Littafan Hausa Novels

The Choice I Made Hausa Novels Complete

Written by Hausa_Novels

The Choice I Made Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[29/09, 8:06 am] +234 916 947 2057: 💨 *THE CHOICE I MADE* 💨

By Hafsat Hisham

*(AYSHER ANGEL)*

 

Page 1

Free page

 

Littafin the choice I made na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

 

A hankali take tafiya a harabar asibitin, tana tafiya tana shedding tears, tana goge hawaye wasu sabbi suna zubowa, she can’t stop crying after what doctor ya fad’a mata, kud’ad’e ne masu yawa, wadanda bata dasu, wadanda bata da hanyar samunsu, mahaifinta yana akan gadon asibiti bashi da lafiya rai a hannun Aallah, he’s dying, fara ce sol har yellow skin dinta yake saboda haske, dogowa ce and slim, good looking er kimanin shekaru goma sha bakwai, tana sanye da long hijab har tana sharar kasa, maroon color, yard mara pattern, she look decent, Salmerh Safwan kenan, ta durkushe a karkashin veranda ta dafe kai tana hawaye, tana k’arama a lokacin da abun ya faru, suna dawowa daga kauye suka hadu da en fashi wadanda suka so ketawa mahaifiyarta haddi, mahaifinta ya shiga tsakani saying suyi mashi ko miye amma kadda su tab’a matarshi shine sukayi mashi wannan ta’addancin wanda yake fama dashi for all those years, amma abun bakin ciki shine bayan wata daya da faruwar abun mahaifiyarta ta saka ya saketa akan dole sannan ta tafi ba tareda ta sake waiwayensu ba, abun da sukayi mashi shine yake fama dashi har tsayin wadannan shekaru….

A hankali ta mik’e heading to the get ba tareda tasan inda zata dosa ba, mutum daya ne ya fad’o mata a rai, shine kadai hope dinta a yanzu, ta bude poss dake hannunta naira dari ukku ne a ciki, akwai nisa tsakanin asibitin zuwa GRA amma bata da zab’in da wuce tafiyar kasa, a kafa ta taka daga asibitin har zuwa GRA….

Sword Of Evil Love Hausa Novel Complete

Tayi turus a bakin get din wani katon mansion wanda yake gari guda, ta tsaya tareda goge hawayen dake fuskarta sannan ta danna bell, mai guard ya bud’e kofar dake gefen get yana ganinta ya washe baki saying,

“Salmerhh…”.

Salmerh tayi crossing dinshi ta shiga ciki, ya bita da kallo cike da mamaki saboda ba halinta bane, ta wuce entry na parlor tayi salaam tareda knocking ta murd’a handle tareda tura kofar ta shiga, tayi appearing a wani katon parlour wanda yake dauke da akalla setin expensive kujeru guda shidda, wata kyakykyawar babe ce zaune tana watching series yayinda maids suke kaiwa da komowa….

Salmerh tsaya tsakiyar falon saying,

“Rumana… Ina yaya sadeeq?”.

Rumana ta dubeta da mamaki tace,

“Salmerh… Meyyy ya faru? You look strange…”.

Salmerh ta ware idanu tareda daka mata tsawa tace,

“Rumana… Whether I look fine or strange that’s upto me… Where is he… I said where is he?”.

Rumana tayi baya da sauri sannan ta nuna mata staircase tace,

“In his bedroom…”.

Salmerh ta juya ta heading to the staircase ta wuce upstairs, Momcy ce ta fito daga kitchen saying,

“Rumana kamar muryar Salmerh naji…”.

Rumana tace, “Itace…”.

Momcy tace, “Where is she?”.

Rumana tace, “She asked for yaya sadeeq tana sama…”.

Momcy tayi jim sai kuma ta juya ta koma kitchen ba tareda tace komai ba…

Saida tayi knocking jin shiru ta murd’a handle tareda tura kofar ta shiga da salaam akan bakinta, yana zaune akan sofa da bottle a gabansa, guntun boxer ne kawai a jikinsa, he’s handsome fari good looking and hot, bazai wuce shekaru a shirin da takwas ba, yayi tsawa ba tareda ya kalleta ba, yace,

“Who are you? What the hell bring you here?’.

Salmerh tayi baya da sauri sannan tace,

“Salmerh ce…”.

Da sauri ya juya inda take tareda ware idanu saying,

“Salmerhh ta…”.

Da sauri ta juya baya ganin guntun boxer ne kawai yake sanye dashi, da sauri ya b’oye bottle dake gabansa, ya fiddo dogon trouser ya zura, da wata husky voice mai sanyi yace,

“Salmerh…”.

Sai kuma ya juya yana layi ya shiga bathroom, jim kadan ya fito ya jingina da kofa tareda folding hannuwa saying,

“My Salmerh…”.

Salmerh ta kalli gefe sannan tace,

“abba yana kwance akan gadon asibiti and he’s drying, likita yace kudin da za’ayi mashi aiki dubu dari biyar da hamsin, aikin gaggawa ne domin ceto rayuwarsa, bani da wadannnan kudaden, bani da hanyar da zan samesu…”.

Sadeeq ya katseta saying,

“But kina dani amma I’m willing to do anything for you Salmerh…”.

Salmerhh ta goge hawayen dake fuskarta saying,

“Zaka biya kudaden?”.

Sadeeq yace, “Yes but on one condition…”.

Sai kuma ya k’arasa inda take ya matse mata har tana iya juyo saukar lumfashinsa, tayi baya da sauri, yace,

“But…”.

Salmerh ta fashe da kuka sannan tace,

“Please ka taimaka min ka ranta min daga baya zan biyaka…”.

Sadeeq ya girgiza kai saying,

“Kudade ne masu yawa bazaki iya ba…”.

Salmerhh ta hade hannayenta waje guda alamar roko tana mai zubar da hawaye tace,

“abba yana kwance akan gadon asibiti rai a hannun Aallah, bana son na rasashi…”.

Sadeeq yace, “Speaking of which zan baki kudin amma idan kin yarda zaki aureni…”.

Salmerh ta ware idanu tana kallonshi yayinda gabanta ya yanke ya fadi, wannan shi ake kira ga koshi ga kuma kwanan yunwa, muryar Abba ne take dawo mata tiryan-tiryan kamar a lokacin yake maganar….

“Salmerh koda bayan raina kadda ki kuskuren auren sadeeq, d’an shaye-shaye ne, wannan abu ne da muka sani…”.

Sadeeq yayi mata waving hand ganin ta lula duniyar tunani, tayi firgigit, ya d’aga mata brow saying,

“Hey you have to decide, ina da aiki, you can’t keep me waiting…”.

Salmerh ta fashe da kuka saying,

“Amma nayi wa abba alkawari akan bazan aureka ba, akan bazan auri d’an shaye-shaye ba…”.

Sadeeq yace, “Funny… Ba zaki auri d’an shaye-shaye ba amma kinzo ki amshi kudi daga gareshi… Da alama baki shirya ceton Abbanki ba… Kije zan shirya…”.

Ya juya mata baya yana kokarin zare dogon trouser da ya saka, da karfi tace,

“Wait…”.

Smile ne yayi escaping akan lips dinsa ya juya tareda zuba mata idanu…

Salmerh tayi jim tana tunani, bata da burin auren d’an shaye-shaye, tun tana k’arama ita da Abba suke da burin ta auri miji na gari, idan ta auri sadeeq burinta ya lalace, amma kuma idan bata yarda ba mahaifinta zai iya rasa ranshi wanda yake daidai da tarwatsewar duk wani buri da take dashi tareda rayuwarta….

Sadeeq yace, “I can’t keep waiting sweetheart…”.

Salmerh ta share hawayen dake fuskarta sannan tace,

“Na yarda zan aureka amma I want you to know that na yarda ne saboda bani da zab’i, saboda bani da wata mafitar, saboda bani da yadda zanyi, I can’t watch him dying, he is the only one I have, ya sadaukar da abubuwa da yawa a saboda ni…”.

 

Littafin the choice I made na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

 

*For those of you da zasuyi payment, zaku tura 600 ta wannan account….*

 

*9169472057*

*Aisha*

*OPAY BANK*

 

*Sai a turo evidence of payment via WhatsApp 09169472057…*

 

*Ko kuma Katin MTN via WhatsApp 09169472057…*

 

Hafsat Hisham *(AYSHER ANGEL)*

*THE CHOICE I MADE

By Hafsat Hisham

*(AYSHER ANGEL)*

 

Page 2

Free page

 

Littafin the choice I made na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

 

Sadeeq ya sauke ajiyar zuciya yayinda smile yayi escaping akan lips dinsa yace,

“Good choice, kinyi zabi mai kyau, ki jirani a compound sai inyi dropping dinki a asibitin, muyi magana akan yadda abun zai kasance, kadda ki cewa Momcy komai, nasan abun da zan fad’a mata…”.

Salmerh tace, “I will tell her nothing, ban san susan Abba yana kwance a asibiti…”.

Sadeeq yace, “Sure ranki ya dade…”.

Salmerh tayi crossing dinsa ta wuce bathroom ta kunna tap ta wanke fuskarta tana juyowa taci karo dashi a bayanta, wani mugun kallo tayi mashi, ya matsa da sauri, tana fitowa idanunta suka sauka akan bottle da yayi hiding d’azu, ta maida idanunta akan fridge dake a bedroom din, saida ta kwashe duk wata bottle na giya dake dakin ta bulbule a bathroom tayi flushing, yana ta kallonta tace,

“Kana da magana ne?”.

Da sauri ya girgiza kai saying,

“No…”.

Saida ta buga tsaki sannan ta fita, ta sauka downstairs to the parlour ta wuce Momcy da Rumana dake zaune ta fice….

Momcy ta bi bayanta da kallo cike da mamaki saying,

“Tana nufin bata ganni bane… What wrong with her?”.

Rumana tace, “I don’t know, da na tambayeta tsawa tayi min…”.

Momcy ta maimaita kalmar ‘tsawa’ yayinda mamaki dake akan fuskarta ya k’aru….

Sadeeq ya sauko wearing expensive shadda, with cap tangaram, expensive cuflinks, expensive wristwatch, expensive slippers, ya zauna akan one seater, Momcy tace,

“Abbakhar what wrong with Salmerh, ta fita a fusace, kuma ta ganni amma ko ta tsaya ta gaidani?”.

Sadeeq yayi jim sannan yace,

“Ina ganin wannan yana da alak’a da dalilin zuwanta amma idan na dawo zan fad’a maki, tana jirana zanyi dropping dinta…”.

Momcy tace, “Alright then…”.

Sadeeq ya mik’e ya fice, Rumana tace,

“Momcy kin lura da yanayinsa kuwa, da alama yasha abar”.

Momcy ta dubeta cike da damuwa sannan tace,

“Rumana ya zanyi? Sakacina ne ya jefashi a halin da yake ciki, Salmerh ce wadda nike ganin zata dawo dashi akan hanya tunda yana sonta amma ai kinji abun da mahaifinta yace, waye zai dauki diyarsa ya bawa d’an shaye-shaye, I’m helpless, komi ya faru dashi I’m to blame saboda nice sanadi, tun bayan rasuwar Alhaji nayi sakaci da tarbiyyar Abbakhar, kaicona…”.

******

Sadeeq ya wuce parking lot ya bud’e wata expensive mota kirar Jeep mai tudu ya shiga tareda mata key ya danna horn mai guard ya wangame mashi get ya danna motan waje, tana zaune akan dakalin dake gefen get din tayi tagumi she’s lost in thought, saida ya danna mata horn sau ukku sannan tayi firgigit, ta mike, a sanyaye ta b’alle murfin motar ta shiga, yana driving tana goge hawaye, yace,

“Miye shawararki?”.

Salmerh tayi jim sannan tace,

“Dangin mahaifina suna zaune ne a wani kauye da ake kira da Mahuta, duk lokacin da mukaje maganarsu a kaina daya ce, suna cewa na girma na isa aure amma Abba ya zuba min idanu saboda karatun boko, suna yawan mashi korafi akan yayi min aure, I have an idea, let us do it in this way ta yadda ba zasu zargi wani abu ba tunda basu san da rashin lafiyarsa ba, gobe zaka kaine kauyen akwai Baffana zan ce mashi kaine wanda nike so, na cewa Abba aure nike so amma yace dole karatu zanyi, ni kuma aure nike so, na tabbata idan na fad’a mashi haka zaice ne ka turo magabatanka ya daura mamu aure, ba zasu nemi Abba tunda nice da kaina nace auren nike so…”.

Sadeeq yayi murmushi saying,

“Great idea… Bravo alaiki…”.

Salmerh tayi mashi wani mugun kallo tareda share hawayen dake fuskarta tace,

“Zanyi wa mahaifina karya ne saboda bani da yadda zanyi, saboda bani fatan rasashi, saboda bani da mafita, ina da mahaifiya amma tunda ta tafi bata dawo ba, tana raye ko bata raye ban sani ba, she abandoned us saboda abun da a sanadinta ya faru…”.

Da mamaki take kallonshi ganin yayi parking a wani restaurant, tana mashi magana, yayi banza da ita ya fita jim kadan ya dawo tareda takeaway, bottle of water masu sanyi da drink, ya ajiye mata sannan ya tada motar yana driving a nutse, ba tareda ya kalleta ba yace,

“Eat… Kici…”.

Salmerh ta tab’e baki saying,

“Mukayi da kai… Nace maka ina jin yunwa ne…”.

Sadeeq yayi mata wani mugun kallo da wutsiyar idanu sannan yace,

“Ban san gardama, one word from you idan ba cin abincin bane ba I will kick you out of my car saidai wani ya biya kudin…”.

Salmerh ta dubeshi da sauri, yace,

“Yeah… I mean it… Idan kina ganin wasa nike, try me…”.

Saida tayi mashi mugun kallo sannan ta bud’e takeaway din, babu laifi taci da yawa kasancewar rabonta da abinci har ta manta, bata tabbatar da tana jin yunwa saida ta fara cin abincin, taci da yawa ta kora da ruwa, tarrda dropping mashi drink din, zaiyi magana ta murtuke fuska, yayi murmushi kawai, yana parking a harabar asibitin ta b’alle murfin motar ta fita heading to ward da aka kwantar da Abba, ji tayi yana kiran sunanta, ta tsaya cak tareda juyawa, ya nufo inda take yana walking a nutse, ya mik’a mata waya yace,

“Wayata ce amma chatting kawai nike da ita, ki ajiyeta a wajenki…”.

Saida tayi jim kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa tareda juyawa ta wuce ward da aka kwantar da Abba yayinda Sadeeq ya wuce ofishin likita….

Tana shiga ward din taja kujera ta zauna tayi tagumi tana kallon Abba yayinda hawaye suke zubowa daga idanunta….

Doctor ne ya shigo ya dubashi tareda bata paper tayi signing, Sadeeq ne ya ajiye mata call tayi picking tareda kangawa a kunnenta….

Daga daya bangaren yace,

“Hello…”.

Salmerh ta rumtse idanu saying,

“Yaa sadeeq ka daina cemin hello kayi min salaam… Wa alaikassalaam… Okay then gani nan fitowa… What… Don’t you dare come in… Na fad’a maka… Better…”.

Tayi hanging kiran tareda mikewa ta fita, ta hangoshi jingine da motarsa, tayi taking steps tareda tsayawa gefenshi, yace,

“Yaushe kike ganin zamu tafi?”.

Salmerh tace, “Bayan sallar subh…”.

Sadeeq yayi jim sai kuma yace,

“Uhmm… Alright then, nayi magana da wani friend dina zaiyi jinyarsa…”.

Da sauri ta dubeshi, yayi murmushi tareda mata waving hand, saying,

“Zan aiko driver ya kawo maki dinner, wife…”.

Salmerh tayi mashi kallon tara saura kwata saying,

“Wace matarka? I’m not your wife yet, kuma ka sani zan aureka ne saboda bani da wata mafitar, otherwise saida in mutu babu aure…”.

 

 

Sadeeq yace, “Ehh duk cikin so ne…”.

Salmerh tace, “Shi son da kanshi, yaushe mukayi haka dashi, koda yake clap for him, yayi k’ok’ari…”.

Sadeeq ya turo baki saying,

“Oho dai, tana so tana kaiwa kasuwa…”.

Salmerh tace, “Ko a kasuwa ba za’ayi cinikinka ba…”.

Ya amshi poss dinta ya zaro kudaden da bai san adadinsu ba ya saka a ciki, ya juya tareda b’alle murfin motar, saida taga fitar motarshi sannan ta juya ta koma ciki, taja kujera ta zauna tayi tagumi tana tunanin abun da take shirin aikatawa, she choice she made, ta shiga gallery na wayar da ta bata ta soma cin karo da pics dinsa looking breathtaking and hot 🔥 majority a London ya daukesu, ta soma cin karo da hotunansa tareda *Y’AN MATA* wasu half gown ne a jikinsu, yawanci yayi hugging dinsu ne, ji tayi ranta ya b’aci ta kashe wayar baki daya…

Bayan sallar Isha’i driver ya kawo mata dinner, yana tafiya ta bada abincin sadaka, taci wanda neighbour dinsu suka kawo….

Da daddare ta kasa bacci tana tunanin zab’in da tayi da kuma consequences dake a ciki, yadda taga rana haka taga dare tana tufka da warware amma duk inda taje ta dawo Sadeeq shine mafitarta a yanzu, tana gama sallar subh, Sadeeq ne yazo tareda wani friend dinsa, tana tafiya tana juyowa tana kallon Abba har ta fice, ya bud’e mata bangaren mai zaman hakanan ta zauna sannan ya zagaya bangaren direba, wata expensive shadda ce a jikinsa dinkin tazarce with cap tangaram, ta tab’e baki ta kalli gefe, yace,

“Ya dai… Did I look hot…”.

Salmerh tace, “Ohhh… Ohhh… Ban ganka d’an kunne bane shiyasa nike ta mamaki, ashe kasan daidai…”.

Sadeeq ya girgiza kai tareda ajiye mata warmer tareda flask yace,

“Kiyi breakfast…”.

Salmerh tayi mashi banza, strictly speaking ya kira sunanta, ta turo baki saying,

“Nayi da kaine nace maka ina jin yunwa… Bana son shiga sharu ba shanu…”.

Sadeeq ya shafa beard dinsa saying,

“Salamatu…”.

Salmerh tayi mashi wani mugun kallo, ji take kamar tayi ball dashi, tace,

“Don’t you dare call me with that name, ka kirani da Salmerh ko kuma kayi shiru da bakinka, ai babu dole…”.

Sadeeq yayi murmushi sai kuma ya murtuke fuska yace,

“Salmerh kiyi breakfast, ban san gardama, if you let me utter one word I will kick you out of my car in koma inda na fito…”.

Salmerh ta tab’e baki tace,

“Ashe…”.

Sadeeq yace, “Try it and you will see, kin san k’aramin aikina ne…”.

Saida tayi mashi mugun kallo, tayi kwafa sannan ta bud’e warmer taci ta kora da tea mai kauri, ta goge bakinta da tissue….

A bakin wani katon boutique yayi parking ya b’alle murfin motar ya fita tareda zagayawa bangaren da take ya bud’e, saida ta kalleshi sannan ta fita yayi gaba tabi bayanshi, suka shiga ciki, one hour later suka fito tana sanye da wata expensive gown brown tayi rolling veil, kafarta sanye da stilletoes masu sling back heel, Sadeeq yana jaye da trolley yayinda take turo baki tana mashi wani kallo, ya bud’e mata daya bangaren, saida ta rufe ta bud’e da kanta sannan ta shiga, ya bud’e backseat ya saka trolley din kasancewar buhun nan abinci ne a boot, ya zauna a bangaren direba yaja motar, Salmerh tayi relaxing tareda rufe fuskarta da veil, tace,

“Idan ka kai Batsari kayi min magana…”.

Sadeeq yace, “Alright then… Sweetdreams…”.

Salmerh tayi zuru tana tunani, bacci ne yayi awon gaba da ita….

A hankali ta bude idanunta tace,

“Where are we?”.

Sadeeq yace, “Batsari…”.

Ta janyo veil ta rufe wuyan rigarta tana mai turo baki tace,

“Shine baka tayar dani ba…”.

Sadeeq yace, “Idan na tab’aki cemin zakiyi iskanci, I was thinking of inyi parking idan kika tashi sai mu cigaba da tafiyar…”.

“Idan kuma ban tashi bai sai kayi ta zama har dare…”.

Saida suka k’ara tafiya sannan suka yanki daji, tana nuna mashi hanya har yayi parking, a wani kauye mai yawan albarkatu, yafi kama da rugga, ta fito tareda shigewa ciki….

Sadeeq yayi tsaye yana binta da kallo, wani saurayin bafullatani ne ya mik’a mashi hannu suka gaisa, kallo daya yayi mashi yaga KAMANNI da yake da ita, Salmerh ta ruga da gudu tayi hugging wata mata saying,

“Inna…”.

Inna tace, “Salamatu kece… Sannu da zuwa…”.

Wata babe ce sanye da kayan fulani ta fito daga bukka tace,

“Baddo…”.

Salmerh tace, “Batuul…”.

Sama’ila ne ya shigo yana janye da trolley dinta yace,

“Ke salamatu haka ake shine zaki baro mutum a waje…”.

Inna ta ware idanu sannan tace,

“Dama tare take da bako, ke dai salamatu anyi shashasha…”.

Salmerh ta dafe kai sannan tace,

“Gosh mantawa nayi…”.

Inna ta girgiza kai saying,

“Sama’ila ka kaishi bangarenku…”.

Shigowa aka soma yi da buhun nan abinci, ta ware idanu tana kallon tulin kayan cikin ranta tace,

“Su kuma wadannan in biyashi da mi, koda yake ban sakashi ba…”.

Taja Batuul suka shiga bukka tana janye da trolley….

Inna ce ta shigo ta mik’a mata kwarya saying,

“Gashi ki kai mashi yana bangarensu sama’ila…”.

Salmerh ta amsa ta fice saida tayi salaam sannan ta shiga, yana zaune akan tabarmar kaba, ta ajiye mashi tace,

“Gashi inna tace in kawo maka…”.

Sadeeq yace, “Na gode amma Baddo haka ake sai ki shigo ki kyaleni a waje, kin shanyani saida cousin dinki ya ganni…”.

Salmerh ta maimaita sunan da ya kirata dashi sai kuma ta juya ta fita ba tareda tace dashi komai ba….

Inna tace, “Waye?”.

Salmerh tace, “Saurayina ne…”.

Sai kuma ta wuce bukka, ta rage kayan dake jikinta ta daura zani ta wuce bayi tayi wanka ta fito saida tayi wa trolley din wani mugun kallo sannan ta dauki kayan data cire ta mayar dasu a ciki ta rufe, ta janyo kayan fulani na saki ta saka from head to toe, looking as fulbe girl as she is, looking gorgeous and lovely….

Wani bafullatanin dattijo ne mai dattaku zaune akan tabarmar kaba yayinda Salmerh take durkushe a gabansa, a hankali tace,

“Baffa akan Abba ne, na gabatar mashi da wanda nike so nace mashi aure nike so amma yayi burus dani, yace shi karatu zanyi ni kuma aure nike so, tare dashi muke…”.

Baffa yace, “Shi Safwan ne yayi haka…”.

Daga gani ranshi ya b’aci sosai, yace,

“Tunda har aure kike so ni kuma zanyi maki shi, kije ki turon shi yaron…”.

 

Littafin the choice I made na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

 

*For those of you da zasuyi payment, zaku tura 600 ta wannan account….*

 

*9169472057*

*Aisha*

*OPAY BANK*

 

*Sai a turo evidence of payment via WhatsApp 09169472057…*

 

*Ko kuma Katin MTN via WhatsApp 09169472057…*

 

Hafsat Hisham *(AYSHER ANGEL)*

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment