Littafan Hausa Novels

Things Fall Apart Fassarar Hausa na Chinua Achebe

Written by Hausa_Novels

Things Fall Apart Fassarar Hausa na Chinua Achebe

 

 

 

 

 

 

 

 

BANGO YA TSAGE

Fassarar littafin Things Fall Apart na Chinua Achebe

Daga Ibrahim Sheme

 

#tsakure

 

BABI NA UKU

 

Okonkwo bai samu irin gatan da sa’o’in sa da dama suka samu ba lokacin da ya ke matashi. Bai gaji rumbu cike da amfanin gona ba daga wajen mahaifin sa. Babu ma rumbun da zai gada. Akwai labarin da ake bayarwa a Umuofia na yadda baban sa, Unoka, ya taɓa zuwa wajen Gijin Tsaunuka da Koguna domin ya tambaye shi abin da ya sa a ko yaushe ba ya samun amfanin gona sosai a ƙarshen damina.

Abban Sojoji Hausa Novels Complete

Sunan gijin shi ne Agbala, kuma mutane kan zo takanas-ta-Kano daga nesa domin su gana da shi. Su kan zo idan wani tsautsayi ya auka masu ko idan sun samu saɓani da maƙwabtan su. Su kan zo domin a duba masu yadda rayuwa za ta kasance masu ko kuma don a tuntuɓar masu ruhin iyayen su da suka mutu.

 

Hanyar shiga gidan gijin wani zagayayyen rami ne da ke jikin wani tsauni, wanda faɗin sa da kaɗan ya ɗara na ƙofar akurkin kaji. Masu zuwa bauta da masu zuwa neman sani daga wajen wannan abin bautar su kan ja cikin su ta wannan ramin har sai sun gan su a cikin wani wuri mai duhu mara iyaka inda a nan Agbala yake. Babu wanda ya taɓa ganin Agbala sai wata jakadiyar sa. Amma ba wanda ya taɓa jan ciki zuwa cikin wannan wuri mai ban-tsoro ba tare da ya fito cike da tsoron irin ƙarfin ikon sa ba. Jakadiyar sa kan tsaya a gaban wata wuta mai tsarki wadda ta hura a tsakiyar kogon, tana bayyana saƙon ubangijin ta. Wutar ba ta ci balbal. Itatuwan da aka hura ne ke haskaka ɗan jikin jakadiyar da ake iya gani.

 

Wata sa’a mutum kan zo ne domin ya tuntuɓi ruhin tsohon sa ko ɗan’uwan sa da ya mutu. An ce idan irin wannan ruhin ya bayyana, mutum zai iya ganin sa ne dishi-dishi, amma ba zai taɓa jin muryar sa ba. Wasu mutanen ma sun ce su kan ji ruhin na tashi sama tare da kaɗa fukafukan su a kan rufin kogon dutsen.

 

Shekaru da yawa da suka gabata lokacin da Okonkwo yana ƙaramin yaro, mahaifin sa Unoka ya taɓa zuwa don ya tuntuɓi Agbala. Jakadiyar a wancan lokacin wata mata ce wai ita Chika. Tana cike da ƙarfin ikon iskan ta, kuma ana matuƙar tsoron ta. Unoka ya tsaya a gaban ta ya shiga ba ta labarin sa.

 

“Kowace shekara,” inji shi a cikin damuwa, “kafin in dasa kowace irin shuka a cikin ƙasa, sai na yi yankan zakara ga Ani, mamallakin dukkan ƙasar nan. Dokar iyayen mu kenan. Haka kuma ina yanka zakara a wajen bautar Ifejioku, gijin doya. Sai in share gona in ƙone ta idan ta bushe. Na kan shuka irin doyar da zarar an yi ruwan fari, sannan in kakkafa masu itace da zarar sun fara tofo. Sai in shiga noma -”

 

“Tsaya haka nan!” jakadiyar ta yi masa tsawa, muryar ta mai tsoratarwa, sa’ilin ta yi amsa-kuwwa a wurin nan mai duhu. “Ba ka yi laifi ga iskokai ko babannin ka ba. Kuma duk mutumin da ke zaune lafiya da iskan sa da babannin sa, to kyawun noman sa ya danganta da ƙarfin hannun sa. Kai, Unoka, duk karkarar nan kowa ya san rashin ƙarfin addar ka da fartanyar ka. Idan maƙwaftan ka sun fita zuwa saran sabon daji, kai sai ka riƙa shuka doyar ka a gonakin da sun gaji, kuma ba su ba da wata wahalar sharewa. Sukan haye rafi bakwai su je su yi gona; kai kuwa sai ka toge a gida kana yi wa ƙasa yankan da ba ta karɓa. Je ka gida ka riƙa yin aiki kamar ɗa namiji.”

 

Unoka mutum ne mara sa’a. Bai mori ‘chi’ ba, wato allan sa na kan sa, don haka rashin sa’a ya yi ta bibiyar sa har zuwa kabarin sa, ko har zuwa mutuwar sa, domin fa bai da kabari. Ya mutu ne sanadiyyar kumbura, wanda hakan mugun abin ƙi ne ga gijiyar ƙasa. Idan mutum ya samu ciwon kumburin ciki da na hannaye da ƙafafu, ba a amincewa ya mutu a cikin gidan sa. A kan ɗauke shi ne a kai shi Mugun Jeji a bar shi a can ya mutu. Akwai labarin wani mutum da ya ja jiki ya dawo gidan sa har sai da aka mayar da shi aka ɗaure shi a jikin bishiya. Wannan ciwon babban abin ƙi ne ga ita ƙasa, saboda haka ba za a binne shi a cikin ta ba. Sai dai ya mutu ya ruɓe a saman ƙasa, kuma ba a yin taron farko ko na biyu na jana’izar sa. Ƙaddarar da ta riski Unoka kenan. Lokacin da suka tafi da shi, sai da ya tafi da sarewar sa.

 

Saboda samun wannan uba irin Unoka da ya yi, Okonkwo bai samu fara rayuwar gata irin ta yawancin matasa ba. Bai yi gadon rumbu ko wani muƙami ba, kai ko ƙaramar mata mai gada ba. Amma fa duk da wannan rashin tagomashin, tun uban sa na da rai ya soma kafa ginshiƙin yin rayuwa mai kyau. Babu hanzari, sannan ga wahala. Amma ya fuskance ta gaba-gaɗi kamar wanda aka yi wa allura. Gaskiya ne cewa allurar da ke jikin sa ita ce fargabar yin rayuwar ƙasƙanci da mutuwa abar kunya irin ta mahaifin sa.

 

*

 

Akwai wani attajiri a ƙauyen su Okonkwo wanda ya mallaki manya-manyan rumbuna guda uku, da mata tara da ‘ya’ya talatin. Sunan sa Nwakibie kuma ya na riƙe da sarautar gargajiya mafi girma ƙwaya ɗaya tilo wadda mutum zai iya samu a karkarar. Wannan mutumin ne Okonkwo ya yi wa aikin da ya samu irin doya na farko da ya dasa.

 

Sai ya kai wa Nwakibie caffa da tukunyar bammi da zakara. Aka kira wasu dattawa maƙwabta, kuma manyan ‘ya’yan Nwakibie maza guda biyu su na wurin a zauren sa. Ya kawo goro da tattasai, waɗanda aka zagaya da su don kowa ya gani, sannan aka dawo masa da su. Ya ɓare shi, yana faɗin: “Duk za mu rayu. Mu na addu’ar samun rayuwa da ‘ya’ya da amfanin gona mai kyau da farin ciki. Za ku samu abu mai kyau da ya dace da ku, kuma ni ma zan samu abu mai kyau da ya dace da ni. A bar shaho ya sauka, ita ma balbela a bari ta sauka. Idan wani ya ce wa ɗayan a’a, to fuffuken sa ya karye.”

 

Bayan an ci goron an gama sai Okonkwo ya ɗauko bammin sa da ke can ƙuryar ɗakin, inda aka je shi, ya kawo shi tsakiyar jama’ar. Sai ya dubi Nwakibie tare da kiran sa “Baban mu”.

 

“Nna ayi,” inji shi. “Na kawo maka wannan ɗan goron. Kamar yadda mutanen mu ke cewa ne, duk wanda ya girmama na gaba da shi, to ya share hanyar samun nasa girman ne. Na zo ne in gabatar da girmamawa ta a gare ka, sannan kuma in miƙa wata buƙata a gare ka. Amma dai mu fara da shan wannan giyar tukuna.”

 

Kowa da kowa ya gode wa Okonkwo sannan ya fito da ƙahon sa na shan giya da ya zo da shi a cikin jakar fatar akuya da ya ratayo. Nwakibie ya sauko da nasa ƙahon wanda ke rataye a jikin rufin ɗakin. Ƙarami daga cikin ‘ya’yan sa, wanda kuma shi ne ya fi kowa yarinta a wurin, ya shiga tsakiyar taron, ya ɗaga tukunyar zuwa kan gwiwar sa ta hagu sannan ya shiga zuba wa mutane giyar. Kofi na farko dai Okonkwo aka miƙa wa, wanda tilas ne ya fara ɗanɗana giyar tasa kafin wani. Daga nan jama’ar suka sha, kuma wanda ya girmi kowa a wurin ne ya fara. Bayan kowa ya sha cikin ƙaho biyu ko uku, sai Nwakibie ya sa aka kira masa matan sa. Wasu daga cikin su ba su nan, sai huɗu kaɗai suka zo.

 

“Shin Anasi ba ta nan ne?” ya tambaye su. Su ka ce tana tafe. Anasi ce uwargidan kuma sauran ba za su iya sha ba kafin ita, saboda haka suka tsaya cirko-cirko suna jira.

 

Anasi mace ce da ta fara manyanta, doguwa kuma ƙaƙƙarfa. Akwai ta da tsare gida, kai da ganin ta ka ga wadda ke mulkin mata a babban gida irin na attajiri. Tana sanye da sarƙoƙin muƙaman mijin ta a ƙafafun ta, waɗanda uwargida kaɗai ce ta isa ta saka su.

 

Ta nufi wajen mijin ta, ta karɓi ƙahon da ke hannun sa. Daga nan ta durƙusa da gwiwa ɗaya, ta ɗan kurɓa kaɗan sannan ta mayar da ƙahon. Ta miƙe, ta kira sunan sa, sannan ta koma ɗakin ta. Sauran matan ma suka sha kamar yadda ta yi, ɗaya bayan ɗaya, sannan suka tafi.

 

Daga nan mazan suka ci gaba da shan giyar su tare da yin hira. Maigida Idigo yana ba da labarin mai ɗebo giya daga daji, wato Obiako, wanda ba zato ba tsammani ya daina sana’ar tasa.

 

“Ruwa ba ya tsami banza,” inji shi, yayin da yake goge kumfar giya daga gashin bakin sa da bayan hannun sa na hagu. “Ruwa bai tsami banza. Kwaɗo ba ya gudu da rana a banza.”

 

“Wasu sun ce wai Boka ne ya gargaɗe shi da cewa zai faɗo daga saman bishiyar kwakwa ya mutu,” inji Akukalia.

 

“Da ma can Obiako wani irin mutum ne,” inji Nwakibie. “Na taɓa ji an ce wai shekaru da yawa da suka gabata, lokacin da uban sa bai daɗe da mutuwa ba, ya je ya tuntuɓi Boka domin ya duba masa. Sai Boka ya ce masa, ‘Tsohon ka da ya mutu yana so ka yi masa yanka da akuya.’ Kun san abin da ya faɗa wa Bokan kuwa? Ya ce, ‘Ka tambayo mini marigayi baba na idan ya taɓa mallakar kaza a lokacin da yake raye’.”

 

Sai kowa ya bushe da dariya ban da Okonkwo, wanda kawai yaƙe ya yi, domin masu iya magana sun ce mai kaza a aljihu ba ya jimirin as. Okonkwo ya tuno ne da nasa uban.

 

A ƙarshe sai matashin da ke raba giyar ya ɗaga ƙahon da ke ɗauke da kingin farin ruwan, ya ce, “Abin da muke ci ya ƙare.”

 

“Ai kuwa mun gani,” inji sauran.

 

“Wa zai shanye kingin?” ya tambaye su.

 

“Duk wanda ke da aiki a gaban sa,” inji Idigo, yana kallon babban ɗan Nwakibie, wato Igwelo, tare da ƙyallin ƙeta a idon sa.

 

Nan take kowa ya amince lallai sai Igwelo ya shanye kingin. Shi kuwa sai ya amshi ƙahon da bai cika ba daga hannun ƙanen sa ya shanye. Kamar yadda Idigo ya ce, Igwelo na da aiki a gaban sa saboda bai fi wata ɗaya ko biyu ba da ya yi auren fari. An ce kingin bammi mai kauri yana taimaka wa mazan da za su shiga wajen matan su.

 

Bayan an ƙare shan bammin sai Okonkwo ya bayyana wa Nwakibie matsalolin da ke damun sa.

 

“Na zo wajen ka neman taimako ne,” inji shi. “Wataƙila za ka iya kintatar ko na menene. Na gama gyara gona amma ba ni da doyar da zan shuka. Na san matsalar mutum ya nemi wani ya amince masa da doyar sa, musamman a wannan zamanin da samari ke tsoron aikin wahala. Ba ni da tsoron aiki. Ƙadangaren da ya faɗo daga kan rimi mai tsawo ya ce zai yabi kan sa idan babu mai yabon sa. Ni na fara neman na kai na ne a shekarun da yawancin mutane ba su daina shan maman uwar su ba. Idan ka ba ni irin doya, ba zan ba ka kunya ba.”

 

Nwakibie ya gyara murya. “Ina jin daɗin ganin matashi kamar ka a irin wannan lokaci da matasan mu duk sun yi taushi. Akwai samari da dama da suka zo waje na da roƙon in ba su doya amma na ƙi saboda na san za su je su turbuɗe ta a ƙasa ne kawai su yi tafiyar su, su bari haki ya kashe ta. Idan na ce masu a’a sai su ɗauka ba ni da kirki ne. Amma ba haka ba ne. Tsuntsu Eneke ya ce tunda dai mutane sun koyi harbi ba tare da kuskurewa ba, to shi ma ya koyi tashi ba tare da ya sauka ba. Na koyi in hana doya ta. Amma zan iya amince maka. Da na kalle ka na san haka. Kamar yadda iyayen mu ke faɗi, Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta. Zan ba ka doya ɗari huɗu sau biyu. Je ka kawai ka gyara gonar ka.”

 

Okonkwo ya fa dinga gode masa, sannan ya tafi gida cike da farin ciki. Ya san cewa Nwakibie ba zai hana shi ba, amma bai yi zaton zai masa alheri irin wannan ba. Bai yi tunanin samun sama da iri guda ɗari huɗu ba. Yanzu dole ya nemi babbar gona. Yana fatan zai samu ƙarin doya ɗari huɗu a wajen ɗaya daga cikin abokan baban sa a ƙauyen Isiuzo.

 

Raba ribar noma hanya ce marasa sauri wajen mutum ya gina nasa rumbun. Duk wahalar da ka yi wa mutum sai ya ba ka kashi ɗaya bisa uku na amfanin da aka samu. Amma duk saurayin da uban sa bai da doya, to bai da wani zaɓin. Kuma wani abu da ya gurɓata lamarin Okonkwo shi ne tilas ya kula da mahaifiyar sa da ƙannen sa mata guda biyu daga ɗan abin da ya ke samu a gonar. Kuma kula da mahaifiyar sa na nufin kula da mahaifin sa. Ba zai yiwu a ce ta dafa abinci ta ci ta bar mijin ta da yunwa ba. Saboda haka tun Okonkwo yana ƙanƙane yake fafutikar mallakar rumbu ta hanyar raba ribar noma kuma yake famar kula da gidan mahaifin sa. Kamar mutum ya riƙa zuba tsaba a buhu mai yawan huji ne. Uwar sa da ƙannen sa na tasu fafutikar bakin gwargwado, amma suna noman kayan abinci na mata ne, kamar su gwaza, wake da rogo. Noman doya kuwa, wadda ita ce sarkin amfanin gona, sai namiji.

 

*

 

Shekarar da Okonkwo ya karɓi irin doya ɗari takwas ita ce shekara mafi muni da za a iya tunawa. Ba abin da ya auku a lokacin da duk ya kamata ya faru; ko dai ya zo da gaggawa ko kuma a makare. Sai ka ce duniyar ta haukace. Ruwan shuka ya zo a makare, kuma da ya zo bai yi wani daɗewa ba. Sai rana mai zafi ta dawo, ta fi kowace da za a iya tunowa zafi, kuma duk ta ƙone shukar da aka yi lokacin ruwan farko. Ƙasa duk ta yi zafi kamar an toya yumɓu, ta ƙone dukkan doyar da aka shuka. Kamar kowane manomin kirki, Okonkwo ya fara shuka ne tun da saukar ruwan farko. Ya shuka iri ɗari huɗu lokacin da ruwan ya ɗauke kuma zafi ya dawo. Ya dinga duba sama wai ko zai ga alamun giza-gizan ruwa, sannan da dare ya kasa barci. Da safe sai ya tafi gonar sa ya ga shuka duk ta langaɓe ta yi yaushi. Ya yi ƙoƙarin kare shukar daga ƙonanniyar ƙasar ta hanyar rufe ta da manyan ganyaye. Amma kafin faɗuwar rana su ma ganyayen duk sai su ƙone su koma ruwan ƙasa. A kullum sai ya sauya su, tare da fatan za a yi ruwan sama da dare. Amma dai haka aka ci da yin fari har makwanni takwas na kasuwa, duk doyar ta mutu.

 

Wasu manoman ba su shuka doyar su ba tukuna. Su ne irin raggayen nan masu ɗage lokacin sharar gonar su har zuwa ƙarshe. A wannan shekarar kuwa su ake wa kallon masu hangen nesa. Sai su riƙa yi wa maƙwabtan su jaje tare da yawan girgiza kai, amma a ran su suna murnar faruwar abin da suke ganin wata dabarar su ce.

 

Okonkwo ya shuke abin da ya rage na daga irin doyar sa lokacin da ruwa ya dawo gadan-gadan. Abu ɗaya ke kwantar masa da zuciya. Doyar da ya shuka kafin farin nan tasa ta kan sa ce, wadda ya samu a ƙarshen daminar bara. Har yanzu yana da ɗari takwas ɗin da ya karɓa daga wajen Nwakibie da kuma ɗari huɗun da ya karɓo a wajen abokin baban sa. Saboda haka zai fara daga farko da ƙarfin sa.

 

Amma daminar bana ta haukace. An ɗibga ruwan shuka fiye da na kowace shekara. Sai a shafe kwana da kwanaki ana sheƙa ruwa kamar da bakin ƙwarya, ruwan yana wanke tulluwar doyar da aka shuka yana kwashe su. Yana tumɓuke itatuwa, yana barin manyan ramuka a ko’ina. Daga nan sai ruwan ya rage ƙarfi. Amma ya ci gaba da zuba har tsawon kwanaki babu ƙaƙƙauwa. Ɗan hasken ranar da ake samu a kowace tsakiyar damina bai zo ba. Shukar doyar ta yi tsanwa shar, amma duk manomi ya san cewa idan babu hasken rana doyar ba za ta yi ƙwaya ba.

 

A wannan shekarar an yi asarar amfanin gona sosai, kai ka ce mutuwa aka yi, domin manoma da dama sun zubar da hawaye yayin da suke tono doyar da duk ta ƙanƙance ta ruɓe. Wani mutum ya ɗaure rigar sa a reshen bishiya ya rataye kan sa.

 

A duk tsawon rayuwar sa idan Okonkwo ya tuno da baƙin cikin wannan shekarar sai ya ji tsigar jikin sa ta tashi. A ko yaushe yana mamaki idan ya tuna daga baya cewa baƙin ciki bai kashe shi ba. Ya san dai cewa shi jajirtacce ne, amma wannan shekarar ta isa ta ragargaza zuciyar zaki.

 

“Tunda dai har na tsallake waccan shekarar,” a ko yaushe ya na faɗi, “to zan kuwa tsallake komai.” Ya kan danganta kasancewar hakan ga irin ƙarfin zuciyar sa.

 

Baban sa, Unoka, wanda a lokacin bai da lafiya, ya faɗa masa a lokacin wannan mugun farin: “Kada ka karaya. Na san ba za ka karaya ba. Kana da zuciyar zaki, mai ji da kan ta. Zuciya mai ji da kan ta ta kan tsallake duk wani shinge da ke gaban ta domin wannan shingen ba ya gaban ta. Ya fi wahala da ban-takaici idan mutum shi kaɗai ne ya gaza.”

 

Haka Unoka ya kasance a ƙarshen rayuwar sa. Tsufa da rashin lafiya sun ƙara sanya shi ya zama mai yawan surutu. Hakan ya kan dugunzuma Okonkwo matuƙar gaske.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment