin Hauwa’u zata iya barin yaro jariri tace zata tafi ba, shifa dama ya gaya hakanne dan yasan bazata iya tafiya ta bar koda Ahmadu ne, balle wannan ɗan yaron ya kalli yaron… innalillahi wa’inna ilaihir’raju’un, kukan da jaririn ya tsilla ne ya dawo dashi daga tunanin,yana kallon yaron daya rufe ido yana kuka sosai tamkar zai shiɗe yana wutsil wutsil da kafafu, da sauri ya fito daga daƙin cikin sarkewar murya yayi saurin kiran sunan ta

 

Hauwa’u a hankali Nenne ta tsaya Cak amma ta kasa juyowa saboda kuka da tausayin ɗanta dazata tafi ta bari a hannun uwar wani na ne neman ɓata mata shiri , takowa Umar yayi har inda take tsaye itada Ahmadu, cikin sanyin muryar sa, ya ce” Hauwa’u ki tafi da wannan yaron ya nuna mata Sa’idu da yanzu yayi Shuru ya koma bacci,……………..

Shuru tayi tana kallon fuskan ɗanta datakejin sonshi, sosai a ranta, sannan ta sake daga kanta taga duk ilahirin jama’ar gidan Abubakar Akawu, suna tsaye sunyi cirko cirko suna kallon su, wasu jikinsu yayi sanyi sosai da lamarin, dan koda basujiba sun fahimta, wasu kuma dadi tamkar su zuba ruwa a kasa susha, dan dama su basason wani dan kabilar da ba nasuba ya shigo cikin su,, idon tane ya sauka kan Goggo rabi da dama Allah Allah take su haɗa ido, tayi saurin girgiza mata kai alamar a’a,

Batare da ta basa amsar maganar ba ta sake kama hannun Ahmadu suka fice daga gidan,suna fita kofar gidan

 

Ta zube a ƙasa tana wani irin kuka mai gigita ƙwaƙwalwar mai sauraro, dan tunda taga Umar bai dakatar da itaba, tasan ya zaɓi zama da en uwan sane akanta kamar yadda Goggo rabin ta faɗa mata, shikenan yanzu ta rabu da yaron ta? taya ne ma ita zata tafi ta bar ɗanta? , yanda take kuka haka shima Ahmadu ke kukan yana kiran sunan, baba baba, take da ɓingel Amin ( yaron mu? yana nuna makeken gidan nasu da hannun….

 

 

Umar kuwa har yanzu yana rike da jaririn cike da ɓacin rai da ɗimuwa, har yanzu bai kauda kanshi daga kallon hanyar da tabiba, yanason Hauwa’u amma bazai iya bajirewa mahaifinsa ba, kasan cewar yanda suka dade basa tare da juna, sannan ji yakeyi tamkar baiyiwa, mahaifin matar sa wato surukinsa malam Jalo adalci ba kuma yasan bazai taɓa yafe masa akan abinda yama ƴar saba,..,..,..,..

 

A hankali ya juya tare da share hawayen sa yana sake riƙe yaron da kyau, ya fita daga cikin gidan, zuciyarsa a cunkushe, tunani yanda zai yi da rayuwar shi، dana ahmabun shine abinda ya bijire masa yanzu, amma dai babu komai abunma yazo gidan sauki tunda, gobe za’ayi daurin aure zai mayar da yaron wajen matan sa, su ci gaba da kula dashi.

 

A can jefen gefen gidan na su inda mahaifinsa yasa ake masa ginin gidan sa inda matan sa zasu zauna.. yaje ya zauna kasan cewar da safe ne duk mazajen dake gidan sun tafi wajen sana’a wasu kuma suna gona babu kowa, hakan ne ya basa damar zama yasan babu mai takura masa. Ya ƙontar da ɗan jaririn yaron daketa faman wasa yana tsotsar fararen yatsun hannun sa, wanda yayi gadonsu wajen mahaifiyar sa,

 

tagumi Umar yayi yana tunanin rayuwar sa na shekarun baya dasuka wuce,,

*Mu koma shekarun baya da suka wuce*..

 

 

To Allah alhamdulilah

UWAR TA GARI CE???

 

 

 

 

Zamu gane hakan nan gaba, in sha Allahu, Wannan littafin dai akwai abinyi acikin shi, mahaifiya ta tafi ta bar ɗanta wata biyu akan za’a mata kishiya. Allah Sarki yaro rayuwa babu uwa ba abu bane mai sauki ba,

 

To mabiya kumuje zuwa, Danjin ya yaruwar SA’IDU zai kasan ce babu uwa,

TAKU HAR ABADA UMMU AZAAN

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment